[Advertisements⬇️]

GARKUWA BIYU COMPLETE BY HASSANA D'AN LARABAWA - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GARKUWA BIYU COMPLETE BY HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*👇

GARKUWA BIYU

*BABI NA D’AYA DA NA BIYU*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K’AI,SARKI MABUWAYI GAGARA MISALI,MAI SHEKARANJIYA DA JIYA DA YAU DA GOBE DA JIBI,WANDA YAYI MINI BAIWA YA BANI BASIRA DA HAZAK’AR RUBUTU DOMIN FAD’AKARWA DA WA’AZANTARWA DA NISHAD’ANTARWA DA ILIMANTARWA.

KAMAR YARDA AKA SABA MASOYANA YAU MA GANI NA DAWO A SHIRYE TSAF DOMIN KU,DOMIN DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA,SOYAYYA DA ADDU’AR DA KUKE MIN TA FATAN ALKAIRI KAD’AI TA ISHENI TINK’AHO DA JIN DAD’I,INA FATAN ZAKU CIGABA,KUMA ZAKU BINI A CIKIN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA *GARKUWA BIYU* DOMIN KUJI WANE SALO YAKE D’AUKE DASHI,KUN SAN A KO DA YAUSHE SALON LITATTAFAINA SUNA SAUYAWA,TO WANNAN MA NASA SALON NA DABAN NE,ALLAH YA BANI IKON FARAWA LAFIYA KUMA NA GAMA LAFIYA.🥰🥰🥰👏👏👏🌹🌹🌹

 

 

A hankali ya shigo da motarsa cikin harabar Gidan,bayan mai gadi ya wangale masa k’aton get d’in,ya nufi parking space ,wucewar mintina biyu ya bud’e murfin motar ya zuro k’ayatattun k’afafuwansa ya sakko,hannunsa rik’e da briefcase, kyakkyawar fuskar sa sanye da glass, ya kulle motar ya tako a hankali cikin tafiyar nutsuwa da d’aukar hankali,da sauri mai gadin ya nufo shi ya zube a gabansa cikin girmama wa.

“Yallab’ai barka da dawowa”

Yayi murmushi yana gyad’a kai.
“Barka kadai Umar,ya Gidan ya wuni?dafatan komai lafiya?

Umar ya sake russunawa.

” Alhamdulillahi mun wuni lafiya,sai dai d’azu naga GARKUWA ya fito daga ciki yana kuka,amma da na tambaye shi yak’i yin magana,gashi can ma zaune a k’ofar shiga parlour ”

Fuskarsa ta nuna rashin jin dad’i,ya D’an waiwaya yana hango yaron zaune ya zabga tagumi, da alamun damuwa a fuskarsa,ya dawo da kallonsa kan Umar ya D’an murmusa.

“Shikenan no problem Umar,koma wajen aikin ka zan ji damuwar da kaina”.

Umar ya mik’e yana godiya,shi kuma ya fara takawa a hankali har ya isa gaban yaron D’an shekara shida,Wanda yake zaune a kan step’s d’in shiga cikin parlour d’in Gidan

Ya D’an d’auki lokaci a gaban yaron yana ta kallon sa cikin damuwa da bugawar zuciya,kafin a hankali ya zame ya tsuguna gabansa,ya d’aga tattausan hannunsa ya d’ora akan hannun yaron yana zame tagumin da yayi,firgigit yaron ya d’ago kansa,yana ganin Wanda yake gaban sa da hanzari ya silalo ya fad’a k’irjinsa yana rik’e wuyansa,hawayen sa ya tsinke ya sauka kan kafad’ar mahaifinsa.

Tsawon minti biyu ya bar yaron yana kuka da shesshek’a,har sai da yaji ya lafa tukunna yasa Hannu ya d’ago shi yana kallon fuskarsa ,yasa Hannu ya share masa hawayen sa,yaron ya bishi da kallo yana k’ara kwab’e fuska zai kuma wani kukan,da sauri ya girgiza masa kai yayi magana a hankali.

“Bana son sake ganin hawaye a idanuwan HAMZA GARKUWA,kai fa jarumi ne Hamza,shi Jarumi baya kuka kullum zuciyarsa a dake take,abin da yasa ma yanzu na k’yale ka kayi domin kaji dad’i ne,ka san wani lokaci idan yaro yana kuka a kan so a barshi yayi domin wata damuwa ta yaye daga k’irjinsa,daga yanayin da naji hawayen ka sun zubo da d’umi na tabbatar na damuwa ne,shiyasa na barsu suka zuba domin kaji sauk’in damuwar,amma menene damuwarka da har ka kasa zama a cikin gida ka fito kana kuka”?

Ya sunkuyar da kai yana wasa da yatsun mahaifin nasa,yayi magana cikin muryar rauni da yarinta.

” Bana son ganin hawayen Ammina ne Abba,shine na fito nan”

“Yau ma tayi kukan ne”?

Ya tambayeshi da Hanzari.

Ya gyad’a kai yayi rau rau da idanu.

” Eh tayi sosai Abba,har idanuwanta sun yi ja”

Ya lumshe idanu ,a hankali ya ambaci.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”
Da hanzari kuma ya mik’e yaja hannun yaron yace .
“Tashi mu shiga ciki”

Yaron Ya mik’e,sannan ya mik’a Hannu yace.
“Abbana kawo jakar na rik’e maka”
Ya mik’a masa,sannan ya rungumeshi a gefensa suka shige parlourn.

Ta na zaune a d’aya daga cikin kujerun parlourn,kanta kwance akan cinyoyin ta,sallamar su bai sa ta d’ago kanta ba,suka tsaya suna dubanta suna sauke numfashi,a hankali ya juya ya kalli yaron Yayi magana a hankali.

“Tafi ka kai min jakar bedroom, daga nan kayi zamanka kayi karatu”.

Ya amsa ya wuce ya na waiwayen su,har ya shige bedroom d’in,shi kuma ya tako a hankali zuwa kusa da ita ya zauna gefenta,a hankali kuma ya kai Hannu ya d’ago fuskarta da ke sunkuye yana son su had’a ido,tsigar jikinsa ta wani mik’e yarrrrr!ganin yadda idanuwanta suka yi ja sosai alamar taci kuka ba da wasa ba,ta bishi da kallo hawaye na k’ara ziraro mata,ya kai D’an yatsan sa ya share mata,sannan ya jata jikinsa a hankali ya rungumeta tsam yana ajiyar zuciya,hannunsa d’aya ya kai kan lallausan gashin kanta Wanda bai cika tsawo da yawa ba yana shafawa,d’aya hannun bisa gadon bayanta yana mata messaging.
Sai da suka d’auki tsawon lokaci a haka kafin ya d’agota daga jikinsa,ya tallabo kumatunta yana k’ok’arin jefa idanunwansa cikin nata,suna had’a idanu ta runtse nata idon,bata fiye son kallon k’wayar idon sa ba saboda maganad’isun dake fizgarta , shi kuma ya lumshe nasa idanun ya bud’e,a hankali kuma cikin maganar rad’a yace.

” Kullum na ganki cikin wannan yanayin sai nai ta tuhumar kaina anya kuwa na cancanci a kirani da GARKUWAR ki?bana son ganinki cikin damuwa ko kad’an,ki taimakawa numfashi na ki daina yawan damuwa domin nima kina sakani a damuwar,ba iya ni kad’ai ba har D’an mu da muka Haifa, me ya saki kuka a yau HIDAYA?kin tuna da k’addarar rayuwarki ne?

Ta girgiza kai a hankali hawayen ta ya kuma gangarowa,ya D’an dafe kai yace.
“Oh my God”

Sannan ya d’ago k’afafuwanta zuwa kan cinyarsa yana duba su yana mammatsawa a hankali,ya d’ago ya kalleta.

“K’afarki tana ciwo ne?ban ga kumburi a tare da ita ba,ko wani wajen nayi miki ciwo ne?

Nan ma ta girgiza kai babu magana.

” Hidaya” ya ambaci sunanta ya na mai k’ura mata idanu,ta d’ago kanta ta kalleshi.

“Menene? Don Allah ki fad’a min”Ya tambayeta idanuwansa cikin nata,ta fara k’ok’arin sunkuyar da kai,da hanzari ya tallabo ta ya marairaice.

” Idan baki fad’a min ba wallahi zan yi Kuka Hidaya ,a yanzu baki ji yadda k’irjina yake ciwo ba ganin hawayen ki”

Ta kwantar da kanta kan kafad’arsa tana ajiyar Zuciya,a hankali tayi magana muryarta na shak’ewa.

“Duniya cike take da mutane mabanbamta,kuma kowa da irin tasa k’addarar,wani Mummuna wani kyakkyawa,wani jarrabawarsa mai tsananin zafi ,wani kuma mai sauk’i,kowa da yadda tasa take zuwar masa a yadda Allah ya k’addara masa,ba kuma wai don ba ya son bayinsa ba yake jarrabarsu,illa domin ya gwada imanin su”

Ta D’an yi shiru tana maida numfashi,shi kam ya k’ura mata idanu,ta gyara zaman ta a jikinsa ta cigaba da magana.
“Wannan kukan da kaga ina yi k’addarar wasu na tausayawa,shiyasa nake zubar musu da hawaye”

Yayi mamaki sosai har ya kasa b’oyewa,da hanzari ya magantu.

“K’addarar wasu kuma Hidaya?yanzu akwai k’addarar da zaki tausayawa wadda ta wuce taki Hidayaa?kin manta jarrabawar ki a rayuwa ne?shin kin manta da taki k’addarar ne?wad’annan su waye da kike tausayawa k’addarar su?

Tayi murmushi mai ciwo.

” A yayin da wasu zasu tausayawa k’addarata da jarrabawata,a lokacin ne ni kuma idan naji ta wasu zan tausaya musu”

“Su wanene”? Ya tambayeta kai tsaye.

Ta amsa cikin girgiza kai.
” Ban san su ba,ban tab’a ganin su ba,Labarin su kawai na karanta ya tab’a ruhi na,kai ma kayi mamaki ko?

Ya d’aure fuska kad’an.

“Wai kina nufin daman kukan da kike yi akan karatun littafi ne?kina nufin labarin wasu kika karanta na k’arya kika zauna kina kuka?ba na hanaki zama ki karanta littafin da kika San zai saki kuka ba?yau kuma na wace marubuciyar kika karanta?

Ta bishi da kallo.

” kamar Kullum,yau ma littafin HASSANA D’AN LARABAWA na karanta mai suna SANADIN HOTO,hak’ik’a labarin ya tab’a min zuciya sosai,kamar yadda sauran litattafanta na HASSANA DA HUSSAINA DA CIN AMANAR RUHI suka tab’a min zuciya”

Haushi ya kamashi,ya fara fad’a a zafafe.

“Na rantse da Allah da zanga marubuciyar nan sai nayi shari’a da ita,akan me zata dinga saka min ke kuka?haka kawai ta zauna ta dinga rubuta k’arya tana saka ku kuka,saboda rashin aikin yi,ku rasa me zaku yiwa kuka wai sai littafi?

Yayi D’an tsaki yana zamewa ya jingina da kujerar.

Zahra tayi murmushi.

” Ba zaka gane ba ne,Abin da baka sani ba shine,ya wanci litattafan HASSANA D’AN LARABAWA Gaske ne sun faru,sannan tana duba abubuwan da suke faruwa a zamanin da muke ciki tayi rubutu a kai,Wanda zai fad’akar kuma ya nishad’antar da mutane,ni dai ina sonta,kuma ina son karanta litattafan ta domin mutum zai k’aru da wasu Abubuwan,duk da ban Santa ba ban kuma tab’a ganinta ba amma zan karb’i Numbarta wajen Sumayya domin muyi magana ni da ita,da man Sumayyan ce ta turo min litattafan na karanta”

Ya D’an yi mata kallon k’asan ido sannan ya lumshe su,a hankali kuma yasa tattausan hannunsa ya rik’o nata hannun mai kama da Auduga don laushi,ya matse a cikin tafin hannunsa,ta d’ago idanuwanta wad’anda basu kasance farare tas ba,saboda akwai wani sirki a tare dasu na lalura,ta dubeshi, fuska babu walwala idanuwansa a kanta ya fara magana.
“Zan b’atawa Sumayya rai My Hidaya,sanin kanta ne cewa duk duniya bana son ganin abin da zai saki kuka ko ya b’ata miki rai,akan me zata baki littafin da zaki karanta kiyi kuka?

Ta jawo jikinta kusa da shi ta zame ta kwantar da kanta kan yalwataccen k’irjinsa ta D’an rungumeshi ta na sauke ajiyar zuciya tace.

” Don Allah kar kaga laifinta,ni na dameta akan ta bani saboda yadda naji ana cewa litattafan sun yi dad’i,wallahi ma hanani tayi nai ta takura mata da naci shine ta bani na karanta,kuma wallahi na k’aru sosai dasu,Don Allah kayi hak’uri kar kayi wa Sumayya komai”

Yayi shiru bai ce komai ba,ta d’ago kanta tana kallon kyakkyawar fuskarsa idanuwansa a rufe,ta D’an shafi fuskarsa cikin sanyin murya tace “ka ji” yayi wal ya bud’e idanun ya sauke akan ta,ya D’an d’aga gira yayi magana a hankali”Menene?

“Kar ka yiwa Sumayya komai” ta ambata cikin shagwab’a.
“OK,ya fad’a yana yunk’urawa ya mik’e da ita a jikinsa.
” Muje bedroom wanka nake so nayi,za ki tayani ko Hidaya na?

Tayi murmushi ta na gyad’a kai sannan ta sak’alo wuyansa ta rad’a masa wata magana.
Shi ma yayi murmushi ya tsuguna gabanta yace.

“Abu mai sauk’i kenan Hidaya na,maza ki hau bayan mijinki Garkuwar ki”

Ta haye bayansa ta kwanta luf tana murmushi,shi kuma ya mik’e yana zunkud’ata suka shige bedroom suna dariya.

Hamza da ke d’akin sa yana karatu jin dariyar da iyayen sa ke yi sai yayi murmushi,hankalin sa ya kwanta,domin damuwar mahaifiyar sa ta na damun sa,ya kuma tabbatar Mahaifin sa yana k’ok’ari sosai wajen tafiyar da da uwar Ammin sa a duk lokacin da ta shiga damuwar,ya lumshe idanu ya mai da kan sa kan alk’ur’anin gaban sa ya cigaba da karatun sa cikin kwanciyar Hankali.

 

Comment
Share
Vote
Pls

*TYPING* 📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

 

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI(SABON SALO)

*DA KUMA*👇

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA UKU DA NA HUD’U*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

Washe gari yana fita wajen Aiki sai Hidaya kawai a gidan,Hamza ma baya nan yana school,tana kwance a bedroom d’in ta hannunta rik’e da wayarta,ta kunna data ta shiga b’angaren watsapp,duba sak’onnin da suke shigo mata tayi,ba wasu masu yawa bane sosai,sak’on da ke sama ta fara dubawa sai ta tarar daga Sumayya yake,ta shiga ta duba sai taga Sumayyan na online a lokacin,amsa mata sallama tayi,Sumayya taga maganar , sai ta kuma turo mata sak’o kamar haka.

“Ykk?ina mutumi na Hamza Garkuwa?

Hidaya ta bata amsa da cewa.

” Lafiya k’alau Sumayya,ina khalifa?dafatan kuna lafiya?

“Lafiya k’alau muke, ya fita office ma.
Wai kuwa kin kammala karatun littafin nan?

Summaya ta zarce da tambayar ta,Hidaya ta bata amsa da cewa.

” Na gama tun jiya wallahi,Yayi dad’i da ma’ana sosai,amma fa na sha kukan tausayin Ya Abbas da Safah Sumayya,ni yanzu ma lambar marubuciyar nake so ki bani saboda na jinjina mata akan namijin k’ok’arin da tayi wajen rubuta litattafan ta masu dad’i da k’ayatarwa,babu shirme ko kad’an”

Sumayya ta turo da emoji na dariya,sannan ta aiko text

“Ai gaskiya tana k’ok’ari sosai fa,yanzu haka wani littafin ta nake karantawa me suna BAHAGON LAYI,Wallahi Hidaya kika karanta littafin nan za ki sha dariya kamar ba gobe,tabbas Aunty Hassana D’an larabawa ta wanke mana zuciya a bisa kukan da muke sha a litattafan ta,wannan babu kuka sai dariya,jiya fa sai da khalifa ya koroni parlour wai zan hanashi bacci da dariya ta,aikuwa da na zauna ina ba shi labarin littafin sai da Yayi ciwon ciki don dariya,gaskiya littafin ya had’ ba kad’an ba,cikin hikima tayi amfani da abubuwan da suke faruwa a zamanin nan ta fad’akar kuma ta nishad’antar”

Hidaya ta tura mata emoji na tsalle da murna da text kamar haka.

“Wallahi har kin sa na fara zumud’i tun kafin na karanta,ki turo min complete document d’in sa please Sumayya,kuma na san kina da numbarta tunda kina cikin group d’in ta,don Allah turo min yanzu,Allah yasa dai idan nayi mata magana ta kulani,naji an ce yawanci marubutan nan girman kai ne da su ,ba sa kula mutane”

Sumayya ta bata amsa.

“Eh ina da lambarta bari na baki,kuma wallahi zaki samu tarba ta mutunci daga gareta,gaskiya bata da wulak’anci,da kin mata magana da zarar ta gani za ta baki amsa cikin karamci,kuma ko littafin ta kike nema zata baki ba tare da jinkiri ba”

Hidaya ta tura mata emoji na tsalle da dariya,sannan ta tura text.

“Masha Allah,amma naji dad’in hakan,yanzu turo min lambar da littafin”

Sumayya ta turo mata lambar ta contact, sannan ta turo mata littafin BAHAGON LAYI,Hidaya tayi mata godiya sosai,sannan ta fita daga chart d’in su ta shiga contact d’in Hassana D’an larabawa,sai taga bata dad’e da sauka daga online ba,hakan yasa kawai ta tura mata sallama sannan ta sauka ta kashe data.

Bayan ta fita daga watsapp sai ta gyara kwanciyar ta sosai,sannan ta shiga wani app na wayarta mai suna (W P S office),ta nan take karatun document,nan da nan taje ta bud’e littafin BAHAGON LAYI,wanda Sumayya ta turo mata,ta fara karatu fuskarta d’auke da murmushi, tun a page d’in farko Hidaya ta fara tuntsira dariya sosai tamkar cikinta zai k’ulle,tayi dariya mai yawa wadda bata tab’a yin irin ta ba har da hawaye,har k’warewa take don azabar dariya,musamman da ta zo gun da Habiba take aljanun k’arya har fad’owa tayi daga gado don dariya,ta ajiye wayar ta dinga shek’a dariya kamar sabon kamun Hauka,sai da tayi mai isarta sannan ta d’auki wayar ta cigaba da karatu.

Tayi nisa sosai tana ta babbaka dariya,har ta zo in da Amina take lugudar bakin Harira,ai Hidaya ba tayi aune ba taji fitsari na Neman kufce mata a wando don dariya,da hanzari ta cillar da wayar ta mik’e da gudu Yayi bathroom, ta tsuguna tayi fitsari tayi tsarki da ruwan d’umi sannan ta fito tana maida numfashin wahalar dariya,tunda ta zo duniya bata tab’a dariya irin ta yau ba,littafin sosai ya wanke mata zuciya,kamata yayi masu lalurar damuwa da hawan jini su nema su karanta,zama tayi ta jawo wayar ta cigaba da karatu,dariya ta kuma sark’eta kamar me,amma Hidaya ta kasa hak’uri sai da ta kammala littafin BAHAGON LAYI tas kafin sallar azahar,da k’yar ta iya mik’ewa don d’auro alwala saboda yadda cikinta ya k’ulle don azabar dariya.

Bayan ta idar da sallah tayi addu’o’i sosai,musamman akan abin da ya shafi rayuwarta,sai ta jawo wayarta tana Neman layin mijinta ganin tunda ya fita bai kirata ba,kuma ta saba idan ya fita sai ya kirata sau goma ma kafin ya dawo,amma yau kamar ya san ta samu littafin da ke tayata hira bai nemeta ba,sau wajen biyar tana gwada kiran amma bai shiga ba,sai taji damuwa a ranta,domin bata son yin nesa da shi kwata kwata,amma tana tunawa da labarin matan BAHAGON LAYI sai ta k’yalk’yale da dariya har da rik’e ciki,tana cikin dariyar Hamza Garkuwa ya d’aga labulen bedroom d’in yana sallama,kawai tsayawa yayi ya bi ta da kallo bakinsa a sake,a tun tasowarsa bai tab’a ganin mahaifiyar sa cikin mad’aukakin farinciki da dariya kamar haka ba,sanin da yayi mata ma tafi bawa kuka da damuwa muhimmanci akan dariya.
Kawai sai ya cillar da school bag d’in sa ya ruga da mugun gudu ya nufe ta yana dariya shi ma,yana zuwa ya fad’a cinyar ta cike da farinciki,ya kalleta yana dariya yace.

“Ammi na waye ya saki dariya haka?”

Ta kuma tuntsirewa da dariya ta shafa kansa tace.

“Su Harira ne My boy”
Ya cigaba da kallonta yana murmushi kumatun sa na lob’awa(dimple)yace.

“Su wanene Harira Ammi na?

Ta rungume shi ta na goge Hawayen da ya fito mata na dariya,sannan tace.

” Ba ka sansu ba My boy,Labarin su na karanta shine suka bani dariya fa”

“Ammi na nima ki bani labarin,ina so nayi dariya kinji” Ya ambata yana rik’e hannun ta.

Ta dube shi sosai tana murmushi,sannan ta girgiza kai tace.

“Kar ka damu zan baka,amma sai kayi karatu mai yawa”

Ya amsa da hanzari.
“Zan yi Ammi na,I swear zan yi karatu da yawa,amma Ammi na kin daina kuka yanzu sai dariya ko?

Tausayin yaron ya kamata,da sauri ta jijjiga kai tayi murmushi tana kallon sa tace.
” insha Allah My boy na daina,yanzu tashi muje ka cire Uniform d’in ka kaci abinci tukun,kar malamin islamiyya ya zo baka kammala ba”

“To Ammi na,ya fad’a yana mik’ewa tsaye,ya nufi k’ofa ya d’auki school bag d’in sa da ya cillar ya fice daga d’akin da D’an gudun sa,ta bishi da kallo kafin ta runtse idanuwan ta ta sauke ajiyar zuciya,tana tuna Abubuwa masu d’unbun yawa da suka sark’afe rayuwarta,rayuwa kenan!duk yadda Allah ya shimfid’a maka ita haka zata kasance maka.

Bayan sallar magriba tayi karatun alk’ur’ani,Hamza ya d’auko litattafan sa suka yi bitar karatu,yaron yana cikin farinciki sosai a ranar ganin yadda mahaifiyarsa take walwala,duk da ya damu dalilin rashin ganin mahaifinsa ya dawo da wuri,tana ganin ya fara hamma ta rufe litattafan tace su je ya kwanta Yayi bacci,har d’akin sa ta raka shi ya sauya kayan bacci ta taimaka masa yayi brush,sannan ya haye D’an k’ara min bed d’in sa,tayi masa addu’a ta shafe masa a jikinsa,ta sakar masa net ta lullub’eshi da bargo,ya rufe idanuwansa,nan da nan bacci yayi awon gaba da shi,Sai da taga numfashin sa ya fara sauka alamar baccin ya d’auke shi sannan ta mik’e ta fito ta ja masa k’ofar.

Parlour ta dawo ta zauna tayi tagumi,shiru har lokacin bata ga sanyin idaniyarta ya dawo ba,har tashi tayi taje ta canja kwalliya me d’aukar hankalin ta bulbula turare da humra,amma shiru,wayoyinsa kuwa har ta gaji da kira basa tafiya,damuwa sosai ta bayyana a fuskarta,ta jawo wayar ta domin ta sake gwada kiran sa kawai sai ta tuna da littafin BAHAGON LAYI,k’ara binkito shi tayi ta fara maimaita karanta shi,kafin wani lokaci sai ga Hidaya na k’yalk’yala dariya har da birgima,har mai gadi ya bud’e wa mijin ta get ba ta ji ba,har sanda mijin nata ya shigo cikin gidan duk bata ji ba,har ya murd’a handle d’in k’ofar bedroom d’in ya shigo duk bata sani ba tana can kan bed kwance tana karatu tana d’irka dariya,cak!ya tsaya a bakin k’ofar ya tsura mata idanu cikin dukan zuciya da tsananin mamaki,me ya sa ka Hidaya wannan dariya haka?me ya dad’ad’a ruhin ta da ta samu farinciki haka?ba zai iya tuna lokacin da yaga Hidayan sa tana dariya haka ba.

Yafi minti biyar tsaye yana ta kallon ta bata saniba,shauk’i na d’iban sa zuwa gareta,k’afafuwan sa har wani rawa suke tamkar ba zasu d’auki gangar jikin sa ba,a matuk’ar kasalan ce ya bud’e murya da k’yar ya ambaci sunan ta.

“Hidaya naaaaaaa”.

 

 

Comment
Share
Vote
pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA BIYAR DA NA SHIDA*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

Jin sautin muryar sa ya sa ta waiwayo ta kalleshi,fuskarta cike da Annashuwa tana k’yalk’yala dariya,yana niyyar takowa domin isa gare ta ta riga shi mik’ewa,da sassarfa ta nufo shi,ya ware hannayensa ya runtse idanu yana son jin ta a cikin ji kin shi,tana zuwa a maimakon ta fad’a ji kin shi kawai sai ta tsuguna gaban sa ta d’ora kanta kan cikin shi,sannan ta rungume k’ugun shi ta d’ora bakin ta dai dai saitin cibiyar shi ta D’an ciza,ya saki Y’ar k’ara kad’an yasa Hannu yana rik’o kanta,sannan ya za me a hankali ya tsuguna gaban ta kamar yadda take a tsugune tana doka masa murmushi me k’ayatarwa.

Hannun ta ya rik’o da Hannu d’aya,d’aya hannun kuma ya dafe cikin shi da shi yana D’an yamutsa fuska yana marairaicewa,cikin wata irin kasala ya fara magana.

“Wannan cizon da kika min idan kika tsige cibiyar za ki rasa ta wasa Hidaya na,ni da na tawo da hanzarin rungumar ki,kawai kuma sai ki tarbeni da cizo?

Ta matse yatsun sa a hannunta har suka ba da k’ara,ya lumshe idanu yana ajiyar zuciya, ta kai yatsan shi guda d’aya bakin ta tana tsotsa,yaji wani zirrr a ji kin shi,da sauri ya fad’a jikinta yana rungume sosai da sakin ajiyar zuciya,sai da ta tabbatar ta gama sanyayar masa da jiki sannan ta tanka.

” ka san dalilin da ya sa na cije ka?”

Ya ka sa magana illa girgiza mata kai da yayi yana lafe a jikinta,ta d’ago shi daga jikinta suna kallon juna sannan tace.

“Hukunci nayi maka fa,tunda ka fita yau ka manta da sha’ani na,baka kirani a waya ba,baka dawo da wuri ba,kawai ka rataye ni ina ta shan sharafina da kokawar tunanin halin da kake ciki”

Ya D’an girgiza kai yana gyara zama a k’asa,sannan ya jawo ta jikin shi ya kwantar kan cinyoyin shi yana shafa kanta,a hankali cikin k’aramar murya ya fara magana.

“Idan akwai ranar da za ta riske ni a fad’in duniyata wadda za ta kasance cikin mantawa da sha’anin ki,zan rok’i Allah ya d’auki raina kafin zuwan ranar,na sha mantawa da kai na fa!amma ba zan iya mantawa da ke ba Hidaya na,”

Yana direwa ta tare shi da tambaya.

“To menene ya tsayar da kai haka?”

Ya numfasa yana yawo da hannuwan sa a jikin ta.

“Yana daga cikin sha’anin ki,batun kwangilar ginin masallaci da makarantar islamiyyar nan ne,shine na tsaya muna tattaunawa da masu Aikin,domin a hanzarta kammalawa da wuri kamar yadda kike so,wayoyi na na kashe su ne saboda kar a dameni da kira,zuciyata ta k’agauta wajen son cika umarnin ki”

Ta jijjiga kai tana jin sonsa na k’aruwa a ruhinta,ya d’ago ta suna kallon juna,tana shirin magana ya riga ta.

“Na jima banga farinciki da walwala a tare da ke kamar yau ba?don Allah Hidaya na me ya faru da ke?sanar da ni da hanzari,ni ma ina son tayaki farincikin”

Maganar sa ya sa ta tuna da littafin,dariya ta k’ara kamata,ta kwashe da dariya ta fad’a jikinsa,yayi baya ya fad’i kwance,ta haye ruwan cikin shi tana dariya sosai kamar zautacciya,kawai shi ma sai ya biye mata ya kama dariyar,ganin dariyar Hidayan wani k’atoton abin alfahari ne a gareshi,sun jima suna dariya kafin da k’yar su tsagaita,da k’yar ta iya magana.

“Me yasa kake dariya?” Ta tambayeshi.

“Dariyar ki ce ta sakani dariya,Da za ki tausayawa d’okina da kin gajarce min shi ta hanyar sanar da ni dalilin yawan dariyar ki a yau,Hidaya na me ya saki dariya haka yau?” Ya tambaye ta.

Kai tsaye ta bashi Amsa.

“Hassana D’an larabawa ce”

A kwance suke amma sai da ya mik’e da hanzari yana tallafar ta jikin shi,ya tsura mata idanu cikin mamaki ya furta cewa.

“Wannan Marubuciyar me saki kuka wai?”

Ta jijjiga kai tana Murmushi,ta zarce da ba shi amsa.

“Ita ce,yau na yi dariyar da ban tab’a yin irin ta ba, wani littafin ta na karanta wai shi BAHAGON LAYI,ban tab’a cin karo da littafi mai sanya nishad’i kamar sa ba,ta cikin Hikima da sanya nishad’i a zukatan mutane ta fad’akar a kan Mata masu wata irin halayya da ke faruwa a wannan Zamanin,Cizon da nayi maka ma a cikin littafin na koyo yanda ake cizon mutum a Cibiya,shine na gwada” ta k’arasa da dariya.

Shi ma yayi dariya yana ta kallonta,dad’i na kwarara a ransa,cikin nishad’i yayi magana.

“Allah ya sa ka mata da alkairi ya biya mata buk’atun ta na alkairi,Hak’ik’a ta gama yi min komai tunda ta sakaki a farinciki,a baya Haushin ta nake ji saboda kukan da take sa ki,amma yanzu ta wanke laifin ta,kamata ma yayi na bata babban tukuici,dan haka wane tukuici kike ganin ya kamata nayi mata? Ya ambata cike da murna da zumud’i.

Tayi murmushi sosai ta zarce da tambayar sa tace.

” Amma ni ma za ka bani tukuicin farincikin ko?”

Ya rik’o kafad’unta cikin shauk’in Soyayya yana lumlumshe idanu ya fara magana.

“Eh zan baki!ai ke kyautar kaina ma zan miki gabad’aya,domin bani da abin da zan iya biyan ki da shi na wannan farincikin”

“Aikuwa kana da shi….!Ta katse shi.

Ya sumbaci goshinta ya cilla idanuwansa cikin nata yana k’ara lumshe wa.

“Da gaske?to menene?fad’i ko menene na yarje miki Hidaya na”

Ta sanyaya murya tana kwanciya a k’irjin shi tace.

“Abin da za ka biya ni da shi shine,ka amince min na bawa Anty Hassana D’an larabawa LABARI NA,domin ta rubuta shi,ina so al’umma da da ma su karanta domin su D’auki wani babban darasi a ciki,kamar yadda dukkan litattafan ta suke d’auke da darussa masu d’umbun yawa,ni ma ina so Labarin mu ya shiga sahun Labaran da za a k’aru da su a fad’in Duniya,Don Allah ka yarje min kayi min wannan Alfarmar,hakan zai k’ara sawa na tabbatar kai d’in GARKUWAR HIDAYA NE”.

Ba k’aramar razana yayi da jin maganar ta ba,tamkar an buga masa guduma a kansa yaji.
A rikice ya d’ago ta cikin wata iriyar razana,idanuwan sa a warwaje yake kallon ta maganar ta nayi masa kuwwa a kunnuwan sa,kallon ta yake yi tamkar wani tab’ab’b’e bakin sa a sake ,yana maida wani irin numfashi da k’yar,bai tab’a tunanin abin da Hidaya zata furta ba kenan,da baiyi gangancin ba ta tabbaci akan zai yi mata ba,me yasa Hidaya tayi wannan tunanin?me yasa take son fallasa sirrin su har duniya ta sani?ya a kayi wannan tunanin ya shiga k’wak’walwar kanta?gaskiya ba zai iya ba,ba zai iya cikawa Hidaya burin ta ba…….!

Kasa magana yayi illa kallon da yake ta bin ta da shi,har ta gaji da jiran cewar sa ta matso ta sake nutsa kanta a cikin k’irjin shi,tayi magana a hankalin.

“Baka ce komai ba kayi shiru?ka amince min?

Girgiza kai yayi duk da ba kallon fuskarsa take ba,jin alamun motsin da jikinsa ke yi yasa ta d’ago ta k’ura masa idanu tana jiran Amsar sa.

Da k’yar ya iya fizgo magana bayan ya sunkuyar da kansa k’asa.

” Kiyi Hak’uri Hidaya na,ba zan iya amincewa da buk’atar ki ba”

Ta zaro idanu tana dafe k’irjinta,a rud’e tace.

“Why…”
“Ba na son abin da zai fallasa sirrin rayuwar mu ne,kiyi Hak’uri da wannan buk’atar ki fad’i wata zan miki kinji”

Hankalin ta ya tashi ganin tana son rasa damarta,ta marairai ce tana rok’on sa.

“Ba fallasuwar Sirri ba ne,babu Wanda zai san labarin mu a ka rubuta fa,za a sauya abubuwa da yawa ta yadda wad’anda suka San mu ma ko sun karanta ba za su gane labarin mu ba ne,Don Allah ka amince min,wannan ce kad’ai buk’ata ta a gareka ka daure ka cika min burina”

Ya d’ago ya kalleta idanuwan sa har sun fara sauya kala,ba k’aramar razana yayi ba da yaga idanuwanta har sun ciko da hawaye,ya rik’o ta cikin sauri cike da damuwa yace.

“Ki bar wannan tunanin please,muyi maganar da za ta yiwu, don gaskiya wannan ba zata yiwu ba”

Ta fashe da kuka ta fizge jikinta ta mik’e da hanzari,a gigice ya mik’e yana k’ok’arin kamata,amma ta goce ta nufi k’ofa ta fice daga d’akin da gudu,ya rud’e ya gigice saboda baya son damuwar ta ko kad’an,da hanzari ya taka ya fice ya bita yana k’wala kiran sunan ta.

“Hidaya!Hidaya!please Hidaya na tsaya ki saurare ni….!

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA BAKWAI DA NA TAKWAS*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

Wani d’aki da ke falon ta shige da gudu tana kuka,tana shiga ta kulle k’ofar ma Dan kar ya biyo ta,gadon d’akin ta fad’a tana cigaba da kuka sosai,babu abin da take buk’ata a wannan lokacin kamar ya yarje mata a rubuta labarin su,amma me yasa ya k’i? Me yasa ya ke jayayya da hakan?.

Har bakin k’ofar ya zo hankalinsa a tashe ya fara buga k’ofar yana kiran sunan ta da rok’on ta akan ta bud’e k’ofar,amma tayi mirsisi ta cigaba da kukan ta,kukan da yake tafasa zuciyar sa da k’irjin sa,babu irin rarrashin da bai yi mata akan ta bud’e k’ofar ba ,tana jin sa tayi masa shiru sai shesshek’ar kukan ta da yake jiyo wa,a hankali ya d’ora kansa jikin k’ofar yana sauke ajiyar zuciya a jejjere,idanuwan sa suka ciko da hawaye,muryar sa da rauni sosai ya fara magana.

“Please Hidaya na ki bud’e min k’ofa,bana son wani Abu ya faru da ke,kin sani ciwon ki baya son damuwa da tashin hankali,Don girman Allah kiyi hak’uri ki bud’e min muyi magana ta fahimta kinji”

Ta na jin sa amma ta share shi,ita fa idan ba furtawa yayi cewar ya amince ba ba zata bud’e k’ofar ba,haka yayi ta magiya amma funfurus tak’i kula shi,duk da zuciyar ta na ciwo akan k’in sauraren sa,tana yi mata gargad’i da tunasar wa da cewa”Hidaya ki Amsawa GARKUWAR KI,kin sani babu wani Abu mai muhimmanci a rayuwar sa da ya kai ki a wannan lokaci,ya kamata ki tausaya masa kar ki sa ka shi a damuwa”

D’ora hannun ta tayi dai dai saitin zuciyarta ta na hawaye,sannan ta fara magana da zuciyar kamar mai magana da Wanda ke kusa da ita.

“My heart kar ki zargeni da saka GARKUWATA cikin damuwa,kawai ina tauna tsakuwa ne domin Aya taji tsoro,idan ba hakan nayi ba ba zai fuskance ni har ya yarje min Abin da nake so ba”.

Ya fi minti talatin yana aikin buga k’ofar cikin damuwa,ganin tak’i bud’ewa kawai sai ya zame ya zauna a bakin k’ofar,ya jingina da k’ofar ya runtse idanuwan sa yana tuna Abubuwa kala kala,a irin Abubuwa da k’addarorin da suka sark’afe rayuwar Hidaya ya kamata ya amince da maganar ta ko domin ta samu farinciki,duk da shi ta sa zuciyar bata son hakan,amma tilas yayi hak’uri da na sa muradin domin cika muradin Hidaya,idan fa har yana so ya cigaba da dawwama da amsa sunan GARKUWAR HIDAYA.

Yadda Zuciyar sa take cikin tunani haka ta Hidaya ta kasance,haka nan ta ta zuciyar ta fi tasa shiga rud’u sosai,Abubuwa da yawa sun faru da rayuwar ta Wanda za ta so mutanen duniya su yi Alk’alanci a kan rayuwar ta da duniyar ta,Mutane guda biyu ne suka amsa sunan GARKUWAR HIDAYA,sune suka taka muhimmiyar rawa na zamantowa GARKUWARTA a rayuwa,sun mata komai ,sun kare ta,sun tsare ta,sun tarairayeta,sun rungume ta,a lokacin da take cikin tsaka mai wuya tun daga Yarinta har zuwa girman ta ko domin saboda Soyayya da raunin ta,had’i da wata gingimemiyar lalura me girma da ta zamo k’addarar ta,a fahimtar Hidaya idan a kace GARKUWA to ana nufin mutumin da ya jib’anci al’amuran ka,kuma ya taimake ka a rayuwa,yayi k’ok’arin tsareka da duk wani sharri da zai sameka,ya hanaka kuka,ya rasa Abubuwa da dama a rayuwar sa domin ya farantawa taka rayuwar,yayi k’ok’arin tsare maka mutuncin ka,ya hak’ura da bin son zuciyar sa domin ya farantawa taka zuciyar,ya gwammace ya rasa Abubuwa masu muhimmanci na rayuwar sa domin ya kyautata taka rayuwar,idan abin farinciki ya sameka ya kan fika murna,idan damuwa ko bak’inciki ya sameka ya kan fika shiga tashin hankali,wannan shi ake kira da GARKUWAR MUTUM,haka nan yawan ci akan samu mutum d’aya ya zamo GARKUWAR mutum,ko ya zama GARKUWAR Mutane da yawa,amma ita Hidayan GARKUWAR ta sun kasance guda BIYU,wad’anda suka taka muhimmiyar rawa a rayuwar ta da duniyar ta,har ta kasa bambance shin wanene ya canacanta a kira shi da GARKUWA ta farko?dalilin da yasa take son Mutane su karanta tarihin rayuwar ta kenan!ko domin su bambance a cikin mutane guda biyun wanene ya dace a kira shi da GARKUWAR HIDAYA?

Wucewar Awa d’aya cif Hidaya na cikin tunane tunane,a lokacin ne kuma ta daina jin motsin mijin nata a bakin k’ofar d’akin ta,ciwon kai sosai take ji kamar kan ta zai tsage,barci ya k’i ziyartar idanuwan ta,a hankali ta mirgina ta mik’e zaune ta rik’e kan nata da hannuwa biyu,Jim kad’an sannan ta mik’e tsaye tana jin juwa kamar za ta fad’i, a hankali ta isa bakin k’ofar ta tsaya,ta D’an sa ka kunnuwanta jikin k’ofar tana son jiyo motsin sa,shiru ko saukar numfashin sa bata ji ba,d’ora hannun ta tayi akan mabud’in k’ofar ta murza key ta bud’e a hankali,yanayin jikinta da taji yana son sauyawa shiyasa take son shan magani,kuma maganin yana parlour, A hankali ta fito daga bedroom d’in tana takawa cikin sand’a har ta isa tsakiyar Parlour’n in da magungunan suke akan center table,kwata kwata bata lura da shi ba yana kwance akan doguwar kujera rigingine,ya rufe fuskarsa da hannayensa sa,d’aukan maganin tayi ta juya a hankali za ta koma d’akin,shi kam daman idanun sa biyu,kuma tun fitowar ta yake kallonta da k’asan idanu,kuma ya san bata ankara da shi ba da ba zata fito ba,sai da tazo dab da shi zata gota shi sannan ya d’ago hannun sa guda d’aya ya rik’o nata hannun,a rikice kuma a tsarace ta zabura saboda abin ya zo mata bagatatan!ta waiwaya da sauri ta na duban sa amma idanuwan sa a runtse suke,ta cigaba da kallon k’ayatacciyar fuskarsa ta ragowar hasken fitilar da ta haskake parlour’n ,a hankali ya soma Jan hannun ta har ya dangana ta da jikin shi yana daga kwance,kan k’irjin shi ya d’ora ta ya kwantar da ita,a tare suka sauke ajiyar zuciyar da ta zo musu,ya sa Hannu yana shafa bayanta har lokacin idanuwan sa a rufe,a hankali cikin raunin murya ya soma magana.

“Me za ki yi da magani cikin Daren nan”?

Tayi shiru babu amsa tana sakin Numfashi,bai damu da shirun ta ba ya sake jefa mata wata tambayar.

” Ba kya jin dad’i ne ?wani gurin na yi miki ciwo ko?”

Sai lokacin ta D’an gyad’a kai a hankali,yayi ajiyar zuciya ya mik’e zaune tare da ita a jikinsa,tana kan cinyoyin sa ya rungume ta a k’irjin shi yana shafa kumatun ta.

“Kina son saka mu a damuwa ko?ban da haka ai kin san ciwon ki baya buk’atar yawan damuwa Hidaya,ita fa Lafiya GARKUWAR jiki ce,ana buk’atar mutum ya dinga yawan kulawa da ita a ko yaushe,kin san wahalar da kike sha idan ciwon ya tashi ,ba ke kad’ai ba,har da ni da na kasance GARKUWAR ki”

Danshin da yaji a k’irjin shi ya sa shi d’ago kanta da hanzari yana duban fuskar ta,hawaye sosai idanuwan ta ke fitar wa,Hannu ya sa ya share mata hawayen yayi miskilin murmushi yace.

“Me kike so?Har yanzun zuciyar ki na nan akan bakan ta na son a rubuta Labarin mu?”

Da sauri ta gyad’a kai alamar haka ne.

Ya rik’o kafad’un ta yana yi mata wani kallo da ta kasa fassarashi,cikin shauk’in k’auna ya kai harshen sa kan fuskarta ya fara lasar hawayen ta yana shanyewa,sai da ya lashe tsaf yana ta faman sakin ajiyar zuciya sannan ya jefata k’irjin shi ya rungume ta tsam,da wata irin murya ya fara ambatar.

“Na amince Hidaya,wallahi na amince Hidaya na,idan har hakan zai faranta Zuciyar ki”.

Wani farinciki ya ziyarci zuciyar ta da ta jima ba taji irin shi ba,Ruk’unk’ume shi tayi cikin murna tana rungumar sa,ya tarbeta shi ma suka karad’e junan su da runguma da sumbata kamar su cinye juna,ganin farincikin ta shine abin da yafi so a rayuwa, idan Hidaya na farinciki ya kan ji tamkar an masa kyautar Aljanna ne.

Wucewar mintuna Hidaya na zuba masa kalaman godiya da Soyayya,shiru yayi yana sauraron ta idanuwansa lumshe,zak’in kalaman na ratsa k’wak’walwar shi,sai da ta kammala sannan ya fara mayar mata da raddi,raddin da bai yi kala ko kama da nata ba,raddin da ya shallake tunanin ita kanta Hidayan,raddin da duk k’uncin da zuciya take ciki muddin aka nufeta da shi sai ta raunana ta girgiza,kafin wani lokaci sai ga ma’auratan suna shirin sumewa a fagen SOYAYYAH……!

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA TARA DA NA GOMA*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

 

*** Ranar sun kwana cikin farinciki tare da faranta ran juna,Hidaya ta dage sosai wajen nuna masa kulawa da godiyar ta gareshi,shi kansa yayi mamakin Hidaya a ranar,domin wasu abubuwan da tayi masa bata tab’a kwatanta yi masa ba,Daren ya sa ka shi cikin darare masu muhimmanci a rayuwar sa.

Sai bayan da Hidaya tayi bacci ne sannan zuciyar sa ta shiga tunani akan wasu abubuwa iri iri da suka wanzu,kawai ya tsinci kansa ne da zubda hawaye mai k’una da zafi,yayi kuka sosai Wanda ya jima bai yi irinsa ba,kuka na kewa da ciwon zuciya,duk da abubuwa sun daidai ta a gareshi amma ba zai tab’a mantawa da baya ba,har sai lokacin da ya koma ga mahaliccin shi.

Kukan sa yayi yawa har ya fara bayyana,ganin Hidaya na motsi ya sa shi had’iyewa ya rufe baki,ya k’ura mata ido yana kallon yadda take bacci cikin kwanciyar hankali,ta k’ara kyawu a idanuwansa,ya kai Hannu ya shafi fuskarta yana tuna yadda ta rikice masa yanzu ta rud’a shi ta rud’a kanta,ya lumshe idanu yana jin tsigar jikin shi na tashi musamman da ya tuna wani Abu da tayi masa Wanda kad’an ya rage ya sumar da shi saboda shauk’i,Hidayan sa Muradin sa,yana rok’on Allah ya tsawaitawa Hidaya kwanakin ta na duniya har ya riga ta mutuwa,duk da Hidayan ta kasance mai lalura!amma kuma kad’an daga ikon Allah ne ya d’auki ran mai lafiya ya bar Mara lafiya.

Sai da k’arfe biyu da mintuna na dare yayi sannan ya iya zare jikin shi daga na Hidaya,ya sa ka mata pillow sannan ya iya mik’ewa ya shige bathroom domin ya tsaftace jikin shi,har lokacin Hawaye yana ratso fatar idanuwan sa,a haka yayi wankan sa na tsarki sannan ya d’aura Alwala ya fito,jallabiya me dogon Hannu ya sa ka da gajeren wando ,ya feshe jikin shi da turare mai sanyin k’amshi,darduma ya shimfid’a ya hau domin sallar nafila,sai ya waiwaya ya kalli Hidayan,har lokacin bacci take cikin kwanciyar hankali tana rungume da pillow a k’irjin ta,yayi murmushi ya sa Hannu ya goge k’wallar idanuwan sa sannan ya kabbara sallah.

Ya dad’e yana sallah hawaye bai bar zuba a idanuwan sa ba,har ya kammala ya d’auki alk’ur’ani ya fara karantawa yana kuka,sosai zuciyar sa tayi rauni,ya karanta izifi biyu sannan ya rufe alk’ur’anin ya soma jero addu’o’i na larabci da Hausa,yana zuwa kan wata addu’a kawai sai ya kife kansa kan gwiwoyin sa yana malalar da hawaye,da k’yar ya iya k’arasa addu’ar ya shafa.

Bai koma bacci ba!kawai sai ya d’auki carbi yana yi wa Annabi (S A W)salati da kirari,idanuwan sa na kan Hidaya,yana zaune ya tuna da HAMZA GARKUWA,kwata kwata bai saka shi a idanuwan sa ba tun da ya dawo gidan,har gashi dare ya tsala,rigimar Hidaya ta mantar da shi komai!mik’ewa yayi a hankali ya fito daga bedroom d’in su zuwa na Hamzan,ba zai iya jurewa zama bai ganshi ba,ya san shi kansa yaron da tunanin sa yayi bacci,tunda tun safe rabon da su ga juna balle suyi magana,yana isa bakin k’ofar yasa Hannu ya bud’e d’akin ya shiga a hankali,ya kai Hannu kan makunnin fitila ya kunna,haske ya gauraye d’akin sosai.

Hamza na kwance kan D’an k’ara min bed d’in sa yana ta bacci lullub’e da bargo,numfashin sa na sauka a hankali,cikin wani irin taku ya k’arasa gaban yaron ya zauna bakin bed d’in,k’ura masa idanu yayi kafin ya sa Hannu ya shafa kan shi zuwa kyakkyawar fuskar shi da D’an k’ara min bakin shi,ya sunkuya ya sumbaci goshin shi,sannan ya dinga karanto addu’o’i na kariya daga shaid’anu yana tofa mi shi yana shafa mi shi a jikin shi.

Ya jima a d’akin kafin ya fito ya koma bedroom d’in su,a lokacin wasu masallatan sun fara kiran sallar Farko,ya tarar Hidaya ta farka tana laluben sa tana kiran sa cikin k’aramar murya,da Hanzari ya k’arasa kusa da ita yana kamata ya rik’e ta a jikin shi ya rungume ta yana fad’in.

“Kin ganni nan fa,kin farka?me kike so?

Ta kwantar da kanta a k’irjin shi,cikin k’aramar murya tace.

” Zan sha Ruwa”.

Da Hanzari ya jinginata da gadon ya mik’e ya fice daga bedroom d’in,Jim kad’an ya dawo da ruwan faro a hannun sa da cup me D’an girma,da kansa ya tsiyayi ruwan ya ba ta ta shanye,ya kuma tsiyaya ya sake bata shi ma ta shanye,ya dad’a mata ta sha rabi ta rage rabi ta na sauke ajiyar zuciya.

Ya dire cup d’in kan bedside, ya waiwayo yana jawo ta jikin shi,kafin yayi magana ta riga shi magana.

“Ina kaje…!?

Ya kai Hannu yana wasa da kunnen ta yace.

” Na je na yiwa GARKUWA addu’a ne,kuma na gan shi,ban samu ganin sa ba da na dawo saboda rigimar ki”

Tayi murmushi ta na gyara kwanciyar a jikin shi ta na lumshe idanu za ta koma bacci,da sauri ya d’ago ta yana kallon cikin idanuwan ta yana hura mata iskar bakin shi.

“Wake up My Hidaya,kinji masallaci can ana kiran Sallah,yanzu za a yi assalatu,tashi nayi miki wanka saboda kar mu rasa Sallah.

Ta na langab’e a jikin shi ya d’auketa har bathroom, da kansa yayi mata wanka saboda jikinta babu k’wari,sai da ya kammala mata sannan ya d’aura mata towel,ta yi brush tare da d’aura alwala,shi ma ya sake alwala sannan suka fito.

Doguwar riga mai hijab ya d’auko mata ya saka mata,sannan yace tayi raka’atanil fijr saboda assalatu tayi,yana ganin ta tayar da sallah yayi sauri ya fice ya nufi d’akin Hamza ya tashe shi,yaron bacci cike a idanuwan sa amma haka ya tashi,ya raka shi bakin toilet ya karanta masa addu’ar shiga band’aki,shi ma ya fad’a,sannan suka shiga,ya sa masa MacLean a brush ya wanke bakin shi,sannan ya fito ya bar shi yayi fitsari da alwala,yana tsaye har ya fito,ya taimaka masa ya cire masa sleeping dress d’in sa ya ba shi Pakistan na riga da wando ya saka,sannan ya kama hannun sa suka fice zuwa masallaci domin sallatar sallar Asuba.

Sun D’an jima har sai da gari ya fara Haske sannan suka dawo gidan,a ktcheen suka tarar da Hidaya ta na k’ok’arin d’ora break fast,ga abincin school da take girkawa Hamza,da sauri Hamza ya nufe ta yana rungume k’ugunta yana murmushi,ita ma tayi masa murmushi ta na Jan karan hancin sa,ya zame ya durk’usa ya gaishe ta.

“Ina kwana Ammi na?”

“Lafiya k’alau!dafatan ka tashi lafiya?” Ta amsa tana kallon sa.

Ya waiwaya ya dubi mahaifinsa da ya jingina da drower d’in ktcheen yana ta kallonsu fuskarsa k’unshe da fara’a,sannan ya juya ya kalli Hidaya yace.

“Eh!na tashi lafiya Ammi na….yau fa har mafarkin granny nayi,yaushe za ta dawo ne…?

” Ta kusa insha Allah”

Mahaifin sa ya ba shi Amsa,sannan ya matso ya durk’usa gabansa ya rik’o hannuwan sa yace.

“Mu je na taya ka shiryawa kar ka makara a school,ka ga Ammin ka dai girki take yi “.

” To daddy”Hamza ya amsa yana murmushi.

Jan hannun sa yayi suka nufi bakin k’ofa,a hankali ya waiwayo ya dubi Hidaya da ke tsaye tana bin su da kallo,wani irin kallo yayi mata tare da kanne mata ido d’aya,ya D’an turo bakin sa alamar sumbatar ta,murmushi tayi tana lumshe idanu,har suka fice daga ktcheen d’in ta juya ta cigaba da aikin ta,zuciyar ta cike da farin ciki.

Bayan ta kammala da kanta ta taya mijin nata Shiryawa a hanzar ce,saboda yadda masu aikin kwangila suka dame shi da waya,tare da Hamza ya fita ya sauke shi School sannan ya wuce.

Ita kam Hidaya sai da ta kammala komai na Aikin gidan sannan ta hakimce a kan kujerar parlour’n ta,ta d’auki phone d’in ta ta bud’e data ta shiga b’angaren WhatsApp, sak’onni suka dinga shigowa a jejjere,cikin ikon Allah taci karo da abin da take so,wato Amsa sallama daga Hassana D’an Larabawa,da hanzari ta bud’e sak’on,sai taga a lokacin ma tana online,fuskar ta ta cika da fara’a,zumud’i ya ishe ta,hannun ta na rawa ta fara k’ok’arin rubuta sak’o domin tura wa Marubuciya HASSANA D’AN LARABAWA…..!

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA GOMA SHA D’AYA DA NA GOMA SHA BIYU*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

“Ina fatan ina magana da marubuciya Anty Hassana D’an Larabawa?”

Abin da Hidaya ta rubuta ta tura kenan.

Sak’on yana tafiya cikin minti d’aya taga alamun Hassana D’an Larabawa na typing alamun dawo da amsa,ta fara murmushi tana jiran ganin amsa.

“Eh ita ce sister,da wa nake magana?”

Hassana D’an Larabawa ta rubutowa Hidaya ,har da emoji mai nuna alamun murmushi.

Hidaya taji dad’i ta mayar mata da amsa.

“Sunana Fatima,amma ana yi min lak’abi da Hidaya,ni masoyiyar ki ce kuma masoyiyar rubutun ki,saboda na k’aru da Abubuwa da dama a cikin su,nayi kuka sosai,haka nan nayi dariya musamman a BAHAGON LAYI,domin jiya har cizon da Habiba tayi wa Malam Arabi a cibiyar sa sai da na gwada akan Mijina ni ma”

Hassana tana karanta sak’on Hidaya ta turo emoji na zare idanu da mamaki,sannan ta turo sak’o.

“Mijin ki kuma?haba Y’ar uwa Fatima! Ai ban rubuta Dan ki kwaikwaya kiyi wa mijinki ba,sai dai kuma idan cizon Soyayya ne”

Hidaya tayi dariya ta gyara zaman ta har da kashigid’a,sannan ta tura Amsa kamar haka.

“Wallahi Anty Laifi yayi min ne,shiyasa na rama da cizo”

Hassana ta tura alamun dariya da sak’o.

“Ayya Fatima!mazajen mu ai sai muna hak’uri da su daman,Allah dai ya kyautata zamantakewar mu da su?

” Ameen Anty Hassana”

Hidaya ta amsa da hakan.Sannan ta sake tura sak’o.

“Naji dad’i sosai da kika saurare ni har nayi magana mai tsawo da ke,hakan ya nuna min abin da ake fad’a akan marubuta ba gaskiya bane,ana yawan cewa kuna da wulak’anci idan akayi muku magana bakwa amsawa mutum,ni kuma yanzu sai naga Ashe ba haka abin yake ba,ba a taru an zama d’aya ba”

Sak’on ya D’an yi minti uku ba tare da Hassana ta duba ba,sai can ta duba ta fara rubuto amsa.

“Sorry Fatima na D’an amsawa wasu magana ne kin jini shiru,Ai gaskiya ya kamata Mutane su dinga yiwa marubuta uzuri,saboda wani zubin suna da ayyuka a gabansu,ga rubutu,hakan yasa idan akayi musu magana ta kan d’auki lokaci babu amsa,amma tabbas akwai masu shariyar,kuma suma muna k’ok’arin nusar da su cewar su dinga kyautata mu’amalar su da mutane,saboda duk mai sonka ya gama yi maka komai a rayuwa,ni ina girmama masoyina,domin bani da abin da zan biya shi da shi na nuna soyayyar sa gareni”

Hidaya na ganin amsar ta jijjiga kai tayi murmushi, sosai ta sake jin k’aunar Hassana D’an Larabawa a ranta,hakan yasa ta kuma tura sak’o.

“Gaskiya hakane Anty Hassana,wannan maganar ta ki ta sa na kuma jin k’aunar ki a raina da fatan zumunci ya k’ullu tsakanina da ke,amma akwai tambayar da nake so nayi miki idan babu damuwa”

Hassana ta dawo da Amsa.

“Babu damuwa,Allah ya sa na sani,kuma Allah ya bani ikon Amsawa”.

Hidaya ta rubuta ta tura.

” Da gaske littafin SANADIN HOTO true life story ne?”

Hassana D’an Larabawa ta tura emoji na dariya da sak’o.

“Tabbas haka ne,Labarin littafin ya faru da gaske,kamar yadda labarin CIN AMANAR RUHI ya faru da gaske”

Hidaya ta D’an zaro idanu ta gyara zama ta tura emoji na mamaki da sak’o.

“Amma gaskiya nayi mamaki Anty Hassana!saboda banga kin rubuta cewa true life story ba ne,kar kiga na dame ki da tambaya pls menene dalilin hakan?”

Hassana ta tura wa Hidaya Amsa.

“Akwai dalili da yawa gaskiya,kad’an daga ciki shine,na san labarin SANADIN HOTO ya tab’awa mutane zuciya da yawa,duk da ban fad’i cewar gaske bane,to ya kike tunani idan na bayyana shi a matsayin gaskiya ne?kinga zai zaunawa mutane a zuciya suyi ta tunanin abin zuciyar su tana yin ba dad’i,sannan ana samun wasu matsalolin da dama akan Rubuta true life story,kad’an kenan daga abin da yasa ban cika rubuta wa ba”

Hidaya ta amsa .

“Hakane gaskiya!to idan babu damuwa ina son na tattauna wata magana ne da ke Anty Hassana,idan har za ki bani damar hakan”

Sai da sak’on yayi minti biyu sannan Hassana ta dawo da Amsa.

“Ina sauraren ki babu damuwa,ina da isasshen lokaci a yanzu babu abin da nake yi”

Hidaya ta turo da emoji na tsalle da murna,sannan ta fara Rubuta sak’o ta tura.

“Anty Hassana tunda na fara karanta litattafanki nake jin kin shiga zuciyata,domin babu wani littafin ki da za a karanta ba tare da an k’aru ba,kina duba abubuwan da suke faruwa kiyi rubutun akai ba tare da shirme ba,haka nan babu batsa sai yawan addini da kike sakawa,kamar littafin CIN AMANAR RUHI wani wa’azi ne me zaman kansa,haka nan ragowar litattafan ki,a lokacin da nake karantawa babu abin da nake hangowa sai tawa rayuwar da k’addarorin da suka sark’afeta,na tabbatar da mutane za su ji labarina akwai muhimman Abubuwa da za su k’aru da su a cikin Labarin,domin ya tattara komai,idan nace komai to ina nufin komai d’in,da na zauna nayi tunani sai naga ni ba Marubuciya ba ce,kin san kowa da baiwar sa,k’ila ni idan na Rubuta Labarina ba zai kai inda nake so ba,haka nan ba zai yi armashi kamar yadda idan ke ce kika Rubuta zai yi ba,shiyasa na zab’eki a matsayin wadda ya dace ta Rubuta Labarina,kuma ina fata da d’okin jin amsa wadda zata sakani farinciki daga gareki”.

Hassana D’an Larabawa ta jima tana Nazari akan sak’on Hidaya kafin ta bata Amsa da cewa.

“Naji dad’i Sosai da kika zab’o ni a cikin dubun dubatar Marubuta domin na Rubuta Labarin ki,duk da dai ban san me Labarin ya k’unsa ba,sai dai akwai sharad’i akan Hakan….!

” Wane sharad’i ne Anty Hassana?” Hidaya ta tambaya.

“Akwai Yanayin Labarin da Hannuna baya Rubutawa,Musamman Labari na Batsa ko Wanda ba zai amfani al’umma ba,domin duk abin da muka rubuta abin tambaya ne,mu na mantawa da Lahirar mu mu na bin rud’in duniya,bayan gidan Lahira shine tabbas a garemu,kamar yadda Allah (S W A)yace a cikin alk’ur’anin sa mai Girma.

“وماھذہ الحیٰوة الدنیا الا لھو ولعب ،وإن الدار الاّخرة لھی الحیوان،لو کانوایعلمون”

(Rayuwar wannan duniya ,ba komai ba ce ,face wasa da wargi.Lallai gidan Lahira shi e rayuwar,da Mutane suna da ilimi).

Zan saurari Labarin ki idan har Wanda ya kamata a rubuta ne to zan rubuta ko domin Mutane su k’aru da shi,hakan ma kuma a bisa wani sharad’in na cewa har sai na tabbatar da amincewar Mijinki wajen Rubuta Labarin,domin a yanzu shine yake iko da ke,a k’ark’ashin sa kike,idan har wad’annan sharud’an suka cika to babu Haufi da yardar Allah zan Rubuta Labarin ki domin Duniya ta karanta.

Dad’i ya kwarara a Zuciyar Hidaya,ta dinga tura stickers da emojis na murna da jin dad’i da dariya,daga k’arshe ta Rubuta sak’o ta tura.

“Insha Allahu zaki sameni mai cika sharud’an ki Anty Hassana,ban tunkare ki ba har sai da na fara samun amincewar mijina,da izininsa komai zai tabbata,haka nan Labari na bai shafi Batsa ko wani Abu da bai kamata ba,Hasali ma ni bana karanta litattafan Batsa,domin suna cutar da mutum da idanuwan sa,haka nan masu Rubutawa na kan yi mamakin yadda suke tak’ark’arewa suna rubuta abin da ba zai amfanesu ba balle ya amfanar da al’umma,illa ma su dinga jawowa Kansu fushin Allah,haka nan su tarawa Kansu zunubai a maimakon lada”

Hassana D’an Larabawa tayi murmushi ta rubuta Amsa.

“Naji dad’in Maganarki akan Mijinki,sai dai duk da hakan zan k’ara bincike akan hakan kafin komai ya fara wakana insha Allah,Batun rubutun Batsa kuma mu na nan mu na yiwa masu yi addu’a da fatan Allah ya shirye su su daina,idan har suka tuba suka daina Allah zai yafe musu ya karb’i tuban su,domin Allah yana cewa.

“یأیھا الذین ءامنوا توبوا الی اللہ توبة نصو حا عسیٰ ربکم ان یکفر عنکم سیٸاتکم”

(Ya ku wad’anda suka yi imani ku tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya,tabbas Ubangijinku zai gafarta muku laifuffukan ku).

Haka nan a wata ayar ya sake cewa.

“و ھو الذی یقبل التوبة عن عبادہ و یعفوا عن السیٸات و یعلم ما تفعلون”

(Shine Wanda yake karb’ar tuba daga wajen bayinsa,kuma yake yin afuwa game da munanan aiyuka).

Dan haka mu na yi musu addu’a da wasiyya da suji tsoron Allah a duk in da suke,su tuba,Allah zai gafarta musu,Allah ya gafarta mana gabad’ayan mu.

Hidaya ta ji dad’in tattaunawar su har bata san lokaci ya k’ure ba,kiran wayar ta da mijin ta yayi ne yasa ta yiwa Hassana D’an Larabawa Sallama,da Alk’awarin zuwa Anjima za su sake had’uwa online ko ta kira ta.

Hassana ta bata Amsa da cewa.

“To babu laifi Fatima,Madalla,Allah ya kai mu lokacin da rai da lafiya”

Hidaya ta sauka online ta fara k’ok’arin d’aga wayar mijin ta……!

 

 

*****************

Bayan kwana biyu Abubuwa da dama sun faru,in da alak’ar Hidaya da Hassana D’an Larabawa tayi Girma,Marubuciya Hassana ta tabbatar da cewa Labarin Hidaya ya dace a Rubuta shi,musamman da ya kasance tsaftataccen Labari kuma duk wasu sharad’ai Hidayan ta cika su,bisa ga amincewar Mijin ta,a lokacin da Hidayan kuma ta bata Labarin ta shiga rud’ewa da k’ara jinjina Buwayar Ubangiji,Wanda shi ke yin komai da ya so a kuma lokacin da ya so,tabbas Labarin Hidaya wani Babban Jigo ne da idan mai karatu yayi nasarar karantawa zai sha Mamaki da Al’ajabi,Haka nan Labarin Hidaya ya tara komai,akwai nishad’i,Soyayya,bajinta,tausayi,fad’akarwa,wa’azantarwa,kulawa,sadaukarwa,jarrabawa,k’addara,aminci,da dai sauran su.

Kwana Hassana D’an Larabawa tayi tana jinjina Labarin Hidaya, tana jin Labarin a Zuciyar ta fiye da duk wani Labari da ta Rubuta,washe gari da safe kuwa bayan ta kammala komai ta fara k’ok’arin Rubuta Labarin Hidaya kamar Haka…..!

 

 

Comment
Share
Vote
pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA GOMA SHA UKU DA NA GOMA SHA HUD’U*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

*FARKON LABARI*

 

***Tana zaune a tsakar gida kan kujera Y’ar tsuguno,dankali ne na turawa a gabanta da wuk’a a hannun ta tana feraye wa,motsin da taji ya sa ta d’ago kai tana kallon bakin k’ofar parlour’n ta.

Tsaye yake ya d’aga labule yana kallonta,idanuwan sa da alamun bacci ya farka,yayi mik’a yana salati kafin ya sauke kallonsa a kanta,a hankali ya ta ko ya fito tsakar gidan ya nufo in da take,yayin da ta dakata da ferayar ta na kallon sa cikin kulawa da murmushi akan fuskarta.

Yana isowa gabanta ya tsuguna ya mik’a Hannu ya karb’i wuk’ar hannun ta,sannan ya d’auki dankalin ya cigaba da ferayewa,a lokacin ne kuma yayi magana.

“Haba Umma,maimakon ki tashe ni nayi Aikin da kaina,ai bai kamata ni ina bacci ke kuma kina aiki ba,ni ya kamata nayi aiki ke kuma ki huta,gashi ma har yamma tayi sosai ban san lokacin da baccin ya kwashe ni ba bayan na idar da sallar la’asar”

Umma tayi murmushi ta dubeshi da kulawa tace.

“Haba HAMZA!wannan ai Aikina ne ba naka ba,gani nayi yau kamar Azumin yana baka wahala shiyasa ma na k’yaleka ban tashe ka a baccin ba,saboda na san shi kansa baccin mai Azumi ibada ne,yanzu nake shirin da na kammala ferayar dankalin nan na taso ka domin kaje bakin titi ka samo mana kayan marmari da dabino da za mu yi bud’e baki da su”.

Hamza ya jinjina kai yana cigaba da ferayar dankalin.

” To Umma,bari na kammala wannan sai na fita na nemo mana,ni na zaci ma akwai ragowar dabinon ai?

“Babu ya k’are wallahi,jiya da yara suka shigo wasa na rarraba musu ragowar”
Umma ta amsa tana k’ok’arin tattara b’awon dankalin za ta kwashe,ganin har ya kammala ferayewa.

Da sauri ya amshi tsintsiyar ya tattara,ita kuma Umma ta karb’i dankalin ta d’auraye ta nufi kitchen domin d’orawa.

Bayan ya zubar da b’awon a shara,ya nufi Famfon da ke tsakar gidan ya d’auraye hannayensa ,d’akin sa ya nufa ya cire jallabiyar jikinsa,sannan ya saka wani yadi na kufta me kyau da ya sake fito masa da asalin kyawun zatinsa,babu Wanda zai kalleshi yace bai haura shekaru Ashirin da wani abun ba,amma a lokacin yana da shekaru goma sha takwas kacal a duniya ne,tsantsar kamalar sa da haibarsa ke sawa Mutane na yi masa kallon Babban mutum.

Yana fitowa daga d’akin sa Umma na fitowa daga kitchen da flask d’in shayi a hannun ta,ta dubeshi tana jin dad’i a ranta sosai,har ta kasa had’iye wa sai da ta furta.

“Ka yi kyau Hamza,yadin nan yana yi maka kyau Sosai”

Yayi murmushi kansa a k’asa yace.

“Asalin kyan ai naki ne Umma,Hamza ke ya gado a fagen kyawu”

Tayi dariya tace.

“Anya kuwa?ai ni na tsufa,kyawun ya fara gushewa kwamanda”

Ya d’ago idanuwan sa ya kalleta da kyautatawa yace.

“Wai Umma menene kwamanda?wataran sai naji kina ambato na da kwamanda”

Ta sauke numfashi tace.

“Sunan ka ai sunan Kwamandan Yak’in uhudu ne,wato sayyadina Hamza,shugaban masu shahada na musulmai,shiyasa wataran nake maka alkunya da kwamanda”

Ya lumshe idanuwan sa ya bud’e yana jinjina kai,a hankali ya furta.

“Allah ya k’ara yarda da aminci ga sahabban manzon Allah (S A W)”

Umma ta amsa da “Ameen” sannan ta zarce da cewa.

“Bari na d’auko maka kud’in da zaka siyo kayan marmarin”

Da hanzari ya tare ta.

“Ki barshi kawai Umma,ina da kud’i fa”

Ta waiwayo ta k’ura masa idanu,kafin tace.

“Kana da kud’i ?ina ka samu kud’i?

Ya D’an Sosa k’eya yana murmushi,ya langab’e kai yana dubanta yace.

” Tun Wanda KHALEEL ya turo min ne fa,har yanzu basu k’are ba Umma akwai ragowa da yawa”

Umma ta girgiza kai tana murmushi tace.

“Ayya!Allah sarki Ibraheem,Allah dai ya saka masa da alkairi,Ubangiji ya bar amintarku har zuwa Aljanna,yadda yake taimakon ka Allah ya taimaka shi a dukkanin lamuran sa shi ma”

Hamza ya amsa cikin shauk’i.

“Ameen Umma,ai khaleel jinin jikina ne Umma,ni da shi tamkar Jini da hanta ne”

Sannan ya zarce da cewa.

“Bari naje nayi sauri na dawo Umma,yamma na dad’a yi bana son Magriba tayi ban dawo ba”

Yayi hanyar fita daga gidan,Umma nayi masa fatan alkairi da dawowa lafiya.

 

 

****************

 

A cikin wani kango suke zaune su biyu,wata mata me kyakkyawar sura tana kwance a k’asa tayi matashi da wata jaka, ga Yarinya da bata wuce shekaru takwas ba zaune a gabanta rik’e da hannayen ta,da doguwar Riga a jikinta Y’ar kanti mai d’ankaren kyau,kanta ba d’ankwali sai kalba da ta zubo har kafad’unta an mata adon duwatsu a kanta,yarinyar siririya ce k’warai,sai dai tana da kyawu dai dai gwargwado.

Yarinyar tana rik’e da hannun Uwar tana girgizawa da ambatar sunanta.

“Mummy!mummy!mummy ki tashi mu tafi daga nan,nan fa bashi da kyau,ki tashi mu koma gida kinji mummy…!

Uwar ta D’an bud’e idanuwanta da suka yi jajir alamun tana cikin tsaka mai wuya,da k’yar ta iya magana tana kallon yarinyar.

” Hidaya bamu da wata hanya da zamu fita daga nan!nan shine mafakar mu!nan shine rufin asirin mu!ko ni ban tsira ba ke ina son ki tsira Hidaya,rayuwar ki tana da amfani a gaba da yardar Allah!shirun nan da kika ga nayi addu’a nake yi Allah ya kawo Wanda zai taimake mu Hidaya”

Hidaya tayi shiru tana kallon mahaifiyarta,bata da wayo sosai da za ta gane maganganun mahaifiyar ta,ta k’urawa bakin ta idanu tana ganin yadda ya bushe da alamun tana buk’atar ruwa,ta kai Hannu ta shafa leb’en mahaifiyar ta ta,tayi magana cikin Yarin ta.

“Mummy kina jin k’ishirwa ko?za ki sha ruwa?

Tayi murmushi ta yi tari, sannan ta gyad’a kai tayi magana cikin nishi.

” Idan Allah yayi nufin shayar da ni zan sha Hidaya,idan kuma shan ruwa na na duniya ya k’are Allah ya shayar da ni na alkausara tare da Mahaifin ki”

Hidaya tayi kasak’e bata fahimta ba,kawai sai ta saki hannun mahaifiyarta ta ta mik’e tana cewa.

“Bari na samo miki Ruwa ki sha kinji Mummy”

Ta d’aga Hannu tana k’ok’arin dakatar da ita akan kar ta fita daga kangon,amma tari ya sark’afeta,ita kam Hidaya tuni ta zura da gudu ta fice daga kangon domin nemowa mummyn ta Ruwan da za ta sha.

 

 

*************

Sauri yake ta yi sosai ganin magriba ta kusa,hannunsa rik’e da ledoji da ya siyo kayan marmari,bai bi ta hanyar da ya bi da farko ba sai ya canja hanya,a ganinsa wannan hanyar da ya biyo za ta fiye masa sauk’i wajen isa gida tunda sauri yake yi.

Yana yanko layin da ke gaban sa yaji layin tsit babu hayaniyar mutane,haka nan babu yawaitar gilmawar mutane da yawa a layin,kansa a k’asa ya zo zai gifta ta gefen wani kango,kamar an ce ya d’ago kansa,karaf!ya ci karo da k’aramar Yarinya tsaye a bakin kangon sai zare idanu take yi tana kalle kalle,har zai wuce sai kuma ya D’an tsaya yana duban ta yana nazarin ta,kamar yadda yake kallonta haka ita ma ta k’ura masa idanu tana kallon sa,can kuma ta maida kallon ta kan ledar da ke hannunwan sa.
Har ya kuma juyawa zai wuce ganin Ummansa tana can jiransa,sai kuma wata zuciyar take k’issima masa me yarinyar take yi tsaye a gaban kango?kuma daga ganin ta kamar a tsorace take,ko d’ankwali babu a kanta ga magariba ta matso,in da take tsaye bakin kangon kuma duk bola ne.

Waiwayo wa yayi ya ta ko a hankali zuwa gabanta,ya tsaya suna kallon juna,ya D’an durk’usa gabanta ya kalli idanuwan ta yace.

“Ke!Me kike yi tsaye a bola kanki babu d’ankwali?maza ki tafi gida magariba tayi kinji ko”

Tayi shiru kanta a k’asa tana kallon ledar hannunsa.
Ya k’ura mata ido jin bata yi magana ba yace.

“Ba kya magana ne?

Sai ta girgiza kai,sannan ta cigaba da waiwaye tana kallon gefen ta da cikin kangon.

Yayi mamaki,amma ya shanye ya sake tambayar ta.

” me kike nema ne?

“Ruwa” ta ambata cikin k’aramar murya da yarinta.

Yayi shiru yana nazari,sannan yace.

“Ruwa?me za ki yi da Ruwa?

Tayi rau rau da ido tana murtsika idon da hannun ta.

” Mummyna zan kaiwa,tana jin k’ishirwa ne..!

“Ina mummyn ta ki?

Ya tambaye ta,haka kawai yaji ba zai iya tafiya ya bar yarinyar ba ba tare da ya ji dalilin tsayuwar ta a Gun ba duk da saurin da take yi,a yadda Zamani ya lalace abubuwan b’arna suka yi yawa akwai tsoro kaga Yarinya k’arama a bakin kango da magariba.

Hannu ta sa tayi masa nuni da cikin kangon tace.

” tana cikin nan..!

Gabansa ya fad’i!k’irjinsa ya buga!tsoro ya fara kamashi,ko dai yarinyar nan Aljana ce?daman gata kyakkyawa ga gashi mai tsawo!sannan ga idanuwan ta wasu iri!amma duk da hakan sai ya samu zuciyarsa da son shiga kangon domin ya ganewa idanunsa abin da ke ciki!

Hakan ya sa ya mik’e tsaye yana duban yarinyar yace.

“Muje ciki naga Mummyn ta ki,sai na bata Ruwan ta sha kinji”

Da hanzari ta saki murmushin murna har da D’an tsallen ta,tayi gaba da sauri,ya bita a baya zuciyar sa na dokawa,haka nan bakinsa na ambatar .

