[Advertisements⬇️]

NI DA YAYA ARMAN - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NI DA YAYA ARMAN

Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

~Marubuciyar~
Komai mukaddari ne
K’addarar soyayya ta
Najmat Abiy
And now
*NI DA YAYA ARMAN*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

*GODIYA* godiya ta tabbata ga Allah (S W T) tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad(S A W) da ahalinsa da sahabbansa ina Godiya Ga Allah (SWT) da ya k’ara bani ikon fara rubuta littafin nan yanda na farashi lafiya ya sa na gama lafiya cikin yarda da amincewarshi.

*GARGAD’i* ban yarda wata ko wani ba su juyamun Littafi ta kowace sigaba muddin Hakan ta faru zan d’auki mummunan mataki.

Littafin nan NI DA YAYA ARMAN k’irk’irarren Labari ne Idan yazo daidai ko yayi shige da labarinki kiyi hakuri arashi ne.

*DEDICATED TO SISTER LEMART L SADEQ*

Y’ar uwa,Masoyiyata,Aminiya,Besty love Bazan tab’a iya misalta soyayyarki a cikin zuciyata ba Allah ya barmu tare my y’ar uwa Rabin jiki littafin nan gabaki d’ayanshi sadaukarwace gareki ki kiyi yanda kikeso dashi 💃💃💃💃

23/May/2022

بسم الله الرحمن الر حىم

*BOOK ONE*📔
🅿️………1&2

“`Kano state“`
~Nasarawa Quaters~

Tsit kakejin unguwar tayi shiru kasancewar ranar da ake gallawa kowa ya na gidajensu Unguwace ta y’an gayu yawaicin masu kudi sunfi zama unguwar gidaje ne na alfarma Chan na Hango wani tafkeken gida mai matuk’ar kyau da tsaruwa da kuma girma na ban mamaki Dan gate din gidan kanshi zai d’auki sama da mota sha biyar gidan gida biyu ne na kusa dashi Shima yana da kyau daidai misali Shima da gate d’inshi amma kuma akwai kofa wacce daga cikin gidan zaka bulla d’ayan gidan ba tare da kasha wahalar zagayawa ba cikin gidan ya hadu komai cikin tsari.

Zaune take ta na guga ta na yi ta na Jan tsaki Inna dake zaune ta na taunar goro ta ce “da yake uban wani ya sanyaki gugar da zaki zauna tun d’azu kina yiwa mutane tsaki aikin b’urut inji tusa” Aira da a cike take daman cike da jaraba ta juyo ta ce “waike inna ina ruwanki dani ne,dandai neman tashin hankali irin naki magana nayi maki ne Dan ayi maki magana ki ce anyi maki Rashin kunya kije ki hada mutum da Abba ni kibarni da gajiya ta ma ta isheni”da ruwana dan ubanki shegiya mai kama da Aljannu figai figai kamar kaza amma sai Rashin arziki cike da ciki” tsaki taja tare da cire gugar ta mik’e tana hada kayan gugar ta ce .

“Kindai kusa mutuwa mu huta ” Inna cike da masifa ta dauki pillow dake kusa da ita ta jefa mata tace “uwarkice Rahama zata mutu Dan ubanki Da gudu Aira ta yi waje ta na Dariya Dan tasan yau ta tabo inna Dan ba abunda ta tsana irin kace za ta mutu.

Ta na fitowa ta na Dariya sai sannan na k’are mata kallo Fara ce Sol farin nata har wani yellow yellow yake doguwace daidai misali sannan bata da k’iba siririyace amma ba Chan ba Dan tsawonta ne ma yasa za akirata da siririya badan haka ba ta na da kibar ta daidai gwargwado,ta na da shape sosai Musamman Hips Dan koya tayi tafiya saisun juya zaka iya kiranta da mai shape din cocacola bata da breast sosai Amma kuma bazaka kirata da kwaila ba Ta na da y’ar doguwar fuska ta na da dogon hanci da kuma k’aramun bakinta da yayi das da kyakyawar fuskarta lips d’inta jawur kamar ta shafa janbaki sanye take cikin wasu English wears Riga da wando ba kallabi kanta bak’in gashinta ne tayi parking Wanda ya dirar mata har gadon baya kyakykyawace sosai ta Bugawa a jarida Saidai daga kaga fuskarta kasan yarinyace girman jikine kawai Allah ya bata amma bazata wuce 17 years ba.

Ta d’ayar kofar ta bi ta shiga cikin gidansu ta na shiga ta Hango Abba akan farar kujera sanye da glass yana karanta jarida kai tsaye wajenshi ta nufa ta na murmushi ta ce ” Abba Sannu da hutawa”Cikin muryar girma da dattako ya d’ago ya Kalleta da murmushi a fuskarsa ya ce “Yawwa y’ar gidan Inna ” sannan ya maida kanshi ga abunda yake hakan yasa ta tafi ta shiga cikin gida.saida na K’are mashi kallo naga kamarshi d’aya da ita sak kawai Haskene ta fishi.

Tana shiga palourn ta tarar da duk y’an gidansu suna zaune yaran na shirin tahfex iyayen kuma na zaune suna hira ta na shiga Mamy ta ce “gwara da Allah ya kawoki yanzu nake. Cewa Aje a kiraki Kuyi shirin Tahfex”Mamy Fara ce itama sosai kamar Aira Saidai basa kama sosai ita Aira ta d’auko farin mahaifiyarta ne Amma sak Kamar Abbanta ta yo.

Turo baki gaba ta yi ta ce Daman banzoba wlh ni na gaji Duka yaushe na dawo daga school bama wannnan ba sanin kanku Waec muke Ni nadauki hutun Tahfex d’innan gsky saimun gama jarabawa” Salati Mamy tayi tace “Aiko baki isa ba wlh ko ki tashi ki shirya ko yanzu nakira Abbanki na fad’a mashi” wara idanu tayi Dan a rayuwa ba Wanda take shakka irin Abba bayason wasa da Ilimi musamman Na Arabi hakan yasata jin Haushi kamar zatayi kuka Mama ce ta ce “Kiyi Sauri Kinga y’an uwanki harsun shirya ai ba a wasa da Ilimi a zamanin nan Daughter bare kuda har kunyi sauka hardace kuke had’ewa kinaga itama harkun tafi Hizif Arba’in ai kamar yaune zakiga kun hade” To Mama bari naje na saka kayan Amma Dan bazan koma ba na tab’o inna tafada ta na Dariya “Murmushi Mama ta yi ta ce ” Ai keda Inna ba a shiga Mamy ko tuni harta tashi ta shiga ciki.

Ta na shiga d’akin ta tarar da Su Amma harsun shirya ta ce “Sister Dan Allah aramun Kayanki insa”tana saka hijab ta ce ” ke ina taki “cikin masifa ta ce ” to ina ruwanki da ina tawa ko Dan nace ki aramun kayan ki shine zaki fad’amun magana “Amma ta ce” To Allah huci zuciyarki kidaga locker ki dauka kinci sa a An goge”Ummy dake gefe ta na chat taja tsaki ta ce “Kede Anyi sokuwa wlh idan nice Saidai ta mutu Amma bazan ba ta ba ta na kanwarki amma duk tabi ta rainaki” Tsaki Aira taja jin Abunda Ummy tace ta ce Ke ina ruwanki shigar shugula kawai ke har kin isa ki shiga tsakanina da Amma kidaina shiga sabgarmu dalla tafada ta na sanya kayan da ta dauko, dariya itama amma tayi ta ce”Ai shine ko ina ruwanta da shiga tsakaninmu” tabe baki ummy dan daman tasan ba a shiga tsakaninsu sanin ta biyewa Aira tsaf zatayi mata Rashin kunya ya sanya Ummy Jan bakinta tayi shiru ta ci gaba da chat d’inta.

Bayan sun dawo da daddare D’akin Inna ta shiga ta na shiga ta fara balbaleta Tayi banza ta kyaleta ganin abun ya fara yawa ya sanyata tashi ta shiga bedroom d’inta ta d’auko wasu manya-Manyan chocolate guda biyu ta kalli inna ta ce “indai kina so in baki to wlh sai kinbar fad’an nan” tuni inna ta fara washe baki ta ce “Ah too Y’ar lele na daman akwai Zumar turawan nan a gidan nan.”

” Dariya Aira tayi tare da mik’a mata tace “Ai fad’an ki yasa bana baki ” amsa inna tayi ta na washe baki ta daga ta fara sha har wani lumshe ido take Aira tayi kasa da murya tace “Ai Hajiya inna sai kinyi shekaru irin na Dabino keda mutuwa ta yi nan kinyi Chan Yanzu Dan Allah My Inna wayarki zaki aromun yanzu zan maido maki ” kai kede Allah yayi miki albarka yarinyar nan Duk a d’iyan Habubakar ke kika fita zakka duk kinfisu hali me kyau bakisan in mutu Sannan ta ciro wayar a d’an tofin ta ta ta mik’a mata ,itadai Aira Dariya kawai take jin yabon da inna ke mata kamar ba itace ta gama balbaleta ba tasan daman tunda ta bata choculate ta kashe bakin.

Itako tashi tayi ta shiga bedroom d’inta ta haye kan Gado tare da Rungume pillow jujjuya nokiar inna tayi tare da dialing number daman tana kanta tana kira taji a kashe ta sake kira yakai goma amma abunda ake cemata kenan kuka ta fashe dashi ta ce “Yaya ina ka shiga tun jiya wayarka kashe na shiga ukku Kardai wani Abu ya sameka, ta jima ta na kuka ta na sabbatu tana kiran number a kashe Dan tab’a saba da missing d’inshi daidai da yini daya ba hakan yasa ta k’ara shiga damuwa da kyal ta samu wajen 1 bacci ya dauketa.

Washegari sukuku ta tashi duk hankalinta ba kwance ba haka dai har taje school tayi jarabawa amma hankalinta ya na wani wajen daban.

©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️

*Government House*

Ko ban fad’a ba kunsadai yanda gov house yake ba sai na bata bakiba wajen fad’an tsaruwarta da kyanta ba duk yanda zan kwatanta kunsan tafi haka.

Yau duk gidan aikace aikace kawai ake da shirye shiryen Abinciccika kala kala Dan tarbar tilon d’an governor mai ci yanzu da zai dawo daga London Mahaifiyarshi Hajiya Fatima yau cikin farinciki take marar musaltuwa Dan sosai tayi missing d’an nata Da misalin k’arfe Shida ya yamma jirginsu ya Sauka a Nigeria Mahaifiyarshi da kanta suka tafi domin tarbarshi .

A hankali yake Saukowa daga matattakalar benen jirgi cikin Tafiyarshi ta k’asaita sanye yake cikin K’anan an kaya da sukayi mugun Karbarshi Fari ne amma ba wai fari Chan ba dogo mai murdaddan jiki yana da saje Wanda shine Babban abunda yake rikita y’an mata lips d’inshi ko har wani ja yake kamar ya shafa wani abu Kyakkyawa ne na Bugawa a jarida daga ganin fatarshi kasan Hutu ya zauna mutum ne Mai ji da gayu Shima kallo d’aya zakayi mashi kasan ya na cikin tsananin farinciki hug din juna sukayi shida mahaifiyarshi cike da son juna da kewar juna suka koma gida suna hirarsu ta y’a da uwa koda suka isa gida baiyi mamakin tarbar da ya samu ba Dan ko da kwana daya ne yayi tafiya haka ake mashi.

Bayan yayi wanka ya sake shiri ya huta mahaifiyarshi da kanta ta dinga feeding d’an nata kamar wani yaro shi kuma sai shagwaba yake mata kamar zaiyi kuka ya ce “Uhm mummy na k’oshi please ki barni haka cikina ya cike”mummy na k’ara d’auko wani spoon din ta ce ” Haba son Bafa kaci da yawa ba nasan a can ba wani cin abinci kake sosaiba ha a d’aga bakin saika cinye na plate d’innan”.

“Murmushi kawai yayi a haka dak’yal har ya ida cinyewa Dan shi ba mutum bane mai fiyason cin abinci ba ya na gamawa ya Mike tare da kallon Mummy ya ce Mummy zan d’an fita please karki hana” Haba son ko fa hutawa bakai ba daga dawowarka ka ce zaka fita “cikin shagwaba ya ce Mummy ba jimawa zanyiba yanzu zan dawo ” To bazaka bari sai ka kara huta wanna”Mummy please” yafada yana hade hannaye,To shikenan Allah ya kiyaye ka kulamun da kanka kuma karka jima”Hug d’inta yayi ya ce “Don’t mention my dear mom saina dawo.

Driver kadai ya tuk’ashi Dan bayason yawo da Security wannan Karin ma yayi kyau sai baza k’amshi yake Dan shigar da yayi ta yanzu ma tafi ta d’azu kyau murmushi kawai yake shi d’aya.

Aira suna zazzaune a palourn inna Ita da su Amma,Haidar sai Ummy duk suna shan labari wajen inna sai kwasar Dariya suke banda Aira da tayi jugum Dan yau ko abincin kirki bataci ba Suka jiyo knocking Haidar ne ya tashi ya je ya bud’e Aira da hankalinta na kan k’ofa ganin mai shigowarne ya sanyata mik’ewa a matuk’ar rud’e ba k’aramun surprise d’inta yayi ba shima tsaye yayi ya na K’are mata kallo sanye take cikin wasu English wears Riga da wando red and black kanta bako kallabi sai gashinta da yake a parke Sosai yaga ta k’ara yimashi kyau da girma A d’an kwanakin da yayi bai ganta ba murmushinshi kawai mai tsada yake sakar mata Ai bata San Lokacin da ta Ruga a guje ba tare da Rungumeshi Farincikin da take ciki tama kasa musaltashi da komai Kuka ta fashe dashi cikin muryar kuka ta ce ……….✍🏿

“`Hmmmm ya kukaji salon Fans kudai muje zuwa ai ba afara komai ba salon na musamman ne Kudai kawai Had’in kanku nake buk’ata ta hanyar comment da zazzafan sharhi ni kuma zan datse damtse wannan Karin ba wasa a zafafe na dawo kamar yanda littafin yake zazzafa Idan Naji comment da sharhi zaku jini idan kuma Naji shiru nima zaku jini shiru ta hanyar yawan comment ne zan gane labarin zai muku dadi ko akasin haka more comment more typing “` 💪🏼🤷🏼‍♀️🙅🏻‍♀️

_*Miss Hajo ce*_
[5/23, 18:16] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………3&4

“My Yaya why did you turn off your phone for two days i could not find you’’ dad dab’a bayanta yafara cikin sigar lallashi ya ce “ I’m sorry my cutie Babe bansan zaki tashi hankalinki haka ba I did this to surprise you shiyasa “sakinshi tayi tare da turo baki ta ce ‘’uhm My Yaya ni nayi fushi ma tunda da gangan kayimun haka ‘’ta turo baki ta koma kan Kujera ta Zauna ta na turo baki ita ala dole anyi mata laifi”Murmushi yayi tare da binta dan yasan ya tab’o y’ar rigimar tashi kamar zaiyi mata rad’a ya ce.

“Sorry my cutie bazan sakeba kinsan fa duk saboda naganki na dawo kiyi hakuri ki janye fushin kinji little sis”Turo baki gaba tayi ta ce “Ni bazan hak’ura ba “kamar zaiyi kuka ya ce “Too na koma chan kenan “juyowa tayi cikin sigar shagwab’a tace “nayi missing din naka shine zakace zaka koma “ta fad’a ta na aika mashi da hararar wasa lakutar kumatunta yayi yace “Nima kewarki ce ta dawo dani I was joking dan ki hakura “To ai nahakura karka sake “murmushinshi mai tsada ya sakar mata ya ce insha Allah bazan sakeba smile mana kinsan kinfi kyau da murmushi “Dariya tayi tare da rufe fuska ta kwance kanta saman kafadarshi sai sannan yayi ajiyar zuciya yace”fatan dai na sameki lfy”gyada mashi kai ta yi tace “Alhmdllh saidai rashin lafiyar kewarka kuma yanzu na warke hope kazo lafiya ya hanya “murmushi yayi yace Nima lfy nadawo sai dai cutar kewarki kuma yanzu na warke ya fada yana shafar kanta ya ce “kinga yanda kika kara girma kuwa cutie Meye sirrin ko dai inna wani abun take baki “.

Dariya tayi tare da rufe fuska tace “Kai yaya ai kaine ma ka kara girma “Tsinkayi murnar inna sukayi “To fa jarabar ta dawo yanzu za a faramun manne manne da tab’e-tab’e a daki ta karasa fada ta na jan tsaki “Dariya duka sukayi Banda Arman da baifiya dariyaba murmusawa kawai yayi ya ce .

“Haba y’ar tsohuwas daga zuwana bako sannu da zuwa bakiyiwa angon naki ba zaki fara halin “tabe baki tayi ta ce “Akai kasuwa indai kaine sannan daka shigo ko gaisheni bakayiba bama ka ganni a wajenba ka tafi wajen fitsararriyar y’ar lelen naka “murmushi yayi yana kallon Aira yanda take aikawa da inna harara yace “afuwan hajjaju Nina isa na kyale uwar gida ran gida Allah huci zuciyarki ran ki ya dad’e kiyi shekaru irin na dabino “lokaci guda inna ta saki rai ta ce “sannu da zuwa Mujahid ya kasar turawan andawo lafiya “lafiya qlau inna fatan kuma mun sameku lafiya “su Amma ne da Haidar suka gaisheshi ya amsa a tak’aice basu damuba saboda daman sunsan duk gidan nan ba wanda yake sakewa ko doguwar magana ta hadasu sai Aira.

Aira ce ta ce “Yaya ka rabu da inna Neman fitina ne kawai irin nata kaga tashi ma mu fita na baka labarin abubuwan da Akayi Baka nan ta fada ta na mikewa tare da kama hannunshi sukayi farfajiyar gidan Sunajin inna na sababi suka kyaleta.

Sun jima a waje suna ta Hira ta bashi labari na dariya yayi itama haka har akai margriba suna nan saida Mummy ta kirashi ya Sanyashi tunawa da ta ce kar ya jima yace mata yanzu zai dawo kallon Aira yayi ya ce “Baby zanwuce Gida Mummy na kirana “nan ta fara shagwaba ita bata gaji da ganinshi ba dakyal ya samu ya lallabata ya tafi gida da niyyar washegari zai dawo yakaita shan ice cream kuma zai taho mata da tsarabarta.

Daren ranar kowannensu Kwanan farinciki yayi Washegari Aira koda ta dawo daga school Lokacin Tahfex nayi langwabewa tayi tace batada lafiya bazataje ba saboda kar Yaya Arman yazo ta tafi.

Da misalin karfe biyar na yamma ya shigo gidan sosai yayi mata kyau cikin riga ash da black din jeans itama tayi kyau cikin atamfarta doguwar riga ta sa malha tayi daurin dankwalinta tare da fito da gashinta baya sosai tayi kyau Arman ko kasa daina kallonta yayi dan ba karamun kyau tayi mashi ba bayan ta shigo gaban Motar ta ce “Yaya na shirya muje ko”Harararta yayi yace a haka zakije gashin kanki duk waje kuma wannan miririn mayafin zaki yafa jeki ki sanyo hijab “kamar zatayi kuka tace “Dan Allah yaya ka bari muje harfa na shirya kuma idan na koma inna ganewa zatai da inda zamu bakaga gyalenma a jaka na sanyashiba “zakija a fasa fitar wlh muddin haka zaki fita gardawa na gane maki gashi ke ko kishin kanki bakyayi “Yafa gyalan tayi ta saman ka tace “to yaya na rufe kan please karka kara cewa wani abu “badan ranshi yasoba suka tafi dan yana bakin cikin mutane su dinga ganemishi surar Airar shi ba danshi kad’ai yasan kalar so da kishinta da yake “.

Wuraren shakatawa sosai yakaita sai murna da farinciki take tabbas farincikinta yadawo rabon da tashiga farinciki haka tun tafiyarshi london kimanin wata biyu kenan.

A hanyar su ta dawowa a mota ya bata kyautar hadaddiyar zoben gold din daya sayo mata sosai tayi farinciki da murna sai godiya takemai shidai murmushi kawai yake yana kare mata kallo.

Suna isa suka fito Hannunsu makale da na juna sai Dariya take ta farinciki tana zabgamai godiya daidai zasu shiga palourn inna Abba na fitowa Sosai gabanta ya fadi cikin dabarbarcewa ta fara kokarin kwace hannunta ya rike gam tare da galla mata harara kamar zatai kuka tace ka sakeni kara rike hannunta yayi ma .

kallon zaki gane kuranta Abba yayi mata tare da wucewarshi sosai nayi mamakin ganin Arman baiko gaishe da Abba ba saima kauda kai da yayi Abba na wucewa Arman ya gallawa Aira harara yace “ita kuma wannan rikicewar da kikayi ta mecece kamar kinga mala’ikan mutuwa “cikin muryar in ina tace yaya ab ba tsaki yaja tare da sakin hannunta ya wuce ya fasa shiga gidan inna durkushewa tayi ta fashe da kuka tasan ba karamun hukunci zata fuskanta a wajen Abba ba ga kuma shima yaya Arman din yatafi kamar fushi ma yayi da ita tana cikin kuka haidar yazo tare da daddabata ya ce “ya Aira Abba yace kizo yanzu yanzunnan ki sameshi a babban palour kika wuce minti biyar kinsan sauran……….✍🏿

Tofa meye dalilin da yasa Aira ta rikice ganin Abba ya ganta tare da Arman ????

Meye dalilin da yasa Arman bai gaishe da Abba ba????

Tukunnama wace Alakace ke tsakaninsu????

Zaku samu amsarkune ta hanyar bibiyata cikin wannan zazzafan labari

* Ta hanyar comment da sharhi tare da sharing shine abunda zaisa na gane labarin yana muku dadi ko akasin haka kuma shine babbar kwarin gwiwar da zaku bani idan kun karanta ku dinga comment tare da sharing sauran grps masoyan asali* 🤗

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/25, 00:17] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE* 📔
🅿️……………5&6

Cikin ta ne ya d’uri ruwa jin Abba na kiranta Cikin kuka ta kalli Haidar ta ce “Na shiga Ukku Haidar Abba Duka na zaiyi ko” Sai yaji yayar tashi ta bashi tausayi girgiza mata kai yayi ya ce “A a ya Aira nidai kawai cewa yayi kizo kuma kinsan Abba bayason yayi kira a bata mai lokaci ki taho muje ” shahada tayi ta mik’e tare da Jan kafafunta Wanda dak’yal suke daukarta tsabar tsoro.

Sosai ta tsorata ganin Abba na safa da marwa a palour tana shiga gabanta ba abunda yake sai fad’uwa juyowar da zatayi taji Abba ya d’auke ta wani gigitaccen mari da saida hankalinta ya gushe na d’an wani lokaci kafin ta d’ago ya k’ara kifa mata mari wani irin ihu ta fasa tare da durk’ushewa ta na kuka.

Cable d’in wayar wuta ya d’auko ya nufeta tare da lafta mata daya azabar da taji ce ta saka Kara sakin wani karan “Na shiga ukku zan mutu” Mama ce ta taso hankali tashe ta rik’e cable d’in ta ce “Dan girman Allah Alhaji kayi hakuri karka daketa DA Wannan Abun” Abba ya juyo ya Kalleta ya ce “Zainab ki rabu dani wannan yarinyar bata jin magana ki barni na koya mata hankali” .

“A a Alhaji Dan girman Allah kayi hakuri ka zauna Tukunnama me tayi Abba na huci ya zauna ya dubi Aira da ta ke kuka wiwi ya ce “Had’iye kukan nan yanzu yanzu nan Dan gidanku ” Cikin Sauri ta Had’iye kukan sai shshsheka da take cikin tsawa ya ce.

“D’ago ki kalleni Munafuka ” Idonta jab’e jab’e da hawaye ta Kalleshi ya ce “Sau nawa Zan rabaki da d’an iskan yaron nan,ban rabaki dashi ba?tana shasheka ta d’aga kai ” Bud’e baki zakiyi kimun magana “k a ra ba mu ” ta fad’a a rarrabe “Fine Kinsan da haka kuma shine kika cigaba da mu’amula dashi ko Watau bakijin magana ta ko rainani ne kika yi?” Cikin kuka ta fara girgiza kai ta ce “Dan Allah Abba kayi hakuri Bazan sakeba”.

” wannan ya zama.last warning da zan k’ara ganinki da yaron can duk irin hukuncin da na yanke maki ki kuka da kanki kina jina”cikin Sauri ta d’ago ta ce “Naji Abba”ki tashi kiban wuri sakarai wacce batasan ciwon kanta ba “hada gudunta Aira ta Ruga tayi dakinsu ta na zuwa ta baje a gado taci gaba da rera kuka Amma Da Ummy su sukayi ta Lallashinta anma kamar k’ara zugata suke.

Mama ko da Mamy sosai basajin dadin wannan al’amarin nasu musamman Abba da ya fi d’aukar zafi , ba Wanda ya kumayin magana cikin su Mamy ta tashi da tsohon cikinta ta tayi d’akinta ta jima ta na hawaye tasan Duka itace silar raba wannan y’an uwa Gashi kuma batajin dad’in yanda Kullum y’arta ta zama kamar jakka akan Arman kullum Abba cikin dukanta yake amma kamarma Kara tunzurata yake Haidar ne ya shigo maza tayi ta Goge hawayen ta Kalleshi ta ce.

” Haidar jeka kiramun Hajara”to Mamy yafada yaje ya samu Aira na Kuka Amma na Lallashinta yace “ya Aira Mamy na Kiranki a d’akinta Gyada mai kai tayi ta tashi ta na Goge hawaye ta bishi ta na zuwa ta zaune gefen Gado Mamy ta kalli Haidar ta ce ” Bamu wuri zamuyi magana “Yana fita ta kalli Aira ta ce ” ke yanzu Hajara Haka zakiyi ta zama kin maida kanki jaka a gida ko,?kowa ya na zaune lafiya amma banda ke,tunda kika San mahaifinki bayason tarenki da shi meye na likemai Ubanki ne shi da bazaki iya rabuwa dashi ba ko kullum kinfison ke kad’ai ake jinki da mahaifinki na rasa uban me yake baki duk kinbi kin lik’emai sakarai Saikije kiyi tayi ai tunda bakison ciwon kankiba”Aira Abu dukya chunkushe mata ga Abba ya gama laftarta ga Mamy ta hauta da fad’a tashi tayi ta na kuka ta fita tayi waje ta ma bar part din gaba d’aya ta koma part din inna.

Gadon ta ta hayaye a abunda take inbanda kuka shin ya zatayi da rayuwarta ,meye laifin ta ida da Arman akan gabar dake tsakanin iyayensu ga Abba ya gama jibgarta itama Mamy zata hauta da fad’a saida ta gama kukanta harta gode Allah tace “Gashi Shima Ya Arman din yayi fushi dani ya kukeso nayi da rayuwata tafada tana wulli da pillow Ta Kara fashewa da kuka ta ce.

” Tun bansan kaina ba na shak’u da kai yaya ARMAN wacce bazan tab’a iya misalta ta da komai ba ,tun bansan kaina ba ,shakuwar dake tsakaninmu babu wanda zai isa ya rabamu koda za a dinga tsaga naman jikina ana barbada attarugu da barkono bazan tab’a iya rabuwa dakai ba ” kuka ta k’ara fashewa dashi ita wai yazatayi da rayuwarta Daren ranar bacci kauracewa idanunta yayi banda kuka ba abunda take sai wajen Asuba bacci ya d’auketa.

©©©©©©©©©©©©©©©

Arman kai tsaye guest house d’inshi ya nufa kwance yake kan makeken gadonshi da komai na d’akin pink ne dakin gabaki dayanshi manne yake da hotunan Aira wasu tun tana yarinya wasu kuma da girmanta wasu tare suka dauka daga shi sai T-shirt da gajeran wando banda tsaki ba abunda yakeja ya ce “Wannan tsoron na mahaifinta da nagani k’arara a kwayar idanunta Tabbas wataran zata iya ruguza alak’armu abunda bazan tab’a jura ba kenan ko sama da k’asa zata had’e ana ruguguwar tashin k’iyama bazan tab’a yarda a rabamu ba my cutie Aira I love her so much,ina jinta har cikin kokon zuciya ta ,i can’t live without her inajinta a jinin jikina,tunaninta bai tab’a barin kwakwalwata ba daidai da second d’aya why Abba yakeson rabamu me mukai musu,ina ruwan mu da rigimarsu” Chan ya numfasa saboda bai saba doguwar magana ba ya ce.