“حسبنا اللہ و نعمل وکیل”

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA GOMA SHA BIYAR DA NA GOMA SHA SHIDA*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

**Tana tafe tana D’an tsalle yana bin ta a baya kamar rak’umi da akala!da bismillah ya saka k’afarsa cikin kangon da Y’ar ledar sa a Hannu,yana kallonta ta nufi wata mata da ke kwance tana ta d’ago Hannu tana magana cikin shak’ak’k’iyar murya ba a jin me take fad’a,har suka isa gaban ta yarinyar ta rik’o hannun ta ,a lokacin ne yaji muryar matar na ambatar .

“Hidaya,kina ina ne Hidaya?

” Gani Mummy,tashi na kawo miki wani zai baki Ruwa ki sha”

Idanuwan matar a rufe suke,amma jin maganar Hidaya sai ta fara k’ok’arin bud’e idanunta da sauri,ina tsugune a gefe mamaki ya cikani,har ta d’ago ta kalleni sosai muka had’a ido,ni na fara saurin magana da cikin tausayawa nace.

“Sannu”

Ta lumshe idanu ta amsa a hankali.

“Yawwa sannu D’an Samari,A ina Hidaya ta binkito ka?

Ya juya ya D’an kalli yarinyar da yaji a jikinsa ita ce Hidaya,sannan ya waiwaya ya dubi matar yace.

” Na zo wucewa ne naci karo d ita a bakin kangon nan,gashi naga magariba ta k’arato,shine na tsaya na tambayeta me take yi a nan?sai take fad’a min ruwa take so za ta bawa mamanta,dalilin da ya sa na biyo ta kenan domin naga me ke faruwa?saboda hankalina ya k’i kwanciya da ganin Yarinya a bakin kango,saboda yadda Zamani ya lalace”

“Ya sunan ka?
Abin da Maman Hidaya tace kenan idanuwan ta a kansa.

Kai tsaye ya bata amsa kansa a sunkuye.

” Hamza,suna na Hamza”

Ta lumshe idanu ta bud’e a hankali,ta k’ura masa idanu sosai,shi kam har lokacin k’irjin sa na bugawa amma yana k’ok’arin nuna jarumta,ta d’auke kallonta daga gareshi zuwa kan d’iyar ta,ta d’ago hannun ta ta shafa kan yarinyar idanuwanta suka ciko da hawaye,tace.

“Ina ganin ka naji hankalina ya kwanta da kai Hamza,k’ila kuma Allah ya amsa addu’ata ne akan rok’on da nayi masa,tabbas Allah ya turo da kai ne domin ka taimaka mana,domin ka zama kariya ga wannan k’aramar Yarinya me rauni,domin ka zama GARKUWAR ta a yanzu, kulawar da ka bata a lokacin nan ya tabbatar min kai mai hankali ne,kuma za ka iya kulawa da ita a kowane hali duk da dai kaima har yanzu baka kai minzalin girma ba,”

Hamza yayi shiru duk kansa ya kulle ya kasa gane abin da take nufi da maganganun ta,yayi kasak’e yana ta kallonta,sai kuma ya kama waige waige kamar me Neman wani abu.Ta lura da kamar yake a tsorace,shiyasa tayi hanzarin kau da tsoro daga fuskarsa ta hanyar canja magana da cewa.

“Aiken ka aka yi ne?naga kamar hankalinka baya nan kana sauri ko?

Da sauri ya gyad’a kai tare da magana.

” Eh!Umma na ce ta aike ni,gashi tana Azumi ne,ina sauri kar magariba tayi ban kai mata sak’on ba”

Tayi k’ok’arin mik’ewa zaune a hankali cikin dauriya,yayi kamar ya taimaka mata ganin sai nishi take,ta dai dai ta zaman ta yayin da Hidaya ta d’ane cinyar ta tana tab’a mata hanci tana wasa,ta rik’e hannun ta sannan ta dubi Hamza tayi D’an murmushi tace.

“Da kyau D’an Albarka!Don Allah Hamza ko za ka yi min wani taimako?

Duk da a tsorace yake amma hakan bai hanashi gyad’a kai ba,cikin k’arfin hali yace.

” Insha Allahu zan taimaka miki Mama,idan har ina da halin taimakawar”

Taji dad’i sosai har murmushi ya bayyana akan kyakywar fuskarta,tana duban sa ta fara magana.

“Zan ba ka wannan yarinyar ne domin ka tafi da ita a cikin duhun magariba,saboda fitar ta cikin haske akwai had’ari,kaje da ita gidan ku ta kwana,gobe da safe idan gari ya waye ka d’auketa ka kaita gidan Marayu,zan baka takardar da za ka basu idan kaje kai musu ita”

Tun da ta fara magana yake zazzaro idanuwa kamar za su fad’o k’asa,daman tubarkalla gashi da ido manya masu kyawu,bakin sa a sake k’irjinsa na bugawa da k’arfin gaske,ganin yadda ya kuma tsorata ya sa ta cigaba da magana.

“Na san za ka tsorata Hamza,gashi kuma lokaci ya k’ure mana balle na baka Labarin komai,ina so ka cire tsoro daga zuciyarka,ni mutum ce,kuma musulma kamar kai,Fatima(Hidaya)y’ata ce da na Haifa da cikina,marainiyace,me rauni ce,akwai k’addarori da suka sark’afe rayuwar ta,d’aya daga ciki Allah ya jarrabeta da ciwon( SIKILA),Akwai dalili mai k’arfi da zai sa na rabu da Hidaya a wannan lokacin ba da son raina ba,domin idan har ban rabu da ita ba rayuwata da ta ta suna cikin had’ari mai Girma,zan gaya maka sunan Gidan marayun da za ka kaita,daga baya insha Allahu idan komai ya warware zan je da kaina na d’auketa,don Allah kayi min wannan taimakon Hamza”

Kammala maganarta yayi dai dai da kiran sallar magariba da ya fara jiyo wa,ya runtse idanu cikin tashin hankali,ya san Ummansa tana can tana jiransa,ga kuma wata gingimemiyar magana da wannan matar ta zo masa da ita,ta ya ya zai iya d’aukar Yarinya ya tafi da ita,kuma har ta kwana da su?wane bayani zai yi wa Umman sa da za ta amince da shi?haka nan wane bayani zai wa mutane idan suka ganshi da yarinyar?haka kawai ace ma sato ta yayi!duk da yana jin tausayin su a cikin zuciyar sa amma ba zai iya wannan taimakon ba!domin akwai babban k’alubale a cikin sa.

Da Hanzari ya mik’e tsaye yana girgiza kai!ya sunkuci ledar da ke gaban sa ya juya da hanzari zai fice daga kangon,taku biyu yayi ya tsaya cak!ba wani Abu ne ya tsayar da shi ba illa tuno wani wa’azi da malamin islamiyyar su ya tab’a yi musu akan taimako,ya jaddada musu matuk’ar sun ga wani yana Neman taimako to su taimake shi,kuma su dinga taimakekeniya a junansu da tsoran Allah ,Alokacin ma har wata aya ya kawo musu,in da Allah (S W A)Ya ke cewa.

“و تعا ونوا علی البر والتقوی”

(Ku yi taimakekeniya akan aikin nagarta da tsoran Allah).

Tunawa da yayi da hakan ya sa jikinsa yayi sanyi,bai san wane irin k’alubabale za su fuskanta ba idan bai taimaka musu ba,a hankali ya waiwayo yana dubanta,tana zaunen tana ta kallonsa,Hidaya kam ta langab’e kan kafad’ar mahaifiyarta ta har ta fara bacci,ta ko wa yayi zuwa gabansu ya tsuguna ya sunkuyar da kai k’asa,a hankali yayi magana.

“Na amince zan taimaka muku”

Wani irin murmushi ta saki zuciyar ta ta cika da murna,Hawayen farinciki ya ratso idanuwan ta,tayi magana cikin d’oki.

“Allah yayi maka Albarka Hamza,Allah ya haskaka rayuwar ka,Allah ya taimake ka kamar yadda ka taimake mu”

Ta D’an muskuta ta janyo wata jaka da ta tada kai da ita d’azu,ta zuge jakar ahankali ta za ro wata takarda ta mik’a masa,ya kai Hannu ya karb’a yana buk’atar k’arin bayani.Ta fara magana idanuwanta a kansa.

“Wannan takardar idan kaje gidan marayu ita za ka basu,da zarar sun karanta abin da ke cikin ta za su karb’i Hidaya a hannun ka”

Ya gyad’a kai cikin Amincewa,ta kuma za ro wata takardar ta mik’a masa,ya kuma karb’a yana kallon ta,ta D’an sunkuyar da kai tana gyarawa Hidaya kwanciya akan kafad’ar ta,ta na Kore mata sauron da ya fara binsu saboda duhun magariba,sannan ta fara magana.

“Wannan kuma takardar ta Hidaya ce,amma ina rok’on ka ajiye mata a gunka,Idan Allah yayi dawowa ta a kusa to zan zo na d’auketa ba tare da ka bata takardar ba,saboda bana son ka bata har sai ta kai munzalin girma ta mallaki hankalin ta,a lokacin ne nake so ta karanta abin da ke ciki,to amma bani da tabbaci akan zan dawo a kusa ko ba zan dawo ba,shin zan sake ganin Hidaya a rayuwata ko ba zan sake ba?wannan duk Allah ne ya bar wa kansa sani,ni dai rok’ona a gareka ka ajiye wa Hidaya wannan takardar,idan idan Allah yayi girman ta a gidan marayu to inaso ka bata wannan takarda idan har ka samu dama,wannan ne taimakon da za ka yi min HAMZA”

K’arfin zuciya yaji sosai a lokacin,shiyasa ya bai wa Maman Hidaya tabbaci akan ya amince da dukkan abin da ta fad’a,a lokacin Hawaye ya zubo mata,ta shafa kan Hidaya ta dinga yi mata addu’a,yarinyar bata san me ke faruwa ba saboda baccin da take,a hankali ta d’ago Hidaya ta mik’a masa ita,ya sa Hannu ya karb’eta ya sab’a ta a kafad’ar sa shi ma,sannan ya mik’e ya d’auki jakar tare da ledar sa a Hannu,Zuciyar sa na ayyana masa taimako zai yi!har ya juya ya fara tafiya idanuwan sa cike da Hawayen tausayi,sai kuma ya juya ya dubeta ,ita ma kukan take yi,a hankali yayi magana.

“Ke kuma fa?anan za mu barki?dare fa yana yi”

Ta girgiza kai hawaye na malala tace.

“Kuje Hamza,kar ka damu dani,ni dai nafi damuwa da tserewar Hidaya cikin bala’in da ke shirin afka mana,ni ma nan da D’an lokaci k’ank’ani Allah zai taimake ni ,kamar yadda ya taimaki Hidaya,ku tafi Hamza,maza ku tafi”

Jin maganarta ya sa ya juya ya fara tafiya a hankali kamar Wanda k’wai ya fashewa a ciki,Hidaya na sharar bacci kan kafad’ar sa,yana jin sa wani iri kamar ba Hamza ba,a haka har ya kusa ficewa daga cikin kangon cikin wani yana yi da na zai fassaru ba,a lokacin ne ya jiyo muryar mahaifiyar Hidaya cikin kuka tana magana.

“Ka rik’e Hidaya Amana Hamza….Don Allah ka zama GARKUWAR ta a lokacin da ba na tare da ita…..,Hidaya bata da kowa a halin yanzu sai kai Hamza……Don Allah Hamza….Don Allah Hamza….Don Allah Ham……

Bai k’arasa jin maganar ba ya fice daga kangon…maganar na yi masa kuwwa a kunnuwan sa…Hawaye na zubo masa suna sauka kan dokin wuyan Hidaya da ke kwance kan kafad’ar sa.…zuciyar sa tayi rauni k’warai da gaske,sosai yake kuka…ba kuma kukan komai ba sai na rabuwar Hidaya da mahaifiyar ta….!

 

 

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU…!* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI DA NA GOMA SHA TAKWAS*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

*FAN’S INA GODIYA DA FATAN ALKAIRIN DA KUKE MIN A KULLUM,ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI* 👏🥰

 

 

*** Umma ta na zaune a tsakar gida kan dadduma ta idar da sallar magriba,carbi ne a hannun ta tana salati da hailala,a gefe guda zuciyar ta cikin tsananin mamaki take sosai da rashin dawowar Hamza gida har magariba tayi,ta san halin Hamza duk wani Aike da za ta yi masa ya kan hanzarta yaje ya dawo akan lokaci ba tare da jinkirtawa ba,to menene dalilin dad’ewar sa haka?anya kuwa lafiya?duk cikin damuwa take jin ranta ta kasa ko da shan ruwa duk da lokacin shan Ruwan ma ya wuce,har lokacin da azumin ta a bakin ta na ranar Alhamis,kamar yadda suka saba yin Azumi a duk wata ranar litinin da Alhamis ita da Hamza.

Ta na nan zaune taji Sallamar sa ya shigo gidan,da Hanzari ta waiwaya ta dubeshi tana amsa sallamar,kuma shigowar sa yayi dai dai da kawo wutar NEPA wadda ta haskake tsakar gidan sosai,Umma ta bi Hamza da kallo ganin sa da Yarinya akan kafad’arsa,ga k’atuwar jaka a hannun sa,kansa a sunkuye ya zo ya gifta ta gabanta ya shige cikin parlour’n ta,kan kujera ya nufa ya sauke Hidaya a hankali Dan kar ta farka,ya gyara mata gashin ta da ya ba zo ya rufe mata fuskarta,ta D’an motsa a hankali tana tura yatsanta guda d’aya a bakin ta tana tsotsa,ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta,tausayin ta na ratsa shi,Yarinya k’arama amma har shafukan k’addararta sun fara bud’ewa,an ambaceta da marainiya mara Uba,ta rabu da mahaifiyarta a shekaru na yarinta,babu dangi na nesa balle na kusa!ga lalura me wahalar da Numfashi.

Hak’ik’anin gaskiya Hidaya ta cancanta a tausaya mata,ajiye jakar ta yayi a k’asa daga gefe,ya sake sunkuyawa ya tofa mata addu’o’i,ya rage yawan iskar fanka,sannan ya juya ya fito tsakar gidan jikin sa a sanyaye.

Umma na nan in da ya barta ko motsi bata yi ba,shi ma wucewa yayi zuwa kitchen ya d’akko wankakken plate,ledar sa ta kayan marmari na hannunsa,ya kwance ta ya juye kayan marmarin a cikin plate d’in,ya d’auka ya fito da su ya k’ara so gaban Umma ya ajiye,a hankali yayi magana cikin sunkuyar da kai.

“Umma ki D’an yi min Afuwa na gabatar da sallar magariba ,saboda kar lokacin ta ya tsere mini”

Yana fad’in hakan ya mik’e tsaye ya nufi toilet d’in tsakar gidan,ya d’auki buta da ke cike da ruwa ya shiga ya gabatar da tsarki,ya fito ya tsuguna ya gabatar da cikakkiyar alwala a nutse,Umma dai sai kallon sa take yi,har ya kammala ya kuma komawa parlour’n ya d’auko wata daddumar ya fito ya shimfid’a ya ta da sallah,kasancewar ko yaje masallaci tuni an idar,shiyasa bai fita ba yayi abarsa a gida,har ya idar yayi addu’oin sa sannan ya waiwayo ya dubi Umma,ganin kallon da take masa sai yayi Murmushi ya matso kusa da ita ya kamo hannun ta ya rik’e,yayi magana yana duban kayan marmarin da ke gabanta da ko kallon su bata yi ba.

“Umma ya ba ki sha ba?Bismillah ki sha mana”

Ya fad’a tare da k’ara turo plate d’in gabanta.

Tayi shiru bata tanka ba sai kallon sa kawai da take yi,haka nan bata da niyyar sha,fuskantar hakan da yayi ya sa ya kuma magana cikin tausasawa yana kallon ta da murmushi akan fuskar sa.

“Umma kiyi hak’uri banyi miki sannu da shan ruwa ba,dafatan kin sha ruwa lafiya?kuma kiyi hak’uri da b’ata lokacin da na yi ban dawo ba,abin da kika hore ni da aikatawa naci karo da shi a hanyata ,shine dalilin rashin dawowa ta akan lokaci”

“Me kenan Hamza?” Umma ta tambayeshi,karo na farko kuma da tun shigowar sa tayi magana kenan.

“Taimako Umma,wani taimako na tsaya yi”ya bata amsa cikin karsashi.

Tayi ajiyar zuciya idanuwanta a kansa tace.

“Wane irin Taimako ne Hamza,wacece wannan da naga ka shigo da ita har ka wuce d’aki da ita?wacece ?ina ka samo ta?

Ya sauke numfashi,cikin Y’ar fargaba yace.

” Wata baiwar Allah ce Umma,mai tsananin rauni da Neman taimako”

Umma tace.

“Mu ma bayin Allah ne Hamza,kuma masu Neman taimako a wajen Allah,kawai ka fayyace min wacece ita?”

Ya kuma sauke ajiyar zuciya sannan yace.

“Zan gaya miki Umma na ,amma don Allah kiyi min alfarma ki fara saka wani Abu a cikin ki kafin na sanar da ke komai,kinga Azumi kika yi,ya kamata ace zuwa yanzun kin ci wani Abu”

Ta yi Murmushi tana yabawa da kulawar da yake bata,ta mayar masa da amsa da cewa.

“Kai ma ai Azumin kayi,kuma har zuwa yanzun ba ka ci komai ba,ta ya ya zan ci alhali kai baka ci ba Hamza”

Yayi Murmushi mai k’ayatarwa har fararen hak’oran sa suka bayyana,cikin jin dad’i yace.

“To mu sha wannan tare Umma,idan muka kammala nayi alk’awarin sanar da ke komai da ya faru daga fita ta d’azu har zuwa dawowa ta”.

Umma ta girgiza kai cike da gamsuwa,tayi bisimillah ta saka hannun ta ta fara d’aukar kankana ta kai bakinta,sai da yaga ta sha sannan shi ma yayi bisimilla ya d’auka ya kai bakin sa ya tauna,ya lumshe idanu a hankali yana jin dad’in yadda suke shan Abu a kwano d’aya shi da mahaifiyar sa.

 

 

 

 

******************

 

Umma ta jima cikin k’urawa Hamza idanu bayan ya kammala fad’a mata abin da ya faru!wani irin mugun tausayin Hidaya na ragargazar zuciyar ta,ka sa hak’uri tayi ta mik’e daga tsakar gidan ta shige parlour’n ta,taje dab da Hidaya da ke kwasar bacci ta tsaya ta tsura mata idanu,a hankali Hamza ya d’aga labulen parlour’n shi ma ya shigo,ya tsaya dab da Umma suka tsurawa Hidaya idanu suna ta kallonta ,Umma ta waiwayo fuskarta cike da alhini ta kalli Hamza,tayi magana a hankali gudun kar Hidaya ta farka.

” Yanzu duk abin da ka fad’a min akan yarinyar nan da gaske ya faru Hamza?”

Ya sauke numfashi ya jijjiga kai yace.

“Abin da mahaifiyar ta ta sanar da ni nima shi na fad’a miki Umma,gaskiyar faruwar abin ko akasin hakan wannan Allah ne masani,sai dai a iya kallon da na yi mata na hango gaskiya cikin idanuwan ta,kuma na kyautata mata zato”

Ta nemi kujera ta zauna,yayin da Hamza ya zauna a k’asa ya tank’washe k’afafuwan sa yana kallon ta,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi magana.

“Wani kokonto ne ya shiga zuciyata Hamza,ka tara hankalinka guri guda ka hango abin da na hango,ta ya ya Uwa mahaifiya za ta bawa Wanda bata sani ba d’iyar da ta haifa?kuma har tayi masa umarnin kai yarinyar Gidan Marayu?ni fa zuciyata a tsorace take Hamza!na fara zaton wani mummunan al’amari akan hakan…..

Da sauri ya fara girgiza kai,fuskar sa cike da alhini ya fara magana.

” Ah ah Umma,kar kiyi mummunan zato akan lamarin wannan Yarinya,domin bamu san komai a kanta ba,abin da yafi gara mu kyautata zato a kanta,sannan yawaita zato babu kyau,musamman mummunan zato,ko domin fad’in Allah mad’aukakin sarki.

“یأیھا الذین ءامنوا اجتنبوا کثیرا من الظن إن بعض الظن إثم”

Ma’ana:(Ya ku wad’anda suka yi imani,ku guji yawancin zato,domin wani b’angare na zato zunubi ne).

Haka nan a wani Hadisi ,Annabi (S A W) yana cewa.”ku guji zato ,domin zato shine mafi k’aryar zance”

“Dan haka Umma mu kyautata zato akan Hidaya da mahaifiyarta ,kar muyi musu mummunan zato”

Umma ta sauke numfashi ta k’urawa Hamza ido tace.

“Haka ne Hamza,tabbas ka tunasar da ni abin da na manta,shikenan babu komai,Allah ya kai mu goben da kaina zan shirya na raka ka gidan marayun domin mu kaita,Allah ya kyautata rayuwar ta”.

” Ameen Umma”Hamza ya amsa yana murmushi.

Suka yi shiru suna kallon Hidaya,sai can Umma ta kuma cewa.

“Ya kamata a tashi yarinyar nan a bata abinci,dole za ta ji yunwa fa”

Ya jinjina kai ya D’an tara gira yace.

“Amma Umma ina tsoron a tashe ta bata ga mahaifiyarta ba tayi kuka! Tunda mu dai ba sanin mu tayi ba”

Umma ta D’an yi murmushi tace.

“Insha Allahu babu abin da zai faru,ba zata yi kuka ba,bai kamata a barta da yunwa ba Hamza,kuma ai kai ta riga ta sanka,tunda har ta nemi kaje ka bawa mahaifiyarta Ruwa”

Hamza ya D’an yi dariya yana sunkuyar da kai,yace.

“To babu laifi Umma,a tashe ta d’in ta samu ta ci abincin,ni fargabata ma ko ya ya mahaifiyarta ta take a yanzu?saboda gaskiya na barta cikin mawuyacin hali,ina jin tamkar na koma inga halin da take ciki a yanzu wallahi”

Fuskar Umma ta nuna Jimami sosai!tace.

“Insha Allah tana cikin Aminci,Allah ya dubeta ita ma,Zo ka tashe ta,bari na had’o mata tea da wancan dankalin da na soya,zai fi mata sauk’in ci”

Umma ta ambata sannan ta mik’e ta fice daga parlour’n.

A hankali ya rarrafa kusa da Hidaya da ke ta bacci hannun ta cikin bakin ta,ya rasa ta ya ya ma zai tashe ta,kawai ji yake k’irjinsa na bugawa fat fat,da k’yar ya iya d’aga hannunsa ya kai kan nata hannun ya zare daga bakin ta,yana zare hannun kamar wadda aka daka ta tsandara wani ihu tana k’ok’arin bud’e idanu,a gigice ya mik’e tsaye yana zare idanuwan sa saboda ihunta ya zo masa a bazata…….!

Ihunta ne ya shigo da Umma parlour’n da sauri,hannun ta d’aya rik’e da kofin shayi,d’ayan plate ne ta zubo dankali,tana shigowa Hamza ya dubeta a firgice yace.

“Wai fa Umma kawai hannun ta da ke bakin ta na cire mata,shine tayi wannan ihun”

Umma tayi murmushi ta ajiye kayan hannun ta,ta matsa kusa da Hidaya da take k’ok’arin komawa bacci bayan ta mayar da hannun ta cikin bakin ta,ta kai Hannu za ta d’ago ta,da sauri Hamza yayi magana.

“Umma ki k’yale ta kawai,kar ki tab’a ta ta sake yi mana ihu”

Umma tayi Y’ar dariya tace.

“Kai dai wani zubin matsoraci ne Hamza,yanzu D’an wannan ihun ne ya sa ka firgice haka?

Ya D’an Sosa kansa yayi murmushi yace.

” Allah Umma ihun ne ya zo min a bazata,kawai fa daga cire mata Hannu a bakin ta shikenan ta zunduma ihu”

Umma tace.

“Ai yara masu tsotsan Hannu ba sa son a na cire musu hannun idan suna tsotsa,kuma da alama tana da hak’uri,saboda yara masu wannan d’abi’ar ta tsotsan Hannu suna da hak’uri ,ba su cika rigima ba”

Umma tana kammala maganarta ta juya ta ciccib’o Hidaya ta d’ora ta kan cinyar ta,a hankali ta fara shafa fuskarta tana ambatar Sunan ta”Hidaya…ke Hidaya bud’e idanuwan ki kinji…”

Hamza yana ta kallon su yana son ganin yadda Hidaya za ta yi idan ta farka,Umma kuma na ta ambatar sunanta tana D’an jijjigata,sai Hidaya ta fara bud’e idanuwan ta masu cike da barci,Umma tana ganin haka ta mik’e tsaye ta dire ta,sannan ta ja hannun ta suka shige bedroom d’in ta,toilet d’in d’akin ta ta kaita ta tsugunar da ita tayi fitsari,tayi mata tsarki,ta wanke mata fuskarta da bakinta,sannan ta kamota suka sake fitowa parlour ‘n.

Har lokacin Hidaya bata gama wartsakewa ba,Hamza na tsaye suka fito,Umma ta zauna ta jawo Hidayan jikinta,ta kalli Hamza tace.

“Mik’o min tea d’in nan ka wani tsaya k’erere a tsaye,ka nemi waje ka zauna mana”

Da hanzari ya d’auko kofin ya mik’owa Umma,sannan ya durk’usa gaban su,ta karb’a tana k’ok’arin bawa Hidaya a baki, babu musu Yarinya ta karb’a ta fara k’walk’wala saboda babu zafi,Umma ta fifita ya huce.

Sai da ta gama sha tas,Umma tace wa Hamza”Mik’o dankalin ka ga har ta shanye shayin,k’ila daman tana jin yunwa fa”

A lokacin ne Hidaya ta fara dawowa hayyacin ta daga sakin da bacci yayi mata,ta d’aga kanta ta k’urawa Umma idanu,Umma na yi mata murmushi,har Hamza ya mik’o dankali yana fad’in.

“Ga shi Umma” a lokacin Hidaya ta d’auke kallonta daga kan Umma ta mayar kan Hamza,k’ura masa idanu tayi,shi ma ya zuba mata ido,ta kuma mai da kallonta kan Umma,sai kuma ta mik’e da hanzari daga kan cinyar Umma ta nufi Hamza ta fad’a k’irjinsa ta ruk’unk’ume shi ta fasa wani gigitaccen kuka da kiran “Mummy naaaaaa……!

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA GOMA SHA TARA DA NA ASHIRIN*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

 

Ya D’an runtse idanu saboda yadda kanta ya bugi k’irjinsa,a gigice ya D’an kauce yana niyyar janye ta,ta k’ara matsawa jikinsa tana ruk’unk’ume shi sosai tana kuka,ya rik’o hannun ta yana shirin b’amb’areta a jikin shi amma ta rik’e shi gam,mamakin k’arfin ta yayi duk da ta kasance siririya matuk’a,ganin yadda yake kokawa da ita tak’i tsayawa sai kuka take tana rirrik’eshi,Umma kam tsayawa tayi kallon ikon Allah ta kasa magana.

A hankali ya waiwayo a gajiye ya dubi Umma,ya narke fuska yace.

“Umma ki mata magana ta sakeni,kinga dai ba wani Abu naci ba duk ta sake gajiyar da ni”

Umma tayi murmushi tace.

“Ai yanzu fa dole sai kayi hak’uri domin kai ta sani,ba Lallai ta yarda da ni ba dole kai za ta mak’alewa Hamza”

Fuska cike da Alhini yace.

“To ni yanzu ya zan yi da ita Umma?ina so naje na ci abinci,Sannan na fita masallaci sallar isha’i,kuma kin san k’arfe Tara ina da waya ni da Khaleel”

Umma ta sauke numfashi ta na kallon Hidaya da ta lafe jikin Hamza tace.

“Lallab’ata za ka yi ta ci abincin,na tabbatar idan ta k’oshi da kanta za ta koma baccin’

Ya D’an girgiza kai,to shi ta ya ya ma zai lallab’ata?gaba d’aya bai ma san ya zai yi ba,ya kalli Umma duk a daburce yake,kukan Hidaya na damunsa duk ta jik’a masa gaban riga da Hawaye da majina,kamar me tsoran magana haka ya daure ya fara ambatar sunanta yana d’ago ta daga jikin sa.

” Hidaya…ke Hidaya tashi kiji wata magana kinji…za ki gun mummyn ki ko?”

Ta na ji ya ambaci Mummyn ta tayi sauri ta d’ago ta kalleshi tana jijjiga kai,har da murmushin ta,fuskarta duk zanen hawaye,ya kalleta yana rik’e hannun ta.

“Za ki je gun Mummy ko?”

Ta gyad’a kai.

Ya D’an sakar mata Murmushi yace.

“Mummy ta je unguwa za ta dawo,in kuma ba ta dawo da wuri ba zan kai ki gun ta,amma idan kina so na kai ki sai kin daina kuka,kuma sai kinje gun Umma na ta ba ki abinci kin ci kinji”

Ya nuna mata Umman,ta waiwaya ta kalli Umman,Umma tayi mata Murmushi, Hidaya ta kau da kai ta kalli Hamza ta mak’e wuya alamar ba zata ba,ya D’an dafe kansa,sannan ya d’ago ya kalleta yace.

“Ba za ki je gun Umman ba?”

Ta gyad’a kai tana k’ok’arin sake fashewa da kuka,da sauri ya girgiza mata kai yana k’ok’arin zaunar da ita kusa da shi,tak’i yarda sai nane masa take,yana ji yana gani haka ta matseshi kamar zata koma cikin sa,Umma dai ta na ta kallonsu ba tayi magana ba.

Janyo plate d’in dankalin yayi ya fara d’ebowa yana kai mata bakin ta,ba musu ta karb’a ta fara taunawa a hankali,ya sauke ajiyar zuciya ya dubi Umma yana marairaice fuska,Umma tayi masa alamar yayi hak’uri na D’an lokaci ne,ya jijjiga kai ya mayar da hankalinsa kan Hidayan yana bata dankalin,ba taci da yawa ba ta daina karb’a alamar ta k’oshi,Umma ta mik’e ta kawo ruwa,ya karb’a ya bata tasha,yadda ya lura ko kallon Umma bata son yi,da sun had’a ido sai tayi saurin kau da kai ta matsa jikin sa,ko me ya sa oho!ya D’an tab’e baki.

Kiran Sallah ya fara jiyowa a masallaci,yana mik’ewa sai ga Hidaya ma tsaye tana rik’o hannunsa,ya rasa ya zai yi,a lokacin Umma dariya ta fara yi masa ganin duk ya rud’e Yarinya ta nane masa,da k’yar ya zaunar da Hidaya ya fara share mata hawayen da yake zubo mata,ya tausasa murya yana kallon ta yace.

“Hidaya ki zauna wajen Umma yanzu zan dawo,masallaci zani in yi sallah,kuma zan yi addu’a Umman ki ta dawo da wuri ko?

Ta D’an yi shiru,sai kuma can tace” Eh”.

Yaji dad’i har yayi Murmushi yace.

“Ko in baki waya ta kiyi game?kin iya game?”

Tayi magana da sanyin murya.

“Eh na iya,ina yi da wayar Mummy na”

Ya fara k’ok’arin zaro waya a aljihun sa yana dariya.

“Da kyau HIDAYA, bari na baki to kiyi,yanzu zan dawo ba zan jima ba,kar kiyi kuka kinji”

Ta girgiza kai,ya kamo mata game ya mik’a mata wayar,ta haye kujerar d’akin har da kashingid’a ta fara buga game tana dariya,mamaki ya kama shi,ya tsura mata idanu yana murmushi,haka kawai yaji dad’in ganin yadda take farinciki,Umma tayi sakato ganin yadda ya shagala da kallon Hidaya har za a ta da sallah a masallaci,sai da ta yi masa magana sannan ya Ankara,kunya ta kama shi,da sauri ya juya ya fice daga parlour’n domin tafiya masallaci,ya bar Hidaya na b’angala dariya ba ta lura da fitar sa ba.

 

 

 

*****************

 

Loakacin da ya dawo gidan sai ya tarar Hidaya har tayi bacci,ga wayar sa nan a gefen ta ita kuma sai bacci take,Umma na zaune tana cin abinci daga gefen ta,zama yayi kusa da Umma ya tsoma Hannu cikin kwanon suka cigaba da cin abincin tare, yayi loma d’aya sannan ya kalli Umma yace.

“Wannan Y’ar rigimar har tayi bacci kenan?”

Umma ta girgiza kai ba tayi magana ba,sai a sannan ya tuna da gargad’in Umma akan magana idan ana cin abinci,saboda za a iya k’warewa,hakan yasa yayi shiru,suka cigaba da ci,lokaci lokaci yana d’aga kai ya kalli Hidaya har suka kammala cin Wanda ke gaban su,Umma ta nemi a dad’o yace ya k’oshi ,ya tattara kwanukan ya fita da su ya wanko hannun sa.

Ya D’an jima suna hira da Umma duk akan Hidaya,sannan ya kalli Agogo yace.

“Umma bari na gudu d’akina,kar Khaleel yayi ta jirana ban kira shi ba”

“To Hamza Allah ya tashe mu lafiya,bari na kai Hidayan cikin bedroom, Allah dai ya sa kar ta farka cikin dare tayi kuka” Umma ta ambata tana niyyar mik’ewa.

Hamza ya amsa da “To ameen Umma”.

Yana kallo har Umma ta ciccib’i Hidaya,duk da bata da wani nauyi saboda sirantakar ta,suka wuce bedroom, sai da yaga shigewar su sannan ya sauke numfashi ya girgiza kai,a salub’e ya fice daga parlour’n zuwa d’akin sa.

Sai da ya kammala komai na al’adar sa ,ka ma daga wanka zuwa shirin bacci da sleeping dress masu kyau,sannan ya nemi waje ya zauna ya lalubo wayar sa da Hidaya ta jefar a parlour’n Umma,sunan Khaleel ya kamo Wanda ya rubuta (JININ JIKINA).

flashing yayi a lambar,wadda ta kasance ta k’asar waje,minti biyu wayar sa ta fara ruri alamar Khaleel ya kira shi,yayi murmushi yana jin wani sanyi a kansa,sannan ya d’aga wayar yayi sallama da k’ayatacciyar muryar sa.

Daga can Khaleel ya sauke numfashi cikin marairaicewa ya fara magana.

” Wai yau ina ka shiga ne Aboki?saura kad’an fa na rusa kuka saboda rashin jin muryar ka akan lokaci”

Hamza ya k’yalk’yale da dariya yace.

“Wane irin kuka kuma Khaleel?wallahi wasu Abubuwa ne yau suka yi min rubdugu sai hamdala kawai,to ya kake? Ya karatu?”

Khaleel ya amsa cikin shagwab’a tamkar mace.

“Gani nan dai kawai Aboki,rayuwar da babu kai a cikin ta ai lami ce,nan d’in babu wani dad’i sai hak’uri kawai”

Hamza yayi murmushi yace.

“To ya za a yi?kowa da in da Allah yake ajiye shi ya tsara masa rayuwa,ba ya yiwuwa daman mutum ya samu duk abin da yake so Khaleel,ka k’ara hak’uri akan Wanda kake yi,gani na ne kawai baka yi fa,amma kullum muna jin muryar juna,kuma kullum kana raina dai dai da second d’aya bana mantawa da kai”

Khaleel yayi ajiyar zuciya har Hamza ya jiyo shi,a hankali yayi magana.

“Shikenan Aboki na hak’ura,tun da babu yadda zan yi da daddy,wai ina Umma ne?ko har ta kwanta?

Hamza ya amsa.

” Eh ta kwanta,da yake yau tayi Azumi duk ta gaji ne”

Khaleel yace.

“Aboki kuna ta Azumi kai da Umma kuna samun lada,ni kuwa na kasa daurewa na dinga na litinin da Alhamis d’innan,gashi yana da falala sosai ko?”

Hamza yayi murmushi yace.

“Sosai ma kuwa!da za ka daure ka dinga yi,yana k’ara lafiya sosai ga jikin D’an Adam,yana durk’usar da zuciya,domin yawan k’oshi da abinci ya kan gadarwa zuciya girman kai da tak’ama da gafala,amma zama da yunwa na wani lokaci kan haskaka zuciya ta zama mai taushi,gami da gusar da k’ek’ashewar ta,ta zama killatacciya da tunani da zikirin Ubangiji,sannan Azumi kan k’untata magudanar jini,wad’anda sune magudanar shaid’an a jikin D’an Adam,domin shaid’an yana gudana a jikin D’an Adam a magudanar jini,haka nan yana k’ara kusanci ga Allah”

Khaleel yana sauraran bayanin Hamza Zuciyar sa na k’ara k’aunar sa,babu ranar da zai yi hira da Hamza bai samu wani Abu da ya k’aru da shi ba,Hamza ai kyakkyawar zuciya ne,yana jin sa tamkar Wanda suka fito ciki d’aya,ya lumshe idanu ya k’ara k’ank’ame wayar yace.

“Nagode Aboki,hak’ik’a kai d’in wani b’angare ne na jikina,Allah ya barmu tare,Ina sonka Hamza”

Hamza ya gyara kwanciya yana runtse idanu,sannan yace.

“Na fi sonka Khaleel,ka yi min abin da na zan manta da kai ba,ka yarda dani ka amince dani,na zama wani sirrinka,kai na daban ne a rayuwata Khaleel, komai kake so idan har ina da shi zan maka”

Khaleel yayi murmushi yace.

“Ina jin bacci,duk da ban gaji da jin muryar ka ba,me za ka fad’a min Wanda zai haskaka zuciyata Aboki na gari?

Kai tsaye Hamza yace.

” Sai dai in maka Nasiha,Nasiha akan tsoran Allah,wadda aka yi mana ranar juma’a yayin hud’uba a masallaci”

Da sauri Khaleel yace.

“Eh ina so Aboki,nima kayi min….

Hamza yayi murmushi yace…….!

” Ina yi mana wasiyya da ni da kai da mutanen duniya a kan muji tsoron Allah,domin tsoron Allah shine matattarar dukkanin alkairi gabad’aya,babu wani alkairi na nesa ko na kusa face tsoran Allah yana zaburarwa a kansa,haka nan,babu wani sharri na kusa ko nesa,a fili ko a b’oye,face tsoran Allah yana ba da Katanga don kariya daga gareshi.
Kuma hak’ik’a tsoran Allah shine Abu na farko da Allah yayi wa mutane farko da k’arshe wasiyya da shi.Allah yana cewa:

“ولقد وصینا الذین أوتوا الکتب من قبلکم و إیا کم أن اتقوا اللہ ”

(Hak’k’a mun yi wasici ga wad’anda a ka ba wa littafi gabaninku da kuma ku,a kan ku ji tsoron Allah)

Hakan nan y kamata mu san siffofin masu tsoran Allah,domin muyi k’ok’ari muyi koyi da su.Kad’an daga cikin siffofin sun had’a da:
Imani,da tsayar da Sallah,da ciyarwa domin Allah,da yarda da abin da Allah ya saukar,da sakankancewa da ranar Lahira.
Yana daga cikin alfanun tsoron Allah :Allah yana karb’ar aikin mai tak’awa ne,kamar yadda yace,

“إنما یتقبل اللہ من المتقین”

(Kad’ai Allah yana karb’a ne daga masu jin tsoron sa).

Yana daga cikin amfanin tsoron Allah,ubangiji zai ba wa mai shi kaso biyu na rahamarsa,kuma ya sanya masa haske da zai rik’a tafiya a cikin sa,kuma ya gafarta masa zunubansa,kamar yadda Allah yace,

“یأیھا الذین ءامنوا اتقوا اللہ و ءامنوا برسولہ یٶتکم کفلین من رحمتہ ویجعل لکم نورا تمشون بہ و یغفر لکمؒ واللہ غفور رحیم”

(Ya ku wad’anda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku yi imani da manzansa,zai Baku kaso biyu daga cikin rahamarsa ,ya sanya muku haske a cikin rayuwarku,ya gafarta muku,hak’ik’a Allah mai yawan gafara ne mai jin k’ai).

Sannan Allah yana sanya wa mai tsoron sa mafita daga duk wani K’unci da damuwa,kamar yadda yace,

“و من یتق اللہ یجعل لہ مخرجا”

(Duk Wanda yaji tsoron Allah,to Allah zai sanya masa mafita)

Dan haka ya kamata muyi guziri da tsoran Allah,domin mu rabauta a rayuwar mu ta duniya da Lahira,domin tsoron Allah shine mafi alfanun abin da bawa zai yi guziri da shi,saboda fad’in Allah ta’ala.

“و تزودوا فإن خیر الزاد التقویؒ واتقون یٰأولی الألبٰب”

(Ku yi guziri ,hak’ik’a mafi amfanin guziri shi ne tsoron Allah, kuma ku ji tsoro na ya ku masu hankula).

Khaleel babu abin da yake rik’e tsoron Allah ,ya kafe shika shikan sa a Zuciyar mumini sai yawan Ambaton Allah a kowane lokaci,a kowane hali,Dan haka babu makawa a dawwama akan zikirin Allah,da tasbihi,tare da godiya ga Allah,ko domin mutum ya samu ya murk’ushe abokan gabarsa guda biyu,(shed’an da son zuciya).

Ina fatan wannan wasiyya za ta shiga Zuciyar mu khaleel,kuma mu zama daga cikin masu aiki da ita.

Zuciyar khaleel tayi sanyi,hawaye ya zubo masa,sosai yaji maganganun Hamza sun ratsa shi,shiyasa ya dinga yiwa Hamza godiya mai tarin yawa,kafin suka yi sallama da juna Zuciyar su cike da kewa.

Hamza ya gyara kwanciyar sa domin ya D’an samu ya runtsa,ko domin ya samu tashi tsakar dare ya gabatar da ibadar sa kamar yadda ya sa ba…..!

 

Comments
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA ASHIRIN DA D’AYA DA NA ASHIRIN DA BIYU*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

K’arfe biyu na dare ya farka,bayan ya shiga toilet d’in d’akin sa yayi tsarki sai ya d’auro alwala,sallolin Nafila raka’a goma sha biyu ya gabatar,bayan ya idar yayi karatun alk’ur’ani,sannan yayi addu’o’i masu tarin yawa,har ya samu kansa da yiwa Hidaya addu’a ta fatan alkairi da samun sassauk’ar Rayuwa a gidan Marayu,haka nan yayi wa Mahaifiyarta addu’a akan duk in da take Allah ya tsare gabanta da bayan ta,sai wajen k’arfe uku da rabi sannan ya koma barci,bai jima da kwanciya ba aka fara kiraye kirayen sallah,haka ya mik’e bacci cike fal a idonsa,ya d’aura alwala yayi raka’atanil fijri,sannan ya bud’e d’akin sa ya fito.

Har k’ofar Umma yaje ya D’an bubbuga mata,bai jima ba ta taso ta bud’e tana muttsika idanu,yayi murmushi ya kalleta yace.

“Umma barcin bai isheki bane?ga shi har za a ta da sallah a masallaci”

Tayi Hamma ta dubeshi tace.

“Ashe har lokaci ya tafi haka,bari to nayi hanzarin d’aura alwala,Masallaci za ka tafi ne?”

Ya amsa yana gyara zaman dadduma a kafad’ar sa.

“Eh Umma Masallaci za ni,dafatan dai Y’ar rigimar nan bata hanaki bacci ba?

Tayi murmushi tace.

” Wai Hidaya?Ai yadda kasan matacciya saboda bacci,ko motsawa bata yi ba baccinta take cikin kwanciyar hankali wallahi”

Ya jinjina kai yana jin dad’i sannan yace.

“Alhamdulillah naji dad’in hakan Umma,ina ta fargabar kar tayi miki kuka Ashe ita baccinta ma ta sha,Lallai ta kyauta da bata wahalar min da Umma na ba”

Umma tayi murmushi, Yayi mata sallama ya wuce masallaci,ita kuma ta koma bedroom domin sallatar Asubahi.

Ya dad’e a masallaci yana Lazimi,sai da gari ya fara haske sannan ya dawo gida,ya koma d’akin sa ya D’an kwanta, bai ma san lokacin da barci ya sake d’auke shi ba.

K’arar kukan Hidaya ne ya farkar da shi,ya mik’e yana salati da addu’ar tashi daga barci,da k’yar ya mik’e ya fad’a toilet yayi brush ya wanke fuskar sa sannan ya fito,bai zauna ba sai ya wuce tsakar Gidan in da yake jiyo kukan Hidaya.

Tana tsaye d’aure da tawul a jikinta,da alamun wanka Umma tayi mata,fuskarta ta k’ara haske sosai,sai dai idanuwanta sun sauya kala duk sun yi ja saboda kuka,sai shesshek’ar Kuka take yi,bata kula da shi ba har ya k’ara so bayanta,lokacin Umma ta fito daga parlour’n ta da man shafawa a hannun ta,tana ganin Umma ta fito ta kuma fasa kuka kamar wadda aka ciza,ta juya da sauri tana kuka,kawai sai tayi arba da Hamza yana k’arasowa,ta ja wata ajiyar zuciya ta tafi da sauri ta rik’eshi tana kwantar da kanta a jikinsa,ya tsaya sakato suna kallon juna shi da Umma.

Umma tayi murmushi ta nufo su tana cewa.

“Yawwa ai gara da ka ta so,tunda ta tashi take Neman ka tana kuka,da k’yar ta yarda nayi mata wanka,nayi nayi mu shiga ciki na shafa mata mai ma amma tak’i,shine na shiga na d’auko na shafa mata a nan kawai”

Yayi murmushi yana rik’o kafad’un Hidaya ya rabata da jikinsa,sannan ya tsuguna gabanta ya kai Hannu ya share mata hawaye,ita kam sai k’ok’arin b’oye fuskarta take a jikinsa,yak’i bata damar hakan,ya dubi Umma fuskar sa da jimami yace

“Na rasa yadda akayi yarinyar nan ta sanni haka Umma,daga had’uwa da ita jiya tayi min wani mugun sani kamar Wanda muka shekara”

Umma ta k’ara sakin murmushi ta jawo kujera Y’ar tsuguno ta zauna,sannan ta dubi Hamza da Hidaya ta lafe a gefen sa tace.

“Ai dole ne Hamza,kai fa kana da shiga rai,nan da nan da mutum yayi maka gani d’aya yake jin ka kwanta masa a rai,kuma ba wai don kai d’in d’ana bane nake fad’in hakan a kan ka,ah ah,kawai gaskiya na fad’a,kuma kai kana da farinjinin yara,kaga dai yadda yaran layin nan suke cika Gidan nan saboda kai,ko Dan Nasiha da tarihin Annabawa da kake musu kullu yau min,Hidaya kuma tilas ta mak’ale maka,tunda kai kad’ai ta sani a halin yanzu,Ni wallahi har tausayin ta nake yadda za ta yi Rayuwar Gidan Marayu, ga ta ba wata ishasshiyar lafiya ce da ita ba,Rayuwar Gidan Marayu kuma ba wata gamsasshiyar kulawa za ta samu ba,saboda ciwonta yana buk’atar kulawa gaskiya,na ga yadda Maman Salma take fama da Salma akan wannan cuta ta sikila,wallahi Hamza ina tausayawa wad’anda Allah ya jarraba da wannan cuta mai wahalar da Numfashi.

Ya sauke numfashi duk ransa a jagule,ba komai yasa hakan ba sai wata gingimemiyar kewar Hidaya da ya fara ji a ransa,sai yaji baya son rabuwa da ita kwata kwata,amma ya zai yi ?tilas ya rabu da ita ya cika umarnin mahaifiyarta ,tausayin ta yake ji sosai,jin ta yake a jininsa tana yawo tamkar wadda suka fito ciki d’aya.

Ita kanta Umma ta fuskanci halin da Hamza ya shiga,kuma ita ma tuni ta fara jin kewar rabuwa da Hidayan,duk da Hidayan ba wani sakin jiki tayi da ita ba amma tana jin ta a ranta sosai tamkar d’iyar ta,lokaci guda taji ta zauna a Zuciyar ta daram.

Da wayo da dabara sannan Hidaya ta yarda Umma ta shafa mata mai,sai da Hamza ya bata wayar sa yace ta rik’e masa zai je yayi wanka ya dawo,a haka Umma ta shirya ta,sai ta rasa kayan da za ta saka mata,hakan ya sa ta jira har Hamza ya kammala shiryawa cikin shadda fara tas me aikin blue d’in zare,ya taje sumar sa da ta D’an fara taruwa,ya fito sai k’amshi yake zubawa yayi fes da shi ainihin zatin kyawun sa ya dad’a fitowa.

Ko Hidaya sai da ta bishi da kallo k’uri har ya iso gabanta ya tafa hannayen sa dai dai fuskar sa,sai ta D’an firgita kad’an,sai kuma ta fashe da dariya har jerarrun hak’oranta suka bayyana,kawai sai shi ma ya tsinci kansa da dariya yana kallonta,lokacin Umma ta fito daga bedroom tana wa Hamza magana.

“Hamza ya za a yi ne?Hidaya tayi wanka babu kayan sakawa”

Ya d’ago ya dubi Umma har lokacin fuskar sa da walwala yace.

“Ai ina jin kayan cikin jakar nan fa kayan ta ne,amma dai duba ki gani Umma”

Umma ta girgiza kai tare da komawa d’akin ta sungumo jakar ta fito da ita,zama tayi ta zuge jakar tana duba kayan,sai ta tarar duk kayan Hidaya ne masu kyau sosai kuwa,yawan ci y’an kanti ne dogayen riguna da riga da siket,sai lace da atamfa da shadda har ma da material su kam basu da yawa,ga takalma wajen kala shida,sai yarirrika da sark’ok’i da abin Hannu da ribbons iri iri na gayu,ga k’ananan pant dai dai jikinta.

Umma ta tsurawa kayan idanu tana mamaki,gaskiya duk in da Hidaya ta fito to daga gidan arzik’i ta fito,domin a cikin sark’ok’in ta har da sark’ar gwal guda biyu,kuma manya ne ba laifi,hakan yasa ta tasa kayan a gaba tayi shiru kawai.

Shi kam Hamza yana can hankalin sa na kan Hidaya da ya kamo mata cartoon a wayar sa tana kallo tana dariya yana taya ta,sai can ya waiwayo ya dubi Umma ya ga tayi kasak’e da kayan a gaban ta,gyara zama yayi yace.

“Umma babu kayan ta a ciki ne?”

Ta sauke numfashi tace.

“Duk ma kayan ta ne a ciki fa”

“To Umma d’auko mata guda d’aya ta saka kawai,sai tayi break fast,kar tai ta zama da towel a jikin ta” ya fad’a a sanda yake k’ok’arin mai da hankalin sa kan Hidaya da take ta nuna masa wayar hannun ta tana cewa “kalli kaga”.

Umma ta zaro mata wani d’an d’asheshen material ja mai duwatsu ,d’inkin doguwar riga ne mai kyau,da flowers milk a jiki,ta d’auko mata takalmi milk color da sarka,sannan tayi mata magana akan ta taso ta sanya kaya a jikin ta.

Ita kam hankalin ta na kan waya har sai da Hamza ya sake yi mata magana sannan ta waiwayo ta kalleshi ta k’ura masa idanu,ya sake mai maita mata maganar sa.

” ki tashi ki sanya kayan ki,ko ba kya so mu tafi na kai ki wajen Mummyn?

Sai ta jijjiga kai ta b’ata fuska,ya zaro idanu yace.

“Ba kya so?me yasa hakan Hidaya?”

“Ni ma ba zani ba tunda ta gudu ta barni” ta fad’a da shagwab’a.

Yayi murmushin yace.

“Ayya Hidaya ki mata Afuwa kinji,wani uzuri ne ya sa ta tafi ta barki,kiyi hak’uri”

Ta D’an yi shiru,sai can ta kalleshi ta rik’o hannun sa tace.

“Amma dai idan ka kaini kai ma za ka zauna a wajen mummy ko?”

Ya kalli Umma k’irjinsa ya buga,Umma tayi murmushi tana kallon su,sai ya girgiza wa Hidaya kai yace.

“Ah ah Hidaya,ni ma zan dawo wajen Umma ta ne mu zauna tare ni da ita”

Bai aune ba yaga hawaye ya fara sintiri a idanuwan ta,ta fara buga k’afa tana kuka wai ita in dai ba zai zauna gun mummy ba ita ma ba zata tafi ba,hankalin sa ya tashi ya rasa ya zai yi ,gashi baya son kukan ta,da ta fara kuka yake Neman nutsuwar sa ya rasa,ya kalli Umma idanuwan sa sun fara sauyawa yace.

“Ya zan yi Umma?”

Tayi ajiyar zuciya ta jawo Hidaya ta rungume ta,abin mamaki sai bata k’i ba,ta kwanta luf a ji kin Umma tana ajiyar zuciya da hawaye,Umma ta dinga Shafa kanta ta kalli Hamza tace.

“Hamza na lura yarinyar nan tana sonka,kuma ba ta son rabuwa da kai”

Ya shafa gashin kansa da ke kwance yana k’yallin gyara,fuska babu walwala yace.

“To ya za mu yi Umma?haka nan za ta yi hak’uri mu rabu……

Bai k’arasa ba yaji muryar sa tayi rauni,da sauri ya mik’e ya fice daga parlour’n hawaye na ciko idanuwan sa.

Umma da ta hango damuwarsa sai taji duk na dad’i,ita kanta ba ta son rabuwa da Hidaya ko kad’an,musamman yanzu da take kwance a jikinta sai take jin k’aunarta na ratsata,da k’yar Umma ta daure ta dinga lallashin Hidaya har tayi shiru,kayan da ta d’auko mata kam k’in sakawa tayi,wai ita irin kayan Ya Hamza za ta saka,Umma ta dinga dariya tace.

” To ban da abin ki Hidaya ina mace ina sa kayan maza?

Kawai sai Umma taji Hidaya ta fara koro zance.

“Ai Umma akwai kayana kalar na sa a nan,ni dai su zan saka muyi iri d’aya kinji”

Haka tilas Umma ta birkice jakar ,sai daga can k’asa ta ci karo da wasu y’an kanti riga da siket,rigar fara me tutoci blue,sai siket d’in kuma blue color, Hidaya ta dinga Murna ta d’auki kayan ta saka da kanta,Umma ta d’auko mata wata farar hula ta bata ta saka,jelan gashinta duk sun bazo kafad’un ta,sai tayi wani irin kyawu na ban mamaki.

Sai lokacin ta fara cigiyar Hamza,Umma tace .

“Yana d’akin sa k’ila,je ki ki kirawoshi ya zo kuyi break fast”

Hidaya tayi tsalle ta tafi da gudunta Umma tana nuna mata k’ofar d’akin,Umma tayi murmushin ganin yadda Hidayan ta fara sakewa,ta shige kitchen domin fito da kayan break fast.

Shi kam Hamza na kwance rigingine akan bed d’in sa,kan sa a sama ya fad’a cikin tunani,duk a jagule yake jin ransa,Zuciyar sa na k’unar Rabuwa da Hidaya,rabuwa ta biyu da yake jin tana tab’a ruhin sa,ya rabu da abin da ya fi so cikin rayuwar sa wato (Khaleel) da k’yar ya jure ya daure wa wannan rabuwa kafin ya samu Zuciyar sa ta sake,kullum yana kukan rashin (Khaleel) kusa da shi,to ga Hidaya ta shigo rayuwar sa cikin kwana d’aya tak!amma yana jinta a Zuciyar sa kamar wadda suka shafe tsawon shekaru da dama.…
Wani Hawaye mai zafi ya tsiyayo masa yana gangarowa ta gefen fuskar sa,tattausan Hannun Hidaya kuma k’arami,shi yaji akan fuskar sa tana goge masa Hawaye,cikin raunin murya kuma yaji tayi magana a shagwab’e..

“Ya Hamza me yasa ka ke Kuka…?”

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA ASHIRIN DA UKU DA NA ASHIRIN DA HUD’U*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

Yana daga kwancen ya D’an waiwayo da kansa yana duban ta,ga mamakin sa sai ita ma yaga hawayen a idanuwanta suna shirin zubowa,ya yunk’ura ya mik’e zaune bakinsa d’auke da salatin Annabi,ya kai Hannu ya murje ragowar hawayen da ke fuskarsa,sannan ya dubeta da D’an murmushi yace.

“Ya dai Hidaya?

Ta kai Hannu ita ma ta goge na ta hawayen,ta turo baki gaba tace.

” Me ya sa ka ke kuka?”

Ya girgiza kai.

“Babu komai Hidaya,kawai na tuna wani abokina ne da yayi tafiya mai nisa,shine kewarsa ta saka ni Hawaye”

Ta rik’o hannun sa tana wasa da yatsun sa,ta kalle shi tace.

“Amma zai dawo ko Ya Hamza”

Ya jijjiga kai alamar eh,sannan ya zarce da cewa.

“Amma dai zai jima bai dawo ba,gashi bani da wani Aboki sama da shi,shi kad’ai me babban Aboki na”

Ta d’an yi dariya kad’an ta zura masa idanu tace.

“To ba gani ba Ya Hamza,tunda baya nan ai ni sai na zama k’awarka kawai”

Yayi murmushi yace.

“Hidaya kenan!ai babu abota ko k’awance tsakanin Namiji da mace,ai ni yayanki ne ke kuma k’anwata ce ko?”

Ta jijjiga tana kallon sa tace.

“Eh kuwa, shiyasama zan dinga ce maka Ya Hamza,shi kuma Abokin ka ya sunan sa?”

Kai tsaye ya amsa mata da cewa, “Khaleel”.

Tayi tsalle tana cewa.

” Ya Hamza zan dinga kiransa Uncle Khaleel ka ji,Mummy na tace idan mutum ya girme ni na dinga ce masa Yaya ko Uncle, idan mace ce kuma Anty ko Adda”

Ya zame hannun sa cikin na Hidaya yana amsawa da.

“Hakan na da kyau yarinyar kirki,ke kuma k’awayen ki guda nawa ne?”

Ta d’aga kanta sama kamar tana tunani har da sa d’an yatsanta a hab’ar ta,ya bita da kallo cike da birgewa,sai can ta sauke kallonta kan fuskar sa ta kamo yatsun ta ta na k’irgawa da su,har ta k’irga guda uku,cikin murmushi tace.

“Ka ga k’awayena haka ne Ya Hamza,Amma na yi fad’a da guda biyu,saura d’aya nake kulawa?”

Ya d’an zaro ido yace.

“Fad’a kuma?Ashe k’anwar ta wa mafad’aciya ce kenan?me yasa kika yi fad’a da su?”

Ta b’ata fuska saboda tuno abin da suke mata tace.

“To Ya Hamza ba su bane sai su yi ta tsokana ta wai k’ashi da rai,ko su ce min k’anjamammiya me ciwon sikila,ko su ce min me idon mage”

Tausayin ta ya kamashi,ta tab’e fuska kamar za ta yi kuma,nan da nan ya fara lallashin ta da cewa.

“Rabu da su kinji my k’anwa,Ai Allah ne ya jarrabeki kuma zai yaye miki tare da duk wani mai ciwon,kuma ke ba k’anjamammiya bace,za ki yi k’iba nan gaba kad’an insha Allah”

Ta saki fuska sosai sannan ta dubeshi tace.

“Kuma idan suka sake tsokana ta za ka rama min ko?za ka doke su ko?”

Ya gyad’a kai yana murmushi yace.

“K’warai kuwa,insha Allah zan zama GARKUWAR ki,babu Wanda zan bari ya tab’a ki Hidaya”

Tayi wani irin tsalle da juyi na murna,bai aune ba yaji ta fad’o kansa tana tuntsira dariyar murna,shi ma sai ya samu kansa da dariyar,da k’yar ya b’anb’areta a jikinsa,sannan ya zaunar da ita kusa da shi suka cigaba da hirar su cikin farinciki.

Umma dai ta ji su shiru ba su tawo ba,amma tana jiyo hayaniyar su musamman Hidaya da take ta zuba masa hira kala kala da zance,shi ba gwanin magana ba ma amma haka ya daure ya biye mata,tana ta d’akko Abubuwa a d’akin tana masa tambaya a kai,shi kuma bai k’osa ba yana ta bata amsa da kulawa.

Sai da Umma ta k’wala masa kira sannan ya mik’e yana amsawa yayi hanyar fita,Hidaya ta cillar da tsintsiyar da ta d’auka wai za ta yi shara,ta bishi a baya da gudu har ta cimmasa ta rik’o hannun sa suka jera har gaban Umma da ke ktcheen ta kammala had’a break fast, ya d’an Sosa k’eya yana murmushi yace.

“Ayya Umma na kiyi hak’uri ban zo na tayaki aiki ba yau”

Tayi murmushi tana rufe flask d’in tea tace.

“Ina za ka tuna dani ka samu Hidaya?ai tun d’azu ina ta jiyo shewar ku,Aiken ta na yi fa tayi kiranka kuzo ku karya shine ta shantake a can”

Ya mik’a Hannu ya karb’i flask d’in,Hidaya kuma ta d’auki wani tire da aka jera cups guda uku a kai,Umma tana cewa “Ajiye Hidaya ba za ki iya ba” ita kuma Hidaya na cewa”Allah zan iya Umma,ni fa ina da k’arfi sosai”

Umma tayi dariya a ranta tana cewa.

“A wannan Lange langen jikin na ki ina wani k’arfi?”

A parlour suka baje suna karyawa su Uku,Hidaya na ta wasanni ta k’i maida hankali kan cin abinci,Hamza ta na fama da ita dai Umma na tayashi har suka Kammala,shi da Hidaya suka kwashe kayan suka fita da su,Hidaya tace alambur ita za ta yi wanke wanken cups da spoon d’in da suka b’ata,Dan kar tayi rigima Umma ta k’yaleta,ta had’a mata Ruwan kumfa ta barta a tsakar gidan ta dawo parlour gun Hamza.

Zaune ta tarar da shi yana danne danne da wayar sa,ta zauna ta dubeshi cikin kulawa tace.

“Ya kamata ka tashi kayi shirin da za ka yi,nima a shirye nake,domin mu wuce mu mik’a yarinyar nan yanzu ko?”

Da wani irin hanzari ya d’ago ya kalli Umma,fuskarsa cike da tashin hankali mara misali,ganin yadda Umma ta zubo masa idanu shiyasa yayi saurin waskewa ya sunkuyar da kai,a hankali yace.

“To Umma,bari na d’auko takardar da za mu kaita da ita,tana cikin aljihun wando na na ranar da na saka,tare da envelop d’in da mummyn Hidayan ta bani akan na ajiyewa Hidaya sai ta girma sai na bata”

A hankali ya mik’e,jikin sa a sanyaye ya fito daga parlour ‘n,Umma ta bishi da kallo tana girgiza kai cike da damuwar rabuwa da Hidaya.

Hidaya na kallon fitowar sa ta fara d’aga Hannu tana yi masa magana.

“Ya Hamza zo ka tayani wanke wanke,sai kayi min d’auraya ko?”

Ya tsaya cak! ya waiwayo yana dubanta cikin wani yanayi,duk ta jik’a jikinta da ruwa,kumfar omo kuwa har a fuskarta tayi faca faca,ya k’ura mata idanu sosai,wata kewa ta mamaye ruhinsa,yaji tamkar ya rusa ihu,Hawaye ya ciko idanuwan sa,da sassarfa ya juya da hanzari ya wuce d’akin sa ko gabansa baya iya gani.

 

**************

 

 

Yana shiga d’akin sa ya kife kansa a bango yana sakin numfashi, idanuwan sa a runtse k’irjinsa na zafi sosai,ya rasa dalilin da ya sa yake jin wani matsanancin ciwon tafiyar Hidaya,bai santa ba !bai sa ba da ita ba!rana d’aya ta shigo rayuwar sa tana son hargitsa masa lissafi!Yarinya k’arama da ita!kuma ya san matsanancin tausayin ta ke d’awainiya da shi! Ya sake lumshe idanuwan sa hawaye na taruwa,a hankali bakinsa ya motsa yana addu’a domin nemawa kansa sauk’in da yake ji a fad’in k’irjinsa,domin ya tabbatar Allah ba ya nufin bayin sa da tsanani sai sauk’i,kamar yadda ya fad’a a cikin littafinsa mai Girma.

“یرید اللہ بکم الیسر ولا یرید بکم العسر”

(Allah yana nufin sauk’i gare ku,baya nufin tsanani)

Haka nan Annabi(S A W)Yana cewa sahabbansa:”Ku sassauta kada ku tsananta,kuyi bushara kada ku Kore” Bukari da Muslim ne suka rawaito shi.

Yana tuna hakan ya sauke numfashi da k’arfi,ya cigaba da addu’a sosai,sai yaji k’uncin Zuciyar sa ya fara yaye wa,musamman da ya tuna cewa,Allah yana sane da Hidaya,domin shine mahaliccinta,shine mai zab’a mata rayuwa a duk in da ya so,haka nan Allah yana jin sa da ganin sa,kuma yana da yak’inin zai amsa masa addu’ar sa wadda yayi Daren jiya,akan Idan zaman Hidaya gidan Marayu alkairi ne Allah ya tabbatar, idan kuma babu alkairi to Allah ya sauya mata da mafi alkairi a rayuwar ta,Ubangiji mabuwayin sarki shi yace mu rok’e shi zai amsa mana mu bayin sa,domin shi makusanci ne a garemu,kuma yana amsa addu’ar duk Wanda ya kira shi .Allah ta’ala yace.

“و إذا سألک عبادی عنی فإنی قریب،أجیب دعوة الداع إذا دعان،فلیستجیبوا لی ولیٶمنوابی لعلھم یرشدون”

(Kuma yayin da bayina suka tambayeka game da ni,to ni makusanci ne,ina amsa addu’a idan ya kirani).

A take yayi Hamdala ga Allah,sannan ya k’ara da salatin Annabi,sai ya ji jikinsa yayi k’wari,Zuciyar sa cike da jarumta,k’afafuwansa da suka yi sanyi suka soma k’arfafa,ya ta ka ya nufi wardrobe d’in sa ya bud’e ya zaro wandon kuftar da ya sa ka jiya da k’addara ta had’ashi da Hidaya,ya zauna a gefen gado ya zira hannuwan sa cikin aljihun wandon da nufin zaro takardar,cikin ikon Allah ya zaro ta ya fito da ita,ga mamakinsa sai yaga iya envelop d’in ce kawai babu takardar da za a kai gidan Marayu, ya ajiye envelop d’in gefen sa ya juya wandon d’aya b’arin yana duba d’aya aljihun,amma sai baiji komai ba,haka yai ta caje aljihun yana zazzagewa amma takarda tace d’aukeni in da ka ganni,ya cika da matsanancin mamaki,saboda shi dai ya san lokacin da Mummyn Hidaya ta ba shi takardun da kansa ya cusasu cikin aljihun sa,to ya akayi yaga d’aya bai ga d’aya ba,wannan takardar kuma ita ce jigon kai Hidaya gidan Marayu, idan babu takardar bai san ya ya zai yi ba,tunda bai san komai ba,bai da masaniya akan abin da ke cikin takardar balle yayi musu bayani da baki,bayani da baki ma ba zai gamsar ba.

Haka ya mik’e yayi ta binciken takardar amma Allah bai sa ya ganta ba,har gwiwar sa ta sare ya fara gajiya,ya zauna bakin gado ya dafe kansa cikin tunanin in da takardar ta yi kamar wata aljana,ya jima a zaune har bai san lokaci na ta tafiya ba,kawai sai jin sallamar Umma yayi a kansa.

Ya d’ago yana amsa wa idanuwan sa sun sauya kala,Umma taji gabanta ya fad’i ganinsa cikin wannan yanayin,da hanzari ta matso ta zauna gefen sa tana kamo hannunsa,cike da kulawa take ambatar.

“Lafiya kuwa Hamza?me ya faru ne tun d’azu ina jiranka?

Bai san lokacin da ya d’ora kansa kan kafad’ar Umman ba,ya saki Numfashi a hankali yayi magana.

” Umma na an samu matsala ne….

Ta d’ago kansa da sauri ta dubeshi,suka had’a idanu,ta ga duk ya wani marairaice,ta k’ura masa ido tace.

“Matsala kuma?wace matsala kenan?”

Ya sunkuyar da kai ya fara magana cikin rauni kamar zai saka kuka.

“Wallahi Umma banga takardar da za a kai Hidaya gidan Marayu da ita ba,tun d’azu nake dubawa amma ban ci nasarar ganinta ba,na rasa in da ta yi,kuma fa a aljihuna na sakata,kuma wallahi Umma ita ce shaidar da za mu kaita da ita,idan babu ba zai yiwu mu kai Hidaya gidan Marayu ba”

Umma na shirin magana suka ji Hidaya a bayansu na ambatar.

“Ya Hamza ni za a kai gidan Marayu?Umma ina ne gidan Marayu kuma …?”.

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA ASHIRIN DA BIYAR DA NA ASHIRIN DA SHIDA*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

 

A hanzarce suka waiwayo suna duban ta saboda basu san da zuwan ta ba,ta na tsaye bakin k’ofar jikinta jagab duk ta jik’e da Ruwan wanke wanke,jikinta na D’an rawa kad’an alamar ta fara jin sanyi,Umma ta dubeta ta k’ak’aro murmushi tace.

“Yanzu haa kika jik’a jikinki da ruwa Hidaya?to muje na sauya miki kaya saboda naji ana cewa ba a son masu irin lalurarki suna zama da jik’ak’k’un kaya”

Mik’ewa tayi tana kama hannun Hidayan za su fice,ta waiwayo ta dubi Hamza da ke zaune kansa a k’asa tace.

“Ka dai cigaba da dubawa ko za a dace a ganta,bari na sauyawa Hidayan kayan jikinta”

Ya jijjiga kai ba tare da yayi magana ba,kuma bai d’ago kansa ba,har suka fice Hidaya na waiwayen sa tana kallon sa.

Kafin Umma ta sauyawa Hidaya kaya tuni Hamza ya birkita d’akin sa Neman takarda,amma ko mai kalarta bai gani ba balle ita,duk ya gigice ya rasa ya zai yi ma,haka ya tattara ya hak’ura ya nufi cikin gida parlour’n Umma domin a san mafita.

Yana sallama Hidaya na zurowa da gudu tana nuna masa kayan da aka sauya mata,tana tambayar sa wai tayi kyau?yayi malalacin murmushi yana jinjina mata yace.

“Kin yi kyau K’anwata sosai”

Ta fara murna tana biye da shi har ya zauna kan kujera,ta fara k’ok’arin hayewa cinyar sa,da hanzari ya hanata hakan ya nuna mata kusa da shi yace.

“Zauna a nan kinji Hidaya”

Ta yi shiru tana duban sa k’uri da idanu,ya sake magana babu walwala a kan fuskar sa.

“Ki zauna a nan nace ko”

Ta tafi a hankali ta zauna,tayi kasak’e duk ranta a jagule ganin babu fara’a a fuskar Ya Hamzan ta,ganin yadda tayi shiru har da D’an tagumin ta sai yayi murmushi ya kalleta yace.

“Hidaya…..

Ta d’ago ta kalleshi tana k’ifk’ifta idanuwa,ya karya wuya yace.

” Fushi kika yi da yayan ki ne?”

Girgiza kai tayi ,Hamza yace.

“To D’an yi murmushi na gani mana”

Aikuwa sai ta saki murmushi mai kyau da ya sa Hamza cikin nishad’i,har bai san lokacin da ya zaro wayar sa a aljihu ya k’yasa mata photo ba,ya d’auketa wajen kala shida,ita kam Hidaya sai canja salo take tana wani iyayi,shi kuma yana dariya.

A lokacin Umma ta fito daga bedroom tana kallon su,sun shagala cikin nishad’i sosai,sai da tayi gyaran murya sannan suka Ankara,Hidaya da tafi da gudu da wayar Hamza a hannun ta ta na nunawa Umma hotunan da ya d’auketa ,Umma ta karb’a ta na dariya tace.

“Iyen ba,Aikuwa y’ammatan nawa tayi kyau sosai”

Ta k’yalk’yale da dariya ta na zama a jikin Umma bayan Umman ta zauna,Hidaya ta maida hankalin ta kan wayar tana wasa,Umma kuma ta dubi Hamza tace.

“Ka ga takardar kuwa?”

Ya girgiza kai cike da damuwa yace.

“Banganta ba Umma,na yi iya duba amma ko k’yallinta ban gani ba,abin ya d’aure min kai sosai”

Umma ta yi shiru,sai can tace.

“To yanzu ya za a yi kenan Hamza….

Ya jefa hannuwa yace.

” Ban sani ba Umma,wallahi ni duk kaina ya kulle ma”

Tayi ajiyar zuciya da tunani iri iri a ranta,tun jiya take addu’ar Allah yasa Hidaya ta zauna tare da su,Hamza ne kad’ai rabon da ta samu a duniyar ta,Wanda ya kasance maraya tun yana cikinta D’an wata biyar,Hamza ne komai na ta kamar yadda ta zama ita ce komai na sa,Ruwa da iska,zafi da sanyi,bazara da damuna duk suna tare,komai shi yake mata,idan bata da lafiya shine mai lura da ita,wani abin ma bai kamata yayi mata ba a matsayin sa na namiji,duk da kasancewar sa D’an cikin ta,amma wani abin dole sai Y’ar uwarta mace,duk wata mace tana buk’atar Y’ar uwa mace ko d’iya mace domin tallafawa juna a bisa wasu larurorin,shiyasa taji a ranta tana buk’atar zaman Hidaya tare da su,haka nan tana tausayawa Hidayan a bisa rayuwar da ta tsinci kanta,ga lalura ga kuma rashin dangi,kulawar da za a bata a gidan Marayu ba Lallai ta gamsheta ba,duk da su d’in ma ba wani k’arfi ne da su ba,amma tana tunanin da taimakon Allah za su iya rik’e Hidayan domin ta rayu da su,bata sani ba ko Allah ne yayi nufin amsa mata rok’onta shiyasa aka nemi takardar aka rasa,wadda kuma tilas sai da ita za a kai Hidayan gidan Marayun,ba tare da b’ata lokaci ba kawai Umma taji Zuciyar ta ta yarje mata su zauna da Hidaya har zuwa lokacin da Allah zai bayyana gaskiya akan lamarin ta.

Hamza dai yana ta kallon Umma ganin ta yi shiru bata ce komai ba,hakan ya sa yayi magana cikin sanyin murya.

“Umma kinyi shiru baki ce komai ba,yanzu ya za mu yi kenan? Ko komawa kangon zan yi ma gani ko har yanzu Mummyn Hidayan tana wajen?

Umma ta sauke numfashi ta dubi Hamza,cikin karsashi tace masa.

” Ni fa ina ganin Allah yayi nufin bamu kyautar Hidaya ne domin mu rayu tare da ita na wani lokaci,abin da nake ganin zai fi kawai shine,mu rik’e Hidaya mu zauna tare da ita a gidan nan,duk ma Wanda ya tambayeni a kanta zan shaida masa cewar Y’ar k’anwata ce aka bani ita daga nesa domin na raineta,tunda dai bani da wasu y’an uwa a kusa sai na nesa,ko ya ya ma gani…?”

A razane Hamza ya d’aga kai ya dubi Umma jin maganganun ta,Abubuwa biyu suka had’e masa lokaci guda,tsananin fargaba!da kuma mad’aukakin farinciki!

Ya dad’e a haka Zuciyar sa na kai komo bisa ga zab’in Umma,cikar farincikin sa shine zaman Hidaya tare da su,amma kuma Alk’awari ya d’aukar wa mahaifiyarta cewa zai kai ta gidan Marayu,bai sani ba ko akwai babban dalilin da ya sa ta nemi hakan gareshi,idan har bai kai ta ba ya karya alk’awari kenan?shikenan ya shiga sahun munafukai?to amma idan maslaha da kyakkyawar rayuwa yake nemawa Hidaya an ya ta cancanta da za ma gidan Marayu?wad’annan tunane tunane su ne suka damu ran Hamza har ya ji kansa ya fara ciwo,amma da ya tuna Allah mai bada mafita ne akan komai sai ya sauk’ak’awa ruhin sa,yayi wa Umman sa kyakkyawan kalami ta hanyar dubanta da cewa.

“Hanzarin ki mai kyau ne Umma na ,Sai dai akwai k’alubale tattare da hakan,abin da nake gani zan yi istihara akan lamarin,duk abin da yafi alkairi Allah ya zab’ar mana,idan zaman ta alkairi ne a garemu da ita kanta Allah ya tabbatar, idan kuma babu alkairi Allah ya musanya da mafi alkairi”

Umma ta ji dad’in abin da Hamza yace,cikin farinciki tace.

“Ameen ya Allah Hamza,zab’in Allah kam shine zab’i mai kyau ba son zuciyoyin mu ba”

Da wannan suka rufe maganar.

 

 

**************

Kwanan Hidaya Uku a gidan,tuni ta sake tamkar gidan su tana walwala sosai,yaran layin da suke shigowa har sun zama k’awayen ta,mamakin su Umma bai wuce yadda Hidaya ta fara mantawa da zancen Mummyn ta ba,ba ta cika tunawa da ita ba.

Hidaya Yarinya ce mai hankali da nutsuwa,sai dai akwai yawan shagwab’a da son wasa,wani zubin Hamza har gajiya yake da wasan ta,in dai yana gidan
bata da abokin wasa sai shi,wani zubin ficewar sa yake ya gudu ya bar mata gidan,idan ya dawo kuwa ta dinga shagwab’a kenan har da kuka,sai ya sha aikin lallashi tukun take shiru.

A tsawon wannan kwanakin da Umma da Hamza suna ta addu’a da istihara,babu abin da zuciyoyin su ke kai irin k’ara jin son zaman Hidaya tare da su,shiyasa kawai suka barwa ransu cewar su cigaba da rik’on Hidaya a wajen su.

Umma bata da yara,amma kuma gidan ta akwai farinjinin yara ko Dan Hamza yana da son yara,kuma ita ma Umman haka,musamman da yake ta iya kitso,yara suna shigowa tana yi musu musamman na layin,kuma bata karb’ar kud’i,domin Umma akwai karamci da mutumci,hakan yasa take zaune da mutane lafiya a unguwar,kuma tana da jarinta a Hannu Wanda Khaleel ya bata,tana saro atamfofi da laces da dai kayan mata duk tana siyarwa,gidajen masu kud’in layin duk suna siyan kayan ta,hakan yasa asirin su yake a rufe.

Satin Hidaya biyu a gidan idan ka ganta za ka d’auka tayi shekara ne,matuk’ar Sabo suka yi ta yadda suke ganin ba za su iya rabuwa da ita ba,a lokacin Hamza ya samu Umma da zancen yana so ya nemarwa Hidaya School wadda za ta dinga zuwa saboda cigaban karatun ta,saboda ya lura yarinyar tana da k’ok’ari sosai,kuma kullum sai tayi masa maganar makaranta,musamman idan taga ya shirya zai tafi ta sa makarantar,lokacin Hamza yana jami’a level 100 yana karantar mass communication.

Lokacin da ya samu Umma a parlour’nta tana zaune tana ware wasu atamfofi da zata aiki Hamza ya kai mata tasha,za a tura su gurin wata Costomer d’in ta a Gombe state,sai da ta kammala sauraren sa sannan ta amsa masa da cewa.

“Hakan na da kyau,sai a nemi makaranta mai kyau a sakata,amma Mara nisa wadda za ta iya zuwa da kanta ta dawo da kanta ko?”

Ya jijjiga kai yana taya ta zura kayan a Leda.

Ta sake magana tace.

“To yanzu nawa kake gani zai isa ayi hidimar karatun ta da su?in yaso sai na ware kud’in na baka,domin babu laifi watan nan na samu riba da yawa Hamza”

Yayi murmushi yace.

“Alhamdulillah haka akeso Umma,Allah ya k’ara sakawa kasuwancin ki albarka,amma ki bar kud’in ki zan yi wa Hidaya komai insha Allah”

Ta tsare shi da idanu da kallon tuhuma tace.

“Me yasa baka son na dinga yiwa Hidaya Hidima ne?komai nace zan mata sai kace kai za ka yi?a sanina kai d’in karatu kake ba wata Sana’a ba,har yaushe za ka iya d’aukar d’awainiyar wani a kanka?”

Da sauri ya tare ta cikin tausasawa.

“Ba haka bane Umma na,bana son na yi ta saka ki kashe kud’i ne akan abin da bakiji ba baki gani ba,ni ne na d’auko Hidaya na kawota gidan nan,ni ya kamata naji da d’awainiyar ta kar na d’ora miki,amma kiyi hak’uri don Allah Umma”

Tayi murmushi tace.

“Ai duk abin da ka kawo tamkar ni ce na kawo Hamza,ka daina kokonto akan hakan,ni Hidaya jin ta nake a raina tamkar kai, babu abin da babu zan mata ba”

“Na gode Umma na” ya fad’i hakan cikin k’ayatacciyar fara’a da ta fito da kyawunsa fili,Sannan yace da Umman.

“Ina Hidayan ne na ji ta shiru?”

Ta nuna masa bedroom tana cewa.

“Tana ciki tana kwalliya,wai yau Hansa’u take partyn Y’ar tsanarta,shine take ta kwalliya wai don tafi kowa kyau….

Hamza yayi dariya yana mik’ewa da fad’in.

” Lallai Ashe yau za mu sha party kenan?bari na lek’a na gano kwalliyar y’ammata”

Umma tayi dariya tana cigaba da had’a kayan gaban ta,shi kuma ya nufi bedroom d’in Umma ya d’aga labulen yana sallama.

Can kan kujerar gaban dressing mirror ya hangota zaune tana kwalliya,ta damb’ara powder duk tayi dabbara dabbara,ga jambaki duk ya b’ata mata gefen baki,kwalli kuwa har k’asan idanuwa da gefe wai tayi hawayen masoya,tun shigowar sa bata lura da shi ba ta na ta sake lamb’ata Abubuwa a fuskar ta,kallon fuskar ta yake yi yana k’unshe dariya,kamar wadda za ta dandali gad’a,bai san lokacin da dariyar ta sub’uce masa ba,k’arar dariyar sa yasa ta waigowa a hanzar ce……..!

 

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI DA NA ASHIRIN DA TAKWAS*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

 

 

Ta sakar masa murmushi a sanda ya k’araso gaban ta ya tsaya yana dubanta,shi kam dariya yake yi,bata gane dariyar da yake ba shiyasa ta tambaye shi cikin zumud’i tace.

“Ya Hamza ka ga kwalliyata,na yi kyau ko?”

Ya girgiza mata kai alamar bata yi kyau ba,sai ta kwab’e fuska za ta yi shagwab’ar da ta saba tace.

“Kalla fa ka gani Ya Hamza,Allah kuwa duk sai na fi su Hansa’u da Maryam kyau,shine za ka ce wai banyi kyau ba?

Yayi murmushi cikin kulawa yace.

” To ai gaskiya na fad’a miki K’anwata,in dai ba so kike nayi k’arya ba to gaskiya ba ki yi kyau ba,wannan abin duk ya b’ata miki fuska fa”

Ta fara turo baki tana buga k’afa wai ita Lallai sai yace ta yi kyau,yayi dariya yace “wai so kike nayi k’arya ne Hidaya”

Ta kamo hannunsa ta rik’e,ta d’aga kanta tana kallon fuskarsa saboda ya kere ta a tsawo sosai.

“Eh Ya Hamza,ni dai kayi k’arya kawai ka ce nayi kyau”

Da sauri yace.

“Subhanallah!ai k’arya babu kyau Hidaya,kullum an fi so mutum ya kasance akan gaskiyar sa tun yana yaro har zuwa girman sa kinji,K’arya zagin Allah ce,Sannan kuma Allah ya tsinewa mai k’arya,domin a Alk’ur’ani mai Girma Allah yace.

“فنجعل لعنت اللہ علی الکٰذ بین”

(Sannan kuma mu sanya tsinuwar Allah akan mak’aryata)

Duk wani aiki da za ka yi idan babu gaskiya da tsoran Allah a ciki to shirme ne Hidaya,ki daina k’ok’arin ganin duk abin da kike so sai kin samu ko da ta hanyar k’arya ne,domin ba zai amfaneki da komai ba daga duniya har Lahira ,gaskiya ita ce tushen dukkanin wani alkairi,gaskiya ita ke sawa bawa ya zama mai hak’uri a kan jarraba,mai godiya yayin samun ni’ima,mai gaggawar aikata alkairi,babu wata halayyar imani da za ta tabbata face sai da tabbatar gaskiya,shiyasa Allah ya umarci bayinsa muminai da jin tsoron sa,da kuma shiga cikin masu gaskiya,sai yace.

“یأیھا الذین ءامنوا اتقوا اللہ و کونوا مع الصٰدقین”

(Ya ku wad’anda suka ba da gaskiyar,ku ji tsoron Allah,kuma ku zama tare da masu gaskiya).

Abin nufi masu gaskiya a imanininsu,da maganganun su,da ayyukansu,da alk’awuransu.

Dan haka a ko da yaushe ki kasance mai fad’in gaskiya da tsayawa a kanta Hidaya,za ki ci riba duniya da Lahira.

Duk da tana da k’arancin shekaru amma maganganun sa sun shigeta,tana kallon sa duk jikinta yayi sanyi tayi magana.

“To Ya Hamza na daina,zan dinga fad’an gaskiya a ko ina ne,kuma na daina k’arya,idan naga wani ma yayi zance ya daina Allah ya hana kuma baya so”

Ganin ta fahimceshi sai yaji dad’i,ya saka mata albarka,sannan yace ta je toilet ta wanke fuskarta,da sauri ta tafi ta wanko kuwa,yana tsaye har ta dawo tana goge fuskar,ya kalleta yaga tayi masa wani kyawu,shi sai yaga ma kamar a kwanakin an dad’a mata wani kyau ne.

Da ta saka shi gaba da rigima tilas shi ya shafa mata powder har da kwalli,yasa mata jambaki kad’an,sai gata ta fito ras,sai da ya kammala mata sai ta tsiro da tsirfa wai ya tsaya ya d’aura mata zanin ta,nan da nan yayi fuska yace.

“Kije Umma ta d’aura miki,babu kyau fa Namiji ya dinga ganin jikin mace,Allah ya haka hakan Hidaya”

Ta bishi da kallo tana cewa.

“To ai kai yayana ne”

Ya amsa mata yana mik’ewa tsaye.

“Duk da hakan,ai ni ba muharramin ki ba ne”

Da sauri tace.

“Muharrami?Ya Hamza menene muharrami kuma?”

Yayi gaba yana cewa.
“Zan gaya miki ko menene,amma sai kin k’ara girma kinji”

Kafin ma tayi wata maganar har ya fice daga bedroom d’in.

Kafin Hidaya ta gama shirin partyn Y’ar tsana ya fice daga gidan zuwa tasha kai sak’on Umma….

Kusan awa d’aya da rabi ya d’auka kafin ya dawo,da yake bayan sallar la’asar ya fita,lokacin da ya dawo kusan k’arfe shida na magariba yayi.

A k’ofar gida ya ci karo da Hidaya da zugar k’awayen ta kusan guda biyar an gama party,tana ganin sa ta kama murna tana nuna wa k’awayen ta shi,duk suka nufo shi suna masa sannu da zuwa,ya amsa musu da murmushi akan fuskarsa sa,ya wuce gaba suka bishi yuuu a baya har cikin gidan,Umma na zaune tana gyara salak za ta yanka ta gansu sun shigo,tayi murmushi a ranta tana cewa “Hamza mai jama’a kenan!

Hidaya da k’awayen ta suka zagaye Umma suna taya ta had’a salat suna bata tana yankawa,yayin da Hamza ke zaune daga gefe yana yiwa Umma bayanin Aiken da tayi masa,sai da ya kammala take ce masa.

” Ni yau sai naga ka dad’e baka dawo ba,ko dai baka samu mota da wuri bane?Insha Allahu dai na kusa siya maka mashin kai ma ka huta haka”

Yayi murmushi yana Sosa kunnensa jin yana k’aik’ayi,ya kalli Hidaya yace ta d’auko masa abin Sosa kunne a d’akin Umma na sa ya k’are,da hanzari ta tashi ta shige d’aki,shi kuma ya mai da hankalin sa kan Umma yana bata amsa da cewa.

“Ba rashin mota ba ne Umma,na dai biya kangon nanne ko zan ci karo da …….

Fitowar Hidaya ta sa yayi shiru,taje har gabansa ta mik’a masa abin da ya aiketa,ya karb’a yana goge kunnen sa da babu wata daud’a a jiki saboda yawan tsaftar sa,tana tsaye a gabansa da alamun da magana a bakin ta,ya dubeta yana cewa.

” Ya dai Hidaya?akwai wani Abu ne?

Tayi murmushi sannan ta zura hannun ta cikin Hijabin ta ta fito da wata farar Leda ta mik’a masa,ya kai Hannu ya karb’a yana kallo yace “menene wannan?

Kanta a k’asa tana Y’ar dariya tace.

” Biscuit da lemo ne da aka bani na partyn Y’ar tsana,shine na kawo maka nawa ka ci”

Sai yaji k’aunarta ta kuma ninkuwa a ransa,Hidaya duk abin da ta ci ko baya nan sai ta rage masa,wataran ma bata iya cin komai muddin baya nan sai ya dawo,Yanzu ga k’awayen ta nan da suka yi partyn tare kowa ya cinye nasa kayan partyn,amma ita ta kasa cin nata ta ajiye masa saboda k’auna,cikin farinciki babu gwasalewa yace.

“To Na gode Hidaya na,bari mu ci tare ko ?sai mu sanwa Umma”

Ta gyad’a kai tana dariya,yayin da Umma ke cewa “Ah ah ni dai na yafe ,ku ci abin ku”

Ya farke ledar biscuit d’in ya zaro guda d’aya yayi bisimillah ya gutsira,tana ta kallonsa bakin ta kamar gonar auduga don fara’a,ragowar da ya gutsira ya kai mata bakin ta,ta bud’e bakin ya saka mata a hankali ta fara taunawa tana kad’a kai alamar dad’i,sannan ita ma ta d’auko ta mik’a masa bakin sa,ya karb’a ya tauna shi ma yana kad’a kai tamkar yadda tayi,ta fashe da dariya tana nunawa k’awayen ta yadda yake yi,su ma suka fara dariya suna kallon sa.

Sai lokacin Umma tayi magana tana cewa k’awayen Hidaya su tashi su tafi gida magariba ta kusa,kowacce tayi sallah sannan su dawo domin ayi karatu,daman kullum bayan magariba Hamza yana Tara yaran mak’ota a tsakar Gidan yana koya musu karatu ko tarihin annabawa da sahhabai.

Duk suka tashi suka tafi,yayin da Hidaya tayi gefe ta fara dakan yajin barkono da Umma ta sakata,Wanda za a ci wake da shinkafa da shi,sai lokacin Umma ke bawa Hamza amsar maganar da ya fara d’azu cewar.

“Wato har yanzu baka hak’ura da zuwa kangon nan ba ko Hamza?in fa ba wani ikon Allah ba da wuya ka sake ganin mahaifiyar Hidaya a wajen nan,kana wahalar da kanka ne kawai,gara ma ka hak’ura duk lokacin da Allah ya nufa za a ganta to babu makawa sai an ganta”

Hankalin sa na kan Hidaya da ke dakan barkono tana y’an wak’e wak’en ta,ya d’auke kallonsa ya mayar kan Umma yana sauke ajiyar zuciya yace.

“To shikenan Umma,Allah ya tabbatar da alkairi,d’azu naji kina maganar siyen mashin ko?kamar kin san shekaran jiyan nan muka gama magana da Khaleel,wai shi da mota zai siya min a satin nan,na nuna ban amince ba shine yayi fushi da ni har yau ya k’i nema na a waya,Idan na kira shi ma baya amsawa”

Umma ta zaro idanu da fad’in.

“Mota kuma?wace irin mota ni Maimunatu ana zaune k’alau?

 

Ya sunkuyar da kai k’asa cikin sanyin murya yace.

“Haka dai yace Umma,ina ta cewa ah ah ya bari zuwa nan gaba ma amma ya k’i ganewa,shine yayi fushi dani”

Umma ta sauke Numfashi ta kira sunan sa.

“Hamza…..

Ya d’ago kansa ya amsa yana duban ta,ta k’ura masa ido tace.

” Ina fatan dai ba kai kake rok’an Khaleel akan yayi maka wani abin ba ko?Saboda ina tsoran yadda yake maka Hidima sosai,abubuwan da yake maka sun yi yawa fa”

Hankalin sa ya tashi jin maganar Umma,da sauri ya janyo kujerar da yake kai ya matso dab da ita ya kamo hannun ta ya rik’e,fuska cike da jimami ya fara magana.

“Umma na ai kin san hali na,kin san tarbiyyar da kika bani ina kanta ban kufce ba,wallahi ban tab’a rok’on Khaleel yayi min wani abin ba,sau da yawa ma yana min kyautar Abu nak’i karb’a,haka kuma yana sawa yayi fushi da ni,kullum yana cemin wai duk abin da ya mallaka kamar nawa ne,amma ban tab’a yardar wa zuciyata hakan ba,don Allah Umma kar zuciyar ki ta zargi D’an ta da rok’o”

Sai Umma taji tausayin Hamza,hakan yasa tayi murmushi ta shafa kansa tace.

 

“Ba zargin ka nake ba,na fad’a ne dai don ka kiyaye Hamza,bana son ka zama mai kwad’ayin abin hannun mutane,hakan na jawo zubewar k’imar mutum,Khaleel kuma ka barni da shi,duk lokacin da ya sakko ya kira ka a waya ka bani shi za mu yi magana,ya kamata ya dinga sassauta Abubuwa kud’in da yake kashe maka sunyi yawa,kuma na san cewar duk ba da sanin mahaifinsa yake ba,saboda yadda Mahaifin sa ya tsani talakawa baya son D’an sa na alak’a da su,ka duba yadda dole Sai da ya raba Khaleel da k’asar nan duk don ya raba abotarku Hamza,na tabbatar idan ya san Khaleel yana yi maka Hidima to da matsala,gara ya dinga sassauta wa yayi wa Mahaifin sa biyayya ko ba haka ba?”

Yayi ajiyar zuciya yana kallon Umma yace.

“Hakane Umma,ni kaina abin da kullum nake nuna masa kenan,amma ya k’i ganewa,Sai ya dinga cemin wai ni jininsa ne,daddyn sa bai isa ya raba mu ba,Umma wallahi ba cin ina yiwa Khaleel nasiha akan kyautata iyaye da jin maganar su da tuni ya fand’arewa daddyn sa,kuma Dan yayi sa a daddyn na sa yana matuk’ar sonsa ne ma…….

Bai k’arasa magana ba suka ji Hidaya ta k’wallara ihu da k’arfi,saamakon yajin da ya shigar mata ido tana dakan Barkono…..

A rikice suka mik’e suka yi kanta,tana niyyar fad’uwa k’asa Hamza ya tarota ta fad’o jikinsa,ganin yadda take yi azaba ta ishe ta sai ya kuma rikicewa ya k’ank’ameta,Umma sai salati take yi,da sauri ta nufi kitchen Dan lalubo gishirin da za ta lasa mata a baki ko idon zai bud’e,shi kam Hamza har ya fara k’wallar tausayin Hidaya ganin yadda take tsalle a jikinsa idanuwa a manne…….!

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA ASHIRIN DA TARA DA NA TALATIN*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

Sai da Umma ta fito da gishiri ta lasa mata a baki sannan ta fara mommotsa idanuwan tana san bud’ewa,da ta bud’e sai ta rufe ta k’ara fasa kuka,Hamza ya sake rud’ewa yana cewa Umma.

“Umma ko mu tafi asibiti ne?kar yarinyar nan ta makance fa”

Dariya ya bawa Umma,amma ta kanne tace.

“Wane irin Asibiti kuma Hamza?Dan kawai yaji ya shiga idanunta sai a ta fi asibiti,yanzu zai ware bari ka gani”

Yayi shiru yana ta kallon fuskar Hidaya har tayi ja,ya kira sunan ta a hankali.

“Hidaya….bud’e idonki kinji”

Cikin muryar shagwab’a tace.

“Idona zai cire ne Ya Hamza idan na bud’e”

Ya girgiza kai tamkar tana ganinsa yace.

“Ba zai cire ba,kiyi bismillah ki bud’e a hankali,zan sake bushe miki ma”

A hankali ta fara bud’ewa da rufewa har suka bud’e tas,abin tausayi duk sun yi jajawur sunyi k’ananu,ya sake jin tausayin ta ya tsirga masa,bakinsa ya sa ya bushe mata idanuwan yana ta jera mata sannu saboda tausayi.

Umma kam sai lokacin tayi dariya tana duban Hidaya tace.

“Raguwa kawai!don D’an yaji ya shigar miki ido kike wannan kwazozoton,ke fa macece Hidaya,in zaki koyi juriya da dauriya ma ki koya,nan gaba ma har girki za ki yi,zafin turiri ma kad’ai ya isheki,gashi in kika girma za ki yi Aure har ki haihu,dole ki zama jaruma Yarinya”

Hidaya dai tai shiru har lokacin bata gama dawowa dai dai ba,sai Hamza ne ya maida wa Umma amsa da cewa.

“Umma barkono ne fa ya shige mata ido,ai dole tayi kuka,ai tayi jarumta ma Dan idan nine sumewa ma zan yi Umma”

“Amma kuwa da anji jiki,yaji ya shiga ido an suma” Umma ta fad’a tana dariya,haka tai ta jan Hidaya da wasa Hamza na tare mata,Hidaya kam saboda Haushin yajin ko abincin cewa tayi ba zata ci ba,Hamza ya biye mata shi ma ya k’i ci,da daddaren ya fita ya sayo musu fura da Nama suka ci,Umma tana kallon su ta fita sabgar su,ta had’a abincin na su ta aika da shi mak’ota saboda kar ya kwana ya lalace…..

 

 

 

*************

Bayan sati d’aya duk wani shirye shiryen kai Hidaya makaranta ya kammala,tana ta murna da tsalle za a sakata makaranta,har da islamiyya Hamza ya nemar mata,babu b’ata lokaci ta soma zuwa cikin nasara da Sa’a.

Har zuwa wannan lokacin kuma cikin ikon Allah ciwon Hidaya bai tab’a tashi ba,don su har mantawa suke yi wai tana da lalurar sikila ma,Hidaya ta murje ta dad’a wani sihirtaccen kyau da girma,kamar ba Y’ar shekara Tara ba,sai dai bata k’i ba sai tsawo da murjewar jiki.

Tana jin dad’in karatun ta sosai,in da aka kaita primary 5 saboda k’ok’arinta,haka nan kullum a gida Hamza yana mata bitar karatu sosai tana kuma ganewa.

Shak’uwar su kuwa sai abin da yayi gaba,Hamza na son Hidaya ,Hidaya na son Ya Hamza,komai tare suke yi,suyi wanke wanke tare,suyi shara tare,Aiken Umma tare suke zuwa,har wanki wataran idan Hamza na yi zagewa take ta tayashi,tunda bai fiye kai wanki ba,rana yake warewa ya fitar da kayansa da na Umma da na Hidaya duk ya wanke.

Kowa a unguwar mamakin shak’uwar Hamza da Hidaya a ke,duk kuma Wanda zai tambayi Umma akan Hidaya ta kan sanarda shi cewar d’iyar k’anwarta ce da ke kano,shine aka kawota nan Kaduna ta zauna tare da su,y’an uwan Umma kuma da ke kano da suka ga Hidaya sai Umma tace musu ai Hidayan d’iyar k’anin marigayi Mahaifin Hamza ce,ta d’akko ta ne saboda tana son d’iya mace kusa da ita,har suka dinga yi mata tsiya da cewa to in dai Hakane tayi Aure mana,za ta iya haihuwar yara da yawa ma ba mace d’aya ba,ita kam Umma tsoron Aure take yi tunda mijinta ya rasu tana da k’arancin shekaru har yau bata yi wani Auren ba,haka nan Kaduna ta rik’eta ta kasa komawa asalin garinta wato kano,tana ji a ranta ko bata yi Aure ba za ta iya kare kanta,zaman ta da D’an ta k’waya d’aya JAL mai albarka ya fiye mata y’ay’a dubu marasa Albarka.

Da yake Hidaya ta kasance mai sakin fuska da fara’a kamar Hamza,sai tayi farinjini,ko ina sonta ake yi,kulawar da Hamza yake bata kuwa bata da misali,komai ya samu Hidaya,duk abin da ya gani ya burgeshi zai siya mata,sai ya koma hidimar Hidaya kawai,ya daina yiwa kansa duk wata Hidima,sai dai yayi wa Umma da Hidaya.

Abu d’aya ke matuk’ar damun Hamza,shine rashin jin Khaleel a waya,tun yana Neman sa ba a d’agawa har Idan ya kira sai a ce a kashe take,duk ya zama tamkar Mara lafiya bashi da walwala,hatta Hidaya ta fuskanci hakan,saboda baya sakewa suyi hira da wasa da karatu kamar da,shiyasa ita ma ta shiga cikin damuwa ta daina walwala sosai,Umma tana lura da su,sai dai bata ce musu kanzil ba,tana jira su bayyana mata damuwar da ke ransu da kansu, ne,musamman Hamza da ta lura har wata rama ya D’an yi……

 

 

*****************

Yana zaune a parlour’n Umma misalin k’arfe takwas da minti Ashirin na ranar Alhamis,ya zabga tagumi ya fad’a cikin tunani,babu abin da yake son ji sai muryar Khaleel,wane irin fushi Khaleel ya d’auka da shi Hakane?ko yayi fushi da shi baya iya kwana biyu bai nemeshi sun shirya ba,amma yanzu kusan sati uku ko hud’u ko muryar juna basu ji ba,an ya kuwa lafiya?ya tabbatar idan da lafiya Khaleel ba zai iya kaiwa wannan lokacin bai neme shi ba,duk kuwa da laifin da yake ganin yayi masa.

Hidaya ta d’aga labulen d’akin tayi sallama,da plate a hannun ta Wanda ke cike taf da abinci,shinkafa da miya da salad har da nama,ta zo ta dire a gabansa,ta bishi da kallo tana cewa.

“Ya Hamza ga abincin mu sauko mu ci”

Ya girgiza kai Yana gyara zama yace.

“Ki ci kawai K’anwata,ni bana jin yunwa ba zan iya ci ba”

Ta yi shiru tana duban sa ganin ya shareta ya d’aga kan sa sama ko dubanta bai sake yi ba,ganin haka ita ma sai taji abincin ya fice mata a rai,daman kuma ranar duk bata jin dad’in jikinta .

Umma ce ta shigo parlour’n,sai ta tarar da su kowa ya ja gefe ya zuba tagumi,ga abincin ta anyi gefe da shi alamar ba za a ci ba,ta kama hab’a tana salati sannan ta dubesu tace.

“Wai ku kwana biyun nan lafiyar ku kuwa?me yake faruwa ne da kuke cikin damuwa haka?na zuba muku ido ne daman naga iya gudun ruwanku,to dai naga tabbas abin naku azimun ne,haka kawai kun d’auki damuwa kun d’orawa ranku,idan d’aya na cikin damuwa sai d’ayan ma ya shiga damuwa,haka ake rayuwar duniya kenan?kai Hamza bud’e baki kayi min bayanin rashin walwalarka ,gashi nan har ita ma k’anwaraka ka sakata cikin rashin walwala…

Maganarta ta katse saboda ganin Hawaye a idanuwan Hamza,ta zaro idanu cikin tashin hankali tace.

” kuka fa kake Hamza?wai menene ya faru ne da na za ka bud’e baki ka gaya min ba?

Hannuwan Hidaya kawai yaji a fuskarsa tana share masa hawaye,yayin da na ta idanun suka cicciko sosai da hawaye,suka yi wani irin k’yalli suna shining, ya kautar da kansa daga gareta ya dubi Umma yace.

“Umma Khaleel……

Sai yayi shiru ya duk’ar da kai k’asa Zuciyar sa na harbawa.

Umma tace.

” Me ya faru da khaleel d’in…?

Yayi ajiyar zuciya,cikin rauni ya soma magana.

“Umma tun ranar da na fad’a miki yayi fushi da ni akan siyen mota har yanzu bai k’ara nemana ba,idan na kira wayar sa bana samu,ban san halin da yake ciki ba Umma,Zuciyata kullum cike da fargaba da tsoro,bana son b’ata masa rai saboda kin san lalurar sa shi ma bata son b’acin rai,ina son sanin halin da Khaleel yake ciki Umma,da ina da hali zan shirya ne na ta fi England domin gano halin da yake ciki,Umma ki tayani addu’a Allah yasa Khaleel Yana cikin k’oshin lafiya”

Ita kanta Umma sai da taji ba dad’i,domin tayi tunanin tuni sun shirya suna waya kuma,tabbas dole Hamza ya damu,domin bata tab’a ganin abokan da suka shak’u da juna kamar Hamza da Khaleel ba,bata manta ranar rabuwar su har suma Khaleel yayi don damuwa,Hamza kam yafi wata biyu kafin ya dawo nutsuwarsa normal,tarihin abotar Hamza da Khaleel babba ce,Wanda Abubuwa suka faru a tsakani da bata son tunawa da su,Allah ne yake rik’e da amincin su har yanzu,amincin da babbar katanga ta so ruwa shi tun suna yara,amma Allah bai nufa ba,ba kuma wata Katanga ba ce illa Mahaifin Khaleel.

Umma ta sauke numfashi ta dawo daga tunanin da Zuciyar ta ta fad’a,nan da nan ta shiga bawa Hamza baki tana fad’in.

“Kayi hak’uri ,insha Allahu babu wani abin da zai faru da Khaleel sai Alkairi,ka dinga yin addu’a in Allah ya yarda a kurkusa za ka ji ya neme ka Hamza,damuwar bata da amfani,sai ka jawowa kanka wata lalurar,kasa Allah a ranka ka dogara da shi zai isar maka kaji”

Ya jijjiga kai hawaye na k’ok’arin zubo wa da sauri ya mayar da su Dan kar Umma ta gani,babu Wanda ya san adadin yawan damuwar da yake ciki,amma zai dage da addu’a akan duk in da Khaleel yake Allah ya tsare masa shi.

Ya juya da nufin kallon Hidaya sai yaga tana hawaye,da hanzari ya rik’o hannun ta yana tambayar ta me ya saka ta kuka,sai kuma yaji hannun ta da d’umi,langab’ewa tayi a jikinsa ta fara murk’ususu tana rik’e ciki wai cikinta da bayan ta na ciwo.

Hankalin Umma da Hamza yayi matuk’ar tashi ganin yadda Hidaya ke malelekuwa,can ta fara wani k’udundunewa tana kukan ciwon k’afa,idan tace nan na ciwo sai tace can na ciwo,sai ga Hamza ya rikice da kukan tausayin Hidaya,musamman da yaji cikin kuka tana ta kiran sunan sa tana cewa.

“Ya Hamza ka taimaka min zan mutu !Ya Hamza cikin!bayana!k’afana!k’irjina!duka jikina ciwo Ya Hamza,wayyo Allah kace musu su daina buga min k’arfe a jikina!Ya Hamza…..Ya Hamza…Ya Hamza ka cire min ciwon zan mutu…….

Kafin wani lokaci Hidaya ta fita daga hayyacinta tana shirin suma!tsananin tashin hankalin da Hamza ke ciki baya misaltuwa,hatta Umma sai da tayi hawayen tausayin ta,ganin abin ya ci tura da sauri ta shiga d’aki ta d’auko hijabin ta ta fito ta tarar da Hamza rungume da Hidaya a jikinsa sai faman Kuka yake yana fad’in.

” Hidaya na don Allah ki tashi ,ina ne yake miki ciwo,tashi mu gani …tashi kinji Hidaya….

Da hanzari Umma tace ya d’auko Hidaya su wuce asibiti,sungumarta yayi tamkar jaririya daman gata shafal,ya rungume ta suka fice daga Gidan a gigice ganin Hidaya na sassank’amewa.

Har bakin titi suka fita sannan suka samu mota,suna tafe amma Hamza gani yake direban baya sauri,sai lokacin yaji sha’awar ina ma yana da motar sa shi ma,da duk wannan jinkirin ba za su had’u da shi ba.

Kafin su isa Asibitin har Hidaya ta suma,ta sank’ame a k’irjin Hamza,shi kam saboda kuka har idanuwan sa sun kumbura,Umma ke lallashin sa tana ta zabga addu’a.

Da gudu likitocin suka amshi Hidaya da ke sume,aka fara bata taimakon gaggawa domin ta farfad’o,Hamza da Umma na tsaye cike da tararrabi,kansa ciwo yake tamkar ya tsage,damuwa tayi masa yawa,ga damuwar Hidaya ga damuwar Khaleel….

Sai wajen goman dare tukun likita yayi musu bayanin ana buk’atar jini za a sakawa Hidaya saboda jinin ta ya fara k’onewa,a lokacin ma likitan fad’a ya dinga yi musu kan an dad’e ba a bawa Hidayan maganin ta na sikila ba,to su gabad’aya ma sun manta Hidaya na da wani ciwo na sikila,saboda bai tab’a tashi ba sai yau,Umma dai ta rasa bakin magana,balle Hamza da yake cikin tsananin tashin hankali.

Yana jin jiri sosai amma haka yace a gwada jininsa a d’iba a sakawa Hidaya idan zai yiwu,haka aka yi kuwa,aka gwada Sai a ka ga yayi dai dai,Umma ta fita Harabar asibitin gun masu siye da siyarwa ta siyo masa Maltina da madara,da farko k’in sha yayi,sai da Umma ta rufe shi da fad’a sannan ya karb’a ya runtse ido ya sha,d’aci kawai yake ji a bakinsa.

An d’ebi jinin Hamza da gaggawa sannan aka jonawa Hidaya da ke ta faman bacci,wajen sha d’aya da rabi na dare Umma ta cewa Hamza.

“Ka koma gida ka kwanta kar abar Gidan ba kowa,ni sai na kwana da ita,gobe sai ka kawo mana abubuwan da za mu buk’ata da wurwuri kaji”

Hamza da ke rik’e da hannun Hidaya ya kalli Umma cike da damuwa yace.

“Umma ki barni na kwana da ita mana,idan ma na ta fi Gidan hankalina yana nan ba zai kwanta ba wallahi”

Umma tayi murmushi tace.

“Hamza jinyar mace ai sai mace,ka daure ka koma,Idan ka kasa baccin ka tashi kai ta salloli ka nemawa Hidaya sauk’in wannan lalura da duk wani mai fama da ita”

Ya mik’e ba don ya so ba,ya sunkuya yana kallon Hidaya da ta zabge lokaci guda kamar wadda ta shekara tana ciwo,addu’a yayi mata sosai hawaye na ciko idanuwan sa,a hankali ya mik’e yana shirin fita sai ga likita ya kawo takardar magungunan da ake buk’ata zuwa safiya,Hamza ya karb’a ya cewa Umma zai biya pharmacy ya siyo da safe ya tawo da su,yayi wa Umma sallama ya fice yana waiwayen Hidaya da ke baccin wahala.

Yana fita bakin Asibitin yaga wani pharmacy daga gefe suna shirin kullewa,da hanzari ya nufe su ya roki’i alfarmar su duba katin da aka bashi,me pharmacy d’in ganin Hamza a rud’e sai ya karb’a ya duba,magunguna ne guda bakwai,yace wa Hamza suna da guda biyar babu guda biyu,sai dai idan guda biyar d’in za a bashi in yaso yaje wani gun ya siyo guda biyun.

Hamza ya nemi ya san kud’in guda biyar d’in ,a kayi lissafi Naira dubu talatin da bakwai,ya karb’i katin yace masa zai zo da safe ya kawo kud’in sai ya karb’i maganin.

Ya jima kafin ya samu abin hawa saboda dare ya fara sosai,lokacin da yaje unguwar su tsit kowane gida a rufe,amma da yake akwai wutar NEPA ko ina da haske tarwai,bud’e Gidan yayi ya shiga sannan ya kulle.

Kai tsaye ya nufi d’akin sa duk jikinsa babu k’wari,abin duniya duk ya taru yayi masa yawa,babu abin da ke d’aga masa hankali idan ya tuna bashi da wasu kud’i sosai,dubu ashirin ce ta rage masa cikin account d’in sa,gashi baya son takurawa Umma ,D’an jarin nata ba wani yawa ne da shi ba,kuma duk a ciki ake hidimar Gidan,Umma bata yarda yayi wani abin da kansa,haka ya kwanta cikin tunane tunanen yadda zai samu kud’in maganin Hidaya,da yaga ya kasa bacci tilas ya mik’e ya fad’a toilet ya d’auro alwala ya fito ya kalli gabas.

Nafiloli ya dinga zabgawa,bayan ya idar ya dinga sharara addu’a,ya d’auki tsawon lokaci kafin ya D’an jingina yana lumshe idanuwan sa da carbi a hannunsa yana ja,shi dai bai wani samu bacci ba a Daren,hankalin sa kaf yana Asibiti tunanin Umma da Hidaya.

Yana idar da sallar Asuba a masallaci ya dawo gida da zummar harhad’a kayan tafiya asibiti,yana shiga d’akin sa yaji rurin wayarsa ,shi gabad’aya ma ya manta da ita,kamar ya share sai kuma ya isa ya d’auka yana dubawa.

Sunan da ya gani ya matuk’ar girgiza Zuciyar sa…take Hawaye ya ciko idanuwan sa a lokacin da ya kai wayar kunnen sa domin amsa kiran………!

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA TALATIN DA D’AYA DA NA TALATIN DA BIYU*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke jin muryar Khaleel na Sallama cikin sanyin murya,kasa amsawa yayi saboda hawayen da ya ratso fuskar sa,jikinsa har wata rawa rawa ya fara,daga can b’angaren Khallel yaji Hamza bai amsa masa sallamar sa ba,hakan ya sa yayi magana a hankali cikin k’ank’anuwar murya tamkar ta marasa lafiya.

“Aboki……kana tare da ni…..?

Hamza ya zame ya zauna bakin gado yana numfarfashi,duk da yaji matuk’ar farincikin jin muryar Khaleel amma cike yake da jin haushin k’in Neman sa da yayi,kuma shi ma idan ya nemeshi baya samun sa,da k’yar Hamza ya sauke numfashi yayi magana murya na rawa.

” Khaleel…! fushi nake da kai Khaleel”

Cikin rauni Khaleel yayi saurin tare shi da cewa.

“Bani da lafiya ne Aboki…..Kayi hak’uri..!?

Hamza ya lumshe idanu k’irjinsa na bugawa saboda tunowa da Hidaya da yayi,cikin alamun tausayawa yace.

” Laifinka ya k’aru kenan Khaleel,kayi fushi da ni kak’i fuskanta ta tsawon lokaci,kayi rashin lafiya ta tsawon kwanaki amma baka sanar da ni ba?ko da bana tare da kai ai zan iya yi maka addu’a Khaleel,me yasa hakan?ka san irin tashin hankalin da na shiga kuwa?ka san irin yadda zuciyata tayi rauni akan tunanin halin da kake ciki kuwa?ban ji dad’in abin da kayi min ba ko kad’an Khaleel, zuciyata tana fushi da kai ”

Khaleel ya marairaice murya ya fara bayani .

“Tsaya kaji Aboki,wallahi a ranar da muka yi sa’insa ni da kai akan siyen mota,ka san na kashe wayar cike da b’acin rai saboda ka k’i yarda,to bayan na kashe ne naji k’irjina yana zafi sosai saboda b’acin rai,shine fa ciwon Zuciya na ya motsa,sai James ne da muke zaune gida d’aya ya kwashe ni muka tafi Hospital saboda na fara fita hayyacina,kwana na biyu ban san in da kaina yake ba,a lokacin ne aka nemi daddy na a waya aka sanar da shi yazo hankalin sa a tashe,a nan daddy ya nemi sanin abin da ya tayar min da ciwon,shine James yake fad’a masa cewar bai sani ba,shi dai kawai ya ji sanda nake waya,daga nan kuma sai tari na da nishi na ya jiyo,shine ya kawo ni asibiti,a lokacin daddy ya karb’i wayata ya kasheta ma gabad’aya ya b’oyeta,shine dalilin da ko ka kira ba zaka samu ba,kuma da na dawo hayyacina babu yanda banyi da daddy ya bani na kira ka ba amma ya k’i,wai sai na warware gabad’aya,har kuka nayi masa saboda na san na barka cikin damuwa ba ka jin murya ta,amma daddy ya k’i fuskanta ta,yau kwanana goma da fitowa daga Hospital amma daddy bai koma Nigeria ba sai yau,yana tare dani yana lura da ni har na murmure,yau d’in ma Anty Kubra ce ta ishe shi da waya shine ya tafi,shine fa na samu na kira ka yanzu…ka ji abin da ya faru Aboki,don Allah kayi hak’uri…….

Hamza ya sauke nannauyar ajiyar zuciya saboda jin bayanin Khaleel,tausayin sa ya kamashi sosai,wannan ciwo yana wahalar da Khaleel,Allah ya yaye masa,Hamza yayi magana cikin nuna kulawa.

“Ayya Khaleel ban sani ba ne,nayi kiranka sau ba adadi bana samun ka,nayi tunanin ko har yanzu fushi kake dani akan maganar shiyasa kak’i kulani,ni zan baka hak’uri Khaleel tunda b’acin ran da na saka ka a ciki ne har ciwon ka ya tashi….kayi min Afuwa ka yafe min Khaleel”

Khaleel yayi murmushi,ya mak’e wuya kamar yana gaban Hamza,yayi magana cikin shagwab’a.

“Ni ba zan hak’ura ba sai ka yarda da wata magana da zan fad’a maka yanzu…

Da sauri Hamza yace.

” Na amince Khaleel…idan har za ta sa ka yafe min laifina”

Khaleel ya D’an yi tsalle ganin ya ci gari ,yace.

“Maganar siyen mota tilas ka amince da ita,sannan shagon nan na Gidan ku da k’ofar sa ke kallon waje za a zo a gyara shi a zuba kantoci,na saro maka wayoyi na zamani sai ka dinga siyarwa,idan kaje lectures ka dawo sai ka bud’e ka zauna,lokacin da baka nan ka samu yaro ya dinga zauna maka,y’an kud’ad’en da zaka dinga samu za su to she maka wata kafar,bana son zaman ka haka babu sana’ar yi Aboki,wad’annan Abubuwa biyun idan ka amince da su to ni kuma zan yafe maka dalilin su”

Tunda ya fara magana Hamza ke jinjina lamarin ,da ya san abin da zai ce kenan da baiyi alk’awari ba sam,yanzu ya zaiyi kenan?hidimar ta yi yawa,Khaleel baya tausayawa kud’i idan yaso kashewa,ko Dan yaga Allah ya hore masa su?domin ko iya kadarorin da mahaifiyar sa ta mallaka masa kafin ta rasu suna da yawa,har da kamfanoni,bayan ta rasu kuma ya samu gado mai d’umbun yawa…..

Jin Hamza yayi shiru yasa Khaleel ya sake magana.

“Karfa kace min ah ah Aboki,domin kayi alk’awari ya kamata ka cika,Idan kuma kana son kuma b’ata min rai ne na koma gadon Asibiti to shikenan ”

Hamza ya sauke ajiyar zuciya, babu abin da yake tsoro irin daddyn Khaleel yaji wannan hidimar da zai masa,tunda ba k’aunar abotar su yake ba,haka nan ga Umma nan a gefe, ita ma ya san ba zata amince ba,hakan yasa yace da Khaleel.

“Ba k’i nayi ba Khaleel, amma Umma bai zata amince ba,hidimar tayi yawa Khaleel…sannan ka tuna daddy ma…

Ya katse shi da sauri.

” Babu abin da zan maka yayi yawa a rayuwa,Hamza baka san yadda kake da k’ima a tare da ni ba ne,ba kuma zaka gane ba,ni dai na san ina sonka Hamza,zuciyata kullum k’ara k’aunarka take,kai Aboki ne nagari,irin Wanda manzon Allah (S A W)ya kwad’aitar da mu akan mu samu,batun Umma ka jingine shi gefe,zan mata bayani da kaina yadda zata fuskanceni…ko ba kai ba ni na riga na saba da kyauta Aboki,in dai ina da shi nafi son nai ta bayarwa,hakan yana sa wa ina jin dad’i idan ina taimakawa Wanda bashi da shi,sannan ka k’yale batun daddy ,ba kud’in sa nake d’iba ina amfani da su ba,nawa ne,halal d’ina ne Aboki,ra’ayin daddy na k’in talakawa daban,ra’ayi na na son taimako daban,shi ma daddyn ina nan ina ta addu’a akan Allah ya shiryar da Zuciyar sa ya gane dai dai”

Hamza yayi shiru har ya kammala jin bayanin Khaleel, sannan yayi magana.

“Duk abin da ka fad’a Hakane Khaleel,na kuma gode da nuna k’auna,yadda kake jina a ranka haka nake jin ka a raina,fiye ma da hakan,na kuma yarda da abin da kake so,sai dai a bisa wani sharad’i guda d’aya”

“Menene sharad’in..?Khaleel ya tambaya.

Hamza yace.

” Na yarda da batun bud’e shago,amma duk ribar da za a dinga samu sai dai mu raba biyu,d’aya taka d’aya tawa,sannan kayan ciki da ka zuba suna nan a matsayin naka ba mallaka ta ba,kawai zan kasance kamar yaron gun mai lura da shi,sannan batun mota ka ajiyeshi gefe,ka sauya min da mashin,ban isa hawa mota yanzu ba,komai da limit d’in sa Khaleel, idan aka ganni da mota yanzu idanu za su yi yawa a kaina,tunda an san talaka ne ni,don Allah ka fahimce ni ka yarda dani da maganata”

Khaleel ya sauke numfashi yace.

“Na ji na amince Aboki tunda haka kake so…

A lokacin Hamza ya d’aga kai ya dubi Agogo,yaga lokaci ya ja sosai, ya san Umma nan can na jiran shi,ga maganin Hidaya da zai siya ya kai,da sauri yace da Khaleel.

” Khaleel muyi sallama haka,Umma na can asibiti ita da Hidaya suna jirana…”bai san lokacin da ya furta hakan ba.

Cikin mamaki Khaleel yace.

“Umma na asibiti?waye ba lafiya?wacece Hidaya Aboki?

Ya jero masa tambayoyi,sai lokacin Hamza ya tuna b’aranb’aramar da yayi,domin kwata kwata Khaleel bai san da maganar Hidaya ba,bai kuma da niyyar fad’a masa a tsukin har sai wani lokaci na daban,amma yanzu tilas ya sanar da shi komai,tunda bakinsa yayi azarb’ab’in furtawa.

Cikin wani irin yanayi Hamza ya fayyacewa Khaleel abubuwan da ya sani game da Hidaya tun daga ranar da ya fara ganinta har yau,da yake Khaleel yana da matuk’ar tausayi sai gashi yana hawayen tausayin Hidaya,ji yake a ransa ina ma yaga Hidayan da idanuwan sa,Aikuwa tilas insha Allah zai taimaki Hidaya,zai tsaya a kan al’amuranta ya zama GARKUWAR ta,zai to she mata duk wata k’ofa da zata wargaza rayuwar ta,haka kawai yaji a ransa yana son Hidaya,duk da bai tab’a ganin ta ba,Lalurar Hidaya ta tab’a ransa,saboda yana ganin yadda masu ciwon sikila suke shan wahala,nan Khaleel ya rok’i Hamza a kan idan yaje asibiti yayi masa flashing,shi kuma zai kira domin su gaisa da Umma,sannan yayi wa Hidaya ya jiki.

A haka suka yi sallama duk zuciyoyin su ba dad’i,sannan Hamza ya mik’e ya fara tattara abubuwan da ya san zai tafi da su asibiti…..

 

 

*****************

 

K’arfe Bakwai da y’an mintuna na safe mota ta sauke shi bakin Asibitin,ya waiwaya yana kallon pharmacy d’in da zai siyi maganin Hidaya,sai ya ganshi a kulle basu bud’e ba,ya fito da ledar da ya zubo kayayyaki da flask d’in Ruwan zafi, sannan ya sallami mai adaidaita sahun,da hanzari ya d’ebi kayan zuwa cikin Asibitin.

Ya tura k’ofar a hankali da sallama, Umma na zaune gefen gadon tana mammatsawa Hidaya k’afafuwanta da suke mata ciwo,Hidayan na kwance hankalin ta a kan k’ofar shigowa,tana ganin Hamza ne ta saki wani k’ayataccen murmushi da ya fito da asalin kyawun fuskar ta,cikin dasasshiyar murya ta marasa lafiya tayi magana tana k’ok’arin mik’ewa zaune.

“Oyoyo Ya Hamza na…..”

Wani farinciki ya mamaye ruhin sa ganin Hidaya ta fara warwarewa,da sauri ya k’arasa ya ajiye kayan hannun sa,ya nufi bakin gadon ya sunkuya yana kallonta fuskarsa cike da murmushi yace.

“Sannu K’anwata…ya jikin na ki?

Ta rik’o hannunsa tana Murmushi tace.

” Da sauk’i Ya Hamza,ina ta Neman ka ban ganka ba,Umma tace min kana gida”

Ya amsa yana damk’e siririn hannun ta a na sa hannun.

“Eh ina can tunaninki ya ishe ni,Ashe har kin fara warwarewa?Alhamdulillah Addu’a tayi aiki kenan,to yanzu menene yake miki ciwo?” Ya zarce da tambayarta.

Ta amsa tana D’an yamutsa fuska..

“K’afata ne Ya Hamza,kamar ana tsira min allura,amma yanzu Umma ta na matsa min ina jin dad’i”

Ya girgiza kai cike da tausayi yana jera mata sannu ba adadi,ita kam sai amsawa take tana kallonsa,zuwan sa yanzu taji dad’in ganin sa,tunda ta farka take son ganin sa daman,ita dai tana son Ya Hamzan ta.

Waiwayawa yayi yana duban Umma da ke had’awa Hidaya tea a k’aramin Kofi,sai lokacin ya tuna Ashe bai gaisheta ba,duk hankalin sa ya tafi kan Hidaya,cikin kunya ya soma gaishe ta,ta yi murmushi tana cewa.

“Sai yanzu ka tuna da ni Hamza..?

Ya Sosa k’eya yana sunkuyar da kai,Umma ta cigaba da juya tea d’in yayin da Hidaya ke cewa Hamza ya cigaba da mammatsa mata k’afarta,haka ya zauna a gefenta ya kai Hannu yana mammatsa mata a hankali,sosai take jin dad’in hakan har da lumshe idanuwa.

Umma ce ta taimaka mata ta yi brush,sannan Hamza ya fara bata tea d’in da k’aramin cokali,tana sha tana shagwab’a shi kam sai biye mata yake,wai ita ya tsefe mata kanta sai Umma ta yi mata kitso,kan ya ishe ta haka,da k’yar ya lallab’ata akan ta bari su koma gida tunda yanzu bata da lafiya.

Yana kammala bata yace da Umma bari ya fita ya siyo maganin,ita kam Hidaya saboda son yawo wai zata rakashi,yayi dariya Yana cewa .

” Da wace k’afar za ki rakani?

Umma da yake ta san akwai kud’i a hannun sa sai bata tambaye shi yadda zai siyo maganin ba,kuma bata san maganin Yana da tsada ba,haka ya fita cikin tunanin yadda zai siyi maganin,dubu Ashirin d’in acc d’in sa ba zata isa komai ba,amma ya san Allah ba zai kunyata shi ba,ya rok’eshi ya hore masa,kuma ya san hanyoyin Allah suna da d’umbun yawa.

Babu abin da ya fad’o a ransa irin yayi maza yaje ya saida wayar sa,in yaso ko k’arama sai ya siya,hakan zai sa ya samu kud’in maganin.

Yana fitowa bakin Asibitin ya kalli pharmacy d’in ya ganshi a bud’e sun fito,Yana shirin tsaida mota domin tafiya kasuwar sayar da wayoyi kawai yaji wayar sa ta yi k’ara alamar shigowar sak’o,a hankali ya zaro ta daga aljihun sa ya duba,zaro idanu yayi k’irjinsa na bugawa saboda ganin alert d’in dubu d’ari cas an tura masa cikin acc d’in sa……!

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA TALATIN DA UKU DA NA TALATIN DA HUD’U*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

Lumshe idanuwa yayi yana jin wani sanyi a Zuciyar sa,sak’on daga Khaleel yake,kamar ya san cikin buk’atar kud’i yake,godiya yayi wa Allah yana ta fad’in “Alhamdulillah” har bai san iya adadin da ya fad’a ba.

Da sauri ya nufi pharmacy d’in,me wajen ya gane shi,nan da nan ya tare shi cikin fara’a suka gaisa,Hamza yace yazo ne akan maganar maganin nan,sai dai bashi da kud’i Cash a Hannu,shin zai iya yi musu transfer ta bank?

Mutumin yace ba damuwa zai iya,ya bashi acc number nan da nan Hamza yayi masa transfer yana daga tsaye,mutumin yana jin shigar kud’in cikin acc number d’in sa ya had’awa Hamza maganin ya bashi,sai lokacin Hamza ke tambayar sa in da zai samu ragowar maganin,mutumin yace ya shiga cikin asibitin akwai wajen siyar da magunguna ya duba ba zai rasa ba.

Hamza yayi masa godiya sosai ya fito rik’e da ledar maganin,ya tsallaka titi ya shige cikin asibitin,bai sha wahala wajen gane pharmacy d’in asibitin ba,ya D’an tarar da layi kad’an,ya jira aka sallame su sannan ya mik’a na sa katin,cikin ikon Allah aka ce akwai maganin da yake ne ma guda biyun,nan ma ya rok’i alfarmar yayi musu transfer suka ce eh zai iya babu komai,nan ya tura musu kud’in dubu takwas da d’ari uku,aka bashi maganin ya had’a da na hannunsa ya fito .

Sanda ya koma d’akin Umma har ta taimakawa Hidaya tayi wanka ta sauya kaya,sai yaga tayi fari sai dai ta rame,ya dubeta yaga duk k’asusuwa a wuyan ta yace.

“An ya Hidaya za ki yi k’iba kuwa?irin wannan rama haka?”

Umma tace.

“Hmmmm!irin lalurar su ai bata barin su k’iba,sai dai su murmure”

Ita kam Hidaya murmushi ta yi tana shafa wuyan ta,ya mik’awa Umma ledar magungunan ,ta karb’a ta duba tana cewa.

“Duka an samu kenan?

” Eh Umma an samu duka,bari nayi wa likitan magana ko?”

Umma tace.

“To babu laifi,Allah yayi maka Albarka Hamza”

“Ameen Umma na”ya amsa yana k’ok’arin ficewa daga d’akin yaji muryar Hidaya ma cewa.

” Allah sarki Ya Hamza,duk ka kashe kud’in ka wajen siyo min magani ko?insha Allahu zan siyi banki idan na samu kud’i in ta tara maka kana amfani da su”

Murmushi kawai yayi ya fice bai ce komai ba,yana jin Umma nan dariya tana fad’in.

“Ah lallai su Hidaya Ashe za a tara kud’i da yawa”.

 

 

************

Lokacin da likitan yazo ya dubata sannan ya bata magungunan tasha,sai da Hamza ya dinga lallab’ata sannan ta karb’a har da Kuka,saboda Hidaya bata son magani ko kad’an,likitan yana ta tsokanar ta yana dariya.

Nan da nan Hidaya ta ware sosai kamar ba ita ce ta lallank’washe jiya ba,likitan ya dinga bawa su Umma shawarwari akan yadda za su kula da lafiyar Hidaya,da yadda ciwon yake,ya fad’a musu a dinga bawa Hidaya kulawa sosai,saboda ciwon ta yana buk’atar kulawa,ya dinga fad’a musu yadda masu ciwon sikila suke jin azaba a jikinsu,yace musu shi kansa yana da sikila,kuma ba k’aramar wahala ya sha ba,yana kan sha ma,yace saboda hakan yayi karatun likita b’angaren cutar domin ya taimakawa masu ciwon,saboda duk yadda za a fasalta maka yadda suke shan wahala ba zaka gane ba in dai ba cutar gareka ba.

Nan Umma da Hamza suka sake tausayawa Hidaya da duk wani mai fama da lalurar,suka yiwa likitan godiya sosai da sosai,a ranar haka Hamza ya shashance a asibitin ko makaranta bai jeba,gashi karatu ya d’au zafi sun kusa fara exam.

Yana ta lallab’a Hidaya sai abin da take so yake mata,har da su tatsuniya sai k’yalk’yala dariya take yi,Umma dai na kallon su tana jin farinciki a Zuciyar ta ganin yadda suke kulawa da junan su,sai lokacin ya tuna da Khaleel yace idan yazo asibitin ya kira shi.

Da sauri ya gyara zama yana k’ok’arin zaro wayar sa cikin Aljihun wandon sa yace.

“Subhanallah,Umma nayi mantuwa fa,d’azu mun yi magana da Khaleel har yace min idan nazo asibitin na kira shi za ku yi magana ke da shi,sannan ya duba jikin Hidaya,shaf na manta sai yanzu,Ashe shirun da naji daga gareshi bashi da lafiya ne Umma,ciwon sa ne ya tashi wallahi”

Umma ta jinjina cike da jimami take nemar wa Khaleel sauk’i a wajen Allah,Hamza yayi masa flashing,cikin minti uku sai ga Khaleel ya kira Video call,Hamza ya amsa sai ga Khaleel zaune akan wata farar kujera a bakin beach,k’afafun sa zube cikin ruwan ,sanye yake da k’ananan kaya da suka yi masa masifar kyau tamkar D’an turawa,yayi haske sosai ga kwantacciyar suma da saje da ya k’a wata fuskar sa,fuskar sa d’auke da wadataccen murmushin da ya k’ara masa kyau,suka haske juna da murmushi shi da Hamza,Khaleel ya D’an harari Hamza,cikin muryar sa mai dad’i yace.

“Ni fa ba da kai zan yi magana ba Aboki,ka fara bani Umman mu naga mahaifiyata,daga nan sai na gaisa da K’anwar mu Hidaya”

Hamza yayi murmushi ya D’an tab’e baki yace.

“To ai ga Umman a kusa dani ….in kuma ka cika min baki sai na hanaka magana da ita malam”

“Afuwan Aboki…don Allah bani Umman mu,na jima ban ganta ba balle naji muryar ta”

Umma na daga gefe tana ta murmushi tana jin maganar Khaleel,Hamza ya kai mata wayar ya zauna ya jingina da kafad’ar ta ,Umma ta kalli fuskar wayar idanuwan ta suka yi arba da Khaleel,wani farinciki ya kamata,Khaleel ya harari Hamza cikin wasa yace.

“To ka kauce mana,ko a gabanka zan gaisa da Uwa ta?

Umma tayi dariya yayin da Hamza yayi masa gwalo ya matsa gun Hidaya,shi kuma Khaleel ya fara gaida Umma cikin tsantsar nuna kulawa da biyayya.

Umma ta amsa tana yi masa ya jiki,har tana k’orafin tsananin ramar da taga yayi,yayi murmushi kawai,a lokacin ya kwantar da murya ya fara tsara Umma da maganganu masu dad’i akan k’udurin sa akan Hamza,babu yadda Umma za ta yi saboda kwarjinin da Khaleel yayi mata tunda suna kallon juna,gashi sai magiya yake surfa mata,tilas Umma tace ta amince,sannan ta dinga yi masa godiya,amma tayi k’orafin ya dinga rage wasu abubuwan Hidimar tayi yawa,Khaleel farinciki tamkar ya zuba ruwa a k’asa ya sha,ya dinga godiya,a lokacin yake tambayar Umma jikin Hidaya,Umma tace da sauk’i,tana mamakin Ashe har Hamza ya bawa Khaleel Labarin Hidaya kenan?

Sun gama magana da Umma sannan Hamza ya karb’i wayar,suka kalli juna da murmushi akan fuskokin su,Khaleel na tsokanarsa wai ya yaga ya k’ara kyau?me Umma take bashi yana ci?Hamza yayi dariya yace” kai da kake k’asar turawa ai Kaine kayi kyau Khaleel, kalli fatarka fa,ni kuwa ina Nigeria jaga jaga muna fama,Khaleel ke k’orafin ai shi a dole yake zaune England, Dan dai babu yarda zai yi ne,amma yafi son zaman k’asar sa Nigeria,Nigerian ma kuma Kaduna kusa da Hamzan,domin baya son zaman Abuja gurin daddyn sa,shi dai Hamza dariya kawai yayi.

A lokacin Khaleel ke cewa Hamza ya bashi Hidaya ya ganta su gaisa,kuma yayi mata sannu,a hankali Hamza ya matsa kusa da Hidaya ya kalleta yana ce mata.

“Hidaya ga Uncle Khaleel za ku yi magana kinji”

Fuskarta na kallon Hamza tayi murmushi cikin zumud’i tace.

“Da gaske ya Hamza?don Allah da gaske ka ke?

Ya jijjiga mata kai yace.

” Eh da gaske!kin ganshi ma fa yana kallonki”

Duk tattaunawar da ake tsakanin Hidaya da Hamza khaleel na kallon su yana murmushi,a lokacin ne Hidaya ta juya a hanzarce ta kalli wayar cikin slow,idanuwan Khaleel da na Hidaya suka yi arba da juna….wata irin fad’uwar gaba Khaleel yaji wadda bai tab’a jin irinta a fad’in duniyar sa ba a lokacin da idanuwan sa suka sark’afe cikin na Hidaya,wani Abu yaji yana masa yawo a jikinsa yana zagayawa jini da tsokarsa yana huda shi,bai san ko menene ba!amma tabbas a lokaci guda yaji Hidaya ta gama zagaye jinin jikin sa.

Yadda yake kallon ta haka take kallonsa tana doka masa murmushi,tayi maza ta juya ta kalli Hamza tace.

“Wannan ne Uncle Khaleel Ya Hamza?

Gyad’a mata kai yayi yana murmushi, Khaleel kam wani sanyi sanyi yake ji a jikin sa,cikin wata irin murya da bai san yana da ita ba ya D’an d’agawa Hidaya yatsun sa guda biyu yace.

” Hi!K’anwar mu ya kike? Ya jikin na ki?

Tayi dariya cikin k’ank’anuwar murya tace.

“Jikina da sauk’i Uncle Khaleel, Ya Hamza yana ta bani Labarin ka ina so na ganka,kullum ina cewa ya nuna min hoton ka sai ya k’i,yau dai gashi na ganka ko?

Ya lumshe idanu yana kad’an kai yace.

” Aikuwa yau Hidaya taga Uncle d’in ta,shi kam Ya Hamza sai mun hukunta shi tunda ya hana Hidaya ganin Uncle Khaleel ko?”

Tayi dariya ta kalli Hamza da ke ta murmushi tace.

“Ah ah a k’yaleshi,bana son a tab’a min Ya Hamza na fa”

Hamza da khaleel suka yi dariya,suka cigaba da hira su uku,Umma kam toilet ta shige tana wanka,sai da Hidaya ta fara Hamma tana jin barci har tana langab’ewa kafad’ar Hamza,sannan Khaleel ya hak’ura yace zai sake kira da daddare suyi hira,yayi wa Hidaya fatan samun sauk’i,lokacin Hamza ya fara yi masa godiya kan kud’in da ya turo masa d’azu,Khaleel bai tsaya jin godiyar ba ya kashe wayar sa saboda baya son godiya.

Hidaya kam har tayi bacci,Umma ta fito daga toilet a dai dai lokacin da Hamza ke k’ok’arin ficewa daga d’akin ta ambaci sunan sa cikin wata irin murya,da hanzari ya juyo ya dubeta yana amsawa,yanayin da ya gani a fuskarta yasa k’irjinsa ya tsananta bugawa……..!

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

 

*BABI NA TALATIN DA BIYAR DA NA TALATIN DA SHIDA*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

 

Jikinsa a sanyaye ya juyo ya dawo d’akin,Umma ta nemi gefen gado ta zauna,shi kam tsugunawa yayi a gabanta ya rik’o hannun ta yana kallon fuskarta da babu walwala ko kad’an,hankalin sa a tashe yayi magana.

“Gani Umma na….”

Ta k’ura masa ido ta ambaci sunan sa.

“HAMZA…

” Na’am Umman Hamza”ya amsa mata.

Ta sauke numfashi ta fara magana cikin wani yanayi.

“Khaleel ya sanar da ni abubuwan da kuka tattauna,amma me yasa baka fad’a min da kanka ba?me yasa ka saka shi ya gaya min da bakinsa?saboda ka san zan ji kunyar sa har na amince masa ko?to ai shikenan Hamza ka yi nasara,na amince masa ne saboda kwarjinin da yayi min,gashi sai magiya yake min,amma gaskiya hankalina bai gama kwanciya da hakan ba,mutane ba za su dubi domin Allah yake mana Hidima ba,za su dubi mune kwad’ayayyu da muka nace masa har yake kashe mana kud’ad’e da hidindimu,Hamza wannan rayuwar ta sauya,kiwon mutum ake ba dabba ba,ina tsoron kar a kaiwa Mahaifin sa gulmar hidimar da yake mana,kasan ba sonmu yake ba,babu abin da ya tsana irin alak’ar ka da D’an sa,ni tun farko ban so har ka amsa masa cewar ka amince da abin da yace ba Hamza,zuciyata tana kokonto akan hakan,bana son abin da zai zo ya tab’a mutuncin mu muna zaune lafiya Hamza”

Ya rud’e ganin damuwar Umma,da sauri ya sake damk’e hannun ta ya d’ora kansa kan kafad’ar ta ya fara magana a hankali cikin ladabi.

“Ki gafarceni Umma,wallahi na rasa yadda zan yi da nacin Khaleel ne shiyasa har na amsa,kuma shi yace zai gaya miki da kansa ba ni na yarje masa hakan ba,amma ni ma ba da son raina ba,kuma dalilin da yasa na amince masa saboda kar na kuma saka masa damuwa a ransa har ciwon sa ya tashi ne,kin san Khaleel da saka Abu a rai Umma,amma don girman Allah ki yafe min idan na b’ata miki rai,bana son ganinki cikin damuwa ko kad’an Umma,kuma insha Allahu babu abin da zai biyo baya sai alkairi”

Umma ta yi shiru ba tace komai ba,ganin yadda Hamza ya shiga damuwa har da k’wallarsa yana ta rok’onta Afuwa sai taji tausayin sa,tayi masa murmushi ta shafa kansa tace.

“Shikenan babu komai ya wuce,Allah ya tabbatar da alkairi”

“Ameen Umma na,Na gode Allah ya k’ara miki Lafiya da Nisan kwana mai amfani” ya fad’a cike da murna.

 

 

 

*********************

 

Kwanan Hidaya biyu a asibitin aka sallameta,cikin ikon Allah ta warware sosai,daman shi ciwon sikila haka yake,idan ya motsa mutum kamar ba zai rai ba,amma idan ya lafa sai kaga kamar mutum bai tab’a ciwon ba ma(Allah ka k’ara mana lafiya).

A wad’annan kwanakin Hidaya ta yi mugun Sabo da Khaleel ta waya,kusan kullum sai ya kira Hamza ko kuma video call domin su sha hira shi da Hidaya da Hamzan,sai Khaleel ya sake shiga Zuciyar Hamza sosai saboda nunawa Hidaya k’auna da yake yi…

Da aka sallamosu haka Gidan Umma kullum a cike da masu zuwa duba Hidaya,y’an unguwar sun yi matuk’ar Sabo da ita,k’awayen ta su Hansa’u kuwa suna manne da ita,hatta y’an uwan Umma daga kano sai da suka zo duba Hidaya.

Hidaya ta cigaba da zuwa makaranta,shak’uwar ta da Hamza na k’ara hab’aka,bata da abokin shawara sai shi,bata da wani makusanci da ya zarce Hamza,duk abin da ya shige mata duhu Hamza take fad’awa,ko Umma bata san wasu abubuwan game da Hidaya ba kamar yadda Hamza ya sani,Hamza shine sirrin Hidaya.

Cikin ikon Allah tuni har an kammala gyaran shagon yayi fes da shi,an zuba wayoyi da charger da condom da earpiece masu tsananin kyau da sauk’i,ga kuma gallelen mashin d’in Hamza Sabo dal na zamani,lokacin da aka kawo mashin d’in kamar Hidaya zata shid’e don murna,haka suka wuni yana zagaya unguwa da ita akan mashin,Hidaya an samu abin hawa,ko makaranta zata sai tace sai ya kaita,duk da makarantar babu nisa,haka zata haye baya ya kaita ya direta,in yana da lecture ya wuce makaranta,idan babu kuma ya dawo gida ya bud’e shago yayi zaman sa.

Sosai ciniki ya bud’e masa sai Hamdala,har da generator Khaleel ya siya masa,yana kunnawa ana kawo chaji sosai a wajen,da yake Hamza na mutane ne,akwai kuma abokan sa guda biyu y’an mak’otan su,Faisal da Anas,idan baya nan sune suke jire masa shagon sa.

Wata uku da bud’e shagon wata ranar lahadi bashi da lecture,Hidaya ma babu makarantar boko,misalin k’arfe sha d’aya na safe bayan ta kammala taya Umma aikin gida tayi wakan ta fes da kwalliya,ta k’ara girma kamar ba ita ba,ta dubi Umma da ke zaune parlour tana hutawa tace.

“Umma ina Ya Hamza ne?

Umma tayi Hamma saboda gajiya tace.

” Yana shago,bai jima da fita ba kina wanka”

Hijabin ta ta d’auka ta saka tayi hanyar fita tana cewa.

“Umma bari naje na goggoge masa kantocin shagon nan,naga jiya duk sunyi k’ura da yawa”

Umma ta d’aga murya tace.

“Kinyi wanka fa,amma zaki kuma shiga aikin k’ura?

Ta fice da sauri tana cewa.

” Na sake wani wankan idan na gama”

Umma ta girgiza kai ta maida kanta ta kwanta gyangyad’i na d’iban ta.

Bakin shagon cike da mutane masu kawo caji da masu siyen abubuwan da suke so,suka matsa mata suka bata hanya,ta d’aga kantar da ta kare tsakanin Hamza da mutane ta shige cikin shagon,Hamza na tsaye yana d’aukowa wani mutum condom da yazo siya,ya waiwayo ya kalleta yayi murmushi yace.

“Har kin shirya?na neme ki ai Umma tace kin shiga wanka”

Ta jijjiga kai tana murmushi tace.

“Eh Ya Hamza, yau fa sanitation zan wa shagon nan duk yayi k’ura”

Ya D’an zaro ido yace”Ayya Hidaya ai zaki b’ata wankan ki”

“Babu komai sai na canza wani Ya Hamza”

Haka ya k’yaleta ta d’au daster ta fara goge goge,shi kuma ya cigaba da sallamar mutane,sai dai Abu d’aya ya dame shi ganin yadda mazan da suke zuwa suka ishi Hidaya da kallon k’urilla,nan da nan yaji ransa ya b’aci, ko me suke kallo oho musu.

Ita kam bata san ma suna yi ba,hankali ta na kan aikin ta tana zubawa Hamzan surutu,ba kuma hirar komai take masa ba sai ta khaleel,yana jinta yana bata amsar maganar da take masa.

Fitsari yaji ya matse shi,Dan haka yace da Hidaya ta bar goge gogen ta kula da shagon zai shiga cikin gida ya fito yanzu,ta amsa da to ,shi kuma ya d’aga Kantar ya fice daga shagon.

Yana shiga ya wuce d’akinsa da sauri,toilet ya shiga saboda jin fitsarin ya matse shi sosai kamar ya zubo a wando,bayan ya gama uzurin sa sai ya fito,ya lek’a d’akin Umma ya ganta kwance a parlour bacci ya kwasheta.

A dai dai wannan Lokacin wata dank’areriyar mota me azabar kyawu ta tsaya dai dai k’ofar Gidan,driver’n motar yana tsayawa ya fito da hanzari ya zagayo ya bud’e k’ofar Gidan baya,wani Hamshak’in mutum ya sako k’afafuwan sa ya fito,jikinsa sanye da kaya na alfarma,daga ganinsa kasan naira ta zauna,ALHAJI MUDASSIR Kenan,Mahaifin Khaleel.

Babu Neman izini ko sallama haka ya taka cikin izza da gadara ya kutsa kansa cikin Gidan,driver kam tsayawa yayi a gindin motar yana jiran sa.

Ita Hidaya bata lura da zuwan su ba ma,hankalin ta ya d’auke kan sallamar mutanen da suke zuwa.

ALHAJI mudassir yana kutsawa tsakar Gidan ya ci karo da Hamza yana k’ok’arin fitowa,da sauri Hamza yayi baya yana duban daddy k’irjinsa na wani irin bugawa da tsananin k’arfi, fuskar daddy tamkar gobara saboda fushi,zubewa Hamza yayi a gaban daddy cikin rawar baki yace.

“Barka …da zuwa daddy…ya …ya hanya..?

Wani matsiyacin kallo daddy ya watsawa Hamza,cikin kakkausar murya ya fara magana da k’arfi yana nuna Hamza da Hannu.

” Kai ka kiyaye ni?bana buk’atar gaisuwar ka,matsiyacin yaro D’an Gidan talakawa jikan mayu,so nawa zan gargad’eka akan mak’alewa yarona ne,wai kai maye ne?nace kai maye ne?haka kawai ka mak’alewa d’ana sai zuk’e masa jini kake,D’an arzik’in da yake da shi wato sai ka k’arar da shi ko?wai kai baka da zuciya a cikin k’irjinka ne?wane irin jarababben yaro ne kai?me za a yi da halin talaka a rayuwa?talaka shegen kansa ne,na tsani talakawa a rayuwa ta domin bak’ar Zuciyar su,ba zan tab’a sonka ba Hamza,idan ka cika D’an halak cikin uwarka da uban ka ka rabu da d’ana,ka fita daga rayuwar d’ana,ka barshi ya sake yayi min biyayya,kai warware asirin da kayi masa,idan ba haka ba wallahi sai Na d’auki mummunan mataki a kanka, asararre kawai……

Hamza kansa a k’asa yana jin duk cin mutuncin da daddy ke masa,K’unci ya mamaye ruhinsa,idanuwan sa suka yi jajir,a dai dai lokacin hargagin daddy ya tashi Umma daga baccin da ta fara,ta taso da sauri ta d’aga labulen parlour’nta tana duban daddy tsaye yana zazzagawa Hamza cin mutunci,Hamza durk’ushe kansa a k’asa Hawayen sa na d’isa,daddy ya waiwaya ya dubi Umma,suka had’a idanu a lokacin da daddy ya cigaba da magana yana mata kallon banza.

“Yawwa fito kiji da kunnuwanki kema,d’anki ya zama kaska rab’i mai jini,to ki ja masa kunne ya fita daga harkar d’ana,ya daina mak’ale masa,bana buk’atar sa a cikin rayuwar d’ana,idan ba haka babu sai na mayar da shi abin kwatance a garin nan,talakawan banza talakawan wofi,na d’aukeshi ma daga k’asar amma kuna bibiyarsa kamar mayu, wannan shine gargad’ina na k’arshe a gareku,Idan kunne ya ji jiki ya tsira…….

Yana kaiwa nan ya saki mugun tsaki ya juya zai fice daga Gidan,yana kaiwa soro suka yi kacib’us shi da Hidaya da ke k’ok’arin shigowa soron a dai dai lokacin,sakamakon man inji ya k’are ta rufe shagon ta shigo ta kirawo Hamza domin a zuba wani,tun daga waje take jiyo hargagi da masifa amma bata san ko muryar waye ba,bangaje Hidaya daddy yayi ya wuce a fusace,Hidaya ta tsorata saosai ta kauce,ta bi k’eyarsa da kallo saboda bata yi nasarar ganin fuskar sa ba,a hankali ta tab’e baki ta nufi cikin gidan.

Hamza ya d’ago yana duban Umma da ta yi mutuwar tsaye,irin wannan ranar take gudu daman,ranar da Mahaifin Khaleel zai sake yi musu tijara a karo na barkatai,shin wai menene laifin su ne?Khaleel ne ya mak’alewa Hamza ba Hamza ne ya mak’alewa Khaleel ba,amma me yasa Mahaifin Khaleel ya kasa gane hakan?shin menene laifin talaka a rayuwa?talaka da ya kasance bawan Allah…!

Hawaye mai zafi ya zubo mata,a dai dai lokacin da Hamza ya d’ago ya kalleta,k’irjinsa ya buga ganin Umma na kuka,ya nufeta hankali a tashe kamar ya kifa,zubewa yayi a gabanta ya rik’e k’afafuwanta ya fashe da kuka mai cin rai yana magana cikin rauni.

“Ki yafe min mahaifiyata,fushin ki gareni babbar masifa ce umma na,nine na jawo miki,daman an ce D’an kuka mai jawa uwarsa jifa,da banyi abota da Khaleel ba da ba a zo an ci mutuncin ki ba,don Allah ki yafe min Umma na,hawayen ki ya bar zuba a kaina,ban san me zan fad’awa ubangijina akan hakan ba,ina kwad’ayin samun aljanna Umma,idan hawayen ki yana zuba a kaina ba zan tab’a samunta ba Umma,don Allah ki yafe min Mahaifiyata”

Kuka sosai Hamza yake mai cin rai,ita ma Umma hawayen ta na d’isa,cikin wata irin Murya a shak’e ta kirayi sunan Hamza.

“HAMZA…..

Ya kasa amsawa saboda kuka sai kallonta da yake yi kawai yana shesshek’a da nishi,ta runtse idanu tace.

” Idan har da gaske ni ce Mahaifiyar ka,ni na tsuguna na haifeka,ni ce na raineka,nice na shayar da kai,ni ce na d’auki d’awainiyar ka tun daga haihuwarka har zuwa girman ka,ni ce uwarka ni ce ubanka,to ina so a yau kayi min alfarmar cire Khaleel daga ranka,ka shafe babin tarihinsa a rayuwar ka,ka manta da shi da duk wani Abu da ya shafe shi,ka mayar masa da duk wani Abu na sa da ke wajen ka,ina so abotarku ta zo k’arshe a yau ba gobe ba……

A dai dai lokacin da Hidaya ta k’araso kalaman Umma na shiga kunnuwan ta,a gigice ita da Hamza suka dubi Umma…k’irjin su ba bugawa,Kansu kamar ya fashe saboda razanar jin kalaman Umma…….!

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU…!* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA TALATIN DA BAKWAI DA NA TALATIN DA TAKWAS*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

 

Umma ta juya a fusace ta shige parlour’n ta,bata tsaya a nan ba sai ta wuce bedroom ma ta kullo k’ofar ta gabad’aya.

Hamza kam bai san lokacin da ya sake fashewa da kuka ba,Abubuwa da yawa sun tarar masa,ga fushin Umma,ga ciwon rabuwa da abin da yake so wato Khaleel, kuma dole ne ya bi abin da Umman sa take so yayi mata biyayya,domin kaf duniya ba shi da kamar ta,babu kuma Wanda yayi wahala da shi tamkar ta,haka nan ya zama tilas idan d’a yana son zama na gari to ya kyauta tawa iyayen sa,musamman ma Mahaifiya,hak’k’in iyaye a musulunci ,hak’k’i ne mai girma,saboda haka ma Allah mad’aukakin sarki ya had’a shi da hak’k’in sa a wurare da dama a cikin alk’ur’ani mai girma,kamar fad’in Allah:

“و اعبدوا اللہ ولا تشرکوا بہ شیـٸا،وبالوٰلدین إحسـٰناوبذی القربیٰ والیتـٰمیٰ والمسـٰکین”

Ma’ana:(Ku bautawa Allah kada kuyi shirka da shi da wani Abu,Sannan ku kyautata iyaye da makusanta da maraya da miskinai).