” Karfa Aje kuma ita Har yanzu Kallon yaya kawai takemun kartace kuma bata sona wulli yayi da laptop d’in dake gabanshi ya ce “Inaaaaa bazaiyuba haka yayi ta zirga zirga ya k’ulla can ya since can ganin kanshi ya fara kullewa ya tashi tare da daura alwala ya fara jera salloli duk adduarshi akan Allah ya bashi Aira Dan shi kanshi ya kasa gane wannan wace irin jarabtar so ce Allah ya d’ora mishi ta yarinyar nan……..✍🏿

Hmm muje zuwa

A gaskiya ina Jin dadin comment dinku sosai masoyan asali kuma ina godiya kwarai da gaske 💃🏾💃🏾💃🏾

*Comment*

*vote*

*Share fisabilillah*#

*_Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/25, 23:13] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………7&8

Washe gari kasancewar weekend kuma basu da jarabawa yasanya bataje ko ina ba a d’aki ta yini tun Inna na tambayar me akai mata har ta rabu da ita sosai take baza ido ganin ko yaya ARMAN zaizo amma shiru hawaye ne ke zarya daga idanunta ta ce “Yaya kai kuma me nayi maka da zakayi fushi dani”.

©©©©©©©©©

Zaune suke a makeken palour shida mahaifiyarshi Magana take mai amma kwata-kwata hankalinshi baya gurin saida ta dafoshi ta ce ” Arman dakai fa nake magana tunaninme kake”Nothing Mummy ina jinki “Hmmm kawai ta ce sannan ta d’ora da cewa.

” Son maganar da na saba fad’a ce dai zan kuma maimaitawa Ka duba kaga ARMAN sa’anninka duk sunyi Aure wasu hada y’ay’a amma kai baka da ma niyyar yi shekararu fa ja suke Son ka duba 33years amma har yanzu baka da iyali ,ina son nima naga Aurenka naga Y’ay’anka karfa ka manta kai kad’ai ne d’ana a duniya kai kad’ai nake dashi Wanda zansamu jikoki daga gareshi ka tausaya mun ko Dan ni Arman plx”.

Numfasawa yayi a ranshi ya ce “Ina wata matsalar ita ma Mummy zatazo da wata a fili kuma cewa yayi ” Mummy karki damu Aure lokaci ne Idan lokacin yayi za ayi”Kullum maganar ka kenan Aure lokacine eh Aure lokaci ne amma anasa niya kaikuwa kwata kwata baka ma da niyyar ma sau nawa ina turaka kaje kaga y’ay’an y’an uwa da Abokaina karshema ka kunyatani kayiwa yaran wulakanci ” .

calm down Mummynah Insha Allahu soon zanyi Aure ina da wacce nake so ita nake jira ne shiyasa” Hararar wasa ta gallamai ta ce “Kullum maganar kenan ka na da wacce kake so ,kuma kak’i fadarta mu Santa,yaushema kake kula y’an matan da har zakaso wata son kodai aljanna ta Aure ka bamu sani ba ” .

Dariya maganar Mummy ta bashi sosai saida ya d’an Dara ya ce “yawwa Mummy ashe kingane aljanarce ta Aure ni shiyasa na mutu a kanta to Kinga sha’anin Aljannu sai a hankali zata rabu dani ku tayani da addua kawai Allah bani ita amma kidaina mun maganar Auren nan kinsan Aljannu da kishi karta kullaceki fa mummy”.

pillow Mummy ta tillamai jin shirman na d’an ta ce ” Watau Arman kadai maidani kaka ko zaka gamu dani ja iri kawai”Dariya yayi tare da gocewa pillown da Mummy ke jefamai yayi Hanyar fita yana cewa “Good bye mom saina dawo “yana fita guyd’s d’inshi sukayo wajenshi dakatar dasu yayi Dan bai fiyason yawo da su ba Motarshi Fara Sol kirar Benz yahau kai tsaye gidan Inna ya nufa ya na shiga mai gadi ya bud’e mashi ya shiga A lokacin Aira na kwance saman sofa ba bacci take ba amma kallo d’aya zaka mata kasan ta na cikin damuwa.

Dagowar da zatayi idonuwansu suka sarke cikin na juna ganin yanda ya hade rai ya basar ya yasanya maida idanunta kasa gabanta na fad’uwa tayi Sauri ta maida hawayen da suka zubo mata Arman na zama ya gaishe da Inna ta amsa tare da cewa “Wai ni Mujahid ina mahaifinka yaje kwana biyu bai lek’o ya gaishe niba ” Baya gari ne Naji Mummy tace yaje Ghana wani metting nima tunda nashigo k’asar bamu had’u dashiba”yana maganar ya na satar kallon Aira ta maida idanunta ta rufe.

“Inna ce ta ce ” To Allah ya maido shi lafiya nikadai a raina nace lafiya Kabir zai kwana biyu baizo ba “shidai Arman baice komai ba sai satar kallon Aira yake inna ce ta tashi ta ce ” Nidai na gaji da zafin nan bari na fita waje nasha iska tafada tare da ficewa farfajiyar wajen kamar jiran fitarta yake ya taso tare da zama kujerar da Aira take a hankali ya ce “My cutie” Shiru tayi kamar bacci take nanko ta na jinshi “Hmmmm nasan kina jina dan idonki biyu wake up zamuyi magana” badan taso ba ta tashi Dan sai yanzu take ganin me tayi mishi da zaiyi fushi da ita.

“kallon ta ya tsayayi yanda idanunta sukayi jawur ga alamar Tasha kuka cike da damuwa ya ce “Kuka kikayi ko Cutie” Kamar jira take nan take ta fashe da wani sabon kukan jin kukanta yake har cikin ranshi rungumeta yayi yana Lallashinta dak’yal ya samu tayi shiru cike da damuwa yace “wa ya tab’amun ke” Shiru tayi ta na shashsheka “ganin shaftun bulala a hannunta yayi ja abunka ga farar fata cike da damuwa ya rik’e hannun ya ce.

” Cutie Abba ya dake ki ko”Gyada mai kayi tana hawaye “sosai ranshi ya b’aci Dan a duniya ba abunda ya tsana sama da b’acin ran airanshi Har takai ga an tab’a lafiyarta wlh ba Dan shi ya haifeta ba da nikadai nasan matakin da zan d’auka cikin zuciyarshi yake maganar nan amma a fili cewa yayi “cewa yayi ki rabu da ni ko” gyada mishi kai tayi ta na hawaye “Dan son gwadata ko tsoro zaisa ta iya rabuwa da shi din yasanyashi cewa” Cutie Tunda Abba bayason mu’amularmu zan hakura na daina zuwa “wata irin zabura tayi tare da Rungumeshi tsam ta gefenshi ta zagayar da hannayenta cikinshi kamar wacce akace za a kwace mata shi tana kuka ta ce .

” kadaina cewa haka Dan Allah ni babu mai rabani dakai ko mutuwa ma tare Zata daukemu “sosai yaji dadin kalamanta cikin zuciyarshi amma Dan son Kara latsata ya sashi cewa” Bakya tsoron irin dukan da Abba yake maki banason Ana tab’amun lafiyarki shiyasa “Ni dukanshi baya mun komai nidai ka daina cewa zamu rabu daman zaka iya rabuwa dani ni bazan iya juran missing dinka ba ko Abba zai kasheni nidai ina son ganinka ” ta fada tana shasheka sosai yaji dadin kalamanta A ranshi “bubbuga bayanta ya fara tare da fara Lallashinta yace.

” Sorry my cutie nima bazan tab’a iya rabuwa dakeba Kisa wannan a ranki babu mai rabamu sai mutuwa kibar kukan nan kinsan kukanki yana tab’amun Zuciya “Lokaci guda ta Had’iye kukan tayi luf jikinshi tana sauke ajiyar Zuciya kokarin Bambareta daga jikinshi yake amma ta kiya saima Kara Lafewa da tayi jikinshi tana shak’ar daddad’an k’amshin turarenshi har wani bacci bacci yake kokarin daukarta shiko bayason Yanda Aira ke rungumarshi Dan yana cutuwa amma ba yanda ya iya ” A hankali ya ce “Cutie son jikinki yayi yawa ” Murmushi kawai tayi ta na lumshe ido ta ce “Turarenka yanamun dad’i yaya” Ko kina so na kawo maki shi”cikin shagwaba ta ce “kamanta ka tab’a kawomun Amma ni idan na shafa banajin dad’in kamshinshi kamar ma ba shiba a jikin ka ne yake k’amshi me dadi” Murmushi kawai yayi ya ce.

“Ya Exam din fatan kina maida hankali” Alhmdllh yaya ina karatu sosai ai “yaya aramun wayarka nayi game” Ciro wayar yayi tare da mik’a mata “gyarawa tayi tare da d’ora kanta a kafad’arshi ta na game din da ta fad’i yayi mata Dariya ganin haka yasa suka fara yi tare yayi ci daya tayi daya idan ta fad’i yayi mata Dariya Shima idan ya fad’i tayi mishi Dariya idan kuma taci tayi ta mashi gwalo Sosai suka shagala Aira harta manta da wani abu waishi damuwa Dan ita daman b’acin rai bai zama cikin zuciyarta.

“Ummy ce ta shigo ita da Amma Duk.kallon Mamaki suka dinga kallonsu dashi Ummy dai tab’e baki tayi ta zauna Amma ko mamakin irin taurin kai iri. Na Aira take ” Amma ce ta gaisheshi ya amsa yana mata dariyar ya fad’i Inna ce Ta shigo tsaki taja ta ce “Ohni Halima ina ganin rayuwa yaran zamanin nan baku San ta ido ba wlh ayi yara baku da aiki sai Rungume Rungume da tab’e tab’e kai nidai Na kusa korarku wlh a daina shigomun Bangare ehe akanme” ta k’arasa fad’a tana zama tare da Mike kafa “yi sukayi kamar bada su take ba saima cigaba da game d’insu sukayi ” inna Haushi ya cikata ta tashi tace “ku tashi ku fita tare da nuna musu hanya turo baki Aira tayi ta ce ” kedai tsohuwar nan baki son zaman lafiya me aka miki kuma”Ubanki akamun ku tashi ku fita nace “Bazamu fita dinba ki daukemu ki fiddamu ta fad’a tana murguda baki ”

Salati inna tayi tare da Goge hawaye ta ce “Ni kike zagi Hajara kai albasa batai halin ruwa ba baki biyo halin mai sunan ki ba Y’ar uwata ba haka take ba kai amma ma wlh an cuceta da aka saka mata sunanki kaico Adda Jaru Allah ya jikanki yasa kina cikin rahama ke kuma bari inje nafadawa ubanki kina zagina ” Jin hakan ya sanya Aira saurin tashi tare da ruko hannun Inna Dan tasan ta kaita wajen Abba ta kade Ta ce .

“Haba my lovely grandy wasan jika da kaka ne fa ni ina ni ina maki Rashin kunya waya haifeni a garin nan” Inna ta tsuke baki tace “ba wani dad’in baki da zakimun ” ta kama hanyar fita tayi Sauri ta bita Tare da ruko ta ta ce “Inna dawo zan baki Zumar turawa wlh ai kina so ko” Lokaci guda Inna ta saki fuska ta ce “da gaske kike y’ar nan ” Eh mana inna da gaske Amma saikin dawo saikin fasa zuwa”juyowa inna tayi tana washe baki ta ce “Daman ai wasa nake maki y’ar albarka ai duk cikin d’iyan Habu ke kika fita zakka ba kamar waccen Zakalkalar bata da aiki sai latsa waya Ko y’ar halawa bata tab’a kawomun ba .

” ta fad’a ta na kallon Ummy Aira ko Dariya hada rik’e cike jin an tabo ummy itako Ko kallon Inda inna take bataiba saima cigaba da chat d’inta da tayi Arman dukda bai fiya Dariya ba saida ya d’an dara jin irin dramar da inna da Aira sukesha Bayan Aira ta kawowa inna coculate din Arman ya tashi ya ce “Cutie zan wuce ” Kamar zatayi kuka ta ce “Yanzu kazo fa ” wara idanu yayi ya ce “Kai cutie nafa jima” Cikin shagwaba ta ce Ni ban gaji da ganinka ba”Durkusawa yayi tare da rada mata wani Abu Wanda koni banjishi ba sainaji ta dago ta na Dariya ta ce.

“promise fa yaya” Dage mata gira yayi ya ce “Gaske” tsalle tayi ta ce “Thnks you my yaya Goodbye sai gobe” Tare suka fita saida taga shigarshi mota tana mishi bye bye tukwana ta koma ciki ta na shiga lokacin Inna ta shige ciki Ummy ta wurga mata harara ta ce .

“kedai wlh kin zama jaka Jiya Abba ya gama jibgarki akanshi yanzu kuma a ganku tare keda bakison ciwon jikinki ba” Turo baki gaba tayi ta ce “To ina ruwanki ” Babu ruwana Jiki ma magayine ta fad’a ta na cigaba da latsa wayarta “Tsaki Aira ta ja kasa kasa ammako kallon y’ar uwar tata take kallon tausayi Dan sosai ta jima da ganewa Aira da Arman sunjima da Fara son junansu so ma ba na wasa Dan wannan abun nasu yafi k’arfin a kirashi shakuwa…….✍🏿

*Share fisabilillah*

_*Miss Hajo ce_*🤙🏿
[5/27, 21:33] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………9&10

Washe gari Aira basu da Exams sungama Waec suna Dan hutun kwana Biyu kafin a fara neco hakan yasa bataje ko ina ba wajen 2 ta lek’a bangarensu Wanda rabon da ta shiga tun sanda Abba ya daketa Bayan ta gaishe da Mama dake palour ta wuje bedroom d’in Mamy “Kwance ta tarar da ita Alamar batajin dadi cike da damuwa tace.

” Mamy meya sameki”Cikin k’arfin hali tace bakomai da sauki bandanjin dad’i ne amma na samu sauki”Zama tayi bakin gadon tare da cewa “Allah Kara sauki kema Mamy kidaina haihuwar nan Gaskiya ni kunya ma nakeji ace uwata zata haihu gashi sai wahala kikesha ” idan na haihu kice d’an ko d’iyar ba k’aninki bane ba shikenan ba marar kunya ku biyun ne harzaki dinga mun complain masu y’ay’a goma suce me ke inaga ke d’aya kikaso a haifeki ma ko Dan ki juya ni yanda kike so “.

Dariya Aira tayi ta ce “Sorry Mamy na Ba haka nake nufi ba wahalar da kikesha ce banso” Ummm Naji dai ya exams din “Mamy yau bamuyi ba Sai next week amma alhmdll” Masha Allah Allah ya taimaka ki dage Aira sosai Kinga kinci Jamb 230 yanda akeso ki dage kici Waec and neco yanda next year makaranta kawai zaku tafi banson shiriritar nan da kika fara koya Aira Kinga dai Mahaifinku Karatu yake so Kuyi tun daga kan Yayyunki kina gani da idonki saida suka kammala degree d’insu aka musu Aure Batare da sunba iyayensu matsala ba inma Akwai soyayya a ranki ki cireta Aira kin tabbatar Mahaifinku bayason Kule kulen samari Karkija ki samu matsala dashi kinsanshi mutum ne mai ak’ida Dan haka ki nutsu ki maida hankalinki ga karatu kinji y’ata karki bani kunya”.

Tunda Mamy ta fara maganar Aira take sauraranta saida ta gama ta ce “Insha Allah Mamy bazaki sameni da matsala ba ” Sannan ta tashi ta ce “Bari naje nayi sallah naga ana kiran Sallar la’asr ” Koda ta fita da Kallo Mamy ta bita Tayi mata maganar nan ne badan komai ba “Saidan zargin da take na Aira Soyayya suke da Arman a zuciyarta ta ce ” Allah yasa ma tunanina karya zama Gaskiya muddin Aira da Arman soyayya suke akwai matsala batason yanda ta zama farin silar raba wannan y’an uwan y’arta ma tazo ta k’ara zama silar k’ara rugujewar zumuncin iyayensu tasan Arman baida wani Aibu amma kuma soyayyarsu da Aira k’ara ruguza abubuwa zatayi da dama ta jima ta na tunanin AL amarin nan kafin ta tashi ta shiga toilet Dan dauro tata alwalar.

Aira Bayan tayi salla Kwanciya ta yi palourn inna tana kallon wani series inna ta fito daga d’akinta kare da waya a hannunta ta mik’awa Aira ta ce “Amshi inji Mujahid ” Cikin Sauri ta Amsa ta gaisheshi ya amsa tare da tambayar ya take”tukwana ya ce ki shirya nan da 30 minutes ina nan zuwa zamu fita amma Bazan shigo ba Dan sauri nake Zan kiraki wayar Inna zaiki fito” To yaya ta fad’a cikin Sauri kafin ta kalli inna ta ce “Inna fa kasan Abba ya fad’a mata ta daina bari na fita ” Lost phone” yafad’a mik’awa inna wayar Tai daga bangarenshi ya cewa inna “Inna Dan Allah Anjima zanzo mu fita da Aira zan yo maki sayayyar kayan marmari ta kawo maki ” Washe baki Inna tayi ta ce “To d’an albarka Saikazo kai nidai nayi sa ar jikoki wlh ” Dariya Aira Tai Dan ita da Arman sunsan logar kashe bakin inna Dan tana da saukin kai indai akwai kayan makulesshe.

Kafin lokacin da yace harta shirya sosai tayi kyau cikin blue din Abaya Jikinta duk stones ne Sosai tayi mata kyau kunsan yanda blue din abun ke karb’ar farar fata flat takalmi tasa batai make up ba sai hoda da kwalli kawai da tasa Sosai tayi kyau ta fito kamar wata balarabiya Tana gama shiri inna ta kawo mata waya ya kira ta amsa mai da gata nan fitowa.

Ta na fita ta Hango motarshi Dan nesa da gidan ta na zuwa ta bud’e front sit ta shiga a hankali ya ce “wow my cutie kece kuwa” Murmushi ta yi tare da rufe fuska “Yau kuma ni akejin kunya ” cikin Sweet voice d’inta ta ce “Yaya ai Kaine kamar yau kafara gani na ” Murmushi yayi ya ce “kinyi kyau ne shiyasa” Kallonshi tayi Sosai yayi kyau cikin Dakakkiyar shaddarshi milk Tasha aikin da shi kanshi abun kallone hularshi ya hada matching colour ga Agogon gold d’inshi da take ta walkiya sosai yayi mata kyau kamar wani ango “A hankali ta ce ” Wow Yaya kaima Kayi kyau Kamar Wanda zaije Zance .

“murmushi yayi ya ce ” Ai zancen nazo ki rakani”yafada ya na tada mota”lokaci guda ta chanza fuska Tare da cewa hmmm”Dadi yaji a zuciyarshi na ganin kishinshi a kwayar idonta dukansu sukayi shiru na d’an wani lokaci kafin ya juyo ya Kalleta ya ce “My cutie ya kikayi shiru ko bazaki rakani zancen ba ” Kallonshi tayi tare da turo baki ta ce “Ni bazanje ba Daman kasan wajen budurwarka zakaje shine kacemun shan ice cream za ka kaini” cike da so da k’auna yake kallonta Dan sosai kuruciyarta take burgeshi ya ce “To saboda me bazaki rakaniba” Saboda bana sonta”Dariya yayi sosai kamar bashi ba ya ce “Ina kika Santa da zakice bakya sonta” turo baki tayi ta kauda kai gefe Sosai ta bashi Dariya ganin yanda take kishin ido bud’e ko wannan alamar kadai ta tabbatar mai da Airanshi itama tana sonshi.

Wuraren shakatawa sosai ya kaita saida ya fara kaita Tasha Ice cream Sukasha hotuna a Wayarshi mutanen da suka sanshi sai mamakin ganinshi da budurwa suke Dan sunsa Arman mutum ne mai kamun kai ba kowace mace ce zata iya tunkararshima ta ce ta na sonshi bare shi karan kanshi yace yana sonta sosai Arman yake burge mutane saboda bashi da girman kai inba saninshi kayi ba baka tab’a cewa d’an Governor ne Dan ko Security bai fiya yawo dasu ba.

Saida ya kaita wuraren shakatawa da shan iska sosai ya kashe mata kudi Inda ya kaita shopping mall ta zaba abunda takeso yawaici duk turarruka ta zab’a da choculate da ta jibgo kamar ba gobe shiko sai karo mata yake inbata ga wata ba ya ce “Cutie ga wata Bayan sun gama ya wuce da ita wani makaken Shagon saida iPhone’s lokacin har Angama kiran Sallar magrib suna shiga masu shagon suka gaisheshi cikin mutuntawa ya amsa ” Kallon Aira yayi ya ce “Baby tayani zab’e Waya zan chanza wacce kikaga ta dace dani”murmushi tayi ta ce .

” Tohm yaya “Nan suka fiddo mata wayoyin tundaga 5× har zuwa iphone13 Ana dauko 13 Din tace yaya wannan tayi kaga itace ake yayi yanzu”tambayarsu yayi kudinta suka fadamashi 720k nan take yayi musu transfer yasa aka sanya mata cover mai kyau tare da Yin register sabon layi tukwana suka fito a hanya sai zud’in wayar take har suka iso bakin gate ” ganin bai fito ba yasanya ta cewa “Bazaka shiga ba” Eh cutie Sauri nake”Kindai iya d’aukar kayan naki ko na shigar miki dasu”Murmushi tayi ta ce.

“Haba yaya kamar wasu da yawa zan iya ” to shikenan “tana niyyar fita yace ” Zaki mance wayarki”Zaro idanu tayi ta ce “waya ta kuma?nida banda waya yaya ka manta” Wadda muka sayo nake nufi takice “Yaya tawa kuma ta fad’a cikin nuna mamaki” mik’a mata yayi ya ce “zakiga number ta a ciki nayi miki save zan dinga Kiranki ta nan idan zamuyi waya” Farincikin da take ciki bai musaltuwa tazo rungumeshi ya kauce ya na Dariya Ya ce “Cutie kin girma fa” Cikin murna ta ce “Thnks you yaya bansan da wani irin baki zan gode Maka ba nagode Allah saka da alkhairi ya k’ara budi Sai jujjuya wayar take wai tata ce “ameen Cutie na bansan godiyar nan haka Kinfi k’arfin komai a wajena ” .

Murmshi ta sakar mashi kafin ta ce “Yaya to ya zan fad’awa y’an gida Kar Abba ya kwace kasan bai fara barinmu rik’e waya ba musamman Na yaji kai ka bani”Ashe baki da wayau Baby karki sake ko da wasa wani ya ganta bare har ma asan ni nasai maki nima nasai maki ita ne badan komai ba saidan nadinga jin muryarki koda na koma Wajen aiki amma kinsan nima banason Abunda zai dinga Zame maki matsala a gida ni zan wuce yanzu sai gobe Idan na leko” .

Thnks yaya insha Allah ba Wanda zai ganta ta fad’a cikin murna tukwana ta dauki sayayyar da sukayi tayi cikin gida sai murna take wai yau itace da waya wayarma y’ar yayi Koda tashiga tayi sa a ba kowa Sai inna Nan ta bawa inna Sayayyar da Arman yayi mata tukwana tayi ciki Sai tsallen murna take nan take ta jona ta chaji saida ta cika tukwana ta bud’e tana budeta taga ya turo mata 10gb cikin zumudi ta shiga Ta dinga d’akko apps har su what’s app da Instagrams su tiktok saida ta d’auko a ranar ta fara setting d’in komai a Daren ranar ma saida suka kusan raba dare suna shan hira da Arman Saida yaga ta fara jin bacci tukwana yayi mata saida safe .

Washegari tunda safe Bayan tayi Sallar asuba harta koma saiga kiranshi saida ya tambaya lafiyarta Daga nan bata koma ba da d’auko numbobin class mates d’inta Wanda take dasu a Littafi duk ta Kwafe ta bud’e what’s App duk tayi musu sallama zumudin wayar ya hanata komawa bacci ta shiga nan ta shiga Chan sai wajen 12 ta fito Bayan tayi wanka ta saka Riga marar nauyi gaishe da Inna taje tayi tukwana ta wuce bangarensu.

A Babban palour ta tarar da Abba ta duk’ursa ta gaishe da shi ya amsa mata cikin sakin fuska taa cewa “lafiya qalau Mamana ya exams din yau bakuyi ko?” Alhmdllh Abba sai gobe zamu fara neco din “Masha Allah Allah taimaka ku dage kinji Allah muku Albarka” Cikin jin dad’in Addu’ar Abba ta amsa da Ameen tukwana ta wuce cikin bedroom d’in Mamy ta gaisheta tare da yi mata ya jiki ta amsa da sauki.

“Mamy ba abunda za a miki bakya buk’atar komai? Eh Aira ba abunda nake buk’ata mai aiki tagama komai Saidai zan aikeki gidan Maman Zarah kawar tau nan dake d’orayi kingane gidan ko?Eh Mamy na gane ta Ai muna zuwa tare ” yawwa to Chan zaki da kinje kice Nina aikoki ta baki sak’on ki kawomun ki gaisheta “Sannan ta zaro dubu d’aya a Jakarta tace ” gashi kihau napep “to Mamy saina dawo ta fad’a saida taje ta d’auko doguwar Hijab d’inta har k’asa tukwana ta tafi.

Ta na zuwa bata jima sosai ba ta amsowa Mamy sak’on ta fito ta na tsaye ta na jiran mai napep wata dalleliyar mota ta faka a gabanta Gaba tayi mai motar ya bita yana mata magiya Dan girman Allah ta tsaya ta saurareshi jin ya had’ata da girman Allah ya sanyata ta tsaya saida ta k’are mai kallo ta ganshi baida laifi dogone baki cike da magiya ya ce ” ki shigo na rage maki hanya bai kamata mace kyakyawa kamarki rana na gallarta ba.

“Yi tayi kamar bada ita yakeba ” Saida ta yi ta had’ata da Allah tukwana ta shiga Dan ta lura zatasha wahalar samun abun hawa nan tayi mai kwatancen Inda zai kaita har kofar gida ya kaita ta fito ta ce Nagode “Me kyau baki bani number ki kuma ba?Kamar ta shakeshi Dan Haushi ta ce.

” Bani da waya”Ta juya kenan ta Hango Motar Arman yayi tsaye jikin mota Rungume da hannayensu ya na kallonta “Cikinta ne ya duri ruwa Dan idan bata mance ba yaya Arman ya jima da mata kashedin akan karta yarda ta kula samari ko ya ganta da wani Wanda hartayi mashi alkawarin bazata kula kowa ba gashi idan ma tayi mashi bayanin rage mata hanya kawai yayi ba fahimtar ta xaiyiba .

Taku Biyu Arman yayi kamar wani Zaki haka ya nufosu Fuskarnan tashi murtuke kamar bai tab’a Dariya ba ita kanta saida ta tsorata da ganinshi haka wani irin kallo ya watsa mata tare da data mata tsawa ya ce wuce ciki” A firgice ta wuce hada gudunta Dan sosai ta tsorata da yanayinshi “Arman ko kallon saurayin yayi ya ce………….✍🏿

*Share fisabilillah *

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[5/28, 21:04] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………11&12

…..” Malam wa ya baka izinin d’aukar yarinyar Chan a mota?cikin gaskiyarshi saurayin ya ce “Kayi hakuri na ganta ne a hanya ta rasa abun hawa shine na rage mata hanya kuma sonta nake ba son yaudara ba so na Aure Dan tunda na ganta Naji ta tafi da imani na ” Wani irin wawan kallo ARMAN ya gallamai ji yake kamar ya shakeshi ta maza kawai yayi ya ce “Matar Aure ce Dan haka karka k’ara bibiyarta ko kaji a ranka kana sonta Wata alaka ta k’ara shiga tsakaninku zan kulleka hope ka gane ya na gama fad’ar haka ya juya ya shige ciki shiko saurayin sosai yayi mamakin jin cewar Matar Aure ce har yana murna yayi Babban kamu cike da jin haushi ya juya.

Aira ko ta na shiga Bangaren inna ta yi sai rarraba idanu take kamar wata marar Gaskiya Daga Amma sai inna a palourn Amma nayiwa Inna Karin karatu tsaye tayi jikin Bango ta kasa ko motsawa ta na haka ARMAN ya shigo daga ganinshi.kasan ranshi yayi mugun b’aci kanta yayi gadan gadan kafin ta juya ya chafkota Cikin zafin nama ya murde mata kunne k’ara ta saki Dan taji zafi sosai Karanta ta jawo da hankalinsu Amma cike da masifa ya ce ” Uban waye wancen d’in Wanda ya saukeki a mota “Cikin kuka Aira ta ce ” Yaya nima bansanshiba Dan Allah kayi hakuri Bazan sakeba ka sakarmun kunne da zafi”

“ke harkinyi girman da zakishiga motar wani k’ato ko ?ina alkawarinmu dake daman idan bana nan irin abunda kike ko?k’ara fashewa tayi da kuka ta ce “a a yaya wlh yau dinma tsautsayine” Sakin murdewar yayi tare da wurgata ta durkushe ta fasa kuka mai tab’a zuciya har cikin ranshi yake jin kukan nata ganin irin kukan da take ya sanyashi sanyaya zuciyarshi dan ba abunda ya tsana sama da kukan Aira Shima durkusawar yayi cikin kwantar da murya ya ruko hannunta ya ce “Sorry ” Bama ta saurareshi ba saici gaba da kukanta da tayi murza hannayenta ya fara ya ce “Sorry my cutie bazan sakeba kema karki sake kinji kinsan banason ganinki da kowani d’a namiji shiyasa na kasa control d’in zcyta please karki sake in baso kike zuciyata ta tarwatse ba ” Rungumeshi tayi cikin kuka ta ce “Bazan sake ba yaya kayi hakuri ” Shafa bayanta yafara nan ya fara Lallashinta kamar ba shine ya gama zafutartaba.

Inna ko da Amma suna nan suna kallon Ikon Allah “Murmushin jin dad’i inna ta yi ta ce ” Allah nagode maka Tabbas mafarkina ya kusa zama Gaskiya Allah cikamun burina na ganin Auren Hajara da Muhajid Tabbas nasan ta silar hakan ne kad’ai za a iya samun sulhu tsakanin iyayensu.

Da misalin k’arfe 10 na dare Aira sanye take cikin kayan bacci Nan ta d’auko wayarta ta ta boye cikin locker ta fiddota ta bud’e data nan tayi ta ganin message d’in mutane na shigowa frnds d’inta na mata congrats Number yaya Arman da tayi save da “My yaya ta shiga taga rabonshi da online one.week kenan Hakanan kawai tayi mai slm Dan daman ya fad’a mata shi chat bai dameshiba gwarama Twitter yana shiga yaga labarai.

Amma ce ta shigo d’akin Aira bata lura ba maza tayi zata boye wayar da sosai ta tsorata Ta ce ” Amma Me kikazo yi”Cikin in ina take maganar murmushi kawai amma tayi ta zauna ta ce “hmm Aira kenan ni bantaba tunanin akwai abunda zaki iya b’oye munba Kinsan tun muna yara bama boyewa junanmu komai kuma muna rik’ewa junanmu sirrikanmu to me yasa kwanannan kike neman chanzamun kinsan dai ko mutum muka kashe bamaiji” Ajiyar zuciya Aira ta sauke tasan hakane tun suna yara basa b’oyewa junansu komai a hankali ta ce “Sorry sis “ya wuce amma ta ce sannan ta Amsa wayar hannun Aira ta ce ” Wow Sis 13 ce fa “Dariya Aira tayi ta ce ” Kina mamaki ne “Sannan taje ta rufo kofar Dan kar Wanda ya shigo ” Amma ta ce wa ya baki 13 Aira “yaya Arman ta bata amsa kai tsare dare da dawowa ta zauna” Arman “Amma ta fada sannan ta ce “Kai amma Allah yiwa Yaya Arman albarka Gaskiya Yaya ARMAN ba k’aramun sonki yake ba Aira” wara idanu Aira tayi ta ce “So fa kikace sis” So kuwa sis Arman ya jima da fara sonki fahimta ce kawai bakiyiba amma Arman ba k’aramun so yake maki ba ko ince kuke yiwa junanku.

“kamo hannunta Aira ta yi ta ce ” sis kina nufin yaya Arman sona yake”kwarai kuwa Ke wace irice Aira da baki gane so ,baki ganin kishinki b’arob’aro a idanunshi Abunda ya faru dazu ma Kad’ai ya isa ya k’ara tabbatar maki da irin son da Arman yake maki Bayan nan ma alamomin soyayyarki da yake gwada maki a fili suke ba a boye ba Aira ko k’aramun yaro zai iya fahimtar soyayyar dake tsakaninku ni a zato na kinjima da ganewa kiyi tunani ki gani”.

Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da lulawa duniyar tunani tun daga rayuwarsu ta baya har zuwa yanzu ,me yasa a cikin gidan ita kadai yake sakewa,me yasa ita kadai yake farantawa,ita kadai ya damu da ita,ita kadai yake kishinta ita kadai da dama Tabbas sai yanzu ta gane Yaya Arman sonta yake sosai gabanta ya fad’i kallon Amma tayi tace “To sis ni kuma ina sonshi? Ta k’arasa fad’a cikin sigar shagwaba Dariya Amma tayi sosai ta ce .

” ke sis wlh baki rabo da abun Dariya ni zaki tambaya ai zuciyarki zaki tambaya”Turo baki tayi ta ce “To fad’amun menene alamomin so?Alamomin so suna da yawa Aira Amma zanfada maki Kad’an daga cikinsu saiki duba kiga idan kina daga cikinsu ” Shak’uwa tayi yawa tana daga cikin Alamun so,damuwa da halin da dayan ku yake ciki “Damuwa da rashinshi a kusa dake koda kuwa na y’an dak’ik’a ne,kishi,shine babbar alamar Zurmiya a cikin soyayya,kyautatawa,ko da yaushe idan kika kalleshi kiji farinciki ya mamaye zuciyarki koda kuwa a waya Ne,jin bazaki iya rabuwa dashi ba duk rintsi duk wuya ” ga sunan da yawa Aira kiyi tunani.

Shiru tayi tare da Zurmiyawa duniyar tunani Tabbas inko hakane so ta jima da afkawa kogin soyayyar yaya Arman soyayyarma ba ta wasaba cike da damuwa ta ce “Tabbas sis najima da Fara son yaya Arman koma Ince da soyayyarshi na ginu tun bansan kaina ba nakejin Duka abubuwan nan da kika lissafo game dashi ina tsananin sonshi son ma bana wasa ba a da haukana na d’auka duk wannan din shakuwa ce saida kika lissafo nagane Abunda ake nufi da so da Chan shirmen banza na kawai nake sannan ta kamo hannun ta tace.

” Sis ya zanyi help me please ina sonshi sosai ya zanyi kin tabbata shima yana sona”Cike da tausayin y’ar uwar tata ta ce “Karki damu sis son da yake maki ya linka son da kike mashi Wanda na gani a idanuna kedai kawai ki bari har zuwa lokacin da zai furta miki” Hakika indai kika samu Yaya Arman sis kingama samun wani jin dad’i a duniya Dan nasan zaiyi wuya a samu Wanda zai kula dake ya nuna maki tsantsar k’auna da soyayya Bayan yaya Arman Dan Arman mutum ne da kowace mace ta sameshi ta more ,Abu d’aya kawai nake Tsoro kuma nake jiye muku Iyayenmu na tabbata Abba Da Daddy bazasu tab’a yarda Kuyi Aure ba inba wani ikon na ubangiji ba shine Babban abunda yake tsoratani”Hawaye sosai Aira take ta ce “Ina sonshi sis Bazan yarda a rabamu dashi ba Abba bazai iya rabamu ba Inajin da sonshi aka halicceni a yanzu bana jin tsoro ko shakkun komai da zan tunkara indai akan a rabamu da yaya Arman ne na gwammace Ranar na mutu”.

ta fad’a tana fashewa da kuka ” Sosai Amma ta tausayawa y’ar uwar tata Rungumeta tayi ta ce “Insha Allahu sis babu mai rabaku sai mutuwa nan tayi ta Lallashinta ranar daki daya suka kwana Wanda Aira baccci kauracewa idanunta yayi sakat tunanin Arman ya hanata bacci da kalaman y’ar uwarta Tabbas tasan indai hakane so to baiyi mata kamun wasa ba yayi mata kamun da ita kanta bazata iya control d’in zuciyarta ba sai Bayan asuba bacci ya d’auketa hakan yasa washegari tayi ranar bacci sai 12 ta tashi.

©©©©©©©©©©©©©

B’angaren Arman Shima hakan ta kasance Dan Sosai yakejin son Aira a ranshi Wanda shi kanshi bazai iya kwatanta shi da komai ba Sosai yakejin Haushi idan ya tuno ganinta da yayi da wani a tsaye tunani yake akan ya fito ya furtawa Aira abunda ke ranshi koko ?zata amince dani ko akasin haka? Ta na sona kamar yanda nake sonta ko har yanzu Kallon yaya takemun?Daren ranar bacci kauracewa Idanunshi yayi Yasan son Da yakewa Aira daga Allah ne Dan koda bai shiga zuciyar zukatan masoya ba yaji yanda sukejiba ya tabbata son da yake yiwa Airanshi babu wani mahaluk’in masoyin da zai iya yiwa masoyiyarshi kalarshi ba.

Washegari jiki ba kwari ya tashi koda mumy ta tambayeshi lafiyanshi qlau kawai yace mata nan take fad’a mashi Daddynshi jirginsu ya taso tun d’azu sun kusa isowa sai sannan ya d’anji sanyi sanyi a ranshi Dan sosai yakeson ganin Daddy Mummy tace yaje ya shirya nan da 30 minutes zai k’arasa.

Arman da kanshi shida Mummy suka taryo Daddy daga Airport Hannun Daddy rik’e da na Arman Dan ko Wanda bai saniba yasan irin tsananin son da Daddy ke yiwa Arman kasancewarshi shi d’aya tilon d’anshi a duniya.

Bayan Daddy ya huta yaci abinci Mummy sai Nan nan take da mijin nata Kallon Arman yayi ya ce “Son ya London d’in Fatan ka dawo lafiya” Lfyqlau Daddy “Masha Allah yaushe kuma zaka koma wajen Aikin naka” ran Monday sukace Daddy nama zata zasu d’an bani Hutu tunda kaga su suka turani London d’in nadawo na zata sunbani ko hutun 2weeks ne amma jiya sun kirani suke ceman Monday suke Son na koma”Dafa kanshi Dady yayi ya ce “Toh nan kusa kenan Kaga yau muna Friday to Allah ya kaimu Monday din Ai nasan d’ana jarumine Shiyasa basason suyi missing d’in aikishi “.

Murmushi Arman yayi Dan sosai yakejin dad’in yanda Daddy kullum ke kod’ashi shi d’anshi jarumine jajirtaccene tun yana yaro haka yake cemashi shi jarumine Ranar Yini sukayi suna Hira da Daddy Dan ko gidan Inna bai lek’a ba Yau cikin hirar ne yake cewa “Daddy Inna na ta nemanka” murmushi yayi ya ce “Insha Allahu gobe idan na huta zanje na gaisheta.

Washegari Daddy da Arman su kaje ya gaishe da Inna shida Security d’inshi Wanda koda yaushe suna biye dashi Arman bai samu ganin Aira ba dan Inna tace mai suna makaranta kasancewar da safe sukaje daga Chan suka wuce asibitoci Dan duba marassa lafiya sannan yayi musu alheri sosai wannan na Daga cikin abunda yasa mutanen jahar suke tsananin sonshi da son mulkinshi danshi mutum ne mai kirki da kuma tausayi ga Gaskiya da rukon amana.

Ran Sunday da dare Arman ya je gidan Inna Dan bankwana da Airanshi koda ya fad’a mata zai koma wajen Aiki kuka ta sanya mashi ita batason yake nesa da ita dak’yal ya lallab’ata yace zasu dinga Video call kullum kuma suna waya duk saiyaji bayason ma Tafiyar Dan dai ya zama dole Amma shi Zama da Airan shi ya fiye da mashi komai.

Tunda Arman ya tafi kullum cikin waya suke da video call kamar ma suna tare Aira suncigaba da Jarabawarsu ta neco ita da Amma sosai suka maida hankalinsu ga karatunsu har yanzu babu Wanda yasan da wayar Aira a cikin gidan Bayan Amma koda yaushe son Arman Kara ninkuwa yake a cikin Zuciyarta.

Ranar da Arman ya cika sati Biyu da tafiya Ranar Su Aira suka gama neco d’insu sai farinciki suke suda class mate d’insu ana tashan hotuna a wayar Aira nan Duk wasu suka amshi numbobinta ranar ji suke kamar karsu rabu daga karshe suka sha kuka musamman Aira ita da frnds d’inta Khady bestynta sosai suka shaku koda yaushe a school tare suke yawo nan sukayiwa juna Alk’awarin ziyartar juna akai akai Sai wajejen 6 suka gama hotuna da bankwana suka fito Bakin gate domin tafiya gida Suna fitowa Wata wulfefiyar Mota Fara me masifar kyau Aira ta gani parke .

Ganin mai fitowar ne ya sanyata wara idanu sosai yayi cikin sky blue din shadda ta tasha Aiki hular kanshi hadaddiya wadda a k’alla zata kai 100k Rungume yake da hannayenshi da suke sanye da Wrist din zinare kara wara idanu tayi Dan tabbatarwa da shi d’inne koko Gizau ne shiko kafeta yayi da idanu murmushi kawai yake sakar mata sosai tayi mashi kyau cikin unifoam dinta Light blue Hijab da Dark blue din wando y’ar k’aramar hijab dinta tare da rafar rigarta da ta sauko har gwuiya anyi mata hular hijab d’in da yadin wandon jelar rigarma haka ji yake Kamar ya je ya rungumota Aira ganin da gaske shi d’inne de gabanta ai batasan lokacin da ta saki Hannun Khady ba ta ruga a guje tayi wajenshi tare da Rungumeshi tama mance ta tsiraran mutanen class d’insu dake wajen Cike da murna da farincikin ganinshi ta ce My yaya……..✍🏿

*Share fisabilillah*

*_Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/30, 23:01] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………13&14

Cikin zazzak’ar muryarshi Mai cike da kassala a hankali ya ce “My Cutie baki girma har yanzu ko kin manta gaban mutane muke kike rungumeni ” ya fada kamar bashi yayi maganar ba murmushi tayi tare da sakinshi ta ce “Sorry yaya murnar ganin kace ta sa na ma manta da mutane a gurin” Aike gimbiyace bakya laifi my cutie “Uhm My yaya ammafa Gaskiya kayi surprise Dina da yawa bantab’a tunanin zaka zoba” Ranar graduation d’in Cutie na guda ace banzoba ai Abu baiyi dad’iba yanzu dai ki shigo mu tafi gida ma ida maganar a hanya ko”to my yaya bari naje nakira Amma Tana barin wajen ya zagaya ya shiga mota.

Aira na komawa khady tayi mata Dariya tace “ummm kwt har anfara love kenan kice mu fara shiri kece bikin farko a mate “harara ta galla mata tace “sa’idinawa kawai yaya nane to sannan tace muntafi sai mun had’e online “tukwana sukayi hug din juna suka rabu Amma na baya Aira na gaba haka suka tafi a hanya sai satar kallonta yake harsuka isa ba mai cewa uffan sunzo daidai bakin gate din inna sukaga fitowar motar Abba ta gate d’in gidansu cikin faduwar gaba Aira tayi k’asa da kanta dan kar Abba yaganta abunda bata saniba tuni yaganta saida taga wucewarsu tukwana ta dago tana sauke ajiyar zuciya Shidai Arman girgiza kai kawai nan ya gyara parking a waje Amma ta fita tare da cewa thnks Aira zata bude motar taji kulle juyowa tayi ta kalleshi saita sakar mai murmushi shima ya mayar mata tare da cewa.

“Ina kika saka wayarki jiya nayi ta kira a kashe”uhm yaya wlh wayarce kasan boyeta nake bana yawo da ita ko tsakar gida dan kar wani yagani shiyasa tana locker d’ita tun jiya sai da zamu sch nadaukota dan muyi hotuna “.

“Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “nazata ba lafiya shiyasa na taho saida nazo nan nake tambayar haidar a bangaren inna yacemun kuna sch yau kuke last paper “wayyo yaya wai saboda baka sameni ba a waya kawai ka taho i’m sorry “ta fad’a ta na langabar da kai”Shitttt Kin manta bakya laifi komai kikayi daidaine my cutie “sannan ya dauko wata karamar waya daga cikin kwali tana gani ya daga ya saka wani sabon sim card tukwana ya bude ta yace “amshi wannan karamace saikidinga yawo da ita yanda duk sanda na kira zan sameki “murmushin jin dadi tayi tace Thnks my yaya”banson godiyarnan fa daman kinsan yau kuke graduation shine baki sanar daniba “uhm yaya na manta shiyasa “Allah bada sa a Ya fitar da sakamako me kyau kawai yace sannan yace “zan wuce dear baki bukatar komai”Eh yaya bana bukatar komai ganinka ma ya wayadas Bazaka shiga ku gaisa da inna ba “dazu mungaisa ai zanje na hutane kafin gobe na wuce “kamar zatai kuka tace “yaya gobe kuma yayi kusa ai”Zandawo soon yanzun akwai aikin da na baro shiyasa I am sorry gobe idan ba jirgin Safe zanhau ba zanbiyo muyi bankwana idan kuma na samu na safe na wuce kawai “hawaye ne suka fara zubar mata tace “shikenan yaya Allah ya kiyaye ya tsaremun kai “handkerchief ya d’auko ya fara share mata hawayen ya ce “Idan nazo kinamun kuka idan zan koma zandaina yawan zuwa dan bakisan yanda nakejin kukanki a cikin zuciyata ba “cikin sauri ta had’iye kukanta da take shirin cashews’

“sorry yaya bazan sakeba banson kana nesa dani ne shiyasa idan ka tafi yaushe zaka dawo “shima ji yake kamar yayi kukan yace “nafi kowa bukatarki a kusa dani dan bayanda zanyine next week insha Allah zanshigo na kwana biyu “to my yaya Allah ya maidoka lafiya “ki kulamun da kanki kinji my cutie “murmushi tayi tace “kaima ka kulamun da kanka sun dan taba hira kadan tukwana yayi mata bankwana ya wuce ji suke kamar karsu rabu da juna.

Aira koda ta shiga gida bata iske kowaba sai Ummy da Haidar da amma da suka dawo tare “Ya Ummy ina y’an gidan naga ba kowa bangaren inna ma bata nan”ta fad’a tana Waige waige “Suntafi kai Mamy asibiti “wara idanu tayi tace “Asibiti kuma me ya sameta “Haihuwa zatai “langabar dakai tai tace “wayyo Allah sauketa lafiya ranar bangarensu ta kwana sai addua take Allah sauke mamy lafiya dakyal bacci b’arawo yayi awon gaba da ita.

************

Arman kai tsaye guest house dinshi ya wuce dan yasan ya biya ta gida Mummy saisunji dalilin da yazo to yace musu saboda Aira ko me hakan yasa ya wuce chan bayan yayi wanka t-shirt kawai ya sanya da gajeran wando fresh milk kad’ai yasha tukwana yabi lafiyar gado dan akwai gajiya sosai tattare dashi yau jinshi yake cikin farinciki saboda ya hadu da Airanshi lumshe ido yayi a hankali ya ce “I love her so much Cox she’s beautiful “tunowa lokacin da yaganta cikin unifoam yake kyakkyawar fuskarta kawai yake ta hangowa da yanda take sakar mai murmushinta mai narkar da zuciya tuno lokacin da ta rungumeshi yayi ji yayi tsikar jikinshi ta tashi kamar wanda aka tsunkula haka ya zabura rumtse idonshi yayi sosai kafin ya bude su mikewa yayi ya dauko wani hotonta sosai tayi kyau cikin Wata black laffaya daga gani hoton bai jima ba kafe hoton yayi da idanu bako kiftawa kafin ya fara shafa hoton yana murmushi shi kad’ai yace “I love you my Aira ina sonki sosai Airata ki soni please ko kadan ne yafada yana marairaicewa (🤣nikam nace Arman karfa ka haukace)rungume hoton yayi a haka baccci me dad’i ya daukeshi cike da mafarkin Airanshi.

*********
Washegari Su Aira su na bacci Ummy ta tashesu cikin murna tace ku tashi yanzu mama ta kira Mamy ta haihu “Aira kamar an tsikareta haka ta tashi tace “da gaske Ya Ummy me ta Haifa”nima ban tambaya ba yanzu dai Mama ta kira tace da asuba ta haihu mu gyara gidan tare da Laure(yar aikin su)ba jimawa zasu dawo.

Cikin murna Aira ta tashi da dinga murna nan suka gyara gidan wajejen 12 su Mamy suka dawo gida inna dauke da jaririn mamy ko duk tayi lakwas Aira sai murna take ganin k’anin nata shima fari me kyau dan duka d’iyan Mamy su ukkun fararene Haidar ne ma baiyo hasken mamy sosai ba nan yan barka da yan uwa suka fara shigowa.

Aira ko bayan flowers ta koma domin kiran Arman taji ya tafi ko zaizo dan taga har anyi la’asr tana sand’o ta ciro k’aramar wayar da ya bata daman ta hardace number dannawa kawai tayi saitaga yamayi mata save da My yaya murmushi tayi tanajin karason Arman na ratsa kowani sassa na jikinta saida kiran ya katse kafin ta kara kira taji kiranshi ya shigo murmushi jin dadi tayi tare da kissing d’in wayar tace I love you my yaya tukwana tayi picking……….✍🏿

Manage ba yawa 😊

Share saboda Allah 👏

🅿️……………15&16

Daga dayan bangaren Arman ya ce “Hello Cutie ykk ” lfyqlau yaya harka tafi ko”ta fad’a cikin sigar shagwaba “Yanzu haka ina Abuja my cutie jirgin 9 nabi shiyasa bansamu nazo nayi maki bankwana ba”.

“Ayya to Sannu ya gajiyar hanya “Alhmdllh ya fad’a yace Yadai Naji kamar kina cikin farinciki my cutie Shakomun ” Dariya tayi jin ya ce Wai shak’omun ta ce “Yaya Mamy ta haihu fa “.

Daga bangarenshi kamar tana ganinshi ya zaro ido ya ce “da gaske cutie Ah dole muyi farinciki me muka samu” Namiji ni nama zaci mace zata Haifa na samu y’ar uwa kawai sai ta haifi namiji”ta fada tana turo baki .

Dariya yayi har tana jiyowashi cikin waya sosai k’uruciyarta ke burgeshi komai ya fito daga bakinta fad’a kawai take cikin shagwaba ta ce ” Dariya ma kakemun ko”Sorry my Beauty Kece kikaban Dariya kince ke mace kikeso ko?”Eh yaya ni mace nakeso ” To yanzu shikenan tunda Mai faruwa ta faru saimuyi addu’ar idan Kikayi Aure Haihuwarki ta farko ki haifo mana mace mai kama da ke ko?wara idanu tayi kamar yana gabanta kunya duk tabi ta lullubeta ga yanda yayi maganar ya d’an kulle mata kai “Ki haifo mana?sai muyi addua?Aranta take maimaitawa me yake nufi ?

tsinkayar muryarshi tayi da cewa ” Yadai cutie kikayi shiru”Uhm “kawai tace duk kunyarshi ma takeji” Shiko bangarenshi da gangan yayi mata har yanzu yana so ya furta mata Kalmar so amma ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar nuna mata k’arara yanda zata gane ko baice yana sonta ba ta d’auko hanya.

Jin tayi shiru ya sanyashi sauya maganar da cewa”Ki d’auko mun hoton kanan namu ki turoman”Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sauya maganar ta ce “To yaya Anjima zand’aukarma” Hango Ummy tayi na nufo wajen cikin Sauri ta ce “Yaya sai anjima Ga ya ummy nan ta maza ta katse wayar ta boye bayanta.

” Ummy ko tab’e baki tayi Dan ta ganta sarai ta ce “Kidaibi A Sannu rawar kan nan taki karta kaiki ta baroki Manya ma Abba ya bida bare ke tsirit” Aira ko kauda kai tayi ta na gunguni Saida taga wucewarta tukwana ta mik’e ta sanya k’aramar wayar a jikinta tayi bedroom d’in Mamy ta k’ara yimata ya jiki ganin d’akin da mutane ya sanya ta juya ranar duk sanda taso ta dauki jaririn hoto a wayarta ta turamai gagara tayi.

Sai washe gari wajen 11am taje gaishe da Mamy ta tarar da Ita ta na Toilet ga Alamun wanka take kuma jaririn na kan Bed shi kadai cikin Sauri ta Ruga part din inna ta ciro wayarta dake locker ta boyeta a jikinta koda ta koma tayi sa a har lokacin Mamy wanka take cikin Sauri ta fiddo wayar ta shiga d’aukar babyn hoto a snap sosai yake yin kyau.

Cikin Sauri ta bud’e data ta shiga ta turama Arman hotunan Sannan ta shiga status tayi status daman bata d’auki number kowa na gidansu ba Dan haka ba Wanda yasanma tana da waya bare har Susan tana chat tana gama dorawa ta sauka ta maza ta kira Arman tana lek’awa Kar wani ya shigo ta na kara wayar a kunne yana d’auka cikin Sauri ta ce .

“Na tura maka hoton ka hau ka gani ” rikicewa tayi ganin Fitowar Mamy tayi tsaye bakin bathroom d’in ta na kallonta maza tayi cikin Rashin gaskiya ta kashe kiran Tare da Boye wayar a bayanta “Wace waya ce na gani a hannunki?ta tsinkayi muryar Mamy ” .

kafin kace me idonta sun cika da hawaye ta fara in ina karya ma take so tayi abun bata saba ba ta kasa “Mamy ta daka mata tsawa ta ce ” nace wayar uba waye na gani hannunki mik’omun wayar Mamy ta fad’a ta na nufota Tashi tayi tana ja da baya ta ce”I m sorry Mamy bazan Sake ba”me nace kinyi da zakice bazaki sakeba kuma wlh na k’ara magana baki mik’omun wayar nan ba zanmiki abunda baki tunani”Tuni Aira ta fara Kuka.

tsawa Mamy ta k’ara daka mata ba arziki ta mik’a mata wayar ta na yayyarfa hannu kamar wacce aka daka “jujjuya wayar Mamy ta fara cike da mamakin ganin wannan tstsadar wayar Dan taga a Instagrams ana tallarta kudinta sun haura 700k ” Kallon tuhuma ta kalli Aira dashi ta ce “Wayar wacece?Tawace Mamy Dan Allah kiyi hakuri kar Abba yaji ” .

ta fad’a cikin kuka “Salati Mamy ta rafka ta salamce ta ce ” Na shiga Ukku ni Rahama Aira lalacemun kikeso kiyi Ki rik’e har wayar kusan 1 million a gidan nan batare da sanin kowaba Aira kunyata ni kikeson kiyi uban wa ya baki wayar wannan me tsada kuma banason kimun k’arya wlh kika kuskura kikamun k’arya saina lillisaki kuma na kira babanki na fad’a mashi maza fad’amun ubanwa ya baki yanzunnan ” Tuni cikin Aira ya fara d’urar ruwa kuka ta k’ara fashewa dashi to ita me za tacewa Mamy Arman zatace ya sai mata kowa ……….✍🏿

*Tofa Fans ku taimaka ku bawa Aira shawara ta shiga matsala wa zatace ya saya mata waya 😰😢gaskiya ni harta bani tausayi*

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/1, 18:30] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………17&18

……Bazaki d’aga baki kimun magana ba dukanki nayi da zakumun kuka”Mamy ta fad’a cikin b’acin rai” Aira ko kuka kawai take ta na yarfe hannu Dan tasan Mamy bata fiya mata haka ba Dan bata iya b’acin raiba.

“Okay bazaki fad’amun ba kenan tunda ni kin rainani bari na kira Abbanku saiki yi mishi bayani ta fad’a tana d’auko wayarta” Aira kamar wacce aka zabura haka ta zabura tareda Rugawa wajen Mamy ta rik’e hannunta ta na kuka ta ce “Mamy Dan Allah karki fadamashi zan fad’a maki wlh y’anzu Yaya Arman ya sayamun”

ta k’arasa fad’a ta na hawaye” Arman?Mamy ta maimaita tana mata wani irin kallo,Saurin sakin hannun Mamy tayi tare da ja da baya ta ce “Dan Allah Mamy karki dakeni bazan sakeba” Arman Mamy ta k’ara maimaitawa zaunawa bakin gadon tayi tana jujjuya wayar na y’an sakanni kafin da d’ago ka kalli Aira dake tsaye tana kuka ta ce “Shi Arman d’inne zai sai maki wannan wayar a wani dalili?Wlh Mamy shi ya sayamun”.