Haka nan a wata ayar Allah ya sake cewa:

“ووصینا الإنسـٰن بو ٰلدیہ حملتہ أمہ وھنًا علی وھن وفصـٰلہ فی عامین أن اشکر لی ولوٰلدیک الی المصیر”

Ma’ana:(Mun yi wa mutum wasiyya da iyayen sa,mahaifiyarsa ta d’auketa shi rauni akan rauni,d’aukan cikin sa da yaye shi shekara biyu,ka gode min da iyayen ka,gareni makoma take).

Ko ba a k’ara ba iya wad’annan ayoyin ma sun isa a gane darajar iyaye da k’imar su ta wuce duk yadda ake tunanin ta,shi yasa Hamza yaji a Zuciyar sa ranar rabuwa da Khaleel ta zo,domin ba zai iya k’etare maganar Mahaifiyar sa ba.

Yadda hawayen sa ke shatata tamkar za su k’are yasa jikin Hidaya wani irin mugun rawa,bata tab’a ganin Ya Hamzan ta cikin wannan halin ba,take ita ma ta fara kuka duk da bata san cikakken abin da ya faru ba,sai dai Umarnin da Umma ta bawa Hamza akan khaleel, ita kanta Umarnin yayi mata tsauri ba ma Hamza ba,duk da bata yi tsawon zama da Hamza ba a D’an tak’aitaccen lokaci ta gane matsananciyar k’aunar da take tsakanin abokan guda biyu,to me ya faru haka da Umma take son datse wannan alak’a mai girma da kyawu?an ya kuwa Umma bai ta zafafa ba?.

A hankali ta ja sanyayyun k’afafuwan ta ta isa in da Hamza ke durk’ushe yana zubar da hawaye,tsugunawa tayi dab da shi hawaye na malala a idanuwan ta,a hankali ta kira sunan sa cikin siririyar murya.

“Ya Hamza…..

Ya d’ago idanuwan sa da suka yi jajir tsabar kuka da tashin hankali,ganin yadda Hidaya ke kuka sai ya k’ara raunata Zuciyar sa,da hanzari ya girgiza mata kai sannan ya mik’e ya wuce ta ba tare da yace mata uffan ba,ya fad’a cikin d’akin sa cikin wani yana yi mara fassaruwa.

Hidaya ta jima a wajen cikin tashin hankali da Hawaye,a rayuwar ta bata son ganin damuwar Hamza,Zuciyar ta ciwo take muddin ta ganshi cikin damuwa,Ya Hamzan ta yana da wata k’ima ta musamman da babu wani namiji da yake da k’imar a tare da ita,haka ta mik’e jiki a sanyaye ta shige parlour’n Umma,ta tarar Umman ta kulle kanta a d’aki,haka ta dawo kan kujera ta lafe ta kwanta tayi lamo kamar mara lafiya,lokaci lokaci hawaye na ziraro mata akan fuskarta.

Gabad’aya sai Gidan yayi wani shiru ba dad’i ko kad’an,kowa babu walwala,ko k’awayen Hidaya masu shigowa su taya ta wasa ranar babu Wanda ya shigo,kamar sun san Gidan babu lafiya,tana nan kwance har azahar ta yi aka fara kiran sallah,tana jin motsin Hamza sanda ya fito ya d’aura alwala ya fita masallaci.

Ita ma ta mik’e kanta na matsanancin ciwo,ta fito ta d’aura alwala,tana dawowa ta tarar Umma ta bud’e k’ofar d’akin,a hankali ta shiga da sallama,sai ta tarar Umman na sallah,da alamun a bathroom d’in d’akin ta ta yi alwala,hijabin ta ta saka ta matsa kusa da Umma ta ta da sallah ita ma,har Umma ta idar ta zauna tana Jan carbi,ita ma Hidaya ta kammala ta zauna tana addu’o’i,ta D’an sa ci kallon Umma,tana so tayi mata magana amma babu fuska,har lokacin Umma a turb’une take,suna nan zaune suka ji sallamar Hamza,Hidaya ta amsa cikin bugun zuciya tana kallon Umma,ya shigo kansa a k’asa salo salo har ya k’ara so gaban Umma ya tsuguna,ya zura hannunsa a aljihu ya fito da mukullai guda biyu ya zube a gaban Umma,kansa a k’asa ya fara magana cikin rawar murya.

“Umma na ina mai k’ara Neman afuwarki a bisa sab’a mikin da nayi,kiyi min Afuwa Ya mahaifiyata,Hamza D’an ki ne mai biyayya a gareki da bin dukkanin abin da kike so matuk’ar bai sab’awa Allah da manzon sa ba,A yau zan bar Khaleel kamar yadda kika umarceni,wad’annan mukullayen mallakin Khaleel ne,d’aya na mashin d’in da ya siya min,d’ayan kuma na shagon da dukiyarsa take ciki ne,akwai cinikin da aka yi daga lokacin da aka bud’e shagon har zuwa yau,zan ware uwar kud’i na mayar masa,zan raba ribar da aka samu na bashi hak’k’in sa na rabin riba,nima na d’au na wa rabi,kamar yadda muka yi alk’awari ni da shi,ina so kibar mukullayen a wajenki,zan tattaro duk ragowar abin da ya dangance shi na kawo miki,zan aika masa da sak’o ta waya sai ya turo a karb’a kawai Umma,ina fatan hakan yayi miki…!?

Umma ta cigaba da Jan carbinta hankali kwance,sai can ta jijjiga kai tayi magana a tak’aice.

” Ya yi,madalla,Allah yayi maka Albarka ”

Hamza ya amsa,sannan ya cigaba da tsuguno,amma Umma ko kallon sa bata sake yi ba,Hidaya kam sai kallon sa take cike da tausayin sa,kansa a duk’e,ganin Umma bata sake magana ba sai ya mik’e ya fice daga d’akin a sanyaye.

A lokacin ne Hidaya ta ji ba zata iya daurewa ba,cikin marairaicewa ta dubi Umma tace.

“Don Allah Umma kiyi hak’uri ki sassauta wa Ya Hamza…kar ki raba shi da Uncle Khaleel, saboda……

Kallon da Umma tayi mata shi ya katseta daga maganar,cikin b’acin rai Umma tayi magana.

” Idan na sake jin bakin ki akan maganar nan idan ranki yayi dubu sai ya b’aci Fatima…..kinji ni ko baki jini ba…?

Hidaya ta jijjiga kai alamar ta ji,sosai ta tsorata da yanayin Umman,tunda har Umma ta kira sunanta na gaskiya tabbas tana cikin b’acin rai,domin bata fiye Kiran ta da Fatima ba ,shiru tayi har sai da Umman ta sake magana.

“Ki tashi ki je kitchen akwai taliya da miya ki zuba ki ci,sannan ki zo ki saka uniform d’in islamiyya ki ta fi ”

Hidaya ta girgiza kai a hankali.

“Ba na jin yunwa Umma”

Umma ta harareta ta tab’e baki.

“Kar ki ji d’in…cikin ki ne ai ba na wani ba”

Hidaya ta mik’e a hankali ta bud’e wardrobe ta Ciro kayan ta na islamiyya ta sauya da na jikinta,ta sanya hijabin ta sannan ta d’auki jakar makarantar ta ta rataya,ta dubi Umma murya a sanyaye tace.

“Umma na shirya …zan tafi”

“Allah ya tsare hanya ya bada ilimi mai amfani”

Abin da Umma tace kenan ta cigaba da Jan carbin ta.

Hidaya ta kad’a kai tana amsawa,ta fice daga d’akin jiki ba k’wari.

A tsakar gida ta tarar da Hamza,yana zaune kan kujera Y’ar tsuguno kansa a sunkuye a k’asa,sai tsinken tsintsiyar kwakwa da ke hannunsa yana za na shi a k’asa kamar me wasa,amma kamar ba a hayyacinsa yake ba,tausayin sa ya sa Hidaya taji hawaye ya cicciko idanuwanta,a hankali ta k’ara so gabansa ta tsaya,amma duk da hakan bai ji motsinta ba hankalin sa ya tafi wani wajen,har sai da ta ambaci sunan sa sannan ya d’ago da sauri ya dubeta,yayi murmushi mai kama da yak’e,idanuwan sa duk sun wani shanye,a haka yake dubanta sannan yayi magana.

“Wai har kin yi shirin tafiya islamiyya?to ai kamar ba ki ci abincin rana ba ko?”

Ta girgiza kai a hankali tace.

“Eh na yi shiri Ya Hamza zan tafi,bana jin yunwa ne shiyasa ban ci abincin ba”

Zaro idanuwa yayi yana b’ata rai yace.

“Ba zaki tafi makaranta baki ci abinci ba Hidaya, maza ajiye jakar kije ki zubo ki ci a gabana sannan ki tafi”

Ta k’ura masa idanuwa sannan tayi magana a shagwab’e.

“To ai kaima baka ci ba,kuma ni ba zan iya ci ba idan baka ci ba,sai dai idan ka yarda na zubo mana tare sai mu ci,kaji Ya Hamza,na zubo mana tare don Allah?”

Yayi kasak’e yana duban ta,shagwab’ar ta na tab’a Ruhin sa,sai kawai yayi murmushi yana jin wani Abu na tsirga masa,ya kuma tabbatar in dai bai ci ba to ba zata ci ba,shiyasa ya jijjiga kai yace.

“Zan ci …jeki ki zubo”

Ta saki murmushin da ya k’ara fidda kyawunta har da tsalle,ta cire jakarta ta dire,har da zare hijabin ta ta d’ora kan igiyar shanya,sannan ta nufi kitchen da saurin ta,ya bita da kallo idanuwan sa kamar su zagwanye,sai da ta shige sannan ya kau da kai yana D’an murmushi.

A plate d’aya ta zubo musu,ta d’auko wata kujerar ta zauna ta saka abincin a tsakiyar su,cokali mai yatsu guda biyu ta d’auko,ta bashi d’aya ta d’au d’aya,ya karb’a yana saka mata Albarka, suka fara cin abincin a hankali,shi kam Hamza ba wani ci yake ba,wasa da cokalin kawai yake,idan ya fuskanci Hidaya zata gane sai yayi sauri ya d’iba ya kai bakinsa,shi gabad’aya ma d’aci abincin yake masa,saboda Hidaya ta ci shiyasa kawai yake cuccusawa.

A haka suka kammala cin abincin, ta d’auko musu ruwa suka sha suka wanke bakin su,Hidaya ta mayar da hijabin ta ta d’auki Jakarta tana yiwa Hamza sallama,har ta kai bakin k’ofar soro taji muryar Hamza na cewa.

“Yau ba kya buk’atar rakiyata kenan?

Ta D’an juyo ta kalleshi,sai ta sunkuyar da kai ta rasa abin cewa,kullum shi take d’anewa ya kaita a mashin,to yau kuma babu mashin,ta ya ya zata ce ya kai ta?

Murmushi yayi ya nufo ta yana cewa.

” Ko babu mashin ai ina da k’afafu Hidaya,muje na rakaki da K’afafuwana kinji Y’ar K’anwata”

Ta saki murmushin murna,ya k’araso ya karb’i jakar makarantar ta ya rik’e,sannan suka jera suka fice cike da annashuwa da k’aunar juna.

Umma da ke tsaye ta tagar bedroom d’in ta ta bi su da kallo tana lumshe idanuwanta, wani Abu na tab’a ranta,kawai sai ta girgiza kai ta bar gurin.

 

A wannan Daren Hamza ya rubutawa Khaleel zungureren sak’o cike da kalamai masu tab’a zuciya,ya kuma rok’eshi akan ya turo a karb’i komai na sa da ke hannunsa,sai dai bai fad’a masa cewar ga abin da daddy ya zo yayi musu ba,ya shaida masa kawai lokacin rabuwarsu ne yayi,kuma kar ma ya nemeshi a waya domin jin ba’asi,Dan ba zai d’aga ya saurare shi ba,sannan yayi masa fatan alkairi da godiya a bisa taimakon sa da yayi tun daga lokacin da Allah ya had’a su har zuwa yanzu.

Hamza ya rubuta wannan sak’o ne cikin kuka da kewar Khaleel, yana turawa ya kashe wayar sa ya zare sim card d’in ya jefar….ya kwanta ya dafe kansa da ke barazanar tarwatsewa….Hawaye na malala har cikin kunnuwan sa,bakinsa na furta”Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”

Lokacin da Khaleel ya ci karo da sak’on Hamza ya fito daga wanka ne d’aure da towel a k’ugun sa,yana goge Ruwan jikinsa da wani towel d’in,shigowar sak’o yaji,k’arar wayar kawai yaji ya tabbatar Hamzansa ne,saboda komai na sa daban ya sa masa a wayar sa,da hanzari ya d’auki wayar yana murmushi ya soma karanta sak’on.

Tamkar Wanda aka bugawa guduma haka yaji,kansa ya sara,k’irjinsa ya dinga tsananin bugu tamkar ya fad’o k’asa,ya dafe saitin Zuciyar sa bakinsa na rawa,Allah ya taimake shi kusa da bed yake,shiyasa ya fad’i zaune ya yarda wayar a k’asa,bai tab’a jin tashin hankali irin na ranar ba bayan ranar mutuwar mahaifiyar sa,da ranar da daddy ya raba shi da Hamza ya kawo shi England da sunan karatu,sai kuma wannan rana da ta zama ta uku a jerin ranakun bak’incikin sa,tamkar Wanda zai zauce haka Khaleel ya riski kansa a wannan rana,duk da maganar da Hamza ya fad’a akan ko ya kira shi ba zai sameshi ba amma bai lamunci hakan ba,wayar da ya jefar ya d’auko hannunsa na rawa ya fara daddanawa don Neman Hamza,idanuwan sa ma basa gani tsabar shiga rud’u,da k’yar ya gano lambar ya soma kira a gigice,amma baiyi nasarar samu ba,kawai sai khaleel ya fashe da wani irin kuka,nan da nan Zuciyar sa ta fara ciwo,ya kira wayar Hamza ya fi sau d’ari a wannan dare amma bai samu ba,haka ya kwana cikin kuka da kewa kamar yadda Hamza ya kasance.

 

 

***************

A wannan tsakanin lokacin ne kuma ciwon Hidaya ya matsa sosai,jininta ya dinga k’onewa,ciwo tamkar Hidaya zata mutu,hankalin Hamza da Umma ya tashi,in kaga Hamza sai kayi hawaye saboda tsananin ramar da yayi,idanuwan sa sun zurma saboda tashin hankali ,duk wani tanadin sa na ribar da ya samu sai da cutar Hidaya ta cinye shi,haka nan D’an jarin Umma duk ya tafi,har ta kai Hamza ya soma zarar kayansa da sutturun sa yana siyarwa duk don ya ceci rayuwar Hidaya.

Har kuma zuwa wannan lokacin Khaleel bai turo ya karb’i dukiyarsa ba,shi kuma Hamza duk da yana cikin buk’atar kud’i bai tab’a kud’in Khaleel ba,yana fatan ya cika alk’awarin da ya d’aukar wa Umma,ba zai sake cin abin Khaleel ba,ba zai yadda wani Abu ya sake had’a shi da shi ba,duk da har lokacin k’aunar Khaleel bata gushe a ransa ba,illa ma dad’uwa da tayi,kullum sai yayi kuka idan ya tuna da Khaleel, ga lalurar Hidaya,Abu ya zame masa goma da ashirin.

Akwai lokacin da ciwon ya sake motsawa gashi basu da kud’i,sun rasa ya za su yi,Umma ta bada shawarar a d’auki sark’ar gold d’in Hidaya a siyar domin a siya mata magani,amma Hamza ya k’i yarda,yace hak’k’in sa ne ya nemarwa Hidaya magani da kud’insa da k’arfinsa,haka Hamza ya dinga fita yana aikin k’arfi yana samun y’an kud’ad’e yana siyawa Hidaya magani,ga maganin masu ciwon sikila da tsada.

Wani dare da ciwon ya matsa wa Hidaya har da suma,suka rikice suka gigice,da ta farko ta dinga kuka tana rik’e k’irjinta,cikin zafin ciwo ta rik’o hannun Hamza tana kuka da nishi tace.

“Ya Hamza zan mutu!ko ina a jikina ciwo yake wallahi!kamar ana sassarani da gatari!Ya Hamza ina son na rayu da kai amma na san mutuwa zan yi,Umma kuyi min addu’a na daina jin ciwon da nake ji,Ya Hamza ka cire min ciwon nan …don Allah ka cire min …

Hamza ya damk’e hannuwanta sosai,Umma tana hawayen tausayin Hidaya,cikin dauriya Hamza yake magana cike da tauhidi da iklasi.

” Hidaya ki yi hak’uri da k’addarar da Allah ya d’ora miki ta wannan cuta,ba ni da ikon yaye miki domin babu Wanda ya isa ya yaye wa wani bawa cuta sai Allan da ya k’addara masa,kamar yadda ya fad’a a cikin suratul An’am.

“و إن یمسسک اللہ بضر فلا کاشف لہ الا ھو،و إن یمسسک بخیر فھو علی کل شیء قدیر”

(Idan Allah ya same ka da wata cuta babu mai yaye ta sai shi,idan ya same ka da alheri shi mai iko ne a bisa kowane Abu).

Ki mik’a lamarin ki ga Allah Hidaya,domin duk wani al’amari na Allah ne.

“إن الاُمر کلہ للہ”

(Dukkanin wani al’amari na Allah ne).

Allah zai yaye miki wannan cuta da izininsa,da ke da duk wani mai fama da ita,haka nan Allah baya d’orawa bawansa abin da na zai iya ba,kiyi hak’uri,wannan lalurar ibada kike yi….

Haka Hamza ya dinga tausarta da yi mata nasiha,cikin ikon Allah sai ta fara jin rangwami akan azabar da take ji a jikinta,har bacci yayi nasarar kwashe ta.

A hankali kuma sai jikinta ya warware,har ma ta cigaba da zuwa makaranta,Hamza yafi kowa murna,kullum addu’ar sa Allah ya bawa Hidayan sa lafiya.

 

 

*****************

 

Wata biyu bayan hakan Hidaya ta k’ara murmurewa,tayi wani girma ta k’ara kyau,shak’uwar ta da Hamza sai abin da yayi gaba kam.

Zaune take a tsakar gida bakin rariya tana wanke wanke,Hamza ya fito daga d’akin sa yana mik’a alamar ya tashi daga barci,lokacin misalin k’arfe d’aya ne na ranar Asabar,ta kalleshi tana dariya tace.

“Ya Hamza kana jin dad’in ka,wato ma baccin rana kake yi ka barni da aiki,don Allah zo ka tayani d’aurayar kwanukan nan mana.”

Ya nufo ta ya tsuguna dab da ita,ya kalleta lokacin da yake tsoma hannun sa cikin Ruwan wanke wanke yana d’auraye wa,yayi magana cikin k’aramar murya.

“Ban ma fa san lokacin da baccin ya kwashe ni ba wallahi,ina karatun exam kawai naji ina gyangyad’i…kuma na san ba komai ke d’awainiya da ni ba sai gajiya.”

Ta mik’a masa wani cup yana d’auraye wa, yayin da take cewa.

“Allah sarki Ya Hamza na,insha Allahu bayan wuya sai dad’i,ni fa har na k’agu ka kammala karatun ka ka zama cikakken D’an jarida,wayyo Allah randa na jika a redio kana karanta labarai wane irin dad’i zan ji Ya Hamza?”

Ta wani lumshe idanu har da dafe k’irji irin tana tsumayin ranar ta zo,yayi murmushi kawai,ya juya yana duban d’akin Umma yace.

“Wai Umma fita tayi ne?ban ji motsin ta ba”

Ta jijjiga kai tace.

“Eh ta fita Gidan Maman salma,Salma ce ciwonta ya tashi shine ta shiga duba ta”

Ya jijjiga kai cike da jimami yana wa Salma addu’ar samun sauk’i,a dai dai lokacin suka kammala wanke wanken,Hamza ya d’ibi kayan ya shiga kitchen da su,ita kuma ta sunkuya tana d’auraye wajen da ruwa da tsintsiya.

A hankali ta d’ago kai jin ana wata murya sassanya me tsananin dad’i tayi sallama,ta bud’e baki za ta amsa amma ta kasa saboda razanar da tayi da Wanda ke tsaye a bakin k’ofar shigowa tsakar gidan,ko daga bacci ta tashi zata shaida wannan k’ayatacciyar fuskar,domin duk da bata tab’a ganin ta a fili ba ta sha ganin ta a waya da hoto,ba kowa bane face Khaleel.

Sanye yake cikin wasu k’ananan kaya bak’ak’e masu matuk’ar kyau da d’aukan hankali,da takalmi sau ciki Wanda ya rufe k’afafuwan sa,kalar ja,sai wata jibgegiyar rigar sanyi me gashi gashi ita ma ja da ya d’ora saman kayan sa,wani sihirtaccen kyau yayi ga k’amshi da ke tashi kamar an yi b’arin turare…

Bayan sallamar da yayi babu abin da ya fara cin karo da shi sai Hidaya,wadda suke kallon kallo a tsananin su,ita fuskarta na bayyana tsoro da mamakin ganin sa,yayin da ta sa fuskar ta bayyana Abubuwa da yawa masu wuyar fassaruwa,sai dai fuskar na d’auke da wani irin murmushi na kammala,idanuwan sa sunyi narai narai wani irin ruwa ya kwanta a cikin su.

A dai dai lokacin da ya nufo Hidaya da ke sank’are a tsaye,a lokacin ne Hamza ya fito daga ktcheen hannun sa da Kofi cike da ruwa yana fad’in.

“Lokacin shan Ruwan ki yayi zo ki sha,kin san dai likita yace ki dinga yawan shan ruwa a kowace rana Hidaya……

Maganar ta mak’ale sanda idanuwan sa suka yi arba da Khaleel,ya saki kofin a k’asa cikin wani yana yi na matuk’ar razana,a kuma wannan lokacin Umma ta shigo gidan tana sallama……

 

Comment
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU…!* 💔✌️

*TARE DA ALK’ALAMIN* ✍️

HASSANA D’AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

*BABI NA TALATIN DA TARA DA NA ARBA’IN*

 

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

 

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

 

 

 

 

 

Kallon kallo kawai aka tsaya yi tsakanin su,kowa Zuciyar sa na tsananin bugu,wata gingimemiyar Soyayya da kewa suka tasowa Hamza a lokaci guda,Soyayyar Khaleel da kewar sa,idanuwan sa suka cicciko da hawaye,k’afarsa ta fara rawa tamkar ba zata d’auki gangar jikinsa ba,Zuciyar sa na ingizashi akan ya je ya tari Khaleel ya rungume shi a jikinsa ko zai samu sauk’in damuwar da yake ji,amma inah!idanuwan Umma sun masa Katanga da aikata hakan,ba zai iya karya alk’awarin ta ba!shiyasa ya zab’i ya wuce d’aki domin ya kaucewa kallon Khaleel da ke tsaye yana duban sa cikin rauni,ya tabbatar idan ya cigaba da tsayuwa tilas sai Zuciyar sa ta ingiza shi akan kula Khaleel, Wanda kuma hakan babban laifi ne da zai aikatawa mahaifiyar sa.

A hankali ya juya baya ya soma tafiya domin shigewa d’aki,a lokacin har hawayen idanuwan sa sunyi nasarar fara zubowa,Hidaya tana fuskantar nufinsa ta yi hanzarin dakatar da shi wajen kiran sunan sa da rawar murya.

“Ya HAMZA…!

Ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba yana sauraren ta,ta cigaba da magana tana kallon kwantacciyar sumar k’eyar sa.

” Wannan fa Uncle Khaleel ne…kuma na tabbatar wajen ka ya zo…amma me yasa za ka tafi ka barshi?ko baka ganshi ba ne…!?

Bai waiwayo ba yayi magana cikin raunin murya.

“Na ganshi Hidaya…amma bani da iko wajen kula shi,har sai mahaifiyata tayi min umarnin aikata hakan”

Shi kam Khaleel tsaye yake cikin wani yanayi,kansa duk’e a k’asa,Abubuwa da yawa sun cika rarraunar Zuciyar sa wadda bata da k’oshin lafiya,a hankali ya d’ago kansa ya dubi Umma,wani irin hawaye ya zubo masa,kawai sai ya nufi Umman da ke tsaye kamar an dasa ta ,ya tsuguna gaban ta,yayi iya k’ok’arin sa na ganin maganar da yake son yi ta fito amma ya kasa,wani tuk’uk’i yake ji a k’irjinsa,hakan ya sa kawai ya dinga girgiza kai yana hawaye.

Matsanancin tausayin sa ya kama Umma,wace irin k’auna Khaleel yake wa Hamza da har yayo tattaki tun daga England ya tawo domin Hamza?ga wata irin rama da ya kwantsama duk dalilin tashin hankalin rabuwa da Hamza,ya baro karatunsa da komai nasa domin Hamza kawai !Anya kuwa idan ta raba wannan Abotar tayi adalci kenan!?

Ganin yadda Khaleel ke faman had’iyar zuciya yana kuka ya kasa magana sai hakan ya tsorata Umma sosai,kar taje wani abun ya faru da D’an mutane !hakan ya sa cikin wata irin murya tayi hanzarin magana,musamman da taga Hidaya ma ta tsura mata idanu,cikin wani irin kallo mai kama da tuhuma ko Neman agaji.

“Hamza kazo gun Khaleel na amince kayi magana da shi” Tana fad’in hakan ta wuce d’akin ta da sauri.

Sai lokacin Hamza ya juyo cikin farinciki,a maimakon hawaye masu d’umi sai hawayen sa ya fara sanyaya,ya k’araso inda Khaleel ke tsugune ya dafa kafad’ar sa,Khaleel ya d’ago idanuwan sa da suke zubar hawaye a hankali ya dubi Hamza,a yayin da Hamzan ya rik’o kafad’un sa ya mik’ar da shi,suka zubawa juna idanu cike da wata irin k’auna,da hawaye a idanuwan su amma Zuciyar su k’al da farinciki,da murna ta ishi Khaleel kawai sai ya afka k’irjin Hamza suka rungume juna suna wata irin dariya,ga kuma hawaye na malala,sai lokacin Khaleel ya samu yin magana ,cikin muryar shauk’i ya ambaci.

“Abokinahhhhh…..!

Hidaya da ke tsaye tana kallon su farinciki ya isheta,ga tausayin su da ita ma ya sakata k’walla,bata san lokacin da dariya ta kufce mata ba,ta d’aga hannuwanta tana tafa musu tana k’yalk’yala dariya.

A hankali suka saki juna suka waiwayo a tare suna duban Hidaya fuskar su d’auke da mad’aukakin farinciki da murna.

 

 

***************

 

Bayan komai ya lafa,Khaleel ya samu tarba ta musamman cike da farinciki,suna zaune gabad’ayan su a parlour’n Umma bayan sun kammala cin abinci,nan Khaleel ke bawa Umma hak’urin duk abin da ya faru har da kukan sa,ita kanta Umma tayi mamakin yadda akayi Khaleel ya san Mahaifin sa ya zo ya ci musu mutunci,sai lokacin Khaleel ke sanar da su cewar sai da ya tsaurara bincike sannan ya gano hakan ta hanyar driver’n daddy,domin shine ya sanar da shi tabbas ya kawo daddy Gidan su Hamza,yace hankalin sa yayi matuk’ar tashi har ciwon sa ya kusan motsawa,yace baya iya bacci saboda tunani,shi abotar sa da Hamza Allah ne ya had’a ba wani mutum ba,Dan haka ba zai iya rabuwa da Hamza ba,kuka sosai ya dinga yi har Zuciyar Umma ta lafa ta tausaya musu,ganin shi kansa Hamzan kuka yake,a lokacin Umma tace ta amince su ci gaba da abotar su,amma bata yarda Khaleel ya cigaba da kashewa Hamza kud’i ba,hakan na janyo wa a dinga zargin wani abin,tilas Khaleel ya hak’ura da hakan,sai dai ya kafe ba zai karb’i abin da Hamza yayi niyyar dawo masa da shi ba,Umma kuma tace dole sai ya karb’a,nan take Khaleel ya yanke hukunci akan cewa ya mallaka wa Hidaya komai kyauta,a matsayin ta na marainiya,a cigaba da kula da rayuwar ta da karatunta da lafiyar ta da wannan jari na shagon da aka bud’e.

Umma ta so yin gardama amma ya kafe ya nace akan hakan,tilas ta hak’ura ta zubawa sarautar Allah idanu,lokacin Hidayan ma bata nan ta ta fi islamiyya,Dan haka ba komai aka tattauna akan idanunta ba.

Kwanakin Khaleel uku a Gidan su Hamza,wad’anda yayi su cikin farinciki tamkar ya dawwama a haka,babu k’yama babu komai ya baje tamkar Gidan su,yana manne da Hamza da Hidaya,Hidaya har fashin makaranta ta dinga yi kullum suna tare suna hira,kulawar da Khaleel yake bawa Hidaya har mamaki take bawa Hamza,lokaci d’aya sun saba da juna bashi da zance sai na Hidaya,haka nan ko band’aki ta shiga Khaleel ya dinga Neman ta kenan kamar wadda ta b’ata,sosai dai Sabo ya shiga tsakanin su.

Sati d’aya cif yayi shirin komawa England, Wanda ko Mahaifin sa bai san yazo ba,kuma ta Abujar ya sauka amma baije gida ba,saboda yasan ba za su kwashe da dad’i ba,kullum dai zancen Hamza baya wuce yiwa Khaleel nasiha akan yiwa Mahaifin sa biyayya,duk da Mahaifin na sa ya kasance wani baud’ad’d’e mai bak’in hali.

Ran da Khaleel zai tafi tamkar marasa lafiya suka zama,suka rungume juna shi da Hamza tamkar ba za su rabu ba suna kuka,Hidaya na gefe ita ma tana na ta hawayen,tana ji a ranta bata son rabuwa da Khaleel saboda yana da kirki,ga dad’in zama ,kuma masoyin Ya Hamzan ta ne,Dan haka take d’aukar sa da k’ima,sai da Umma ta dinga lallamin su sannan suka hak’ura,in da Khaleel zai wuce abuja domin samun jirgin da zai Lula da shi England.

Suka yi wata irin rabuwa Mara dad’i mai cike da kewa da zubar hawaye,Khaleel yana ji a ransa zaiyi duk mai yiwuwa domin ganin ya k’auracewa zaman England zuwa k’asar sa Nigeria.

Hamza da Hidaya sun fi sati d’aya kafin su dawo hayyacin su kewar Khaleel ta sake su,kullum ba su da zance sai na sa,duk da suna waya har ma da video call.

 

 

*****************

*BAYAN SHEKARA BAKWAI*

 

Abubuwa da yawa sun faru cikin wad’annan shekaru,na farinciki da akasin haka,na farincikin bai wuce kammala karatun da Hamza yayi ba,Wanda ya zama cikakken D’an jarida,sai dai har zuwa lokacin bai samu Aiki ba,haka nan shagon siyar da wayoyi ya bunk’asa sosai,Hamza yana tarawa Hidaya dukiyar ta kamar yadda Khaleel ya mallaka mata wajen,duk da cewar har lokacin bata san wajen mallakinta ba ne,a zatonta mallakin Ya Hamza ne,da kuma wasu Abubuwa makamantan hakan.

Na bak’inciki kuma ba zai wuce rashin lafiyar Hidaya ba,wadda take matuk’ar shan wahala idan ta motsa,dan ma cikin ikon Allah ba sa rasa kud’in siyen magani,daga baya ma sai Khaleel ya had’a su da wani babban likitan ciwon sikila,wanda komai Khaleel d’in ne ke biya,sai kuma bak’incikin rashin Khaleel a kusa,Wanda har zuwa wannan lokacin bai dawo Nigeria ba,domin Mahaifin sa ya dage akan sai yayi karatu mai zurfi,a kullum Hamza na tausar sa akan yayi hak’uri komai yayi farko zai k’arshe har ya zama Labari ,a kwana a tashi tilas wataran zai dawo,yayi hak’uri kuma ya dage da addu’a.

Zuwa wannan lokacin Hidaya na da shekaru goma sha shida cif!ba kuma lallai ka shaidata ba saboda wani irin girma da tayi na fara cikar budurci,sai dai har lokacin bata da k’iba,sai dai cikar baya da mazaunai,kyawun ta kullum k’ara fitowa yake yi sosai da sosai,haka nan Hamza,wanda ya zama cikakken saurayi mai ji da wani sihirtaccen kyau da haiba,ga nutsuwa da hankali ,uwa uba Addini,tsafta da kamala.

Har zuwa wannan lokacin kuma babu Wanda ya tab’a fitowa ko ya furta cewa yana son Hidaya,saboda yadda ake rad’e rad’in Hidayan Y’ar tsuntuwa ce,da yake zancen duniya baya b’uya,haka nan duk yadda mutum ya kai da son rufe wani Sirri idan Allah yayi nufin tonuwar sa sai ya bayyana.

Wannan wani k’alubale ne ga rayuwar Hidaya,duk da Hamza ya kanyi k’ok’ari wajen ganin ya hana hakan tasiri,da gaske yake son zama GARKUWAR Hidaya,baya barinta tayi kuka idan aka ci mutuncinta a waje,ya kanyi duk yadda zaiyi domin ya kareta,an sha fad’a da Hamza akan Hidaya,Hamza ya sha dukan mutane akan Hidaya.

Wataran ta kanyi kuka idan ta tuna rayuwar ta,wadda kullum Hamza ya kan d’aurata akan ta dinga yiwa mahaifiyarta addu’a,Allah ya kareta a duk in da take,kuma Allah ya bayyana ta.

Sai dai Hidayan jinsa kawai take,amma a ranta bata fatan taga mahaifiyarta,wadda ta gudu ta barta tun bata da wani wayo,babu wani uzuri da zata yi mata akan hakan,domin tsakanin d’a da uwa sai Allah amma har ta iya gujemata shekaru da dama ba tare da waiwayenta ba,ita kam Umma da Hamza sun fiye mata komai a rayuwar ta,mutanen da suka rik’e ta bisa Amana suka lura da rayuwar ta da tarbiyyarta,suka gwammace su kwana basu ci abinci ba akan ceton rayuwar ta,suka kareta ga duk wani Abu mara kyau,kullum burin su ta samu kyakkyawar rayuwa,suka tsaya akan ilimin ta Wanda yanzu haka tana shekarar k’arshe ta kammala secondary school,ta sauke alk’ur’ani mai girma da wasu litattafai, a yanzu hadda take yi har tayi nisa,wai shin me zata cewa wad’annan bayin Allah da suka tallafi rayuwar ta alhali basu da wata alak’a ta jini da ita….?

 

***************

Cikin cikakkiyar muryar sa mai d’auke da wani amo mai Jan hankali ya shigo tsakar gidan da sallama,Umma da ke zaune tana ninke wasu kaya ta amsa sallamar sa tana masa sannu da zuwa,ya amsa yana zama kusa da ita cikin gajiya,sai dai fuskarsa d’auke da tarin farinciki take.

Umma ta dubeshi tana fad’in.

“Daga ganin fuskar ka ina zaton an dace ko?”

Ya gyad’a kai yana tayata ninke wata riga yace.

“K’warai kuwa Umma,addu’ar ki gareni ta yi tasiri,yau dai na samu an d’aukeni aiki a gidan redion jihar Kaduna,da matsayi babba da albashi mai kauri”

Umma ta washe baki cike da murna take fad’in.

“Alhamdulillah ala kulli halin,ina taya ka murna Hamza,Allah ya sanya alkairi ya baka damar sauke nauyin da ke kanka,yau ina cike da farinciki wallahi,kai Allah abin godiya”

Shi Hamza yawan farincikin da Umma take shine musababbin jin na sa farincikin ya ninku sau ba adadi,haka Umma tai ta sakawa aikin Albarka cike da jin dad’i,ya dinga amsawa da “Ameen Umma na”

Har suka kammala ninkin bai ga Hidaya ba,hakan ya sa ya tambayi Umma ina Hidayan take.

Umma ta tab’e baki tace.

“Ta na d’aki ta k’unshe kanta ni ban san me yake damunta ba tun d’azu,nayi tambayar duniya amma tak’i magana sai hawaye take,kuma yanayin ta bai nuna min ko bata da lafiya ba,kawai miskilancin ta ne ya matsa,sai kaje gareta kaji abin da ke damunta,Dan kai kad’ai take gayawa damuwarta ko abin da ya shafe ta”

Ya girgiza kai nan da nan yaji damuwa ta mamaye k’irjin sa,shi fa Sam baya son damuwar Hidaya,ya kan fita shiga damuwa idan tana cikin damuwa.

Mik’ewa yayi a hankali ya nufi parlour’n Umma, bai ganta anan ba,hakan ya sa ya wuce bedroom kai tsaye ya d’aga labulen had’e da sallama.

Tsayawa yayi cak yana duban ta,ta na kwance rub da ciki da wata doguwar riga a jikinta duk ta d’ame ta halittun ta sun bayyana a fili,yaji wani yammm!a jikinsa,ya runtse idanu yana fad’in “A ‘uzu billahi minash shaid’anir rajeem” Saboda wani Abu da yaji Wanda bai tab’a jin irin sa ba,shed’an na k’awata masa surorin Hidaya,Hidayan da ya d’auketa tamkar ciki d’aya suka fito,bai tab’a jin hakan ba kuma sai yau,to me yasa yau yaji hakan?

A hankali ya fara takawa domin isa gareta,motsin sa yasa ta mirgina ta tashi tana goge hawayen idanuwan ta,yana kallonta yayi maza ya kau da kai saboda yadda k’irjin ta ya fito a cikin rigar sosai,Zuciyar sa na wani irin bugawa ya wuce wardrobe in da kayan Hidayan suke a jere reras suna k’amshi,ta bishi da kallo lokacin da ya bud’e ya saka Hannu ya zaro wani dogon hijab d’in ta,kansa a k’asa ya nufo ta har ya isa dab da ita ya mik’a mata hijab d’in,ta karb’a fuskar ta cike da alamun tambaya.

“Ki saka a jikin ki” abin da yace kenan,sannan ya jawo kujerar dressing mirro ya zauna yana fuskantar ta,har lokacin kuma ya kasa d’aga ido suyi four eyes da juna,domin ba zai iya jure hakan ba.

Bayan ta saka ta sunkuyar da kai ta cigaba da goge hawayen da yake zubo mata,a hankali ya d’ago kai ya dubeta,har lokacin bata sauya a idanuwan sa ba,gabad’aya Hidayan ta sauya masa kamar ba Hidayan sa ba,wadda ya raineta tun da k’ananan shekaru har zuwa girma,hawayen da take fitarwa yana tab’a ransa,idan yaga tana kuka sai yaga kamar ya Gaza a kan amanarta da ya d’auka.

Cikin sanyin murya ya ambaci sunan ta.

“Hidayahhhhh…..!

Yadda ya ja sunan ita kanta sai da tsigar jikinta ta tashi,cikin wani slow ta d’ago shanyayyun idanuwan ta masu sirkin ja saboda lalurar ta,suka had’a idanu,a tare suka yi saurin kau da kai saboda sak’on da ya shiga jikin su mai kama da shocking.

Ya sake kiran sunan ta a karo na biyu da rawar murya,ta amsa ita ma cikin rawar muryar.

” Me ya same ki kike kuka?baki da lafiya ne..!?

Kamar ya to no hawayen ta,nan da nan ta kuma b’allewa da hawaye har da shesshek’ar kuka,hankalin sa yayi matuk’ar tashi,a rikice yace.

“Kin san dai kukan ki ba k’aramin tashin hankali yake sakani ba,ki fad’a min abin da ya saka ki kuka kafin ni ma ki sakani kukan…!

Ta san tabbas zai iya yin kukan,domin ba yau ya fara sakata a gaba yayi kuka idan tana yi ba,cikin rauni ta d’ago tayi magana a hankali kuma a tak’aice.

” Ya Hamza jini…..!

Ya ji maganar wata iri,ya kasa gane abin da take nufi,iya hangensa bai gano ba saboda a tak’aice tayi maganar kuma babu ma’anarta a bayyane,shiyasa ya D’an tara gira yana duban ta yace.

“Jini kuma?jini a ina….!?

Ta sunkuyar da kai ta fara yi masa bayani a hankali cikin k’aramar murya.

” D’azu ne da na shiga toilet zan yi fitsari,shine na…na…naga… jini …naga jini a pant d’i na yana fita ta jikina…”

Wata gingimemiyar kunya ce ta taso ta rufe Hamza,domin shi mutum ne mai tsananin kunya,yayi shiru kansa a k’asa,Hidaya ta girma kenan,domin a yadda tayi bayani tabbas al’ada ce ta zo mata,k’ila rud’ewar da tayi ne ya saka bata fahimci hakan ba.

To amma me yasa ta kasa fad’awa Umma amma shi ta fad’a masa?ko Dan ya kasance shine abokin shawarar ta kuma sirrin ta?ya rasa ma mai zai ce mata,a hankali ya jiyo muryar ta cikin kuka tana fad’in.

“Shikenan wata lalurar ta sake shiga ta kenan Ya Hamza…!?

Da sauri ya katseta cikin girgiza kai.

” Ah ah Hidaya,kar ki rud’a kanki mana,girma ne yazo miki fa,ko baki karanta a islamiyya ba?ai kin san Haila ko?abin da mata suke yi idan sun girma?

Hidaya tayi shiru tana tunani,sai lokacin ta gane yanayin da ta shiga,Ashe haila ce ta zo mata bata gane ba har tayi b’aramb’ara ma,wata dank’areriyar kunya ta rufto mata,ta fad’i kwance a kan gadon tana cukuikuye kanta cikin hijab d’in ta,ji take tamkar ta nutse a k’asa don kunya,ita kuwa me ya shiga kanta har ta kasa ganewa?bayan sun karanta a makaranta sau ba adadi?

Murmushi kawai Hamza yayi ya mik’e tsaye ya fice daga d’akin,har lokacin Umma nan zaune tana jin redio,tana ganin sa ta kalleshi tace.

“In ce ko ta fad’a maka abin da take wa kuka..!?

Yayi k’asa da kai yana fad’in.

” Eh Umma….am…ina zuwa dai “yana fad’in hakan yayi sauri ya fice daga gidan.

Umma ta bishi da kallo kawai cikin mamaki.

Tana nan zaune minti bakwai da fitar sa sai gashi ya dawo da bak’ar Leda a hannun sa,ya zo ya tsuguna gaban ta kansa a sunkuye ya kasa had’a idanuwa da ita,a hankali ya mik’a mata ledar yana fad’in.

” Umma ga sak’on Hidaya,ayi hak’uri a nuna mata yadda zata yi amfani da shi…yarinyar ta cika rud’ewa da yawa ne,ummmm…bari in je waje Faisal na jira na”

Kafin ma Umma tayi wani yunk’uri tuni Hamza ya fece da saurin sa,tayi sakato da bak’ar Leda a Hannu,sai da ya fice sannan ta sauke numfashi a hankali ta kwance ledar Dan duba abin da ke ciki…zaro idanuwa tayi ganin Audugar mata wadda ake tare jinin al’ada da ita wato (Always)…….!

 

Comment
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

BABI NA ARBA’IN DA D’AYA DA NA ARBA’IN DA BIYU

 

 

***Wani irin mamaki ya cika Zuciyar Umma,yanzu daman abin da Hidaya take b’oye mata kenan?amma shine har ta iya fad’awa Hamza a matsayin sa na Namiji?Kawai sai Umma ta mik’e da hanzari ta nufi d’akin da ledar a hannun ta.

Tana shiga ta tarar da Hidayan a tsaye tana niyyar shiga toilet,Umma ta D’an harareta kad’an ta ambaci sunanta.

“Fatima….!

Hidaya ta amsa gaban ta na fad’uwa,duk lokacin da Umma ta kira ta da Fatima to tabbas tana cikin fushi ne ko b’acin rai,Umma ta ta zauna gefen gado tace.

” Zo nan…!

K’arasowa ta yi a hankali ta durk’usa a gaban Umman kanta a sunkuye,fuskar Umma a d’aure ta fara magana.

“Me yasa baki da cikakken hankali ne,yanzu ki rasa wa zaki fad’awa kina haila sai Hamza?Hamza fa namiji ne amma kina mantawa da hakan,ba kowace magana ya kamata ki tattauna da shi ba,ni menene amfani na da ba zaki gaya min damuwarki ba?a matsayin mahaifiyarki nake Hidaya,kuma ciwon y’a mace na y’a mace ne,wannan rayuwar ba komai kake sakin jiki ka fad’awa Namiji ba,ko da kuwa uwarku d’aya ubanku d’aya,saboda yadda zamani ya lalace,na san kyakkyawan tarbiyyar da na Baku daga ke har Hamza,amma akwai rud’in zamani,Wanda nake addu’ar Allah ya kare ku daga shi,Hidaya ki dawo cikin hayyacin ki!duk wani abin da ya shafe ki in dai na kunya ne to ki dai na fad’awa Hamza,ki sameni ki fad’a min,ko kuma ki fad’awa Hansa’u ko Sumayya,duk za su baki shawara ta gari,amma ke a ce baki da abokin shawara da fad’awa sirrinki sai Hamza,ina jin kina mantawa da cewar Hamza Namiji ne,kuma bai kamata ya san wasu Abubuwa da suka shafi sirrin ki ba ko…!?

Haka Umma tai ta yi wa Hidaya fad’a,ita kam kanta a k’asa idanuwanta sun cicciko da hawaye,tabbas babu wada take fad’awa damuwar ta sai Ya Hamza,to amma gaskiyar magana wannan rud’ewa ta yi,shiyasa bata fahimci yanayin da take ciki ba ma kwata kwata,shirun da ta yi yasa Umma ta sake k’are mata kallo,rigar jikinta kanta bai kamata Hamza ya ganta da ita ba,ko ba komai a kwai shaid’an ,ga kuma sharrin zuciya,duk da kullum ana addu’a.Hakan yasa Umma ta k’ara ce mata.

“Irin wad’annan kayan ma bai kamata kina saka su ba matuk’ar Hamza na gidannan,ba wai takura miki nake son yi ba,ina k’ok’arin sauke nauyin hak’k’in tarbiyyar ku da ke kaina ne,zuciya bata da k’ashi Hidaya,duk tarbiyyar mutum da kaucewa sharrinta wani zubin tana kai mutum ta baro,Dan haka ki tattara ire iren wad’annan kayan duk ki Adana su ki daina sakawa,duk lokacin da Allah ya sa na aurar da ke sai ki sanya su a d’akin mijin ki”

Sai lokacin Hidaya ta d’ago kanta cikin shagwab’a tana dafa cinyar Umma,ta shagwab’e fuska tace.

“Aure kuma Umma?wane irin Aure?ni babu wani aure da zan yi Umma, domin ba zan iya rabuwa da ku ba..!

Umma ta yi murmushi tana duban ta tace.

” Aure kam ya zama dole Hidaya,domin idan ba a aure da ke kanki ba a sameki ba,Dan haka ki shirya kin kusa aure kina kammala secondary school zan miki aure”

Hidaya ta zaro idanu,sosai ta cigaba da yi wa Umman shagwab’a jin maganar ta,to ita da wa za su yi Auren?ita da bata da saurayi ko farinjini bata da shi?haka nan bata hango yadda zata iya rayuwa ba tare da Umma da Ya Hamza ta ba,tana ji a ranta mutuwa kad’ai za ta iya rabata da wad’annan mutane a rayuwar ta.

Haka Umma tai ta tsokanar ta ita kuma Hidaya na shagwab’a,sai da Umma taga Hidaya ta fara hawaye sannan ta k’yaleta tana dariya,lallai abin na Hidaya azimun ne,tun ma kafin Auren ya zo har an fara daru da ita?to ina ga Auren kuma ya zo?duk da bata fatan rabuwa da Hidayan ita ma,akwai abin da take sak’awa a ranta Wanda take fatan ya tabbata,za ta fi kowa murna da farinciki.

Umma da kanta ta nunawa Hidaya yadda za ta yi amfani da (Always)d’in,sannan ta zaunar da ita tana karanta mata yadda zata tsare kanta da jikinta,da yadda zata kaucewa kula maza da yawan wasa da su,duk da ta san Hidayan ba kula maza take ba idan ba Hamza ba,ko su Faisal abokan Hamza sai dai kawai su gaisa,amma bata hira da su ko kula su,da zarar ma sun fara janta da magana ko wasa Hamza zai yi kicin kicin da fuska,shi bai yarda wani namiji ya kula Hidaya ba,ban da Khaleel babu Wanda Hamza yake bari yayi hira da Hidayan, Dan Khaleel har waya ya siyawa Hidaya,wadda kullum suke hira ko Hamza baya nan,Hamza bai tab’a damuwa da hakan ba,saboda ya yarda da Khaleel fiye da komai.

Sannan Umma tace mata ta lura da iya kwanakin farawar ta da gamawar ta,ta sake koya mata wankan tsarki duk da sun karanta a makaranta,sannan tace da zarar ta ji alamun zuwan sa kar ta dinga bari ana sani,saboda shi wannan abin b’oyeshi ake ba bayyana shi ba.

Hidaya taji dad’in bayanan Umman, ta kuma yi mata alk’awarin zata kiyaye da yardar Allah.

Tun daga wannan kuma sai aka shiga Y’ar kunya tsananin Hidaya da Hamza,da k’yar suke iya had’a idanu,Umma dai tana lura da su bata ce musu kanzil ba,daga baya kuma sai suka ware suka koma kamar da.

Hamza ya soma zuwa Aiki cikin nasara da Sa’a,Ranar da Hidaya ta ji muryar Ya Hamzan ta a redio yana karanto labarai cikin harshen turanci kamar ta suma don murna,ta dinga k’yalk’yala dariya tana tsallen murna,Umma dai dariya kawai take mata ganin murnar ta har ta yi yawa.

A lokacin ne kuma Khaleel ya siyawa Hamza mota dalleliya,duk yadda Umma ta so hanawa k’i yayi,wai Hamza ya wuce hawa mashin yanzu,tunda ya samu aiki tilas a siya masa mota ya dinga zuwa gun aiki da ita,haka nan yasa ma’aikata masu gini suka zo k’ofar gidan aka ja baranda aka katange aka saka get,wai domin Hamza ya samu wajen ajiye motar sa.

Su dai sukan rasa bakin magana ma akan hidimar Khaleel, Hidaya kam yawan ci ma kayan da take sakawa shine yake turo mata,wasu ma duk bata saka ba saboda k’anana ne kuma d’amammu,hakan yasa Umma duk ta d’ebe ta Adana mata wai sai ta yi Aure za ta saka”

Tun daga wannan lokacin kuma Hamza ya rik’e lokacin fara al’adar Hidaya,da zarar lokacin yayi zai siyo mata pad ya kai mata har d’akin Umma ya ajiye mata ba tare da magana ba,in ta gani sai ta d’auka,ko Umma ta d’auka ta bata.

Hidaya ce mai bud’ewa Hamza get da zarar ya dawo daga Aiki,duk yadda yaso hanata tak’i,da ta ji k’arar motar sa za ta yi sauri ta fito ta zuge masa get,sai ta fita ta shiga motar su shigo barandar tare,sannan ta fita ta rufe get d’in,kullum haka take yi,Hamza yana jinjina k’aunar da Hidaya ke masa,duk da yana ganin k’aunar da yake mata ta ninninka wadda take masa.

 

 

 

********************

 

Ranan litinin da safe Hidaya ta fito daga wanka,da sauri sauri take shiryawa domin tafiya makaranta don kar ta yi latti,gogaggun uniform d’in ta ta d’auko ta fara sanya wa a gurguje,Umma ta shigo d’akin da Kofi a hannun ta cike da kunun gyad’a da ya sha madara, a dai dai lokacin da Hidayan ta zame towel d’in jikinta tana k’ok’arin zura riga a jikin ta,idanuwan ta suka sauka a k’irjin Hidaya da suka cicciko sosai suka fara girma,daman tunda al’ada ta zo mata ta fuskanci wani irin girma da Hidayan take yi,musamman k’irjinta da bayan ta,ga kwankwason ta ya k’ara fad’i, jikinta kuma sai k’ara murjewa yake yi,hakan yasa Umma ta ji a ranta ya kamata ta siyawa Hidaya brezia ta dinga sanya wa,kar ta dinga ragaje ragaje a cikin riga tunda sun fara girma sosai.

Hidaya ta waiwayo jin motsin Umma bayan ta saka riga da wandon,ta d’au hijabin ta tana cewa.

“Yau dai na makara Umma,ban ma san lokacin da bacci ya d’aukeni ba bayan nayi sallar Asuba,sai farkawa nayi naga lokaci ya k’ure haka,ni da wuya ma na zauna nayi break fast,na sayi wani Abu a school kawai”

Umma ta mik’a mata kofin hannun ta tana zama bakin gado tace.

“Ungo nan maza zauna ki shanye,ba zaki tafi makaranta da yunwa ba,yau dai gabad’ayan mu makara muka yi,shi ma Hamza Ashe bai farka ba,ina ktcheen na jiyo motsin sa a d’akin sa.”

Hidaya ta amshi kofin ta zauna ta fara kurb’a a hankali,ji take kamar ta tashi sama,bata cika son makara a makaranta ba,ta kusa shan rabin Kofi Hamza ya shigo d’akin,k’amshin turaren sa duk ya baibaye su,yayi matuk’ar kyau cikin shigar shadda Ruwan siminti,ya d’ora hular da ta dace da kayan,sosai yayi kyau kamar wata D’an Daren goma sha biyu…

Durk’usawa yayi yana gaida Umma,ta amsa fuska a sake,Hidaya ma ta gaishe shi,ya amsa yana dubanta sannan ya kalli agogo yace.

“Ke daman har yanzu baki wuce makaranta ba?

Ta dire kofin kunun gyad’a tana cewa.

” Ya Hamza wallahi makara nayi yau,ban san me yasa ma Sumayya bata biyo min ba,ko k’ila tayi gaba”

Ya gyad’a kai yana kallon kofin da ta ajiye da ragowar kunun a ciki.

“Menene wannan…!? Ya fad’a yana kallon kofin.

Tayi dariya da fad’in.
” Kunun gyad’a ne Ya Hamza”

Umma ta dubeshi tace.

“Ko za ka sha a zubo maka?na sanka baka fiye sonsa ba shiyasa,amma ga tea can na dafa maka”
dubi Hidaya da ke gyara zaman hijab d’in ta tana rataya jaka,yace.

“Mik’o min ragowar kunun naki na sha”

Ta D’an zaro idanu tace.

“Ya Hamza ragowata ne fa,shi zaka sha..!?

Yayi mata wani kallo sannan ya dubi Umma yace.

” Umma ji wannan yarinyar da wani zance fa,to yau na saba shan ragowar ki,dalla ni mik’o min kawai”

Ta yi dariya kawai ta mik’a masa,ta in da ta sa bakinta nan ya mayar da na sa bakin ya shanye kunun tas ya dire kofin,Hidaya na ta kallonsa tana murmushi, ya mik’e tsaye ya kalleta yace.

“Wuce muje na direki,daman na san ragin hanya kike so shiyasa kika k’i tafiya,ba wata makara da kika yi”

Hidaya da Umma suka yi dariya,suka yi wa Umma sallama tana ta yi musu addu’ar dawowa lafiya,sannan ta cewa Hidaya idan ta dawo ta shiga mak’ota gidan su Salma ta karb’i mukullin gida,ita za ta je Unguwar sarki gidan wata k’awarta ta dubata bata da lafiya.

Hidaya ta amsa da “To” Sannan suka wace ita da Hamza.

Har k’ofar makaranta ya kaita,sai da yaga shigarta tana ta d’aga masa Hannu sannan ya lumshe idanu duk jikin sa yayi wani la’asar,wani Abu na mintsinin sa a Zuciyar sa game da Hidaya,sai dai har lokacin ya gagara tabbatar da abin da yake ji d’in…gani yake tamkar shak’uwa da tausayi ne kawai ,ba abin da Zuciyar take sak’a masa ba….!

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA ARBA’IN DA UKU DA NA ARBA’IN DA HUD’U

 

 

 

 

K’arfe biyu na rana Hidaya ta taso daga makaranta,tare suka tawo da Sumayya wadda ta kasance k’anwa ga Faisal abokin Hamza,da yake gidan su Sumayyan ya fi kusa da kan hanya a k’ofar Gidan suka tarar da Faisal da wasu abokanan sa guda biyu,zaune kan dandamalin k’ofar gidan suna hira,suna ganin su Hidaya suka bi su da kallo har suka k’araso suka dab da su,Faisal ya washe baki yana kallon Hidaya tamkar ya cinyeta D’an ya,ita kam sunkuyar da kai ta yi cikin kunya ta gaida shi tare da abokanan sa,da hanzari suka dubeta suna amsawa,Sumayya ma ta gaishe su suka amsa.

Suka yi sallama Sumayya ta shige gida,ita kuma Hidaya ta wuce domin k’arasawa gida.

Tana wucewa Faisal ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya girgiza kai yana lumshe idanuwan sa,Habib ya lura da shi,Dan haka ya dafa kafad’ar sa cikin shakiyanci yace.

“Abokina ya dai?na lura duk sanda ka ci karo da yarinyar nan sai ka fita hayyacin ka,ko dai sonta kake ne..!?

Faisal yayi murmushi yace.

” idan ma sonta nake son bashi da amfani,domin na san na zan tab’a samun ta ba ”

“Me yasa kace haka?ka san abin da Allah zai yi a gaba ne? Cewar Habib.

Kan Faisal yayi magana d’aya abokin na su mai suna Shazali yayi magana cikin tab’e baki.

” Ai dole ya fad’i haka Habib,waye zai auri Y’ar tsuntuwa wadda ba a san asalinta ba?duk wannan kyan na ta kyaun D’an maciji ne bashi da wani amfani,Sannan a yadda wannan Hamzan yake kaffa kaffa da ita ka san kansa yake wa tanadi,wa ya sani ma ko tun yanzu yana amfana da ita?domin kulawar da yake bata ta yi yawa wallahi”

A fusace Faisal ya dubi Shazali cikin b’acin rai yace.

“Amma Shazali ka bani mamaki wallahi,ka rasa wa za ka yi wa mummunan zato sai mutumin kirki irin Hamza,Wanda kowa ya san halayen sa na gari a unguwar nan,to idan ma kansa yake wa tanadi ai ba laifi bane,domin duk duniya babu ma Wanda ya cancanta ya kasance miji ga Hidaya sai Hamza,domin shine ya santa fiye da kowa,babu wani namiji da zai bata kulawa fiye da shi,sai dai kuma idan Allah bai k’addari ya zama mijinta ba,Wallahi Shazali ka yi gaggawar yin istigfari,domin ka fad’i magana mara dad’i akan D’an uwanka musulmi Wanda ba hakan ba ne,Manzon Allah (S A W)Yace.

” idan zaka fad’i magana to ka fad’i alkairi ko ka yi shiru…” Don haka ka kiyaye.

Habib yace.

“Tabbas baka kyauta ba Shazali,Ai ko wani kaji ya fad’i irin wannan maganar akan Hamza sai in da k’arfin ka ya k’are,Hamza mutumin kirki ne mai ilimin addini da kiyaye dokokin Allah,Hamza ko nasiha zai maka ya kan kafa maka hujja da ayoyin alk’ur’ani mai girma,Dan Allah ka daina aibata shi Shazali,hakan bashi da kyau ko kad’an”

Shazali ya sauke numfashi cike da nadamar furucin sa,magana zarar bunu,kuma yayi danasanin furtawa,duban su Faisal yayi cikin muzanta yace.

“Insha Allahu ba zan sake ba,sharrin zuciya ne ya saka ni furta hakan da zugar shaid’an,kun san shi shaid’an duk in da yake ba ya son a zauna lafiya,burinsa ya ga ka aikata wani Abu na sab’on Allah,amma ni da kaina na tabbatar da Hamza mutumin kirki ne,Na gode da tunasarwar ku gareni abokai na”

Faisal da Habib suka ji dad’in nadamar furucin da Shazali yayi,nan suka cigaba da hirar su da suke yi akan yadda siyasar Nigeria take garawa.

 

************

Bayan ta karb’i mukulli ta bud’e gidan abin da ta fara yi bayan cire unifoam shine Sallar azahar,tana idar wa ta duba ktcheen ta tarar da abinci cikin kula Umma ta dafa musu kafin ta fita,jalop d’in macaroni da kayan lambu sai k’amshi take,nan da nan ta zuba ta nufi parlour ta hard’e ta fara ci,a Zuciyar ta tana wa Umma addu’a da jinjina fannin iya girki,shiyasa a kullum Umma cikin koya mata girki take kala kala,haka nan idan suka je kano gidan K’anwar Umma Anty Salamatu anan ma tana koyar na zamani,domin Anty Salamatu har makaranta ce da ita ta koyawa mata girkuna na gargajiya da na zamani.

Da ta kammala cin abincin ta mike ta fita da plate d’in ta d’aura ye ta mayar da shi muhallin sa,mukullin d’akin Hamza ta d’auko ta je ta bud’e,gyaran d’aki take so tayi masa,nan ta fara ta gyara tsaf duk da babu wata k’ura kasancewar sa mai tsafta,ta d’ebi singlet d’in sa da gajerun wanduna da ta lura ya saka duk ta wanke masa ta shanya su a toilet d’in d’akin sa,ta kunna burner ta zuba turaren wuta,nan da nan d’akin ya d’auki k’amshi mai dad’i,har zata fita ta lura da wani hoto D’an k’arami a jikin bed side drawer a mak’ale,dawowa tayi ta d’auki hoton tana kallo tana murmushi, mutum uku ne a jikin hoton,gefe da gefe Hamza da Khaleel ne,sai ita a tsakiya,Hamza zaune a cikin studio na gidan redio,ya mak’ala abin saurare a kunnuwan sa,hannayen sa d’auke da takarda yana kallo alamar labarai yake karantawa,fuskar sa d’auke da murmushi,Khaleel kuma zaune cikin wani lambu mai kyau,yana sanye da k’ananan kaya kamar yadda yafi saka su a kowane lokaci,ya hard’e hannuwan sa a kan gwiwoyin k’afafun sa,ya karkata kai ya kanne ido d’aya yana wani smile mai kyau Wanda ya bayyana fararen hak’oran sa farare tas, sai na ta hoton Wanda tayi kyau duk da babu kwalliya a fuskar ta,don lokacin ma shagwab’a take wa Hamza ta turo baki,kanta ko D’an kwali babu,shine ya d’auke ta hoton da wayar sa a lokacin,Hamza yana son hoton Sosai, idan ya kalla yana saka shi nishad’i.

Zama tayi ta na k’arewa hoton kallo,da alamun zuwa yayi aka fitar masa da shi aka had’a da na sa da na Khaleel, ta kai Hannu tana shafa hoton domin duk sun yi kyau sosai,sai da ta kwashe tsawon lokaci kafin ta fito ta rufe masa d’akin.

Kafin Umma ta dawo har ta k’ara gyara gidan Sosai, tayi girkin dare tuwon shinkafa miyar Agushi da taji wadataccen busasshen kifi,sai k’amshi ke tashi,wanka ta fad’a,bayan ta fito tayi hanzarin saka kayanta tayi sallar la’asar ,Dan har lokacin ta ya d’an gota,ta san da Ya Hamza na nan da ta sha fad’an k’etare lokacin sallah,domin baya wasa da sallah kuma baya shiri da mai wasa da ita.

Akwai lokacin da ya sameta tana kallo a TV har akayi sallah bata tashi ba saboda yadda film d’in da take kallo ya d’auke mata hankali,ranar ma Umma bata nan,yana shigowa ya tambaye ta ta yi sallah ta zauna tana kallo?ta fara Sosa kai tana cewa ah ah yanzu za ta tashi tayi,ya kalli agogo yaga tuni lokaci ya k’ure,ai bata tab’a ganin b’acin ransa irin ranar ba,ya dinga zazzaga mata fad’a kamar ya doketa,yace muddin za ta dinga wasa da sallah to za su b’ata,shi kansa yayi mamakin yawan fad’an da ya dinga surfa mata,sai da yaga tana kuka sosai tana bashi hak’uri sannan ya koma yi mata nasiha akan kiyaye sallah da tsananin girman ta a gun Allah (S W A),Bata manta lokacin ba,kanta a k’asa durk’ushe a gabansa tana hawaye,shi ma ya tsuguna yana kallon ta,murya cike da kyautatawa ya fara magana.

“Hidaya a ko ina kika kasance to ki zama mai tsai da sallah akan lokaci da kulawa da sharad’in ta,domin ita ce mafificin Abu,in ji manzon Rahama Alaihis salatu wassalam,haka nan sallah tana sadarwa tsakanin bawa da ubangijinsa,sallah ta kasance ita ce abin faranta ran masana Allah,kuma hutun zukatan su,gata kuma tana hani ga aikata alfasha da mummunan aiki,Allah ta’ala ya ce:

“إن الصلوٰة تنھیٰ عن الفحشاء والمنکر”

(Hak’ik’a sallah tana hana alfasha da mummunan aiki).

Haka nan Allah mai tsarki da d’aukaka yayi kira zuwa kiyaye ta,yace:

“حفٰظوا علی الصلوٰت والصلٰوة الوسطی وقومواللہ قنٰتین”

(Ku kiyaye salloli,da kuma Sallah ta tsakiya,kuma ku tsaya kuna masu biyayya ga Allah)

Hidaya sallah ita ce maraba tsakanin kafirci da imani,domin jabir ya rawaito cewar,manzon Allah (S A W)Yace,”Hak’ik’a abin da ke tsakanin mutumin da kafirci ba wani Abu bane face barin sallah”

Akwai ayoyi da hadisai da yawa da suka yi magana akan Sallah da kiyaye ta akan lokacin ta,farkon abin da za a yi wa bawa hisabi da shi ranar Lahira shine sallah,idan ta cika tayi kyau to dukkanin wasu ayyukan bawa sun yi kyau ,idan aka samu akasin haka kuma sai innalillahi wa inna ilaihir raji’un,Dan haka Hidaya ina yi miki wasiyya da ki kiyaye sallah!ki gabatar da ita yadda Allah yace ayi,kuma ki yi ta akan lokacin ta,sannan ki kyautata ta”

Sallamar Umma ce ta katse Hidaya daga tunanin ta,ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana amsawa,Zuciyar ta cike da k’aunar Ya Hamza saboda kyawawan d’abi’un sa da kiyaye dokokin Allah.

 

 

*****************

Da daddare tana kwance akan kujerar parlourn Umma da wayar ta a hannun ta tana chatting, hira suke ita da Khaleel cikin Annashuwa da jin dad’i,Hidaya sai k’yalk’yala dariya take yi,har Umma ta gaji da jiyo dariyarta daga d’aki ta leko tana kallon ta tace.

“Wai ke lafiyar ki kuwa kika ishi mutane da dariya..!?”

Hidaya ta d’ago kai ta kalli Umma fuskar ta d’auke da murmushi sosai tace.

“Wallahi Umma Uncle Khaleel ne yake ta saka ni dariya fa,kin san shi da zaulaya”

Umma ta girgiza kai ta na cewa.

“Ai shikenan Allah ya shirye ku” Ta juya da nufin komawa d’aki,da sauri Hidaya ta tare ta da cewa.

“Umma wai ina Ya Hamza ya shiga ne?tun d’azu banji shigowar sa ba”

“Ya tafi zance wajen budurwar sa….!

Umma ta ambata kai tsaye tare da shigewa bedroom.

Hidaya da ke kwance taji saukar maganar tamkar aradu,ta mik’e da hanzari a gigice tana zare idanuwa ta,mik’ewa tayi da sauri ta bi Umma d’akin,ta tarar da ita tana shirin tub’e kayan ta domin shiga wanka,Hidaya ta k’arasa da sauri ta rik’o hannun Umma tana firfito da idanu,cikin rawar murya tace.

” Umma me kika ce?kamar naji kince Ya Hamza ya tafi zance gun budurwar sa?kamar haka kunnuwana suka ji ko…!?

Umma ta dubeta tace.

“Eh haka nace,tad’i ya tafi,daman bai gaya miki bane?

Haka kawai Hidaya taji k’irjinta na tsananin bugawa kamar ya fad’o,taji Zuciyar ta ta yi zafi Sosai,hawaye ya ciko idanuwan ta jikin ta ya kama rawa,a sanyaye ta saki hannun Umma ta juya baya,bata son Umma taga hawayen ta,cikin wata irin murya da saura kad’an ta fashe da kuka tace ” bai gaya min ba Umma,ban ma san yana da wata budurwa ba…”

Umma ta kalli bayanta da ta juya d’anyi murmushi sannan tace.

“Ayya!ni na zaci ma ya fad’a miki saboda naga ke ce abokiyar shawarar sa,sai ku hak’a ku binne ba tare da na sani ba,to amma ya naga kamar ranki ya b’aci da maganar?ko baki yi farincikin jin cewar yayanki yana da budurwa zai yi Aure ba?

Tamkar an cakawa Zuciyar ta mashi haka taji,a lokacin tuni hawaye ya fara gangarowa kan kumatun ta,cikin k’ank’anuwar murya tayi magana.

” ina farinciki Umma,kawai dai nayi mamaki ne da bai fad’a min ba…..

Ta kasa k’arasawa saboda yadda muryar ta ke shak’ewa,Umma ta girgiza kai ganin yadda Hidaya ta rud’e sosai,sai kawai ta share zancen ta mik’a Hannu ta d’auko wata bak’ar leda tana cilla mata sannan tace.

“Hmmm wannan kuma ita ku ke da shi,ba mai shiga tsananin ku ku bashi kunya, ni ga tsaraba nan na siyo miki da na fita d’azu,ki d’auka ki bud’e sai ki ga idan sunyi miki”

Tana fad’in hakan ta shige bathroom ta bar Hidaya tsaye k’ik’am cikin fitar hayyaci da sarawar kai,a dai dai lokacin ne kuma Hamzan ya d’aga labulen d’akin ya shigo da sallama,Hidaya ta kasa amsawa ta bi shi da kallo tamkar idanuwan ta su fad’o,ita sai taga ma bai tab’a yi mata kyawu kamar lokacin ba,sai k’amshi yake zubawa ya d’au wanka,sai ta ji wani bak’inciki a ranta tamkar Zuciyar ta ta babbake,ta tabbata daga gun budurwar shi yake kenan?shine har da gayu haka,duk da dai kowane lokaci cikin gayun yake.

Kallon juna suka fara yi cikin wani yanayi,tsugunawa yayi a hankali ya d’auki ledar da Umma ta cillo mata ya rik’e a hannun sa yana kallon ta,ya matso dab da ita yana fad’in.

“Hidaya me ye wannan…!?

Ta kautar da kai tana Jan hanci,ya sake karkata kansa in da ta mayar da na ta kan yana kallon fuskar ta da ta sunkuyar yace.

” Zan shigo kenan naji Umma na cewa ga tsabar da ta siyo miki,ni gaskiya Hidaya ban yarda ba kullum idan Umma ta fita ke take siyawa tsaraba,amma ni ba a min kara a D’an siyo min,yau dai ko me Umman ta siyo miki sai dai mu raba tare ni da ke aha”

Wani takaici ya kamata,yaje ya dawo daga wajen budurwa tad’i zai zo ya dame ta da zance,karo na farko a rayuwar ta da ta tab’a jin zafin Ya Hamzan ta a ranta kenan,Hannu ta kai cike da haushi za ta fizge ledar ,yayi saurin d’agawa sama yana matsawa,fuskar sa d’auke da murmushi yana girgiza kai yace.

“Ah ah K’anwata,ki bari na kwance sai a raba biyu ki d’au rabi na d’au rabi”

Hidaya ta shagwab’e fuska sosai,ta fara tsalle tana son cafko ledar,shi kuma ya k’i bata damar hakan,idan ya d’aga sama sai ya sauke hannunsa k’asa ya b’oye a bayan sa,yana zagaye d’akin yana dariya,ita kuma sai bin sa take tana son ya bata,ganin sai wahalar da ita yake yi sai ta kama dira k’afafu a k’asa cike da shagwab’a tana son yin kuka tana cewa.

“Ya Hamza ni ka bani Abu na mana ….

Mak’e ka fad’a yayi kamar yaro,yana murmushi yace.

” Na k’i,ni fa yau sai mun raba ko menene a cikin ledar nan…!

Da taga ba zai bata ba wahalar da ita yake yi kawai sai ta tsaya cak tana duban sa,shi kam a hankali ya fara warware k’ullin ledar yana bud’ewa,yana kammala bud’ewa ya zazzago abin da ke ciki,kawai sai ga brezia kusan guda shida masu soso,sababbi dal y’an k’anana dai dai Brest d’in Hidaya….da sauri Hamza ya sake su a k’asa suka tarwatse tamkar ya tsorata,ya d’ago kansa suna kallon juna shi da Hidaya ,dukkan su cikin zare idanuwa da dukan k’irji………!

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA ARBA’IN DA BIYAR DA NA ARBA’IN DA SHIDA

 

 

***Wani irin kallo ya bita da shi kafin ya D’an sunkuyar da kai yana Sosa k’eya,ita kam Hidaya jikinta ne ya kama rawa kar kar ganin Abubuwan da suka zubo a ledar,tayi k’asa da kai cikin wata muguwar kunya da ta rufe ta,a dai dai lokacin kuma Umma ta bud’e k’ofar bathroom ta fito daga wanka,k’arar bud’e k’ofar ya k’ara firgita su suka wani zabura kamar su ruga da gudu,Umma ta bi su da kallo sannan ta dubi brezia d’in da ke zube a k’asa a watse,Hamza kamar ya nutse don kunya,cikin azama ya d’aga k’afafu yayi saurin ficewa daga d’akin har da had’awa da D’an gudun sa.

Yana fita Umma ta maida kallon ta kan Hidaya da ke tsaye tsamo tsamo kai a sunkuye,cikin alamun fad’a fad’a Umma ta fara magana.

“Yanzu ke Fad’imatul Hidaya baki da wani Sirri na kanki kenan?komai da ya shafeki sai kin fad’awa Hamza ko kin nuna masa?rigar nono ma da ake son sayata sai da kika nuna masa?to me kike so ya gani kenan?iya gejin girman da k’irjinki ya fara ko kuwa…!?

K’irjin Hidaya ya buga da k’arfi,Hawaye ya tawo mata,nan da nan ta fashe da wani irin kuka tana cewa.

” Ni wallahi Umma bai nuna masa nayi ba,shine fa ya k’wace wai sai dai mu raba abin da kika siyo min,ni dai wallahi ba ruwana ba laifi ba bane…!

Umma ta D’an yi mata gwalo yadda ba zata gani ba,ta juya baya tana D’an murmushi ta k’ara kunna Hidaya,domin cewa tayi.

“To shi da bashi da nonuwan saka brezia mai zai yi da ita?sai dai da yake ya kusa Aure sai ki bashi ko guda uku ya saka a lefe kawai,duk da k’ananu ne ina tunanin za ta yiwa matar da zai aura kad’an…”

Hidaya ta ji kamar Umma ta caka mata wuk’a a k’ahon zuciya,kawai sai ta sake rushewa da kuka ta fad’a gadon Umma tana jin zuciyar ta na ciwo,Umma ta tab’e baki ta nufi wardrobe tana cewa.

“Ai sai ki yi ta kukan…!tun da baya miki wahala…!”

 

 

 

******************

 

Duk ranar Hidaya haka ta kasance kamar mara lafiya babu walwala,hawaye kuwa har gajiya suka yi da zuba,haka kawai da ta tuna cewa Ya Hamza yaje zance wajen budurwa sai ta kama hawaye,ta rasa me yasa hakan,bata san me yasa take jin b’acin rai idan taga Hamza ya kula wata mace ba,duk da ma bashi da kule kulen y’ammata,duk abin da take Umma na lura da ita,Sosai taji dad’in yadda ta kunna Hidaya,a wani salo na ta na son cimma k’udurin ta,haka nan take tunanin saura Hamzan shi ma.

 

Washe gari Hidaya ta tafi gidan su Sumayya za su yi karatun jarrabawa,Umma ma ta D’an fita,sai Hamza kawai da bai fita Aiki ba,saboda ciwon kai da ya tashi da shi,yana kwance a parlour’n Umma akan doguwar kujera,idanuwan sa a lumshe,tunane tunane sun cika zuciyar sa,har Umma ta d’aga labulen d’akin ta shigo da sallama bai ji ba,sai da ta ambaci sunan sa da k’arfi sannan ya bud’e idanuwan sa da suka sauya kala,ya mik’e zaune yana dafe kansa,cikin kasalalliyar murya ya dubi umma da ke tsaye da k’atuwar Leda a hannun ta fal da kaya yace.

“Umma har kin dawo?sannu da dawowa.”

Ta nemi gefen sa ta zauna,sannan ta amsa.

“Yawwa sannu ya kan na ka?ko har yanzu yana ciwon ne…!?

Ya lumshe idanuwan sa.

” yana yi Umma,amma dai ya ragu tunda na sha magani”

“Allah ya k’ara sauk’i,Allah ya sa ba maleria ba ne…..wai har yanzu Hidaya bata dawo ba ne…?

Ta zarce da tambayar sa.

Ya jijjiga kai ya jingina da bayan kujerar yana lumshe idanuwa,ambatar sunan Hidaya kad’ai na tab’a ruhin sa.

Umma ta D’an sa ci kallon sa tace.