” chabd’i Mamy tafada tukwana ta ce “Fad’amun yanzunnan wace alak’ace ke tsakaninki dashi Dan ubanki ,meye ke tsakaninku ” Mamy wlh ba komai kawai zumunci muke dashi Mamy kin mance Yaya na ne fa”Ubanki ke da yayan Duka su sauran y’an gidan ba y’an uwanshi bane ko ke kad’aice y’ar uwarshi alak’ar dake tsakaninki dashi suma haka take su me yasa bai saya musu wayar ba saike kad’ai ya zab’a ya sayawa”.

kasa tayi ta kanta tana hawaye ta ma rasa wace amsa zata ba Mamy “koma meye ke tsakaninku ai zamuji sannan ki gaggauta mayar mashi da Wayarshi muddin kina gujin b’acin raina marar jin magana kullum kinfison ki dinga jawomun magana yanzu da Abbankune yaga wayar nan da ni kaina basaikinjamun ba ki mayar mashi da Wayarshi ko ki kiramunshi ni nafada masa yazo ya Anshi abunshi bansan d’iyan iskanci idan kuma ba haka ba sainayi kwatsakwatsa da wayar”.

cikin Sauri ta d’ago ta ce “a a a Mamy wlh bama saikin kirashi ba zan mayar masa da yadawo insha Allahu nagode da bazaki fad’awa Abba ba ” Tsaki Mamy taja ta mika mata wayar tare da d’aukar jaririnta da ya fara tsala kuka Aira ko cikin Sauri ta amshi wayar ta sakata A siket ta fice daga bedroom d’in ta na fitowa palour ta tarar da Ya Umar da matarshi (Babban yayansu ss ne ya na aikine a Kebbi tare yake tafiya da matarshi khadija sai idan sunzo su sauka gidansu))cikin murna tace Lah ya yaushe kukazo”Murmushi yayi ya ce “Yanzu muka Iso little sis ” sannunku da zuwa yaya Anzo lafiya ya hanya “Alhmdllh ya Rashin ji ya na nan ko yayi sauk’i ” Dariya tayi ta ce “Yaya ai ni bana Rashin ji ” Zadai kidaina y’ar gidan Inna “kallon Khadija tayi ta ce ” .

Ina yini Aunty”Lafiya qalau “ta fada a takaice tab’e baki tayi Dan daman Chan haka halin Matar Yayan nasu take ba mutuncin kirki ya isheta ba shiyasa ma ko gidanta basa zuwa ” Bari naje na fad’awa su Mama kunzo “.

“Aira tafada ta na nufar d’akin Mama da Mamy duk ta fad’a musu zuwan su ya Umar a tare suka fito su Mamy na musu barka da zuwa Suka amsa cikin sakin fuska har khadija Dan Duk iskancinta bata fiya yiwa su Mama da Mamy ba khadija ce Ta amshi jaririn hannun Mamy tare da yiwa Mamy barka tace ” Allah raya “nan Shima ya Umar yayima Mamy barka Daman sunji haihuwar ne yasa suka taho Aira ganin Mamy da Mama sun d’auki hankalinsu ya Umar yasa tayi saurin fita ta nufi part d’in Inna.

bedroom d’inta ta shige tare da rufewa ajiyar zuciya ta sauke ta ce ” yau na tsallake rijiya da baibai da Mamy ta fad’awa Abba Aida na shiga ukku”kiran Yaya Arman tayi kamar zatayi kuka ta fad’a mashi komai kuma Mamy ta ce Wai na maido maka wayar ta fad’a kamar zatayi kuka”.

Daga bangarenshi ya ce “bana kyauta a maido mun Kuma bana kyauta na amsa ko wani nayiwa bare ke Dan haka karma ki maidomun ” To yaya ta ce fa Ta Kara ganinta Fasa ta zatayi kuma ina tsoron karta Fad’awa Abba “Arman duk Haushi ya isheshi yana jin haushin yanda iyayen Aira ke nuna mai kamar ba Wanda bai had’a komai da ita ba kamar ba kanwarshi ba Mamyn ma da yake ganin dama dama a Wajenta itama nema take ta kwatsa” .

Ya fada cikin ranshi a fili ko tsaki yaja baimasan yayi ba ya ce “Kinji dai abunda na fad’a sanin kanki ne bana magana biyu ta rage ruwanki ko ki yadda ita ko kiyi sadaka da ita ko ki fasata komai kikayi taki ce Dan haka karki k’aramun magana akan dukkan wani abu da zan baki ko na baki hope kinfahimta ” Cikin sanyi Aira ta ce “Na gane Yaya yi hakuri Bazan sake ba nasan ranka ya b’aci Naji kamar kana fad’a “saiyaji ta d’an bashi tausayi yasan halinta Sarai akan wannan D’an abun saita yini ta na kuka hakan ya sashi kwantar da murya ya ce .

” raina bai b’aci ba my cutie yaya za ayi my Aira ta ta b’atamun rai Y’ar lele na ai bakya laifi “Ajiyar zuciya ta sauke ta ce ” Uhm “Shima Uhm” din ya mayar mata yana mata Dariya ita ma dariyar tayi tanajin sanyi Cikin zuciyarta “ARMAN ne ya ce ” Naga hoton k’ananmu yayi kyau naga ma kamar yaso ya sato kamannin my cutie d’ina kodan ya samu ya d’anyi farinjini wajen y’an mata ammafa my Cutie d’ina ta fishi kyau nesa ba kusa ba .

“Dariya Aira tayi sosai ta ce ” Allah my yaya kace na fishi kyau”Eh mana ki daina hadamun kanki dashi ma “Dariya tayi ta ce ” kai yaya Shima fa yana da kyau sosai”idan babu ke ba amma idan Dake musamman kuka Kara fuska mummuna zakiga ya koma kin manta Kyanki dishe kyan wasu yake “Dariya tayi sosai ta ce ” to ni da kai kuma wa yafi kyau”Shima murmushi yayi ya ce “Ni mana Aini na taimaka maki da har kyan naki ya fito idan ba haka ba Ai kema kyan naki da baikai haka ba nine na taimaka maki”

Cikin shagwaba ta ce “Kai yaya wlh nafika kyau” Dariya yayi sosai take burgeshi idan tana shagwaba hakan yasa ya biyeta sukayi ta gardama yana mata Dariya saida suka kwashe kusan awa Ukku suna waya batare da sun gaji da Hira ba daga karshe ma Video call suka koma Dan yau Arman baida aiki yana gida Nan Aira tayi tamai labari Dan rufo d’akin ma tayi Dan kar wani ya shigo ko da zasuyi salla kin kashewa sukayi kamar suna tare Ranar haka suka yini Dukansu sai farinciki suke Dan Aira harta manta ma da Maganarta da Mamy koda zasuci abincin dinner tare sukaci Shima ya zubo nashi ita ma ta zubo nata suna ci suna kirga spoon Din da kowa yayi ta waya dukda basu da cin abinci sosai ranar saida sukaci sosai.

har wajen 11pm suna video call idan zatayi wani abun taje tayi ta dawo Shima haka Saida yaga bacci ya d’auketa murmushi yayi yana kallonta ta waya Yajima yana kallon yanda take baccin yana karajin sonta na ratsa kowani sassa na jikinshi saida yaga wayar ta birgima Alamun baccin nata yayi nisa tukwana ya kashe ganin baya ganinta ranar dukansu kwanan farinciki sukayi batare da tunanin wata damuwa ba.

Ana jibi suna Aira na bangaren Inna wajen la asr ta fito ta nufi bangarensu tana shiga taga Yaya Aysha na fitowa daga mota driver na fito mata da akwatinta Aida gudu Aira ta Ruga ta Rungumeta Itama Aysha Rungume kanwar tata tayi cikin muryarta mai cike da iyayi ta ce “I really miss you my Fav sis ” Itama cikin murna Aira ta ce Miss uh 2 my Fav Aunty da bakinan gidan ba dad’i nafi kowa rashinki “Murmushi Aysha tayi ta ce ” Ai yanzu nadawo Sis mundaina Rashin juna ko”Gyada mata kai tayi ta na amsar hand bag d’inta ta rik’e mata Aysha tabs driver umarni ya shiga da akwatinta ciki tana dafe da Aira suka nufi haryar ciki Sai murnar ganin y’ar uwar tata ta ke Aira ta ce “Aunty Ya malesia d’in wai kina nufin harkun gama karatun gaba d’aya ” Alhmdllh sis karatu kam mun kammala sai Kuma bautar Kasa burin Abba yau ya cika “Cikin murna Aira ta ce ” Wow congratulations sis ta fad’a tana Kara Rungumeta Itama Rungumeta tayi ta ce “Thnks my sis yanzu kuma saura ku munyi waya da Ummy ai kwanaki take fad’amun kun kammala s s c e d’inku sai jiran result.

” Wlhko Aunty mungama kai wlh Aunty Ummy bata da kirki duk lokacin da nace mata ta had’ani dake ko a waya Ne wlh kiyawa take Dana dame ta ma cewa tayi “karna k’ara damunta tunda ba waya ta bace nima nayi zuciya nasayi wayar kuma wai kinma sauya layi itama bata dashi” Dariya Aysha tayi ta ce “Kai Ummy ta na nan da halin nan nata kenan Wai har yanzu Abba bai baku waya ba ki ce dai har yanzu tsautsatsauran ra ayin nan na Abba na nan na Sai an Je university idan yanzu baku fara rik’e waya ba fisabilillah yaushe zaku rik’e Baku sanin halin da duniya ke ciki Gaskiya Abba yanzu An waye y’an 10 years ma suna rik’e waya bareku “.

murmushi kawai Aira tayi batace komai ba shiyasa duk yayyinta tafi son Aunty Aysha jininsu yazo d’aya sosai ga tana mugun sonta tana tunanin yanda Aysha ta k’ara wayewa Dukda daman a waye ta tafi amma k’asar wajen nan da taje karatu ka k’ara kilewa….✍🏿

*Share plx*

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/1, 22:52] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………19&20

Suna isa a palour suka tarar dasu Mamy da gudu Aysha taje tayi hug d’in Mamy da Mummy tana musu iyayin tayi missing d’insu Mamy na murna tana mata oyoyo” Sai sannan Aysha ta lura da mutanen dake palourn wasu baki ta gaishe su Ganin jariri a hannun wata ya sanya ta kalli Aira ta ce “Sis wa ya haihu” .

Mamy Airata bata amsa “wow Kice nazo A daidai Allahsa dai ba ayi suna ba Kuma shine ko a fad’amun sannan taje ta amshi jaririn tace ” wow ammafa yaso yayi kama da sis Aira “Haka kowa yakecewa Cewar Mamy Mama ko Kallon Aysha kawai take da shigar dake cikinta K’ank’anin kaya ne jiens da Riga danma bata da jiki hakan yasa basu d’ame ta ba ga wani uban glass da ta dageshi saman goshinta .

Aysha black beauty ce tana da kyau ba fara ba ce Amma bata da bak’i sosai irin choculate colour d’innan amma daga ganinta kasan akwai iyayi da malle ” ita Mama duksai kunya ma ta kamata Ganin da mutane itako Aysharma ko a jikinta hakan yasa Mama ta fara aika mata da Harara ganin batasan da ita ba yakeba ya sanya Mama kyaleta saida tagama iyayinta tukwana taja Aira sukayi Bedroom d’insu .

koda su Ummy da Amma suka ganta suma sai murna suke suna daka tsalle suna murnar ganinta Aira tace “Su daina karsu b’alla mata yaya” suna haka Mama ta shigo ta kalli Aysha ta ce “Ke yanzu Aysha ba kunya haka kika ketaro tundaga wata k’asa kikataho a haka kamar ba y’ar musulmi ba ” Aysha na tubure fuska ta ce “Haba Mama daga dawowata Ko Sannu da zuwan kirki fa bakimun ba zaki fara mun fad’a me shigar nan tayi kuma” .

Mama ta girgiza kai ta ce “Ai daman Nasan sai Abunda yayi gaba a nan ma ya aka k’are bare anturaki wata k’asar da ba uwa ba uba ba mai tsawatar maki dole likkafa taci gaba shiyasa tun farko banso Alhaji ya tura ki wata k’asa karatu ba to wlh mu nan ba Chan bane Dan haka kar in Kara ganin kinyi wannan shigar kinfito wannan shigar ko tsakar gida Inda kunya kinyita bare waje idan kin gama hutawa kije abincinki na dining Mama ta fad’a tare da barin d’akin.

Aysha gunguni tayi kasa_kasa saida Mama ta fita ta ce ” Aifa nadawo wlh su har yanzu sunk’i su waye mu Chan ba ruwan wani da wani ina laifin wannan shigar ta fad’a tana tab’e baki “(nikam hajjo nace ikon Allah Ayshar nan za Aje da ita ).

Bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin Wata doguwar Riga (Abaya)mai shegen kyau maron kallonta Aira tayi ta ce ” Wow My Aunty kinyi kyau”Lakutar kumatunta tayi ta ce “Thnks kanwa Sannan ta fiddo wata irinta ta mik’awa Aira ta ce ” ga taki nan daman tare nayi mana Anko ki shirya kafin na gama cin abinci zamu fita outing “.

Tsalle Aira ta daka tare da Rungumeta ta ce ” Thnks Aunty shiyasa nake sonki da yawa tukwana ta maza ta cire kaya ta d’aura towel tayi bathroom danyi wanka Amma ce da Ummy suka hade baki wajen cewa “mu ina namu” Bansayo da kuba da gani sai Besty na zamuyi ankon”Amma tace “Aifa kindawo yanzu za a fara gwada mana wariyar da aka saba Ummy ko taja k’aramun tsaki ta ce ” ko kunya wai wani bestynta k’anwarta ta Ukku amma kamar wata sa arta duk saisun rainaki”.

murmushi Aysha tayi ta ce “Kede kina nan da halin nan naki na shegen son girma to meye a ciki kanwar tau ta ukkun saime ke nan gani kike kinma girmi kowa To nidai karkimun Rashin kunya tunda ba a girmanba ” Tab’e baki Umny ta yi ta ce “Ni mancewa ma nake kingirmeni Duka shekara biyun da wani Abu sannan ked’in mate Dina ce Ke bare kice kinfini aji nima dai yanda kika gama Degree d’innan nan da sati Ukku zan kammala saime banbancin kinje Malesia ne ni kuma ina B U K saime a ciki”.

Dariya kawai aysha tayi ta wuce parlou ta ce “Kanki akeji ta na fita ta tarar da bak’in duk sun tafi kai tsaye dining ta nufa taci abinci me rai da lafiya Aira ko cikin Sauri ta fito daga wanka ta shirya cikin doguwar Riga irin ta Aysha sosai tayi mata kyau ta fito kamar wata balarabiya sai baza k’amshi take hoda da kwalli kawai ta shafa sai lipstick sosai tayi kyau ta dansa madaidaicin takalmi marar tsawo ta yafa k’aramun belt din Rigar kwantaccen gaban gashinta ya fito wa iya zubillahi zo kuga yanda Aira tayi kamar wata balarabiya Tana fitowa ta tarar da Aunty Aysha ta kammala cin abincin kallonta tayi ta ce “.

wow my kanwa kinganki kuwa “Sai sannan su Mamy suka Kalleta Suma sunga tayi kyau Mama tace “wannan gayu haka sai ina kuma” Murmushi tayi ta ce “Mama Aunty Aysha zan raka Unguwa” Mama tace “Tofa daga dawowa bako hutawa k’afar yawo” Mama ganin gari ne fa kawai zanyi”ta fad’a ta na ruko Aira ta gyara mata yafa Belt din nata ta ce “Yau akwai kashe hotuna sis ta fad’a suna Tafawa” Mamy ce ta ce “Aifa K’auna ta dawo Aysha da Aira tsohuwar zuma” Dariya Aysha tayi ta ce “Fad’i da k’ari Mamy Aini duk ita kadai nafi missing” .

Mama ko ta ce “Ai Halin ne yazo d’aya shiyasa ” dariya Mamy ta ce “Kuma Hakane yaya Halin Aira da Aysha duka d’ayane ba abunda Aira ta rago na Aysha Dariya Aysha da Aira sukayi.

suna haka Abba ya shigo palourn Bayan ya zauna har k’asa ta duk’ursa ta gaishe da Abba ya amsa sai farinciki yake ya ce ” An kammala karatu ko Aisha Allah ya miki albarka Allah baki abunda kike nema duniya da lahira yanda kika farantamun Allah baki masu farantamun miki nagode da yanda kikayi mun biyayya akan komai baki bani matsala ba karatun da na turashi shi kikayi ba tare da kin bak’antamun ko an tab’a kawomun koken ki ba Ko ki biyewa samari dukda dai ba yawo nake dake ba Naji dadi sosai Allah maki albarka”

“Ameeen Aisha ta amsa sosai tayi farinciki da Addu’ar mahaifin nata sannan ya ce ” Kamar yadda Yayyunki Maryam da umar Bayan kammala Degree d’insu na kaisu Aikin Hajji da umrah insha Allahu kema ki shirya zaki Fara zuwa umrah kafin lokacin aikin Hajji yayi Allah maki albarka sosai Aysha tayi farinciki marar musaltuwa ta ce “Abba nagode nagode Allah saka da alkhairi Allah ya k’ara budi” Aira ko tana tsaye duk tayi sanyi tasan Abba da ita ya ke na cewa “aysha bata bashi matsala ba Dan haka yakece ma Aira idan yana mata fada yace ” ita ce Ke neman bashi matsala cikin y’ay’anshi .

Amma hakan bai hanata taya y’ar uwarta ta farinciki ba jita ke Daman Ita “Saida Abba ya gama sanyawa Aysha albarka tukwana ya tashi zai shige ciki A hankali Aira ta ce ” Ina yini Abba”ba tare da ya Kalleta ba yace “Lafiya” Dan tun sanda yaganta motar Arman Bayan dukan da yayi mata amma ta raina shi bata daddara ba yanzu ya tsaya yana tarasu ita da shi ya ga gudun ruwansu.

.sosai Aira bataji dad’in yanda Abba ya amsa mata ba saida ta Goge hawaye Aysha ma saida tayi mamaki Dan tasan yanda Abba keson Aira dukda Abba bai gwada banbanci tsakanin y’ay’anshi Amma a yanda tasani yafi nunawa Aira so saisuka Alak’anta hakan Da sunan mamansu ne da take dashi “Saida suka fito Aysha ta ce ” sis ya naga Abba bai kulaki ba “Wlh nima bansaniba Aunty ” .

tafada tana Goge hawayenta “makullin key Aysha ta amsa hannun driver ta tuk’a su suka tafi Aira na front seat gidan kawar Aysha suka fara zuwa basu jima ba Suka fito tukwana Suka wuce Wurin wani shak’atawa sosai Aysha tayi ta kashe musu selfie da wayarta iPhone 12 pro ita da Aira sosai suke kyau kamar wasu twins saidai kowa ya gansu yasan Aysha ta girmi Aira a shekaru Bayan nan su shiga wajen shan ice cream suna cikin sha wayar Aysha tayi ringing.

ta d’auka ita dai Aira bataji me Dayan bangaren aka ceba saiji tayi Aysha ta ce ” Okay Baby ka shigo zaka ganmu da marun Abaya”bata katse wayarba suka hangoshi yana nufo su aysha murmushi ya kasa barin fuskarta harya karaso ya zauna chair din kusa da ita.

“Aira dai na kallonsu kawai take Shima ba laifin yana da kyau gashi Daga gani kamar akwai Naira Aysha cikin farinciki tace” Nayi missing naka my baby Tunfa sanda ka kawomun ziyara rabon da muga juna kusan 5months ta fad’a tana shagwaba “Shima cikin so da k’auna ya Ce ” Miss you too my prince’s kinsan yau ba cikin k’aramun farinciki nake ba na ganinki sannan ya kalli Aira da take kallonsu ya ce .

“Dear ko ita ce k’anwar tamu da ake ji da ita ” Aysha tace “Eh baby itace ” Aira ko “yafada yana kallon Aira murmushi tayi ta ce ” Eh ina yini “Lafiya qalau kanwarmu y school gsky yayarki Naji dake fa kusan kullum saitayimun maganarki” murmushi Aira tayi ta ce “Ai nima ina ji da ita sosai ” Aira najin Aysha da Saurayinta na zuba love ita dai cikin ranta mamaki take daga karshema barin wajen sukayi suka koma Dan nesa da ita tana nan zaune rik’e da wayar Aysha taji wani yayi mata sallama ba tare da ta d’ago ba ta amsa .

“zan iya zama Hajiya” Ba matsala ta fad’a ta na kauda kai”y’an mata bazaki kalleni ba “yafada yana murmushi kamar bazata d’ago ba sai kuma ta d’ago ta ganshi wani dogo mai matsakaicin jiki ya sha shaddarshi me kyau.

kauda kai tayi yana b’ata rai Dan bata son takura ” ina yini Hajiya Sannu da hutawa”Lafiya “ta fad’a ta na kauda kai” Kamar bazai magana ba saikuma ya ce “Tun d’azu na hangoki ina son nayi maki magana kikamun kwarjini na kasa Sai yanzu dak’yal nayi shahada na taho Dan na fad’a maki abunda ke cikin zuciyata Gaskiya tunda nake bantab’a ganin macen da ta burgeni ba sama dake nayi yawo wurare da dama Amma bantab’a cin karo da macen da sace zuciyata kai tsaye ba idan ba ke ba fatan baza a watsamun ruwa a k’asa ba za a amshi tayi na hannu bibbiyu” .

Aira ji tayi kamar ta shakeshi Dan Haushi tace “d’an naci a zuciyarta amma a fili cewa ta yi” Kayi hakuri ni bana soyayya a gida an hanani”Saiki fara a kaina na tabbatar zan sanyaki farinciki “tsaki taja cikin ranta ta ce ” maye “Nan yayi ta mata magana da magiya tayi banza ta Kyaleshi Suna Haka Aysha ta dawo ita kad’ai ga Alamun saurayin nata ya tafi Tana ganinta Aira ta mik’e ta ce ” Aunty Aysha mu tafii”.

Kallon Aysha saurayin yayi ya ce “Auntynmu ina yini” murmushi Aysha tayi ta ce “lafiya qlau brk da hutawa” yawwa Aunty gwarama da Allah ya kawomun ke nasan zaki taimakamun ki shawomun kanta tun d’azu nake nan amma ank’i bani dama gimbiyar tawa dai ga alama akwai mulki “Dariya Aysha tayi ta ce ” karka damu Insha Allahu zanmata magana haka take “kai amma nagode Wlh Aunty kinyi taimako amma ya sunan gimbiyar tawa” Hajara Amma ana ce mata Aira”wow so sweet name “nikuma suna na ABUBAKAR YUSUF MADUGU”ni D’an sokoto ne nazo bikin aboki na ne ni bakone a garin nan.

Ah Babban suna sunan Abbanmu”cewar Aysha ” kice ina da manyan y’ay’a to yanzu Aunty yaza ayi naga kamar Sauri kuke zaku wuce ko zaki taimakamun da number ta”wlh bata da waya yanzu kam”to Dan Allah kozaki taimakamun da taki saimuyi magana”ba matsala Aysha ta fad’a tare da karantomai number ta.

rafar y’an 500 ya Aje musu Aysha taki amsa dak’yal ya samu ta amsa tare da mashi Godiya ya wuce “Aira ko duk Haushi ya isheta saitajima mutumin duk ya bata Haushi ga haushin Aunty Aysha da ta biye mai.

A mota Aira ta kalli Aysha ta ce ” Aunty wannan Wanda yazo wajenki d’azu waye”baby Abdulkarim kenan Boy friend d’ina ne kuma mijina insha Allah tafada tana murmushi wara idanu Aira tayi cike da mamaki ta ce “To Aunty yaushe har kuka hadu keda kika tafi karatu kuma nasan kafin ki tafi Abba baya barin kowa zance ” Dariya Aysha tayi ta ce “Aira kenan kede kawai ayi sha ani amma ni tun ina s. S three nake soyayya ta a b’oye kawai dai ina nunawa Abba ne amma soyayya ta nake ke yanzu fa kai ya waye akanme ace Y’an mata gand’ama gand’ama damu ace ba samari yaushe garin zai waye my Abdul a Airport muka had’u dashi tun lokacin tafiyata karatu ta farko tun daga lokacin muke soyayya ina sonshi sosai Shima haka yana ziyarta ta chan akai akai munshaku sosai Dan tun bayanzu ba yakeson muyi aure na ce yayi hakuri ya jira lokacin da Na gama karatu gashi yanzu kuma alhmdllh yanzunma maganar ce mukayi nace ya samu Abba yanzu ba wannan maganar ba Wannan Sadiq din yana da hankali wlh sosai ga nutsuwa ki nutsu Kuyi soyayyarku saina dinga had’aku kinji kanwata baki da matsala dani ba meji”.

Turo baki Aira tayi ta ce “Ni Gaskiya Aunty kibar zancenshi ni baimun ba bama wannan ba kinsan Abba ya hanamu nikuma bazanyi Abunda ya hanaba Gaskiya gwara Na hakura nayi karatuna kawai yanda yakeso din”galala Aysha tayi tana kallonta tana tuki ta ce “Amma wlh Aira baki da wayo to maza kiyi sakakka irin na Aunty Maryam ta biye Dokar Abba harta gama Karatu bata da saurayi Abba ya had’ata da d’an Abokinshi dukda ba wani sonshi sosai take ba ta hakura danma yanzu suna son juna Amma ai Kinga batayi mata dad’i ba b’ata auri Wanda takeso ba To wlh kika biye kema haka zakuyi nidai ba ruwana tunda na kama My Abdul Dina” .

Tab’e baki Aira tayi ta ce “Uhm Aunty yaya Arman fa Yama hanani kula samari fa kuma nayi mashi alkawari bazan kula kowa ba ” galala aysha tayi ta na kallonta ta ce “Ke amma sakaraice ma Hajara har wani Arman ne zai hanaki kula samari to idan baki kula samari ba ubanwa zai Aure ki ko Shi Arman d’inne zai Aureki iyeeeeee kujimun ikon Allah ” Aira daram Gabanta yayi irin mummunan fad’uwa jin Kalmar Aunty Aysha ta k’arshe “Ko shi Arman d’inne zai Aure ki?????!!!!!…………..✍🏿

*Ni da Yaya Arman Book1 ne Free Book2 Ba free book ba ne Na kud’ine Book one zai k’are ne daga Page 30 daga nan za mu shiga Book two kai tsaye Ba tare da Gargada ba zaku iya fara biya tun kafin a k’are Book one zaku turo katin MTN #200 ta wannan number 07026166536 tare da shaidar biyanku ta 07026166536 y’an niger kuma ku bini pc ta number nan dana d’ora +2347026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain a ciki*

_Normal group = #200_

_PC = # 300_

_V t u # 300_

*Sainajiku masoyan asali na tabbata bazaku tab’a nadamar sayan littafin nan ba darajarshi tafi ta #200 kachal na barshi ne hakan kawai saboda kauna da soyayya ga masu buk’atar a tallata musu hajarsu su tuntub’eni kai tsaye a number wayata kamar haka 07026166536 zamuyi ciniki cikin sauk’i insha Allahu sainajiku Masoyan asali na tabbata bazakuso ayi zazzafar doguwar tafiyar nan babu ku ba*👯‍♀️🙇🏽‍♀️🙇🏽‍♀️🙇🏽‍♀️

*Share fisabilillah*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/2, 09:31] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………21&22

Sosai gabanta ya fad’i sai yanzu ma ta tuna da Dan ayi Aure ake soyayya Shiru tayi ta na ta sak’e sak’en a ranta Tanajin Aysha nayi mata fad’a tayi mata banza ta kyaleta Har suka isa gida Suna isa Aira kai tsaye Part din Inna ta nufa Dan lokacin har Angama kiran magriba.

“Bayan tayi salla a palourn zaune tayi tana lazumi kafin ta tashi innace ta shigo ta na fad’a tana cewa ” Haba nidai wlh ana wahalshe dani ace Dan kinibibi Kamar Rahama god’ai god’ai da ita Bata iya wankan jariri ba koma ta iya Dan iskanci batayiwa d’anta wanka ba saini to zanga Ranar da babuni ubanda zai dinga musu ai duk gani na ne ya kawo hakan malalata kawai tun daga zamaninmu aka dena haifo mutanen kwarai Wai kamar Rahama da in Auren k’auye ake y’arta ma saita Aurar da Y’a Amma tsabar iskanci sai an wahalshe dani “.

Aira na jinta tayi mata banza Dan ba kowani fad’an inna take tankawa ba ” Tsaki Inna taja ta kalli Aira Dan ta tsani tana fad’a a mata banza in ba a bata hakuri ba gwara ko tankawa kayi ta ce “Ke kuma y’ar gidan malalaciya Daga gidan ubanwa Kike Rabonki da nan tun azahar ina kikaje ” Tsaki Aira taja tare da tashi tayi bedroom d’inta ta na jin Inna na cewa “Uwarki da ubanki kikayiwa tsaki ba niba fitsararriya mai ido a tsakar ka ” Murmushi kawai tayi dan yau ba y’an fad’an take ba shiyasa bazata biyewa inna ba ta na shiga d’akin ta kulle Dan yau batajin ko dinner zata iyayi sbd ciye ciyen da sukayi a waje.