” Aikuwa ya kamata ta dawo gida haka,ko Dan ta duba kayayyakin nan da na siyo mata idan sun yi mata ….

Ya bud’e idanu a hankali ya dubi Umma,sai Umma ta sake cewa cikin murmushi.

“Au!tunda ma gaka ai sai ka tayata dubawa,domin naga kusan ra’ayin ku ya zo d’aya,kayan Auren ta na fara siya domin na fara ragewa,kar lokacin ya zo Abubuwa suyi min ya…….

Maganar Umma ta katse saboda wata zabura da taga Hamza yayi cikin zare idanuwa yana kallon ta,a rikice yace.

” Aure kuma..!?wane irin Aure Umma..!?Hidayan za a yi wa Aure..!?

Ya jero tambayoyi.

Umma ta mik’e ta nufi hanyar d’aki tana cewa.

“Au wai ban gaya maka ba daman?Ai na kusa Aurar da Fatima,Auren wuri zan mata ba zan barta ta sangame ba..kai dai da ka zama tuzuru ka k’i Neman matar Aure kai ta zama Hamza…Hidaya kam nan da wani lokaci k’ank’ani za ka ganta a gidan mijinta”

Tana kammala magana ta shige d’akin ta ta barshi sake da baki da hanci da idanuwa,cikin wani yana yi na miliyoyin tashin hankali da firgitarwa…..!

Umma kam tunda ta shige d’aki take murmushi mai kama da dariya,tana ganin wasan da ta buga tsakanin Hamza da Hidaya zai yi tasiri kamar yadda take so….

 

 

****************

Kwana biyu da hakan Hamza da Hidaya suna cikin damuwa,ita Hidaya ma kam kullum sai ta yi kuka,a ganin ta Ya Hamza yayi mata babban laifi da har ya kasa sanar da ita ya samu matar Aure,sai dai taji maganar a bakin Umma,wannan babban laifi ne da take ganin yayi mata,saboda basa b’oyewa junansu sirrikan su,amma Ya Hamza ya b’oye mata wannan,haka nan kuma take jin tsanar wadda yake so d’in duk da bata san kowace ce ba.

Daga b’angaren sa shi ma hakan take!ko nace ma ya zarce hakan,domin Hamza ko bacci ba yayi sai yawan tunani,babu abin da ke cin Zuciyar sa irin idan ya tuna da kalaman Umma,wai zata aurar da Hidaya,to ga wa zata aurar da ita?ga wani haushin Hidayan da yake ji ganin ta b’oye masa,domin gani yake ai ta san komai,Hamza dai har wata rama yayi ta musamman saboda damuwa,sai suka zama sirikan juna shi da Hidayan,babu kulawa da juna da zama suyi hira da juna kamar yanda suka saba,ko cikakken kallon juna basa yi sai dai a dinga satar kallo,da an had’a idanuwa ayi saurin kau da kai ana basarwa,Hidaya na ganin Ya Hamzan ta ya daina yayin ta,tunda ya samu mai d’ebe masa kewa,ya bata matsayi fiye da na ta,in ta tuna hakan sai hawaye ya zubo mata,sai ta faki idanun Umma ta share.

Haka Hamza ma ke ganin Hidayan a matsayin wadda ta juya masa baya,a ganinsa ta samu Wanda ya fishi,shiyasa ta daina bashi kulawa kamar baya,duk da bata daina yi masa komai ba,kullum ita take dafa masa abinci,ta gyara masa d’aki,tayi wankin singlet da jallabiyoyin sa,da duk wani aiki da ya dangance shi,yawan zama suyi hira ne da magana kawai ta daina.

Umma na kallon takun su,tana murna tayi Abu domin su hankalta,sai taga Abu na neman zame mata D’an zani,yo D’an zani mana!ita a yadda ta lura tun Hamza da Hidaya na da matakin k’ananan shekaru suka fad’a tarkon Soyayya da K’aunar junan su,har kuma zuwa girman su,amma har izuwa wannan lokaci sun kasa yardar wa junan su cewa son juna suke so irin Wanda yake rikid’ewa ya zama Auratayya,a ganin su so irin na Yaya da k’anwa kawai suke yi,shine dalilin da ta jefa wannan game d’in a tsakanin su wai domin su Ankara su furtawa junan su Soyayya,amma inah!sai ta lura ma gabad’aya sun kaucewa tsarin,a maimakon k’udurin ta ya tabbata,sai wankin hula yake son kai ta dare.

Sai dai duk da hakan ta zuba musu ido domin taga gudun Ruwan su,sannan tana addu’ar idan da alkairi a lamarin Allah ya tabbatar.

Ko da Hamza suka yi waya da Khaleel sai da ya gane yana cikin damuwa,yayi ta tambayar sa dalilin damuwar amma ya kasa sanar da shi komai,to me zai ce masa?saboda za a aurar da Hidaya yake fushi ko me?tunda dai shi bai furta yana son Hidayan ba balle a ce kishi yake,tilas Khaleel ya k’yale shi,sai kuma ya wanke masa zuciya da albishir d’in dawowar sa Nigeria a cikin wannan satin,a matsayin cikakken Lauya me kare hak’k’in D’an Adam,musamman wad’anda aka zalinta.

Wannan albishir tamkar na zuwa aikin hajji ya zame wa Hamza,farinciki ya yawaita a Zuciyar sa Wanda ya jima bai ji irin sa ba ko makamancin sa,saboda murna ko kammala wayar basu yi ba ya katse ta ya ruga parlour’n Umma fuska kamar gonar auduga domin kai rahoto.

Umma na zaune k’afafuwan ta kan cinyar Hidaya tana yanke mata farce,ya fad’o d’akin kamar an jeho shi har sai da suka razana,Umma ta dubeshi tace.

“Kai lafiyar ka kuwa…!?

Ya k’arasa gaban ta ya tsuguna har kafad’ar sa na k’ok’arin gogar ta Hidaya,ta yi hanzarin matsawa,ya rik’o hannun Umma yana wata irin dariya yana fad’in.

” Umma na ki tayani murna,cikin satin nan Khaleel d’ina zai dawo k’asar nan gabad’aya…yanzu ya gama yi min albishir….

Wani irin farinciki ya kwarara a Zuciyar Umma,har ma da Hidaya da tsananin murna ya sa tamkar ta tashi ta buga tsalle,ta rufe bakin ta da hannayen ta tana zaro idanu cikin tsananin murna,Umma kam hamdala kawai take wa Allah da jin wannan magana,lallai tilas a taya Hamza murnar dawowar babban abokin sa Wanda ya zame masa D’an uwa….

Juyawa yayi yana duban Hidaya,suka had’a idanu,wasu kibiyoyi suka tsikari cikin idanuwan su,k’irjin su yayi wata irin bugawa,tsigar jikin su ta tashi,da sauri Hidaya ta kautar da idanuwan ta,ta mik’e da hanzari ta fad’a d’akin Umma,shi kam Hamza bin ta yayi da idanu tamkar dolo,yana lumshe idanuwa da sakin wata nannauyar ajiyar zuciya…..

Umma ta bi shi da kallo yayin da na sa idanuwan ke kan k’ofar d’akin Umma da Hidaya ta shige….!

 

 

 

****************

Cikin kwanakin sai Hidaya ta samu walwala sosai,ba domin komai ba sai yawan kiranta da Khaleel yake su sha hira,ko suyi video call har ta watsap hira suke sha,da yake Khaleel gwanin iya tsara zance ne,gashi da shagwab’a tamkar mace,yanayin yadda yake magana kad’ai wani zubin yana narkar da Zuciyar Hidaya.

Khaleel kam tuni yake son fallasa asirin Zuciyar sa game da Hidaya,wata soyayya yake mata wadda bai tab’a tunanin akwai ta a duniya ba,tun ranar da ya fara ganin ta yaji fad’uwar gaba sonta ya addabeshi,ya rayu da soyayyarta tsawon wannan lokaci,Wanda ko Hamza bai furtawa ba saboda yana jiran ya dawo k’asar sa gabad’aya sannan ya bayyana manufar sa,

Da gaske yake son Auren Hidaya domin ya taimaki rayuwar ta,ya inganta ta ta yadda zata zama d’aya daga cikin matan da duniya zata yi alfahari da su,yana son Hidaya,so mara misali,yana ji a ransa kuma ita ma zata so shi,haka nan kowa zaiyi alfahari da Auren su.

Hamza kam sai ya share ta,ganin yadda ta watsar da shi kawai sabgarta take,shi ma ya shiga sabgar shirye shiryen taron Jinin jikinsa wato Ibraheem Khaleel…

Saura kwana d’aya Khaleel ya dawo Hamza na zaune a d’akin sa,waya ce a kunnen sa,fuskarsa d’auke da murmushi suna hira da Khaleel,Khaleel d’in sai shagwab’a yake masa wai shi yake so yazo Abuja ya tarbeshi a airport, shi kam Hamza tsoron had’uwa da daddy yake yi,sai Khaleel ke ce masa kar ya ji komai in dai daddyn sa ne ya sauya,ya fara watsar da halayen sa mara sa kyau,Dan har ce masa yayi yana jin kunyar abin da yayi wa su Hamzan a rayuwa,kuma zai nemi afuwar su,nan da nan Hamza yaji farinciki ya kamashi,ya tabbatar wa Khaleel cewa insha Allah gobe da wurwuri zai tawo Abuja,domin yana son jirgin ma ya sauka a gaban sa,Khaleel yayi ta murna,daga k’arshe ya sanyaya murya yace da Hamza.

“Abokina ina son mu tattauna wata magana ni da kai,amma mu barta sai na dawo sai mu yi insha Allah…”

Hamza ya sauke ajiyar zuciya yace.

“Ni ma ina son yin magana da kai akan wani Abu da yake damuna,amma bari na bar maganar zuwa lokacin da zaka dawo sai mu tattauna gabad’aya ko….?

Khaleel yayi murmushi yace.

” Aboki ka san yanayin da muryarka take ciki kuwa…?

Hamza ya amsa da .

“Ah ,ah,wane yanayi take ciki..!?

Khaleel ya kwashe da dariya yace.

” Allah ta yi min kama da Wanda ya fad’a tarkon soyayya,Aboki ko ka fara soyayya ne ban sani ba…?

Hamza ya lumshe idanu,k’irjinsa na bugawa sosai yace.

“Ta ya ya kayi saurin d’agoni Khaleel? Ya ya akayi ka gane zuciyata ta fad’a tarkon soyayya?

Khaleel ya sauke numfashi ,a hankali yace.

” saboda ni ma ina cikin irin yanayin …..ni ma na fad’a tarkon Soyayya da K’auna…!

Hamza yayi k’asa da murya yana jin shauk’i kamar ya narke,ya lumshe idanuwan sa ya rufe su ruf sannan ya cewa Khaleel.

“Haka kawai ta addabi zuciyata Khaleel, yanzu haka da sonta nake rayuwa a jikina,raina na sonta,zuciyata na k’aunar ta,idanuwana na begenta,jikina na mararinta,bana bacci Khaleel ,saboda yadda tunanin ta yake tsinkamin zuciya,daman haka so yake Khaleel…!?haka yake da narkar da Zuciyar ma’abota Soyayyah…!?

Shi ma Khaleel ya sanyaya murya,cike da shauk’i ya fara bawa Hamza amsa da hanzari.

” Eh Aboki,tabbas duk abin kake ji akan wadda kake so nima haka nake ji akan wadda nake so,ko ma fiye da haka,ta makantar da idanuwana fa,ta to she kunnuwana daga jin duk wata dad’in magana idan na tata ba,ta kanainaye ruhina da sassan jikina gabad’aya,sai nake jin muddin ban sameta a duniyata ba zan iya rasa raina Aboki……fatana idan na ambata mata soyayya ta ta rik’e hannuwana ta kaini inuwarta,sannan……

Ya kasa k’arasawa saboda yadda shauk’in soyayya yake tab’a ruhinsa,shi kam Hamza idanuwan sa a lumshe suke,Ashe da shi da Khaleel d’in duk d’aya ne kenan!tunda duk cikin su babu Wanda ya bayyana wa wadda yake so soyayyar,idan kuwa hakane lallai suna ruwa…..

“Ina sonta Khaleel….ta shiga zuciyata saboda tarbiyyarta da nutsuwar ta,son da nake mata shine farincikin duniyata…ina samun lafiya ne idan har ina tare da ita….ruhina na fad’a min da ita na dace a zaman duniyata….zuciyata na martaba ta…ita ce mafarkina a kullum….ina sonta adadin yadda baki ba zai iya furtawa ba…….

Hamza ya furta wad’annan maganganun a lokacin da hawayen soyayya suka ratso fatar idanuwan sa.

” Wow…!Khaleel ya ambata cikin karad’i,sannan ya zarce da magana cikin wani yana yi.

“Lallai Aboki ka zarme da yawa,daman fa an ce irin ku Malamai kun fi kowa iya soyayya,zan so sanin wadda ta zama mai nasara,eh dole na kira ta mai nasara,domin sai mai nasara ce zata same ka a matsayin miji….don Allah Aboki wacece ….!?

Har lokacin idanuwan Hamza a lumshe suke,yayi ajiyar zuciya yace.

” H….

Maganar sa ta katse lokacin da yaji motsi a gabansa,ya bud’e idanu a hankali,sai ya ci karo da Hidaya a gabansa,wadda ke rik’e da flask a hannun ta ta kawo masa abinci,kuma tun kafin ta shigo d’akin take jin wasu irin kalamai da Ya Hamzan yake furtawa akan wacce yake so…kalaman da suka kusa fasa mata k’ok’on kanta,kalaman da ta ji tamkar zubar garwashin wuta a filin zuciyarta…bata san lokacin da k’afafuwan ta suka yi a zarb’ab’in shigewa d’akin ba tare da sallama ba,idanuwan ta cike da hawayen da ta rasa ko na menene…

Wani kallo Hamza ya bita da shi idanuwan sa na narkewa,da gasken gaske Hidaya ta gama da ruhinsa gabad’aya,ita kam wani haushin sa take ji,shiyasa kawai ta dire flask d’in abincin ta juya da hanzari gudun kar yaga hawayen ta…cikin wani yana yi bakin sa yayi azarb’ab’in kiran sunan ta da rawar murya….

“Hidayaaaaaaa…..!

Ta tsaya chak! Ba tare da ta juyo ba,k’afafuwan ta na rawa,tana fata da d’okin jin cewa akan ta yake furta wad’annan kalaman,sai dai ina!ta san da wata yake,Ya Hamza a matsayin K’anwa ya d’auke ta,ta rasa ma ta yadda aka yi zuciyarta ta fad’a kogin sonsa,duk da zuciya tana son mai kyautata mata…kuma Ya Hamza shine Wanda ya kyautata wa rayuwar ta tun daga yarinta zuwa girman ta ….tilas ya zama abin so a gareta….

A maimakon taji muryar sa ta ambata mata abin da take fatan ji !kawai sai ta tsinci muryar da ambata mata cewa.

” Ki shirya gobe da wurwuri za ki rakani Abuja domin mu tari Khaleel a airport…….!

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

 

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA ARBA’IN DA BAKWAI DA NA ARBA’IN DA TAKWAS

 

 

 

***Wani irin shock taji a jikinta,ta samu Zuciyar ta da shiga K’unci,amma haka ta daure ta amsa cikin rawar murya ba tare da ta juya ba.

“To Ya Hamza,Allah ya kai mu goben lafiya….!

Tana fad’in hakan ta fice da hanzari,ya bi ta da kallo yana sauke ajiyar zuciya,sai lokacin ya tuna ma Ashe waya yake da Khaleel, hakan yasa ya maida wayar kunnen sa suka cigaba da magana.

 

Da ya sanar da Umma cewar zai d’auki Hidaya su ta fi Abuja taren Khaleel da k’yar ta amince,sai da ya dinga yi mata magiya tukunna,haka kawai taji a ranta bata son ya tafi da Hidayan,bata san kuma menene dalilin hakan ba,tunda ya sha d’aukar ta su ta fi kano dangin Umman,kuma suje lafiya su dawo lafiya ba tare da wani Abu ba.

Washe gari kam k’arfe takwas na safe sun shirya tsaf !daga Hidayan har Hamza suna ta fama da fad’uwar gaba wadda basu san ko ta menene ba,haka nan Hidaya ta kwana da tunanin wayar da suka yi ita da Khaleel a Daren jiya,wadda yake fad’a mata cewar ta taimake shi ta bi Hamza Abuja domin tararsa,yana so yayi wani Abu da zai bata mamaki,ta kasa gane me yake nufi,sai dai ta samu Zuciyar ta da fargaba sosai akan wane mamaki uncle Khaleel yake son ba ta…?

Kamar had’in baki,kayan da Hamza ya sanya iri d’aya ne da na Hidaya,wani boyel ne me kyau green da ya d’inka musu tare,yayi musu kyau sosai,Hidaya ta sha d’inkin doguwar riga wadda ta kamata daga sama,ta bud’e daga k’asa,ta saka farin Mayafi da fashion fari na sark’a da yari,sai agogo shi ma fari,mayafin ta da takalmin ta ma fari ne, Wanda ta yane jikinta da shi,babu kwalliya sosai a fuskar ta illa powder da wet lip da ya sa lips d’in ta suke k’yalli da walwali,don Hamza har satar kallon bakin ta ya dinga yi….

Shi ma sai yayi amfani da farar hula mai ratsin green a ciki,da takalmi green,wani irin kyawu suka yi na ban mamaki tamkar wasu fure,Umma kanta ta k’yasa su,ta dinga murmushi tana kallon su tana addu’a a Zuciyar ta na cikar burinta,har bakin mota ta raka su tana musu fatan alkairi da isa Abuja lafiya.

Sun fara tafiya a kan titi shiru babu me magana,Hamza na kallon gabansa yana tuk’i,Hidaya kam tana kallon gefen hanya da bishiyoyin da su ke wucewa,k’amshin da Ya Hamza yake ya saukar mata da wata irin kasala,duk yau sai taga yayi mata wani mugun kyau da bata tab’a gani a tare da shi ba,fatarsa har wani shek’i take,Zuciyar ta ta sake rauni sosai,tana ji ina ma Ya Hamza ya bayyana mata soyayyar sa,da sonsa ta rayu,babu wani namiji da take jin ya tunbatsa a filin Zuciyar ta sai shi,amma irin kalaman da taji yana zayyanawa akan wacce yake so jiya ya tashi hankalin ta,kwana tayi tana hawaye,da zarar ta ga Umma zata ga hawayen ta sai tayi saurin sharewa,ta san Ya Hamza yayi mata nisa,yanayin yadda yake bata kulawa tamkar alamun so ta d’auke shi,Ashe Zuciyar ta bata gaya mata dai dai ba,gara ma tun wuri ta cireshi a ranta ta maidashi matsayin sa na baya wato yayanta,tunda shi ma a k’anwa ya d’auke ta.

Da taji Zuciyar ta ta dameta da tunani sai ta kife kanta a kan cinyar ta kawai tana sakin ajiyar zuciya,hawaye na son tawo mata,ita kuma bata son ya gani balle ya fuskanci yanayin da take ciki

A b’angaren Hamza shi ma tuk’in kawai yake yi,amma Zuciyar sa na ga Hidayan,ji yake tamkar ya d’auke ta ya tsaga k’irjinsa ya cillata filin Zuciyar sa ya rufe,yau yake son ya kawo k’arshen komai!burinsa ya had’u da Khaleel ya fallasa masa sirrin Ruhin sa domin ya samu sauk’i,daga nan kuma sai ya tunkari Hidayan,ya jinkirta bai sanar da ita bane saboda bai ma san ta yadda zai fad’a mata ba,ya tabbatar Khaleel zai bashi shawarar hanyar da zai bi domin ya sanar da itan,shi kuma Khaleel sai ya sanar wa Umma,saboda yana jin kunyar kallon tsabar idanun Umma ya fad’a mata cewar yana son ta bashi Hidaya ya Aura….

Har suka isa Abuja babu Wanda ya kula wani a tsakanin su,su Kansu suna mamakin yadda suke share junansu kamar wasu abokan gaba.babu abin da ke tashi a motar sai saukar numfashin su da kuma karatun alk’ur’ani da Hamza ya saka a motar,shiyasa ma suka sami Kansu cikin nutsuwa sosai.

A hankali ya shiga da motarsa airport d’in ya faka ta,ya kalli agogon hannunsa sai yaga lokaci har ya k’ure,tuni jirgin da Khaleel ya hau ya sauka,hanzari kawai yake domin yayi ido biyu da Khaleel, amma dole ya fara Neman toilet ya rage mararsa saboda wani fitsari da ya matse shi sosai,ya kashe motar yana wani lumshe idanu da fad’in”Alhamdulillah “Sannan ya waiwaya ya dubi Hidaya da sai lokacin ta d’ago kanta,ya D’an tsura mata idanuwan sa yana duban ta,ita kam sai ta sunkuyar da kai tana wasa da zoben hannun ta,saboda bata son kallon tsakiyar idanuwan sa,ya sauke ajiyar zuciya ya ambaci sunanta a hankali.

” Hidayaaaaaa….!

Kanta a k’asa ta amsa tana muskutawa,taji kiran har cikin tsakiyar kanta,tsigar jikinta na mik’ewa yarrrrr !

Ya D’an yi baya da hular kansa ya shafa goshinsa,sannan ya sake kallon ta yace.

“Ki D’an yi min hak’uri kad’an ki zauna cikin motar,zan je na gabatar da wani uzuri ko da minti biyar ne,idan na dawo sai mu shiga ciki,don na san tuni Khaleel ya sauka yana jiran mu.

Gyad’a kai tayi kawai,murya a sark’afe tace.

” To Ya Hamza……!

Yayi murmushi sannan ya b’alle murfin motar ya fita,sai lokacin ta sake d’aga idanu ta bi bayansa da kallo,tafiyar sa kan ta abar Sha’awa ce,yana tafe a nutse cikin wani irin kwarjini da Allah yayi masa baiwarsa,baki sake take kallon sa har ya shige wata kwana,sai lokacin ta d’auke idanuwan ta ta runtse su tana sauke ajiyar zuciya, sai ta samu bakin ta da furta cewar.

“Ya Allah na! Ina rok’on ka ka bani Ya Hamza a matsayin mijin Aure na,Ya Allah kai ne ka halicci zuciyata da sonsa tun ban san menene son ba !Ya Ubangiji na mamallakin komai da kowa ina son Ya Hamza,ina k’aunar sa,shi kad’ai nake so Ya Allah !sarki na ina Neman taimako gareka ka cika min burina,kasa Ya Hamza ya zama alkairi a gareni…..!

Ta share k’wallarta da gefen hannun ta,ta koma ta jingina da kujerar ta tana lumshe idanuwanta, kusan minti goma tana a haka ba taji dawowar Ya Hamza ba,a hankali ta bud’e idanuwan ta,tana hangen mutane jefi jefi suna kai kawo a harabar airport d’in,bata san me yasa ba,kawai sai ta tsinci kanta da bud’e murfin motar ta fito,ta shak’i wata iska mai dad’i ta lumshe ido,rufe motar tayi ta jingina da ita tana gyara lullub’in gyalen da ke jikinta,mutane na wucewa wasu na kallon ta ,musamman maza,sai taji ina ma bata fito ba,sai dai ta gaji da zaman motar ne gabad’aya, shi kuma Ya Hamza daga minti biyar yanzu kusan inti goma sha biyar kenan amma shiru bai dawoba,haka dai ta cigaba da tsayuwa jikin motar tana son ganin ta in da Ya Hamzan zai b’ullo.

 

 

 

*****************

Shi kam Hamza ya samu ya rage mararsa sai yaji sakayau,ya fito daga toilet d’in Wanda ya kasance na maza(male).

Yana fitowa zai karya kwana in da zai samu Hidaya kawai sai idanuwan sa suka kai kan wata mata,k’irjinsa yayi bala’in bugawa saboda yadda matar tayi masa mugun kama da Mummyn Hidaya,domin ko daga barci ya tashi zai iya shaidata,ya bita da kallo bakin sa a sake k’irjinsa na dokawa,ganin tana shirin b’ace masa da hanzari ya taka yabi bayan ta,sai dai yadda jikinsa ya mutu sai ya kasa sauri,illa d’aga mata Hannu da ya dinga yi yana ambatar .

“Mummy…Mummy…Mummy….!

Ko waiwayowa bata yi ba,domin bata san ma yana yi ba,yana biye da ita yana k’wala kiranta har suka je wajen wasu dandazon mutane da kowa yake harkokinsa,tana shigewa cikin mutanen nan ya nemeta tsaf ya rasa,nan da nan ya rud’e shi ma ya kutsa tsakanin su yana ta dube dube idanuwan sa a warwaje,Iya duban da zai yi baiyi nasarar ganin ta ba,a rikice ya fara bin mutane yana tambayar su wai basu ga wata mata sanye da bak’ar doguwar riga ba,wasu suce basu ganta ba,wasu kam kallon tab’ab’b’e suke masa duk da gashi nan tsaf da shi,amma yadda yake magana a rikice jikinsa na rawa sai suke ganin yana da matsala k’ila…

Hamza haka ya dinga zagaye gurin yana fatan idanuwan sa suyi katarin ganin ta,amma ko mai kama da ita bai gani ba,kamar yayi kuka haka yaji,ya dafe kansa yana ambaton Allah.

 

 

*****************

 

A hankali yake tako steps d’in jirgin domin sakkowa,cikin jerin mutanen da suke k’ok’arin sakkowa,sanye yake da suite bak’a wadda ta amshe shi,idanuwan sa sanye da bak’in glass da ya k’ara masa kyau kasancewar sa fari tas,sai da ya sakko k’asa sannan ya kai Hannu ya zare glass d’in yana kallon mutanen da ke warwatse a wajen…

Mutane ne dank’am a wajen,wasu a zaune wasu a tsaye,wad’anda suka zo taren y’an uwan su,daga gefe ALHAJI Mudassir (Daddy)ne tsaye rungume da Hannu a k’irji,daga gefensa matarsa ce Anty Kubra,sai y’ay’anta guda biyu mace da namiji ,Sameera da Sameer,wad’anda ba za su wuce shekara takwas zuwa goma sha d’aya ba,dukkanin su fuskar su d’auke da murmushi da zumud’in hango Khaleel yana isowa wajen su….

Tun ma kafin ya k’araso daddy ya d’aga k’afa ya isa gareshi,yana zuwa suka rungume juna cikin kewa da murna,daddy sai shafa kan Khaleel yake yana jin wata matsananciyar k’aunar sa a ransa,musamman da daddyn na sa ya zama wani mutumin kirki sab’anin baya,kuma ya san addu’ar da Hamza yasa yake masa ne tayi tasiri,tare da k’ok’arin Anty Kubra mace mai kirki da d’ora mijinta akan dai dai.

Sun jima rungume da juna kafin Khaleel ya zame jikinsa ya nufi Anty Kubra da ke ta kallonsa tana murmushi,yana zuwa ya durk’usa yana gaishe ta,cikin fara’a da kulawa take amsawa da.

“Lafiya k’alau ibraheemul Khaleel dafatan ka dawo lafiya?ina fatan kuma ka dawo da shirin Aure,domin tuni na gama shirin aurar da kai yadda kayi girman nan ya kamata ace zuwa yanzu ina da suruka a Hannu.”

Wani irin murmushi ya saki yana janyo hannun k’annensa yana shafa Kansu,cikin karsashi ya amsa mata yana kallon daddyn sa yace.

“Karki damu Anty,ban sauka k’asar nan ba sai da shiri na,a yau zan gabatar muku da wadda nake so insha Allah,kuma ko cikin sati d’aya kuke buk’atar ta zama matata ina da yak’inin hakan zai tabbata insha Allah…

Daddy da Anty Kubra farinciki ya ka ma su,cikin zumud’i suke fatan ganin matar da Khaleel ya zab’o a matsayin matar da zai aura,Khaleel ya d’aga kai ya fara hange hange kamar mai Neman wani Abu,har suka lura da shi,daddy ya dube shi yace…

” Kana Neman wani Abu ne…!?

Ya gyad’a kai yana yamutsa fuska yace.

“Eh daddy ina Neman Aboki ne,mun yi da shi zuwa wannan lokacin zai zo airport d’in nan,amma kuma har yanzu shiru..”

“Wai Hamza kake nufi…!?

Anty ta ambata tana kallon sa.

Ya amsa da cewa.

” Eh Anty,naga security nan ba kowa suke bari ya shigo nan ba,k’ila a waje ya tsaya,ku D’an jira ni na duba shi please”

“OK ka hanzarta” Daddy ya ambata yana dafa kafad’ar sa.

Khaleel yayi murmushi ya gyad’a kai,sannan ya juya da hanzari ya nufi harabar airport d’in har da D’an gudun sa.

 

*****************

 

Har lokacin tana tsaye jikin motar,kamar ta fashe da kuka saboda jiran Ya Hamza,ya tafi ya shanyata ya manta da ita.

Wata irin iska ce mai k’arfi ta taso kamar guguwa,Hidaya taji iskar na shirin d’auke ta ta jefar da ita,tunda ba k’iba ce da ita ba,da hanzari ta juya tana shirin bud’e motar ta shige,sai iskar ta janye mayafin jikinta ta tafi da shi,a rud’e Hidaya ta kuma juyawa tana k’ok’arin kamo mayafin ta da iska ta d’auke,amma ina yayi mata nisa,da hanzari ta D’an taka da gudu tana mik’a Hannu da niyyar kamowa,a dai dai lokacin da iskar ta soma lafawa,mayafin ya fara yin k’asa,ya sauka a fuskar Khaleel da ya k’araso wajen domin duba Hamza,ruf ya rufe masa fuska.

Hidaya ta tsaya tana maida numfashin tsoro,tana kallon yadda mayafin ta ya fad’a jikin wani namiji Wanda bata san ko wanene bane,saboda yadda k’ura ta cika mata idanuwan ta,shi kam Khaleel k’amshin da ke jikin mayafin ya soma shak’a yana lumshe idanu,kafin yasa hannun sa a hankali ya soma zareshi shi daga fuskar sa ya rik’e a hannun sa,sannan ya dubi Hidaya da ke tsaye,ya sakar mata murmushi me tafiya da hankalin mutum,yana mata wani kallo tamkar idanuwan sa za su tsiyaye…

Zaro idanuwa Hidaya tayi sosai saboda ta shaida fuskar sa,wani irin murmushi ya sub’uce mata bata shirya ba,cikin tsananin murna ta rufe bakin ta idanuwa warwaje ta ambaci.

“Uncle Khaleel kai ne…!?da gaske kai ne…!?wayyoo your highly welcome Uncle Khaleel…..!

Wani irin taku ya fara yi tamkar d’awisu zuwa gabanta,baki sake take kallonsa tana wani irin murmushin farinciki,shi kam yanayin fuskar sa ta had’a Abubuwa da dama,kamar fata,d’oki,shauk’i,soyayyah,k’auna,bege,kewa,da sauran su.

Yana zuwa gaban ta ya ci burki ya wani tsura mata idanu,mik’a mata mayafin hannunsa yayi,ta mik’a Hannu a hankali tana shirin karb’a,ta d’ora hannun ta a gefen mayafin ta rik’e,yayin da shi yake rik’e da d’aya gefen,idanuwan sa a kanta tamkar ya narke,suna kallon juna ya bud’e baki da k’yar yace.

” Zahrahhhhhhh…..!

Hidaya ta waiwaya gefen ta domin taga Zahran da Khaleel ya ambata,amma bata ga kowa ba,dawo da kallonta tayi zuwa gareshi,tana juya idanuwa a hankali da tambayar sa ina Zahra …!?

Cikin wani yanayi ya rangwad’a kai gefe ya k’urawa Hidaya idanu ya fara magana cikin wata k’ayatacciyar murya.

“Kalli cikin idanuwa na Zahra….za ki samu Labarin abin da yake cikin zuciya ta…..!

Sai Hidaya ta samu kanta da kallon sa,da sauri ta rintse idanuwan ta tsigar jikinta na mik’ewa saboda wani Abu da yake fitowa ta cikin idanuwan sa…cikin wata murya ya sake cewa.

” Kin gani Zahraaa..!?kinga abin da ke ciki ko…!?

Girgiza kai tayi cikin rawar jiki,har lokacin kuma suna rik’e da mayafin a tare,da k’yar ta fizgo magana cikin rawar murya..

“Wai wacece Zahra Uncle Khaleel…!?ban ga Zahran da kake ta ambata ba…!

Kawai sai ya zare mayafin daga hannun ta, ya warware shi yana yafa mata a kanta,sannan ya lek’a fuskar ta yana murmushi yace.

” Ai babu wata Zahra bayan Hidaya….idan har baki gano abin da yake cikin zuciyata ta idanuwana ba, bari na fassara miki……ILOVE YOU WITH ALL MY HEART HIDAYA…..!

A razane ta d’ago idanuwa cikin fitar hayyaci tana duban sa,a dai dai lokacin da Hamza ya iso gaban su yana duban su cikin wani yanayi,kunnuwan sa kuma suka jiye masa gingimemiyar Kalmar da Khaleel ya furtawa Hidaya……..!

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

 

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA ARBA’IN DA TARA DA NA HAMSIN

*Kuna son karanta littafin nan amma sharhi yana gagarar ku*🤗

 

 

 

***Ji yayi gabad’aya kunnuwan sa sun toshe,idanuwan sa sun makance,k’afafuwan sa kuwa tamkar an sage masa su,tashin hankali mara misaltuwa ya samu kansa ciki,ya tawo da tashin hankalin b’acewar Mummyn Hidaya a idanuwan sa,sai kuma ya zo ya tarar da wani tashin hankalin da yake Neman katse numfashin sa…

Tamkar Khaleel ya san da zuwan sa ya waiwaya ya dubeshi,da wani irin hanzari ya nufo shi fuskar sa cike da fara’a,yana zuwa ya bud’e Hannu ya rungume shi yana k’ank’ame shi,ya runtse idanuwan sa yana jin wani farinciki na d’awainiya da shi,burinsa ya cika,zai cigaba da zama da Hamza yana ganinsa yana jin dad’i…

Hamza kan k’ok’arin aro jarumta kawai yake,amma ya kasa,ji yake tamkar Zuciyar sa zata fad’o k’asa tsabar bugun da take,lamo yayi a kafad’ar Khaleel yana k’arewa Hidaya kallo tamkar ya sume,ita kanta jikinta har lokacin rawa yake tayi wani tsuru tsuru tana tsuma…

Yanayin yadda Khaleel yaji jikin Hamza ba k’wari sai ya d’ago shi daga jikin sa,cikin wani yana yi ya tsura masa idanu yace .

“Aboki ya na ganka haka…!?

Cikin daburcewa Hamza ya samo abin cewa.

” Ba na jin dad’i ne Khaleel, cikina naji yana ciwo,ga zazzab’i da ke son rufe ni yanzun nan”

Khaleel ya dafa kafad’ar sa cikin jimami yace.

“Sorry Aboki,bari nayi wa su Daddy magana suna ciki,mu fara zuwa hospital a duba ka kafin mu wuce gida ko…!?

Hamza yayi saurin girgiza kai yana rik’o hannun sa yace.

” Ah ah barshi kawai,akwai magani a gida idan na koma zan sha,tunda na riga na ganka ma inason mu wuce yanzu,saboda Umma tace min na dawo mata da Hidaya da wuri,kar mu kai dare…”

Sai Lokacin ma Khaleel ya juya ya kalli Hidaya da ke tsaye kanta a sunkuye,sai ya k’yalk’yale da dariya ya dawo da kallonsa zuwa ga Hamza yace.

“Aboki wannan K’anwar ta ka Y’ar k’auye ce gaskiya,magana d’aya duk ta rikita ta,wai fa cewa nayi ina sonta,ina son Auren ta,shine duk ta rikice haka…”

Hamza ya ji tamkar ya dab’a masa wuk’a,amma haka ya shanye ya had’iye,cikin matuk’ar basarwa yace….

“So kuma..!?Hidayan kake so Khaleel..!?

Khaleel ya gyad’a kai yana lumshe idanu cikin shauk’i yace..

” Eh Aboki,ina matuk’ar sonta da k’aunar ta,tun ranar da ka fara haska min fuskar ta a asibiti da muka yi video call,ban k’ara samun sukuni a rayuwa ta ba,k’aunar ta ta mamaye min ruhina Aboki, babu abin da ke haskawa a idanuwana idan ba K’anwar ka ba,kayi min alfarma Aboki,ka amince min ka bani K’anwar ka Hidaya na Aura,za ka bani ita Aboki….?

Da wani irin sauri Hidaya ta d’ago kai jin maganar Khaleel, ta k’urawa Hamza idanu tana son jin kalar amsar da zai bayar,shin zai amincewa Khaleel ne ko kuma zai bayyana na sa son da yake mata,domin ta riga ta hango sonta a idanuwan sa,bata san dai dalilinsa na k’in furtawa ba…

Hamza kam shiru yayi yana duban Khaleel, b’angare d’aya na Zuciyar sa na fad’a masa cewar”Hamza kar ka cuci kanka,ga damar ka ta samu,kayi amfani da ita wajen bayyanawa Khaleel cewar Hidaya taka ce,kai ne zaka Aure ta,kar ka bari wannan damar ta sub’uce maka,Hidaya da kai ta fi dacewa ba wani ba”yayin da d’aya b’arin ke ce masa”inah !tabbas Hamza ka makara,kayi nauyin baki har Khaleel ya riga ka furtawa,muddin kuma ka hana Khaleel Hidaya baka yi adalci ba,Khaleel yayi maka komai a rayuwa,kai mai iya hak’ura da farincikin ka ne domin ka sadaukar masa da shi,musamman da ya kasance mai lalura,idan ka hana shi Hidaya komai zai iya faruwa da shi,haka Allah ya k’addara,daman can Hidaya ba rabonka ba ce shiyasa kayi nauyin baki wajen furtawa har Khaleel ya riga ka…..

Ganin yadda Hamza yayi shiru ya k’i furta komai sai khaleel ya narke,ya marairaice fuska ya rik’e hannun Hamzan har k’walla ta soma taruwa a idanuwan sa,cikin wani yana yi ya juya ya kalli Hidaya da soyayyarta ta yi masa mugun kamu,sannan ya waiwaya ya zuba wa Hamza ido cikin sanyin murya ya fara magana.

 

“Don Allah Aboki kar kace min ah ah,kar kace min ba zaka bani Hidaya ba,ba rantse da Allah na yadda nake jin ta a zuciya ta zan iya mutuwa idan ban sameta ba,don Allah ka bani ita wallahi ina sonta….

Yayi shiru tare da zirarowar hawaye,cikin k’arfin hali Hamza ya d’aga Hannu ya goge masa hawayen,sannan yayi murmushi mai kama da yak’e yace.

” Khaleel…da gaske kana son Hidaya…!?

“Ina son ta ….!?Khaleel ya ambata yana lumshe idanu.

Hamza yaji rauni matuk’a a ruhin sa,amma duk da hakan ya daure yayi murmushi yace.

” Duk wani Abu da ya dangance ni mallakin ka ne Khaleel, ita kanta Hidayan tana yi min wani kallo ne na nine komai na ta,ma’ana nine uwa,uba,D’an uwa,dangi,da komai na ta,kaga kuwa ina da iko da ita kenan,kuma babu wani Abu da zan umarceta da shi ta k’i yi,haka ne ko ba haka bane….!?

Hamza Khaleel yake tambaya,amma a fakaice Hidaya ya cillawa tambayar,wadda ke gefensu tsaye cikin matuk’ar tsoro da razana,idanuwan ta na kan Ya Hamza tana girgiza masa kai hawaye taf a idanuwan ta,domin ta fuskanci abin da yake son yi,kuma shine Abu na k’arshe da zai yi Wanda za ta fitar da rai ga Auren sa,domin babu wani Abu da zai umarceta ta kasa yi masa,Hamza bai sani ba ne,amma tana ganin duk wasu Abubuwa da ya lissafo yanzu k’imar sa ta zarce hakan,Hamza shine komai,idan aka ce komai to komai d’in fa kenan……

Jijjiga kai Khaleel yayi da fad’in.

“Hakane Aboki…!

Hamza yayi murmushi mai ciwo ya kalli gefe ya fara magana.

” To idan kuwa hakane babu abin da zaka nema a guna ka rasa muddin mallakina ne,Khaleel da yawun bakina nake furta maka har zuwa zuciyata,cewar,na mallaka maka Hidaya ta zama matar Aure a gareka…..

Hidaya ta runtse idanu da mugun k’arfi,tana jin hajijiya na kwasar ta kamar ta kifa,shikenan Ya Hamza ya gama da su!ya cutar da zukatan su!ya saka musu tabo mara gogewa har abada!innalillahi wa inna ilaihir raji’un.

Shi kam Khaleel tsabar murna bai san lokacin da yayi tsalle ya fad’a k’irjin Hamza ya rungume shi ba,ji yake Hamza ya gama yi masa komai a duniya,kalaman godiya da yabo da jinjina kawai Khaleel ke zubawa Hamza,yayin da Hamzan ya kasa gane matakin da Zuciyar sa take ciki,kawai dai ya san zai iya hak’ura da komai domin Khaleel.

Zubawa Hidaya idanuwa yayi,wadda ke masa kallon da ya kasa gane yanayin sa,kafin tayi wani irin murmushi da bai tab’a ganin sa a fuskar ta ba,sannan ta girgiza kai ta juya ta bud’e murfin motar su ta shige tare da rufewa da k’arfi.

Hamza ya runtse idanuwan sa yana jin wani iri,sai dai aikin gama ya gama,a dai dai kuma lokacin da su Daddy suka iso gare su suna kallon su rungume da juna.

 

 

*******************

 

A matuk’ar kunyace Daddy ya iya gaisawa da Hamza,saboda matsananciyar kunyar da ta rufe shi bisa ga cin mutuncin da ya dinga yi masa shi da mahaifiyar sa,amma sai Hamza ya nuna ma kamar babu wani Abu da ya faru,har ya sake bawa daddy mamaki bisa ga furucin da yayi,saboda yadda daddyn ya dinga Neman afuwarsa da yafiyar sa da fad’in sharrin shaid’an ne da zuciya,da kuma abokai masu bashi shawara akan k’in talakawa,a lokacin ne Hamza da ke durk’ushe gaban daddy ya sunkuyar da kai ya fara magana.

“Ka daina bani hak’uri Daddy, ai kai d’in ubana ne,kuma duk wani Abu da uba zai yi wa D’an sa ba zai kasance da cutar wa ba,duk wasu Abubuwa da suka faru a baya sun wuce,ban tab’a kallonka da su ba,ni a mahaifi nake kallonka,musamman da ya kasance bani da wani uba da zan kalla naji dad’i,ban san mahaifina ba,ban tab’a ganinsa ba,na zo duniya ne a lokacin da shi kuma ya barta,don haka kai mahaifina ne Daddy, ni dai rok’ona a gareka ka barni da Khaleel, kar ka kuma rabani da shi,ina son Khaleel Daddy, kuma domin Allah nake sonsa ba domin abin hannunsa ba.. …

Wad’annan kalamai sun dad’a girgiza Zuciyar Daddy, har ma da Anty kubra da ke gefe tamkar tayi hawaye jin kalaman Hamza,Daddy ya sake tabbatar da cewa lallai Hamza ya cika D’an halak,domin duk irin tozarcin da yayi masa bai d’auki fushi da shi ba,har ma yana kallon sa a matsayin uba?kenan ya tura masa aniyarsa?irin su Hamza kad’an ne a duniya..

Khaleel kam wannan rana babu Wanda ya kai shi farinciki,babu wani guri a Zuciyar sa da yayi ragowa Wanda babu k’aunar Hamza a ciki,bai had’a komai da Hamza ba,amma tun ranar da suka fara ganin juna Allah ya jarrabesu da wata irin k’auna tamkar sun fito ciki d’aya ne.

Babu yadda su Daddy basu yi ba akan Hamza ya bi su gida ya huta ya ci abinci kafin ya koma Kaduna,saboda su basu ma san shi da Hidaya ya zo ba,a tak’aice ma dai basu san wacece Hidaya ba,amma ya kafe akan cewa Umma tana jiransa ne,kuma yana son komawa gida ya sha magani,ya dinga basu hak’uri,tilas suka hak’ura,nan Daddy yake cewa Hamza ya gaida Umma,kuma ya bata hak’uri kan abubuwan da suka faru kafin ya zo da kansa, daga nan Daddy da Anty kubra da yaran suka wuce wajen motar su suna jiran Khaleel ya kammala magana da Hamza ya zo su wuce gida.

Khaleel kam bai so rabuwa da Hamza a wannan lokacin ba,yana ta shagwab’a,sai da Hamza ya dinga bashi hak’uri kafin ya yarda,sai kuma Khaleel yace.

“Aboki da ka bari na sa driver’n Daddy ya tuk’a ku ya maida ku Kaduna,tunda baka jin dad’in jikin ka anya za ka iya tuk’i kuwa..!?

” Zan iya insha Allah Khaleel..! Cewar Hamza yana murmushi.

Khaleel ya jijjiga kai ba Dan ya so ba,suka tattaka suka k’arasa gaban motar Hamza,Khaleel da kansa ya bud’ewa Hamza murfin motar bayan sun rungume juna,Hamza ya shiga ya zauna k’irjinsa na ta dokawa,musamman da ya waiwaya ya kalli Hidaya da ke zaune a gefe ta k’udundune kanta kan cinyar ta,sai ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya.

Shi kam Khaleel duk ya za ci kunya ke damun Hidaya,shiyasa ya zagaya b’amgaren ta ya lek’o kansa ta tagar motar yana tayi mata dariya da tsokanar ta akan in zata sake ta sake,domin shi d’in D’an soyayya ne,dole ta zage ta rage kunya ta koyi soyayya a nunawa juna k’auna,wannan kalamai da Khaleel ke yi ya sake saka Hidaya cikin wani mugun hali,balle kuma Hamza,Wanda ke ta murmushin yak’e Zuciyar sa na ci da wuta.

Da k’yar suka yi sallama,Khaleel na fad’in gobe zai zo Kaduna da wurwuri,duk da yadda Hamza ya so hanashi saboda ya zauna ya huta ko dan doguwar tafiyar da yayi amma ya k’i hanuwa,wai shi k’arewa ma tattarawa zai yi ya dawo Kaduna da zama,da k’yar dai Khaleel ya bar su suka tafi,kuma har lokacin Hidaya bata d’ago kanta ba duk wata magana da suke yi,a haka Hamza ya ja mota cikin sanyin jiki suka fice daga airport d’in,yayin da Khaleel ya bi su da kallo yana d’aga musu Hannu yana jin tamkar ya bi su…….

 

Sun yi nisa da tafiya akan hanyar su ta komawa Kaduna,da k’yar Hamza ke iya jan motar saboda yadda yake jin jikinsa tamkar ba na sa ba,tsananin tashin hankalin da ke tare dashi ba don Allah ya kiyaye ba zai iya zubar da su a hanya,kad’an kad’an yake juyawa yana duban Hidaya da ke k’udundune da kanta a cinyar ta sai gumi take had’awa duk da A C d’in da ke motar,ita kad’ai ta san halin da Zuciyar ta take ciki,daurewa kawai take,amma suna zuwa tsakiyar wani daji dauriyar ta ta k’are,ta kasa rik’e kukan ta,bata san lokacin da ta fashe da wani gigitaccen kuka na tashin hankali ba.…

Saura kad’an sitiyarin ya k’wace daga Hannun Hamza saboda wata muguwar tsorata da yayi,da sauri ya gangara gefen Hanya yayi parking,a gigice ya waiwaya yana duban Hidaya wadda ke gurshek’en kuka kamar me,tana jin ya tsaya da motar ta d’ago kanta,fuskarta kaca kaca da hawaye,da hanzari ta b’alle murfin motar ta fice da saurin ta tana kuka,kawai ji tayi ta fara tafiya har da D’an gudunta ba tare da ta san in da za ta ba.

A rud’e Hamza shi ma ya b’alle murfin bangaren sa ya fita daga motar,da hanzari ya taka ya bita yana k’wala mata kira,inah!Hidaya kuka kawai take tana tafiya da D’an gudunta babu waiwaye,Hamza bai san lokacin da ya taka da gudu ya bita ba cikin tsananin tashin hankali,da k’yar ya cimmata ya sha gaban ta,ta kauce tana k’ok’arin sake tserewa,ganin haka sai yayi abin da ya jima bai yi ba tunda ta soma girma,wato ya rik’o hannun ta cikin wani yanayi na rud’ewa da gigicewa,cikin wani irin nishi yake fad’in.

“Meye hakane Hidaya..?ina zaki ne wai..!?

Fizge hannun ta ta yi tana k’ok’arin juyawa cikin kuka,ya runtse idanun sa yana jin kamar ya fad’i,cikin dauriya ya sake damk’e hannun ta k’ak’am yace.

” kar ki bamu wahala Hidaya,jikina babu k’wari zan iya fad’uwa wallahi”

Sai lokacin ta iya kallon sa,idanuwan ta tamkar gauta Dan jan da suka yi,jikinsa ya kama rawa tsigar jikin sa na mik’ewa ganin kalar idanuwan ta,girgiza mata kai yayi,sai ta sake fashewa da kuka,baiyi aune ba kuma ya ji ta fad’a jikinsa tana goga kan ta a k’irjinsa ,tana gurshek’en kuka,Hamza yaji wani bala’in tausayin ta da tausayin kansa,da k’yar ya iya d’ago kanta ya girgiza mata kai,ya kai Hannu ya share mata hawayen ta,yana so yayi magana amma ya kasa,hannun ta ya ja kawai suka nufi gun motar su,har lokacin Hidaya na kuka mai sauti da shesshek’a.

Suna shiga motar ya kulle k’ofofin Dan ma kar ta sake yunk’urin fita,ya juya yana kallon ta duk idanuwan sa sun zurma saboda tashin hankali,kansa kamar ya fashe,da k’yar ya iya yin jarumtar magana.

“Don Allah kiyi hak’uri Hidaya…na yi miki katsalandan cikin rayuwar ki wajen bawa Khaleel ke ba tare da yardar ki ba,wallahi Hidaya Khaleel na da wani matsayi gareni da ba zai tab’a misaltuwa ba,duk wani Abu da na zama ta silar Khaleel ne,ya yi min komai a rayuwa,ba zai iya Neman wani Abu gareni na hanashi ba,nayi masa wannan alk’awarin ne saboda ina tunanin na isa da ke…..

A wani irin slow Hidaya ta d’ago ta zuba wa Hamza idanuwan ta,da sauri ya sunkuyar da kai,ba zai jure kallon idanunta masu cike da Abubuwa ba,cikin wata murya mai cike da rauni ta fara magana har lokacin tana hawaye.

” Ya Hamza…tabbas ka isa da ni,kuma ka isa ka sani aikata komai ko da kuwa zuciyata bata son hakan,matuk’ar dai abin bai sab’awa Allah da manzon sa ba,Ya Hamza ba wai ina kuka ne don ka mallakawa Uncle Khaleel ni ba,ina kuka ne saboda cutar da zuciyata da taka Zuciyar da ka yi,cuta mara warkewa har abada,a yau zan fad’a maka abin da ban tab’a fad’a maka ba,Ya Hamza ina sonka,ina k’aunarka,ina burin na zama matarka,na fara son ka tun ban san menene son ba,na rayu da k’aunarka a zuciya ta ta yadda babu wani namiji da nake gani a idanuwana idan ba kai ba,kamar yadda na san cewa kana sona kana k’aunata,amma ka kasa bayyana hakan a gareni a matsayin ka na d’a namiji,ta ya ya ni da nake mace zan iya ajiye kunya ta na bayyana maka hakan?tabbas mun yaudari zukatan mu Ya Hamza,ba mu yi wa junanmu adalci ba,ni na dad’e da gane cewa kana tsananin sona,amma ban sani ba ko kaima kana k’yamar Auren mace Irina ne,wadda take da matuk’ar rauni da cutar da maza ke gudun mata masu irin ta,mara asali wadda mahaifiyar ta ta gujeta tun daga yarinta……

Chak Hidaya ta tsaya da maganar ta,saboda wata muguwar tsawa da Hamza ya daka mata,wadda taso tsinka mata hanjin cikinta,ta runtse idanu da k’arfi ganin ya d’aga Hannu yana shirin kai mata mari a fuskar ta…..

 

 

 

Comment
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA HAMSIN DA D’AYA DA NA HAMSIN DA BIYU

 

 

***Sauke hannun sa yayi bai maretan ba,ganin yadda ta tsorata,musamman da ya kasance bai cika yi mata tsawa ba,sai dai yau ta matuk’ar b’ata masa rai akan munanan kalaman da ta dangana kan ta da su.

Fuska a d’aure,a fusace yake wani irin kallon ta yace.

“Idan har kika sake ambatar kanki da wannan munanan kalaman ranki zai b’aci,domin zan iya dukan ki wallahi Hidaya,wane irin hargitsewa k’wak’walwarki tayi har kike fad’in wannan kalaman …!?

Cikin fitar hayyaci tace.

” Yanzu Ya Hamza fad’ar gaskiyar da nayi shine alamun hargitsewar k’wak’walwa?k’arya nayi?shin baka sona d’in ne?ko kuwa zaka rantse babu b’urb’ushin sona a Zuciyar ka..!?

Ya wani kauda kai cikin dukan zuciya,yayi magana a hankali.

“Kin tab’a ganin in da Yaya yak’i K’anwar sa?fad’in ina son ki ko bana son ki ai gidadanci ne Hidaya..!?

Ta girgiza kai cikin hawaye.

” Kar ka kufcewa maganata Ya Hamza,ka gane abin da nake nufi,ba irin wannan son ba,so na soyayyah,so na Aure nake nufi Ya Hamza….

Yayi mata wani kallo da ya k’ara hargitsa ta,sannan ya kawar da kai yace.

“Ni da bakina na tab’a furta miki cewar ina yi miki irin wannan son ne..!?

” Ko baka furta ba idanuwan ka sun fallasa ka,fuskar ka ta nuna ka,Labarin zuciya a tambayi fuska,ni na san kana sona,in kuma ba haka ba ka rantse cewar baka sona…!?

Ya d’aga mata Hannu yana dafe kansa,da k’yar yayi magana.

“Please Hidaya mu bar maganar nan,ko ina son ki ko bana son ki Abu d’aya kawai na sani,shine,ba zan so kaina domin na k’untata wa wani ba,wanin ma kamar Khaleel, muddin ina da yadda zan yi to zan yi domin na sa ma masa farinciki,Manzon Allah (S A W) yace.
” ka sowa D’an uwanka abin da kake sowa kanka”

Dan haka mu rufe maganar nan iya ni da ke,bana son wani ma ya ji ta,Khaleel da ke ya dace,kuma insha Allah zan yi Iya k’ok’ari na domin ya zama miji a gareki,sai dai kuma idan kin watsa min k’asa a idanuwana kin k’i amincewa ne”

Hidaya tayi wani murmushi na takaici,ta goge hawayen ta tsaf ta kalli Hamza tace.

“Allah kar ya nuna min ranar da za ka bani Umarni na k’etare shi,tunda har ka zab’i farincikin khaleel akan farincikina da naka shikenan Ya Hamza,ni kuma na amince zan maka biyayya,zan auri Khaleel ko da ba shi zuciyata take so ba,zan zauna da shi har na rabauta da soyayyar sa”

Wannan magana ta tara ma’anoni kala kala a Zuciyar Hamza,Wanda ke son sadaukar da farincikin sa akan abokin sa Khaleel, Khaleel d’in da ya nuna masa so iya so,ya gwammace ya b’ata da kowa akan Hamza,shiyasa yake son sakawa Khaleel da gingimemiyar sadaukarwa….

Daga wannan maganar Hidaya bata sake cewa komai ba,illa maida kanta da tayi jikin kujera ta kwantar,sannan ta runtse idanuwan ta,tana ta ambaton Allah a ranta ko za ta ji salama.

Hamza kam da k’yar ya tashi mota suka fara tafiya,k’wak’walwar kansa gabad’aya ta cushe,burinsa su isa gida ya samu ya kwanta ko zai samu nutsuwa,amma tabbas yana cikin tashin hankali.

 

 

 

******************

 

 

A maimakon Umma taga sun dawo cikin farinciki sai taga akasin hakan,dukkan su a hargitse suke,Hidaya tunda ta shige d’aki ta kwanta ko motsinta Umma bata sake ji ba,haka ma Hamza,Wanda ya shige d’akin sa ya kwanta lamo yana jinyar Zuciyar sa,mamaki ya ishi Umma,tai ta tambayar Hidaya ko wani Abu ya faru ne amma Hidaya ta kafe akan babu komai,kawai kanta ke ciwo,Umma dai ta san ba haka bane,amma ta k’yaleta da fad’in idan tayi tsami ai za ta ji.

A Daren ranar Khaleel ya addabi Hidaya da turo sak’onni na soyayya,wai ya kasa zaune ya kasa tsaye tunda har yanzu baiji amsarta ba,ta taimakawa numfashinsa da Zuciyar sa ta bashi amsa,ko zai samu ransa ya kai safiya a jikinsa,ita Hidaya ma gabad’aya abin d’aure mata kai yayi,ganin yadda lokaci guda Khaleel duk ya rikice mata,kalaman k’auna da soyayya kamar an masa gori,sai zazzago mata su yake.ta rasa da wane Abu ta burge Khaleel ta k’ayatar da shi har yake mata wannan son,ya fita kyau,ya fita Asali,ya fita kud’i da d’aukaka,gata nakasasshiya mai fama da ciwon sikila da maza ke gudun mata idan suna da shi,to ita kuwa menene abin so a tare da ita…!?

Da ta zurfafawa Zuciyar ta tunani sai kawai taga dacewar amsawa Uncle Khaleel k’udurin sa,ko domin yadda ya kawar da kansa wajen hangen ita d’in ba kowa ba ce face Y’ar tsuntuwa me lalura,amma ya runtse idanuwan sa daga hakan ya zab’o ta cikin dubban mata da suka fita komai,sannan kuma ya kasance zab’in Ya Hamzan ta,Hamzan da take jin sa can cikin k’ololuwar Zuciyar ta…

Tana gama yanke shawara da Zuciyar ta ta d’auki wayar ta,ta rubutawa Khaleel gajeran sak’o Wanda ke bayyana amincewar ta ga soyayyarsa,da bashi amanar kanta gabad’aya,tana turawa ta kashe wayar ta cillata k’ark’ashin pillow, Dan ta san muddin Khaleel yayi katarin ganin wannan sak’on to ba zai barta ta huta ba,zai iya kaiwa har wayewar gari yana yi mata sambatun soyayya…

Wani kuka mai cin rai ya tawo wa Hidaya,ta cusa kanta cikin pillow ta dinga kuka da hawaye tana jin ciwo a Zuciyar ta,ciwon son Ya Hamza,Wanda ta tabbatar a yanzu yayi mata nisa,haka ta shafe tsawon Daren babu bacci sai kuka da ciwon k’irji..

Da asuba bayan sun yi sallah ita da Umma a gida,sai Umman ta waiwaya ta kalleta ta ambaci sunan ta,Hidaya ta amsa a hankali muryarta duk ta dusashe tsabar kuka,idanuwan ta kam sun kumbura suntum,Umma ta girgiza kai ta k’ura mata idanuwa tace.

“Na yi na yi ki fad’a min abin da ke faruwa kin k’i ko?duk da na san baki cika tattauna matsalarki da ni ba amma ya kamata na san wannan,domin na hangi tarin damuwa a tattare da ke Hidaya,ba ma ke kad’ai ba har da yayan na ki shi ma na hangi damuwa a tattare da shi,amma dukkan ku kun k’i fad’a min damuwar ku a matsayi na na mahaifiyar ku,jiya ina jin ki kwana kika yi kina kuka babu bacci,shi ma Hamzan fitilar d’akin sa a kunne ta kwana alamar bai yi barci ba,kuma ko sallar Asuba bai fita ba yau a gida yayi abarsa,na kuma tabbatar duk abin da zai hana Hamza fita masallaci to babba ne,kuma na san kin san komai,Dan haka ki bud’e bakin ki ki fad’a min menene yake faruwa da ku…..!?

Hidaya tayi shiru,tuni hawaye sun sake tsinke mata,ta sunkuyar da kanta kan cinyoyin ta tana kuka,Umma tayi sakato tana kallon ta cikin tashin hankali,babu yadda bata yi akan Hidaya ta fad’a mata ba amma Hidaya tak’i,sai kuka kawai take tana shesshek’a….

Ganin haka sai Umma ta mik’e da sauri ta fice daga d’akin zuwa d’akin Hamza,tun daga bakin k’ofar take jiyo kamar yana kakarin amai,da hanzari ta bankad’a k’ofar ta shiga,yana tsugune yana ta kakari aman ya k’i fitowa sai kad’an,saboda babu komai a cikinsa,tsawon ranar jiya zuwa Daren bai iya cin komai ba tsabar damuwa,yana jin shigowar Umma yayi sauri ya d’auraye bakinsa da fuskar sa ya fito.

Tana tsaye tana kallon sa har ya zauna bakin gadon sa a hankali jikinsa babu k’wari,ta bishi da kallo taga kwana d’aya duk ya zabge,fuska babu walwala cikin kulawa tace.

“Wai ciwon cikin ne ya saka amai…!?

Ya gyad’a kai yana yamutsa fuska yayi magana a hankali.

” Eh Umma,aman ma ya k’i fitowa har k’irjina ya fara ciwo”

Tayi masa wani kallo,Sannan ta girgiza kai tace.

“Kai ciwon k’irji,Hidaya ciwon k’irji,to me yake faruwa haka..!?

Ya d’ago kan sa da sauri ya kalli Umma,ganin kallon da take masa yayi saurin sunkuyar da kansa k’asa,lumshe idanuwan sa yayi kafin yace.

” Umma ai ni yunk’urin amai ne ya saka k’irjina ciwo,ita kuma ai kin san ciwon k’irjin ta yana da nasaba da lalurarta,tunda ba yau ta fara yi ba…”

Umma tayi murmushin takaici tace.

“Hamza….!

Ya d’ago kan sa a hankali yana amsawa.

” Na’am Umma na…!

Ta nemi wata kujera da ke gefe ta zauna,sannan ta maida hankalin ta kansa tana duban sa ta fara magana.

“Jiya lafiyar Allah ka d’auki Hidaya kuka tafi Abuja tare,a maimakon naga kun dawo cikin murna da farinciki sai naga akasin hakan,kun dawo cikin damuwa,Hamza jiya Hidaya bata yi bacci ba,kwana tayi tana kuka,kaima kuma naga alamun baka yi baccin ba,domin ko sallar asuba baka fita ba,ina son sanin meke faruwa,na tambayi Hidaya ta k’i sanar da ni komai sai kuka,tilas kai ka sanar da ni,idan ba haka ba ranka zaiyi mummunan b’aci,me kayi wa Hidaya…!?shin ko ka cutar da marainiyar Allah ne…!?

A rikice Hamza ya d’ago kansa jin maganar Umma,kawai sai ya zame k’asa ya rarrafo gabanta ya kama hannuwan ta ya rik’e,idanuwan sa a kan ta cike da rauni ya fara magana.

” Umma ai kin fi kowa sanin halina tunda ke kika haifeni,kin sani a duniya babu wani da zai cuci Hidaya ina kallo na barshi,balle ni na cuceta,wallahi Umma da ina da hali ko sauro ba zan bari ya ciji Hidaya ba,ni d’in GARKUWAR HIDAYA NE kin sani…

Idanuwanta a kansa tace.

“Eh na sani,to amma ina son sanin menene mak’asudin kukan ta..?menene ya sakata cikin wannan halin..!?

Ya runtse idanu,sai yaga gara ya fad’awa Umma gaskiya kawai,shiyasa yayi k’asa da kai yayi magana cikin rawar murya.

” Mun fara kewar rabuwa da juna ne Umma,saboda a jiya da muka je Abuja Khaleel ya bayyana wa Hidaya cewar Yana son ta,yana son ya aureta..shine abin da ya saka ta…..

Ya kasa k’arasawa saboda yadda yaga Umma ta zabura kamar wadda taga abin tsoro,ta k’ura masa idanu cikin fitar hayyaci da gigicewa tace.

“So kuma?Ibraheem d’in ne ke son Hidaya?to kai kuma fa?ya za ka yi da son da kake mata?

Ta jero masa tambayoyi a hargitse,ya sunkuyar da kai yana k’ok’arin maida hawayen sa da ke son fitowa,ya girgiza kai yace.

” Ai ni Umma ban tab’a furtawa cewar ina sonta da Aure ba,ban ji hakan a zuciya ta ba,Hidaya matsayin k’anwata na d’auke ta”

Cikin fushi da k’unan rai Umma tace.

“Ni za ka yi wa k’arya Hamza….!?

Yayi saurin girgiza kai yana rik’o hannun ta,a kid’ime yace.

” ah ah,kiyi hak’uri Umma”

Ta fizge hannun ta ta mik’e tsaye tana kallon sa fuska babu walwala tace.

“Kai zan bawa hak’uri Hamza,domin ka tafka kuskuren da za ka yi danasani,kana son Abu ka kasa yardarwa kanka hakan,har ka bari wani ya rigaka furtawa, wanin ma Wanda ba za ka iya hanashi komai ba,kowa ya kalleka ya san kana son Hidaya,haka duk Wanda ya dubi yarinyar nan ya san tana sonka,amma shine kake son cutar da zukatanku,shikenan aikin gama ya gama,domin ko ni ba zan iya hana Khaleel Hidaya ba,domin bani da hujjar hakan,duk wasu Abubuwa da na dinga yi a kwanakin nan domin ku nake,ina so ne ku bayyana wa juna kuna son junan ku,a maimakon hakan sai kuka juya baya,kuka yi nauyin baki,musamman kai da ka kasance namiji,kai ne mai laifin Hamza,ina cike da bak’incikin ba kai za ka auri Hidaya ba,domin a yanzu bani da wani buri da ya wuce hakan, kai ne kafi kowa sanin Hidaya,kai ne ka raineta,kai ka san halayen ta,Hidaya tarbiyyarka ce,kai mahaifiyarta ta dank’awa amanar ta,kai ne Wanda baka gajiyawa da ita idan lalurarta ta tashi,kai ne Wanda za ka iya yarda ka rasa komai Dan ka tallafi rayuwar Hidaya,Hidayan da bata da kowa sai kai sai ni,kai ne Wanda za ka zauna da ita ba tare da ka yi mata gorin wani abin ba,me ya sa hankalin ka ya gushe har ka kasa gane hakan Hamza,wane namiji ne kake tunanin zai iya yiwa Hidaya duk wad’annan abubuwan da na lissafa?Na yarda Ibraheem mutumin kirki ne, mai imani da tausayi ne,amma Mahaifin sa kuma fa?kana tunanin Hidaya ba za ta samu k’alubale da shi ba?ko dangin sa?ka dawo cikin hankalin ka Hamza…lallai ka tafka babban kuskure Wanda ba zai gyaru ba….

Kawai sai Hamza ya fashe da kuka,maganganun Umma sun k’ara d’aga masa hankali,wata gingimemiyar soyayyar Hidaya ta taso masa,k’ok’arin dannewa yake amma ya kasa,ya matsa ya rungume k’afafun Umma yana wani irin kuka na tashin hankali,cikin wata irin murya yace…

“Umma na k’addara ce,Umma na jarrabawa ce,Na shiga uku ya zan yi….!?

Hawaye ya ratso ta idanuwan Umma,wani mugun tausayin Hamza ya rufe ta ganin yadda maganganun ta suka rud’a shi,ita kuma ta yi su ne domin ya gane kuskuren da ya tafka,ba wai don ta tayar masa da hankali ba,duk da ta san haka Allah ya k’addara,komai nufi ne na Allah,amma tabbas da sakacin Hamza,kenan akwai yiwuwar ta zauna ta taushi Zuciyar sa saboda kada dukan yayi masa yawa..

Zama tayi a in da ta tashi,ta rik’o hannuwan sa ta na duban yadda yake kuka da hawaye sosai,sai ta dafa kansa ta sanyaya murya tace.

” Tabbas k’addara da jarrabawa sun same ka Hamza,to amma ina son sake tuna maka cewa,shi Allah mai buwaya da d’aukaka,mai hikima ne cikin jarrabarsa ga bayin sa,da abin da yake jarrabar su da shi.Ya kan jarrabi bayin sa wani lokaci da abin farinciki,wani lokacin kuwa da tsanani,duk wannan jarrabawar da gwadawar domin ya bayyana godiyar mai godiya da hak’urin mai hak’uri ne.Allah mai girma da d’aukaka yana cewa.

“و لنبلونکم حتیٰ نعلم المجھدین منکم والصبرین و نبلوا أخبارکم”

Ma’ana (Kuma wallahi za mu jarrabe ku don mu san masu jihadi daga cikinku,da masu hak’uri,kuma don mu jarrabar hak’ik’anin lamarinku).

Ni yanzu babu abin da zan hore ka da shi sai hak’uri,ka yi hak’uri Hamza, kuma ka ambaci “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un” saboda masifar da ta sameka,domin Allah ya ce Annabi (S A W)yayi wa masu hak’uri bushara,cikin suratul bak’ara….

“وبشر الصٰبرین،الذین إذا أصٰبتھم مصیبة قالوا إنا للہ و إنا إلیہ ر ٰجعون،أولٸک علیھم صلو ٰت من ربھم ورحمہ،و أولٸک ھم المھتدون”

(Kuma ka yi wa masu hak’uri bushara.wad’anda idan masifa ta same su sai su ce.daga Allah muke,kuma zuwa gare shi muke komawa.Wad’annan suna da tsoran daga ubangijinsu da rahama,kuma wad’annan sune shiryayyu).

Ka yi hak’uri Hamza, sannan ka ambaci wannan ayar,Allah zai sauk’ak’a maka,sannan ya mu sanya maka da mafi alkairi a rayuwar ka….

Sai Hamza ya matsa ya kwantar da kansa a kan cinyar Umman sa, hawayen sa na sauka suna jik’a jikinta,da wata irin murya yake ta nanata “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” ya dinga fad’arta sau ba adadi yana kuka,yayin da Umma take shafa kansa ta na hawayen tausayin sa……!

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

 

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

BABI NA HAMSIN DA UKU DA NA HAMSIN DA HUD’U

 

 

***Umma ta jima tana rarrashin Hamza a d’akin sa,Wanda yake cikin tashin hankali da tsananin kuka kamar ba zai bari ba,da k’yar ya yi shiru saboda yadda Zuciyar sa ta fara sanyi a bisa innalillahin da ya dinga karantawa,tabbas k’addarar sa ce ta zo,jarrabawar sa ce ta zo,idan yana son ya cinye ta kuma dole sai yayi hak’uri akan duk wata k’addara da ta same shi Mummuna ko kyakkyawa,tun da Allah da kan sa yake fad’a a cikin alk’ur’anin sa mai girma cewar ya halicci komai da k’addara.

“إنا کل شیء خلقنہٰ بقدر”

Ma’ana(Mun halicci komai da k’addara).

“و خلق کل شیء فقدرہ تقدیر”

(Kuma ya halicci kowane Abu,kuma ya k’addara shi k’addarawa).

Haka nan duk wani D’an Adam ba abin da yake so ne yake kasance wa ba,sai abin da Allah ya nufa,domin fad’in Allah ta’ala.

“و ما تشاءون إلا أن یشاء اللہ رب العلٰمین”

Ma’ana(Kuma ba abin da kuka so ne yake kasance wa ba,sai abin da Allah ubangijin talikai ya so wakanarsa).

Ayoyin da Umman sa ta karanta masa,da wad’anda suka zo Zuciyar sa a yanzu,sun isa su sa ya gane cewar hak’uri da wannan k’addara da ta same shi tilas ne,idan har yana so ya cinye jarrabawar sa,haka nan Allah ya gani bai so kansa akan D’an uwansa abokin sa Khaleel ba,ya tabbatar sakamako mai kyau zai iske shi watarana,shiyasa yaji k’arfin imani da k’addara ya shige shi.

Umma ta bar d’akin sa cike da tausayin sa,ta koma d’akin ta ta tarar da Hidaya har bacci ya kwasheta akan daddumar da tayi sallah,hawayen da ta zubar duk ya bushe akan kyakkyawar fuskar ta,sai Umma taji tausayin ta ya cika Zuciyar ta,ta san baccin da bata samu jiya da daddare ba take ramawa,shiyasa bata yi yunk’urin tashin ta ba ta barta ta cigaba da baccin ta kawai…..

Har wajen misalin k’arfe goma na safe Hidaya na bacci,Tuni Umma ta gama aikace aikacen ta tayi break fast,Wanda ta d’auka da kanta ta kaiwa Hamza har d’akin sa, ta tarar da shi yana karatun alk’ur’ani cikin kamala da nutsuwa,sai ta ji dad’i a ranta.

Bata bar d’akin ba kuma sai da ta saka shi a gaba ya ci abincin,duk da ta lura cusawa kawai yake ba don yana masa dad’i ba,sai lokacin Umma ke tambayar sa ya ya jikin nasa? Ko za su je asibiti ne a duba shi,nan ya tabbatar mata ba ma sai sun je asibiti ba da sauk’i, har ma yake tambayar ta jikin Hidaya,ta tabbatar masa Hidayan har zuwa lokacin bacci take yi,sai ya D’an yi murmushi kawai ya sunkuyar da kan sa k’asa.

K’arfe sha d’aya da mintuna biyar muryar Khaleel ta kwarara sallama a tsakar gidan,lokacin Hidaya ta farka tana toilet tana wanka,Umma kuma na zaune a parlour’n ta,yayin da Hamza ke kwance a d’akin sa yana baccin ramuwa shi ma,Umma taji kamar muryar Khaleel, gaban ta ya D’an fad’i,ta mik’e da sauri tana d’aga labule, sai kuwa tayi arba da shi tsaye a tsakar gida fuskar sa cike da murmushi,Kwarjinin sa ya cika wa Umma idanu,ta ga ya k’ara wani girma da kyau tamkar wani balaraben misra,bata san lokacin da ta washe baki ba tana fad’in.

“Lale marhabin da Ibraheem, barka da zuwa bak’on turai”

Khaleel yaji farinciki sosai da ganin Umma, da sauri ya k’ara so gaban ta ya zube gwiwoyi a k’asa,cikin matuk’ar ladabi yake gaishe ta cike da fara’a,Umma cikin jin dad’i take amsawa tana fad’in.

“Wannan ba don nayi maka kyakkyawan sani ba ai ba zan ganeka ba Ibraheem,sai na d’auka wani bak’on balarabe muka yi daga k’asashen larabawa”

Yayi dariya cike da k’aunar Umman a ransa,Umma kam cewa take”shigo ciki Ibraheem, shigo mu k’ara gaisawa na ganka sosai”

Ya cire takalman sa ya bita har cikin parlour’n, Umma ta kasa zaune ta nufi kitchen ta kawo masa lemo da cincin,haka kawai taji tana murna da ganinsa,shi kansa Khaleel yana jin Umma a ransa ne tamkar mahaifiyar sa,ko domin yadda ta d’auke shi tamkar Hamza..

Umma ta zauna suna ta hira ita da Khaleel, tana tambayar sa Abubuwa da dama game da karatun sa da rayuwar sa,shi kuma yana bata amsa cike da ladabi,haka nan yake cin cincin da lemon duk da basu kasance masu tsada ba kamar abincin da ya saba ci,shi sai yake jin dad’in na Umman ma fiye da kowanne,Umma halayyar Khaleel tana birgeta,saboda baya k’yamatar su ko abin hannun su duk da kasancewar mai abin duniya.

Nan Umma ke masa k’orafin me yasa ba zai zauna ya gama hutawa ba?jiya jiyan nan daga dawowarsa amma har ya d’akko k’afa ya tawo Kaduna? Sai yayi murmushi kawai yace.

“Umma ina son na zo na ganki na gaishe ki ne,Sannan na duba jikin Aboki,saboda jiya mun rabu baya jin dad’in jikinsa,kuma tun jiyan nake Neman wayar sa a kashe,shine na kasa zama nayo sammako na tawo”

Umma ta jinjina kai tace.

“Allah sarki!ai jikin na sa da sauk’i ma,yanzu ma bacci yake yi a d’akin sa”

Tana rufe baki sai ga Hidaya ta fito parlour’n daga cikin bedroom, wadda ta fito daga wanka d’aure da babban towel a jikinta,sai k’arami da ta lullub’a a saman kanta,ta fito parlour’n ne da niyyar tambayar Umma in da ta ajiye mata wata doguwar rigar ta da Hamza ya siyo mata,tana son ta saka ta a lokacin,kwata kwata ma bata san Khaleel ya zo ba balle taji muryar sa a parlour’n, har sai da ta fito parlour’n tana wa Umman magana sannan ta Ankara da shi..

K’irjinta yayi bala’in bugawa da k’arfi,yayin da Khaleel ya bita da wani sumammen kallo tamkar ya mik’e ya cafkota yake ji,shauk’in amsar da ta rubuta masa Daren jiya na k’ayata ruhinsa,baki sake yake kallon ta yana jin yadda take zagaye jinin jikinsa,ita kuwa tamkar a tsorace take kallon sa,domin da ta san yana nan babu abin da zai fito da ita parlour’n ko cikakkun kaya ne a jikinta balle towel,k’afafuwan ta suka soma rawa,da wani irin hanzari ta juya ta shige bedroom d’in da gudu tana nishi.

Shi kam cikin mutuwar jiki ya bita da kallo,kafin ya sauke ajiyar zuciya yana shafa gashin kansa,ya juya a hankali yaga Umma na kallon sa,wata kunya ta kamashi,da sauri ya sunkuyar da kai k’asa,sai kuma ya mik’e da sauri yana fad’in.