Ta na zuwa Sauri tayi ta cire kaya ta fad’a toilet ta yi wanka tana fitowa tasa kayan bacci ana kiran isha I nan ta tada salla saida ta gama ta tashi ta ninke hijab ta d’auko k’aramar wayarta da babba ta baje kan Gado wara idanu tayi ganin missed call d’in Arman rututu a k’aramar wayarta cikin Sauri ta Danna mashi kira saida ta katse tukwana ya kira cikin Sauri ta d’aga ta ce “Hello my Yaya ina yini” Ajiyar zuciya taji ya sauke daga bangarenshi ya ce “Nayi ta kira Baki d’auka ba ina kika shige” Sorry yaya wlh Aunty Aysha ce tazo shine na rakata unguwa”Yaushe tazo?Dazu “da ina da ina kikaje” gidan kawarta muka fara zuwa daga Chan muka wuce wajajen shakatawa amma waje biyu kawai mukaje muka dawo”Ita Aysharce daga dawowarta zata d’aukanmunke ku tafi yawo me yasa da zaku tafi baki fad’amun ba kafin nan ma wasu kaya kika fita da su?

“sorry yaya na manta ban fad’a maka ba Bansa matsatsun kaya ba wlh doguwar Riga ce a ma baje take Aunty Aysha ta sayo mana Nida ita idan kana soma saina turo maka hoton ka gani”ba sai kituroman ba na yarda Amma fad’amun Gaskiya akwai saurayin da yace ya na sonki?gabanta ne ya fad’i sai sannan ta tuna da Sadiq

cikin y’ar in ina ta ce “ya ya ba kowa” Aira kenan a tunaninki Idan kikayimun k’arya bazan gane ba baki saba karya ba Dan haka duk sanda kikayi ganewa nake oya fad’amun Gaskiya”Kamar zatayi kuka ta ce “To yaya bazakayi fad’a ba ” Eh bazanyi ba gsky kawai nakeson ki fad’amun”

Ajiyar zuciya ta sauke nan ta bashi labarin had’uwarsu da maganarsu da Aunty Aysha bata b’oye mashi komai ba “Sosai ranshi yayi mugun b’aci cikin fad’a da masifa ya ce ” Ita Aysharce daga zuwanta har zata fara koya miki biye-Biyen Samari,”

“yaya Dan Allah kayi hakuri “Tafada kamar zatayi kuka ” Cutie bakiyimun komai ba Amma Aysha tayi mugun bani mamaki Yazama dole gobe na shigo garin na kad’e mata warning Sannan duk sanda ya kirata ta baki ko kika bashi number ki kukayi mu’amula ko soyayya Allah ya isa ban yafe miki ba kinsan dai Mahimmancin Allah ya isa sarai(😆😂oh ni Arman hada Allah ya isa sai kace ubanta).

Sosai Aira tayi mamakin kalaman Arman wai Allah ya isa Amma dayake tasan idan ranshi ya b’aci saida lallab’o tafi kowa iya zama dashi shiyasa ta ce “To Yaya Bazanyiba Goben da gaske zaka zo” ta fad’a ta na son sauya maganar “Eh cutie zanzo Amma kwana biyu zanyi na juya” Cikin murna Aira ta ce “Amma Naji dad’i my yaya Allah ya kawomun kai lafiya” Ameeen my Cutie ya fad’a tare da cewa Good night kiyi bacci yanzu nasan kingaji”murmushi tayi mai cike da so da k’auna ta ce “Have a nice dream yaya saida Safe”.

Tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita washegari Suna Yaro yaci suna Abdullahi za ana cemai Ameer sosai gidan ya cika ranar da mutanen Arziki Kanwar Abbansu Aira ma dake Aure a Kaduna Mama Halima tazo tare da y’arta Hafsat sa’ar Aira ce kuma kawarta ce sosai Ranar Aira jinta take cikin Farinciki duk inda tayi Hafsat na biye da Ita Da misalin k’arfe biyar na yamma sosai Aira tayi kyau cikin Wani tsadaddan lace black and blue sai ratsin pink sosai ya amshi farar fatarta batayi wata make up kamar koda yaushe hoda da kwalli kawai ta shafa

Sosai tayi kyau kamar ka saceta ka Ruga a lokacin ta na bedroom d’inta dake d’akin inna Bayan ta gama shiryawa ta feshe jikinta da turarruka masu k’amshi drawer gefen gadon ta ta bud’e cike yake choculate kala kala kamar kaje Kanti duk Wanda yaya Arman yake saya mata ne manya biyu kawai ta d’auko ta fara sha Dan yunwa takeji sosai tunda safe rabonta da abinci Dan ita daman haka take batacin abincin sabga

Nan Tasha hotunan ta sosai tana gamawa tayi status a what’s app tana ganin amfara comment akan hoton ta maza ta kashe datar ta sauka wayarta ce k’arama tayi ringing ganin Yaya Arman ne ya sanyata picking cikin Sauri ta ce “Yaya Badai har kazo ba ” Daga bangarenshi ya ce “Yanzu haka ina bakin gate d’in gidan Inna ” Tsalle ta daka ta safko daga Gado ta ce “Wow Sannu da zuwa yaya ka shigo mana” bazan shigo ba cutie Naga akwai mutane a wajen kinfi kowa sanin ban fiya son taron mutane ba Kidai fito Kawai ”

“to yaya ga ni nan “ta fad’a ta na saurin Saukowa daga gadon cikin Sauri ta boye babbar wayarta a locker ta rik’e k’aramar takalmi da gyale ta zira tayi Sauri ta fito a palour ta tarar da mutane gaishesu tayi ta fita A farfajiyar gidan ta gamu da Hafsat Hafsat ta ce ” Aira ina zuwa naga kina shirin fita”Taho ki rakani wajen YAya Arman zani”

Dariya hafsa tayi ta ce “Ah koda nace wannan show d’in kice love za a sha wannan k’auna keda Yaya Arman har yanzu akwaita kenan” Murmushi Aira tayi tanajin dadi har cikin ranta ta kama hannun Hafsa ta ce “Ai kauna ta na nan Hafsa *NI DA YAYA ARMAN* Mutu ka raba Dariya Hafsa tayi ta ce ”

Allah yarda ni daman najima da sanin soyayya kuke wlh”wara idanu Aira tayi ta ce “Rufamun Asiri waya fad’a maki soyayya muke kawai dai k’auna ce muke ” Uhm idan tayi tsami dai maji cewar Hafsa suna fita suka tarar dashi a cikin mota back seat driver na gaba Zage glass din motar yayi ya tsaya kallonta sosai ta tafi dashi ba k’aramun masifar kyau tayi mashi ba baisan lokacin da ya sakar mata murmushi ba Itama mayar mashi tayi Dan sosai yayi mata kyau cikin Dakakkiyar shaddarshi da Tasha aiki fara Hafsa ce ta ce

“Ina yini Yaya” Lafiya qlau Hafsa yau a gari”murmushi tayi ta ce “Wlhko Yaya Suna mukazo tare ma muke da Mama ” Aira ce ta shagwabe ta ce “Yaya bazaka fito ba wai ka hakimce a cikin mota” Dan murmushi yayi ya ce “So kike na fito a gama kalle maki ni wannan wankan nakine ke kad’ai” Dariya tayi ta ce “Wayau dai kawai cikin shagwaba ta ce ” ni fa yunwa nakeji ba abunda naci tun dazu”wara idanu yayi ya ce “Subhanallahi garinya aka barmunke da yuwa” Yaya ban iyacin abincin Taro shiyasa”ai zama bai ganmu ba maza-maza shigo muje restaurant yanzunnan”

ya fad’a yana bud’e mata Kofar da yake ciki Kallon Hafsa tayi ta ce “Sis taho muje” Girgiza kai Hafsa tayi ta ce “A a kije kawai Sis Mama ta ce Zan rakata gidan Daddy su gaisa Dan muna sa ran gobe zamu koma ” To shknan saimun dawo Aira ta fad’a tana shigewa batare da shakkar komai ba Restaurant mafi kusa ya kaita saida ta tabbatar da ta koshi tukwana suka fito Suna shiga mota Yaji kiran daddy yana d’agawa nan Daddy ke shaidamai akwai Wani metting da za ayi karfe Tara a Zaria kome yake ya maza ya tafi Zaria yanzu yaje ya wakilceshi da to Arman ya amsa mashi Kallon Aira yayi da take latsa Wayarshi ya ce.

“Cutie
zamuje mu saukeki a gida yanzu Tafiya ta kamani zanje zaria zan wakilci Daddy wani metting ” Yaya Dan Allah ka tafi dani Daman bantab’a zuwa Zaria ba Saidai mu wuce ta cikinta in zamu wuce Dan Allah kaje dani”tafada ta na marairaicewa “Rik’e hannunta tayi ya ce ” Kiyi Hakuri my cutie Amma bazaiyu na tafi dake Zaria da Daren nan ba Kuma idan munje dinma bamusan tsawon lokacin da za a d’auka ba kiyi hakuri next time idan nazo zan daukeki da kaina na kaiki kiga ko ina da rana ”

“nidai Allah yaya ban yarda ba katafi dani kawai ” Dafe kanshi yayi ya ce “Aira case Ce ” to so kike na tafi dake na ja maki fad’a a gida Kin manta dare ne Zaiyi”Yaya wlh har muje mu dawo ba maiji ni daman b’angaren Inna nake kuma bamai sanin ma Inda naje”Ba yanda Arman baiyi ba Dan kar ya tafi da ita amma ta nace daga karshe ma kuka tasa mai hakan yasa ba yanda ya iya dole suka tafi tare tana ganin an tafi ta sauke ajiyar zuciya sai murna take daman ita tanason tafiyar mota a rayuwarta

karfe takwas da wani Abu tayi musu a Zaria Rasa Inda ma zaikaita yayi hakan yasa ya yanke shawarar kaita gidansu Wani abokinshi kafin su gama metting d’in Abokin nashi ma bai gari mamanshi ta amshesu hannu bibbiyu Daga nan Arman ya wuce wajen metting d’inshi Hankali kwance nan Aira taci abinci sai nan nan y’an gidan suke da ita Dan Arman ya ce Musu kanwar sa ce Aira ganin Har 10Arman baizoba tana ta jiranshi Har bacci yayi awon gaba da ita.

Arman ko metting d’in saida ya jasu Har 11:30 hankalinshi duk ya rabu gida biyu ga tunanin Aira daya baro.

Koda ya koma maman su abokinshi hanashi daukarta yayi ta ce su barwa safiya ba irin yanda bai yiba amma ta hana tace bazasu tunkari hanya da Daren nan ba ga kidnappers da sukayi yawa suyi hakuri su barwa safiya ba yanda Arman ya iya sai hakura yayi yaje ya kama hotel ya kwana Aira ko tana baccinta bata San wainar da ake toyawa ba saida ta farka da asuba Ta ganta a wannan gidan Kan Gado Sosai gabanta ya fad’i ta ce.

“Na shiga ukku ba dai a gidan nan na kwana ba ” Sai sannan ta tuno da gida ba Wanda yasan Inda take Cikin firgice ta tashin hankali ta tashi Kanwar Abokinshice ta shigo Dan tada ta tayi salla Tazo ta isketa harta tashi Wanka Aira taje tayi ta mayar da kayan jikinta ta fito suka bata break fast mai rai da lafiya taci tana gamawa Arman yazo Godiya sosai Arman yayi musu tare da alheri Aira ma Godiya tayi musu dukda firgicin da take ciki.

B’angaren gidan su Aira basu lura da Aira bata gida ba sai wajen 11pm Inna ta rikice ta nufi part din su Mamy ta fad’a musu Aira da bata gida Nan aka shiga nemanta lungu da sak’o ba a ganta ba Sosai suka shiga tashin hankali musamman Mamy hada kukanta Har 1 ana neman Aira ba a ganta ba ranar kwanan zaune sukayi Bcci saidai barawo.

Hafsat ce da tasha baccin ta wajen Asuba ta farka Taji kamar ana neman Aira lokacin duk suna palourn Inna sunyi jugum Hankali tashe har Abba daya kasa zaune ya kasa tsaye inna ko inbanda kuka ba abunda take Hafsa dake bacci jikin mamanta ta ce “Mama Wai Aira ce bata dawo ba kowa” Duk kallonta mutanen dake palourn sukayi a tare sukace “ko kinsan Inda take ne Hafsa” Tashi tayi ta ce “Eh jiya dai da Yamma wajen magriba Yaya Arman yazo Nina rakata wajenshi tace yunwa takeji zaikaita joint taci abinci da tare zamuje saina ce Zan raka mama gidan Daddy shiyasa lokacin da muka dawo ni nazaci ma harta dawo”

“Salati dukansu sukasa musamman Mamy kuka ta fashe ta ce ” Na shiga ukku Airance tabi Arman suka kwana waje”Abba ko Shi kadai yasan yanda yaji a cikin ranshi safa da marwa kawai yake yama rasa wani irin hukunci zai yanke mata “Inna ko Salati ta rafka ta ce ” ku bari sudawo muji dalili Dan nasan Tarbiyar Mujahed da Hajara sarai bazasuyi wani abunda bai kamata ba ni har hankali na ma ya kwanta tunda tare take da d’an uwanta”duk kallon mamaki suka bi inna dashi saikuma suka Jinjina kai Abba ko ya kasa magana sai safa da marwa da yake “Mama Halima ce ta ce

” Dan Allah yaya ka kwantar da hankalinka Tunda dai anji Inda take sai a jirari dawowarta”Cikinsu ba Wanda Abba ya tankawa shi kadai yasan Zafin da yakeji cikin ranshi.

Aira ko tun a mota take yiwa Arman kuka tasan yau Abba yasan bata kwana gida ba ta shiga ukku kasheta zaiyi tun yana Lallashinta har ya rabu da ita 7:20 tayi musu a Kano Kai tsaye gidan Inna suka isa Ba yanda Arman baiyi da ita ta fita ba amma taki sai kuka ta ke “tausasa murya yayi ya ce ”

“Kinga irin haka nake guje miki shiyasa Banso kika Bini ba Amma kika dage yanzu ki kwantar da hankalinki ki shiga nasan ma bazasu Gane ba Tunda Bangaren inna kike kuma inna ba d’akinki take shiga ba shiru Aira tayi ta na tunanin kuma hakane k’ilama Allah ya rufa mata asiri basu sani ba Kallonshi tayi cikin sigar shagwaba ta ce.

“To bazaka rakani ba yaya” Idan na rakaki wani zai iya ganinmu Amma idan kikashiga ke kad’ai ba mai ganewa zaisu zaci ma kinfita ne sayan wani Abu Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Hakane Yaya to sai Anjima ” Murmushi yayi mata ya ce “kije ki k’ara hutawa saimunyi waya Ko na shigo”

gyad’a mai kai tayi bata samu damar ma mayar mai da murmushinba ta nufi bakin gate a hankali ta kwankwasa mai gadi ya fito ya bud’e yana mata kallon mamaki.

Ajiyar zuciya Aira ta sauke ganin farfajiyar gidan ba kowa Arman ko yana ganin shigarta ya sauke ajiyar zuciya driver ya jashi suka tafi Aira ko gabanta na fad’uwa haka ta tinkari k’ofar d’akin.

saida ta tofa addu’oi tukwana ta yi bismillah ta tura kofar a hankali kamar Munafuka tana bud’ewa tayi turus ganin Duka mutanen Gidansu a palour zata iya cewa a rayuwarta bata tab’a shiga tashin hankali irin na ranar ba baya tayi da Sauri tare da Niyyar Rugawa Kafin tayi taku d’aya Abba ya chafkota cikin zafin nama da b’acin rai yayi mata wani irin
Mahaukacin ruk’o tare da d’auketa da wani gigitaccen mari…………..✍🏿

*Kamar yanda na fad’a a page 30 In-Sha-Allah zamu gama book one ma ana free page kenan ku hanzarta biya tun kafin a kammala book one if you want to subscribe pay #200 katin MTN to 07026166536 hoton katin ko transfer masu Vtu suma zasu tura ta number tare da shaidar turowan amma su #300 wanda basu da buk’atar group ma ana ta pc za a tura musu suma #300 zasu biya ta number da na d’ora zasu tura y’an Niger kuma kumin magana ta wannan number +234-7026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain na 200 sai a saka ku Group karku manta book d’innan garab’asa ce babba da na sakeshi a 200 kachal Darajarshi tafi ta 1k Ni da Yaya Arman ba a fara komai ba bama a shiga wasan ba wannan duk somin tab’i ne hmmmmm wasan na nan gaba wannan shi ake kira koda kud’inka saida rabonka wannan salon na musamman ne masoyan asali ku harzarta ku biya nasan babu wanda zaizo ayi doguwar tafiyar nan batare da shiba saina jiku*💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾

*Share fisabilillah*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/4, 22:40] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………23&24

Aira jinta tayi cikin Wata duniyar ta daban kafin tayi ihu ya k’ara kifeta da wani marin da yafi na d’azu k’ara ta fasa cikin gigicewa Abba ko ranshi yayi kololuwar b’aci Wayar dutsin guga ya ciro Tare da wullata kanta ya bugi da Bango Nan ya hau lafta mata ta ko ina ihu take tana neman d’auki Abba ko baimasan tanayiba Dukanta kawai yake kamar baitab’a saninta ba.

Duka mutanen dake d’akin saida suka tausaya mata Dan ko jakki aka yiwa dukan nan Yagamu da azaba dukda haushin Aira da Mamy keji Amma saida ta tausaya mata Cikin kuka taje ta rik’e Abba ta ce “Dan Allah kayi hakuri Abbansu Karka kasheta” .

Bankad’eta Abba yayi Kad’an Ya hana ta fad’i cike da masifa ya ce “Ai gwara ta mutu Da ta d’auko mun magana mutuwar ta ta fiyemun rayuwarta ” Cigaba da laftarta yayi Aira ko suma ce kawai batayi ba Inna ma Tana kuka ta taso ta dinga ba Abba hakuri ya kyaleta Baimasan ta nayi ba.

Dak’yal dai Mama Halima ta rik’e Hannun Abba ta ce “Dan Girman Allah Yaya ka rabu da ita wlh ta daku karka mata illa nasan bata kyauta ba da ciwo amma kayi hakuri ka zauna ” Dak’yal ta samu Abba ya zauna yana huci Aira ko Wajen Aunty Aysha ta ruga da gudu ta Rungumeta ta na kuka itama Rungumeta Ayshar tayi tana kuka Dan Duk wani mai imani saiya tausayawa Aira irin bugun da Tasha.

Cikin tsawa Abba ya ce “Munafuka K’aramar karuwa Har kinyi girman da zakibi namiji kuje ku kwana waje ni zaki tozarta ki kunyata a idon al’umma ni da daraja da kimata da komai “Abba ya fad’a yana nuna kanshi” Aira ko sosai Kalmar k’aramar karuwar tayi mata ciwo Kara fashewa tayi da kuka magana ma ba kasa Mamy ma kanta saida Kalmar Tayi mata ciwo “Fad’a sosai Abba ya shigayi Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba yana cewa .

” Duk cikin y’ay’ana ban haifi y’ar iskaba tun daga kan Yayyunki saike y’ar karshe_Karshe Zaki gagareni ki bani matsala Tun yaushe na rabaki da d’an iskan yaron nan baki rabu dashi ba Abu har yayi k’amari kun Fara kwanan hotel hotel k’aramar yarinya dake ni zaki daukowa magana to baku isa ba Dagake har shi har ubanshi nafi k’arfinku wlh idan kuma da kene aka had’u aga bayana to ta Allah ba takuba kinja kin fita daga raina harna Fara tantamar ma Anya Nina Haifeki kuwa”.

Innalillahi wa inna ilaihiraji’un Mama Da Mama Halima suka fad’a a tare Mama ta ce “Haba Alhaji wannan wace irin magana ce Kai da ranka ya b’aci baka iya control d’in bakinka wannan Maganar Ba Abun yi bace ” Mama Halima kuka ta sa ta ce “Haba Yaya Wannan wace irin rayuwace kaida d’an uwanka Amma kun zama kamar Annabi da kafiri kawai kun biyewa shaid’an yayi tasiri a cikin zuciyar ku Wlh saboda ku yasa ko garin nan Banason zuwa kun Riga kun b’ata mana zumunci Kun b’ata zumuncin y’ay’anmu “.

Mamy ko Itama kukan take sosai Maganar Abba ta k’ona mata rai cike da b’acin rai Ta tashi ta sab’i d’anta ta ce “Idan ba kai bane ubanta saika fad’i uban nata kokuma da ita nazo daga gidanmu Abun kuma ya tashi daga kanta ya koma kaina sharrima Ake neman K’ullamun kenan saikaje asibiti a Auna jininka da nata idan ba y’arka bace saika nemi ubanta ka maida mai”

sannan ta kalli Aira tace ” Ke kuma hankalinki ya kwanta saiki zubda ruwa a k’asa kisha kinja Anyimun wulakanci burinki yau ya cika”Ta k’arasa fad’a cikin kuka tare da barin Palourn.duk saida sukaji ba dad’i musamman Aira da ta k’arawa kukanta Volume inna ko tsaki taja ta ce “munafuka duk ba kece silar komai ba “.

Abba baiko kula mamy ba saima ya tashi ya ce zanje wajen ubanshi na Mashi warning Rikeshi Mama Halima tayi ta ce Dan Allah kayi kayi hakuri kar kaje Bari a kirashi yaya Kabir d’in yazo a sasinta tunda haka kakeso wannan Maganar Ba ta waje ba ce tukwana ya zauna yana huci.

Aunty Halima ta kira Abbansu Arman Bayan sun gaisa ta ce “Yaya Dan Allah kazo gidan Inna yanzu tana son ganinka da Sauri” Subhanalla innarce ba lfy ko wa cewar Daddy”Lafiya qalu yaya kaidai kawai kazo “To gani nan yanzunnan” Cikin Sauri Daddy Ya taho Dan a tunaninshi Inna ce ba lafiya Kafin minti Ashirin Ya Iso gidan.

Suna zazzaune Kamar y’an zaman makoki Daddy Ya shigo Security d’inshi Ya umarta su tsaya a waje Har PA d’inshi Yana shigowa ganin Inna ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Ai nama zaci Inna ce ba lfy hankali na harya tashi” .

Lafiya qlau Yaya ka zauna “Bayan Daddy Ya zauna Mama Halima na kuka ta ce ” Yaya Dan Allah Dan Girma Allah ku taimakemu ko ba Dan mu ba Dan Allah Kuyi hakuri ku janye wannan gabar Dake tsakaninku da tashin hankalin nan kamar Ba y’an uwa ba karku manta yaya ciki d’aya ba wasa ba ne Wlh kullum Da Bakin cikin wannan abun nake kwana nake tashi Ku taimakemu ku fahimci Juna na tabbata hatta ran iyayenmu dake k’asa basajin dad’in abun nan na tabbatar da suna raye da bazaku mana haka ba “.

Abba ne Ya tashi cikin fad’a ya ce “Daman Halima dalilin da yasa kika kirashi kenan to babu wani saurin shiri tsakani na da mutumin nan Sannan ya kalli Daddy Ya nunashi da yatsa ya ce .

” Kashe ne zan maka Akan Lalataccen d’anka Jiya ya d’aukar mun y’a sun kwana waje Dan haka kajawa Dan iskan d’anka kunne ya rabu da y’ata na rabasu sunk’i rabuwa nan gaba na k’ara ganinshi da ita Zan d’auki mummunan matakin da kowa saiya koka Dan wlh ka sake d’anka ya lalatamun tarbiyar y’a ko yayi mata ciki Kotu ce Zata rabani dakai”.

Cikin b’acin rai Shima Daddy Ya tashi cikin masifa ya ce “Daman saboda wannan dalilin ne kuka kirani sannan Shima ya nunashi da yatsa ya ce ” Karka k’ara kiran d’ana da lalatacce y’arka ce lalatatta tunda har ka kasa bata tarbiyar da har ta bishi ta kwana Sannan kai zakayiwa y’arka kashe ba ni ba Idan ka isa da ita Kai zaka rabata dashi ba ni ba bazan rabasu d’inba Kuma da kake maganar abun Kunya ,y’a mace ke abun Kunya ba d’a namiji ba Dan haka idan ma yayi mata cikin kai da y’arka kukayi abun Kunya ba ni da d’ana ba Hope ka gane ”

Yana gama Fad’ar Hakan Fuuu yayi waje Duka Wanda ke Palourn Babu Wanda bai koka ba Musamman Mama Halima da take ganin tazo kiran gyara gashi an k’ara b’arna Shima Abba cikin b’acin rai da k’unar rai ya tashi ya fice daga palourn Tabbas yau Aira ta Ja Amfad’a mashi magana masu ciwo Aira ko Sosai take kuka ita kam ta shiga Ukkunta ya zatayi da rayuwarta da gudu tayi d’aki ta haye Gado ta na kuka mai tab’a zuciya.

Yinin ranar Kowa sukuku ya yishi Haka dai akayi soye Rai duk babu dad’i musamman Mamy da zata iya cewa ranta yafi na kowa b’aci Aira ko ranar yinin D’aki tayi ko abinci bata iya ciba Tasha kukanta Har ta gode Allah ga shaftun bulalun Abba da suke mata mugun rad’ad’i.

Daddy ko cikin b’acin rai ya nufi gida yana zuwa Ya d’auke Arman da Mari Arman da jin Marin kawai yayi a sama dafe kumcinshi yayi ya tsaya yana kallon Daddy karo na farko kenan a tsawon Rayuwarshi da Daddy Ya tab’a daga hannu ya dakeshi cikin fad’a Daddy Ya ce.

“Ubanme yasa ka d’aukar musu y’a ina ka kaita har kuka kwana Waje Kaja yau an fad’amun maganganu masu zafi a saboda kai To daga yau bakai ba y’arsu na Rabaka da ita indai nine mahaifinka bakai ba ita tunda ba kanwar uwarka ba ce “Arman sosai ranshi ya b’aci Daman shi bai iya b’acin raiba ” yace “Daddy daman A saboda Aira ne ka dakeni?Cikin fad’a Daddy Ya ce ” A saboda ita d’in zan iya k’aramaka fiye da Wanda na maka Tukunnama fad’amun wata alak’ar ce Ke tsakaninku da bazaka iya rabuwa da ita ba ”

“Daddy sonta Nake Kuma Auranta zanyi itace matata bazan rabu da ita ba kome zakuyi Saidai Kuyi Amma bazamu tab’a rabuwa da junan mu ba Fad’anku bazai shafemu ba ” So Mummy da Daddy suka fad’a a tare Bai jira sun Sake cewa wani Abu ba cikin b’acin rai yayi Hanyar waje Mummy na kirashi ta na cewa

“Son dawo ina zaka kuma” Dan tasan Halin d’anta bai iya b’acin raiba musamman da har daddy ya mareshi shiyasa basusan b’ata mai rai Dan Duk maganar da tazo bakinshi fad’a yake “Amma ko juyowa Arman baiyiba Mumy zata bishi Daddy cikin fad’a ya ce ” ke kuma ina zaki bishi ki rabu dashi mana yaje duk inda zaije yaro ne”

“Cikin marairaicewa Mummy ta ce “Alhaji kasan halin Arman Da zuciya ka bari na bashi hakuri” Tsaki Daddy yaja Ya wuce yabar mata palourn Mummy bin ARMAN tayi lokacin da ta fita harya ja mota yabar Harabar gidan ba yanda ta iya ta koma ciki cike da tunanin Arman d’in Daman Aira ce yake so shiyasa duk lokacin da ta yi mashi maganar Aure yake cemata yana da wadda yakeso cikin ranta ta ce .

“Kaikam son Soyayya batazo maka cikin Sauk’i ba ka kamu da son wacce iyayenku bazasu bari ku mallaki juna ba Sosai tashiga damuwar halin da D’an nata zai shiga Dan tasan Arman ba k’aramun so ne yake yiwa Aira ba Tunda har ya iya furtawa iyayenshi kai tsaye.

Arman kai tsaye Airport ya nufa Yana zuwa ya yanki ticket na zuwa Abuja Allah ya taimakeshi akwai jirgin da zai tashi Kafin 1 hour jirginsu ya d’aga Abuja.

B’angaren Aira har 6 tana daki ga wani zazzafan zazzabi da ya zubar mata Aysha ce ta je ta sameta Da kyal ta lallab’ata ta fito tana rik’e da hannunta a palour ta zaunar da ita ta na mata Sannu tukwana ta d’auko abinci ta dinga bata a baki dak’yal ta samu take karb’a kadan taci tace ta k’oshi.

Man zafi Aysha ta d’auko ta dinga shafa mata tukwana ta b’alla mata magani dak’yal ta samu ta Had’iye kallon Aunty Aysha tayi ta ce ” Thnks Aunty”Amma ce dake zaune ta ce “Sannu Aira” tsaki Aira taja tare da kauda kai Dan Duk haushin mutane take ji”.

jan bakinta amma tayi shiru dan tasan Aira akwai huce haushi,Hafsa ma dake gefen Inna ta ce “Ko baki lafiya Sis” Itama banza Aira tayi mata ,Aiysha ce ta ce “Kwanta Kan kujera ki huta kinji kanwata” gyada mata kai tayi tare kwanciya ta kalli sama ta rufe idanunta Tunanin yaya Arman ne kawai yazo mata a kwalwa taya ma zaiyu ace su rabu da juna duk wannan dukan da tasha batajin zata iya rabuwa dashi ga haushinta na zarginsu da Abba sukayi Abba hada cemata karuwa sosai ranta ke mata k’una gashi tasan Momy ba k’aramun fushi tayi da ita ba .

Hafsat ce ta kalli inna ta ce “Inna Dan Allah Na tambayeki Allahsa ki fad’amun” Inajin Hafsatu fad’amun tambayarki”Inna wai me ya had’a Daddy da Abba basa jituwo nidai tsawon Rayuwata tunda na tashi a haka na sansu Kuma Idan Na tambayi Mama dalili saitak’i fad’amun ta ce Wai Family issue d’insu ne basainajiba Abun Yajima yana d’auremun kai Dan Allah Inna fad’amun”

“Gyara Zama Inna tayi tare da cewa “Aiko yau zakiji labari tiryan tiryan y’ar nan ki gyara zama kisha labari inbanda abun Halima meye abun boye a Lamarin nan da duniya ma ta sani sannan ta fara da cewa……….✍🏿

*Tofa Abu ya rikice ya kuke tunanin Abba da Daddy zasu d’auki al’amarin nan kowannansu yad’au zafi*

*Ya makomar soyayyar ARMAN da AIRA zata kasance nan gaba Bayan al’amari ya k’ara rikicewa*

*Tofa ga wata sabuwa Hafsa tayi tambayar da kowannenku ke jiran Amsarta bari mu gyara zama Dan shan labari wajen Inna Dan nasan harkun k’agu kuji dalilin wannan gabar*😂

Share fisabilillah

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/5, 18:30] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️…………..25&26

…..Kabir Da Abubakar y’an uwane Wanda suka fito ciki d’aya ma’ana uwa d’aya uba d’aya su Ukku ne a wajen iyayensu Abubakar ne Babba Sai Kabir da Abubakar ya bashi shekaru Ukku a duniya sannan Autar su Halima da har an cire ran Haihuwarta.

Saida khabir ya bata sama da shekaru sha biyu Halima Nada wata Ukku Allah yayiwa mahaifinsu Malam Umar rasuwa Mahaifiyarsu Hajara ita taci gaba da kula da su Iliminsu,cinsu,shansu,suturarsu da koman su Tasha wahala sosai akansu Dan dangin ubansu Tunda mahaifinsu ya rasu basu tab’a taimaka musu da komai ba .

Nida Hajara uwammu daya ubanmu ubanmu daya mu biyu kenan a wajen Iyayenmu Koda Allah yayiwa mijin ta rasuwa Saina dawo Wajenta daman mijina ya jima da rasuwa bantab’a haihuwa ba na d’auki y’ay’an Hajara tamkar nawa suma haka suka daukeni tare muka cigaba da kula dasu har Allah ya kawo girmansu.

Sun taso cikin Had’in kai da son juna Abubakar tun yana Yaro yake da sha’awar siyasa yayinda shi kuma Kabir yake da sha’awar kasuwanci Koda Abubakar ya gama jami’a ya fad’a kasuwanci Sosai ya habaka Inda Har yayi Aure ya auri Zainab y’ar nan kano ce mace mai hakuri Shima Kabir yana kammala karatunshi ya fad’a harkar kasuwanci kafin kace me sun Tara arziki me yawa Su suka dinga kula da ni da Mahaifiyarsu tare da kanwarsu da suke ji da ita.

Shima Kabir yayi Aure ya Auri Fatima y’ar gidan Wazirin Adamawa a Chan ya ganta ya aurota itama mace ce y’ar gidan mutumci ana haka ne Abubakar ya fad’a harkar siyasa yayinda shi kuma Kabir yake cigaba da kasuwancinshi Dan harkokinshima yawaici a waje yake yinsu.

Kabir d’anshi d’aya a duniya Muhajed (Arman )tundaga kanshi bai sake haihuwa ba Abubakar ya rik’e mik’amai da dama a cikin wannan jahar tamu A siyasa kuma ya tab’a Senator A shekarun Baya .

Zainab ta haifamai Yara Biyar Umar,Maryam,Aisha,Fauziya(Ummy),sai autarta Halimatu da aka sanya mata suna na” ana haka ne Allah yayiwa Mahaifiyarsu Rasuwa mutuwar da ta girgiza Al’umma musamman ni da Y’ay’anta munshiga damuwa sosai daga karshe kuma mukayi tawakkali ga Allah Yaranta suncigaba da daukata tamkar uwa Inda Abubakar lokacin da ya Gina wannan gidan Da muke ciki ya waremun bangarena guda Sosai suke kula.dani shida Kabir.

Ana hakane k’watsam Kabir Ya had’u Da Rahama y’ar asalin Garin Agadez Bayan rasuwar iyayenta take zaune wajen Babban Yayanta tare da matarshi dake zaune a nan kano yake kasuwancinshi Fara ce sosai ga kyau irin jajayen buzayen nan masu masifar kyau Tunda ya ganta Kabir ya rud’e ba k’aramun so yake mata ba Nan ya samu suka sasinta ita ma har ta Fara sonshi .

Wasa wasa magana ta fara k’arfi Wanda har iyaye suka shiga Aka kai kud’in gaisuwa wajen yayanta ganin yanda Kabir ya rud’e kullum zancenshi Rahama Ya sanya Abubakar cewa shikam ya kaishi yaga wannan rahamar da zata haukata mai k’ani Nan Kabir ya jashi ya rakashi Har gidansu Rahama Koda ta fito Abubakar ya d’ora ido a kanta Yaji duk duniya baitab’a ganin macen da tayi mishi a rayuwa ba sama da ita

Lokaci guda ya kamu da matsanancin sonta Dak’yal ya iya daidaita kanshi suka gaisa tare da musu fatan Alkhairi Kabir yayi mata bayanin yanda suke da Abubakar ta gaidashi cikin girmamawa Har lokacin ya kasa Daina kallon ta .

ita kanta saida ta tsargu tunda Abubakar ya ganta kullum da tunaninta yake kwana yake tashi Ana Hakane Tafiya Ta kama kabir China akan kasuwancinshi Nan ya mik’awa Yayan nashi ragamar komai game da rahama tare da cemai Dan Allah ya dinga kula mai da ita har ya dawo sannan duk abunda take buk’ata ya dinga zuwa yanaji Dan a lokacin waya bata wadata ba.

Tunda Kabir yayi Tafiya Abubakar ya dinga zarya gidan su Rahama Kulawa ta musamman yake bata fiye da wadda Kabir ke bata Tun bata sakewa dashi har tazo ta sake dashi Cikin Dabara Abubakar yayi yanda yayi ya sace zuciyar Rahama A lokacin taji ba Wanda take so saishi.

nan suka k’ulla soyayya mai karfi wanda har akazo ga maganar Aure dukda yayanta da farko ya hana saida ya lura Rahamar na mugun so shiyasa ya hakura ya ce abubakar ya turo iyayenshi Koda yaxomun da maganar korarshi nayi na shiga f’ada Inda na shiga ba tanan nake fitaba Ba yanda baiyi ya shawo kainaba amma naki Nace ba ruwana a maganar Auren cin amana .

Dangin mahaifinshi ya sama ya saye su da kudi su sukaje suka nema mai Auran Rahama cikin k’ank’anin Lokaci ba ayi wata guda ba aka d’aura musu Aure har lokacin Kabir na China Ranar Da aka daura Auren Ranar ya dawo garin Inda ya tarar da wannnan tashin hankalin Wanda ya girmi tunaninshi Yayanshi uwa d’aya uba d’aya ya ci amanarshi ya Aure mai Matar da zai Aura .

Ranar munga tashin hankalin da bamu tab’a gani ba Dan Kabir dukansu shida Abubakar daman suna da zafin kai Shak’e Yayanshi Kabir yayi Ya hau zaginshi da Tsine mashi Wanda dak’yal na samu maza suka rabasu Tofa tun daga lokacin nan suka k’ulla D’aurarriyar gaba da k’iyayya a lokacin Kabir yafi d’aukar abun Da zafi Inda Yayi Aniyar saiya yi mashi ramuwar gayyar abunda yayi mai.

Rahama da Zainab sun had’e kansu sosai dukansu basu da tashin hankali sosai Rahama ke girmama Zainab haka d’iyan Zainab suna girmama Rahama sosai baka tab’a cewa kishiya da kishiya ne dukda kuwa lokacin Mijinsu Yana rid’in Rahama Dan yaso ya nuna yafi sonta a fili amma rahamar Ta k’iya ta nuna batason gwara ya dinga musu adalci kar ya rikita musu Zama .

Ana Hakane Rahama ta samu ciki Sosai Ya d’ora son duniya akan cikin saikace lokacin ne za a fara Mashi Haihuwa Haka Rahama tayi ta rainon cikinta sosai take samun kulawa daga wajen mijinta da kuma Zainab Dan ni haushinta nake ji tunda ta zama silar had’a y’ay’ana fad’a har cikinta ya isa haihuwa ranar wata Juma a ta haifi y’arta kyakyawa Fara Sol wacce ta dameta fari da kyau Tunda aka haife yarinyar kowa ke sonta yayyinta kamar su cinyeta musamman Aysha .

Ranar suna Yarinya taci suna “Hajara sunan Mahaifiyarsu kenan ” A lokacin da Aka haifeta Mujahid duk Juma a yana kawomun ziyara Da mahaifinshi ya hanashi zuwa kwata_kwata dak’yal da kuka da kuma na nuna mashi Ya daukeni ba uwa ba hakan yasa Kabir ke barin d’anshi zuwa wajena sosai nakeson Mujahid kamar yanda Tunda aka Haifi Hajara nake sonta Dukda dai bana son uwarta data hadamun y’ay’a fad’a.

Koda yaushe Hajara na bangarena inba kuka tayiba akaita wajen uwar sosai Mujahed ke sonta tun tana jaririya Danshi ya sanya mata Sunan Aira daga nan sunan ya bita a lokacin Mahaifin Aira baya hana Mujahid mu’amula da Aira Dan har lokacin yana jin nauyin K’anan nashi yasan shi yayi mashi laifi hakan yasa bai d’auki abun da zafi ba Dan koda Aira ta girma Har fita Mujahid yake da Ita Yayo mata sayayya a saboda Aira Mujahid Koda yaushe da ya dawo daga Makaranta ya na gida na yana like da ita harta girma.

itama kuma sosai ta shaku dashi koda yaushe tana lik’e dashi Dan idan baizoba Haka zatayi ta kuka Ta rikice sai in yazo ake samun Lafiyarta Bayan Haihuwar Hajara da shekaru Hud’u Rahama ta sake haihuwar d’anta Namiji Aliyu Haidar tun daga kanshi kuma haihuwar ta tsaya mata Chak sai yanzu kusan Bayan shekara goma ta sake haihuwar wannan yaron

Koda Mujahid Yaje Karatu k’asar Misra duk hutun da suka samu saiya taho Dan Ganin Aira Haka har ya kammala karatunshi Inda yana gamawa ya samu aiki a CBN Abuja Dan abunda ya karanta kenan har lokacin Mahaifin Aira bai damu da Taren Aira da Arman ba Dan ko da ya samu aiki Abuja tofa duk karshen mako saiya taho yaganta.

Ana Hakane shekaru Biyu da suka wuce Abubakar ya fito takarar gwamnan wannan jahar ganin haka ya sanya Kabir cewa Shima ya samu damar da zai rama Abunda Yayan nashi yayi mashi Shima ya fito takarar gwamna a wata jam’iyar Wanda Duka su biyun aka tsaida y’an takarar gwamna.

Sosai Abun ya bak’antawa Abubakar Nan aka shiga siyasa ba kama hannun yaro dukansu kamar ba y’an uwaba Dan yanda mabiyar kowannensu ke sukar d’ayansu musamman mabiyar Kabir wakoki da maganganu na habaice habaice na y’an siyasa aka shiga yiwa Abubakar ba yanda banyi dasu ba akan cikinsu wani ya janye amma sukak’iya Hatta kanwarsu Halima da tayi Aure ta auri wani soja a Kaduna Inda ta haifi hafsat kusan sa annin Aira ce kwana ashirin Aira ta bata Dan kusan tattare akayi Auren Halima da Rahama Halima yaranta biyu Hafsa itace babba sai kaninta Sadiq ita kanta ba irin tashin hankalin da bata shiga ba akan siyasar da y’an uwan nata suka fito Dan tuni zance ya baza duniya .

zancen Cin Amanar da Abubakar yayiwa Kabir Y’an siyasa sukayi Amfani dashi dukda ba kowa yasan maganar ba amma suka yayata maganar ko ina Wanda da wannan ne suka samu damar kayar da Abubakar siyasa Dan Sun sokeshi da cewa tunda yaci Amanar d’an uwanshi suma talakkawa zai iyacin Amanarsu Inda suka zab’i Kabir a matsayin gwamnan wannan Jahar yanzu.

Abubakar ya shiga tashin hankali ba Kad’an ba akan wannan Abun da d’an uwanshi yayi mashi wannan ya k’ara rura wutar k’iyayyar junansu Wanda Abubakar yakejin tsabar kiyayyar Kabir fiye da wacce kabir yake mashi Tun daga lokacin Abubakar ya raba Mujahid da y’arshi amma sukaki rabuwa kullum yaganta tare dashi saiya daketa Amma washegari sai ka gansu tare .

daman Hajara wajena take tun tana yarinya to anan suke haduwa da mujahid dan baya shiga gidan su Abubakar ya daina yiwa Mujahid magana ya daina Amsa gaisuwarshi Dan k’iyayyar Mahaifinshi Ta shafeshi Mujahid ganin Idan ya gaishe dashi baya amsawa ya sanya ya daina gaisheshi kwata_kwata Duk yanda Abubakar yaso Raba Mujahid da Hajara gagara abun yayi shakuwarsu sai abunda yayi gaba har zuwa yanzu dai ya kasa rabasu.

To Yau dai kinji Dalilin wannan Gabar da k’iyayyar Duka akan mace macen ma Rahama shiyasa kikaga bana son Rahama inbanda ma ina son d’iyarta da me zanyi da Rahama Mayaudariyar da ta raba mana Kan iyalai Duka fa itace munafukar da ta had’a abun nan da batace tana son Abubakar d’inba da duk haka ta faru ba”

” amma Munafukar Mayaudariyar ta tashi daga kan k’ani ta koma Yayanshi ku yanzu duk a tarihi da kuka taba ji ina kuka tab’a ganin Anyi haka “Inna ta k’arasa fad’a tana hawaye Tare da murje ido ta ce ” Ai Tsakani na da Rahama sai Allah ya isa Nasan da Adda Hajara na raye da bazata yarda A auro mata wannan annobar Rahamar ba “Inna takarasa fad’a ta na shaftar Majina”.

Hafsat ce da aka gama bata labari saida tayi hawaye jin wannan sark’ak’k’kiyar ta ce Daman ashe wannan dalilin ne ya had’a Daddy da Abba Jin Inna na shiruftu Daga karshe tana zagin Mamy ya sanyata B’ata rai ta ce ” haba Inna Daga cewa ki bani labari kuma sai kihau kuka da Zage_Zagen Mamy nidai shikenan labarin ya isa Haka ”

“Yoke y’ar nan ba dole na zagi Rahama ba Dole kiga nayi kuka idan na tuna da Abun nan ” Aira da tunda Inna ta fara labarin tana jinta tayi shiru sosai surutun ya dameta saida taga ta fara zagar mata uwa ya sanyata tashi cike da Masifa tana hawaye ta kalli inna ta ce.

“Karki sake zagarmun uwa me tayi maki da zaki hau zaginta tun d’azu fa ina jinki na kyaleki” Cikin masifa Inna ta ce “to Mai ido a tsakar ka ai bansan kin damu da uwar taki ba Sai kin rama mata An Zage ta d’in”To wlh karki sake zagarmun uwa tunda uwa ba fin uwa tayi ba kowa son uwarshi Yake ke da dadi a zagar maki taki uwar”

Aira ta fad’a tana gallawa Inna harara”Kuka Inna ta fashe dashi ta ce “Shikenan yau Hajara kin zageni amma kedai ba y’ar arziki bace tun kina yarinya nake wahala dake naci kashinki naci fitsarinki uwarki Haihuwarki kawai zata gwadamun amma badai wahala dake ba shine yau Kika saka mun da Zagi ”

Mama Halima da ta shigo lokacin taji abunda Aira ke cewa Inna “Tsawa ta dakawa Aira ta ce ” Dan Ubanki Aira Inna sa’arkice da zaki fad’awa wannan maganar kin manta uwarmuce itad’in zaginta kike shirin yi ko me koma Ince zagin nata kikayi “kuka Aira ta fashe dashi ta ce “Mama fa tun d’azu take zagarmun uwa na kyaleta Kuma ni ba zaginta Nayi ba Daman Kullum idan ta tashi gidan nan bata zagin uwar kowa sai tawa ” .

ta k’arasa fad’a tana kuka Tsaki Mama Halima tayi ta ce “Ta zagi uwar taki ko Dukanta tayi kin mata wannan Rashin kunyar Dan baki da ta ido” Inna ko kuka take tana cewa “Rabu da Ita Halima ta haifu ai Tsautsayi ne ya kaini na tab’a jinin Rahama sakayyace tamun dan haka yau yau d’innan saikin barmun b’angare ki koma chan gidanku inma kasheki uban naki zaiyi ya kasheki daman ni nake Daure maki gindi yau ko ya k’are bani ba ke maza_maza fitarmun daga gida”

”Inna tafada tare da mikewa ta rike k’ugu “Kuka Aira ta fashe dashi tare da tashi Tayi d’akinta Da gudu tana kuka ta fiddo duk wani abunda take buk’ata a akwati Ta janyota Ta fito Mama Halima ta Kalleta ta ce ” Ke ina zaki”Gidanmu zan koma sannan ta kalli inna tace “Daga yau idan kin k’ara gani na wajenki duk abunda kikaga dama kimun” ta fad’a tare da ficewa tana hawaye”.

“Ikon Allah ” Mama Halima ta fad’a tare da tab’e baki Hafsa ce ta ce “Ni wlh Mama Aira har ta bani tausayi dama baki mata fad’a ba ga Abba ya daketa da safe yanzu sun b’ata da Inna kuma fa Mama innar ita ta dinga zagin Mamy wlh konice Aka zagi uwata haka zanyi ”

Harararta Mama Halima tayi mata ta ce “To kema zagarta Dan ubanki Da yake sa’arkuce” Cikin Sauri Hafsa ta tashi tana Dariya ta bi Bayan Aira Dan tasan itama maman tata gwanace wajen fad’a yanzu ta gane ashe Duka ukkun Mama da Daddy da Abba Duka halinsu d’aya na fad’a Dan yanda taga yanda Daddy da Abba sukayi fad’an nan da safe har sunfi ma mamanta fad’a .

Suna fita Aysha ma ta tashi Dan ita daman ba gwanar zama bangaren Inna bace “Mama Halima tayi ta Lallashin Inna ta ce ” Dan Allah Inna ki daina zagin mamanta inma zakiyi kidainayi a gabanta Kinga ba dad’i”Tsaki Inna taja ta ce an zageta d’in ko kema bayansu d’in zaki shiga ko gobe saina zageta”Shiru mama Halima tayi Dan tasan Halin Inna ta rikice sai da lallab’o.

Aira kai tsaye gidansu ta nufa ta na kuka Mama kad’ai ta tarar a palour Mama ta ce “Lafiya Aira ya na ganki da akwati kina kuka kuma” Gidanmu na dawo ta fad’a tana kuka tare da shigewa Dakinsu na y’an matan gidan tana shiga ta saki akwatin Tare da Fad’awa Gado ta saki kuka mai ciwo…………✍🏿

*NI DA YAYA ARMAN book 2 it’s not Free it’s for sale if you wan’t subscribe pay 200 only katin M t n hoton katin ko transfer #200 Naira to 07026166536 Vtu #300 Pc wanda basa bukatar a Sakasu grps suma #300 y’an niger zaku iyamun magana ta wannan number +234-7026166536*

*Share fisabilillah*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/7, 10:24] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………27&28

….Sosai take kuka ta ma rasa Inda zata tsoma ranta taji sanyi yayyinta ba irin Lallashin da basu mata ba amma tak’iya saida ta gaji Dan kanta tukwana ranar ma da mugun zazzab’in ta kwana Wanda zazzab’in duk na tunanin Arman ne .

Washegari koda ta tashi bata lafiya sosai dak’yal ta samu tayi salla ta koma Ta lullub’e da bargo dukda zafin da ake Ba yanda su Ummy basuyi ba akan ta fito ko tea ne Tasha amma tak’iya har Ayshar mutuniyartata ba yanda batayi ba amma ta kiya.

Ganin sosai jikinta yayi zafi ya sanya su tsorata Amma ce ta je ta samu Mamy ta ce “Mamy Aira bata lafiya fa kixo kiga jikinta yayi zafi sosai” Cike da b’acin rai Mamy ta ce “me zanyi mata taje tayi ta ciwon ina ruwana” Ganin ran Mamy bace ya sanya Amma Zuwa ta fad’awa Mama Taje ta dubata taga har yanzu zafi jikinta.

Wajen Abba Mama Taje ta lallabashi akan ya fiddo mota akai Aira Asibiti Dak’yal ta lallabashi ya kira Family doctor d’insu ba ayi minti Talatin ba saiga Dr Bashir yazo tare da Abba suka shiga Mamy ta rakasu har d’akin da Aira take Haidar na gefenta Aysha na Jik’a ruwa tana shafa mata a ka dr yace meke damunta Amma tayi mai bayani dan har lokacin Aira ta kasa tashi kanta ji take kamar zai rabe gida biyu.

Kallon Dr Bashir Abba yayi ya ce “idan ka duba ta ka auni jininta Kayi mata har awon Ciki” Ciki kuma Alhaji “Mama ta fad’a cikin mamaki Duka saida sukayi mamakin maganar Abba Aira ko hawaye kawai take tasan shikenan yanzu Abba ya daina yarda dani ta fad’a cikin zuciyarta hawaye na zarya daga idanunta.

” Okay to Alhaji”Doctor ya fad’a Abba ko baiba Mama amsa ba ya fita cikin k’ank’anin lokaci Dr ya duba ta ya dauki jininta ya tafi dashi da niyyar zaije ya Auna Haidar ne yaje wajen Mamy ya ce .

“Mamy Dan Allah Kije ki duba Ya Aira wlh bata da Lafiya yanzu ma Dr yazo ya duba ta Hada Awon ciki wai Abba yace ayi mata”Cike da tashin hankali Mamy ta ce ” Shi Abban naku ne ya kira Dr yace ya mata awon”Eh Mamy wlh y’anzu ma Dr ya d’auki jininta ya tafi kuma sai kuka take”Sosai ran Mamy ya b’aci fitowa Palour tayi.

Mama Halima ce da Hafsa tare da Inna dayake Chan suka kwana suka shigowa yi musu bankwana zasu wuce suna zaune suna Gaisawa da Abba Mamy ta shigo ranta matuk’ar b’ace ta nufi wajen Abba tare da kama k’ugu ta ce.

“Shine har da kiran Doctor kace yayiwa y’ata awon ciki inbanda tsabar wulakanci da tonon asiri wannan ai sharri ne ma kake shirin yiwa y’arka Shi doctor d’in da ka kira Me zai d’auketa kasan abunda zaije ya k’ara ya fad’a nan gaba to Ta Allah bata mutum ba insha Allahu y’ata bazata tab’a abun kunyar da ake so tayi ba Tunda uwarta banyi ba Itama bazata tab’ayi ba”

” Cikin fad’a Abba ya ce “Wlh Rahama zanyi mugun sab’a miki karkiga kina wani zafuce zafuce ina kyaleki ba tsoronki nake jiba Ina kyaleki ne darajar Y’ay’anki inba hakaba baki isa kizo ki dinga fad’amun maganganun banza ina kyaleki ba ” Tsaki Mamy taja ta ce “Karka k’ara ragamun d’in daga yau ” Mama Halima ce ta ce “Haba Rahama da hankalinki da komai ki dinga yiwa mijinki Haka Ku sanyawa zuciyarku ruwan sanyi kar k’aramar matsala ta zama babba mana Kaima yaya baka kyauta ba Akan me zaka kira doctor ayi mata awon wani ciki me ya had’a Aira da ciki ”

dukanku kunfini sanin abunda nakeyi ne Dan haka kar Wanda ya k’ara mun magana akan Abunda zan aikata ko na Aikata “Inna ce cikin Masifa ta ce ” Kede Rahama baki da mutunci wlh Ko baki girma mashi matsayin mijinki ba Ai kin Yi karar ina wajen Y’arki d’in banza zakizo kina fafatu akanta y’ar da wahalar ta ma bakisaniba Sai in k’irga so nawa kika tab’a wanke mata kashi harta girma ke inkina da kunya kin d’aga baki kiyi magana Akan Y’arki y’arma ta fari in banda lalacewar zamani hada cewa wani y’arki Inajinma kece kika zugota jiya ta zageni Ai tunda ga Kanmu aka daina haifo mutanen kwarai wlh”

“Inna ta k’arasa fad’a cikin Masifa “Mamy bata tanka mata ba sai zama da tayi ta na girgiza k’afa Masifa sosai Inna ta shiga surfa Masifa Inda ta shiga ba tanan take fita ba ana haka Doctor Ya shigo Samun wuri yayi ya zauna Dr yace ” Alhaji mungama awon ba komai ke damunta ba Maleria ce sai tunani da ya fara mata yawa Awon cikin ma ba komai Duka Maleria ce ta sanyata ciwon sannan ya mik’awa Abba result d’in da leda ya ce “ga magungunan da za adinga bata kuma yanzu zanyi mata allura insha Allahu Zata samu sauk’i”

Tashi Mamy tayi ta ce “Alhamdulilla Abunda ake son dai baifaruba akan y’ata kuma sai a tari wani sarkin” ta fad’a tare da wucewarta d’akinta duk da Kallo suka bita Girgiza kai Mama Halima tayi a ranta ta ce “Lallai Yaya Inbanda Rahama wa ya isa ya fad’a mashi maganganun nan a kwana lfy” Dr ko tashi yayi yaje Dan yiwa Aira Allurar “Inna ce taja tsaki ta ce .

” Aikin banza Ai shiyasa Tun farko na hanaka Auran Yarinyar Chan kuka dage sai ita farin ne kawai ya d’ebeku amma ni daman Nasan ba mutuncin kirki zatayi ba yanzu wa gari ya waya shidai Kabir Allah ya taimakeshi kaikuma da ka jajib’o saikaji dashi Dukta salamceka ta asirceka inaga tsoronta kakeji ma ko to ni ba kai bane ni bata salamceni ba Ai naso wlh ta Tankamun yau da taga yanda tsaffi ke Rashin mutunci Yau da saitabar gidannan dukda d’anyen jegon tunda ba gidan ubanta bane wai nan gani take ta haifi maza biyu zatawa mutane iskanci to ko Nigeria ta haife ni sai in koreta tunda bata da mutunci”.