“Umma bari na duba Aboki a d’akin sa”

Yana fad’in hakan yayi saurin ficewa,ya bar Umma zaune cikin tunanuwa barkatai.

 

 

********************

 

Da sauri Hamza ya bud’e narkakkun idanuwan sa jin Khaleel ya fad’o kansa yana dariya,kallon juna suka yi,Hamza yayi murmushi k’irjinsa na bugawa,Khaleel ya janyo hannunsa yana mik’ar da shi zaune,cikin Y’ar dariya yayi magana.

“Aboki ka wartsake gani na zo fa”

Hamza ya D’an yi Hamma yana lumshe idanuwan sa,kan sa na sarawa,cikin dusashewar murya ya dubi Khaleel yace.

“Khaleel me yasa ka tawo?kamata yayi fa ace ka zauna ka huta sosai”

Ya girgiza kai yana wani lumshe ido yace.

“Ni ba zan iya zama ba ne,na barka baka jin dad’i,na kwana da kai a raina,gashi ina son ganin Hidaya, ko domin nayi mata godiyar amincewar da tayi da soyayyata,Aboki jiya na yi kwanan farinciki da na riski sak’on Hidaya dangane da amincewa ga soyayya ta”

Hamza yaji wani Abu mai kama da bak’inciki a Zuciyar sa,da sauri ya fara addu’a yana korar shaid’anin da ke son kawo masa farmaki,yayi wani murmushi da ya k’ara masa kyawu ya dubi Khaleel yace.

“Amma na yi farinciki da jin hakan sosai,Aboki na ya samu mace ta gari,yayin da k’anwata ta dace da miji na gari”

Sai khaleel yayi murmushi ya rik’o hannun Hamza yace.

“Maganar da take cin raina kenan,har na ce maka idan na dawo za mu tattauna,sai gashi cikin ikon Allah Ubangiji ya kawo min mafita da wuri,na dace a karon farko,yanzu sai kai Aboki,ina son ka bani Labarin soyayyar ka,kuma ina son sanin wacece tayi sa’ar samun ka?domin da alamun kana tsananin sonta,bi sa ga yadda naji kana zazzaga kalamai a kanta…

Gaban Hamza ya fad’i,ya rasa abin cewa,ko giyar wake ya sha ai ba zai iya fad’awa Khaleel cewar Hidaya yake so ba,da k’yar ya samu abin cewa wajen fad’in.

” Wasa nake maka Khaleel, babu wata da nake so a raina”

Khaleel ya dube shi da hanzari cikin mamaki yace.

“Wasa kuma?daman ana wasa da So ne Aboki..!?

Hamza ya runtse idanu yana sakin numfashi ya kasa magana,Khaleel ya tsura masa idanu yace.

” Bana son k’aryataka ne Aboki,domin k’arya ba halayyarka ba ce,amma gaskiya zuciyata bata amince cewar wai wasa kake ba,domin yanayin ka yayi kama da Wanda soyayya ta yi masa mugun kamu..”

Shi kan sa Hamza ba jin dad’in k’aryar da ya zuba yake ba,kawai ya rasa abin fad’a ne,shiyasa yake ta istigfari cikin Zuciyar sa da Neman yafiyar Allah,a hankali ya dubi Khaleel da ya zuba masa idanu yace.

“Kai ma ka san bana b’oye maka komai,idan akwai wacce nake so kai ne mutum na farko da zan sanarwa,ka yarda wasa kawai nake maka,kalaman da kaji na yi a waya kawai a wani littafi na karanta,shine na kwaikwaya na fad’a maka,ina so ne na gane shin na iya soyayyar?idan na samu wacce nake so zan iya fad’amata irin kalaman?dalilin da yasa kenan fa,amma ba wai don na samu wadda nake so d’in ba,ka yarda da ni Khaleel…!

Khaleel yayi ajiyar zuciya tare da murmushi yace.

” Na fahimta Aboki,kuma na gasgata ka,amma na so ace zuwa yanzu kaima kana da taka masoyiyar a Hannu,domin na so ranar Auren mu ta kasance rana d’aya,amma da alamun a yanzu zan rigaka shiga daga ciki,don yadda Hidaya ta mamaye ruhina ina jin ko wata biyu ba zan iya jira ba tare da ta zama mata ta ba,domin a lissafina saura wata d’aya ta kammala secondary school ko..?”

Hamza ya gyad’a kai yana D’an murmushi yace.

“Eh hakane Khaleel, amma da wuri haka?me ya sa kake hanzari?

Khaleel shi ma yayi murmushi me kama da dariya yace.

” To menene abin jira Aboki?tunda har ta amsa min tana sona ai kawai ta zama mata ta a kurkusa shine tabbacin cikar soyayyar mu,ni yanzu ma please ka tashi kaje ka kawo min ita d’akin nan,sosai nake mararin ganin ta,ina jin kunyar Umma ba zan iya kiran Hidaya a gaban ta ba..”

Sai Hamza ya jijjiga kai,ya zame hannun sa daga na Khaleel yana k’ok’arin sakkowa daga gadon,Khaleel ya matsa,shi kuma ya sakko jiki ba k’wari ya fice daga d’akin,yayin da Khaleel ya bi shi da idanu yana jin sabuwar k’aunarsa a ransa .

 

 

 

******************

 

Umma zaune kan kujera,yayin da Hidayan ke zaune a k’asa Umma na yi mata Kalba a kanta,Umma tana so tayi wa Hidaya zancen Hamza amma tana tsoron kar ta tono Zuciyar Hidayan har tayi kuka,a gefe guda kuma ita kanta Hidayan tambayoyi ne fal a ranta da take so tayi wa Umman,musamman akan abotar Ya Hamza da Uncle Khaleel, tana son jin yadda aka yi suka san juna har suka shak’u haka,alhali shi Khaleel gidan su yana abuja,shi kuma Ya Hamza Kaduna,to ta ya ya suka had’u har suka yi wannan shak’uwar tamkar y’an uwa na jini?wad’annan tambayoyin da ma wasu sune suka addabi Hidaya a Zuciyar ta me cike da rauni…

Hamza ya shigo parlour’n Umma da sallama cikin siririyar murya,kallo d’aya yayi wa Hidaya da kanta ke sukuye yayi saurin d’auke idanun sa,kullum k’ara kyau take a idanuwan sa,shi sai yaga yau d’in har gashin kanta ya sauya masa,kamar ba shi ne kusan yake gyara mata kan ba ma kan ta girma sosai ya daina,Dan a can baya har tsifar kai shine yake mata,wataran har wankin kan ma shine yake mata,da ta fara girma ya daina yi mata kam an sha daru,yace Umma ce za ta cigaba da yi mata,in dai za a yi kuwa to da kukan ta ake yi, shi kam Hamza sai dai yayi ta lallashin ta.

Zama yayi kan kujera kusa da Umma, yana wani lumshe idanuwan sa,Umma ba tayi magana ba sai shine ya sake duban Hidaya a karo na biyu sannan ya kawar da kai,a hankali yace.

“Keh…ki tashi kije Khaleel yana son magana da ke”

Hatta Umma sai da ta kalleshi,balle Hidaya da ta d’ago a hanzarce ta k’ura masa idanu cikin bugawar zuciya,kallon da take masa yana son saka shi wani hali,shiyasa yayi saurin d’auke kansa daga gareta yace.

“Baki ji abin da nace ba ne…!?

Cikin marairaicewa da shagwab’a ta amsa da cewa.

” Ya Hamza kitso fa Umma take min”

Ya amsa yana Jan hanci.

“Abar kitson,idan kin dawo a k’arasa”

Zumb’ura baki tayi cike da haushi,shikam sai ya kashingid’a ma yana lumshe idanuwan sa,da yaga bata tashi ba sai ya bud’e idanunsa kad’an yayi mata kallon k’asan ido,cikin wata irin murya mai kama da fad’a yace…

“Kar ki bari na tashi baki rigani tashi ba,Allah zan mareki ne Hidaya,kin san bana son taurin kai ko…?

Da hanzari ta tashi tana hawaye,ta figi hijabin ta da ke kusa da Umma ta zumbula sannan ta fice da sauri.

Ya bita da kallo har ta fice,kafin ya d’auke kansa yana D’an sakin tsaki kad’an,a hankali yayi magana bayan ficewar ta,gabad’aya ma ya manta da Umma da ke zaune a wajen..

” Gulma kawai…an ce kije Khaleel na kiranki kin tsaya wata gardama…kamar ba ke ce kika amsa masa kina son shi ba”

Kawai muryar Umma yaji tana magana.

“Lallab’ata fa ya kamata ka yi Hamza,ni banga abin fad’a ba,yanzu gashi nan kasa ta ta fi tana Kuka”

Shiru yayi yana ajiyar zuciya,ya kwanta lamo kan kujerar yana takurewa kamar mai jin sanyi,Umma ta girgiza kai cike da tausayin sa,sannan ta tashi ta nufi kitchen domin d’ora abincin rana.

 

 

****************

 

Ta d’aga labulen d’akin ta na sallama cikin siririyar murya,Khaleel da ke kwance rigingine yayi saurin mik’ewa cike da farincikin ganin ta, a bakin k’ofar ta tsaya ta kasa k’arasowa kanta a sunkuye,ga hawaye sai sharara suke yi ta kasa tsayar da su,da sassarfa ya k’araso gaban ta ya tsaya yana ambatar sunan ta cikin wata daddad’ar murya mara amo.

“Hidayaaaaa….

Wani irin yarrrr taji a sassan jikinta,kawai sai ta durk’ushe a wajen ta k’udundune kanta cikin Hijab tana shesshek’ar kuka,hankalin Khaleel a tashe shi ma ya bita ya durk’ushe gaban ta,ji yake tamkar ya kamata ya rungume a k’irjinsa,wata irin k’aunarta yake ji tana tsumashi,jikinsa har rawa yake,sunkuyawa yayi saman kanta yana k’ara ambatar sunan ta.

” Hidaya….tashi ki gani….d’ago kanki ki kalleni kinji”

Ta k’i d’agowa ta kalleshi, illa ma k’ara k’udundune kanta da tayi,yayi yayi ta d’ago amma tak’i,cikin wata irin murya ya sake matsarta sosai yace.

“Zan rungumeki Hidaya,wallahi zan rungumeki idan baki d’ago kin tashi ba”

A zabure ta d’ago ta na k’walalo idanu,ganin sa dab da ita yana mata wani kallo sai tayi maza ta runtse idanuwan ta tana sakin ajiyar zuciya,ya k’urawa fuskar ta ido yana bin hawayen ta da kallo,ya narke murya cike da soyayya yace.

“Ina ma na aureki,da wad’annan hawayen naki sun zamo Ruwan sha na a yau,kwad’ayin su nake Hidaya”

Maganar da yayi ta saka ta bud’e idanuwa ta kalleshi, k’irjinta ya nata bugawa da k’arfin gaske,ya wani lumshe ido yana gyad’a kai alamar tabbatar mata da abin da yake nufi.

Sai ta sunkuyar da kai kawai tana jin wani Abu na zagayawa da ita,ya sake rage murya kamar mai rad’a.

“Na kwana cikin farincikin da ban tab’a riskar kaina a ciki ba Daren jiya,kin faranta min a bisa amincewar ki ga soyayya ta,ina sonki Hidaya,ina tsananin k’aunarki masoyiyata,Allah ya cika min burina na mallakeki a matsayin mata ta”

Tayi shiru ba magana,duk a takure take jin ta,shi kuma Khaleel ya dage sai ta amsa da Ameen,tilas ba don ta so ba ta bud’e baki da k’yar tace”Ameen”.

Haka Khaleel ya saka ta a gaba da surutu da ambata mata soyayya,ita mamakin sa ma take,daman haka ya k’ware a magana? Duk ya kanainayeta ta rasa yadda zata yi,tun ba ta amsa masa magana har ta soma amsawa kad’an kad’an,wannan yafi komai yi masa dad’i.….

Bai barta ba sai da yaji an fara kiran sallar azahar,sannan yace ta shiga gida tayi sallah,ta turo masa Aboki su ta fi masallaci,kasa ma mik’ewa tayi saboda yadda k’afafuwanta suka yi sanyi,sai da yace ko ya d’aga ta ne?sannan ta mik’e da hanzari,ya tuntsire da dariya yana bin ta da wani shu’umin kallo,yana fatan Allah ya kai damo ga harawa…

Da sassarfa ta fito daga d’akin,suka yi kacib’us da Ya Hamza shi kuma yana k’ok’arin shiga,kallon sa tayi fuskar sa da danshin ruwa alamun alwala ya d’aura,idanunsa sun yi ja sun koma ciki,a sanyaye take duban sa kamar ta rik’e shi take ji,wallahi tana son Ya Hamza,babu yadda zata yi ne kawai,shi kam d’auke kansa yayi kamar bai ganta ba.

Wata irin juyowa yayi yayi a slow jin ta rik’o hannunsa k’am,idanuwan ta sun ciko da hawaye ta ambaci sunan sa.

“Ya Hamza……

Khaleel ya d’aga labulen d’akin yana kallon su tsaye suna kallon juna,ga hannuwan su a sark’afe….

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA HAMSIN DA BIYAR DA NA HAMSIN DA SHIDA

 

 

 

***Wani irin shock ya ji a jikinsa kamar an watsa masa Ruwan sanyi,cikin wani irin yanayi ya zame hannunsa daga na Hidayan yana kawar da kan sa,murya a cunkushe yayi magana kamar me fad’a.

“Ke fa kin fiye rigima da yawa,ke naga alamar Hawaye ba ya miki wahalar zuba,Malama wuce ciki kiyi Sallah, idan kin idar ki kawo mana abinci nan”

Khaleel ya k’ura masa idanuwa yana kallon yadda ya ci mur yana wa Hidaya wani kallo,ita kam jikinta ne ya k’ara sanyi,a hankali ta juya ta wuce hawaye na sake kwararo mata kan fuskar ta,ita kad’ai ta san matakin da Zuciyar ta take ciki,Ya Hamza ya gama da ruhinta da gangan jikinta da gaske.

Hamza ya D’an saki k’aramin tsaki yana niyyar wucewa cikin d’akin,amma duk Khaleel ya babbake k’ofar,d’agowa yayi ya kalleshi suna duban juna,ganin wani kallo da Khaleel d’in ke masa sai gabansa ya fad’i,Amma cikin dakewa ya karkace baki yana duban sa a d’age yace.

 

“Idan ka gama kallon na wa bani Hanya na wuce”

Khaleel yayi farrrrr da ido yana murmushi,ya k’i matsa wa,sai da Hamza yasa hannunsa ya D’an ture kafad’ar sa sannan ya samu hanya ya wuce,Khaleel ya biyo bayan sa yana dira k’afafu kamar me shagwab’a yana kamo hannun Hamza,waiwayowa yayi ya dubeshi ,sannan ya dubi hannunsa da Khaleel d’in ya rik’e,da wata irin murya ya ce.

“Wai meye ne?”

Khaleel ya langab’e kai,sannan ya dubeshi yayi magana a hankali.

“Aboki ka daina yiwa Hidaya fad’a,sannan ka daina zare mata ido kana hararan ta,wannan k’wala k’walan idanun na ka sai su tsorata ta fa..”

Hamza ya masa wani kallo kafin ya saki k’aramin Numfashi ya ce.

“OK,a barta ta sangarce kenan?”

Khaleel yayi shiru yana girgiza kai, Hamza ya kawar da kai yana tab’e baki ya ce.

“Daga kai har ita shagwab’ar ku tayi yawa,ina jin dai idan kunyi Auren shagwab’ar za ku dinga dafawa kuna ci ko?”

Khaleel ya k’yalk’yale da dariya jin maganar Hamza,shi kam murmushi kawai yayi ya kalli agogo sannan ya sake duban Khaleel d’in ya ce.

“Ka tsayar da mu za mu makara a masallaci fa,ka shiga kayo alwala mu wuce”

Yana fad’in hakan ya wuce gun wardrobe d’in sa yana k’ok’arin sauya kayan jikinsa,shi kuma Khaleel ya wuce bathroom d’in Hamza domin d’aura alwala.

 

 

 

*******************

 

Basu wani jima sosai a masallaci ba suka dawo,Hamza ya haye gado ya kwanta rigingine idanuwan sa a lumshe, ga carbi a hannunsa irin na dannawan nan yana ta salati,shi kuma Khaleel kan carpet d’in ya kashingid’a yana danna wayar sa,suna a haka suka ji sallamar Hidaya,Khaleel ya wani zabura ya mik’e zaune da hanzari, k’urawa k’ofar shigowa ido yayi har ta shigo kanta a sunkuye,hannun ta d’auke da babban tire an jero abinci da abin sha akai,da sauri Khaleel ya mik’e ya nufe ta ya mik’a hannu ya karb’a sai faman sannu yake mata kamar wadda tayi wani aiki,ya ajiye a k’asa ya juya yana kallon ta tana k’ok’arin ficewa daga d’akin,da sauri ya rik’o gefen gyalen ta yayi magana a hankali.

“Ina zaki My love?ki tsaya mu ci abincin tare mana…”

D’an zaro idanu tayi tana satar kallon Hamza da idanuwan sa ke runtse,ta girgiza kai da fad’in.

“Na k’oshi Uncle Khaleel”

Ya langab’e kai yana bin k’aramin bakinta da kallo,yayi narai narai da fuska ya ce.

“Ni fa ba Uncle ba ne yanzu,My Husband za ki dinga kirana kinji”

Hannu ta kai ta rufe idanuwan ta jikinta na rawa,ta san Ya Hamza yana jin su,amma ko motsi bai yi ba balle ya tanka musu,ganin yadda ta k’unshe fuska sai abin ya bawa Khaleel dariya, wata irin dariya ya kama yi yana fad’in.

“Ni dai kunyarki tayi yawa My love,gaskiya ki rage ta Don kar ta dinga cutar da ni”

Ita gabad’aya kusancin da ke tsakanin su ne ya addabeta,duk ya kanainayeta k’amshin turaren sa ya dami hancinta,so take kawai ta bar d’akin amma khaleel ya hana ta,wai tilas ta zauna su ci abinci tare,sai da yaga tana shirin kuka Sannan ya k’yale ta yace ta tafi idan sun gama cin abincin zai sake kiranta.

 

Juyawa tayi da hanzari kamar ta kifa ta fice,wai k’iri k’iri yau Ya Hamza kallonta ma baya son yi,kuma yana ji ana tababa akan ta ci abinci amma ya share ko bud’e idanu ya k’i yi,mutumin da shine yake sakata a gaba kan ta ci abincin kamar zai mata d’ura,amma yau ya nuna bai damu da ta ci ba,duk ya wani sauya mata kamar ba Ya Hamzan ta mai tsananin son ta da kulawa da ita ba.

Hawaye ya kawo mata ziyara,a hankali ta kai Hannu ta share wasu na k’ok’arin sake zubo wa.

Sai da ta fita Sannan Hamza ya iya bud’e idanuwan sa yana jin kansa na sarawa,idanuwan sa sun yi jajawur sun sauya kala,Khaleel durk’ushe yana niyyar zuba musu abincin,ya d’ago kansa suka had’a ido da Hamza,gabansa ya D’an fad’i ganin yadda Hamzan duk ya wani yamutse,tasowa yayi ya zauna kusa da shi,Hamza ya mik’e zaune suna kallon juna,kamo hannunsa Khaleel yayi ya damk’e,cikin kulawa ya ce.

“An ya Aboki ka ji garau kuwa?duk wani iri nake ganinka ko dai ciwon cikin ne har yanzu?”

Hamza ya girgiza kai ya k’ak’aro murmushin dole,yayi magana a hankali muryar sa kamar ta mai jinya.

“Na ji sauk’i fa Khaleel, ka share kawai,sauko mu ci abincin”

Ya zame hannunsa ya mik’e tsaye ya wuce in da abincin yake,Khaleel ya bi shi da kallo yana girgiza kai, tabbas akwai abin da yake damun abokinsa,kuma in sha Allahu zai yi k’ok’arin binkitowa domin yayi masa maganin sa.

Ko da suna cin abincin gabad’aya ya lura Hamzan ba ci yake ba,wasa da cokalin kawai yake yana jujjuya shi,da sun had’a ido kuma sai yayi masa murmushi ya sunkuyar da kai.

 

 

 

****************

 

Hidaya kam kai tsaye bedroom d’in Umma ta shige,ta haye gado ta cusa kanta cikin pillow ta saki wani marayan kuka mai cin rai,anya za ta iya hak’ura da Ya Hamza kuwa?za ta iya hak’ura da soyayyar sa da ke cin Zuciyar ta?ya gama zagaye ko ina a jikinta har bata san yadda zata kwatanta ba,duk da shi ma Khaleel d’in ba k’in sa take ba,amma dai bata jin sa a ranta kwatankwacin yadda take jin Ya Hamzan ta..

Kuka sosai take yi har Umma ta shigo ta same ta a haka,tausayin Hidaya ya kama Umma,ta matsa ta zauna kusa da ita tana dafa bayan ta,Hidayan ta d’ago a tsorace tana kallon Umma,sai Umma ta runtse idanu saboda yadda taga fuskar Hidayan har ta fara kumbura saboda kuka,Hidaya ta fad’a kafad’ar Umma ta sake fashewa da kuka.

A hankali Umma ke shafa bayanta tana lallashinta,da gaya mata kalamai masu dad’i da hak’urk’urtar da Zuciyar ta, kamar yadda ta dinga janyowa Hamza ayoyi da hadisai akan hak’uri da k’addara da jarrabawa haka ta dinga janyo wa Hidayan,Umma bata gushe ba tana jin yadda hawayen Hidayan yake kwarara a k’irjinta,ta d’ago kan Hidayan ta share mata hawayen ta da tafukan hannun ta,Sannan tace mata.

“Kar kiji Haushin Hamza Fad’ima, kiyi masa uzuri kinji,Hamza ba zai tab’a iya hana Ibraheem komai ba,Ibraheem mutumin kirki ne Fad’ima,Kuma wallahi yayi wa Hamza halacci a rayuwa fiye da in da ba kya zato,ta kowane fanni Ibraheem yayi wa Hamza tazara da zarra,ya fishi asali da gata,ya fishi kud’i da d’aukaka,ya fishi kyau da ilimi,Fad’ima Abu d’aya Hamza zai gwadawa Khaleel, shine ilimin addini,Wanda shi ma Khaleel d’in ba baya ba,amma duk da hakan Khaleel ya zab’i Hamza cikin dubban mutane domin ya zama abokin sa,ya zama aminin sa,ya zama komai na sa,Fad’ima na rantse miki da Allah Khaleel GARKUWAR Hamza ne,kamar yadda Hamza ya zama GARKUWAR ki,kiyi hak’uri Fad’ima,ki mik’a lamuranki ga Allah k’i cire duk wata damuwa da ke ranki, ki yawaita addu’a, Allah zai zab’a miki abin da Ya fi alkairi a rayuwar ki”

Hidaya ta k’urawa Umma idanu,cikin fitar hayyaci ta kamo hannun Umman ta rik’e,da wata irin murya ta fara magana a hankali.

“Umma na kiyi min wata alfarma,don Allah ina so ki fad’a min asalin had’uwar Ya Hamza da Uncle Khaleel, ko domin na san dalilin da ya sa suke wa junansu wannan zazzafan so haka,Wanda d’ayan su zai iya sadaukar da duk wani Abu da yake so ga d’ayan,komai kuwa son da yake wa abin,don Allah Umma ki fitar da ni daga wannan duhun zuwa cikin haske”

Hidaya ta d’aga hannayen ta alamar rok’o,Umma tayi Murmushi ta d’aga kanta tana tuna baya,ta sauke kallon ta kan Hidaya ta fara magana kamar haka……!

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA HAMSIN DA BAKWAI DA NA HAMSIN DA TAKWAS

 

 

***Kamar yadda kika sani cewar Khaleel da Hamza abokai ne wad’anda suka shak’u da junan su,ba ke kad’ai ba ni kaina ina mamakin yawan k’aunar juna da suke yi,haka nan mutane ma.

Asalin Mahaifin Khaleel a da mazaunin kaduna ne,cikin wannan Unguwa ta (Tudun wada)wadda ta had’a mutane iri iri kama daga masu kud’i zuwa masu k’aramin k’arfi da rufin asiri.

Ba zan manta ranar da had’uwar Hamza da Khaleel ta samo asali ba,wata rana da yammacin ranar litinin misalin k’arfe biyar na yamma, na cewa Hamza ya d’auki tsintsiyar kwakwa yaje k’ofar gida ya share,saboda a ranar na fita unguwa, da na dawo sai na tarar da k’ofar gidan duk Datti,yara sun sha rake da gyad’a duk sun zubar da b’awon, shine dalilin da ya sa nace ya je ya share wajen domin yayi kyan gani.

Hamza ya d’auki tsintsiyar ya fice domin sharewa,lokacin yana D’an shekara Tara kacal a duniya,lokacin da ya fara sharewa akwai ragowar yaran layin da ke gefe suna ta buga ball,lokacin yammacin yayi musu dad’i saboda a safiyar an yi Ruwan sama gari yayi luf luf,Dan duk gefen hanya ma ga Ruwan nan ya kwanta da cab’alb’ali bai gama bushewa ba.

A dai dai kuma lokacin ne Khaleel ya ratso cikin layin na masu k’aramin k’arfi,akan keken sa mai kyau na y’ay’an masu kud’i,lokacin shi ma shekarunsa ba za su haura taran ba,sanye yake da k’ananan kaya y’an kanti a jikinsa,sabon keke Daddyn sa ya siyo masa shiyasa yake ta shawagin sa a kai,har Allah ya kawo shi layin,da yake bai fiya fita ba ma idan ba makaranta za shi ba,shiyasa duk bai ma san yaran bayan layin ba.

Shigowar sa layin yayi dai dai da sanda yaran suka buga ball d’in da k’arfi,aikuwa ball sai tayi kan khaleel ta buge shi da k’arfi a gefen fuskar sa,zafin da Khaleel ya ji shine ya sa ya saki sitiyarin keken bai sani ba,ya fad’o k’asa cikin cakwakwalin da ya b’ata wajen,keken ya bi shi yana k’ok’arin danne shi Allah yasa ya fad’i gefen bai danne shi ba.

Da sauri Hamza ya waiwaya jin k’ara kamar ihu,yar da tsintsiyar hannunsa yayi da hanzari yayi kan khaleel yana k’ok’arin d’ago shi daga k’asa,su kuma yaran ganin Khaleel ya fad’i sai suka kama dariya har da tsalle,wasu na yi masa gwalo,hakan ya b’ata ran Hamza bayan ya d’ago Khaleel, ya dube su fuska cike da fushi yace.

“Yanzu ku Anas abin da kuka yi ya kamata kenan?kun sa mutum ya fad’i a k’asa sakamakon buga masa ball amma shine kuke masa dariya maimakon ku ba shi hak’uri? Zalintar sa kuka yi fa,Kuma kun manta ko jiya malam Shehi ya karanta mana cewar Allah baya son zalinci?ya haramtawa kansa zalinci,Kuma mu ma ya sanya shi a tsakanin mu abin haramtawa,kada muyi zalinci,haka Allah fa yace,baku kyauta ba Anas,kuyi hanzarin ba shi hak’uri domin kun cutar da shi”

Duk sai jikin yaran yayi sanyi,musamman ma Anas d’in,da sauri suka bawa Khaleel hak’uri,Wanda yake ta yatsuna fuska yana jin k’yank’yamin jikinsa da k’wab’ab’b’iyar k’asa ta b’ata,gyad’a musu kai kawai yayi alamar ya hak’ura,Hamza kam da ya lura da yanayin sa sai ya dube shi cike da kulawa yace.

“Ka yi hak’uri ka ji,ga gidan mu mu shiga sai ka wanke in da ya b’aci a jikin ka”

Khaleel ya D’an k’urawa Hamza idanuwan sa kyawawa,sai Kuma ya D’an saki murmushi ya gyad’a kai,Hamza ya sunkuya ya d’ago keken Khaleel d’in ya rik’e yana turawa,suka jera Hamza na gaba Khaleel na biye da shi a baya suka shige cikin gidan,suka bar su Anas tsaye suna bin su da kallo.

Ina parlour naji muryar Hamza na k’wala min kira,na d’aga labule na fito ina kallon sa shi da yaron da ban sani ba,ya jingine keken jikin bango ya dube ni yace.

“Umma muna da ruwa ko?wannan ne ya zo wucewa kawai su Anas suka buga masa ball ya fad’i,dubi duk jikinsa ya b’aci,bamu ruwa ya D’an wawwanke kinji Umma”

Na girgiza kai ina jajantawa saboda kayan sun yi kaca kaca,idan ma aka ce za a wanke k’asar to zai jik’e ne sharkaf,sai nace da Hamza.

“Ai kayan sun b’aci da yawa fa,ba zai yiwu a wanke suna jikinsa ba,zai iya jik’ewa sosai”

Hamza ya D’an yi shiru,ya kalli Khaleel d’in sannan ya juyo ya kalleni yace.

“To Umma ya cire sai a bashi kayana ya sanya kawai,tunda kanmu d’aya na san za su yi masa ko?”

Mamaki ya kama ni,haka kawai bamu san yaro ba bamu san daga ina yake ba sai mu bashi kaya?amma da naga yadda yaron yake ta kallona sai na amsawa Hamza da to kawai,Hamza yayi murmushin dad’i.

Bayan na bashi kayan ya sauya sai lokacin ya ke gaisheni,har na tambayi sunan sa yace min sunan sa Khaleel, sai naji yaron ya shiga raina farat d’aya da alamun yana da hankali sosai,Hamza da kansa ya wanke masa keken in da ya b’aci,sannan ya dubi Khaleel d’in yace.

“Ka bar kayan na ka anan zan wanke maka,gobe in Allah ya kai mu sai na kawo maka gidan ku,ina ne gidan na ku?”

Khaleel yayi murmushi yana kallon Hamza,yayi magana cikin siririyar murya.

“A layi na biyu nake,gidan mu shine na Uku a layin”

Na D’an ji dammm !saboda ni na gane gidan,Ina bi ta layin wataran,layin gabad’aya masu kud’i ne mazauna cikin sa,amma shi Hamza bai ma gane ba,duk da hakan sai ya gyad’a kai yace.

“To zan kawo maka in sha Allah,ga keken ka ka hau ka tafi kar mamanka tayi maka fad’a ko?”

Sai Hawaye ya ciko idanuwan Khaleel, ya dube mu yace.

“Ai Mamana ta rasu,sai dai Daddy na”

Hamza ya girgiza kai cike da tausayi yace.

“Allah sarki!ni ma Baba na ya rasu!

Na dube su dukan su,sai naga jikinsu yayi sanyi,sai suka ban tausayi,na shafa kawunan su nace.

” Allah ya jik’an iyayen ku,ku dinga yi musu addu’a kunji”

Suka gyad’a kai suna kallon juna,daga nan Khaleel ya d’ane keken sa,Hamza ya raka shi har waje ya tafi,shi Kuma ya d’akko tsintsiyar da ya Yar ya dawo gida ganin magriba ta kawo kai.

Hidaya wannan shine Asalin had’uwar Hamza da Khaleel.

A ranar kafin magriba tuni Hamza ya wanke kayan Khaleel k’al ya shanya su a igiya,sannan ya d’aura alwala ya tafi masallaci, ni dai na zuba masa idanu ban ce komai ba,
Da safe da aka kawo wuta Hamza har da goge wa Khaleel kaya,mamakin yadda ya d’au Khaleel da muhimmanci na dinga yi sosai.

Misalin k’arfe sha biyu na rana na aiki Hamza ya siyo min kayan miya,ni Kuma ina sharar tsakar gida kawai naji sallama,d’agowar da nayi Ina amsawa sai naga Khaleel ne,na washe baki ina fad’in.

“Ibraheem kai ne? Yanzu kuwa Hamza ya ke fad’in zai zo ya kawo maka kayan ka”

Ya k’araso yana murmushi da bak’ar Leda a hannun sa,ya durk’usa ya gaisheni cike da ladabi,na amsa fuska a sake ina tambayar sa mutan gidan su,a lokacin Hamza ya dawo daga aike,ya tsaya turus yana kallon Khaleel, shi ma Khaleel d’in ya juya yana kallon sa,suka yi wa juna murmushi mai k’ayatarwa,sannan Hamza ya k’ara so yana ajiye kayan miyan,ya dubi Khaleel yace.

“Ina ta sauri in gamawa umma aiki na kai maka kayan ka,Ashe ma ka riga ni zuwa kai”

Sai Khaleel ya jijjiga kai yace.

“Ni ma kayan ka na kawo maka fa,nawan Kuma ka barshi ka cigaba da sanyawa”

Nayi sauri nace.

“Ah ah Khaleel na za a yi haka ba,kayan ka masu kyau da tsada sababbi ba zai yiwu ka bada su ba,tuni ma har ya wanke maka ya goge maka,sai kawai ka tafi da abin ka”

Ya girgiza kai yace.

“Allah ni Umma ban zan karb’a ba na bar masa,ina da su da yawa fa sun min yawa ma”

Na yi shiru kawai ina duban Khaleel, yayin da Hamza ya shiga kitchen ya d’akko roba da wuk’a,ya juye kayan miyan yana k’ok’arin gyarawa,Khaleel ya mik’a min ledar kayan Hamza da ya sa,ya matsa kusa da Hamzan yana k’ok’arin taya shi gyaran,sai Hamza ya d’ago ya kalleshi yana murmushi yace

“Ka iya gyaran kayan miya ne?”

Khaleel ma yayi murmushi ya girgiza kai yace.

“Ah ah ban iya ba,koya min zaka yi sai na taya ka kawai”

Ni dai na cigaba da shara ta na bar su nan suna maganganun su da gyara kayan miya,da suka kammala ma tare suka je kai markad’e.

Kafin me Khaleel da Hamza sun yi mugun Sabo a ranar,Kamar sun jima da juna,hatta abincin rana a gidan Khaleel ya ci ranar,naga dai bashi da niyyar tafiya sannan nace masa.

“Ibraheem ya kamata ka tafi gida kar a neme ka fa tunda ka dad’e”

Bai so tafiyar ba,amma sai ya amsa min da to,sannan yace yana so su tafi da Hamza domin shi ma yaga gidan su,ban so hakan ba dai amma na daure nace shikenan suje babu komai,sannan nace wa Hamza kar ya jima ya dawo da wuri.

Hamza ya amsa min sannan ya bi shi suka tafi,basu tarar da Daddyn Khaleel ba,sai matarsa Anty Kubra,har gaban ta khaleel ya kai Hamza yana nuna mata shi a matsayin sabon abokin sa,ta karb’i Hamza Hannu bibiyu da yake mace ce me kirki,ta rik’e Khaleel kamar ita ta haifeshi,sai dai ta yiwa Khaleel fad’an me yasa ya fita ya dad’e?Daddyn sa ya yo waya yana Neman sa,sai k’arya tayi tace yana bacci,shi dai Khaleel dariya kawai yayi ya figi hannun Hamza suka nufi d’akin sa,haka ya dinga rakito abubuwa yana bawa Hamza,shi kam Hamza ma a tsorace yake saboda yadda yaga girman gidan,ga kayan more rayuwa nan kala kala,d’akin Khaleel kan sa abin kallo a yaba ne.

Ya kasa sakin jikin sa,sai Khaleel ne ya dinga Jan sa da hira, ya d’akko hotunan mahaifiyar sa ya dinga nuna masa,abubuwan ci da sha kuwa Hamza har gajiya yayi da ganinsu,ranar dai Hamza ya ga karramawa.

Tun daga lokacin wata irin abota mai k’arfi ta shiga jikin wad’annan yaran,babu ranar da ba za su ga juna ba,ban fiye barin Hamza na zuwa gidan su Khaleel ba,amma shi kam Khaleel kusan kullum sai yazo,da zarar an tashi daga makaranta zai faki ido ya tawo gun Hamza,wata irin k’auna Khaleel yake nunawa Hamza ta musamman,shi ma Hamza yana son Khaleel.

Tun Daddy bai gane yawan fitar da Khaleel yake ba har ya fara ganewa,ya tsare shi kuwa da tambayoyi akan hakan,kai tsaye Khaleel ya fad’a masa cewar gun abokin sa yake zuwa,mamaki ya ishi Daddy,shin waye abokin sa?ta ina suka had’u?Khaleel d’in da ko yaran layin su y’ay’an masu kud’i baya shiga sabgarsu,amma har yake da wani aboki a wani layin?sai Daddy ya barwa ransa cewar zai yi bincike ya gano wanene abokin da Khaleel yake fad’a”

Kwana biyu muka ji Khaleel shiru bai zo ba,hakan yasa naga Hamza duk ya shiga damuwa,amma ya kasa tambayata akan yana so yaje gidan su Khaleel, saboda ya san bancika son zuwan sa ba,ni Kuma akwai abin da nake hangowa,ban cika son mannewa masu kud’i ba saboda ba kowa ke son talaka ba cikin masu kud’in,da kaina dai da naga damuwar Hamzan tayi yawa nace yaje ya dubo yaga ko lafiya,aikuwa ya dinga murna da walwala ya shirya ya tafi.

Sai da yaje ya tarar Ashe Khaleel d’in ba shi da lafiya ne,shi kansa Khaleel d’in yaji dad’in ganin Hamzan,daman kewar sa ta ishe shi,ya dinga murmushi yana daga kwance,Hamza yayi masa sannu ya amsa,suna nan zaune Daddyn Khaleel ya shigo,sai ranar Hamza ya tab’a ganin sa,Daddy ya dubi Hamza shek’ek’e,sannan ya tambayi Anty Kubra cewar wannan wanene?ta ba shi amsa da cewar “shine Hamza,abokin Khaleel”.

Yanayin Hamza kad’ai ya nuna wa Daddy cewar ba D’an masu kud’i bane,hakan yasa yaji Sam bai masa a ransa ba,ya dinga ciccin magani yana hararar Hamza,yayin da Khaleel ke tayi wa Daddyn shagwab’a shi kuma yana biye masa.

Daddy ya so ya kori Hamza,amma saboda baya son b’acin ran Khaleel sai ya bar shi,sai dai ya k’udurtawa ransa tilas ya raba abotarsu,baya son D’an sa ya rab’i talakawa balle a goga masa dattin talauci.

Da Hamza ya dawo ya sanar da ni rashin lafiyar Khaleel, sai naji duk na damu,washegari kawai sai Hamza yaga nayi shiri na soya Y’ar awarata nace yazo ya rakani na duba Khaleel, Hamza yayi ta murnar kulawar da na bawa abokin sa,ya d’auki flask d’in awara muka tafi gidan su Khaleel.

Mun samu tarba ta mutunci gun Kubra,Khaleel kam yafi kowa murnar ganinmu,Kuma a gabana ya bud’e kwanon awarar ya ci abarsa,har Anty Kubra na mamaki,ganin ana ta fama da shi yaci abinci amma ya k’i,kayan dad’i kala kala,amma ya b’ige da cin awara.
Ni dai har muka dawo ban ci karo da Daddyn Khaleel ba,saboda an ce min yayi tafiya zuwa Abuja shi da wani abokin sa Alhaji Maude,murnar bud’e wani babban kamfani da aminin su mai suna Alhaji Taufiq ya bud’e.

In tak’aice miki Labari Hidaya,haka abotar Khaleel da Hamza ta cigaba da k’arfi da hab’aka,suna girma suna k’ara son juna,duk yadda Daddyn Khaleel yayi domin ya raba su hakan ya kasa yiwu wa,Hamza makarantar gwamnati na saka shi saboda bamu da k’arfi,amma sai da Khaleel ya san yadda yayi Daddyn sa ya mayar da Hamza ta su makarantar ta yaran masu kud’i,duk da baya son hakan,bak’incikin Daddy bai wuce yadda Khaleel yake matuk’ar son Hamza ba.

Khaleel baya gajiya da hidimtawa Hamza,har suka girma suka kusa kammala secondary school abotar su na k’ara k’aimi,in dai kaga d’aya zaka ga d’aya,babu irin gulmar da ba a kaiwa Daddy akan ya raba su,wai Khaleel yana mana hidima sosai,gadon da mahaifiyar sa ta bar masa duk mune muke cinyewa,tun baya tsayawa ya kula har abin ya fara shigar sa,yaji gara ma su bar garin Kaduna gabad’aya su koma Abuja,ta yadda za su daina ganin juna gabad’aya.

Da ya fad’a wa khaleel za su tashi ranar yaga tashin hankali,don Khaleel da girman sa amma kuka ya dinga yi da birgima akan ba za shi Abuja ba,shi dai a barshi gun Hamza zai zauna,hankalin Daddy yayi matuk’ar tashi ya rasa ya zaiyi,shine ya nemi shawarar abokin sa Alhaji Maude, nan take Alhaji Maude ya bawa Daddy shawarar ya d’auke Khaleel gabad’aya ya raba shi da k’asar ma,ya fake da zai kaishi Holland karatu kawai,ai dole dai ya hak’ura,

Wannan shine Asalin tafiyar Khaleel England karatu,tafiyar da yayi ta cikin tsananin tashin hankali da kuka,domin a ranar da za su tafi har gidan nan Daddy ya ta ko domin ya d’au ki Khaleel Wanda ke mak’ale da Hamza tun farar safiya suna kukan rabuwa,a ranar Daddy ya ci mutuncin mu,yasa Hannu yana Jan Khaleel Wanda ke kuka sosai,daga k’arshe ma sumewa yayi,amma don rashin tausayi haka Daddy ya fita da Khaleel, kuma bai fasa kai shi England ba,yayin da su Daddyn suka koma Abuja da zama gabad’aya.

Ko a lokacin baya da na so raba abotar Khaleel da Hamza Mahaifin Khaleel d’in ne yazo ya ci mutuncin mu Hidaya,shine abin da ya b’ata min rai har na so raba abotar,daga baya kuma tausayin su ya saka na hak’ura na barsu suka cigaba da Abotar su.

Wannan ce Asalin rabuwar Hamza da Khaleel a muhalli d’aya,sai dai zuciyoyin su na manne da juna,basu tab’a mantawa da juna ba duk da basa tare,Na sha wahala kafin Hamza ya jurewa rashin Khaleel a hankali.

Mamakin Daddy bai wuce duk da ya raba su amma basu daina abota ba,Khaleel bai dai na hidimta mana ba,saima abin da ya k’aru,hakan yasa ya sake tsanar mu ni da Hamza.

Hidaya babu abin da za mu ce da Khaleel sai godiya da fatan alkairi,wallahi tallahi bakina yayi kad’an wajen bayyana miki yawan hidimar Khaleel a garemu,Allah kad’ai ya sani,yaron nan ya so mu,ya k’aunace mu,ya hanamu muyi kuka,kullum burinsa muyi dariya,Hidaya ke da kanki kiyi alk’alanci,kinga ya dace Khaleel ya nemi wani Abu gurin Hamza ya hana shi?kina ganin Khaleel bai cancanta Hamza ya sadaukar masa da komai ba?

Hidaya da Hawaye ke zuba a idanuwan ta ta dubi Ummi Umma cikin fitar hayyaci,kawai sai ta fad’a k’irjin Umma ta wani fashe da kuka tana rungume Umman…….!

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA HAMSIN DA TARA DA NA SITTIN

 

 

 

***Umma ta rungume Hidaya tana jin tausayin ta a ranta,a hankali ta shiga yi mata nasiha tana kwantar mata da hankali,Hidaya tayi kuka sosai a jikin Umma kafin hawayen ta ya lafa,ta d’ago ta dubi Umma cikin rauni tace.

“Umma duk mutumin da zai kyautata muku a rayuwa ya so ku to tilas nima na so shi,duk mutumin da zai k’i ku ya tsane ku tilas nima na tsane shi,a yanzu na ji a raina na k’ara son Uncle Khaleel, amma kuma ina jin tsanar Mahaifin sa”

Umma ta rufe mata baki ta girgiza kai tace.

“Kul!kar na sake jin hakan daga gareki,na baki wannan labari ne ba don ki tsani Daddy ba,sai don ki san yawan k’aunar da Khaleel ya nuna wa Hamza,wadda ta cancanci shi Hamzan ya saka wa Khaleel da mafiyin ta,ma’ana ya hak’ura da ke ya barwa Khaleel, kuma a yanzu Daddy ya shiryu,duk yayi nadamar abubuwan da ya aikata marasa kyau a baya,don haka shi ma ki kalleshi a matsayin uba ko domin darajar Khaleel da ya ke son zama GARKUWAR ki”

Hidaya ta jijjiga kai tana rik’o hannun Umma, ta kalleta tace.

“Umma duk wata GARKUWA da zan samu a bayan ki take ke da Ya Hamza,ni dai kune GARKUWA ta”

Umma tayi murmushi ta sauke numfashi tana k’ank’ame hannun Hidayan,sannan tace.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Mutum biyu ne GARKUWAR ki Hidaya,wato Hamza da Khaleel, ni kai tsaye kawai ki d’aukeni matsayin mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeki”

Sai Hidaya ta k’ara jin k’aunar Umma sosai,ta matsa ta kwanta a kafad’ar ta hawaye na sake ratsowa fatar idanunta,Umma ta sake rungume ta tana cigaba da fad’a mata alkairan da Khaleel yayi musu a rayuwa,bata gushe ba har sai da Zuciyar Hidaya ta fara aminta da cewar za ta karb’i Khaleel amma a rashin Hamza…..!

A haka ta samu barci ya kwasheta a jikin Umma, sai da baccin yayi nisa sannan Umman ta zame ta ta gyara mata kwanciyar ta fice daga bedroom d’in zuwa parlour.

Bata jima da zama ba Hamza ya shigo, ya nemi waje ya zauna,Umma ta dubeshi tana tambayar sa Khaleel, sai Hamza yace.

“Ya shiga toilet ne zai yi wanka,wai zafi yake ji”

Umma ta gyad’a kai,suka yi shiru na mintuna,sannan Hamza ya muskuta ya dubi Umma yace.

“Wai yarinyar nan ta ci abinci kuwa?”

Umma ta dubeshi kamar bata gane ba tace.

“Wa fa..!?

” Hidaya” ya ambata a tak’aice.

Umma ta girgiza kai tace.

“Bata ci ba,bacci ma take tana d’aki”

Ya D’an yamutsa fuska yana shafa kai,sannan ya dubeta yace.

“A tashe ta taci Umma,na lura yanzu bata wani cin abinci sosai,kuma zama da yunwa bashi da amfani”

Umma ta gyara zama tayi murmushi tace.

“Ai ita ba Yarinya ba ce Hamza,ta san yunwar cikinta,dole idan ta tashi zata nemi abincin da kanta”

Ya kawar da kai yayi magana a hankali cikin jan numfashi.

“To Umma ba gara Yarinya akan ta ba ma,kina ganin fa yanzu ta maida kuka da damuwa sana’ar ta,duk ta k’warzabi kanta ta hanawa ranta sukuni”

“Duk jirgi d’aya ne ya kwasoku ai,da kai da itan D’an juma ne da D’an jummai” inji Umma kenan tana kallon sa.

Sai kawai yayi shiru kansa a sunkuye,can kuma ya mik’e ya fice daga parlour’n, Umma ta bi shi da kallo kawai.

Tana nan zaune ya sake shigowa,ta d’aga kai ta kalleshi,rik’e yake da plate ya zubo abinci a kitchen, da alamun Hidayan ya zubo wa tunda d’aki ya nufa,Umma bata ce masa komai ba har ya shige.

Cikin bacci Hidaya taji ana ambatar sunan ta a hankali,ta fara bud’e idanuwa tana dafe kanta da ke ciwo,tana daga kwancen ta bi Hamza da kallo da jajayen idanuwan ta,dire abincin yayi kan dressing mirror ya juyo ya dubeta.

“Tashi zaune” abin da yace kenan idanuwan sa a kanta, da k’yar ta fara k’ok’arin mik’ewa,yabi kwantaccen gashinta da kallo sanda ta jawo D’an kwalin ta ta d’aura,sannan ta kalleshi suka had’a idanuwa,ya lumshe idanuwan sa yayi magana fuska babu walwala.

“Ki shiga toilet ki wanko bakin ki da fuskar ki kizo ki ci abinci”

Ta D’an marairaice fuska tana shirin magana,yayi hanzarin dakatar da ita da hannun sa sannan yace.

“In dai ba amsar ” To” ce zata fito daga bakin ki ba bana son jin komai, tashi kiyi abin da nace kawai”

Tilas ta tashi tana b’ata rai ta shige toilet d’in,wani haushi take ji,d’azu a gaban Khaleel ai nunawa yayi bai damu da cin abincin na ta ba,shine yanzu tana baccinta zai zo ya tada ta,Kuma sai wani d’aure mata fuska yake.

Haka ta kuskure bakin ta ta wanke fuskar ta,sannan ta fito,yana tsaye inda ta barshi kansa a k’asa,ta k’araso ta zauna bakin gadon,ya juya ya d’auko abincin ya mik’a mata,karb’a tayi tana kallon sa,ya karya wuya yana kallon ta k’asa k’asa yace.

“Maza ki cinye shi,yawan wasa da cin abinci shiyasa har yanzu kika kasa yin kumari,haka kike so in d’auke ki in bawa Khaleel d’in jiki duk k’ashi?

Wannan magana ba k’aramin b’ata mata rai tayi ba,bata san lokacin da tayi masa wani irin kallo ba,ba tare da shawara da zuciyqrta ba kawai ta ji bakinta na furta masa cewar.

” To ai irin mu ake yayi,shi ma Uncle khaleel d’in ba zai so in yi k’iba ba domin kar na dinga cika masa Hannu ”

A razane Hamza ya dubi Hidaya yana mamakin fitowar wannan kalamin daga bakin ta, bakin sa a sake,zuciya ta tunzuro shi,yana niyyar magana ya jiyo muryar Khaleel a parlour’n Umma,kawai sai yayi wa Hidaya wani kallo mai tarin ma’anoni ya kad’a kai ya fice,ta bishi da kallo a ranta tana cewa “nima na rama” sai kuma taji hawaye ya zubo mata,musamman da ta fuskanci maganarta ta b’ata ran Ya Hamzan ta,gefe tayi da abincin ta fad’i kwance kan gadon tana sharar hawaye.

 

 

*****************

 

Khaleel dai da k’yar ya iya juyawa Abuja a ranar da magriba,saboda a yammacin sai da ya d’auki Hamza da Hidaya suka fita a motarsa domin zaga gari,da k’yar ma Hamzan ya bi su don dai Umma ta saka baki ne,Hidaya ta nemo rakiyar Sumayya suka tafi tare su hud’u.

A wannan fitar Khaleel ya kashewa Hidaya kud’i sosai kamar ba gobe,har sai da Hamza ya dinga yi masa fad’a,amma yace shi a barshi ai matarsa ce,komai yayi a kanta dai dai ne,sai Hamza ya share shi bai kuma bi ta Kansu ba ya shiga Hidima da wayar sa.

Shi kam Khaleel kulawa da soyayya ya dinga nunawa Hidaya,kalamai na soyayya masu dad’i kuwa babu adadi a bakinsa,har sai da Hidaya ta k’ara tabbatar wa lallai Khaleel D’an love ne na hak’ik’a,ya iya soyayya k’arshe.

Ita kanta Sumayya sha’awar su ta dinga yi,har tana jin Ina ma ta samu saurayi irin Hamza ko Khaleel, da ta gama morewa a duniyar ta.

Ko da Khaleel ya koma gida bai bar Hidaya ta huta ba,wayar safe daban ,ta rana daban,ta dare daban,tun Hidaya bata saba ba har ta fara sabawa ita ma,ta kan mayar masa da amsa idan yana maganganun sa,

Tuni soyayyar Khaleel da Hidaya ta fantsama,a dangin Khaleel babu Wanda bai san da soyayyar ba,hatta Daddyn sa,kuma abin mamakin shine kwata kwata Daddyn bai nuna k’yamar abin ba,kasancewar ya fara canja d’abi’arsa mara kyau ta k’in talakawa,sannan an sanar masa Hidayan d’iyar Umman Hamza ce,ga yadda Khaleel gabad’aya ya haukace akan son yarinyar,ya san ko me zai yi da wuya Khaleel d’in ya hak’ura da Auren ta,dalilin da ya sa ya amince kenan ba wai don yaji a Zuciyar sa yana son abin ba.

Cikin wata biyu maganar Auren Khaleel da Hidaya tayi k’arfin gaske,an kawo kud’i da sa rana wata biyu masu zuwa,Umma dai sai siyen kaya take tana ajiyewa,tana so ta nunawa Hidayan gata sosai,bata son tayi kukan rashin wani Abu,shiyasa ta dage sosai.

Yayin da Khaleel ke Cikin farinciki yana jin ba ya shi a fad’in duniya,a lokacin ne kuma Hamza ke rama da k’ek’ashewa kamar kud’in guziri, shi dai ya san ya fawwalawa Allah komai,kuma ya hak’ura da Hidayan,amma bai san abin da yasa ya kasa cire ta a ransa ba,kullum tunaninta da mafarkinta yake,idan suka kasance guri d’aya kuma ya kan rasa ya zai yi,musamman yanzu da take k’ara nane masa,duk wasu shirye shiryen bikin shi ta d’orawa,wai shine zai yi komai,yace mata ta nemi Hansa’u da su Sumayya sune mata k’awayen ta da suka san komai,amma shi namiji ne bai sani ba,sai tayi murmushi tace masa.

“Ya Hamza bani da K’awar da ta fika a duniya,dole kai zaka zamo babbar K’awata a biki na”

Ramar da Umma ta ga yana yi sai ta d’aga hankalin ta, ta zaunar da shi tayi masa nasiha iya nasiha,da maganganu masu dad’i,da hak’urk’urtar da Zuciyar sa,ya dinga share hawaye yana gyad’a kai ya kasa magana,ita kanta Umma ranar sai da tayi hawaye,saboda mugun tausayin da Hamzan ya bata,tabbas Maryam kabir mashi tayi gaskiya da tace (so babbar cuta ne).

Lokacin biki na matsowa a sanda Hidaya ke Cikin fargabar rabuwa da Umma da Hamza,har ta kai bata iya barci saboda damuwa,sai kuka Cikin dare,kafin me ta kuma ramewa sosai,bata son nuna damuwarta saboda kar Umma da Hamza su damu,sannan bata son Khaleel ya fuskanci damuwar ta Dan kar ta saka shi Cikin wani hali,don tuni ta fara koyawa zuciyarta yadda za ta so Khaleel, ganin shine zai zama mijinta babu yadda zata yi,in dai nuna kulawa da tsantsar soyayya da nuna tausayawa ga mace na sa mace ta so namiji, to tabbas dole ta so Khaleel saboda babu ta in da ya Gaza,sai dai ta san Son Hamza a jininta yake,ba zai tab’a fita ba har ranar da numfashin ta zai bar gangar jikinta.

 

*****************

 

Sati biyu da yin candy d’in Hidaya aka kawo lefenta,Wanda fad’ar kayan da aka jibga k’auyanci ne,kuma duk kayan zab’in Hamza ne,Khaleel ne ya saka ya zab’ar mata komai,saboda a cewar Khaleel d’in Hamzan ya fi shi sanin abin da ya dace da Hidayan sa masoyiyar sa.

A satin da za a fara biki kuwa gabad’aya Khaleel ya tattaro ya dawo Kaduna,saboda zirga zirga ta mishi yawa,gashi yana cuku cukun fara aiki a babbar kotun Abuja bayan bikin su.

Hamza ma b’angaren aikin sa na tafiya dai dai,babu abin da ke damun sa kamar yadda y’ammata suka saka shi a gaba da sunan soyayya,har gidan redio kai masa ziyara suke,waya kuwa har rasa wadda zai d’auka yake,gashi shi a ransa ba wata soyayya,yana ganin yayi rashin ta tunda ya rasa Hidaya a fad’in duniyar sa.

K’anwar Umma da ke kano ce takanas ta dira a Kaduna, da kayayyakin gyaran amare,domin sana’arta ce,nan da nan ta fara gyaran Amarya Hidaya,wadda cikin kwana uku da wuya ka shaida ta idan ka ganta,tsabar kyawun da tayi,ga matsanancin k’amshin da ya ratsa jikinta,ko ya ya ta gifta sai guri ya jima yana k’amshi.

Ango Khaleel ya rud’e matuk’a,burin sa kawai a shafa fatiha Hidaya ta zama mallakin sa.

Da yake Hidayan ustaziya ce babu wani shiri na rak’ashewa da tayi,duk da kuwa Khaleel yaso a yi biki na kece raini,amma Hamza da Hidaya suka k’i amincewa,tilas ya hak’ura,domin farincikin mutanen nan guda biyu ya fiye masa komai.

Babu dinner balle wani party,illa walima k’ayatacciya da aka shirya iya mata kawai,yayin da maza ma za su yi tasu daban,an yi abubuwa kadaran kadahan kamar yadda Hamza ya nunar a yi,babu fariya ko almubazzaranci na kud’i.

Duk shagalin bikin kuma da ake yi Daddy baya nan,ya tafi k’asar China akan business d’in sa,shi kansa bai san dalilin da yasa baya d’okin Auren D’an sa da yake matuk’ar so ba,Daddy bai dira a Kaduna ba sai ana saura kwana d’aya d’aurin Auren Khaleel da Hidaya,da yake gabad’aya suka tattaro daga Abuja zuwa Kaduna domin a gama bikin a nan,cikin tsohon gidan su Khaleel d’in da suka bari,tuni aka k’ara gyara shi domin a gabatar da bikin,in da Hidaya da Khaleel za su zauna a b’angare guda da aka ware musu tsawon sati d’aya,daga nan su d’unguma zuwa Abuja domin cigaba da zama a can.

A Daren ranar da Daddy ya sauka Kaduna, yana zaune shi da Anty kubra a bedroom d’in sa,suna magana akan d’aurin Auren da za a yi gobe,sai Daddy yaji k’arar wayar sa,nan da nan ya d’auka yana murmushi yayi magana.

“Alhaji Maude manyan gari,ina fatan ka iso kadunan dai,domin fa da safe k’arfe goma ne za a d’aura Auren”

Anty Kubra ta b’ata rai jin mijinta ya ambaci sunan Alhaji Maude, haka kawai bata son alak’arsu duk da dai tare ta gansu,Alhaji Maude ba mutumin kirki bane kwata kwata,tana wannan tunanin ta jiyo muryar Alhaji Maude na bawa Daddy amsa murya a cushe.

“Mudassir me ya shiga kanka ne?yaushe har ka yi lalacewar da za ka bari Khaleel ya auri yarinyar da ba a san asalinta ba?Y’ar tsuntuwa !tsintacciyar mage wadda bata mage!mara asali!shegiya wadda bata da uwa da uba!me kuma lalurar sikila….!

Zumbur Daddy ya mik’e tsaye cikin tsananin fad’uwar gaba,a tsorace yana zare idanu yace.

” Wace irin magana ce wannan Alhaji Maude? Me maganganun ka suke nufi?kana nufin yarinyar da Khaleel zai aura ce take da duk wannan tawayar?K’anwar abokin sa Hamza ce fa”

Anty Kubra ma dafe k’irjinta tayi jikinta na tsuma da tsananin tsoro,domin duk ta ji maganar da Alhaji Maude yayi,shi kam Alhaji Maude a fusace ya sake yin magana.

“K’warai kuwa,domin naji yo maganar ne daga majiya mai tushe,shi kansa Khaleel d’in ya san ba K’anwar Hamza ba ce,ya san bata da Asali,tsintar ta suka yi har ta rayu da su,kai kana ina har hakan ke shirin faruwa baka yi bincike ba?wane irin uba ne kai?

Daddy duk ya rud’e a gigice yake gabad’aya,cikin wata irin murya yake cewa.

” Ban sani ba Maude, wallahi ban sani ba,ni fa nan ko yarinyar ban sani ba,ban tab’a sha’awar ganinta ba balle har nayi bincike a kanta,tunda dai an ce min k’anwar Hamza ce,ni gabad’aya daman ba son Auren nake ba,kawai don naga Khaleel d’in ya makance akan son yarinyar ne,amma ai ba sa’ar aurensa ba ce,ni da nake son Khaleel ya samo Y’ar manya wadda ta dace da shi,innalillahi wa inna ilaihir raji’un, yanzu menene abin yi Alhaji Maude? ”

Anty Kubra jikinta na mazari duk ta jik’e da zufa tsabar tashin hankali,ta k’ara zaro idanuwa a sanda taji muryar Alhaji Maude na fad’in.

“Abin yi zai wuce ka hana Auren gabad’aya ne,domin muddin ka bari akayi wannan Aure to ina rantse maka da Allah sunanka zai b’aci!darajarka zata zube!k’imarka zata fad’i k’asa warwas!zaka barwa bayanka abin fad’e,ina shawartarka ka gaggauta d’aukan matakin dakatar da wannan Aure kafin a d’aura shi gobe,idan ba haka ba zaka yi danasani mara amfani Mudassir”

Alhaji Maude na kaiwa nan ya kashe wayarsa ya bar Daddy da waya a Hannu baki a sake,jikinsa na karkarwa tamkar mai jin sanyi,a hankali ya zame ya zauna bakin gado yana sakin gwauron numfashi, hannunsa dafe da kansa,ya d’ago ya dubi Anty Kubra da tayi mutuwar tsaye,da k’yar ya fizgo magana ya ce.

“Kubra kinji wani bala’i kuma?da me Khaleel yake ji da yake Neman janyo min wannan tarangahuma haka?da mutuncina da komai ya rasa wadda zai aura sai shegiya Y’ar tsuntuwa?

Anty Kubra ta janyo salib’ab’b’en jikinta zuwa kusa da daddyn ta zauna,da k’yar ta saita kanta daga razanar da tayi,cikin k’arfin hali ta fara magana.

” Daddyn Khaleel kar ka rud’a kanka,wannan magana tana buk’atar bincike Sosai, ka daina yarda daga an fad’a maka magana ka d’auka,wani abin k’arya ne ba gaske ba,idan ma kuma gasken ne k’ila akwai wani b’oyayyen al’amari,domin na tabbatar Khaleel yadda yake da hankali ba zai auri mace me aibu ba,sai dai idan k’addarar sa ce haka,ka kwantar da hankalin ka zuwa Safiya sai kayi bincike kafin d’aurin Auren kaji”

Daddy ya share zufar goshin sa idanunsa jajir tsabar b’acin rai,sannan yace da Anty Kubra.

“Idan nayi binciken maganar Alhaji Maude ta zama gaskiya fa?ya za a yi kenan?”

Anty Kubra tayi shiru jiki a sanyaye ta rasa abin cewa,Daddy ya runtse idanu ya cigaba da cewa.

“Na tabbatar abin da yafi dacewa shine na hana wannan Auren,to amma K’alubalen shine Khaleel, banga ta in da zai iya hak’ura da yarinyar nan ba Kubra,tunda har ya san aibun ta amma ya gwammace ya aureta a haka saboda tsananin son da yake mata,na san Khaleel zai gwammace ya rasa ransa a kanta,ni kuma ina son rayuwar d’ana,Kubra kin sani ina matuk’ar son Khaleel, ta ya ya kike ganin zan b’ullowa wannan al’amari”

Anty Kubra ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Daddy tace.

“Ina ganin tunda lokaci ya k’ure ka hak’ura a d’aura Auren kawai,bayan an d’aura duk wani bincike sai ya biyo baya,kafin nan mun yi tunanin hanyar da za a biyo wa lamarin,amma yanzu idan aka ce wata magana mai kama da hana Auren za ta b’ullo to za a b’ata goma d’aya bata gyaru ba,zamu iya shiga mugun hali Alhaji,domin zamu iya rasa Khaleel, don Zuciyar sa ba lafiya ne da ita ba,sannan a zo mata da wannan babban gib’in abin akwai razanarwa gaskiya,ka hak’ura a d’aura kawai,in yaso sai a san yadda za a b’ullowa lamarin kafin mu wuce Abuja”

Daddy yayi baya ya fad’i akan gadon cikin matsanancin tashin hankali,kansa na sarawa kamar ya tsinke,ya rasa tudun dafawa,shin dakatar da Auren zai yi ya hana amma kuma ya rasa D’an sa da Ya fi so?ko kuma hak’ura zai yi a d’aura Auren D’an sa da shegiya Y’ar tsuntuwa sunan sa da record d’in sa ya b’aci…..???

 

 

 

 

comments
share
vote
pls

 

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SITTIN DA D’AYA DA NA SITTIN DA BIYU

 

 

***Gabad’aya kan Daddy ya kulle ya rasa mafita,ji yake tamkar kansa zai tsage tsabar tunani da tsananin tashin hankalin da ya samu kansa a ciki,wata Zuciyar na ayyana masa ya kira Khaleel a Daren ya bayyana masa komai domin ayi ta ta k’are,yayin da wani b’angaren ke gargad’insa akan hakan,domin dai komai zai iya cab’ewa har a rasa hanyar gyarawa.

B’angaren Khaleel yana tare da abokanan sa wad’anda suka yo tattaki tun daga England domin halartar d’aurin Auren sa,amma Hamza baya tare da su yana gida,babu yadda Khaleel bai yi da shi akan yazo su kwana tare ba amma ya k’i yarda,yace akwai uzurin da yake son gabatarwa a Daren Wanda yana buk’atar killace kansa,haka Khaleel ya hak’ura ba don ransa yaso ba.

A Daren misalin k’arfe d’aya da rabi dare ya tsala,Hamza ne zaune a d’akin sa ya rasa abin da yake masa dad’i,hannayensa dafe da kan sa da ke barazanar tarwatsewa tsabar damuwa,idanuwa sa sunyi jajir sun koma ciki tsabar kukan da ya sha,har a lokacin ma Kuma hawayen ne ke sintiri a kyakkyawar fuskar sa ,ya kai Hannu ya share hawayen a sanda wasu suka k’ara b’ullowa,shi dai ya san ya hak’ura da Hidaya, da zuciya d’aya ya barwa Khaleel ita,to amma bai san menene ya sa ta kasa barin Zuciyar sa ba,sai yanzu ne ma yake jin wata matsananciyar k’auna da soyayyar ta,bai san ya zai yi ba,zafin da yake ji a tsakiyar k’irjinsa yana sawa yaji tamkar ba zai kai safiyar gobe da rai a jikinsa ba.

Hannuwa biyu ya d’aga yana wa Allah kirari da rok’o a gareshi domin ya yaye masa damuwar sa,hawaye na zuba a idanuwan sa yake rok’on ubangiji kan ya cire masa son Hidaya daga Zuciyar sa,ya san Allah yana jin sa Kuma yana ganin sa,kuma shine yace kada a kirawo waninsa idan ba shi ba,domin babu mai amfanar ka Idan ba shi ba,shine da kan sa yace a rok’eshi zai amsa ,Allah (S W A)yayi umarni da addu’a a cikin ayoyi masu yawa,a cikin suratul gafir ya ce.

“و قال ربکم ادعونی أستجب لکم”

Ma’ana(Kuma Ubangijinka ya ce ,ku rik’e ni,na amsa muku)

A cikin suratul yunus ma ya sake ce wa.

 

“ولا تدع من دون اللہ ما لا ینفعک ولا یضرک،فإن فعلت فإنک إذا من الظلٰمین”

(Kada ka kirawo wani ba Allah ba,Wanda ba zai amfaneka ba,Kuma ba zai cutar da kai ba,idan kuwa ka aikata haka,to lallai kai kana cikin azzalumai)

Sannan wannan lokaci na tsakiyar dare Allah yana amsa addu’ar bayin sa,ya zo a cikin sahihul bukari ,Manzon Allah (S A W) ya ce.

“Ubangijinmu kan sauka kowane dare zuwa saman duniya yayin da sulusin dare na k’arshe ya rage,sai ya ce” wanene zai kira ni na amsa masa? Wanene zai ne mi gafarata na gafarta masa?”

Wad’annan ayoyi da Hadisai su ne suka sake bawa Hamza k’warin gwiwar mik’a kokensa zuwa ga Ubangijin sammai da k’assai,Wanda ya halicci zuciyar mutane Kuma kowa da irin ta sa,ya sanya k’addara da jarrabawa a tsakanin bayin sa domin ya gwada imanin su da tauhidin su.

Hamza yayi addu’o’i masu yawa cikin Daren,a k’arshe ya fashe da kuka sosai yana fad’in.

“Ya Ubangijina makad’aici na fake zuwa gareka cikin lamarin ka,na d’aga tafukan hannayena na k’ask’antar da kaina,ka yarda dani ko zan rabauta,kayi min Rahama da gafara ya Allah,ka cire min Hassada da bak’inciki a zuciya ta,ka haneni da cutar da D’an uwana musulmi,ka cire min son wannan baiwa ta ka a zuciya ta da RUHI na,Ubangijina ina son in had’u da kai lami lafiya ina mai farinciki,bana son ka kamani da mummunan laifi na son matar Aure, Allah ka karb’i rok’o na ka sanyaya min zuciyata ka mu sanya min da mafi alkairi a rayuwata,duk abin da ka aiwatar a kaina dai dai ne,bana bak’inciki da jarrabawarka ya Allah,na karb’eta da Hannu bibiyu ina mai biyayya a gareka,Allah ka bani ikon jure rashin ta da kewarta a duniyata,Allah kai ka halicci zuciyata da tsananin sonta,sai kuma ka hanani ita domin ka jarraba imani na,na hak’ura ya Allahu,na barwa Khaleel ita,Allah ka sa hakan ya zama mafi alkairi a garemu baki d’aya”

Yana kammala wa ya ji wani sanyin dad’i a ransa,wata irin nutsuwa ta saukar masa,take ya mik’e da k’arfin gwiwa ya nufi wardrobe d’in sa ya bud’e,idanuwan sa suka sauka kan abin da yake son gani,Hannu ya mik’a ya d’auko abin cikin k’ura masa idanuwa yana tuna lokacin da aka damk’a masa amanar abin.

Envelope ce wadda mahaifiyar Hidaya ta dank’a masa ranar ta bashi amanar Hidayan,ya kuma rik’e amanar bai tab’a jin sha’awar bud’ewa domin ganin abin da ke ciki ba,ya runtse idanu yana tuna sanda mummyn Hidayan ke jaddada masa ya ajiyewa Hidayan envelope d’in,Sannan ya bata a lokacin da ta girma ta mallaki hankalin kanta,to idan kuwa hakane babu wani lokaci da ya cancanta ya bawa Hidaya wannan sak’on irin wannan lokacin da take shirin zama matar Aure, a yanzu Hidaya take da cikakken hankali domin rayuwar ta za ta sauya akasin ta baya.

A hankali ya bud’e idanuwan sa yana sakin numfashi ya sauke kallon sa kan envelope d’in da ta sha ajiya tsawon shekaru,ya girgiza kan sa ya bar gaban wardrobe d’in,ba tare da b’ata lokaci ba ya taka a hankali ya fice zuwa tsakar gidan su da yake tsit, baka jin motsin komai…..

Hasken da ya gauraye tsakargidan shine ya ba shi damar lura da Hidaya da ke zaune a dandaryar k’asa,kanta matse a tsakanin cinyoyin ta,duk da kanta a sunkuye yake hakan bai sa ya kasa shaidata ba,ko cikin miliyoyin mata Hidaya ta shiga zai iya binkito ta saboda tsabar sanin da yayi mata,k’irjinsa ne yayi matsanacin bugawa ganin ta zaune a wajen cikin talatainin Daren da kowa yake bacci,gidan na su cike yake da mutanen da suka zo kwanan biki,musamman dangin Umma na kano.

Cikin sanyin jiki yake tafiya har ya k’ara sa kusa da in da take zaune,tsugunawa yayi dab da ita yana kallon ta cikin dukan zuciya,cikin kyarmar murya ya ambaci sunanta a hankali tamkar me yin rad’a.

“Hidayaaaaaa”

Bata yi tsammanin jin kiran ba,shiyasa ta d’ago kanta a zabure, cikin tsoro ta sauke ganin ta kan Hamza da ke tsugune a gaban ta,idanuwansu na had’uwa suka ji wata irin fad’uwar gaban da basu tab’a ji ba,Hawaye ne shab’e shab’e yayi wa fuskar Hidaya Zane,har fuskarta ta ta kumbura,kallon da Hamza ke mata cikin tsananin mamaki ya sa ta hanzarin mik’ewa tsaye da sauri,shi ma mik’ewan yayi har lokacin idanuwan sa a kanta ya kasa magana,bai yi aune ba sai jin Hidaya yayi ta afka k’irjinsa da k’arfi,ta rungumeshi k’ak’am tana cusa kanta cikin tsakiyar k’irjinsa da ke mugu mugun bugu,ta fashe da wani irin Kuka na rauni da soya zuciya,muryarta har ta dusashe da k’yar take iya magana wadda Hamza ne kad’ai yake jin me take cewa cikin kuka.

“Ya Hamza na kasa jurewa… Ya Hamza na kasa daurewa rashin ka…Don Allah Ya Hamza ka aureni…ni na yarda na cire kunya ta na bayyana maka soyayyata….wallahi ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba…Ina sonka …ina k’aunar ka…da kai na rayu tun daga k’uruciyata zuwa girmana…..ban san kowa ba idan ba kai ba….babu wanda ya kai ka sanin kimata da mutuncina…ka taimakawa Ruhina da Numfashina ka cigaba da zama GARKUWA ta,Ya Hamza don girman Allah ko sau d’aya ne ka furta cewa kana So na….kar ka barni…kar ka gujeni….kar ka juya min baya please Ya Hamza na…i can’t explain how much I love you,you are the hope of my life,I’m always happy when I see you beside me,you are the happiness of my life,I love you more than anything in my life,I love you so much Ya Hamzaaaaaaa….…!

Hidaya gabad’aya ta rikicewa Hamza,shi ma ta rikita shi,domin wani irin tsattsauran rik’o da tayi masa tana malalar da hawayen ta a jikinsa,yanayin da Hamza ya shiga ba zai fassaru ba,shi tsoro ma yake kar Umma ko wata ta fito a gansu a haka,cikin tsakiyar dare a tsakargida rungume da juna,jikinsa ya kama karkarwa yana rawa,Hidaya so take ta kasheshi kawai ta huta,bata San dauriyar da yake ba tana son tayar masa da hankali,ganin irin k’wak’umar da take masa cikin fitar hayyaci tana shirin suma a jikinsa sai ya sake tsorata,da sauri ya rik’o kafad’unta yana jijjigata domin ta dawo hayyacin ta,ganin yadda take langab’ewa tana shirin zubewa a k’asa kawai sai ya cafki hannun ta ya fizgeta suka fad’a cikin d’akin sa da hanzari jin motsi kamar za a fito.

 

Yana rik’e da hannun ta guda d’aya,ya tura k’ofar d’akin da Hannu d’aya ya rufe,sannan ya waiwayo ya dubeta cikin tsananin tashin hankali,sosai jikinsa yake mugun rawa ganin yadda Hidayan take wani irin kuka tana had’iyar zuciya tamkar ta shid’e,mugun tausayin ta ne kawai yake d’awainiya da shi,shiyasa ya rik’e hannun ta ya zauna kan d’aya daga cikin kujerun d’akin jikinsa a sanyaye,yayin da ya janyo hannun ta ya durk’usar da ita a gabansa tana ta faman kuka.

Da k’yar ya iya bud’e baki ya fad’a mata gajeriyar kalma.

“Kiyi hak’uri…!

Ta girgiza kai tana k’ara damk’e hannunsa sosai kamar Wanda zai gudu ya barta,a hankali tayi magana tana kallon sa hawaye na sharara.

” Na ka sa hak’urin Ya Hamza…Ba zan iya ba”

“Za ki iya Fad’ima”
Yayi saurin katseta cikin rauni tamkar shi ma ya fashe da kukan,Hidaya ta k’ura masa idanu jin ya ambaceta da Fad’ima, sunan da Umma ce kawai tafi ambatar ta da shi.Ya ci gaba da magana cikin sanyin murya idanuwan sa a kanta.

“Hak’uri wani abu ne da yake da wahala a rayuwar duniya Hidaya,amma Idan kika jure kika jajirce za ki iya,Hak’uri tamkar ingarman da baya tuntub’e ne,tamkar takobin da baya dakushewa,tamkar rundunar da ba a tab’a karyata ba,tamkar ganuwar da bata rusuwa,Hak’uri da nasara y’an uwan juna ne,duk in da aka samu hak’uri to wataran za a yi nasara,babu wani k’arfi ga bawan da bashi da hak’uri, kamar yadda babu shi babu cin nasara a rayuwa,Hidaya Allah ta’ala yana ce wa.

 

“یأیھا الذین ءامنوا اصبروا و صابروا و رابطوا واتقوا اللہ لعلکم تفلحون”

 

Ma’ana(Ya ku wad’anda suka yi imani,ku yi hak’uri, kuma ku jure,kuma ku zama a cikin shiri,kuma kuji tsoran Allah ko kwa rabauta).

Bayan haka Allah ya bayyana k’aunarsa ga bayin sa masu hak’uri.ya ce,

 

“واللہ یحب الصبٰرین”

(Allah ya na son masu hak’uri).