Shidai Abba baice komai ba Dan yasan Inna sarai inta rikice hakan yasa ya dinga lallab’ata Nan Dr ya fito yayiwa Abba sallama Mama Halima ce ta shiga d’akin da Aira ke ciki lokacin Ta tashi tana rama Sallar da batai ba “Koda ta gama sosai Mama Halima ta shiga yi mata nasiha cikin nutsuwa Akan ta yiwa iyayenta biyayya ta daina abunda basaso ” Insha Allahu Mama bazan sakeba “yawwa Mamana Allah miki albarka idan iyayenki sun huce kije ki basu hakuri kinsan yanzu cikin fushi suke ” tana hawaye tace

“Insha Allahu Mama zan basu hakuri” Mama ta ce “To mudai zamu wuce ai zakizomun Hutu ko tunda kun gama karatu bare kice makaranta Dan nasan halinki sarai bakison zuwa kinamun hutu” Insha Allah Mama indai Abba ya yarda zanzo”.

Ranar su Mama Halima da Hafsa suka juya Aira ji take kamar ta bisu Dan gidan baya mata dadi .

Aira ita ciwon biyu yayi mata ga na Rashin jin muryar Arman kwana biyu Dan wayarta tayi mata mugun b’oye daga babbar har k’aramar.

Cikin kwana biyu Aira taji sauk’i ta warware sosai yanzu sai damuwar fushi da Iyayenta keyi da ita Dan Mamy ko magana bata mata sosai Abun yake damunta Yau tana zaune a dakinsu ganin ba kowa ya sanyata saurin d’auko wayarta Karama ta kunna ta maza ta shige toilet Dan karma wani ya shigo ta dannawa Arman Kira Saida ta gama ringing tukwana ya kira.

Muryarta cike da damuwa kamar zatayi kuka ta ce “Yaya ina ka shige kwana biyu” Bangaren ARMAN Ajiyar zuciya ya sauke Dan tun ranar da ya koma Abuja Yake cikin damuwa yasan tunda Daddy yayi wannan fushin to yasan Abban Aira ne yayi mashi Rashin mutunci yasan ba k’aramun Duka Tasha ba tsoronshi d’aya Kada Ta tsorata ta rabu dashi hakan yasa duk ya shiga damuwa gashi yayi ta Kiran layin Ta kashe

“Aira kina Lafiya ya fad’a cikin sanyi” Kamar zatayi kuka ta ce “Lfyqlau yaya sai kewarka da tamun yawa” Nima Ina nan kewarki ta addabeni My Aira Please kuyimun Alk’awarin duk wuya duk rintsi bazaki rabu dani ba idan kika rabu dani zan shiga mawuyacin hali please my Cutie”Kuka Aira ta fashe dashi cikin kuka ta ce

“Yaya bazan tab’a rabuwa dakai ba Abunda ban tab’a kawowa a kwalwata ba Dan Allah kar Daddy yasa ka rabu dani nasan Shima yanzu bayason alak’armu tunda suka sake rigima da Abba” Karki damu my cutie Daddy bazai iya rabamu ba “Bai tambayeta Abunda ya faru ba Dan bayason k’arin b’acin rai sun tab’a Hira sosai Aira duk sai taji Kashi tamanin na damuwarta ya tafi

haka Shima bangaren Arman din ta kasance Arman yace kina jina My cutie” yace Eh Yaya”Daga yanzu karki k’ara nuna muna tare karki sake wani ya lura da muna tare Ko garin nazo Bazan k’ara yarda nayi sakacin da har zai zame maki matsala banason yawan dukanki da ake Zamuyi Abotarmu cikin sirri kinji”Kamar yana gabanta ta gyad’a mai kai tace “to yaya ” sannan kicewa su Abba da mamy kin rabu dani ko sun tambayeki kinji”To yaya tafada Sun Kara tab’a Hira Kad’an tukwana sukayi bankwana cike da Shauk’in k’aunar juna.

Bayan kwana biyu Aira taje ta samu Abba a lambu ta dinga bashi hakuri tana kuka tun bai kulata ba haryazo yace ya hakura amma da sharad’i saita rabu da Mujahid Goge hawayenta tayi ta ce “Abba insha Allahu mun rabu bazan k’ara mu’amula dashi ba ” Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce “da ko kikayi hakan da kin taimaki kanki kuma kin nemu hanyar da zamu samu Masalaha a tsakaninmu Allah yayi miki albarka” Cike da farinciki Aira ta ce “Ameen Abba nagode”.

Daga nan d’akin Mamy ta nufa ta isketa tana Bawa Amer madara durkusawa tayi ta bata hakuri tayi banza ta kyaleta ” Kuka ta fashe dashi tare da rik’e k’asar zanin Mamy ta ce “Dan girman Allah Mamy kiyi hakuri ki yafemun bazan sakeba Mamy na tuba”Shiru Mamy tayi saikuma ta ce ”

“Haba Aira tuban ki wannene bansaniba sau nawa zakiyi Abu kice bazaki sakeba karshe kizo kiyi Wanda ya linka na baya ai yanzu ni kinfi k’arfina kuma ba ruwana dake”Mamy wlh yanzu na tuba Allah nadaina bazan sakeba Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce “Tashi muyi magana indai da gaske kike bar kukan” cikin Sauri Aira ta tashi ta zauna gefen Mamy Kallonta tayi in serious talking ta ce “kin yarda kin rabu da Arman d’in koko?cikin Sauri tace………….✍🏿

*Share fisabillah*

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/8, 22:32] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………29&30

” Mamy na rabu dashi Shima kuma nasan Daddynshi ya rabashi dani tunda bakusan mu amulata dashi”Yawwa ko kefa Aira ki taimakamun ki fiddani kunya ki rabu dashi sannan ki daina abunda zaidinga jamun Zagi kinji”Gyada kai tayi tace “Insha Allahu Mamy Na daina” Allah sa da gaske kike na yafe maki duniya da Lahira Allah maki Albarka ”

“Sosai Aira taji sanyi a ranta tace ” Ameen Mamy nagode sosai”sosai Mamy ta saki jiki da Aira ta dinga janta cikin dabara ta Tambayeta ta ce ” ranar da kuka tafi ina kikaje kuka kwana badai abunda yayi maki ko idan da Abunda ya faru fad’amun wlh ba maiji kuma bazan dake kiba kinji na rantse ”

Nan Aira ta bawa Mamy Labarin komai Da ya faru daga karshe ta ce ” Allah Mamy Gaskiya na fad’a maki ba abunda yamun ni yaya baitab’amun maganar banza ba kawai zargine kuke amma shi ba haka yake ba”wata nauyayyar Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta tabbata Aira idan ta fad’i magana haka take Dan bata karya

Sai sannan taji sanyi a ranta ta cire zargin dake ranta daman duk wannan Abun da tayiwa Abba itama akwai zargin a ranta kawai Dai abunka ga d’a da uwa ne “to yanzu shikenan komai ya wuce na yarda ki kiyaye nan gaba Dan Allah” to Mamy “sannan tace ” Mamy banishi na rik’e maki ta fad’a tana mik’a hannu ta amshi Ameer tare da pidarshi ta sab’eshi a kafad’a ta fito palour Sai murna take yanzu Hankalinta kwance ta sasinta da Iyayenta.

Haka rayuwa taci gaba Aira na shan wayarta da Arman a b’oye babu Wanda ya fahimta Kullum idan Sadiq ya kira Aysha idan ta bata wayar kin amsa take ba yanda Aysha batayi da itaba amma saita k’iya tun yana kira har ya hakura ya daina kira Wanda hakan sosai yayiwa Aira dad’i.

Amma ta koma bangaren Inna kullum Inna da kewar Aira take kwana take yini Dan tayi mugun Shak’uwa da ita gashi taga Airar tayi zuciya ko bangarenta bata k’ara shigowa dak’yal a daddafe Inna ta daure tayi sati biyu ba Aira sosai kewarta ta dameta gashi Shima Arman bai sake zuwaba duk Abu ya dameta.

Yau Aira y’an gidan su duk suna zaune a palour ana hira da misalin Tara na dare har Abba da su Mamy Amer na Bayan Aysha ta goyashi Inna ta shigo Aira na ganin shigowarta ta kauda kai Wajenta Inna ta nufa ta ce “Haba y’ar lelena daman zaki iya fushi dani Duka ina duniyar take bare mu dake cikinta biko nazo ki taho mu koma gidan duk bayamun dad’i da kika tafi” Turo baki Aira tana zunbura Baki ta ce

“Keda kika koreni ni ba Inda zani kije Chan takwarartaki ta dinga tayaki kwanan ni bazan koma ba”Inna ta Goge hawaye ta ce ” Haba Hajara Dan Kinga ina sonki shiyasa kikemun wulakanci to wai ba na baki hakuri ba ki taho mu tafi “ba Inda zani ni ki tafi ” Sudai su Mama suna gefe suna Dariya kasa kasa Dan Inna da Aira sai Allah haka zasuyi fad’an kuma inna tadawo tana bata hakuri”cike da Masifa Inna ta juya ta kalli su Mamy ta ce

“ku yanzu cikinku ba mai bata hakuri Kunajina kukayi banza dani Dan kun rainani ke Rahama ba y’arki bace Baki isa kice tayi hakuri kodan daman Nasan ai ke kike zugata shiyasa yanzu ta gujeni kiwon d’an makwarwa ne nayi ” tafada tana Goge hawaye “Cikin ladabi Mamy ta ce ” kiyi hakuri Inna ni wlh banzugata ba Dan kar nayi magana kuma kice ina ruwana shiyasa amma kiyi hakuri sannan ta harari Aira ta ce “Tashi ku tafi” Turo baki Aira tayi ta ce “Mamy itafa da kanta ta koreni har cewa tayi karna k’ara zuwan mata” Inna tace

“Kai Hajara banda sharri a ina na koreki ” Abba ne ya ce “Mamana tashi ku tafi banson doguwar magana” Tashi Aira tayi ta ce “To Abba a ranta sosai taji dad’i Dan daman kamar a k’aya take bata samun damar shan waya da Arman Yanzo ko gidan Inna ko kwana zatayi tana waya dashi ba mai sani d’akinta ita kad’aice kawai ta gwada batasone Dan inna tasan Taji Haushi Akwatinta ta d’auko wayoyinta daman suna ciki ta fito ta harari Inna ta ce .

” To muje kuma wlh kika k’ara korata ko kika zagi Mamy na taho har abada bazan koma ba”To y’ar lelena Inani ina Kara korarki ni daman Chan ban zagar maki uwa ba Rahama ai y’ar kirkice bakiji sunan ba Rahama duk Inda kikaji an ambaci Rahama ai andace bakiga ba ko mutum mutuwa yayi ba Rahama ake nema mashi “Dariya Aira tayi sosai hada rik’e cike tace ” To shikenan My Inna muje suma su Abba Dariya sukayi sosai Har Mamy wai yau itace Inna ke yabo .

Su Aira na fita Mamy ta tashi ta cewa Mama”Yaya saida safe “To Auntynsu Allah tasheni lafiya Mama ta fad’a ” Mamy ta kalli Aysha da murmushi fuskarta ta ce “Yau ko tayin bacci zai miki” Dariya Aysha tayi ta ce “Mamy muje saina kwantar dashi Dan karya tashi suna zuwa d’akin Aysha kwantar da Amer Sannan ta kalli Mamy ta na Sosa kai ta ce ” Uhm Mamy Dan Allah wani taimako zakiyimun”Mamy tace “inajinki Aysha fad’a kai tsaye insha Allahu indai zan iya zan maki shi”

Cike da kunya Aysha ta bawa Mamy labarin Saurayinta Abdulkharim da hadu Airport daga karshe ta ce “Shine yanzu yace yanason yazo ya gaishe da Abba shine nake tsoron yiwa Abba magana Dan Allah Mamy ko zaki fad’a masa nasan ke zai fahimce ki ” Murmushi d’auke da fuskar Mamy ta ce “Ah masha Allah kice munkusa shan biki amma gsky Naji dadi karki damu Insha Allahu zanyi mashi magana ba matsala” Godiya sosai Aysha tayiwa Mamy Dan tasan daman itace zata fad’awa Abba direct yayi na’am.

Mamy Bayan ta fito daga wanka jikinta daure ta towel ta dauki amer tana cikin sauyamai kaya Abba ya shigo kauda kai tayi kamar batasan yashigo ba Dan tun sanda sukayi rigima ta ke fushi dashi cikin kwantar da murya Abba ya ce “Haba sarauniyar mata Farar mace alkyabbar mata wai har yanzu baki huce ba Fushin nan ya isa Haka kinsan bazan jureba Airar ma data had’amu na yafe mata”.

” hmmm kawai mamy tace taci gaba da abunda Take Abba ya ce “To wai ba nace kiyi hakuri ba Haba my rahama bansanki da rashin yafiya ba “cike da kissa Mamy ta ce “hmm ya wuce Abban Aira amma karka sake irin haka gaskiya” Cike da farinciki Abba ya ce “Bazan sakeba Amma kema ki daina fad’amun magana son ranki gaban kowa”

Murmushi kawai tayi a take suka shirya kamar basu tab’a fadaba(Su Abba da Mamy Daman ba a hakura da love ba😂🙈) cikin hikima Mamy ta fad’awa Abba sak’on Aysha sosai yayi farinciki daman yanzu kuma burinshi tunda ta gama karatu Aure kuma alhmdllh tunda ta samu cikin Sauk’i.

Haka rayuwa taci gaba Aira komawarta gidan Inna sosai tayi mata dadi Dan tana samun damar shan wayarta da Arman da vedio call tarayyarsu taci gaba saima shakuwa da suka k’ara An sanya bikin Aysha Da Abdulkharim wata hud’u masu zuwa Wanda aka had’e da na Ummy itama Bayan gama karatunta Saurayinta ya turo Wanda dukansu cikin garin suke sosai hakan yayiwa iyayensu dadi.

Su Abba ganin Aira ta nutsu ya sanya suka saki jiki da ita suke hamdalar ta rabu da Arman musamman mamy

Arman saida Yayi wata biyu baizo garin ba Dan tunda Abba ya dakeshin nan bai sake zuwaba kullum Mummy cikin lallabashi take akan yazo tayi kewarshi Dan Arman ko sati biyu bayayi baizoba amma wannan tafiyar har wata biyu baizo tasan fushi yayi dak’yal ta samu ta shawo kanshi ya ce zaizo.

Ranar da zaizo Aira sai Farinciki take Dan ya sanar mata ji take kamar ran sallah Tunaninta d’aya Inda zasu had’u Dan yace mata ko gidan Inna bazai dinga zuwa ba Dan kar a dinga samun matsala tana cikin tunani Dan tun d’azu yace mata jirginsu zai tashi wata dabara ce ta fad’o murmushin jin dad’i tayi Tabbas wannan shawarar ita ce kawai mafita cikin Sauk’i………..✍🏿

😱tofa wata shawara ce Aira ta yanke ?????

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/8, 22:36] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️……………31&32

……Cikin Sauri taje tayi wanka ta yi shirin Tahfex cikin ash din kaya da doguwar hijabinta jakar ta ta d’auka ta saka k’aramar wayarta Arman yana kiranta ya shaida mata yashigo garin kwatancen tahfex dinsu tayi mai ta ce a chan zai sameta da to ya amsa mata dan daman yasan Tahfex din.

tana zuwa part d’insu Amma harta shirya napep suka Tara suka tafi suna gab da zuwa bakin get d’in makarantar Aira tace me napep din ya ajesu “Suna fitowa cikin marairaicewa Aira ta kalli Amma ta ce ” Dan Allah taimako d’aya zakiyimun Yaya Arman ne zaizo mu gaisa bazanje makaranta ba Dan Allah ki Rufamun asiri kicewa Malam banda lafiya”.

“girgiza kai Amma tayi ya ce ” Aira kenan Allah shiryeki Kardai kuje wani wajen daga nan a ina zan ganki idan antashi “ba Inda zamu sis ngd sosai Basu ida maganar ba ta Hango motarshi hug din amma tayi ta ce idan antashi zaki ganni ”

Amma ta wuce ciki itakuma Aira tayi baya cikin Sauri har taje Inda motar take back sit ya bud’e mata Inda yake ta shiga juna suka sakarwa murmushi Dukansu sunajin shauk’in k’aunar junansu Arman ya ce ” I really miss you my cutie “Cikin shagwaba ta ce ” Miss you too my yaya Ya hanya”Alhamdulilla fatan na sameki lfy .

“Sosai suka dinga hira cikin nishad’i da Annashuwa har lokacin tashinsu yayi ganin anfara fiffitowa yasanya Aira Kallonshi ta ce ” My yaya antashi Kar malamin mu ya ganni”To my cutie sai gobe Ai zamu had’u ko “murmushi tayi ta ce ” Insha Allahu “wasu manyan ledoji ya mik’o mata guda biyu d’aya kayan makuleshene su choculate, biscuit’juice kala kala d’ayar kuma Kaza ce gashin oven guda biyu ” .

Kallonshi tayi a hankali ta ce “Thnks Yaya ” Harararta yayi ya ce “ban hanaki yimun Godiya ba” Cikin shagwaba ta ce “Yaya aidole na maka Godiya ko Allah idan muka gode masa dad’i yakeji ya k’ara mana fiye da Wanda ya bamu a baya” Murmushi yayi ya ce “na manta fa mutuniyar tawa ustaziya ce ” Dariya tayi tare da rufe fuska Rafar y’an dubu d’aid’ai ya mik’o mata cike da tsoro ta ce.

“Dan Allah yaya kayi hakuri amma Bazan karba ba inma na karba Allah bansan Abunda zanyi dashi ba” Lokaci guda taga ya murtuke ya ce “Na k’ara magana baki amsa ba ranki zaiyi mugun b’aci kinsan dai banason gardama kuma bana kyauta a maidomun ko a k’i Amsa” Badan Aira ta so ba ta amsa ta ce “Nagode Yaya ” lokacin da Arman ya tafi amma ta Iso Suka jera Suka tafi gida a k’asa Nan Aira ta nunawa Amma abunda Arman ga bata sosai Amma tayi mamaki ta ce.

“Chab Kedai Kibi A hankali wlh kuma karki k’ara Amsar kudinshi ko ran nashi zai b’aci karki amsa ai dole ya huce ” To Sister Aira ta ce “Sannan ta mik’awa Amma dubu Ashirin ta ce ” ga naki sis”kin Amsa amma tayi Aira tayi ta mata magiya ta ce “Dan Allah ki amsa wlh ni Banmasan ta yanda zan kashesu ba ” Amsa Amma tayi ta ce “Nima d’in bansan tayanda zan kashesu ba bari dai kawai na amsa” Suna isa gida Aira tayiwa kudinta mugun boyo kayan da ya kawo mata kuma ta ba Inna wasu Inna sai sa mata albarka take taci Wanda ta iyaci sauran ta kaiwa su Amma.

Washegari da Yamma Aira ta shirya cikin hijab d’inta ta gida blue kasancewar Alhamis basa Tahfex a d’aki ta samu Mamy na linki Bayan ta gaisheta ta ce “Mamy Dan Allah gidan su Khady nake son naje idan kin barni zan duba ta bata da lafiya”

“Ke ya akayi kikasan bata da lafiya”jiya da naje islamiya k’anwarta take fadawa Malam kinsan Tahfex d’inmu d’aya “To shikenan kije amma karki jima Dan Allah sannan ta mik’a mata dubu d’aya ta ce ” Kiyi kudin transport A a Mamy ki barshi ina da kud’in da Abba ya bani jiya da zani Tahfex “Maida kudinta Mamy tayi batare da ta ce komai ba.

Aira ko tasan wannan karyarce kadai zatayi mamy ta barta ta fita Aira tana zuwa gidansu Khady sun dan taba hira ba ajima sosai ba Arman ya kira ta ba Khady tayima Arman kwatancen gidan ba ayi minti sha ba sai gashi Nan Aira tayiwa Khady bankwana ” Khady ta ce “haba kwt daga zuwanki daman Nasan zuwan nan naki ba banza ba ” Dariya Aira tayi ta ce “Karki damu Besty zandawo nayi maki yini akwai labari” Har bakin get Khady ta rakata ganin ta shiga motar Arman ya sanyata Juyawa Aira ko da Arman yawo sukasha waje waje cikin nishad’i da Annashuwa Ganin magriba ta gabato ya sanya Aira cewa .

“Yaya ka maidani gida Mamy ta ce kar nayi dare ” Okay nima gobe zanwuce ki kulamun da kanki kinji kyakyawata”B’ata fuska tayi cikin shagwaba ta ce “Yaya jiya kazo ka ce kuma gobe zaka wuce” Kinsan yanayin Aikin namune bamuda Hutu sosai Amma ai kinsan bazan jima ba zanzo na k’ara ganinki”Cikin shagwaba ta ce “Yaya daman fa waccen tafiyar saida kayi wata kusan biyu bakazoba”

” yanzu bazan sake dadewaba tunda my prince’s bataso kamar karsu rabu da juna Arman ya tsaida mata napep ya bashi 10k mai napep sai Godiya yake saida yaga tafiyarta tukwana ya juya cike da kewarta a duniya shidai ya kasa gane wani irin sone Allah ya jarabceshi dashi na Aira Kwata_Kwata Ko wajen Aiki yaje Allah_Allah yake yazo ya ganta daidai da second d’aya da zai samu dama bazaiso yayi batare da Airanshi ba cike da so da kewarta ya koma gida washegari ya koma Abuja.

Aira sosai take fachaka da kudi Dan ko Abincin gidan ta daina ci saidai ta aiki mai gadi ya sayo mata abunda take so Ummy da Aysha sunyi da ita ta fad’a musu Inda Take samun kud’i amma taki fadamusu .

Yau Aira ta shigo d’akin Mamy kenan ta tarar da Haidar yana yiwa Amer wasa “K’arasa shigowa tayi ta ce ” yau kuma Kaine d’an rainon kuma fa kayi kyau da rainon”Hararta yayi ya ce “Mamy ce tace na rik’e mata shi nayi maki kama da d’an Reno matsala ta dake wulakanci wlh ya Aira”Dariya tayi ta ce ” Kardai kamun Rashin kunya kayiwa Arziki kulli Yaro “Naji ya fad’a tare da mika mata Amer amsarshi tayi ta ce .

” Ina mamyn take”Tana Part d’in Abba “yawwa nasan ba yanzu zata dawo ba Aikenka zanyi yi Sauri kaje ka sayo mana Kaza da ice cream da shawarma ta fad’a tana fiddo kudi cikin siket d’inta” wara idanu Haidar yayi ya ce “Kam ya Aira ina kika samu kudi dubu goma ce fa kika bani ”ya fad’a yana juya kudin da ta bashi” Hararshi tayi ta ce “Dan kaci sa a zanci dakai shine Zakawa kanka inbazaka sayoba ban kudina” washe baki Haidar yayi ya ce “Chab wa yaga banza ya bari” Dariya Aira tayi ta ce “Uban son banza”.

Tana nan zaune tanayiwa Amer wasa sai Dariya yake Ba ayi minti sha biyar ba Haidar ya dawo da leda hannunshi plate suka d’auko suka baje kazar suka fara ci Haidar sai sawa Aira albarka yake tana Dariya ta ce ” shegena banza ta samu”Dariya yayi ya ce “Aiko banza ta samu Allah karo na banzar muci mu nare.

basu ida cinye kazarba kowa ya d’auki robar ice cream suka fara sha basusan ba Mamy ta shigo saida sukaji ta ce ” Ubanme Kuke ci “cikin rud’u Aira ta tashi tare da ja baya Shima Haidar tashi yayi Kallon kayayyakin dake gadon tayi ta kalli Haidar ta ce ” wa ya baku”Nuna Aira Haidar yayi cikin tsoro ya ce “ita ta bani na sayo mana” Kallon Aira Mamy tayi cikin b’acin rai Ta ce “Waya baki kud’i Dan ubanki harkika bada akayo wannan uwar sayayyar” .

yarfe hannu Aira ta fara tare da mik’ewa kan gadon ta fara hawaye ta ce “Dan Allah Mamy Kiyi Hakuri bazan sakeba” Ubanki keda hakurin tambayarki nayi ko hakuri nace ki bani Munafuka sai anyi magana ta dinga yarfewa mutane hannu tana bada hakurin munafurci cewa nayi wa ya baki kud’i”Haidar yayi saurin cewa “Mamy saurayin Aunty Aysha ya bata “.

Kallonta Mamy tayi ta ce “Na tambayi Aishar gyada mata kai tayi ta ce ” Eh”Dannawa Aisha kira Mamy tayi tana zuwa ta Kalleta ta ce “Wai saurayinki Aysha ya ba Aira kud’i” Kallon mamaki Aisha tayiwa Aira ta ido Aira ta dinga nuna mata ta rufa mata asiri ta ce Eh “Eh Mamy shi ya bata ” jin Abunda Aisha ta fad’a ya sanya Aira sauke ajiyar zuciya Gaskiya Haidar ya taimaketa har ya fita tunanin wannan mafutar Dukda baisan wa ya bani ba .

“Itama Mamyn Ajiyar zuciya ta sauke ta ce ” To angode sannan ta kalli Aira ta ce “Shine ko ki fadamun” nazata fad’a zakiyi shiyasa banfad’a maki ba “kede kika sani cewar Mamy Aira da Aisha suna fita suna Shiga Dakinsu Aisha ta tsare Aira da Tambayoyi akan saita fad’a mata Inda ta samu kudi badan Aira taso ba ta fad’awa Aisha Arman ne ya bata har wayar da ya bata saida ta fad’a mata ” cike da mamaki aysha ta ce “Chabd’i amma Aira wlh kunfini rawar kai har ki rik’e har iPhone 13 ba tare da sanin kowaba”turo baki Aira tayi ta ce.

” to Karki fad’awa kowa”Ba Wanda zaisani sister Amma ki fad’amun soyayya kuke da Arman koko ki fad’amun Gaskiya insha Allahu zan taimaka maki da shawarwari”k’asa da kanta Aira tayi wasu zafaffan hawaye na zubo mata ta ce “Aunty ina sonshi sosai nima bansan tun yaushe na fara sonshi ba amma dai na sani ina matuk’ar sonshi son da bazan iya rabuwa dashi ba ” Cike da tausayin y’ar uwar tata Aysha ta ce “Nasan Hakan zata faru Aira banyi mamaki ba najima da zargin kuna son junanku keda Arman Amma shi ya tab’a fad’a maki yana sonki”.

Girgiza mata kai Tayi ta ce “A a a a” Karki damu sis komai zaizo da sauki insha Allahu nima zanbada gudummawata d’ari bisa d’ari Dan Gaskiya Arman dake ya dace haka kema dashi kika dace Allah dai ya sa iyayenmu su yarda Ku auri juna”Sosai Aira taji dad’in yanda Aysha ta nuna tanason tarenta da Arman Ranar sun jima suna Hirarraki.

Haka Rayuwa taci gaba Aira sosai ita da Arman suke shan wayarsu Idan yazo kuma tasan dabarar da zatayi ta fita ba Wanda cikin iyayensu ya k’ara gane tare take da Arman sosai hankalinsu ya kwanta musamman Abba yana murnar Aira ta rabu da Arman baisaniba saima gaba da yayi.

Komai aka sakawa Rana sai yazo ya rage saura sati Ukku biki Aysha Da Ummy suka tafi Umrah sai ana jibi za a fara event d’in suka dawo sosai suka k’ara kyau dan sunsha gyara a Chan baki na nesa da na kurkusa duk sunzo Har Yayarsu Aunty Maryam da ke Aure a Lagos tazo tare da yaranta Zainab(Yasmeen) Ahmad,Sadiq Aunty Halima ma da Hafsa duk sunzo.