Hidaya ba Wani Abu ba ne hak’uri face hana kai raki,da hana harshe kokawa,da kuma hana gab’b’ai make make da kekketa suttura da makamantan hakan,Hidaya duk wani Abu da kika ga ya faru to da sanin Ubangiji, shine ya tsara komai akan mu da rayuwar mu,shine ya tsara cewar ke d’in ba matata ba ce,matar Aboki na Khaleel ce,shiyasa Allah bai nufe ni da furtawa ba har ya riga ni,tabbas ko zan b’oyewa kowa ba zan iya b’oye miki ba,Ina son ki ! Na fara son ki a ranar da idanuwa na suka had’u da naki tun kina k’aramar ki,ranar da mahaifiyar ki ta dank’a min amanarki a hannuna,tun daga ranar nake son ki har rana irin ta yau da nake san son da nake miki ya sauya zuwa na y’an uwan taka,domin na had’u da Allah na lami lafiya Hidaya,kar ki damu kinji,ko baki sameni ba kin samu makwafina,babu ta in da Khaleel zai gaza da ke a fannin rayuwa da zamantakewa,ni dai ina so ki cire komai a ranki kiyi zaman aurenki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,ki manta da cewar Hamza ya tab’a yi miki So na soyayyah,hakan zai sa na k’ara tabbatar wa Hidayana mai hak’uri ce,Hidayana mai juriya ce,Hidayana mai biyayya da tarbiyyace,Hidayana mai k’ok’arin bin abin da Allah yake so ce,Hidayana mai…….

Wani irin rik’o da tayi wa hannun sa tare da fashewa da kuka shine ya dakatar da shi,cikin kukan take kallon sa zuciyar ta na bankwana da shi,harshen ta na karkarwa wajen furta masa kalamai kamar haka.

“Madalla da kai Ya Hamza,Madalla da nagartaccen mutum irin ka mara son zuciya,Madalla da samun irin ka a duniyata,Madalla da kyakkyawar rayuwar da na gabatar tare da kai daga yarinta zuwa girmana,Kalmar da ka ambata min ta ka kana so na ta wanke min dukkanin k’uncin zuciya ta,kuma daga yau zan sa d’ambar Hak’uri da jajircewa domin ganin na cim ma nasara kamar yadda kake kwad’aita min,Ya Hamza na hak’ura da kai,zan auri Uncle Khaleel nayi masa biyayya,fatana ka cigaba da yi min addu’a da d’orani akan hanyar dai dai da zarar zan kauce….!

Wani irin murmushi ne ya sub’ucewa Hamza,ya lumshe idanuwan sa yana jin salama a zuciyar sa,yana fatan Allah ya cigaba da ba su dangana,sakin hannuwan ta yayi sannan ya juya a hankali ya d’akko envelope d’in nan ,ban da aikin kallon sa babu abin da Hidaya take yi,yayi mata alamar ta mik’o hannun ta,a sanyaye ta d’ago hannun a lokacin da ya d’ora mata envelope d’in kan tafukan hannayen ta yana shirin magana,a lokacin ne kuma suka ji yo muryar Umma tana buga k’ofar a hankali tana ambatar sunan Hamza…….!

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SITTIN DA UKU DA NA SITTIN DA HUD’U

 

 

 

***Hidaya kam tsoro ne ya kamata Dan har firgita ta D’an yi tana zaro idanu,shi kam Hamza sai ya mik’e da k’warin gwiwa ya nufi k’ofar ya bud’e a hankali,Umma ta shigo d’akin tana duban sa da idanuwan ta masu cike da barci,Sunkuyar da kan sa yayi a k’asa Zuciyar sa na harbawa,ta waiwaya ta kalli Hidaya da ke durk’ushe k’asa hannayen ta rik’e da takarda,ga hawaye na zuba a idanuwan ta, taka wa tayi a hankali ta nufi gefen gadon Hamzan ta zauna,shi ma tura k’ofar d’akin yayi sannan ya ta ko ya biyo ta a hankali ya tsuguna a gaban ta kamar yadda Hidayan ke tsugune, Umma ta cigaba da dubansu cikin rauni tana tausayawa halin da suka samu kansu a ciki,a hankali Umma ta bud’e baki ta fara magana cikin wata irin murya mai sanyi.

 

“Hamza me yake faruwa ne na same ku kai da K’anwar ta ka cikin Daren nan a muhalli d’aya?

Cikin dukan Zuciya ya d’ago ya kalli Umma,Sannan ya ce.

” Na kasa bacci ne Umma,sai kawai naji zuciyata na ingizani kan na fita daga d’akin nan ko zan ji sauk’i,fitar da nayi ita ce silar cin karo da ita a tsakar gida cikin talatainin dare tana kuka,shine na kasa jurewa na janyo ta d’akin nan domin na rarrasheta na kwantar mata da hankali,Sannan na bata wani sak’o mai tsananin Girma a gare ta ”

“Wane Sak’o ne…!? Umma ta tambaya idanuwan ta a kan sa.

Ya amsa yana kallon Hidaya da kanta ke sunkuye hawayen ta na d’isa a k’asa.

” Sak’on Mahaifiya zuwa ga y’arta Umma,A yau ne na Isar da Sak’on Mahaifiyar Hidaya zuwa ga Hidayan,gata nan a hannun ta na bata”

Hidaya ta d’ago a hanzarce tana kallon sa fuskarta cike da tambayoyi kala kala,domin bata fahimci abin da yake nufi ba,Sai ya jijjiga mata kai fuskarsa d’auke da murmushi yace mata.

“Ranar da Mahaifiyar ki ta dank’amin amanarki ta bani wannan muhimmin sak’on domin na isar da shi gareki da zarar kin Girma kin kai munzali irin wannan ,shiyasa ni……

Hamza ya dakata da magana ganin yadda Hidaya ta mik’e da Hanzari ta cillar da takardar da ke hannunta a k’asa,sannan ta fashe da kuka ta na goge hannayen na ta a rigar da ke jikin ta,cikin kuka take fad’in.

” Ba na buk’atar duk wani Abu da ya fito daga hannun wannan matar,ni ba mahaifiyata ba ce!ban santa ba!bana sonta bana k’aunarta!bana k’aunar duk wani Abu da ya danganceta! Ya Hamza kalli nan !Umma ita ce Mahaifiyata! ita ce wadda na Sani !ita nake so ita nake k’auna ! Amma ba wannan matar da ta gudu ta barni ba !bata San ci na ba!bata San sha na ba!bata San suttura ta ba !bata San karatuna ba balle batun lafiya ta! Ya Hamza kar ka sake kusanta ni da wannan matar da bata yi min komai a rayuwa ba…..

Kafin Umma tayi wani yunk’uri tuni Hamza ya aiwatar da abin da ya niyyata cikin matuk’ar fushi da rawar jiki,wani irin gigitaccen mari ya sakarwa Hidaya Wanda ya sakata kifewa a cinyar Umma cikin d’aukewar numfashi na wucin gadi,Fuskar sa d’auke da mummunan fushi da tashin hankali mara misali ya fara nuna ta da yatsan sa hannuwansa da jikinsa na rawa,Hidaya kam k’ank’ame Umma tayi ta na wani irin nishi saboda yadda Marin ya gigita k’wak’walwar kanta,abin da bata tab’a ji bane a rayuwar ta,yanzu da ta ji shi shiyasa ta gigice ta rasa in da za ta sa kuncinta domin ta ji dad’i.

Umma ma a gigice take da jin k’ak’k’arfan Marin da ya sauka a fuskar Hidaya Wanda bata tab’a tsammanin Hamzan zai iya ba,bata tab’a tsammanin shi da yake matsayin GARKUWAR Hidayan zai iya kai Hannu jikinta da sunan duka ba,d’agowa tayi da hanzari ta na shirin magana,kafin ta kai ga yin magana Hamza ya riga ta farawa a fusace,gabad’aya ya manta da cewar lokacin tsakiyar dare ne.

“Kin bani matuk’ar mamaki!yanzu na san cewa tsawon shekarun da nayi ina d’oraki kan tarbiyya basu amfaneki da komai ba!Hidaya wace irin Halittar zuciya ce da ke haka?wane irin taurin kai ne da ke?Mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeki ita kike fad’awa wannan kalaman?har kike ambatar cewa bata tab’a yi miki komai a rayuwa ba ! Kin manta ita ce wadda ta d’auki tsawon cikin ki wata Tara a jikinta?ta sha fama da laulayin ki da rashin lafiya kala kala,tayi nak’uda mai zafi yayin haihuwarki! Duk da wahalar da kika bata amma ta haifeki tana mai tsananin sonki da k’aunarki!daga lokacin da ta haifeki take kula da ke da lamarin ki ko k’uda bata son ya tab’aki,ki hanata barci!ki hana ta cin abinci!idan kika yi kuka ita ma sai tayi kuka!idan baki da lafiya ta shiga damuwa!ki mata kashi ki mata fitsari!bata dukan ki bata hantarar ki a dukkanin wani laifi da za ki yi mata,sai dai tayi miki addu’a! Ta kan hak’ura da farincikin ta domin ta sama miki naki farincikin!ta kan gwammace ta shiga damuwa da K’unci akan ke ki shiga! Wannan ita ake kira uwa !Mahaifiya!dukannin wad’annan abubuwan da tayi miki baki gani ba?har kike fad’ar munanan kalamai a kanta? Idan baki yi hanzarin tuba ba za ki tab’e,domin Allah zai yi fushi da ke akan tsauraran kalaman da kike fad’i akan mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeki,Girman iyaye ya wuce gaban wasa!Allah ya umarci a girmamasu !kada ayi tir da su!a fad’a musu kalamai masu dad’i.Allah ta’ala yana cewa a cikin littafinsa mai girma.

 

“فلا تقل لھما أف ولا تنھرھما وقل لھما قولا کریما”

Ma’ana(kada kace musu tir,kada ka yi musu tsawa,ka fad’a musu magana mai girma”mai dad’i”).

Matuk’ar kina fad’in kalamai masu zafi akan Mahaifiyar ki zan raba hanya da ke Hidaya!Zan gujeki kwatankwacin yadda b’era ke gudu idan yaga mage!zan nisanta kai na da ke da duk wani Abu…….

Ya kasa k’arasa maganar sa saboda wani hawaye mai zafi da ya tsinke masa,Hidaya ta kuma fashewa da kuka tana rik’e Umma GAM cikin fitar hayyaci,tausayin ta ya kama Umma ganin yadda kumatun ta ya kumbura yatsun Hamzan rad’a rad’a a fuskarta, amma ta san laifin Hidayan ne,duk maganganun da Hamzan ya fad’a gaskiya ne,rik’o Hidayan tayi sosai tana rufe mata baki ganin gunjin kukan da take yi a tsakar Daren nan,Hidaya ta girgiza kai tana cire hannun Umma daga bakin ta,sannan ta fara magana cikin shesshek’a da hawaye.

“Umma ki tayani baiwa Ya Hamza hak’uri, yau nayi masa babban laifin da har duka ya shiga tsakani na da shi!abin da bai tab’a yi min ba a rayuwata!Don Allah ki bashi hak’uri ba zan kuma ba!ba zan sake fad’in munanan kalamai akan Mummyna ba!

Umma tayi murmushi idanunta cikin na Hidaya ta ce.

” Ban da shirme irin na ki Hidaya wanene ya fad’a miki ana fad’awa iyaye mugwayen kalamai?wallahi tallahi na tabbatar muhimmin Abu ne ya saka mahaifiyar ki ta rabu da ke a wancan lokacin!babu Wanda ya kai Uwa son D’an ta!kinga kuwa ba zata tab’a gudunki domin son ranta ba,Mahaifiyar ki tana k’aunarki!kuma komai Daren dad’ewa zata nemeki idan har tana da rai a filin duniya”

Hidaya ta gazgata kalaman Umma,kuma tayi nadamar furucin da ta yi,a hankali ta ja jiki ta matsa kusa da Hamza da ya kau da kai daga gareta,cikin muryar kuka take bashi hak’uri tana ta fad’in.

“Ka yi hak’uri Ya Hamza na tuba!

Sai da ya jima kafin ya dubeta idanuwan sa jajir!sannan yayi magana a hankali.

” Shikenan ya wuce amma ki kiyaye gaba!

Sosai taji dad’in yafe matan da yayi,ta rarrafa ta d’auko envelope d’in da ta cillar ta rungume a k’irjinta,sai taji wata k’aunar Mummyn ta da bata tab’a ji ba ta ratsa k’irjinta,lumshe idanuwa tayi tare da gangarowar hawaye mai zafi kan fuskarta.

Hamza da Umma suka k’ura mata idanuwa cikin tunanuka barkatai da ya cika zuciyar su…..!

 

 

 

 

***************

 

Daddy ya kwana cikin fargaba da dukan zuciya har zuwa wayewar gari da ya rasa tudun dafawa,kuma a safiyar ALHAJI Maude ya ishe shi da waya akan dakatar da d’aurin Auren,ya dinga yi masa Famfo yana tunzira shi da maganganu marasa dad’i akan Hidaya,hankalin Daddy ya sake tashi sosai har yaji kome zai faru ba zai bari Auren Khaleel da Hidaya ya kasance ba.,Saboda baya son sunan sa ya b’aci ko kad’an,sai dai kuma rayuwar D’an Sa fa?akwai buk’atar ya zurfafa tunani akan hakan……

Yayi matuk’ar namijin k’ok’ari wajen b’oye damuwar sa har zuwa lokacin da aka hallara wajen d’aurin Auren, idanuwan sa akan Khaleel yana hango wani mad’aukakin farinciki a fuskar sa da bai tab’a cin karo da shi ba,sai yaji K’unci ya mamaye ruhinsa,a lokacin da ake shirin d’aura Auren Alhaji Maude ya bayyana a wajen a gigice,Mutane dank’am kamar tsaki kowa ka gani cikin walwala,haka ya dinga tsallake mutane har ya isa inda Daddy ke zaune,zuwan sa yayi dai dai da Shafa fatihar D’aurin Auren…..!

 

Shin da wa aka d’aura…..?Da Khaleel d’in ne ko kuwa…?

 

 

Comments
share
vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SITTIN DA BIYAR DA NA SITTIN DA SHIDA

 

 

 

***Dab da kunnen Daddy Alhaji Maude ya sunkuya a rikice,yayi magana a hankali yadda ba Wanda zai iya jin abin da ya fad’a.

“Mudassir har an d’aura Auren ne…!?”

Da k’yar Daddy ya iya jijjiga kansa cikin dukan zuciya da Alhini,Alhaji Maude bai fahimci jijjiga kan Daddy ba shiyasa ya k’ara rage murya Dan kar a jiyo shi yace.

“Kuma da Khaleel d’in aka d’aura…!?”

Daddy ya kasa magana tsabar k’uncin da yake ciki,yayin da hayaniyar mutane tayi yawa kowa cikin fara’a ana ta gaishe gaishe,Alhaji Maude ya damk’i hannun Daddy da ke zaune gumi na yanko masa,da k’yar ya daddafa ya mik’e ya bi bayan Alhaji Mauden da ke jan sa zugui zugui tamkar rak’umi da Akala,Mutane sai gaisuwa da fatan Alkairi suke kawowa Daddy yana amsawa cikin yak’e tamkar Wanda aka yi wa dole,sai da suka fice daga cikin jama’a har zuwa in da Alhaji Maude yayi parking motar sa ya bud’e suka shiga.

Cikin matuk’ar fusata Alhaji Maude ya dubi Daddy ya zuba masa harara kafin yayi magana.

“Tabbas Mudassir ka bani mamakin da baka tab’a bani ba!yaushe ka zama sahorami sullutu haka?kana ji kana gani D’an ka ya d’auko kara da kiyashi amma ka kasa d’aukar mataki har ka bari aka d’aura Auren?wallahi Mudassir ka gama da rayuwar ka!ka yi wa rayuwar ka tabon da ba zai tab’a goguwa ba har abada!ka had’a jininka da jinin shegiya Y’ar zina Y’ar kwararo!duk wani tarihin samuwar yarinyar nan ina da shi a tafin hannuna ! Wai ina ka kai taurin kanka na baya da har ka yi sanyi haka?ina ka kai muguntar ka da bak’ar zuciyar ka da har a wannan lokacin ka kasa juya Khaleel ?Me ya sa a wannan lokacin ka kasa d’aukar shawarata ?bayan duk wasu Abubuwa da kake gabatarwa a rayuwar wa nine k’ashin bayan su ! Kuma kana ganin nasara idan har na baka shawara”

Kamo hannun sa Daddy yayi idanuwan sa jajir !yayi masa nuni da can nesa in da Khaleel da Hamza da sauran Abokanan su ke tsaye,kowannen su bakin sa a bud’e tsabar murna da farinciki,musamman Khaleel da tsananin farincikin da yake ciki ba zai misaltuba,hannuwan sa sark’afe da na Hamzan suna nane da juna,cikin rawar baki Daddy ya fara magana.

“Dubi yawan farincikin da Khaleel yake ciki Maude !So kake na katse shi na maida shi bak’inciki?tun Khaleel yana yaro nake juyashi yadda nake so a matsayina na Ubansa mai tutiyar ina k’aunarsa !ko baya son Abu haka yake biye min yayi min biyayya,Zuwa wannan lokacin da ya girma ya mallaki hankalin sa ya kamata nima na barshi ya shak’i iskar y’anci !Alhaji Maude duk wasu Abubuwa da muka shuka a baya a yau ina danasanin su,kullum k’ara girma muke mutuwa na doso mu !ya kamata muyi hankali musan duniya ba matabbata ba ce !abin da baka sani ba jiya wallahi kwana nayi banyi bacci ba,amma da na rufe idanuwan babu abin da nake gani Sai (Taufik’ )….

Cikin zaro idanuwa Alhaji Maude yace .

” Taufik’ kuma..!? Taufik’ d’in da ya riga yayi nesa da rayuwar mu…!?

Daddy ya jijjiga kai hawaye na ciko idanuwan sa..

“K’warai kuwa! Na rantse maka da Allah a kwanakin nan shine kawai yake dawowa cikin zuciyata da kwakwalwata,ban San dalilin hakan ba !sai dai ina tunanin kamar sakayyar sa ce take dumfaro mu Maude ! Wannan kad’ai da wasu dalilan ya sa na kasa maida hankali kan hana Auren Khaleel, domin kar na sake tafka wani kuskuren a rayuwa ta, Wanda nayi ma a baya ina rok’on Allah ya yafe min,kuma a yanzu babu abin da yake raina irin son ganin TAUFIK’ domin na nemi yafiyar sa kan manak’isar da muka shirya masa a baya tsawon shekaru ….!”

Wani irin murmushi Alhaji Maude ya saki,Wanda duk wani mai saurin fahimta yana ganin wannan murmushi ya San na mugun ta ne !cikin ransa yana cewa”Har abada ba zaka sake ganin Taufik’ ba Mudassir !kuma yadda naga bayansa da sunan ka kai ma a shirye nake da naga bayanka !sai na rusa duk wata soyayya da alak’a da ke tsakanin ka da D’an cikinka !sai nayi maka tabon da sai ka gwammace baka zo duniya ba !Sai na sa D’an ka na cikin ka ya gujeka ! Ya k’yamace ka !ya tsane ka !Yadda ka rusa min target a wannan lokacin har ka bari aka yi wannan Auren to sai na lullub”e rayuwar ka da musibu na sharri wad’anda baka isa ka kufce musu ba,Mu zuba mu gani …..!?

K’wank’wasa glass d’in motar da aka yi shine ya katse tattaunawar su,Abokan Daddy ne da y’an uwa masu Neman sa domin yi masa fatan Alkairi akan Auren D’an sa Khaleel da aka d’aura.

 

 

 

********************

 

 

Rana ce mai matuk’ar d’unbun tarihi da soyuwa a zuciyar Khaleel, a lokacin da ya tabbatar an d’aura Auren sa da Hidaya Sai hawayen murna ya zubo masa,ya kwantar da kansa jikin Hamza ya rungume shi k’am yana hawaye yana ta fad’in “Alhamdulillah ala kulli halin” Shi ma Hamzan tarbarsa yayi ya rungume shi yana runtse idanuwa da sakin ajiyar zuciya mai girma, shikenan komai ya k’are,Hidaya ta zama ta Khaleel, Allah ubangiji ya cigaba da ba shi hak’uri da k’arfin Zuciyar.

An cigaba da hidimar biki a ranar,Wanda Khaleel babu yadda baiyi ba akan yaga Hidaya bayan d’aurin Aure hakan ya gagara,su Hansa’u da Sumayya suka dinga Ja masa rai suna masa dariya,ya marairaice masu kamar zai yi kuka yana rok’onsu,amma suka dage akan ya hak’ura tunda yau ne za a kai ta gidan sa,sai ya cinye ta ma k’arewar Kallo,har Hamza sai da yaji Haushin b’oye Hidayan da ake yi ya kalli su Sumayya fuska kadaran kadahan yace.

“Ku bashi matarsa ya ganta mana,menene abin b’oyo haka tunda har an d’aura Auren ai kuma komai ya k’are”

Sumayya ta D’an yi dariya cike da ladabi ta dubi Hamza tace.

“Ya Hamza mu fa a ka’ida ba zai ganta ba har sai mun kaita gidan sa ya sa yi baki tukun”

Ya yamutsa fuska yana tab’e baki yace.

“Meye siyan baki kuma?au wai daman har yanzu ana wannan al’adar ne?

Hansa’u tayi caraf tace.

” Sosai ma Ya Hamza ana yi,kuma mu bakin tamu amaryar tsada ne da shi sosai sai an wahala kafin a siye shi”

Wani miskilin murmushi Hamza tayi yace .

“Allah ko? To kar ku manta fa ita kanta gabad’ayan ta mallakin Khaleel d’in ce balle wani bakinta”

Ya waiwaya yana duban Khaleel da ya langab’e yana sauraren su,ya kanne ido d’aya yana d’aga girarsa yace .

“Ka San shawarar da zan ba ka?

Khaleel ya jijjiga kai yana murmushi, Hamza ya dafa kafad’ar sa ya matsa dab da kunnen sa yana masa rad’a,Khaleel ya d’ago yana kwashewa da dariya yana ruk’unk’ume hannun Hamza,fad’i yake cewa.

” Exactly Aboki…Na rantse sai na cinye bakin nan tassssssss….Aboki komai ma sai na cinye….bazan bar ragowar komai ba…..”

Dariya Hamza yayi suka tafa, yayin da su Sumayya suka bi su da kallo basu fahimci dariyar da suke ba.

 

Tun da aka d’aura Auren Hidaya ke faman kuka da hawaye sharaf sharaf,tun Umma na lallashin ta har ta rabu da ita ta shiga sabgar ta da mutane,kafin wani lokaci zazzab’i ya rufe ta Sai rawar sanyi take yi,da taji za a dame ta ma d’akin Hamza ta gudu tayi kwanciyar ta a can,saboda baya d’akin yana tare da su Khaleel.

Sai wajen Azahar da ya shigo canza kaya sannan ya tarar da ita k’udundune kan bed d’in sa,Sosai ya rud’e yana tabayarta me ya faru?babu magana sai hawaye !da ya fahimci zazzab’i take da sauri ya fita ya nemo mata maganin ta,saboda baya son ciwonta ya tashi,sun samu an dad’e bai motsa ba,har abinci yayi wa Sumayya magana ta kawo mata,ya tasata a gaba tana kuka sai da ta ci sannan ya bata maganin ta sha,Yace ta shiga toilet tayi alwala,haka ta mik’e jiki ba k’wari zuciyar ta cike da tausayin Ya Hamzan ta,ta d’auro alwala ta fito,yana zaune har tayi sallah,Sai yace ta kwanta ta huta zuwa la’asar saboda hayaniyar mutane tayi yawa,sai Neman Amarya ake yi kowa sai ace masa bata jin dad’i.

Ta sha baccinta sai k’arfe hud’u da mintuna na yamma sannan Hamza ya kira Umma a waya yace a tashe ta tayi sallar la’asar,Umma da kanta ta je d’akin Hamzan ta tashe ta,cikin ikon Allah sai ta tashi ragau da ita ba zazzab’in,Umma ta sa ta sake wanka tayi Sallah,sannan Hansa’u ta rangad’a mata kwalliya,nan da nan Amarya Hidaya ta fito ras da ita sai walwali da d’aukar ido take yi,Shagali ya sake b’arkewa a cikin gida,y’an kid’an k’warya sai cashewa ake mata na tik’ar rawa da lik’i, Sai da aka fara kiran sallar magriba sannan aka dakata.

K’arfe takwas dai dai Hidaya durk’ushe cikin d’akin Hamza a gaban sa tana kuka,yayin da Hamzan ke ta lallashin ta da kalamai kyawawa masu cike da ilimi,yana karanta mata darajar Aure da martabar sa,Sannan ya umarceta da ta tsare Salla da karatun alk’ur’ani, da yawan ambaton Allah da istigfari,Sannan ya fad’a mata maganar da ta sake raunata zuciyqrta da sakata hawaye mara misali,domin cewa yayi.

“Hidaya a da nine GARKUWAR ki,amma yanzu baki da wani GARKUWA da ya wuce Khaleel, ki bishi ki masa biyayya fiye da kowa a Duniya,wallahi idan kika aikata haka za ki tsira har ki samu Aljanna mad’aukakiya”

Yana gama wannan jawabin K’anwar Umma ta shigo d’akin domin fita da Hidaya,har sun je k’ofar fita Hamza ya yayi magana cikin sanyin murya.

“Ina takardar da na baki jiya?

Hidaya ta waiwayo ta d’ago kanta ta kalli Hamza fuska duk hawaye,ta d’ago tafin hannun ta nuna masa takardar,cikin muryar kuka tace .

“Ina tare da ita Ya Hamza”

Yayi murmushi ya russunar da kansa k’asa saboda hawayen da ke shirin zubo masa,yayi magana a hankali.

“Shikenan ki rik’e ta Hannu bibiyu,kuma idan za ki duba ta ki ringaji a Zuciyar ki kamar Mummyn tana gabanki,kuje Allah yayi miki Albarka ya sa ki shiga a sa’a”

Mik’ewa yayi ya shige toilet da sauri,yayin da Hidaya ta sake fashewa da kuka mai k’arfi,da k’yar K’anwar Umma ta ja ta suka fita daga d’akin.

An kai ruwa rana kafin a b’amb’are Hidaya daga jikin Umma,Sosai ta ruk’unk’ume ta tana shirgar kuka har da birgima,Umma kanta sai da tayi kukan rabuwa da Hidaya,shekara da shekaru suna tare amma yau sun rabu!ta San da Hamza ta aura babu abin da zai raba su,amma ya za su yi da hukuncin Ubangiji?

Haka aka rankaya domin kai Hidaya gidan ta,wadda tsananin kuka da yadda zuciyar ta ke tafasa take jin kamar ta mutu ta huta da d’acin rabuwa da Umman ta da Ya Hamzan ta.

 

 

****************

D’aki ne na alfarma da aka shirya shi da k’ayatattun kayan d’aki na musamman,duk da kasancewa ba nan ne muhallinsu da zasu dawwama ba,amma duk da hakan Khaleel yayi Namijin kokari wajen k’ayata wannan Muhallin.

Kowa ya fashe aka bar Hidaya kad’ai ita da Hansa’u da Sumayya,wad’anda suke ta lallashin ta ganin yawan kukan da take,Hansa’u cewa take.

“Ki rage kukan nan Hidaya,Auren soyayya kuka yi ke da Uncle Khaleel ba Auren K’iyayya ba,Don Allah kiyi hak’uri kar ki janyo ciwon ki ya tashi ! domin kin san yawan damuwa tana tayar da ciwon,wannan rana kamata yayi ki d’auketa ta farinciki ba akasin hakan ba,Ki bud’e idanuwa ki dubi baiwar da Allah yayi miki Hidaya,kin samu Miji na gari wanda bai rasa komai ba ! Me tsananin sonki da k’aunarki da begen ki, kamata yayi ki godewa Allah ba kiyi ta kuka ba……

Sumayya ta sauke tagumin da tayi ta saki ajiyar zuciya,fuska cike da jimami ta fara magana.

“Hmmm ! ke dai bari Sister Hansa’u, ni gabad’aya Hidaya ta sanyayar min da jiki na,wannan kuka da take kamar wadda aka kawo ta gidan mak’iyin ta?”

Sai lokacin Hidaya ta d’ago kai ta kallesu da kumburarriyar fuskar ta da tasha kuka,cikin dusashewar murya tayi magana hawaye na sake b’ullowa.

“Ba zaku fahimci kukan da nake ba k’awayena,abinda nake so kawai ku sani shine,ban riski wata rana a rayuwata da ta kasance min cikin yanayi guda biyu ba kamar wannan,ma’ana farinciki da akasin sa”

Da sauri Summaya ta tare ta da cewa.

“kamar ya ya ?fahimtar da mu Hidaya”

Hawaye na zirarowa tace.

“Yau d’in ranar farin cikina ce,haka nan ranar bak’in cikina ce!

A hanzarce suka dubeta suna shirin magana,motsin shigowa da sallama da k’amshin wani daddad’an turare ya dakatar da su.
Khaleel ya bayyana cikin k’ayatacciyar shigar da ta sake fito masa da asalin kyawunsa da haibarsa,kamalarsa ta cika gurin tsaf,Haske da walwali ne kawai suke fitowa a fuskarsa mai d’auke da k’ayataccen murmushi,idanuwansa akan Hidaya da kanta ke sunkuye tana sharar hawaye,Su Hansa’u suka bishi da kallo suna amsa sallamar sa,a zuciyar su suna fad’in “Gaskiya Hidaya kin dace da samun miji irin Khaleel”

A tare suka gaishe shi,ya amsa cike da kulawa da fara’a,Sannan ya zarce da cewa.

“Aboki yace in sanar da ku cewa dare ya fara yi,dan haka yana waje yana jiranku domin ku k’arasa gida tare dan duk an fashe babu kowa”

Hidaya na jin ya ambaci Aboki tayi zumbur ta d’ago kanta,ashe daman Ya Hamzan ta ya rakota gidanta kenan?to amma me ya sa yak’i shigowa?kamar Khaleel ya san tambayar da ke ranta taji yana cewa da su Sumayya.

“Na yi na yi ya shigo tunda shine babban Aminin Ango amma yak’i,wai cewa yake a wane k’auyen na tab’a ganin yayan Amarya ya halarci gurin siyen bakin k’anwarsa?na ce yazo a matsayin Aminin Ango mana,amma yace ba za a yi wannan zubar da girman da shi ba”

Su Sumayya suka yi dariya shi ma yana taya su,suna mik’ewa dan shirin tafiya sai gani zumbur ni ma na mik’e na rik’o hannun Hansa’u dake gab da ni,Uncle Khaleel ya waiwayo ya tsura min idanuwansa yana min wani gajiyayyen kallo me tafiya da numfashin mutum,da k’yar ya iya motsa bakinsa yayi magana a hankali kamar zai had’iyeni don kallon da yake min.

“D’an saketa kinji my love ! Aboki na jiransu dare yana sake yi kuma”

Fashewa nayi da wani irin kuka kamar zuciyata zata fito,Hansa’u tayi tayi ta k’wace hannunta amma ta kasa saboda rik’on da nayi mata me k’arfi kamar zan b’allata ina kuka,ban ma san lokacin da Uncle Khaleel ya zagayo ta bayana ba,kawai jina nayi a jikinsa yayi min wata shegiyar runguma ya dabaibayeni,bakinsa dab da kunnena ya fara yi min wata irin magana da zak’inta ya so juyar min da kaina.

“D’an cika ta ! Sakar mata hannu kar ki b’allata kinji my love ! saketa ! saketa don Allah !

Ban ma san lokacin da hannuna ya saki hannun Hansa’u ba,saboda tasirin da jikinsa yayi wa jikina,tamkar jik’ak’k’en tsumma haka na lafke a jikinsa yana rungume dani,ina ji ina gani su Hansa’u da Sumayya suka fice daga d’akin,a lokacin da Uncle Khaleel yake sake k’ank’ameni jikinsa yana sauke ajiyar zuciya me tsananin k’arfi a jejjere…..!

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SITTIN DA BAKWAI DA NA SITTIN DA TAKWAS

 

 

 

 

***Tun a lokacin Uncle Khaleel ya soma bautawa jikina da wata irin soyayya da lallashi na musamman,tun ina kuka har sai da hawayena suka k’afe k’af saboda zuk’e su da yayi,ina a jikinsa ya hanani motsi sai yadda ya juyani,har tsayuwa ta gagare mu sai gamu mun zube a gefen gado cikin numfarfashi.

Sai nake ji a zuciyata an ya za a samu mutumin da ya iya rarrashin mace da kalamai da gab’ob’i irin Uncle Khaleel kuwa?domin bai barni ba sai da kuka na ya tsaya tsaf ! har ma ya sakani murmushin da ban shirya ba,daga nan kuma ya jani toilet d’in cikin bedroom d’in muka d’auro cikakkiyar Alwala tare ,Bayan fitowar mu muka gabatar da Sallah Raka’a biyu a nutse.
Mun kwashe lokaci mai tsawo muna addu’o’i ni da Uncle Khaleel,kafin ya saka hannuwansa masu albarka ya kama kaina yayi min adduar da duk wani Ango yake wa Amaryarsa a daren farko,adduar da Manzon tsira alaihis salatu wassalam ya koyar da mu,tunda ya kama kaina yana karanta adduar nake jin wani sanyin dad’i na shiga tsokar jikina,wani yammmm ! nake ji, babu inda bai amsa ba a sassan jikina,tsigar jikina na mik’ewa yarrrr !

Ina Zaune tsuru tsuru ilahirin jikina ya mutu murus ban san dalilin hakan ba,har Uncle Khaleel ya mik’e tsaye ya fice daga d’akin,na sauke ajiyar zuciya ina runtse idanuwa na,wani sanyi sanyi nake ji tamkar wadda zazzab’i zai kawo mata farmaki.

Ina nan zaune ya sake shigowa da sallama,da k’yar na amsa cikin kasalalliyar murya,yazo gabana ya zauna kafad’ar sa na gogar tawa,a tare muka sauke numfashi tamkar wutar lantarki ta jamu saboda wani maganad’isu dake fizgar junanmu,ajiye tray d’in hannun sa yayi wanda ke d’auke da wani plate da gasassun kaji cike fal sun sha kayan had’i sai k’amshi ne ke tashi,ga kuma sassanyen juice da yoghurt a gefe,sai cups da fork .

Da kan sa ya ciyar da ni duk da na so yi masa gardama,amma wani kallo da yayi min tilas na bud’e bakina yana ciyar da ni har na k’oshi,da zarar hawaye ya ratso idanuwana zai kafeni da na sa idanuwan da wani sihirtaccen kallo wanda yake kassaramin gab’ub’uwan jikina,tilas nake maida hawayen ba da shiri na ba.

Sai da ya tabbatar da na k’oshi sannan shi ma ya ja gaban sa ya fara ci,a na ci yana kallona,da mun had’a idanuwa ya sakar min murmushin sa me k’ara masa kyawu da cikar kamala,a haka har ya kammala,ya sake jajibata muka yi toilet muka wanko bakin mu muka fito.

Wardrobe ya wuce ya bud’e ya zaro wata sleeping dress me azabar kyau,sai dai tana da d’an kauri ba mai bayyana jiki ba ce,har in da nake tsaye a tsorace ya iso gareni,Mik’o min yayi yana murmushi Sosai sannan ya ce.

“Karb’i ki sanya ki kwanta kiyi baccinki nasan kin gaji ko?”

Gyad’a kaina nayi cikin dukan zuciya na mik’a hannu na karb’i rigar daga hannunsa,Ya wani lumshe min idanuwansa yana karya wuya idanuwansa a kaina tamkar ya lasheni,a hankali kuma ya juya yana fad’in.

“Ina zuwa.”

Ni dai jikina a sanyaye yake har ya fice daga d’akin,cikin matuk’ar tsoro na sauke ajiyar zuciya na nemi gefen gadon na zauna,babu abin da ke raina sai Umma da Ya Hamza,ko ya suke yanzu?ko sunyi barci?ko suna cikin kewata?Hawaye mai d’umi ya zubo min ! Na sa bayan hannuna na share ina shesshek’a zuciyata tana ciwon rabuwa da su a muhalli d’aya.

Sai da na share Mintuna goma a haka,ganin Uncle Khaleel bai shigo ba sai na mik’e na cire kayan jikina na mayar da rigar baccin a jikina,na d’an fesa turare kad’an saboda iya k’amshin da ya manne min a fatar jikina ma ya wadatar,ko ya ya ka matso jikina tilas ka shak’i k’amshi mai dad’i da nutsar da zuciya.

Har na kammala bai shigoba,hakan ya sa na haye gadon na takure guri d’aya,sai nake jina tamkar wata marainiya a lokacin ! tamkar wadda ta rasa komai da kowa !duk da zan iya cewa na rasa komai d’in,babu mahaifiya a tare dani balle mahaifi,babu Ummana a kusa da ni,babu Ya Hamza GARKUWA TA”

To amma ai akwai Uncle Khaleel,wanda Ya Hamza yayi ta nanatamin cewar a yanzu shine komai nawa ! shine GARKUWA TA,shine komai a gareni.

Zuciyata ta kuma karyewa ! wani kuka ya tawo min irin me tokare k’irjin nan,nayi ta shatatar da hawaye yana jik’a min pillow d’in da na d’ora kaina,tsawon lokaci ina kukan da ban san tak’amaimai dalilin yin sa ba,ni dai kawai na samu zuciyata ne cikin matsanancin rauni da kewar Abubuwa,a hakan naji motsin shigowar Uncle Khaleel…

Chak ! na tsayar da kukana,saboda bana son yaji har na saka shi a damuwa,bai nufo in da nake ba sai ya nufi wata drower ya d’auko alk’ur’ani mai girma ya zauna kan wata kujera da ke gefe ya soma karanta suratul Rahman cikin murya mai dad’i da Nutsuwa,Wannan karatu da yake yi shi ya sanyaya min ruhina na dinga jin salama a k’irjina da ya tokare,Idanuwana a lumshe tamkar me bacci ko motsi bana yi,ya jima yana karatun kafin yayi addu’o’in sa ya shafa,ina ji yana tayi wa Ya Hamza addu’a da fatan alkairi mara yankewa,yawanci adduarsa akan Ya Hamza take,hakan yasa na k’ara tabbatar da cewa Uncle Khaleel ba k’aramin so yake wa Ya Hamzana ba.

A lokacin da ya kammala yaje ya maida alk’ur’anin sai naji takunsa ya nufo in da nake,na sake runtse idanuwana tamkar mai bacci ina sakin numfashi a hankali,nan kuwa tsoro ne ya cika zuciyata kamar ta faso k’irjina ta fito,ina jinsa ya hawo gadon a hankali wai gudun kar ya tasheni,bai san idona biyu ba,Can gefe ya kwanta rigingine yana ajiyar zuciya tare da runtse idanuwansa,sai naji yana ta ambatar “Alhamdulillah” ya dinga fad’a har ban san adadin yawan Hamdalar da ya dinga yi ba.

kusan minti Ashirin sannan naji yana matsowa a hankali har ya iso dab da ni,k’irjinsa ya had’u da bayana,tsigar jikina ta mik’e yammm! yayin da naji ya saki gwauruwar ajiyar zuciya me tsananin k’arfi,zuro hannuwansa yayi ta gabana yayi min wata kyakkyawar runguma da taso rikitani,amma na maze na cigaba da nuna cewa ni d’in fa bacci nake yi,a haka ya dinga mannemin har saida jikinmu ya game wuri guda,sassanyar Numfashin sa na sauka a kan dokin wuyana yana tada tsigar jikina.

Shi a zatonsa bacci nake,shiyasa naji ya fara wata irin magana a hankali cikin rad’a,wata irin magana da ta dinga ratsa fatar jikina zuwa naman jikina har ta b’ulla cikin k’asusuwa ta kassara b’argon jikina,ina matse a jikinsa yake maganar dab da kunnena cikin rawar jiki da shesshek’a….

“D’azu Aboki yace min kar na bar komai….Na cinye komai…kar na rage komai….yace min idan yace komai to yana nufin komai…..Su Sumayya suka yi min rowar ganinki wai sai na sayi bakinki,Ni kuma basu san cewa dukkanki nake so ba ba iya bakinki ba….Wallahi ina sonki Hidaya…ina sonki tun ranar da na fara ganinki a duniyata….Na rayu da dakon soyayyarki tsawon shekaru wadda naso na bayyana miki ita a daren yau….sai dai ba zan iya katse miki baccin da kika fara ba….amma a yadda nake jina zan kwana ne cikin wahala da kewa ! ina ma bakiyi bacci ba ! ina ma na iskeki ido biyu ! ina ma zaki karb’i bak’unci na a yanzu ! ban tab’a jin wani yanayi mai tsananin girma a tare dani kamar yanzu ba Hidaya !I love you ! I love you very much ! I cant explain how much I love you !

Sai ya sake wani irin k’ank’ameni kamar zai maidani cikinsa,ina jin ruwa mai d’umi na sauka kan dokin wuyana yana gangarawa k’irjina,na san ba kowane ruwa bane face hawayen Uncle Khaleel da yake kwarara ! hawayen Soyayyah ! hawayen k’auna ! hawayen bege ! hawayen sha’awah ! hawayen komai !

Bantab’a jin tausayinsa ba irin lokacin,na dinga jin wani abu na ratsani yana mamayeni mai kama da soyayyarsa da k’aunarsa,sai naji kamar na bayyana masa cewar ba bacci nake ba ko dan ya samu cikar burinsa,amma na kasa hakan,wani hawaye ya tawo min,nayi hanzarin shanye abuna don kar ya gane.

Haka ya dinga sambatun sa a jikina,sambatun soyayyah! har bacci yayi nasarar kwasheshi yana ta ambatar yadda yake sona! Ni kuwa idanu ba bacci,zuciyata na ta kai kawo ! sai bayan awa biyu da baccin sa sannan nima baccin ya saceni,wani irin bacci mai tsananin dad’i da ban tab’a samun irinsa a rayuwata ba.

 

 

 

*************

 

 

 

Wajen k’arfe goma sha d’aya na daren Umma na zaune babu bacci a idanuwanta,babu abinda take jira sai shigowar Hamza cikin gidan saboda dare yayi,ragowar y’an bikin duk sun yi baccin gajiya ita kuwa idanuwanta tar babu alamun bacci a cikinsu,sai Sha d’aya da rabi ta ji shigowar sa ya kulle gidan,sannan taji ya bud’e d’akinsa ya shige,a hankali ta mik’e ta nufi d’akin nasa don ganin yanayin da yake ciki.

Lokacin da tayi sallama ta shiga a tsaye ta tarar da shi yana k’ok’arin cire rigar da ke jikinsa,ya waiwayo a hankali rigar a hannunsa yana amsa sallamarta,a hankali ya saki murmushi murmushin da ya fito da tsananin ramar da yayi a fili,cikin k’aramar murya ya ce.

“Ummana baki yi bacci ba kenan?”

Umma ta samu kujerar d’akin ta zauna tana dubansa cike da tausayawa tace.

“Banyi ba Hamza,ina jiran shigowarka ne naga dare yayi amma baka shigo ba”

Ya d’an sunkuyar da kai yana jin k’aunar mahaifiyarsa na linkuwa a ruhinsa,ya d’an zame ya zauna gefen gadon sannan ya d’ago kai yayi murmushi yana duban Umman yace.

“Na tsaya tawowa da su Hansa’u ne Umma,daga nan kuma na tsaya sallamar ragowar abokanan mu da suka zo taya mu muranar biki”

Umma ta jijjiga kai,cikin rauni tace.

“Alhamdulillah da aka gama bikin nan lafiya lau,naji dad’i sosai,to ya ka baro min Fad’imar?dafatan dai ta daina kukan?”

Ya girgiza kai,a hankali yace.

“Ban sani ba ko ta daina,domin nidai ban shiga ciki na ganta ba”

“Me yasa hakan Hamza?”
Umma ta tambaye shi idanuwanta a kansa.

Yayi shiru bai ce komai ba kansa a sunkuye,har Umma ta sake kiran sunansa .

“Hamza”

A hankali ya d’ago kai k’walla na taruwa a idanuwansa ! Umma taji tausayinsa matuk’a,shiyasa ta sanyaya murya tace masa.

“Kayi hak’uri kaji Hamza ! Ka cire komai daga ranka,ai kayi namijin k’ok’ari kuma Allah yana sane da kai da hak’urin da kayi,kuma zai maka babban tukuici ta inda baka zata ba,na san kana jin ciwo a zuciyarka sosai,na san kana jin kewa a ruhinka ! na san ba wanda zai san abinda kake ji sai wanda ya tab’a d’and’anar abinda ka d’and’ana Hamza !amma duk abinda kake ji da sanin Allah ! domin tuni Allah ya rubuta komai da zai faru har izuwa tashin k’iyama.
Allah yana cewa.

” ألم تعلم أن الله يعلم ما فى السماء والأرض,إن ذالك فى کتب,إن ذالك على الله يسير”

Ma’ana( Shin ba ka sani ba ne,cewa Allah yana sane da abin da yake cikin sama da k’asa.Lalle wannan yana cikin littafi.Lalle wannan wani abu ne mai sauk’i a gurin Allah).

Don haka duk wani yanayi ko halin da ka samu kanka a ciki to da sanin Allah,kuma idan kayi hak’uri da juriya to zaka rabauta,Allah da kansa yana yin albishir zuwa ga masu Hak’uri,kasan wannan sai dai na tunasar da kai Hamza,Don Allah kayi hak’uri ka fawwalawa Allah komai,ka rage yawan damuwa duk da nasan kana k’ok’arin hakan,amma ramar nan da kake tana tayar da hankalina Hamza”

Hamza dai hawaye tuni ya wanke fuskarsa,kuka sosai yake yi nasihar Ummansa na shigar sa,babu abin da ya sake raunata zuciyar sa irin maganar da Umma ta cigaba da yi akan ya daure ya nemi matar aure shi ma yayi aure,hakan zai sa ya samu sauk’in wani abin,sai yake ji a zuciyar sa anya kuwa zai iya son wata bayan Hidaya?wadda ya rayu da ita da sonta tsawon shekaru masu yawa?to ba zai yanke hukunciba dai tunda Allah shine masanin komai da kuma abin da zai faru a gaba.

Umma dai bata bar d’akin ba har sai da ta sa Hamza ya karanta alk’ur’ani mai girma domin ya samu sauk’in zuciyar sa kan damuwar da ta cunkusheta,domin duk lokacin da kake cikin wata damuwa in dai ka karanta alk’ur’ani za ka samu sauk’i, Ambato ne mai hikima ! tafarki madaidaici !shine wanda soye soyen zukata ba sa karkacewa da shi ! harasa ba su rikicewa da shi,malamai ba sa k’oshi da shi!baya tsufa saboda yawan karantawa ! Abubuwan mamakin sa ba sa k’arewa ! wanda yayi magana da shi ya yi gaskiya ! wanda yayi aiki da shi zai sami lada ! wanda yayi hukunci da shi ya yi adalci ! wanda yayi kira zuwa gareshi ya yi kira zuwa tafarki madaidaici ! wannan shine littafin Allah wato (Alk’ur’anil kareem).

Kafin wani lokaci sai damuwar Hamza ta yaye a daren,saboda falalar karanta alk’ur’ani,har ma ya samu bacci mai dad’i wanda ya jima bai samu ba a rayuwar sa.

 

 

***********

Ina takure kamar mai jin sanyi a lokacin da muka idar da sallar asuba,har ma gari ya fara haske saboda karatun da muka tsaya yi,idanuwa na suka soma lumshewa alamar bacci na kawo min ziyara,Uncle Khaleel ya rufe alk’ur’anin gaban sa ya dubeni da murmushi akan kyakkyawar fuskarsa,a hankali kamar me rad’a ya ambaci.

“Barci….?”

Gyad’a kaina nayi ina yin hamma,ya k’ura min idanuwansa da na hango zallar sha’awata a cikinsu saboda wani irin sauya kala da suka yi,da sauri nayi k’asa da kaina saboda yadda naji jikina ya soma rawa rawa,idanuwansa a kaina yace min.

“Je ki ki kwanta,amma ki cire wannan hijabin”

Da hanzari na mik’e na nufi gadon,na cire hijabin na ninke na ajiye kan bedside drower,sannan na haye gadon ina kwanciya,duk abin da nake idanuwan sa a kaina,sai a lokacin ne ya naji yo muryar sa mai tsananin dad’i yana ce min.

“Ki d’an rage min guri kad’an zan zo na tayaki baccin ni ma,kinji My love”

ina jin maganarsa sai na matsa can lokon gadon na bar masa fili mai yawa,har ya kammala abin da yake ya iskeni har in da nake.

chak naji ya d’aukoni kamar jaririya ya dire ni a kan k’irjinsa,ya mamayeni ya rungumeni tsaf,k’amshin da jikinsa ke fitarwa mai tsananin dad’i ya cika min k’ofofin hancina,kunya ta saka ilahirin jikina rawa kar kar kar,ya saka hannuwansa masu taushi yana shafa bayana tare da k’ara nutsar da kaina a k’irjinsa,na sake runtse idanuwana ina sauke ajiyar zuciya a sanda naji yana shafani tamkar wata mage,sannan cikin k’aramar murya yake fad’in.

“Za ki iya tuna sau nawa na tab’a cewa Ina sonki?”

Girgiza kaina nayi domin ba zan iya magana ba,jikina ya mutu murus da sak’on da yake aika min,sarai yaji girgiza kan da nayi,shiyasa cikin wata irin shesshek’a ya sake ce min.

“Tun da nake ambata miki soyayyar na tab’a nuna miki ita a zahiri kuma a aikace?”

Nan ma girgiza kai nayi har hawaye ya soma ciko idanuwana tsabar jin dad’in abubuwan da hannun Uncle khaleel suke min,birkitoni yayi yana tallafe da ni,na koma k’asa yayin da yake saman jikina,amma bai sakar min nauyi ba duk da shi d’in siriri ne,runtse idanuwa na sake yi hawaye na fito min,yayin da naji bakinsa dab da hancina yana wata irin magana,k’amshin da ke fitowa kad’ai daga bakinsa ya isa rud’ar da mutum.

“To Don Allah Hidaya ki bani dama mana !bani dama ko da y’ar kad’an ce yau na nuna miki ! Na rantse miki Soyayyar ba irin wadda ake juyawa baya ba ce! kinji Hidayanahhhhh……!

ji nayi ma kawai ba zan iya yi masa musu ba,gabad’aya Uncle Khaleel ya birkita min kaina,wata irin birgima ya soma yi a jikina tare da wasu abubuwa tamkar zai shid’e min,fad’i yake cikin kyarmar murya da sark’ewar numfashi.

“please Hidayaaaaa ! Na rok’eki don Allah Hidayaaaa! don Allah ! don Allah ! don Allah !

Ganin zai zauce min ban san lokacin da na bashi dama ba,hakan ya k’ara rura wutar abin da yake ji,kafin wani lokaci Uncle Khaleel ya zama mahaukaci tuburan a jikina,domin tsintar bakinsa nayi cikin nawa yana wasu abubuwa da ban san da su a duniyar mu ta mutane ba,kafin ya cire bakin sa ya gangaro k’irjina,anan wuta ta d’auke min d’if.

Ban tashi dawowa hayyacina ba sai da naji yana kuka sosai yana karanto wata addu’a,kafin kuma ya had’e jikinsa na jikina cikin wani yanayi mara fassaruwa,ni dai azabar da ta ratsani ji nayi kamar zan sume,babu abin da ke yawo a kaina sai kukan Uncle Khaleel cikin wani yanayi yana fad’in.

“Hidaya Zan mutu ! zaki kashe ni Hidaya ! wayyo Allah My Love…!

Daga hakan ban sake tuna komai ba har zuwa sanda ya gama bidirinsa,yayi kid’ansa yayi rawarsa,yayi biji biji da ni a wannan lokaci.

Ban tashi sanin in da kaina yake ba sai da na jini cikin ruwan zafi,na saka kukan da ya tayar masa da hankali,ya dinga lallashina yana sakamin albarka har ban san adadi ba,shine ya gasa min jikina yayi min komai,bakinsa bai gajiya da yabona da saka min albarka da kuma nanata min kalaman soyayyah ba…

Hatta break fast da kansa ya dafa min,da riritawa da lallashi da labaran ban dariya ya dinga ja na har na samu naci wani abin,ina jikinsa ya cikani da soyayyarsa wadda ta cika ruhina taf,domin tashi d’aya naji Uncle Khaleel d’in ya mamaye ko’ina a sassan jikina da zuciyata har ma da Raina.

Lokaci guda wayarsa ta d’auki k’ara,ina a jikinsa ya d’aga alokacin da naji yana mik’a gaisuwa zuwa ga wanda ya kira,na tabbatar da daddyn sa ne,har suka kammala wayar ya ajiye,ya dawo da hankalinsa kaina yana tallafo fuskata ya sakar min murmushi,lumshe idanuwa nayi saboda kunyarsa da nake matuk’ar ji,a kunnuwa na naji maganar sa yana cewa.

“Shine jiya kika dinga kiran Umma da Aboki su zo su ceceki ko?amma gaskiya Aboki ya yarfeki da yak’i amsa kiranki ya zo ya k’waceki a hannuna,ko da yake ma ai shine yace min in cinye komai ! kar na rage komai ! kuma na karb’i shawarar sa na cinye komai d’in ko My love?ko akwai abin da ya rage wanda ban cinye ba yanzu na cinye shi?”

Ban san lokacin da na k’ara nutsa kaina a k’irjinsa ba,kunya kamar ta kashe ni,shi kam dariya ya dinga yi min yana sake rungumeni,haka ya cikani da tsokana da soyayyah har ya direni kan gadon ya mik’e tsaye yana cewa.

“Bari naje daddy na kira na,yanzu zan dawo mintuna kad’an”

Fuska a k’unshe na jijjiga kaina,yayi murmushi ya sunkuyo ya d’an lalubeni ya ragewa kansa zafi,kafin ya kad’a kai ya fice fuska cike da annashuwa da farinciki.

Sai da yayi wajen minti biyar da fita sannan na samu y’ar nutsuwa na bud’e idanuwa na,nayi kasak’e zuciyata k’al,can kuma takardar da Ya Hamza ya bani ta fad’o min a rai,takardar da yace ta fito ne daga hannun mahaifiyata a lokacin da ta dank’a masa amanata,take naji zuciyata na zakwad’in ganin me takardar ta k’unsa,da hanzari na mik’e jikina na rawa na nufi jakata da na sakata a ciki,d’akkota nayi na dawo gefen gadon na zauna na fara k’ok’arin bud’e envelope d’in,ina bud’ewa na fara k’ok’arin zazzago abin da ke ciki,abubuwa guda biyu ne suka fad’o kan cinyata,wata farar takarda mai d’auke da Rubutu,sai wani hoto guda d’aya tal da na bishi da kallo ina yi masa kallon sani daga nesa nesa,ajiye hoton nayi na d’auki takardar na warware domin ganin abin da ta k’unsa……!

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SITTIN DA TARA DA NA SABA’IN

 

 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un ! innalillahi wa inna ilaihir raji’un ! innalillahi wa inna ilaihir raji’un !”

Abin da zuciyata take ta maimaita wa kenan,saboda bakina ba zai iya motsi ba ma falle wani furuci ya fito daga ciki tsabar gigicewa da rud’ewar tunani,ban tab’a cin karo da abin da ya tayar da hankalina ya dugunzuma min tunani irin wannan sak’o na mahaifiyata ba,kafin wani d’an lokaci tuni kammaninaa sun sauya,k’irjina na ci da wuta kamar ya babbake,hawaye kuwa tamkar an kunna famfo irin me zuba da gudun nan,hankali na tuni ya soma fita daga jikina,bani da wani buri illah cika burin da mahaifiyata ta umarceni a kansa,bayan hakan kuma fa?sai son ganinta da mararin rab’ar jikinta! domin ni ma d’in naji abin da mutanen duniya suke ji idan suna tare da iyayen su ! to amma tambayar ita ce !

Ina zan ganki mahaifiyata?
Yaushe idanuwan mu za su ga juna?
Yaushe Numfashina da na ki za su gauraya a muhalli d’aya?
Yaushe zan sake jin d’umin jikinki kamar yadda kowane d’a yake son jin d’umin jikin mahaifiyar sa?
Yaushe…?yaushe…?yaushe…? duk yaushe wad’annan abubuwan za su faru…?

Runtse idanuwana nayi cikin matuk’ar ciwon zuciya da sartun hawaye,Na rungume takardar a k’irjina ina kuka sosai ina nadamar bak’inta da na dinga gani,Allah ya sakawa Ya Hamza da alkairi ya biya masa buk’atunsa na alkairi,abinda zuciyata take nanatawa kenan,dalilin shine jigon da yake sarrafani wajen hanani aibata mahaifiyata,wadda a kullum yake fad’amin tafi kowa sona da k’aunata! ban tab’a yarda da hakan ko amincewa ba sai da na karanta rubutun da ya fito daga hannunta.

To wai shin a yanzu menene ya ragemin ne?Na tambayi kaina cikin kuka da Nadamar rayuwa.

Sai naji zuciyata na bani amsa da cewa.

“Cika umarnin Mahaifiyarki shine abu na farko da za ki yi,duk da hakan abu ne mai tsananin had’ari da wahala,kuma gashi lokaci ya k’ure miki,amma duk da hakan ki k’ok’arta ki aiwatar Hidaya,hakan zai sa ko da ba ta duniyar ta kasance mai alfahari da ke domin share mata kukan ta da kika yi”

A lokacin da k’arfin zuciya ya shigeni,alokacin ne kuma na jiyo muryar Mijina Uncle Khaleel yana k’wala min kira tun daga parlour,fad’i yake.

“Kina ina ne?fito kinyi babban bak’o,Daddy da kansa ya zo ya ganki kafin ma kije ki gaishe shi”

Hoton da ke hannuna na sake bi da kallo,kafin cikin hawayen na saki wani irin murmushi wanda ban tab’a yi ba ina girgiza kai,jin muryar Uncle khaleel na sake dumfaro bedroom d’in da sauri na had’a takardar da hoton na cusa su k’ark’ashin pillow,da hanzari kuma na wawuri hijab d’ina na zumbula na jawo shi ya rufemin rabin fuskata saboda bana so Uncle Khaleel ya fuskanci halin da nake ciki a yanzu.

Mik’ewa nayi zan nufi parlour’n,ina zuwa bakin k’ofa muka ci karo zai shigo ni kuma zan fita,da saurin sa ya mamayeni ya rungumeni tsaf a jikinsa,wani sanyin dad’i naji duk da zuciyar ta wa babu dad’i,kuka nake son yi amma na tabbatar idan nayi zan tada hankalinsa,kuma zai nemi jin ba’asi,wanda ko kusa ko alama a yanzu ban shirya sanarda shi komai ba,ajiyar zuciya ya dinga saki a jejjere yana k’ara rungumata,kafin a hankali ya fara magana cikin murya k’arama.

“Kinga wai fa daga zuwa kiran Daddy shine yace min na rakoshi ya ga y’arsa,tun da dai bai tab’a ganinki ba,nace ma ya bari na kawo masa ke amma yak’i yarda,har da ce min wai menene dan Uba ya gaida y’ar sa?ai durk’usawa wada ba gajiyawa bane”

Luf nayi a k’irjinsa ina jin dad’in kulawar da mahaifinsa ya bani,Allah sarki ni da Ya Hamza da muka rasa namu mahifan !hawaye ya tawo min nayi hanzarin mayar da shi.

A haka ya ja hannuna muka fice zuwa parlour’n kaina a k’asa.

A tsaye muka tarar da Daddyn yana jiran isowar mu,Uncle khaleel yayi magana cikin shagwab’a da murmushi hannayen sa rik’e da nawa hannun.

“Daddy ya ka tsaya baka zauna ba?

Cikin zaulaya Daddyn ya bashi amsa da cewa.

“Ina jira a bani umarnin zama ne”

Dariya Khaleel yayi yana jana har gaban Daddyn ya tsugunar da ni shi ma ya tsuguna,sannan ya d’aga kansa sama yana kallon Daddyn da ke tsaye yana duban mu fuskarsa kadaran kadahan,cikin muryar ladabi Uncle Khaleel ya ce.

“Ga d’iyarka na kawo maka Daddy,ka sanya mana albarka da ni da ita”

Daddy yayi murmushi ya nemi waje ya zauna kan kujerar da ke dab da shi,yayin da Uncle Khaleel ya janyo hijabina baya domin fuskata ta bayyana,cikin k’aramar murya mai cike da soyayya kuma yake fad’in.

 

“ke fa kunyarki tayi yawa,to dai a gaban Daddy kike wanda ya kasance mahaifi a garemu baki d’aya,ya kamata ki bud’e fuska ki dubeshi ya dubeki tunda yau ce rana ta farko da kuka had’u da juna tsawon lokaci”

Haka kawai na samu kaina da fad’uwar gaba ban san dalili ba,a hankali kuma na d’ago kaina da nufin kallon Daddy domin na gaishe shi,a lokacin ne shi ma Daddyn ya karkato da kallonsa zuwa gareni,karaf idanuwan mu suka sark’e da juna,bakina na bud’e da niyyar furta gaisuwa gareshi amma sai maganar ta gagara fitowa tsabar bugawar da kaina yayi tare da matsanancin tsoron da ya shigeni.

K’ura min idanuwa Daddyn yayi cikin wani irin kallo mai kama da na mamaki ko al’ajabi,yayin da jikina ya d’auki wani mugun rawa kar kar kar,wata irin mik’ewa nayi a razane har hijabin da ke jikina na niyyar tad’eni na fad’i,da sauri nayi baya na d’ago hannuna ina nuna Daddyn da hannuna jikina na mazari amma bakina ya kasa furta komai,Daddyn yana daga zaune yake kallona ya kasa fuskantar abin da nake nufi,yayin da Uncle Khaleel ya mik’e a tsorace yana kallona ganin yanayin da na shiga na mugun firgici a take,k’ok’arin takowa yake gareni cikin gigicewa yana ambatar .

“Hidaya lafiyarki kuwa?me ya faru ne?me ya gigita ki haka?

kafin ma ya k’araso na d’aga hannuna na dakatar da shi cikin wani irin nishi da numfarfashi,idanuwana a warwaje tamkar me shirin ta da iskokai,birki ya ci yana zuba min narkakkun idanuwan sa a tsorace,a yayin da na juya da gudu na nufi cikin bedroom d’in da muka fito dan k’ara tabbatar da zargina.

A rikice Uncle Khaleel ya juya yana kallon Daddy,wanda shi kansa Daddyn cikin tsananin mamaki yake,cikin wata wahalalliyar murya da tamkar arota yayi yayi wa Daddyn magana.

“Daddy wai me yake faruwa ne?kalli halin da yarinyar nan ta shiga,an ya kuwa lafiya lau take?

Daddy yayi shiru alamar nazari,kafin ya sauke ajiyar zuciya mai k’arfi ya dubi Kahleel da ke tsaye cikin d’imuwa ya ce da shi.

“Bi ta ka duba halin da take ciki”

Jijjiga kai Uncle Khaleel yayi cikin sanyin jiki,kafin yaja k’afafuwansa da suka yi masa nauyi zuwa in da na nufa.

Ni kam ina shiga babu in da na nufa sai bakin gado,a hanzarce na d’aga pillow na zaro takardar da na gama karantawa yanzu wadda ta fito daga hannun mahaifiyata,ba takardar nake son gani ba,hoton da ke tare da takardar shi nafi muradin sake kalla domin na tabbatar da zargin da zuciyata da idanuwa na suke min,k’urawa hoton ido nayi cikin fitar hayyaci,nan take k’wak’walwar kaina ta cigaba da haska min da tabbatar min da cewar tabbas abin da nake gani d’in gaskiya ne.

A haukace na cillar da hoton,na juya domin nufar palour’n k’irjina na ci da wuta,domin bana cikin hankalina,ji nake yi zan iya yin komai a lokacin.

Dab da bakin k’ofa na sake cin karo da Uncle Khaleel wanda ya biyo ni d’akin dan ganin abin da ke faruwa,gani na a haukace ya sa ya k’ara gigicewa ya rik’o ni gam yana shirin jefani k’irjin sa ya rungume ni,tamkar wata dutse haka nayi k’ik’am a gabansa nak’i bashi damar hakan,ya jefa idanuwansa cikin nawa idanuwan da suke d’auke da buhu buhu na tashin hankali,cikin wani irin yanayi ya soma girgiza kafad’una yana magana a rud’e kuma a gigice.

“Wai meye haka ne?me kike yi haka ne?me yake damun ki ne?Hidaya ki dawo cikin nutsuwarki ki fad’a min menene yake faruwa?za ki tarwatsa min kaina My love….please me…..

kafin ma ya k’arasa maganarsa na fizge jikina daga gareshi,cikin wani irin fushi kuma na sa hannaye na daki k’irjinsa ina tunkud’eshi gefe guda,Da sauri ya durk’ushe k’asa cikin tsananin azaba yana daf’e k’irjinsa tare da wani d’an ihu yana fad’in “ahhhhhh…subhanallah… !, saboda dai dai gefen zuciyar sa na daka,shi d’in kuma me rarraunar zuciya ne wadda take cike da ciwuka.

Ko kallon in da yake ban yi ba na wuce a haukace na zuwa palour’n,in da na tarar da Daddyn a tsaye cikin firgici saboda jiyo k’arar da Khaleel yayi.

Ban tab’a sanin cewar ina da k’arfi ba,ban tab’a sanin cewar ramammu irin mu masu sikila za su iya aikata abin da na aikata ba,sai dai na san cewar b’acin rai babu abin da baya sakawa,domin ban tsinci kaina a ko’ina ba sai gaban Daddy,wanda nake nufar sa jikina na rawa matuk’a da gaske,hankalina kam tuni ya gushe a sanda na ci burki a gabansa,na d’aga hannuna na sharara masa wani uban mari wanda sai da hular kansa ta fad’i a k’asa,gidan kansa sai da ya amsa tsabar k’arar marin,ban kuma tsaya nan ba sai ga hannaye na shak’e da kwalar rigar sa na matse shi ina girgiza shi.

Dai dai lokacin da Khaleel ya rarrafa ya fito daga bedroom d’in,akan idanuwan sa na waskawa mahaifinsa mari !akan idanuwan sa na ci kwalar mahaifinsa ! akan idanuwan sa ni matar auren sa nake girgiza mahaifinsa ! da me zai kwatanta wannan tashin hankalin da yake neman kai shi lahira? kafin ya dawo daga mutuwar ido biyu sai ya tsinto muryata cikin k’ara da tsananin tashin hankali ina fad’awa mahaifinsa munanan kalamai.

“Tunda uwa ta ta haifeni na fad’o duniya har zuwa yanzu da na girma ban tab’a cin karo da tsinannen mutum irin ka ba,gafalalle mara mutunci,mara tausayi mara kyawawan d’abi’u,mara haiba mara kamala,mara kirki mara kyawun zuciya,asararre wanda ya zo duniya a banza zai koma a wofi,Na rantse da girman Allah ko zan yi yawo babu komai a jikina sai naga bayanka ! yadda ka sa mutane da yawa kuka a duniya kaima sai ka koka kafin ka bar duniyar ! domin sai …..

Wani irin wurgi naji an yi dani gefe guda a lokacin da aka fizge hannuwana daga wuyan Daddy,wanda idanuwansa ke warwaje sunyi tulu tulu tsabar shak’ar da yaji,wani irin tari ya sark’afeshi,Uncle Khaleel ya juyo kaina a gigice yana nuna ni da hannunsa d’aya,hannu d’aya kuma yana rik’e da Daddy wanda ke maida numfashin wahala yana ta wani irin tari,da k’yar Khaleel ya iya fizgo maganar da yake son yi har ya samu ta fito.

” Wannan fa mahaifina ne Hidaya! shine fa uban da ya tsuguna ya haifeni ! kin sha k’waya ne da kike furta wad’annan munanan kalaman a kansa? me ya shiga kanki cikin k’ank’anin lokaci ya sauyaki daga halittar da na sanki?

A hanzarce na mik’e daga fad’uwar da nayi ina yiwa Daddyn wani kallo na muguwar tsana mara iyaka,kafin a zafafe na juya na kalli Uncle Khaleel da yake rik’e da Daddyn,cikin wata b’atacciyar murya na mayar masa da raddin maganarsa.

“Ai na fi kowa sanin mahaifinka ne! na san cewar babanka ne ! sai dai ka sani baka yi sa’ar uba ba ! baka more ba da ka zamo jinin wannan azzalumin mutumin mara imani da tsoran Allah ! ayau ina danasanin had’a hanya da shi,ina bak’inciki da na same shi a matsayin uban mijina…kuma wallahil azeem hakan ba zai saka ni fasa k’udirina akan sa ba…domin..

Marin da aka zabga min mai tsananin zafi shine ya dakatar da ni daga maganata,kafin na dawo hayyacina Uncle Khaleel ya cukumeni kamar yadda na cukumi mahaifinsa,cikin k’araji da tsananin masifa kamar ya shid’e yake jijjigani yana kifamin maruka da d’aya hannun a jejjere,bakin sa na kumfa wajen zazzago min kalamai cike da masifa.

“Kar kiyi amfani da damar da kika samu a kaina ki ce zaki wulak’antani,kar kiga son da nake miki ya kai k’ololuwa ki nemi ki kasheni a tsaye,tabbas ina sonki Hidaya,amma son da nake miki bai kai son da nake wa farcen mahaifina ba,wallahi duk wanda yace zai tab’a min mahaifi sai in da k’arfina ya k’are a kansa,zan iya hak’ura da ke da son da nake miki in zab’i mahaifina,me mahaifina yayi miki?me Daddyna yayi miki da kike masa wad’annan mugayen abubuwan?yau ne rana ta farko da kika fara ganinsa a duniyar ki,amma me ya shiga kanki da kika tozarta shi a gabana?giya kika sha?ko haukacewa kika yi?tambayarki nake ki ban amsa kafin nayi k’asa k’asa dake na taka wuyanki,soyayyar da nake miki ta ci uwarta! ita soyayyar ta ci ubanta! na bita na tattaketa na murje mata wuya in dai akan mutuncin mahaifina ne”

Ba zan iya k’irga adadin marin da Uncle Khaleel yayi min ba yana zuba min bala’i da masifa cikin hargowa da kumfar baki,kafin kace me kumatuna sun kumbura suntum,amma ban saduda ba,bala’in da ke ci na a k’irjina ya fi gaban kwatance,zuciyata tafasa take yi ina k’ara jin tsanar Daddy a raina,burina naga bayansa ! muradina naga babu shi a doron duniya !

Cikin wani irin layi na tamkar ina cikin maye nake duban Uncle Khaleel da idanuwa na,wanda nake hangar abubuwa guda biyu cikin na sa idanun,wato Soyayyata da ta jima a tare da shi,da kuma tsanata da ta fara kafuwa cikin mintunan da suka gabata,cikin wani irin murmushi na bak’inciki na dubeshi nace.

“Mutunci…? wannan tsohon najadun kake ambatawa mutunci?wannan tambad’ad’d’en mutumin kake zatarwa mutunci da kima?wannan …..

Wani wawan marin Uncle Khaleel ya sake kifamin wanda yayi sanadiyyar fashewar bakina da hancina,nan da nan jini ya fara bin fuskata,amma duk da hakan banji komai a raina ba,banji zan iya dakatawa da abinda zuciyata ta niyyata ba,ko gezau banyi ba,illa sake k’ura masa idanu da nayi cikin yanayi na masifaffen tashin hankali,a lokacin da na riski hawaye ya fara malala a kumatunsa yana bin jinin da ke fita ta hancina da bakina da kallo,a lokacin ne nima naji wani hawaye mai tsananin zafi ya kawowa idanuwana ziyara,cikin dakakkiyar murya na fara magana ina duban cikin idanuwansa da suke a juye.

“Ko kashe ni zaka yi ba zan fasa kiran wannan mutumin da azzalumi ba,ko ratayeni zaka yi ba zan fasa kiran sa mugu mara imani ba,Uncle Khaleel ko tsireni zaka yi ba zan fasa.

Wani irin shak’o wuyana yayi ya gara ni da garu ya matseni,cikin mugun rawar jiki ya sake kifa min gigitaccen marin da ya kusa wucewa da numfashina,bakinsa na mugu mugun kyarma yake ambatar.

“Ba za ki daina zagin mahaifina a gabana ba ko?ba za ki daina ambatarsa da mugayen kalamai ba ko?za ki sa na yanke miki hukunci mai zafi Hidaya,za ki sa na aikata abinda baya cikin tsarina,za ki sa muyi mutuwar kasko ni da ke ,za ki sa….

Wani irin tari me k’arfi ya sark’afe shi yayin da ya sakeni yake dafe k’irjinsa cikin wahala,ban dubi yanayin da yake ciki ba saboda na kai matuk’ar k’urewa a fagen tashin hankali,shiyasa na cigaba da zagin Daddy a gabansa ina antaya masa bak’ak’en maganganu marasa dad’i,yayin da Daddyn ke durk’ushe kai a k’asa ya kasa ko d’ago idanuwa ya dube ni baiyi ba,sai dai fa hawaye ne ke sharara suna bin fuskarsa.

Duk da azabar da Uncle Khaleel ke ji a k’irjinsa hakan bai hana shi d’agowa ba,yana dafe da k’irjinsa yake kallona yana zubar da hawaye,wani kakkauran zagi da nayi wa Daddy shine ya baiwa Uncle Khaleek damar rufeni da wani irin duka yana gaura min mari,da hargowa kuma yana tsananin kuka yake fad’in.

“Tun da kin k’i jin maganata,tun da kin k’i dainawa na hak’ura da ke,ba zan iya kallon matata ta sunnah tana zagin mahaifina wanda ban da kamarsa ba a gabana,na hak’ura da ke Hidaya… na barki bari na har abada….na hak’ura da soyayyarki ko zata zama ajalina…na haramtawa kaina ke har duniya ta nad’e….domin baki da wani amfani a gareni….na sakeki Hidaya …saki d’aya…saki biyu…..saki uku….ke idan ma ana saki dubu to ayau na sakeki saki dubu Hidaya…..na sake ki….na sakeki….nace na sakeki Hidayaaaaaaaa

Yana fad’in wannan kalamin yayi wurgi dani hanyar k’ofar fita daga parlour’n,a dai dai sanda Ya Hamza ya d’aga labulen parlour’n da sallama wata mata na biye da shi a bayansa,a lokacin ne na fad’i gabansa tim bisa wurgin da Uncle Khaleel yayi dani.

A gigice Ya Hamza ya durk’ushe gabana,kunnuwansa na masa kuwwa bisa ga kalmar sakin da Abokin sa yake ta furta min,jinin da ya gani yana fita ta hancina da bakina shi ya sake firgitashi,har bai san lokacin da ya saka hannuwan sa cikin kid’imewa ya tarairayoni zuwa jikinshi ba,da k’yar na iya bud’e idanuwa na cikin azaba da wahala na dubeshi,cikin k’arfin hali na rik’o wuyan rigar sa idanuwa na na shirin k’ak’k’afewa,da hannu nake nuna masa Daddy,kafin nayi nasarar fizgo maganar da nake son yi.

“Ya Hamza…..wancan azzalumin ne ….ya kashe min ….mahaifina….Ya Hamza don Allah…ko da na mutu a yanzu ….ina so ka d’aukar min fansa….ni ma ka kashe min shi….don Allah Ya Hamza…..

Ina fad’ar wannan maganar na fara wata irin shak’uwa da nishi,kafin na sulale a k’irjinsa a matsayin sumammiya…..!

 

 

 

*zan tafi hutun sati biyu tunda bakwa comments sosai*🙄🙄🙄

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SABA’IN DA D’AYA DA NA SABA’IN DA BIYU

 

 

 

 

***Wata irin muguwar zufa ce ta yankowa Ya Hamza ,gabad’aya jikinsa babu in da baya rawa yana rik’e da Hidaya tsabar tashin hankali mara misali wanda ke d’awainiya da shi,idanuwansa akan ta yana duban fuskarta da idanuwanta a rufe babu numfashi a tare da ita,d’agowa yayi cikin matuk’ar tashin hankali ya dubi Khaleel da ke tsaye hannayen sa dafe da kansa,domin maganar da Hidayan tayi kafin ta sume ta kai k’urewa wajen d’aga hankalin sa,me Hidaya take nufi da cewar Daddyn sa ne ya kashe mahaifinta? shin wanene mahaifin na ta?ya akayi Daddy ya san mahaifinta har ya kashe shi?ya aka yi Hidayan ta san haka?tambayoyi da yawa ne suka cika k’wak’walwarsa ,wanda kuma bashi da mai ba shi amsa cikakkiya sai Hidayan da furucin ya fito daga bakinta.

Bai san lokacin da ya zabura yayi kan Hidaya da ke kwance jikin Hamza a sume ba,yana isa dab da su kawai sai k’afafuwansa suka kasa d’aukarsa ya zube a gabansu,hannun sa na karkarwa ya d’aga yana niyyar aza shi jikin Hidaya,a fusace Ya Hamza ya d’ago kansa cikin matuk’ar fushi,idanuwan sa kamar gauta saboda jan da suka yi,zuciyarsa kamar ta faso k’irjinsa ta fito,ya rasa yadda zai kwatanta wannan d’umbin tashin hankalin da ya zo ya tarar,shi da ya tawo cikin farinciki da annashuwa,amma ya zo ya tarar da tashin hankalin da bai tab’a gani a duniyarsa ba.

Dab da hannun Khaleel zai isa jikin Hidayan Ya Hamza ya daka masa tsawa me bala’in k’arfi cikin hargowa,cak Khaleel ya tsaya yana bin Hamza da kallo baki a sake kamar wani shashasha,idanuwan sa a birkice,Hamza ya sake rik’e Hidaya gam a jikinsa yana wa Khaleel wani kallo mai cike da fassarori iri iri,kafin ya bud’e baki cikin matuk’ar fushi da b’acin rai ya ce.