Haka aka fara hidimar biki sosai amaren sukeyin kyau ranar farko akai Friend evening rana da biyu walima rana ta Ukku Aka d’aura Auren Bayan kowacce an kaita gidan mijinta sosai Aira suka sha kuka musamman ita da Aysha Da dare aka shirya Dinner sosai amaren da angwayen sukayi kyau Wajen da ake dinner ma an kawatashi Aira ma ba abarta a baya ba Sosai Tasha kyau cikin wani tsadadden lace d’inta purple Anko anyi mata Riga da siket rigar mai dagewar nan sosai kayan suka amsheta ga make up d’inta da tayi bala’in mata kyau ko gyale bata yafe ba.

haka aka fara gudanar da programs d’in cikin tsari Bayan anyi hotuna aka fara rawa sosai Aira ta saki jiki take rawa saboda ansa wak’ar da take mugun so kuma daman tace a bikin yayyin nata saita chashe Sosai ta burge mutanen dake wajen sai lik’i maza ke mata ganin haka ya sanyata saurin Zamewa ta fita daga filin rawar Taje ta zauna a kan chair

tana zama wani ya biyoto ya zauna kusa ta isa Tare da cewa “Y’an mata yakike Gaskiya kin hadu ba k’arya kin burgeni sosai Dan Allah zan iya samun number wayarki” D’agowa Aira tayi ta Kalleshi daga k’asa har sama sannan taja tsoki,.

wayarta babbar ta fiddo zaro ido tayi ganin missed call d’in Arman rututu cikin Sauri ta Danna mai kira Abun mamaki sai taji ringing d’in daga bayanta juyawar da zatayi idanunsu suka sartse cikin na juna Fuskarnan tashi a murtuke Kamar bai tab’a Dariya ba ya sanya hannuwanshi cikin Aljihu sosai Aira tayi mamakin ganinshi ko dai gizau ne yake mata amma ai da Yamma ma sunyi waya yake ce mata yana Abuja Bata gama wannan tunanin ba Taji ya……..✍🏿

*Kamar yanda na fad’a a page 30 zamu gama book one ma ana free page to na k’ara muku page biyu wannan shine page din biyun karshe da zamu gama freee Wanda suka sayane kad’ai suke da damar cigaba da karanta wannan littafin ga mai buk’atar saya ya tuntub’eni ta wannan number 07026166536 haka zalika masu buk’atar a tallata musu hajarsu suma su tuntub’eni kan number wayata*

*NORMAL GROUP #200*
*V T U #300*
*PC #300*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/9, 12:56] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

“`MALLAKAR“`
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

_Last Free Page_
*BOOK ONE*📔
🅿️……………33&34

……..Ya Janyo hannunta janta ya fara yi tun tana tirjewa harta hakura Dan sosai ta tsorata suna fita farfajiyar wajen Hall din Ya wullata Ta fad’i dafe kanta tayi Wanda da kyal ya hana ya buge kuka ta fashe dashi ta ce.

“Yaya Airanka ce fa da kajimun ciwo fa” Cike da b’acin rai Arman ya nunata da yatsa ya ce “Daman irin abunda kike bana nan,ki shiga filin rawa kina karkada jikinki ko wani k’are da doki yana karewa halittarki kallo kega mahaukaciya,ko gyale babu ga wannan tsinannun kayan da suka matseki ya mukayi dake kwanaki ban hanaki rawa ba sannan ban hanaki saka matsatsun kaya ba ,ban hanaki mu’amula da maza ba ,Duka abubuwan da na hanaki yau na kamaki da kaifinsu daman irin abunda kike bana nan” ya k’arasa fad’a cikin d’aga murya .

Aira sosai tashiga tashin hankali tasan Idan ran Arman ya b’aci bai iya fushi ba Batasan lokacin da ta tashi ba ta fad’a jikinshi tare da sakin kuka ta ce “I’m so sorry yaya Bazan sakeba forgive me please kayi hakuri ” Ajiyar zuciya Arman ya sauke sai yaji zuciyarshi tayi sanyi yana daga cikin abunda yake k’ara mishi k’aunar Aira da idan tayi laifi zata bashi hakuri koda kuwa itace mai Gaskiya bata da girman kan bada hakuri.

daddab’a bayanta ya fara cikin kwantar da murya ya ce “yi shiru daina kukan is okay na hakura Amma karki sake kinji my cutie idan ba so kike zuciyata ta buga ba ” Sosai Aira taji dad’i k’ara Rungumeshi tayi tare da Murmushi ta ce “Thnks yaya shiyasa nake sonka kana da saurin yafiya” Sai kuma ta rufe bakinta sai yanzu ta tuna b’aram b’aramar da tayi murmushi Kad’an Arman yayi sannan ya janyeta daga jikinshi

kama hannunta yayi ya bud’e mata mota suka shiga ta na Front sit shi kuma yana mazaunar driver A hanya Aira ta ce “Amma Yaya ya akayi kazo wajennan Bayan nasan baka gari kuma bakasan Wajenba” Cutie kenan Kin manta yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba”Cike da mamaki Aira ta ce “Yaya kiwon mutum kuma me kake nufi” Ina nufin kome mutum yake a idon mutane yanda akai nazo wajennan a isha’i ma ina Abuja Wajen 9:45 haka Wani Abokina Dake nan kano ya kirani yake Cemun yaga kanwata wajen wata dinner.

Sosai nayi mamaki nace wace kanwartau sai yake Cemun nahau what’s app zai turomun videon ta na gani idan ita ce “Ina hawa ya turomun videon ki kina rawa wasu tsinannun y’an iska na miki lik’i karkiga yanda hankalina ya tashi ban k’arasa Kalla ba na tashi na tafi Airport na yanki ticket na taho Ina zuwa na kirashi yayimun kwatancen wajen shi kanshi saida yayi mamakin cewa Na shigo garin”

Cike da mamaki Aira ta ce “Chab Amma abokin nan naka anyi Dan sa ido to shi a ina ya sanni” A Hoto”Hoto kuma yaya a ina kenan Nida ba post din hotona nake social media ba “Hararta yayi ya ce ” kima fara mana ki gani”

Dariya tayi ganin yanda yayi maganar ta ce “wace ni wa ya haifeni a garin nan ” Dariya yayi Kad’an sosai Komai Aira tayi take burgeshi ya ce “a d’akina da ya tab’a shiga Yaga hotunanki a lokacin ya nuna mun yana sonki na cemai kanwata ce kuma anyi mata miji Sai ya hakura ” murmushi Aira tayi ta ce “Me ma zanyi da d’an sa ido gwara da kace mashi haka dukda dai ba ayimun mijinba”.

Harar wasa yayi mata yace “wa ya fad’a maki ba ayi miki miji ba Ai nariga da zab’a miki mijin da ya dace dake ko bazaki amince da zab’in yayanki ba” Murmushi tayi tare da Kauda kai ta kalli gefen titi Dan batason maganar”Baikara cewa komai ba harsuka isa gida lokacin 12pm danma Allah yasa a gida Ansan Dinner sukaje kuma a motar gida sukaje A ita za a maidosu saitaje ita gaba tayo,

Bye bye tayiwa Arman Ta ce “Sai gobe yaya daan Allah gobe ka shigo Inna fa na nemanka” karki damu cutie zanshigo goben “Thnks my yaya bye bye ta fad’a tana daga mai hannu saida yaga shigarta tukwana ya wuce guest house d’inshi Dan yanzu yaje government house Mummy cewa zatayi ba Lafiya ba gwara ya bari sai gobe yaje ba .

Washegari Aira da Amma sukaje suka gygyarawa yayun nasu gida saida yamma suka nufo gida kamar karsu rabu A Hanya Aira ta ce ” Amma bakiga Aunty Aysha iyayin nan yau duk tayi lakwas ko bata lafiya dai bakiga ba a sanyaye take ba Yau shikuma Yaya Abdul sai wani lillike mata yake ba ko kunya a gabanmufa dazu yayi mata kiss”.

Dariya Amma tayi ta ce “Kikak’i tambayarta kafin mu taho kema da kukafi kusa baki saniba bareni y’ar karoro ko mu koma ki tambaya” Waro idanu Aira tayi ta ce “Rufamun Asirin Har ya koro mu” Dariya Amma tayi sosai ta ce

“Nikuma ya Ummy ce ta ban Mamaki ji fa yau hada cewa Dan Allah karmu tafi mu bari sai Bayan Isha’i Yaya Usman ya maidamu yau ko jarabar babu “Dariya Aira tayi ta ce ” Ba dole taso muk’i tafiya ba Barin gida ai saidole Ni ko tausayi bata banba yanzu dai shikenan mune manya a gida Aira ta fad’a tana murna Dariya Amma tayi ta ce “Wlhko muci karanmu ba babbaka Har suka isa gida Suna gulmar yayyin nasu.

Bayan kwana biyu Arman ya koma Wanda dak’yal Ya shawo kan Aira saida ya shaida mata nan da two weeks zaidawo yayi hutun One months sosai Aira tayi farinciki haka ko akayi baiyi sati biyu ba ya dawo Aira jinta take cikin Farinciki Marar musaltuwa Tunda yazo Aira ta tarki k’aryar fita Wanda Aysha ce ta d’aure mata gindi saita kira Mamy ta ce ” Dan Allah Aira tazo ta tayata Aiki haka Mamy zata barta batare da kokontoba Dan yanzu Hankalinta ya kwanta a tunaninta Aira harta mance da ARMAN.

A palourn Aysha suke zauniya su sha Hirarsu Saisu shafe awa Hud’u suna Hira Yauma yazo Aysha ta sa Aira ta kawo mashi snacks Kad’an yaci Shima Dan Aisha ta nuna bazataji dadi ba Sosai Aira da Arman suke shan hira Sai wajen magriba Arman ya tashi yace zasu wuce ”

“tashi Aira tayi ta ce ” bari naje nayi mata bankwana saimu tafi “ta fad’a ta na Zuwa Palourn Chan ciki Inda Aysha take da mijinta ” Abdul ya ce su Aira manya Angama Shan Love din”Dariya tayi tare da rufe fuska ta ce “Kai yaya kaima haka zakace Nasan Aunty zata fad’a maka ” Aysha dake jikin mijinta kallon Aira tayi ta ce “Ai yanzu ba wani rufe rufe y’an matan Abba yanzu kuma sai ina”.

Uhm gida zamu wuce”Okay to ki gaishe da mutanen gidan”To Aunty zasuji “Saikuma yaushe ” Sai idan kuma an barni kinsan dazu dak’yal Mamy ta bari cewa tayi nafiya miki zarya”Dariya Aysha tayi ta ce “Lallaima Mamy Danma batasan ba ba saboda ni ake zuwaba Duka zuwan na Arman”

Dariya tayi ta ce “Kai Aunty Nifa saboda ke nake zuwa Yanzu dai munwuce kar ya gaji da jira” Okay to Allah kiyaye Aira harta juya zata fita Aysha ta kira sunanta Juyowa tayi tashi Aysha ta kama hannunta ta ce “Sis karki bari wata matsala ta afku kidinga bi a hankali kinsan Abba yasan kuna had’uwa da Arman a gida na ni kaina na shiga ukku sannan ku daina yawo barkatai a gari Dan Allah saboda gudun zargi ”

k’asa tayi da kanta ta ce “Insha Allahu Aunty zan kiyaye ” Hug din juna sukayi tukwana Aira ta tafi Bayan Aira ta tafi Mijin Aysha ya ce “My love abunda kike kina kyautawa kuwa?Cike da mamaki Aysha ta ce ” Me Dia”Na barin Aira da Arman suna kebewa anan mana Bayan iyayenku a yanda kika fad’amun sun rabasu me zaisa ki basu shawarar su hakura da juna Ita kuma ki bata shawarar ta tunkari karatunta Amma wannan hanyar da kika bud’e musu ba mai bullewa bace

yanda Abba keda burin y’ay’anshi suyi karatu banga Alamun ko Kad’an a idon Aira akwai wani karatu a ranta ba bakiga Duka Rayuwarta a soyayyar ARMAN take tafiya ki bata shawarar Ko bazata rabu da shi ba ki nuna mata karatu zatayi kafin inma auran ne ya biyo baya bakiganin yarinyace marar wayau”ya k’arasa fad’a yana Jan numfashi

“Shiru Aysha tayi Tabbas hakane cike da damuwa ta ce ” Baby bazaka gane bane Aira da Arman suna matuk’ar son junansu Wanda ni kaina bazan iya kwatanta maka kalarsa ba ta Riga ta mutu a kanshi tun kafin tasan kanta Shima kuma haka sauya musu ra’ayi Abu ne mai wahala dalilin da yasa kuma nake barinsu zuwa nan dole ne fa saisun had’u a koma ina ne gudun kaucewa hanya kasan ance duk Inda mace da namiji suka had’u na ukkunsu shaid’an ne dukda nasan ba halinsu bane amma kiyayewa na da kyau hakan yasa nace su dinga zuwa nan yafi kwanciyar hankali akan suje wani wajen daban

Ina son y’ar uwata Abdul sosai bantaba Jin a raina ba wai ba ciki d’aya muka fito da Aira ba sonda nake mata yafi son da nake yiwa wanda muke uwa d’aya uba d’aya Dan haka bazanyi Abunda zai chutar da ita ba “hakane kuma baby da wata ya wannan Allah dai ya kawo musu mafita cikin Sauk’i ” Ameen Aysha ta fad’a .

Aira ko Arman har gida ya maida ita kullum saisun had’u idan basu hadu ba idan zata tahfex to sun hadu idan ta dawo Innace ta fito Cikin masifa Kallon Aira tayi tare da mik’a mata wayar ta ce ” kiramun Mujahid laifin me nayi mishi da ya daina zuwa wajena “Aira ta kira mata Mujahid yana ganin kiran Inna murmushi yayi ya kira cikin Masifa Inna ta ce ”

Mujahid ko d’an fari na kashe maka ai sai haka watanka nawa rabonka da gidana “Hakuri Arman ya dinga bawa Inna tare da cewa gashinan zuwa yanzu Lokacin da yazo Aira na zaune akan sopa tana kallon wani series a Bollywood Hankalinta na wajen ya shigo tana ganinshi itama ita yake kallo kashe mata ido yayi girgiza kai tayi ta na murmushi inna ko washe baki tayi ta ce “”

” Ko kaifa mai gidan Har hankali na ya kwanta ashe ma kana garin shine Ko kazo ka gaishe ni ko”To yanzu ba nazo ba y’ar tsohuwa sai a rufe chapter ya fad’a yana zama kan sopa K’asa Inna ta zauna Suka shiga gaisawa da Arman sai zolayanta yake dayake tana son ganinshi yau ko fad’an Babu Kallon Aira tayi da take kallo ta ce .

“Hajara bakiga Mujahid ba ne Kika wani kauda kai” Juyowa Aira tayi ta ce “Na ganshi Inna ta fad’a tana kauda kai” Hakan da tayi duk cikin shirinsune “Salati Inna ta farka ta kalli Arman ta kalli Aira ta ce ” Nashiga Ukku ni Halima ba dai Iyayenku sunyi nasarar raba ku ba.

Kallon Inna Aira tayi ta kalli Arman dake satar kallonta tashi Inna tayi Ta kamo hannun Aira ta janyota ta had’a da na Arman ta fashe da kuka ta ce “Karku sake Iyayenku su zama sanadiyar lalacewar daddaddiyar Tarayyarku mai cike da Albarka Na tabbata Allah da abunda ya gani ya had’aku Karku sake ko dad’i ko wuya suyi nasarar rabaku koda bana numfashi Duk sanda alak’arku ta lalace to ina da tabbacin komai ya Riga da ya lalace Iyayenku bazasu tab’a Shiryuwa ba muddin bakwa tare da junanku Kune nake fatan ku zama silar Daidaituwar Iyayenku kuyimun Alkawari Dan Allah bazaku rabu ba kodan ni ko da bana raye” .

Aira tunda Inna ta fara jawabin nan take kuka Rungume Inna tayi Cikin kuka Ta ce “Insha Allahu Inna munmuki Alkawari sannan ma kina raye insha Allahu” Arman ma Rungume Inna yayi cikin k’arfin hali ya ce “da yardar Allah Inna zamu sanyaki Farincikin da kike buk’ata da ranki insha Allahu” Allah yayi muku albarka Ya nunamun Ranar da nake ta tsumayen jira da raina da lafiya”Kallon juna Arman da Aira sukayi sai kuma Aira ta sadda kai.

Washegari Aira na bangarensu ta na Wanki A washing machine Mamy ta lek’o ta ce “Aira idan kin gama ki shirya zaki rakani Gidan Safiya zanyi mata barka” To Mamy Ai na gama ma bari naje na shirya Cikin kankanin lokaci ta shirya a parking space ta tarar da Mamy “Mamy ta ce duk’ursa na goya maki shi ” Cikin marairaicewa Aira ta ce “Goyo kuma Mamy ki bari na daukeshi wlh d’annan naki nauyi garai Yaro wata shidda ai Yama wuce goyo ni banma iya goyon ba” Hararta Mamy ta yi ta ce “To yau saiki koya idan dankine wazai goya miki ” Dariya Aira tayi ya ce “Maid house mana Mamy yanzu Dan Allah taimaka ki bari na rikeshi a hannu” to Naji raguwa muje Motarta Mamy da dauko tayi mata key suka bar gidan Aira na gaba da Amer a hannunta.

Suna isa gidan Safiya Mamy tayi mata barka Hjy Safiya ce ta ce “Wai Rahama y’armuce ta zama Haka Allah mai iko kice kin kusa Taramu” Dariya Mamy tayi ta ce “Aikodai ku iyaye saiku fara shiri Fita Aira tayi ta basu waje Arman ta kira tayi mashi kwatancen Inda Take cikin k’ank’anin lokaci ya kira ya shaida mata yazo.

tsayuwar Hijab d’inta ta gyara tukwana ta fita A mota ta tarar dashi ciki ta shiga Arman ya ce ” kindai maidani bita zaizai ko My cutie duk Inda kikayi ina binki”Dariya Aira tayi ta ce “Yaya kenan ni kuma a kirani da me da duk Inda naje ina kiranka” Sun tab’a Hira Kad’an cikin nishad’i Sun kwashi wajen minti Talatin Mamy koda suka gama fira da Hjy Safiya suka fito sosai tayi mamakin k’in ganin Aira da batayi ba Tana fitowa waje bata ganta ba Aira ko ta cikin mota ta Hango Mamy sosai gabanta ya fad’i ta ce “Na shiga ukku ‘”

‘Kallon Inda take kallo ARMAN yayi ya ce ” Daman tare kuke da Mamy”Eh wlh yaya wlh banzaci har zata fito yanzu ba”To yanzu yi Sauri ki fita danma Mamy ce Ai da sauki “Kamar wacce kwai ya fashewa haka Aira ta fito daga motar Sosai Mamy ta kafeta da idanu ganin Fitowarta daga mota Aira ko dukta tsure bin motar da Kallo Mamy tayi Bayan ya tafi Kallon Aira tayi da ta kasa motsi ta daka mata tsawa ta ce ” Saikizo mu wuce gida ko”

“Cike da tsoro Aira ta shiga Mota Mamy ta zagaya ta tada Ranta na matuk’ar k’una tama rasa ita ina zata saka ranta game da Lamarin Aira daman basu rabu ba kenan Aira ko duk ta tsure jira take taji zagi ko saukar dukan Mamy amma bataji ba harsuka isa Mamy Saidai ta Kalleta ta girgiza kai ta ma rasa abunda zatace ” Suna isa Aira ta ce “Mamy Dan Allah kiyi hakuri” girgiza kai kawai Mamy ta yi ta ce “Allah ya shiryeki Allah ya shiryeki ita kad’aice Addu’ar da zan dinga maki ta fad’a tare da shigewa ciki Aira ko kamar wacce kwai ya fashewa Haka ta shiga part d’in Inna idan ta tuno kuma da karfafa gwuiwar da Inna tayi musu saitaji sanyi A ranta.

Bayan Sati Biyu Da misalin k’arfe goma Na dare Aira na kwance wayarta tayi ringing d’auka tayi Dan tasan Arman ne kad’ai ke kiranta ” ki shirya yanzu ina palourn inna zamuje wani wuri,Cike da mamaki Aira ta ce fita kuma Yaya ?ina zamuje a Daren nan “kede kiyi abunda nace kinsan dai bazanyi Abunda zai cutar dake ba Kuma kinfi kowa sanin bansan gardama ” Badan Aira ta lamunta ba ta ce To yaya Doguwar Hijab Ta d’auko tare da sanya flat takalmi ta fesa turare d’an Kad’an ta fito a palour ta tarar dashi shida Inna tana fitowa Inna ta ce.

“To kumaza kuje Allah kiyaye” Kallon Mamaki Aira takebin Inna Dashi to ina zasu a Daren nan Arman ko har yayi gaba binshi baya Aira tayi Tana zuwa harya tada Mota da yake ciki ya shigo da ita Aira na shiga suka ja suka bar gidan daman get man ya bud’e musu kofa.

Aira dai zuciyarta cike take ta tunannika kala_Kala”A wani katoton shagon make up taga yayi parking Kallonshi tayi murmushi yayi mata ya ce “muje ko” Itama mayar mashi da murmushin tayi”Ta bishi suna shiga Shagon y’an mata biyu Aira ta tarar Duka sun girmeta Cikin girmamawa suka dinga gaishe da ARMAN ya amsa sama sama Mai kwalliyar ta ce .

“yallab’ai ko ita ce ” Gyad’a mata kai yayi ya ce “ita ce so nake kiyi mata kwalliyar da Baki tab’a yiwa wata irinta ba ko nawane zan biyaki” Dariya Zey tayi ta ce “Angama yallab’ai kai kanka dak’yal zaka ganeta” Haka nakeso Rafar y’an dubu ya bata guda biyu Zey sai Godiya take dan yau ta warke Kallonshi Aira tayi Shima ita yake kallo murmushi ya sakar mata bata samu damar mayar mashi ba saboda a tsorace take saikuma ta tuna Ai Arman bazai tab’a abunda zai chutar da ita ba hakan yasa ta saki jikinta.

Fita Arman yayi ya ce zaije ya dawo itadai tana zaune mai make up ta sanyata tayi wanka a toilet d’in Shagon tana fitowa ta bata wata had’ad’d’iyar gown Fara ita kanta Aira saida ta tsorata da ganin rigar Dan bama zata iya kwatanta Misalin kud’inta ba irin rigunan Amaren nan ce Amaren ma sai d’an waye da wane Bayan Aira ta sanya rigar sosai tayi chif a jikinta kamar a jikinta aka d’inka rigar.

Ba b’ata lokaci aka shiga tsansarawa Aira kwalliya ta ban Mamaki saida suka shafe sama da Awa d’aya tukwana aka gama ya subhanalla Ai Ni kaina kasa gane Aira nayi ta sani sauya kamar ba ita ba tayi wata irin masifar kyau Wanda ko mace ta ganta saita yaba da kyan da tayi mai make up cewa take masha Allah a Gaskiya bantaba make up mai kyan wannan ba kodan nayi a jikin me kyau ne kanwata ki godewa Allah Gaskiya yayi miki kyau da baiwa kala kala”

“murmushi Aira tayi ta ce “Nagode hotuna Sosai Zey da abokiyar aikinta suka dinga wa Aira 11:30 Zey wayarta tayi ringing itadai Aira bataji me akace ba daga dayan bangaren Taji dai ita ta ce ” Eh Angama Yallabai yanzu haka muna shirin Tahowa da ita ne bada jimawa ba “tana gama wayar itama ita da d’ayar suka shirya cikin wasu Riga da sicket pink rigar siket din bak’i

rigar Anyi rubutu a jiki an rubuta *A & A* k’asar rubutun kuma anrubuta HBD MRS..sauran rubutun taga An rufe da wani Abu ita dai bata tambayesuba har suka gama shiryawa suka fito a wata dalleliyar mota suka shiga Aka jasu suka tafi Basuyi wata diguwar tafiya ba motar ta tsaya Alamun sunzo wajen da zasu Kallon Aira sukayi tare da kama hannunta Zey ta d’auko wani Farin kyalle sai kamshi yake Duka zanan heart ne jikinshi zagayawa sukai suka rufewa Aira idanu dashi itadai kawai binsu take taga ikon Allah.

a haka suka dinga Jan hannunta idonta Rufe suna zuwa wani waje taga sun damk’a hannunta jikin na wani ko wata ita dai bata bambance ba tana nan tsaye anyi kusan 5 minutes tukwana taji Wanda yake rik’e da hannun nata ya fara since mata Kyallen da aka rufe mata Idanu Har ya isa sincewa yana gama sincewa Taji suka wajen ta d’auko satin wak’ar Love mai narkar da zuciya wara idanunta tayi Dan son ganin Da gaskene ko mafarki take Arman ta Kalla dake sakar mata murmushi sosai yayi kyau sanye yake cikin bak’ar coated Fuskarnan tashi Cike da annurin farinciki a cikinta.

Juyawa tayi ta kalli wajen Bata San Lokacin da ta furta Kalmar wow ba “Duka wajen Anyi mai decoration na ban mamaki ko biki Sai y’ar gata zata samu wannan daular Duka wajen kuma robobine ga wasu danjoji da suke Rubuta Happy Birthday Aira Wasu na fita wasu na fitowa ga kuma mutane Sunkai 20 Sanye da Riga An rubuta *A A HBD MRS ARMAN* Photographer ko sunfi biyar hada Camerar gidan wasu gidajen television ta gani bama ta Tantance gidan television d’inba Juyawa tayi ta kalli wata k’atotuwar Laptop dake nuna duk abunda suke Alamun Live Kenan Kallon Arman tayi da ya ke ta kallonta Yasan dole tayi mamakin duk wannan Abun da ya shirya .

Ai batasan lokacin da ta fad’a Jikinshi ba ta saki kuka ” Tallabota yayi cikin rad’a ya ce “Kiyi shiru mana so kike ki b’ata make up d’inki ko so kike mutane suce Matar tawa saurin kuka gareta ” Dagowa tayi ta Goge hawayenta saikuma ta zumb’uro mai baki Murmushi yayi ya kama hannunta .

A wani makeken High Table suka Je K’atoton cake shake wajen zan iya cewa tunda nake ban tab’a ga cake mai girma da Kyanshi ba Ga wata had’ad’d’iyar agogo dake Juyawa a Gaban wajen Rik’e hannunta yayi Tare da wuk’a a hannunsu.

Mutanen wajen ne suka hau lissaafi daidai lokacin da 12 ta kusa Bugawa 1,2,3,4,5,6,7,8,9,10 Arman ya kama hannunta suka Yanka cake Duka wajen tab’i ya d’auka tare da wakar Happy Birthday Aira sosai wak’ar tayi Bala’in dad’i Aira zata iya cewa cikin rayuwarta bata tab’a shiga farinciki irin wannan ba kwata kwata ta ma mance yau ne ranar birthday d’inta sai yanzu ta tuna .

Ita ta fara bashi cake d’in a baki tukwana Shima ya bata ya na Gama bata Ya amshi Abun magana tare da kallonta duka camera na kanshi

k’asa da kanta Aira Tayi Ya fara magana cikin zazzak’ar muryarshi kamar haka “Alhamdulilla Alhmdllh Alhamdulilla My Love sister she’s +1 year God bless you for many more years Happy Birthday Lover for you is the real,real,real,a deal a really ,really really big deal You are my North Star and help me know my direction in life you make me happier and a better person Happy Birthday to you My cutie Aira I Love I Love I Love you so much My Cutie Please Love Me my Aira sannan ya durk’usar da gwuiwarshi har k’asar Inda take tare da kallonta ya had’e hannayenshi biyu Alamun rok’o ya ce ” will you marry me?………..✍🏿

*Tofa ya kenan Arman ya k’ara ringimo wata rigimar ya kuke tunanin iyayensu zasuyi idan sukaga wannan birthday d’in a duniya*???

*Wani irin mataki kuke tunanin Abba Da Daddy zasu d’auka Kuna tunanin zasu bari wannan Abun ya tafi a banza kuwa*??

*Yau dai Arman ya fito ya bayyanawa Aira tare da duniya Kalar son yake mata tilon d’an governor guda ya dukursawa mace cikin bainar Jama’a*

*Iyayensu zasu samu daman raba su kuwa*???

*ya makomar soyayyarsu zata kasance nan gaba Zasu mallaki juna ko akasin haka*

*Idan iyayensu suka samu damar rabasu ya kuke tunanin halin da wannan masoyan zasu shiga yanda suke jin bazasu iya cigaba da rayuwa ba ba tare da d’ayansu ba*

*Shin Abba da Daddy Zasu shirya kuwa*?????

*Duka wannan Amsoshin zaku samesu ne kai tsaye idan kin biya 200 kachal zaku karanta cikin kwanciyar hankali karku bari kice sai an sata a kawo maki ki karanta ba girmanki bane Hajiya ki biya ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali darajarshi tafi ta kudin na barshi hakane a saboda k’auna da soyayya Masoyan Asali*💃💃💃

*wannan shine last page na free page na wannan littafin kamar yanda na fad’a daga yanzu sai Wanda suka biya ne suke da damar ci gaba da karanta wannan k’ayattacen littafin mai cike da salon burgewa sannan duk Wanda zata saya ta saya da zuciya d’aya Karki saya ki fitar mun da Littafi kud’in karantawa kika biya ba na mallaka ba Kunsan dai mahimmanci hak’k’i Sarai bazanyi Allah ya isa ba Ammafa ban yafe ba akwai hak’k’i ni da yaya Arman koda kudinka saida rabonka nasan babu wacce zataso ayi tafiyar nan babu ita ga masu bukatar saya ga tsarin yanda biyan yake*

*Normal group Transfer Ko hoton katin MTN #200 kachal*

*PC Wanda basa buk’atar sakasu group ta PC zandinga tura musu zasu biya #300*

*VTU 300*

*Zaku turo ta wannan number 07026166536*

_Saimun had’e a Paid group_

Taku har kullum

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

👇

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]