“Idan har ka sake hannuwanka suka sauka a jikinta wallahi nine ajalin hannuwan,domin sai na kakkarya su nayi makamashin wuta da su,daman haka ka ke?daman kai azzalumi ne?daman ba son Hidaya ka ke ba kasheta ka ke son yi?Khaleel kaine yau ka fitarwa da Hidaya jini a jikinta?kaine yau ka wulak’anta Hidaya mafi munin wulak’anci?ka manta alk’awarin da kayi min?ka manta cewar ka fad’a min za ka rik’e min ita amana ko k’uda ba za ka bari ya hau kanta ba?ka manta kace min za ka zama GARKUWAR ta? ka manta kace min ba za ka bari tayi kuka ba?ka manta kace min aurenku mutuwa ce za ta rabaku?duk ka manta da wad’annan abubuwan har ka samu damar tab’a min lafiyar jikinta,ka manta ita d’in me rauni da lalura ce Khaleel?yau a gaban idona kayi wa Hidaya wannan tozarcin da ko a mafarki ban tab’a tunaninsa ba?ka saketa cikin kwana d’aya rak da aurenku,kayi mata saki mafi muni da wulak’anci,Khaleel ko kad’ai za ka rage min a duniya daga yau na barka,kuma wallahi duk da kasancewarka Lauya sai na bi kadin abin da kayi wa wannan baiwar Allah ko komai nawa zai k’are…….

Wani irin zazzafan hawaye ya zubowa Hamza,bai tab’a ganin tashin hankali irin na lokacin ba,ya kau da kai daga kallon Khaleel da ke sandare a gabansa,ya runtse idanuwa da k’arfi kafin ya fashe da wani irin kuka yana rungume Hidaya a jikinsa,cikin wata irin murya yake magana harshen sa na sark’ewa.

“Ummana kinyi gaskiya ! daman kin fad’a min babu wanda ya san mutuncin Hidaya kamar ni,babu wanda zai rik’eta amana sama da ni,babu wanda zai jure rauninta da lalurarta kamar ni,Hidaya ki yafe min,na cutar da ke da na had’aki da wanda bai san darajarki ba,wanda yayi min k’arya yace min zai zama GARKUWAR ki….ashe yayi hakan ne domin ya cim ma wanni k’udurinsa a kanki…..kwana d’aya da aurenki yayi miki saki irin na bidi’a har saki uku….!

Hawaye ya cigaba da kwarara a idanuwan Ya Hamza yana kuka sosai,yayin da ya saka gefen rigarsa fara tas da ke jikinsa yana gogemin jinin da ya b’ata min fuskata zuwa jikina….

Kamar wani gunki haka Uncle Khaleel yayi kasak’e ya zubawa Ya Hamza idanuwa,shi sam ma baya wani fahimtar abubuwan da Hamzan ya ke fad’a,abu d’aya ne ya ke ta yawo cikin kwanyar kansa yana sake hargitsa shi,wato yadda Hamzan ya ke fad’in wai ya saki Hidaya,wai da bakinsa ya furta cewar ya saketa,shi sai yake jin ma abin tamkar almara,domin shi dai bai ma san lokacin da ya furta sakin ba,Khaleel bai sake shiga tashin hankali ba sai da yaga Hamza ya juya cikin kuka yana kallon matar da ke bayan sa a tsaye hannuwan ta aka,ita ma d’in fuskarta jage jage da Hawaye,a hankali cikin raunin murya yace mata..

“Aunty za ki iya d’aukar Hidaya mu tafi ko na d’auke ta…?

Cikin Hawaye ta ce.

“D’auke ta Hamza,hannaye na ba za su iya rik’onta ba”

Hamza ya sake rungumota jikinsa ya mik’e tsaye da ita a hannayensa tamkar wata jaririya,ya cigaba da kallon fuskarta da ta kumbura yatsun Khaleel kwance kan kumatun ta,ga gefen kanta ma ya kumbura saboda yadda ya garata da garu,nan da nan wani bak’inciki da tsanar Khaleel ta kuma d’arsuwa a zuciyar Hamza,sosai yake jin ciwo a k’irjinsa da tsananin zafi..
A salub’e Khaleel ma ya mik’e yana rik’o hannun Hamza da ke d’auke da Hidaya,cikin wani irin yanayi na tamkar mai tab’in hankali da rashin nutsuwa yayi magana yana nishi.

“Aboki …..ina za ka kai min matata…!?

Wani irin matsiyacin kallo Hamza ya dank’arawa Khaleel,idanuwansa tamkar su fad’o k’asa,cikin matuk’ar fusata da gigita yayi magana .

“Sakar min hannu”

Da yake Khaleel bai tab’a ganin Hamza cikin irin wannan fusatar ba sai ya tsorata,a hankali ya saki hannun Hamzan yana ta had’iyar zuciya idanuwansa jajir hawaye ya cika su,ya k’urawa Hamzan idanu kansa tamkar ya fashe yake ji,Hamza ya kawar da kai yana jin k’unci a ransa,ya dubi matar da ke tsaye ya ce.

“Mu tafi Aunty”

Ta juya ta nufi k’ofa tana share hawayen fuskarta,yayin da Hamza ya rufa mata baya yana tafiya a hankali hannuwansa d’auke da Hidaya,sai da yaje bakin k’ofa sannan ya tsaya ya waiwayo a hankali ya dubi Khaleel da ke tsaye yana kuka da nadamar rayuwa,a hankali ya cigaba da kallonsa yana ayyana abubuwa kala kala a zuciyar sa,kafin ya girgiza kai su k’urawa juna idanuwa,Hamza yayi magana cikin wata irin murya”

“Zan cigaba da amsa sunan GARKUWAR HIDAYA a ko yaushe ! zan tabbatar da cewar nayi shari’a da dukkan wanda ya zalunceta ! ba zan bari a zalunceta ba domin amanata ce ! ni bana zalunci kuma bana shiri da duk wani azzalumi ! ina so ka sani cewa a yanzu Hidaya bata da wani had’i da kai…komai da ke tsakaninku ya k’are domin saki uku k’warara kayi mata…idan saki d’aya ne ko biyu zan barta cikin d’akinta ta kammala iddarta kamar yadda Allah (S W A)ya umarta,amma yanzu fa?komai ya k’are tsakaninka da ita Khaleel…yanzu tsakani na da kaine…ba zan d’auki hukunci da hannuna kamar yadda ka d’auka ba…amma ka sani akwai k’aramar hukuma,sannan akwai babbar hukuma wato Allah (S W A).

Sannan ya juya ya dubi Daddy da ke tsaye kai a sunkuye yana hawaye,wani bak’in Daddyn yake gani a idanuwan sa ,cikin wata irin murya ya fara magana bayan ya kautar da idanuwan sa daga kallon Daddyn zuwa kan fuskar Hidaya da take cikin rai kwakwai mutu kwakwai.

“Har yanzu ina kallonka a matsayin uba Daddy ! amma muddin na tabbatar da abin da Hidaya ta fad’a a kanka to zanyi yak’i da kai,duk da kana tak’ama da k’arfin dukiya ! to ni kuma zanyi tak’ama da Allah mahallicina da cikar izzarsa da buwayarsa domin na yak’e ka,domin ko Allah baya son zalunci ! kuma ya haramta shi a tsakanin sa mu bayinsa kada wani ya zalunci wani ! Don haka ka jira ni Daddy….!

Iya nan maganar Hamza ta tsaya,ya juya ya fice da Hidayan sa d’auke a hannunsa yana hawaye,ya bar Khaleel a tsaye yana kuka kamar ya zauce,yana jin danasanin zuwan wannan rana a duniyarsa da babu ranar da ta kaita bak’i a idanuwan sa,domin hankalinsa ya gushe bai ma san abinda ya aikata ba,Daddy kam k’afafuwansa ne suka kasa d’aukarsa,sosai jikinsa ke rawa yana neman zubewa a k’asa,kafin ya kai k’asan sai ganin Khaleel yayi yana k’ok’arin fad’uwa hannayensa dafe da k’irjinsa dai dai zuciyarsa,idanuwansa na lumshewa yana wani irin nishi mai k’arfin gaske kamar ransa zai fita,da wani irin hanzari Daddyn ya rik’o shi jikinsa yana rungume shi yana ambatar sunasa a rikice.

Khaleel ya dinga cije lab’b’ansa yana nishi saboda azabar da yake ji a k’irjinsa,idanuwan sa suna son rufewa amma k’ok’ari yake ya bud’e su,bakinsa na mugun rawa yana son yin magana amma ya rasa abin da zai cewa Daddyn,bai san ta ina zai fara ba,bai san wane kalami zai furta ba,sai dai zuciyarsa cike take da d’okin sanin shin da gaske abin da Hidaya ta fad’a gaskiya ne?shin da gaske Daddyn sa ne ya kashe mata mahaifi?

Duk wani k’arfinsa ya tattaro ya rik’e kafad’un Daddy,kallon fuskar Daddy yake wadda ta tattare tsabar tashin hankali da shiga rud’u,ga hawaye sosai yana zuba,shi tunda yake ma a rayuwarsa bai tab’a ganin Daddyn cikin irin wannan yanayin ba.

Ganin Khaleel ya kasa magana duk da yunk’urin da yake ta faman yi wajen maganar,shine dalilin da yasa Daddy ya tallabo fuskar Khaleel d’in ya zuba masa idanu,kallon idanuwan Khaleel d’in yake da suka birkice suna fidda wani irin hawaye mai zafi suna gangarowa,cikin wata irin murya me rauni Daddy yayi masa magana,kafin yasa hannun sa d’aya ya shiga share masa hawayen da suke zuba.

“D’ana Khaleel,bud’e bakin ka ka furta min duk abin da yake zuciyar ka,ni kuma nayi maka alk’awarin fad’a maka gaskiya a duk yadda ta zo ”

Khaleel yayi wani irin murmushi hawaye na sake zubowa akan fuskarsa,ya rik’e hannuwan Daddy yana girgiza kai,can ya fara magana yana d’an tari,maganar bata fitowa sosai.

“Daddy kai mahaifina ne…wanda na baiwa matsayi guda biyu..wato matsayin uwa da uba tunda bani da uwa…bayan kai bani da wani makusanci da nake jin sa a zuciyata kamar Hamza…kafin kuma Hidaya ta shigo rayuwata… Daddy kullum Hamza na fad’a min darajar iyaye da matsayin su a wajen mutum…kullum shine yake umarta ta da yi maka biyayya…Hamza yana fushi dani idan na sab’a umarnin ka…kullum yana nanata min bani da kamar ka duk duniya musamman ma da ya kasance kai kad’ai nake da shi..babu mahaifiyata a fad’in duniya… A yau na yanke wannan hukunci mai zafi ne akan Hidaya dalilin ta tab’a k’imar ka…ta tab’a min mutuncinka…ni kuma ba zan iya jurewa ba…saboda kullum Hamza yana fad’a min in yi fito na fito da duk wanda zai tab’a min iyaye..domin ban da tamkar su…Sai dai a yau na manta da abu d’aya…wanda shi ma Hamza ya kan tunasar da ni akansa…ya kan ce min “Khaleel a duk lokacin da kaji ranka ya b’aci ko kana cikin fushi to kar ka yanke wani hukunci,ka ambaci (Hasbunallahu wa ni’imal wakeel)sannan kayi istigfari kace(Astagfirullah wa atubu ilaihi)to Allah zai sanyaya maka ruhinka da salama har ka samu farinciki,a lokacin ne za ka yanke hukunci abisa abinda ya dumfaroka,amma muddin baka yi haka ba,to duk hukuncin da ka yanke daga baya sai kayi danasani akan sa” Daddy ina tuna ranar da Abokina Hamza ya fad’a min wannan maganar..yau gashi na rasa shi…haka nan na rasa rabin rayuwata…

Yayi shiru yana maida numfashi hawaye na zuba,shi dai Daddy kallonsa yake yi shima yana hawayen sosai,Khaleel ya sake damk’e hannun Daddyn ya cigaba da magana cikin wahala

“A wata rana da ta shud’e Abokina Hamza ya tunasar dani azabar da Allah yake wa mak’aryata,har ma yayi min nuni da ayar nan da Allah yake cewa.

“فنجعل لعنت الله على الکذبين”

(Sannan kuma mu sanya tsinuwar Allah akan mak’aryata).

Sannan Hamza ya fad’a min cewar babu kyau iyaye suyi wa y’ay’ansu k’arya,saboda addininmu ya nuna cewa dole ne a guji yin k’arya a cikin tarbiyyar y’ay’a,domin su tashi a cikin gaskiya kuma su saba da ita,hakan zai sa y’ay’a su saba da fad’ar gaskiya da aiki da ita,to a yau ina so ka fad’a min gaskiya mahaifina,domin ka zama cikin wad’anda Allah yake sakawa gaskiya da gaskiyar su.

“ليجزي الله الصدقين بصدقھم”

“Daddy ina so ka fad’a min gaskiya…me ka sani game da Hidaya…?shin da gaske kaine ka kashe mahaifinta…?shin wanene mahaifin na ta…?Don Allah Daddyna ka fad’a min kafin ruhina ya bar gangar jikina….!

Wani irin fashewa da kuka Daddy yayi,hawayensa na sauka akan fuskar Khaleel da ke tallafe da shi.

 

 

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SABA’IN DA UKU DA NA SABA’IN DA HUD’U

 

 

***Ya Hamza na d’auke da ni a hannayensa har zuwa gida,yana gaba Aunty na biye da shi a bayansa tana sharar hawaye,shi kam tuni ma hawayensa ya k’afe sai idanuwansa da suka yi jajur,sai wani masifaffen d’aci da yake ji a bakinsa.

Aunty ce ta iya sallama a yayinda suka kutsa kai cikin gidan,yanayin muryarta mai cike da rauni ya sa Umma da wata mata da ke biye da ita suka d’aga labulen d’akin da hanzari suna fitowa daga parlour zuwa tsakar gidan,cikin matuk’ar tashin hankali Umma ta fara zare idanuwa tana nuna Ya Hamza da hannunta,bakinta na rawa take ambatar.

“Me ya faru da ita na ganku haka?me ya faru ne Hamza?ina mijin na ta?

Ya Hamza bai ce da Umma komai ba illah wucewa da yayi ya shige cikin d’akinsa ina d’auke a hannunsa,Umma ta bishi da idanu kafin ta waiwaya ta dubi wadda suka shigo tare da Hamzan,hawayen da ta gani a idanuwanta shine ya k’ara dugunzuma ta,cikin rud’u ta rik’o hannunta tana tambayarta.

“Me ya samu Hidaya naga ba ta motsi?kun sanar da ita cewar Mahaifiyarta ta zo yanzu ne?ko kun sanar da ita cewar ke k’anwar Mahaifiyarta ce?ba cewa nayi da ku kawai kuje ku tawo da Hidayan da mijinta ba?don komai ya zo da sauk’i”

Fashewa Aunty tayi da kuka ta kasa cewa komai,sai kallon yayarta take yi da ta tsura mata idanu cikin wani yanayi,wato(Mummyn Hidaya).

Ganin tak’i yin magana sai kuka take hakan ya sa Umma da Mummy suka dubi juna cikin dukan zuciya,kawai sai Umma ta taka da hanzari ta bi Hamza d’akinsa,yayin da Mummy da Aunty suka rufa mata baya…

Hamza suka tarar zaune ya dafe kansa saboda tsananin sara masa da yake tamkar ya cire, ga Hidaya ya shimfid’eta akan bed d’in sa tayi samb’al ko motsi bata yi,cikin matuk’ar fusata suna shiga Umma ta fizgo Hamza kamar ta kwad’a masa mari ta fara magana cikin fushi.

“Kai wai ba magana nake maka ba ne?me ya same ta ko bata da lafiya ne?ina mijin na ta yake? za ka yi magana ko sai na b’ata maka rai?”

Hawaye ne ya ratso fatar idanunsa,da k’yar ya iya duban Umma yayi magana a hankali.

“Eh bata da lafiya Umma,na kawo ta nan ne domin in yi tunanin asibitin da ya kamata na kaita,domin ba zan kaita asibitin da take ganin likitanta ba”

Umma ta sake magana cikin k’ulewa.

“Babu abinda yake b’ata min rai da kai Hamza irin wani zubin ayi maka tambaya ka bayar da amsa a baud’e,to koma dai menene ya faru ai bai kamata tana cikin wannan halin ka kawo ta gida ka shimfid’eta ba,wai menene yake faruwa yake faruwa ne?menene dalilinka na k’in kaita asibitin da take zuwa?wai shin ma ina Ibraheem d’in ya ke?”

Tambayoyin da Umma ta jero masa kenan,cikin matsananciyar damuwa ya dubeta ya ce.

“Ba zan kaita asibitin bane saboda wasu dalilai masu k’arfi,kin sani Umma Khaleel shine yake d’aukar d’awainiyar komai na Hidaya wajen kula da lafiyarta,to yanzu babu wata alak’a tsakaninsa da Hidaya da hakan zai cigaba da faruwa….

“Ban gane ba,wane irin babu wata alak’a tsakaninsu?ko ka manta cewa yanzu bata da wani makusanci da ya kaishi?ka manta cewar Ibraheem mijinta ne?”

Wani bak’inciki ya sauka a zuciyar Hamza,bai ma san ta yadda zai bud’e baki ya fad’awa Umma cewar Khaleel ya saki Hidaya har saki uku ba,matsawa yayi daga gaban Umma ya k’arasa gaban Mummy da ke tsaye idanuwanta akan d’iyar ta tana yi mata kallon yaushe gamo!kawai sai ya durk’usa gabanta cikin hawaye ya fara magana idanuwansa akan Mummyn.

“Kiyi hak’uri Mummy….a lokacin da kika bani d’iyarki kin bani ita ne cikin k’oshin lafiya da kuzarinta,har ma kika yi ta jaddada min cewar na rik’e miki ita amana bata da kowa…kar na bari a cutar da ita…na zama GARKUWARTA…sai gashi yau da na tashi dawo miki da ita kin ganta akasin yadda kika bani ita…ban rik’e miki amana ba Mummy…ban cancanta a kirani da GARKUWAR HIDAYA ba…

Salatin da Umma ta saka da k’arfi shine ya dakatar da Hamza daga maganarsa,hannayenta akanta idanuwa zuru zuru take duban Aunty da take sanar da ita cewar “Khaleel ya saki Hidaya saki uku” wata hajijiya ce ke kwasarta tana shirin kaita k’asa,tuni hawaye ya ciko idanuwanta ya fara kwarara kan fuskarta…

Kawai gani suka yi Mummy ta fara tafiya a hankali ta nufi gefen gadon da Hidaya ke kwance,a zatonsu gun Hidayar ta nufa,a maimakon hakan sai suka ga ta ci birki gaban wani hoto da ke kan bedside drawer,d’aukar hoton tayi ta k’ura masa idanuwa tana kallo cikin dukan zuciya,a hankali ta waiwayo ta dubi Hamza a rikice tayi magana karon farko.

“HAMZA GARKUWA,bayan kai da na gani a hoton nan,ga Hidaya a tsakiya,wanene wannan da ke gefen hoton kuma?”

Hamza ya kasa magana kai a sunkuye,sai Umma ce cikin hawaye ta ce.

“Shine Khaleel…abokin Hamza da aka d’aura musu aure a jiya shi da Hidaya”

Cikin tsabar tsoro Mummy ta ce.

“Yayi min kama da wata bak’ar fuska ne a idanuwa na,don Allah Umman GARKUWA sanar da ni wanene Khaleel?kuma wanene mahaifin sa?”

Cikin hawaye Umma ta sake magana.

“Ya kamata muyi hanzarin kai Hidaya asibiti saboda ko motsi bata yi,idan muka nutsu komai da kike buk’atar ji sai na sanar da ke”

Girgiza kai Mummy tayi,cikin wata irin murya ta ce.

“Ko sunan mahaifin Khaleel kad’ai ina so ki fad’a min a yanzu,ba zan iya jurewa zuwa lokacin da kike so ba”

“Sunan sa Alhaji MUDASSIR” Umma ta fad’a idanuwan ta akan Mummy”

Wata irin razana Mummy tayi ta saki wata k’ak’k’arfar k’ara kafin idanuwanta su k’ak’k’afe tayi baya tana shirin fad’uwa,da sauri Umma da Aunty suka tarota ta fad’i a jikinsu babu numfashi a tare da ita…

 

 

*******************

 

 

 

Kukan da Daddy ya fashe da shi shine ya sake jefa Khaleel cikin shakku da matsananciyar fargaba,ya tsurawa Daddyn na sa idanu yana jin kamar ya mace ya huta da k’unci da fargabar da ke addabar ruhinsa,sosai hawayen da Daddy yake yi ya sake jefashi cikin tunanuka barkatai,cikin raunin murya Khaleel yake ta rok’on Daddyn sa akan ya fad’a masa gaskiya,yana ta ambatar “Don Allah Daddy ka fad’a min….Don Allah ka fad’a min ya mahaifina…” amma ko kad’an Daddyn ya kasa bud’e bakinsa yayi magana sai kuka da yake yi yana rik’e da kafad’un Khaleel d’in.

A hankali Khaleel ya soma yunk’urawa yana niyyar tashi daga jikin mahaifin na sa,ya zame hannuwan Daddy daga jikinsa,da k’yar ya iya mik’ewa tsaye yana cije bakin sa,wata muguwar rama ta bayyana a gareshi yayi wani zuru zuru cikin lokaci k’ank’ani,yana layi kamar d’an maye haka ya wuce Daddy ya fara takawa a hankali,Daddy ya d’ago yana kallon bayansa cikin hawaye sosai,da k’yar ya iya bud’e baki yayi magana yana ambatar sunan d’an na sa.

“Khaleel…!

Khaleel ya k’i juyowa balle ya tsaya,ya cigaba da takawa a hankali yana had’a hanya tamkar ya kifa,Daddy ya sake d’aga murya ya ambaci sunansa da k’arfi.

“Khaleel…juyo ka zo gareni kaji Khaleel”

Duk da hakan bai juyo ba,illah cikin bedroom da ya nufa hankalinsa a tashe,ya bar Daddyn sa tsugune a wajen yana kuka cikin garari.

Kan gadon d’akin ya nufa,hannunsa dafe da k’irjinsa,zuciyarsa ciwo take sosai yana jin kamar ta faso k’irjin na sa,bai tab’a ganin mummunar rana irin wannan da ya rasa komai ba,shi yana jin tunda ya rasa Hamza da Hidaya a duniyarsa to ya rasa komai.

Gefen gadon ya zauna yana dafe kansa,bai san me ma zaiyi ba,d’ago shanyayyun idanuwan sa yayi ya zuba su akan wani hoto da ke gefen gadon,k’arami ne sosai kuma yanayin hoton yayi kama da irin hotunan da,hannun sa na karkarwa ya d’auko hoton ya tsura masa idanuwa yana kallo,hawaye ya sake tsinke masa suka fara sharara da gudun su,rungume hoton yayi a k’irjinsa yana kuka sosai,cikin k’aramar murya da bata fita sosai yake ce wa.

“Ina ma kina da rai …ina ma kina duniya Mahaifiyata…ina ma baki tafi kin barni ba…da a yadda nake d’in nan gurinki zan zo…ki rungumeni jikinki ki rarrasheni …ki kwantar min da hankali da kalamai masu dad’i ko zan ji sanyi a raina…sai dai kuma bakya nan …kin min nisa mai yawa…kin tafi kin barni…gurin wa zanje a yanzu…?a lokacin da babu ke sai Allah ya bani Hamza…sannan ya k’ara min da Hidaya…yanzu gashi duk sun barni…saboda munin abin da na aikata…ni kuma k’addarata kenan…jarrabawata kenan…Innalillahi wa inna ilaihir raji’un….!

Khaleel kuka yake sosai kamar ransa zai fita,bai tab’a tsintar kansa cikin kewa da rauni irin lokacin ba,ji yake kamar shi kad’ai yake rayuwa a filin duniya,ya rasa ina zai jefa kansa yaji sanyi,sai da yasha kukansa ya k’oshi sannan ya iya ajiye hoton mahaifiyar sa,alokacin ne idanuwan sa suka ankara da wani hoto da takarda a gefensa,mik’a hannu yayi cikin sanyin jiki ya d’auki hoton,babu wanda idanuwansa suka gani sai mahaifinsa a jikin hoton,hoto ne dad’ad’d’e tun zamanin yana yaro k’arami,mamakin yadda akayi ya samu hoton a wajen yake,domin shi dai bashi hoton ma kwata kwata,to ya akayi aka same shi har kan shimfid’ar su?

Wani tunani ne ya d’arsu a ransa,da gaggawa ya ajiye hoton ya d’auki takardar da yake ji ita ce musababbin komai,jikinsa na rawa ya warware ta ya zuba mata idanuwansa k’irjinsa na tsananin bugu,fatansa kawai ya karanta abin da takardar ta k’unsa kafin numfashin sa ya bar gangar jikinsa.

 

*Assalamu Alaikum ya ke y’ata*

*Na san a lokacin da wannan takarda zata riskeki kin girma,kin kai munzalin da hankali ya shigeki tare da nutsuwa,kin san fari kin san bak’i,kin san abu mai kyau kin san mara kyau,k’ila a lokacin da zaki karanta takardar ina duniya ko kuma nima na mutu kamar mahaifinki,yake y’ata,ki sani cewar ban guje miki don wani abu ba,illah don son tseratar da rayuwarki daga hannun wani azzalumin mutum,wanda shine ya kashe mahaifinki,haka nan kuma yake so ya kashe mu ni da ke,na zab’i in guje miki in kai ki gidan marayu ne saboda kar azzalumin mutumin nan ya bibiyeki har ya samu nasara a kanki,domin hankalinsa ba zai tab’a kaiwa ya fahimci kina gidan marayu ba,ni na yarda in mutu idan har ke zaki rayu,domin ki d’aukar mana fansar abinda wannan azzalumin mutum yayi mana,zan tafi in da ba zaki ganni a kusa ba,idan har ina raye lokacin da ya kamata na bayyana a gareki zan bayyana,na san za ki shiga cikin k’unci da gararin rayuwa saboda rashin kowa a tare da ke,gashi kina da lalurar da kike buk’atar matallafi a tare da ke,amma zan barki a hannun Allah,domin babu wanda zai kula da ke sama da shi,shine ya halicceki ya bani ke kuma ya fini sonki*

*Sannan buk’atata a gareki ita ce,ina so in baki umarni a matsayina na mahaifiyarki,abu d’aya za ki yi ki inji a raina cewar kin biyani d’awainiyar da nayi a kanki,wajen d’aukar cikin ki da haihuwarki da rainonki,wannan buk’ata ba wata bace illa ina son ki kashe min wanda ya kashe mahaifinki da hannunki Hidaya,ga hotonsa nan zan bar miki domin ya zame miki jagora wajen gane ko wanene shi,da hannunki nake son ki d’aukar min fansa ki kashe shi kar ki barshi da rai,idan har kikai min haka ko da bana duniya zanyi farinciki da ke,zan san na haifi me share min kukana,zanji a duniya ba a yi wata y’a mai biyayya kamarki ba,wannan hoton mutumin da zaki gani tare da takardar nan shine wanda nake so ki kashe,domin azzalumi ne,mugu ne,mak’etaci ne*

*Zan tafi na barki cikin tsananin sonki da k’aunarki,ina fatan Allah ya kula da ke ya tsareki da tsarewar sa*

*Daga Mahaifiyarki*

 

Takarda k’arama,amma girmanta yafi girman dutsen dala da gorondutse a idanuwan Khaleel,shike nan ta tabbata Mahaifinsa shine ya kashe mahaifin matarsa?Wannan bala’in daman Hidaya ta gani ta gigice haka har ta aiwatar da abin da ta aiwatar?in haka ne Hidaya bata da laifi kenan?domin idan shine hakan ta faru da shi kisan ma zai iyayi ! mutuncin Daddyn kawai aka tab’a masa ya yanke d’anyen hukuncin da bashi da misali,to ina ga kashe masa shi akayi?kuma yayi ido biyu da wanda ya kashe masa mahaifin?me zai faru kenan?

Bai tab’a jin nadamar zuwansa duniya irin yau ba! bala’in ciwo da yake ji a zuciyar sa ya kai mak’ura,wani irin gigitaccen amai ne na tashin hankali ya yunk’uro masa da k’arfi,take ya fara kelayashi idanuwansa na k’ak’k’afewa,a maimakon aman ruwa ko na abinci sai ga jini na fitowa har ta hancin sa,har da guda guda,malelekuwa kawai yake yana rik’e k’irjinsa da yake jin yayi masa mugun nauyi,adai dai lokacin aka banko k’ofar d’akin aka shigo,Daddy ne da Aunty Kubra suka shigo a gigice,shigowarsu kuma yayi dai dai da fad’owar Khaleel daga gadon zuwa k’asa,jini na zuba yayin da idanuwan sa suka yi sama,Numfashin sa ya bar gangar jikinsa….!

 

 

*Kuyi hak’uri yau kad’an nayi,bana jin dad’i ne ina ciwon kai,ku tayani addu’a*👏

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SABA’IN DA BIYAR DA NA SABA’IN DA SHIDA

 

 

 

***Cikin tsananin tashin hankali suka nufi Khaleel,Daddy ya tsuguna ya tarairayo shi jikinsa yana kuka da ambatar sunansa,ganin Khaleel d’in baya motsi bare numfashi sai hankalinsa ya sake mugu mugun tashi,ya rasa ya zaiyi sai girgiza shi yake yana kuka yana ambatar.

“Khaleel…Khaleel don Allah ka tashi kar kayi min haka…ka tashi zan fad’a maka dukkan abin da ya faru…don Allah kar ka tafi ka barni kamar yadda mahaifiyarka tayi min…ka tashi d’ana …don Allah ka tashi ka dubeni….!

Aunty Kubra da ke tsaye tana kuka salati kawai take rafkawa ganin yanayin da Khaleel yake ciki,tana son Khaleel tamkar ita ta haifeshi,saboda biyayyar da yake mata da son y’ay’anta.

Durk’usawa tayi dab da Daddy da ke rik’e da Khaleel d’in yana ta surutai kamar ya zauce,a hankali ta kai hannu kan k’irjin Khaleel da jini duk ya b’ata shi,dafa k’irjin tayi bakinta d’auke da salati tana hawaye,da k’arfi ta sauke wata ajiyar zuciyar jin dad’i,ta waiwayo ta dubi mijinta ta girgiza kai tayi magana.

“Daddyn Khaleel d’aukeshi muyi hanzarin kai shi asibiti,naji zuciyarsa na bugawa da k’arfi ba mutuwa yayi ba,d’aukoshi bari nayi hanzarin fitowa da mota”

Tana fad’in hakan ta tashi ta fice da hanzari,yayin da wani sanyi ya kwarara a zuciyar Daddy,cikin gaggawa ya d’ago Khaleel da ke sume ya sanya shi kan kafad’ar sa yayo waje da shi,duk da hakan hawaye bai bar zuba a idanuwansa ba.

Aunty Kubra ke jan motar,yayin da Daddy ke zaune a bayan motar rungume da Khaleel a jikinsa,tsananin tashin hankali ya kasa tsayar da hawayen da yake saraftun zubowa a fuskarsa,ita kanta Aunty Kubran bata cikin wata nutsuwa sosai,amma duk da hakan tana tuk’i sai da tayi wa Daddy magana ta ce.

“Da wannan kukan da kake dama addu’a kayi masa,domin babu abinda Khaleel ke buk’ata a yanzu sama da ita”

Sai ga Daddy ya fara nemo addu’ar da zaiyi,da ya kamo wannan sai ta kufce,da ya janyo wannan sai ya manta,babu abinda ke d’awainiya da shi sai firgici da k’urewa a fage na tashin hankali. A haka har suka k’arasa babban asibitin da Khaleel ke ganin likitan ciwon zuciya tun bayan dawowarsa daga England.

 

 

 

***************

 

B’angaren su Hamza tashin hankalinsu ya zarce misali,domin su abin yayi musu rufdugu,ga Hidaya kwance ga Mummy kwance,(wannan shi ake cewa d’a kwance uwa kwance).

Umma da Aunty kuka suke yi sosai,basu ma san ya za su yi ba,har ruwa Umma ta d’ebo ta yayyafawa Mummy da Hidaya amma ko motsi basu yi ba,wannan ya sake d’aga hankalinta ta dubi Hamza da ke sandare a tsaye ta daka masa tsawa har da zagi,abinda bata tab’a yi masa ba.

“Don ubanka don uwarka kaje ka fito da mota mu kai bayin Allan nan asibiti,idan suka mutu za su rataya a wuyanka akan banzan tunanika Hamza,ka kaimu asibitin da Hidayan take ganin likita domin nan ne muke da tabbacin samun abinda muke so”

Ko Umma bata fad’a ba tilas ya aikata hakan duk da ransa bai so ba,shi so yake ya yanke komai da yake tsakaninsa da Khaleel,saboda ya kai mak’ura wajen b’ata masa rai,yayi masa abinda bai tab’a zato ba,ya wulak’anta masa amanarsa,duk da hak’urin da yayi ya bar masa ita,duk da soyayyar da yake mata a filin duniya.

Jikin Hamza a salub’e ,yana jan k’afa da k’yar haka ya fice ya fito da motar,da kansa ya dawo ya d’auki Hidaya da take langab’e tamkar matacciya,Umma da Aunty suka ciccib’o Mummy ,dukan su suka shiga motar,yayin da Hamza ya fige ta da gudu suka nufi asibiti domin ceton lafiyar Uwa da y’arta.

 

 

*****************

 

Asibiti d’aya duk aka nufa da su,Khaleel b’angaren masu ciwon zuciya,yayin da Hidaya aka nufi b’angaren masu ciwon sikila da ita,sai Mummy kuma da wani likitan na ban yake duba ta.

Kafin cikar awa d’aya Mummy da Hidaya sun farfad’o har an musu allurar bacci domin k’wak’walwar kansu ta huta abisa firgicin da suka tsinci kansu a ciki,Khaleel ne dai an sha wahala kafin ya farfad’o,bayan farfad’owar ta sa ma sai bala’in ciwo ya ishe shi,yana shure shuren azaba yake wa likitan nuni da acire masa zuciyar gabad’aya ta isheshi,likitan kansa ya tausayawa Khaleel matuk’a ganin halin da yake ciki, sai da yayi masa wasu allurai sannan zafin rad’ad’in ya ragu,har ma ya samu kansa cikin wani irin wahalallen bacci mai cike da mafarkin Hamzan sa da Hidayan sa.

Sai bayan Yamma lik’is sannan Mummy ta farka daga wahalallen baccin,tunda ta farka kuma take wani irin kuka mai cin rai da zuciya,rarrashi babu irin wanda Umma da Hamza ba su yi mata ba,amma ta kasa yin shiru,daga k’arshe ma tunb’uke ledar k’arin ruwan tayi daga hannunta ta mik’e tsaye a gigice,Umma tayi saurin rik’e ta fuska cike da damuwa take fad’in.

“Ki yiwa girman Allah ki sanyawa zuciyarki salama,kinga ba cikakkiyar lafiya ne da ke ba kar a kuma samun wata matsalar”

Mummy cikin hawaye ta ce.

“Barni Umman Garkuwa,matsala kuma ai na riga da na gama shigarta,tunda jinina ya had’u da jinin MUDASSIR”

Cikin tsananin mamaki Umma ta dubi Hamza da ke zaune idanuwan sa a runtse,gani yake ya fi kowa shiga tashin hankali,a yanzu da yake zaunen nan babu abin da ke zuciyarsa sai Khaleel,ta k’arfi yake k’ok’arin cizge shi daga ransa amma ya kasa,ayanzu haka son ganinsa yake,domin ya san Khaleel d’in yana cikin wani hali na garari,kuma ya san ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba,Zuciyar sa ba ta iya jure manyan tashin hankali.

Juyo da kallonta tayi kan Mummy bayan ta d’auke idanuwanta daga kan Hamza,cikin wani irin murya Umma ta cewa Mummy.

“Me yasa kika ce haka?daman kin san Alhaji Mudassir mahaifin Khaleel?naga daga fad’a miki shine mahaifin mijin Hidaya kika rud’e har kika fita daga hayyacin ki”

Mummy tayi wani murmushi na tsananin takaici da bak’inciki,ta basar da maganar Umma,illah jefowa Umma tambaya da tayi ita ma.

“Ina Hidaya…!?

Umma ta cigaba da kallonta kafin ta bata amsa da cewa.

“An mata allurar bacci ne,yanzu haka Sajida na tare da ita a d’akin da aka kwantar da ita”

Mummy ta runtse idanuwan ta tana sakin ajiyar zuciya,a hankali kuma ta fara bud’e su ta sauke ganinta kan fuskar Hamza,ta ambaci sunan sa cikin dakakkiyar murya.

A hankali ya bud’e idanuwansa da suka sauya kala ya dube ta,tana dubansa ta jefa masa tambaya.

“Ranar da na baka Hidaya na baka wata takarda ka ajiye mata,har na rok’i alfarmar kar ka bata sai ta girma,sai kaje gidan Marayun ka bata,tsawon lokacin da na tafi na barku na san cewar baka kai Hidaya gidan marayu ba,kuma hakan duk yana cikin shiri na da tsari na,haka nan duk wata rayuwa da Hidaya ta gabatar tare da ku ina sane da ita,ina bibiyar lamuranku,fallasa kaina ne kawai na kasa yi saboda ina gudun harin da wani azzalumi zai kawo min daga ni har Hidayan,shiyasa na zab’i b’oye kaina,amma ba don ina son hakan ba,Hamza na san cewa kayi wa Hidaya rik’o na gaskiya,kai da mahaifiyarka,ka zame mata GARKUWA na farko,Bibiyar da nake muku ta yanke ne a ranar da ka ganni a airport har na guje maka,tabbas ni ka gani Hamza,ban san abinda ya kawo ka airport ba a ranar,ni kuma zanyi tafiya ne zuwa wata k’asa domin halartar k’arawa juna sani akan aikin Shari’ah,ni nan da kuka ganni babbar alk’aliya ce,kuma na zab’i na zama alk’aliya ne saboda na aiwatar da wani nufina na yankewa wani azzalumi hukunci,idan har Hidaya bata cika min burina ba,ba wani buri bane kuma illah ta kashe min Alhaji Mudassir mahaifin Khaleel da hannun ta…

Hamza bai razana da jin maganar Mummy ba,saboda ya san kwanan zancen,Umma ce dai ta firgita ainun,cikin zazzare idanuwa take duban Mummy tana mata kallon mahaukaciya,tana shirin magana ta ji Mummy ta cigaba da magana tana tambayar Hamza….

“Shin Hamza ka bawa Hidaya wannan ajiyayyiyar takardar kuwa..!?

Hamza ya lumshe gajiyayyun idanuwansa yana sakin ajiyar zuciya,cikin wani yanayi ya dubi Mummy ya ce.

“A jiya sak’onki na tsawon shekaru ya isa hannun Hidaya,kuma ina da tabbacin wannan sak’on shine ya kawo babban rud’a ni a yau”

Idanuwan Mummy a kansa ta ce.

“Wane irin rud’ani kenan?”

Mik’ewa tsaye Hamza yayi,sannan ya juya baya ya daina kallon Mummy,sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya fara magana cikin taushin murya.

“Babban rud’ani,wanda ya janyo sanadiyyar katsewar babbar sunnah ta Annabi,ba kuma komai ya janyo hakan ba sai umarnin da kika bawa Hidaya na aikata mummunan aiki a matsayinki na mahaifiyar ta,a maimakon kiyi mata umarni da kyakkyawan aiki,Umarni da kyakkyawan aiki na nufin umarni da abinda Allah da manzonsa suke so,da abin da shari’a ta yarda a kansa,yayin da umarni da mummunan aiki kuwa yake nufin,umartar aikata abin da Allah da manzonsa suka hana,kuma shari’a ta bayyana muninsa.

Allah mad’aukakin sarki ya umarci bayinsa muminai da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki,inda yake cewa:

 

“ولتکن منکم أمة يدعون إلى الخير و يأمرون بالمعروف وينھون عن المنکر ,و أولئك ھم المفلحون”

Ma’ana( A samu wasu jama’a daga cikinku suna kira zuwa ga alkairi,sannan suna umarni da kyakkyawan aiki kuma suna hana mummunan aiki,wad’annan sune wad’anda suka rabauta) suratu Ali – Imrana.

A wani wurin Allah mad’aukakin sarki ya bayyana cewa wannan al’umma ita ce mafi alherin al’ummun da aka samar a cikin mutane,saboda umarninta da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki,Allah ya ce:

 

“کنتم خير أمة أخرجت للناس تأمرون بالمعروف و تنھون عن المنکر و تؤمنون بالله”

(Kun kasance mafiya alherin al’umma da aka fitar wa da mutane,kuna umarni da kyakkyawan aiki,kuma kuna hana mummunan aiki,Sannan kuna yin imani da Allah).

Manzon Allah (S A W) ya bayyana mana cewa umarni da kyakkyawan aiki da hana mummunan aiki wajibi ne na shari’a,da shi al’umma take tsira daga azabar Allah.

A lokacin ne Hamza ya juyo yana kallon Mummy,idanuwansa cike taf da hawaye,ita ma Mummy da jikinta ya fara sanyi ta zuba masa idanu tana kallonsa,cikin taushin murya Hamza ya cigaba da magana.

A cikin tarbiyyar da na bawa Hidaya na gwada mata yiwa iyaye biyayya a bisa umarnin da suka bayar,kullum ina fad’amata darajar iyaye da k’imarsu,na san cewar da wannan tayi amfani wajen yarda da abin da kika umarceta na kasancewarki mahaifiya a gareta,Sai dai abu d’aya da Hidaya ta manta,wanda shi ma na karanta mata shi,babu biyayya cikin sab’awa mahalicci,kisan kai sab’on Allah ne mai girma,ba a yarda ayi umarni da aikata shi kai tsaye ba, matuk’ar ba ta hanyar shari’a aka bi ba.Na san cewar dole Hidaya ta gigita da umarninki,wanda da ta aiwatar da shi da babu abin da zai hana ta shiga cikin bala’i da masifa mabayyani,Na san ke ma a lokacin da kika rubuta wannan takarda ba kya cikin kamalalliyar nutsuwa Mummy,burinki kawai d’aukar fansa,wanda kuma da kinyi hak’uri kin barwa Allah ko kin bi tsarin shari’a to da duk wasu abubuwan basu faru ba”

Sai ga Mummy ta fashe da kuka,hawaye yaraf yaraf ta dubi Hamza ta ce.

“Madalla da kai HAMZA GARKUWA,madalla da wannan bawan Allah mai umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki”

Hamza ya runtse idanuwansa ya sunkuyar da kansa k’asa,hawayen sa na d’isa akan tayel d’in da ke shimfid’e a k’asa,cikin murya mai rauni ya ce.

“An karb’o wani hadisi daga Huzaifa d’an yamani,Allah ya yarda da shi,ya ce,Manzon Allah ( S A W) ya ce, “Na rantse da wanda raina yake hannunsa,ko dai ku yi umarni da kyakkyawan aiki,ku hana mummunan aiki,ko ya kusata Allah ya aiko da azaba a kanku,uk’uba daga gareshi,sannan ku rok’eshi ba za a amsa muku ba” Tirmizi ne ya rawaito shi.

Yana tsayawa da maganar sa Mummy ta share hawayen ta,Sannan cikin wani irin murmushi ta ce.

“Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da amincin Allah su k’ara tabbata ga fiyayyen halitta ,manzon Allah (S A W), da iyalensa da sahabbansa,da wad’anda suka bi su gaba d’ayan su har zuwa ranar sakamako,kyakkyawan k’arshe yana ga masu tsoron Allah,da masu umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki”

A hankali gabad’ayan su suka waiwaya jin an bud’e k’ofar d’akin,Aunty Sajida ce rik’e da Hidaya da ke takawa a hankali saboda rashin k’warin jiki,ta kuma wani irin zurmawa kanta ko d’ankwali babu sai gashin ta da ya bazo akan kafad’un ta duk ya hargitse,fuskarta tayi wani irin haske,sai dai har lokacin kuma kumburin marin da Khaleel da daddala mata bai baje ba,Kallo d’aya Hamza yayi mata yayi maza ya kau da kai k’irjinsa na tsananin bugawa,sai ya fara ambatar Allah a ransa,yayin da Hidayan ta tsaya cak ta zubawa Mummy idanuwa tana kallonta,wani irin abu take ji yana mamaye jikinta yana ratsa b’argonta,bata san matar ba,amma kallo d’aya tayi mata taji zuciyarta ta girgiza,a hankali Hidaya ta maida kanta kan Hamza da alamun tambaya a idanuwanta,ganin ya kawar da kansa daga gareta sai ta juyar da kallonta zuwa ga Umma,sannan ta d’ago hannuwanta tana nuna Mummy tana tambayar Umma da idanuwan ta shin wacece wannan?Umma tayi wani miskilin murmushi kafin ta bud’e baki cikin taushin murya tayi magana.

“Mahaifiyarki ce Fad’ima….wannan ita ce Mummyn ki Hidaya…je ki gareta kiji d’uminta kamar yadda ko wane d’a yake son jin d’umin mahaifiyar sa”

Sai Hidaya ta zare jikinta a hankali daga jikin Aunty Sajida,a hankali ta soma takawa jikinta na rawa ta nufi Mummy da ke tsaye tana kallonta cikin wani yanayi mara fassaruwa,har Hidayan ta je gabanta ta tsaya cak,suka zubawa juna idanu suna wani irin duban juna, A hankali Hidaya ta d’aga hannunta ta kai jikin Mummy tana tab’ata da niyyar tabbatarwa,zuciyarta na rawa,da k’yar ta iya bud’e baki cikin dasasshiyar murya ta ce.

“Ke ce ?da gaske ke ce Mummy na?ke ce Mahaifiya ta?”

Bakin Mummy ya kasa furta komai,illa jijjiga kai da tayi alamar tabbatarwa da Hidayan cewa ita d’in dai ita ce mahaifiyarta,da Hidaya tayi wani irin juyi na tsananin murna sai gata a k’irjin Mummy ta rungumeta tana cusa kanta cikin k’irjinta,Mummy ta tarbeta suka rungume juna kamar za su had’e su zama abu d’aya,take Hidaya ta fashe da wani irin wahalallen kuka mai ban tausayi,surutai take yi tana jin numfashin ta na sama kamar zai d’auke tsabar murna.

“Ka na ina Ya Hamza…ka zo ka gani yau ga Mummy na ta zo gareni…zo ka tayani farinciki ya Hamza…daman kana ta fad’a min cewar in dai tana raye zan ganta…kana ta cemin komai daren dad’ewa za ta zo gareni…yau ga ranar ta zo…kana ina Ya Hamzana…Lallai yau na dad’a gasgataka…..

Kan Hamza a sunkuye yana zubar da hawayen tausayin uwa da y’a,Aunty Sajida ma na kuka,yayin da Umma ma ke kuka tana ji a zuciyarta duk wanda ya zama dalilin raba tsakanin wannan y’a da uwa na tsawon lokaci to hak’ik’a ya cika babban azzalumi…..!

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SABA’IN DA BAKWAI DA NA SABA’IN DA TAKWAS

 

 

 

 

***Da k’yar Mummy ta iya d’ago kan Hidaya daga k’irjinta,ta tsura mata idanu tana kallon yadda hawaye yayi mata kaca kaca a fuskarta,hannu ta kai tana share mata,a yayin da wasu suke sake b’ullowa kamar ana tunkud’o su,girgiza mata kai Mummy tayi tana mayar da nata hawayen da ke k’ok’arin sake zubowa,Hidaya ta kasa jurewa,ta sake afkawa k’irjin mahaifiyarta tana sake k’ank’ameta kamar za ta gudu,wani irin dad’i mara misali na kwarara a ruhinta,wai yau ita ce rungume jikin Mummyn ta,me yafi wannan dad’i a duniyarta?

Da k’yar Mummy ta iya janye Hidayan suka zauna bakin gado,amma duk da hakan Hidayan tana manne da ita,sai faman kallonta take tana rik’e mata hannu da kwanciya kan kafad’arta,murna duk ta ishe ta,sai can ta waiwaya tana duban Hamza da ke k’ok’arin bud’e k’ofa ya fita daga d’akin,a hankali cikin dasasshiyar murya Hidaya ta ambaci sunan sa,tasayawa yayi cak sannan ya waiwayo suna duban juna,da sauri ya kawar da kai saboda baya son kallonta sosai,a hankali tayi magana tana murmushi.

“Ya Hamza kaga Mummy na ta zo ….yau ta tuna dani ta zo gareni”

Shi ma murmushin yayi wanda ya k’ara masa kyau,sannan ya mayar mata da amsar maganarta.

“Na ganta Hidaya,har ma na riga ki ganinta fa,kuma ina tayaki murna”

Sakin hannun Mummy tayi,sannan ta taso a hankali ta nufo in da yake tsaye,tana zuwa gabansa ta tsaya tana kallonsa,d’ago kansa yayi ya dubeta,hawaye ya gani sun cicciko idanuwanta,cikin wata irin murya ta karya wuya ta fara magana.

“Ya Hamza ai na sani…wallahi na san babu wanda zai taya ni murna a duniya sama da kai…Ya Hamza ka fad’awa kowa…ka fad’a da babbar murya cewar Mummyn Hidaya ta bayyana…ina so kowa ya tayani murna…murnar saduwa da Mahaifiyata…Ya Hamza har Uncle Khaleel ina so ka fad’a masa domin ya tayani murna….!”

A hanzarce ya zuba mata idanu jin ta ambaci sunan Khaleel,da mugun mamaki yake kallonta,sai yaga ta girgiza kai hawaye ya sake zubo mata,ta saka bayan hannunta ta share,sannan ta cigaba da magana cikin raunin murya.

“Ka yi mamaki da na ambaci Uncle Khaleel ko?ai ba zan tab’a fushi da shi ba har na daina numfashi,saboda shi GARKUWA ta biyu ne a gareni,kaje wajensa ka fad’a masa cewar yau Mahaifiyata ta bayyana,kuma na yafe masa duk abin da yayi min,ba ma shi kad’ai ba,duk wanda ya san ya tab’a yi min wani abu mara dad’i ,ko na zalunci,ko na ha’inci,ko ya zage ni ,ko ya aibatani,a yau duk su sani na yafe musu,darajar Mahaifiyata,mutum d’aya ne ba zan iya yafe masa ba a duniya wato DADDY”

Tana fad’in hakan ta juya,ta bar Hamza tsaye yana binta da idanu,kafin ya lumshe idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya.

 

 

 

 

****************

 

Sai a washe garin ranar sannan Khaleel ya fara dawowa hayyacinsa sosai,idan ka ganshi ba zaka shaida shi ba saboda tsananin ramar da yayi,tunda ya dawo hankalinsa kuma bashi da aikin komai sai kuka da zubar hawaye,Aunty Kubra tana iya k’ok’arinta wajen lallashi da yi masa nasiha akan hak’uri amma ya gaza,sosai zuciyarsa ta tab’u akan abin da ya faru,bashi da wani buri a yanzu illa ganin Hamza da Hidaya,to amma da wane idanuwan zai dube su?

Bud’e k’ofar d’akin akayi,Daddy ne ya shigo jikinsa a salub’e yana tafiya da k’yar,bayan sa Alhaji Maude ne rik’e da ledoji ya zo duba Khaleel,Khaleel na ganinsu yayi maza ya juya musu baya hawaye na zubo masa,baya son ko kallon Daddyn sa kwata kwata,a lokacin ne Aunty Kubra ta bud’e k’ofar toilet d’in d’akin ta fito,ita ma kanta ganin Alhaji Maude sai da taji ba dad’i a ranta,ta tsani mutumin k’warai da gaske,anan ta tarar Daddyn sai magana yake wa Khaleel amma yayi banza da shi yak’i juyowa ya dube shi sai kuka yake yi,matsawa tayi sosai tana lek’a fuskar Khaleel d’in,cikin tausayi ta girgiza masa kai tayi magana.

“Khaleel wannan ba d’abiarka ba ce,kana ji mahaifinka na magana kana share shi?tare da abokinsa yake fa,me yasa hakan?”

Cikin kuka Khaleel yayi magana da k’yara.

“Bana son ganinsa Aunty…Don Allah ki ce ya fita daga d’akin nan…zuciyata za ta buga idan ina kallonsa”

A gigice Daddy ya dubi Aunty suka had’a idanu,cikin fushi Aunty ta juya tana duban Khaleel zata yi magana,da hanzari Daddy ya dakatar da ita,sannan ya sunkuyar da kai jiki a sanyaye,muryar sa na rawa ya dubi Khaleel ya ce.

“Shikenan zan tafi Khaleel tunda baka son ganina,kayi hak’uri”

Yana fad’in hakan ya juya yana kallon Alhaji maude,cikin sanyin murya yace masa.

“Mu je Alhaji Maude”

Alhaji Maude ya dire kayan hannunsa,sannan ya juya yayi gaba zuciyarsa k’al da tsananin murna,Daddy ya biyo shi jiki a sanyaye,yana tafe yana waiwayen Khaleel da ke ta faman kuka,hawaye ya cicciko idanuwan sa,da hanzari ya fice daga d’akin yana goge idanuwan sa da gefen babbar rigar jikinsa,ya bar Aunty Kubra da binsa da kallo bakinta a sake.

Yana ficewa Aunty Kubra ta mayar da kallonta kan Khaleel,cikin b’acin rai ta ce da shi.

“Amma ka bani mamaki Khaleel,wannan wane irin tozarci ne kai wa mahaifinka haka a gaban abokinsa?me yayi maka da ya cancanci irin wannan sakayyar Khaleel?Mahaifinka ne fa da yayi silar zuwanka duniya”

Da k’yar Khaleel ya iya k’arfin halin mik’ewa zaune,hawaye na zuba a idanuwansa,kallon Aunty yayi da ta zuba masa idanu tana kallonsa,sai ya sunkuyar da kai ya fara magana a hankali cikin rauni.

“Da gaske bana son ganinsa Aunty,kuma nayi hakan ne saboda gudun fad’awa halaka,domin muddin idanuwa na za su dinga ganinsa zan iya yin wani abu wanda ya sab’awa Allah Aunty”

Aunty ta nemi kujerar gefen gadon ta zauna tana fuskantarsa,idanuwanta cike da tsananin mamaki take duban Khaleel,kafin ta girgiza kai tayi k’arfin halin yin magana.

“Me yake faruwa ne Khaleel?Na kasa gane kan abubuwan da suke faruwa tun daga jiya zuwa yau,me ya faru da kai ne a jiyan?kuma ina matarka take?

Runtse idanuwa Khaleel yayi da k’arfi kafin ya sake fashewa da wani irin kuka me cin zuciya,cikin wata irin murya yace wa Aunty Kubra.

“Aunty na sake ta,wai na sake ta da bakina,wai nine na saki matata Hidaya har saki uku kwana d’aya da auren mu”

A zabure Aunty Kubra ta mik’e tana salati,maimaita salati take da innalillahi bakinta na karkarwa,duk ta gigice tana jin maganar na mata kuwwa a kunne,Khaleel ya bud’e idanuwan sa hawaye na zuba kamar famfo,ya cigaba da kallon Aunty Kubra,ya kai hannunsa ya dafe k’irjinsa saboda yadda yaji ya motsa masa da azabar ciwo.

“Aunty hak’ik’a naci amanar Aboki da Hidaya,na d’aukar masa alk’awarin zan rik’e masa ita amana,zan zama GARKUWARTA,amma na gaza hakan tun ba a je ko’ina ba,Aunty jiya da hannuna na dinga dukan Hidaya ina marinta,banji tausayinta ba,ban duba rauninta ba,ban duba lalurarta ba,ban fasa dukanta ba har aboki ya shigo ya ganni,Kuma a gaban idanuwan sa nayi wurgi da ita ina ambata mata saki” yana zuwa nan ya sake rushewa da kuka.

Aunty ta kuma saka salati hawaye na cicciko idanuwan ta,jikinta babu in da baya rawa,a hankali ta kuma neman waje ta zauna jin tana shirin fad’uwa k’asa,cikin gigita ta sake duban Khaleel tayi magana a rud’e.

“Saki uku fa naji ka ambata Khaleel…me tayi maka haka..?me ya jawo hakan ?

Cikin kuka ya ce.

“Daddy ne Aunty…Daddy ne ya janyo komai”

Aunty ta sake rikicewa,hannayenta dafa da kuncin ta ta ce.

“Bangane ba Khaleel,ban fahimta ba,kamar ya ya Daddyn ka shi ya janyo komai?shine ya saka ka sake ta?”

Khaleel yayi shiru ya kasa magana ya cigaba da kuka,idanuwan sa har wani janyewa suke tsabar bala’in kukan da yake yi,mugun tausayin sa ya cigaba da ratsa zuciyar Aunty,tana jin kukansa da damuwarsa na tab’a ruhinta,a hankali ta sassauta murya ta dube shi ta ce.

“Khaleel ka daina wannan kukan don Allah,wallahi ba k’aramin d’aga min hankali yake ba,yadda zanji damuwar Sameer da Sameera a raina kaima haka nake jin taka,domin duk d’aya na d’auke ku kamar yadda ka d’aukeni a matsayin mahaifiya,ka bud’e bakinka ka fad’a min abin da ya faru har ya janyo saki tsakaninka da matarka kwana d’al tal da aure,kuma sakin ma irinna bidi’a mara kyau Khaleel,wanda ko Allah shine ya halatta shi amma baya son sa,ni ban san abin da ya faru ba tun jiyan,amma zuciyata tuni take fad’a min wani abu mara dad’i ya faru,duk da ban za ci girmansa ya kai haka ba,bayan kun fito da Daddyn ka da kaje gaishe shi da safe,baku jima sosai ba ya dawo min a firgice wai na zo na tayashi lallashinka yayi maka laifi,shine ka shige d’aki ka kulle kanka,da muka zo shine muka ganka cikin mawuyacin hali kana aman jini har ka fita daga hayyacinka,shine muka rud’e muka kwasoka zuwa asibiti,ni gabad’aya ma na manta da zancen matarka sai da komai ya fara lafawa sannan na tuna,shine na tambayi Daddyn ka ita,shi kuma yak’i cemin komai akanta har zuwa yanzu,don Allah Khaleel ka fad’a min,shin mahaifinka ne ya umarceka da ka saki Hidaya ko kuwa?domin zuciyata ta fara zargin hakan saboda wasu abubuwa da suka faru tun kafin a d’aura auren ku”

Khaleel ya d’ago kansa ya dubi Aunty,yayi wata irin ajiyar zuciya,Numfashi na masa wahalar shak’a,a haka ya daure ya fara magana yana kallon Aunty Kubra,wadda ta zuba masa idanu kamar ta cinye shi saboda k’aguwar jin maganar da zai fad’a.

“Aunty na rantse miki da Allah ban tab’a ganin bak’ar rana irin jiya ba,ranar da tazo da abubuwa na tarin bak’inciki a gareni da sauyin rayuwa,kin sani Aunty ina tsananin yiwa mahaifina biyayya tun ina yaro,komai ya umarceni ina aikatawa ko da ni bana son abun,ba kuma komai ke sa hakan ba sai yawan Nasihar da Abokina Hamza yake min akan girmama iyaye da fifita buk’atarsu akan ta kowa,matuk’ar bata sab’awa Allah da manzonsa ba,Hamza ne kullum yake k’ara cusa min k’aunar Mahaifina da kare masa mutuncinsa,dalilin da yasa kenan jiyan na aikata abin da ban ma san nayi ba,na saki matata wadda nake tsananin so da k’auna,saboda ta zagi mahaifina a gabana,ta ci mutuncinsa ta tozarta shi,shine na zame masa GARKUWA,na kare shi na kare masa martaba da mutuncin,nayi abu cikin rashin sani wanda yafi dare duhu,domin ban sani ba ashe Hidaya tana da dalilinta na aikata hakan ga mahaifina,dalili kuwa mai k’arfi wanda nake bak’incikin sanar miki da shi a halin yanzu”

Yayi shiru yana maida numfashi yana jin kamar ya mace a wajen dan bak’inciki da k’uncin da yake ji ya dabaibaye ruhinsa,Aunty ta tsura masa idanu cikin numfarfashi da dukan zuciya tana shirin jin dalilin da yasa Hidaya ta aikata hakan akan Daddy,wanda ya janyo mata saki uku kwana d’aya rak da d’aura auren ta.

Runtse idanuwa Khaleel yayi hawaye ya gangaro da gudu,yana shesshek’ar kuka ya cigaba da magana.

“Aunty….Aunty…Aunty ashe Daddy ne ya kashe mahaifin Hidaya…ashe Daddy ne ya zama silar barin Mahaifinta duniya….shine ya zama ajalinsa…shine ya kashe mata ubanta mahaifi….Daddy ne….Daddy ne Aunty….!

Sai ga Aunty rigijib ta fad’o daga kan kujerar da take zaune tsabar tsoratar da tayi,hannuwanta akan ta ta saka saka salati da k’arfin gaske,wani mugun kuka ya kufce mata tana ambatar “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” ita kuka ,Khaleel Kuka, har kukan Khaleel ya fara yawa ya fara wani irin tari da shak’uwa kamar zai mace.

 

 

 

******************

 

 

Tana kwance lamo akan gadon Umma,ba bacci take ba illa tunanin da ya addabi ruhinta,tunani guda biyu,tun bayan dawowarsu daga asibiti take son su zauna ita da Mummyn ta suyi maganganu a tsakanin su,amma hakan ya gagara,gabad’aya Mummyn tak’i ce mata komai,sai dai taji suna ta hirarsu da Umma da Aunty Sajida,sai kuma tunanin Uncle Khaleel da ya addabi ruhinta,da ta runtse idanuwanta shi take gani,ko bacci take mafarkinsa take,kewarsa take ji sosai a ranta,idan ta tuna soyayyar da ya nuna mata daren da aka kaita gidansa har wani hawaye take yi,so take ta ganshi duk da akwai katanga tsakaninta da shi,tana jin k’iyayyar mahaifinsa amma shi tausayi da soyayyarsa ne suka sami matsuguni a ranta,ta san k’ila yana cikin wani hali,ina ma za ta ganshi,ina ma za su yi ido biyu da juna,wallahi da ta furta masa kalmar yafiya da afuwa,domin ta san yana can yana zargin kansa da cutar ta ,da cin amanar ta,yana can yana tuhumar kansa da kasa zame mata GARKUWA kamar yadda ya so,bata tab’a sanin akwai wata soyayya mai zak’i da dad’i a filin duniya kamar wadda Khaleel ya nuna mata ba,sai gashi Soyayyar ta katse a dai dai lokacin da take cikin tsananin buk’atar ta,ita kuma k’addararta kenan! karb’ar tikitin saki uku kwana d’aya tal da zamantowar ta matar aure,shikenan yanzu sai dai a kirata BAZAWARA,kalmar da ko a baki bata da dad’in fad’a,to amma ya zata yi da hukuncin ubangiji?wanda shine mai tsara komai yadda yake so akan wanda yake so kuma,a maimakon ta dinga jin zafin Khaleel a ranta,sai aka samu akasi take jin wata irin soyayyar sa a ranta wadda bata tab’a ji ba,da yawan mutane ta kanji suna cewa “idan namiji ya saki mace,to dukkansu sukan samu kansu cikin nadama da tsananin son juna,musamman wanda saki uku ya shiga tsakani” ashe kuwa hakane! tunda gashi tana jin hakan a filin zuciyar ta,idanuwan ta na mararin ganin Uncle Khaleel ! kunnuwanta na son jin muryarsa da dad’ad’an kalamansa ! hancinta na d’okin jin k’amshin jikinsa ! ilahirin jikinta na buk’atar Uncle Khaleel gabad’aya…!

Lokaci d’aya ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ! ta wawuri pillow ta matse a k’irjinta gam hawaye na sharara da gudu,kuka take haik’an tana furta wasu irin maganganu cikin gushewar hankali da k’wak’walwa.

“Me ya sa ka guje ni Mijinahhhh…?me yasa ka tafi ka barni lokacin da nake buk’atar ka…? me yasa ka nisanceni bayan na mallaka maka komai…?har ma ka cinye komai…! Don Allah Allah da manzon sa Uncle Khaleel…Don Alk’awarin da kayi min na zamo wa GARKUWATA ka zo gareni….! ka zo na ganka Uncle Khaleel….wallahi INA TSANANIN SONKA”

Kalamanta suka sauka a kunnuwan Ya Hamza ! wanda ya shigo da nufin bata magungunanta domin ta sha,domin sai ya sakata a gaba sannan take sha,wani irin bugawa k’irjinsa yayi da k’arfi,kukan da take yi cikin rauni da kalaman da take furtawa sunyi matuk’ar sanyaya jikinsa,hajijiya ya ji tana kwasar sa kamar ya fad’i,a hankali ya dafa bango yana ambatar”Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” a zuciyar sa.

 

 

 

 

 

*Idan bakwa comeents zan ajiye alk’alamina,bana jin dad’i ma amma hakan nake daurewa in muku saboda yadda kuke son littafin,amma sharhi ya dinga gagararku haba*🙄🙄🙄

 

 

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA SABA’IN DA TARA DA NA TAMANIN

 

 

 

****A sanyaye ya juya ya fasa shiga d’akin,domin bai ma san ta ya ya zai fuskanceta tana wannan kukan ba,a yanzun ma ba k’aramin motsa masa mikin da ke zuciyarsa tayi ba,gabad’aya ta taso masa da wata irin kewar Khaleel shi ma.

Umma da Mummy suka waiwayo suna kallonsa lokacin da ya k’araso parlour’n,da hanzari ya aro jarumta dan kar su gane yanayin sa,Umma ce ta cigaba da kallonsa sannan tayi magana.

“Wai har ka bata maganin kenan?”

Girgiza kai yayi yana shirin zama kan kujerar da ke gefensa,a hankali ya dubi Umma yayi magana.

“Ah ah ban bata ba,da alamun kamar barci ta fara yi shiyasa na k’yaleta zuwa lokacin da za ta farka”

Umma ta d’an murmusa ta ce.

“Ai gara ta samu tayi barcin zai rage mata damuwa,tunda muka dawo daga asibitin nan na lura tana cikin damuwa,na san k’ila sakin da Khaleel yayi mata ne yake damun zuciyarta,to amma ya zata yi ?haka Allah ya k’addara zai faru”

Shiru Hamza yayi baice komai ba,sai can ya dubi Mummy da tayi shiru tana jin maganganunsu kawai,har zaiyi magana kuma sai ya fasa ya sake maida kansa k’asa yana sakin ajiyar zuciya. Mummy ta lura da shi shiyasa tayi murmushi ta kalleshi ta ce.

“Ya dai GARKUWAR HIDAYA akwai wata magana ne?”

Girgiza kai kawai yayi cikin k’aramin murmushi,yayi shiru ya kuma yin k’asa da kansa.

Mummy ta dubi Umma suka had’a ido suka yi murmushi,sannan ta dawo da ganinta kan Hamzan,cikin muryar kyautatawa ta ce.

“Labarin zuciya a tambayi fuska! akan fuskarka na hango tarin maganganun da ke zuciyar ka GARKUWA,don haka bud’e bakinka ka fito da komai,kar ka bar komai a ranka,domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa”

kafin ma yayi magana Ummansa ta cafe zancen tana kallon Mummy.

“Aikam dai gara ki fad’a masa,domin wannan GARKUWAR ta ki bashi da wani hali sai barin kashi a cikin,wanda barin da yayi masa har yayi masa babbar illa cikin cikinsa”

Mummy bata gane zancen Umma ba,amma shi Hamza sarai ya fuskanci abin da take nufi,murmushi kawai yayi bai ce komai ba,illa duban Mummy da yayi ya fara magana cikin nutsuwa.

“Mummy daga ni har Hidaya zuciyoyinmu cike suke da son sanin abubuwa da dama daga gareki,na farko sanin alak’ar Daddy da mahaifin Hidaya,na biyu tabbacin Daddy ne ya kashe shi da kuma dalilin yin kisan,na uku dalilin gujewarki a rayuwar Hidaya tsawon lokaci,na hud’u son sanin yadda akayi kike bibiyarmu da sanin halin da muke ciki,na biyar dalilin bayyanarki garemu a dai dai wannan lokaci,na shida….

“Dakata GARKUWA” Mummy ta katseshi cikin k’aramin murmushi,sannan ta cigaba da ce wa.

“Duk wad’annan tambayoyin ni zan amsa muku su? Lallai kun had’ani da aiki babba” Cikin sigar zaulaya tayi maganar,Hamza ya d’an shafa kwantacciyar sumar kansa yana jingina da bayan kujerar da yake zaune,cikin wani irin murmushi shi ma ya dubeta ya ce.

“Eh Mummy,duka muke so har ma da k’arin wasu tambayoyin,don Allah a taimaka ko dan mu san yadda za mu tunkari lamarin Daddy wajen shari’a”

Ambatar sunan Daddy ma bata so,amma hakan ta cije bata bayyana ba,illa murmushi da ta sake yi wanda ya zamto na takaici a gareta,sannan ta cewa Hamza.

“To kar ka damu GARKUWA,da yardar Allah za ku ji komai da kuke buk’atar ji daga gareni,akwai dalilin da ya saka har yanzun ban gaya muku ba”

Gyad’a kai yayi tare da ce wa.

“To shikenan Mummy Allah ya nuna mana lokacin”

“Ameen ya Allah” Mummy ta fad’a,sannan ta d’auke kanta daga gareshi ta mayar da hankalin ta kan Umma suka cigaba da hirar duniya da abubuwan da suke faruwa a wannan zamanin.

Hamza yana zaune yana sauraren su shiru da shi,can ya d’auko wayarsa yana d’an danne danne har ya shiga gallery,da hoton su ya fara cin karo shi da Khaleel,wanda suka d’auka ranar d’aurin aure,Khaleel ya dafo kafad’arsa suna murmushi,sunyi matuk’ar kyawu mara misali,k’urawa fuskar Khaleel idanuwa yayi kamar ya ciroshi daga jikin hoton,wata k’walla na taruwa a idanunsa,a hankali ya danne wayar ya kashe ta ma gabad’aya ya jefa cikin aljaihunsa,sai kuma ya mik’e a sanyaye ya dubi Umma,yayi magana a hankali.

“Umma bari na d’an fita gun su Faisal”

Umma ta amsa,ya nufi k’ofa ya fice yana jan k’afa,gabad’aya baya jin dad’in yanayin jikinsa,shi kansa idan aka bashi gado a asibiti tabbas zai kwanta ne,saboda yanayin da yake jin jikinsa da zuciyar sa,a tsakar gida ya tadda Aunty Sajida tana aiki,yayi mata sannu sannan ya wuce ya fice daga gidan ma gabad’aya,Aunty Sajida ta bishi da idanuwa har ya k’urewa ganinta.

A can parlour ma Mummy da kallo ta bishi,sai da ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya,cikin murmushi ta ce .

“GARKUWA kenan”

Umma ta d’anyi dariya kad’an tana duban Mummy ta ce.

“Wato dai kin sakawa Hamza suna GARKUWA ko? to wai shin GARKUWAR Hidaya kike nufi ko kuwa?”

Mummy ta jingina da bayan kujerar da take kai tana duban Umma,tayi murmushi mai kyau ta ce.

“Ki godewa Allah ki k’ara godewa Allah da ya baki Hamza a matsayin d’a,Hamza ba iya GARKUWAR Hidaya ya tsaya ba ! shi d’in GARKUWA NE a komai !

Sai Umma tayi murmushi tana jin dad’in yabon da d’anta yake samu a kullum.

 

 

****************

 

Wannan magana da Khaleel ya fad’awa Aunty Kubra ita ce magana mafi muni da ta tab’a ji a kunnuwanta,wai mijinta ne yayi kisan kai! tayi kuka a ranar kuka mara misali,har ta dinga danasanin kasancewa a matsayin matar Daddy,duk da yanzu alamu sun nuna ya shiryu,amma kisan kai babban tabo ne da zai iya shafar rayuwar y’ay’anta ko a gaba.

A maimakon ta cigaba da rarrashin Khaleel sai ita ma take neman me rarrashinta,har sai da taga kukan bashi da wani amfani a gareta sannan ta hak’ura ta daina,sai dai lokaci zuwa lokaci ta kan ji hawayen ya zubo mata,ta kai hannu ta share.

Ko wayar Daddy k’in d’agawa tayi,saboda ko muryarsa bata k’aunar ji,abu d’aya kawai take son sani,shine yadda akayi Daddyn ya kashe mahaifin Hidaya,a yaushe hakan ta faru?kuma menene dalilin kisan?duk yadda zuciyarta ke zakwad’in samun wad’annan amsoshi bata kai Khaleel ba,ji yake tamkar yayi fiffike ya tafi gurin Hidaya ta warware masa komai,hakan yasa ya dinga yiwa likitansa magiya yana kuka akan ya sallameshi,iya rarrashi likitan yayi masa akan ya bari ya sake murmurewa amma Khaleel ya k’i amincewa,tilas likitan ba don ya so ba a washe gari ya rubuta takardar sallama ya basu,tare da kafa sharud’a masu yawa wajen kulawa da lafiyar Khaleel d’in.

Suna shirin tafiya sai ga Daddy ya zo,daga Khaleel d’in har Aunty Kubra babu wanda ya dubeshi,dan wani mugun kallo ma da Aunty Kubran tayi masa sai da ya yamutsa masa y’an hanjin sa,tsoro ya kamashi dan ya san tabbas Khaleel ya fad’a mata komai,kuma ya san in zai kwana dubu yana nufin kare kansa ba za su saurare shi ba.

Ya na ji Khaleel yana cewa da Aunty Kubra shifa ba zai shiga motar sa ba,gara ya hau motar haya ta mai dashi gida ko ya tafi da k’afarsa,bai k’ara jin mamaki ba sai da yaji Aunty Kubran ta mayar masa da amsar cewa”Ni ma ba zan hau motar Daddynka ba Khaleel,ni yanzu tsoronsa ma nake yi,mutumin da yayi kisan kai ai abun tsoro ne,muje mu shiga tawa motar mu tafi,daman da ita na zo asibitin nan randa muka kawo ka”

Daddy yana tsaye kamar gunki yana duban su,har Aunty Kubra ta gama ficewa da kayansu ta saka a mota,sannan ta dawo tana tambayar Khaleel shin zai iya tafiya ko sai ta rik’eshi,Khaleel yace zai iya,saboda jikinsa babu k’wari garin mik’ewa har yana shirin fad’uwa,Daddy ya zaburo zai rik’e shi,Khaleel ya janye jikinsa da sauri yana d’auke kai gefe guda,sannan ya gyara tsayuwar sa ya fara takawa a hankali kamar mai tausayin k’asa,ya rame sosai duk ya zurma,yayi fari fat dogon hancinsa ya k’ara fitowa,leb’ensa yayi jajur,yayin da idanuwan sa suka k’ara fitowa da wata irin kala.

Yana tafe Aunty Kubra na biye da shi har zuwa wajen mota,Daddy yana tsaye suka tafi suka barshi a d’akin,ya rasa ma mai zaiyi,haka shima ya janyo jiki ya fito a salub’e,yana kallo Aunty Kubra ta bud’ewa Khaleel k’ofa ya shiga ya zauna,ita ma ta zagaya ta shiga ta rufe,sannan ta tayar da motar suka fice daga harabar asibitin,A sanyaye Daddy ya k’arasa wajen tasa motar ya shiga ya tayar ya rufa musu baya,gara ya bisu gida ayi ta ta k’are kawai.

Sun fara tafiya kan titi Khaleel yana ta takure jikinsa yana lumshe idanu,sanyi yake ji sosai,har sai da ya waiwayo ya dubi Aunty yayi magana a hankali.

“Aunty a kashe A C d’in motar nan,sanyi nake ji”

Aunty ta kai hannu ta kashe tana cigaba da tuk’i,fuska babu walwala ta ce.

“Don dai kawai ka damu a sallameka ne Khaleel,amma ni na san baka gama warkewa ba,har yanzu jikinka baiyi k’warin da ake so ba”

Murmushi yayi mai ciwo,kafin ya girgiza kai yayi magana.

“Ai Aunty jikina ba zai tab’a dawowa yadda ake so ba,balle kuma zuciyata da ta riga ta gama raunata gabad’aya”

Hanzarin dubansa tayi ta d’an harareshi,sannan ta ce.

“Kar ka kuma fad’in hakan Khaleel,Ai Allah (S W A)shine yake d’orawa bayinsa cuta,kuma shine yake yaye musu,kar ka cire rai da rahamar Allah,sai kaga ka warke sumul kamar baka tab’a wata cuta ba”

Murmushi ya sake yi,sannan ya ce.

“Haka ne Aunty,tunda kin ambaci Allah” Sai kuma yayi shiru ya d’an rufe idanuwansa yana maida numfashi,Aunty ta cigaba da tuk’in ta kowa yayi shiru.

Sun d’an yi tafiya mai nisa suna dab da zuwa wata kwana sai Khaleel ya bud’e idanuwan sa,gyara zamansa yayi sannan ya waiwaya ya kalli Aunty Kubra ya ce.

“Ba gida zaki kaini ba fa Aunty”

A d’an sace tayi masa kallon mamaki ita ma ta tambaye shi.

“Ina zan kai ka?”

Kai tsaye ya amsa.

“Gun Hidaya da Aboki”

Sai da Aunty ta sake rik’e sitiyarin motar sosai saboda yadda ya so kufcewa daga hannunta tsabar mamakin maganar da Khaleel ya fad’a,cikin wata irin murya ta ce.

“Khaleel me kace?na kaika gun Hidaya?nufinka in kaika gidansu yanzu fa! kai kuwa wane k’warin gwiwa ke gareka da har za ka iya tunkarar wad’annan mutanen bayan manyan laifukan da ka aikata musu?”da wane ido za ka kallesu Khaleel?”

Wani hawaye ne ya ciko idanuwan sa har ya zubo kan kyakkyawar fuskarsa,ya ja numfashi ya runtse idanu yayi magana cikin rauni.

“Ko ma da wane ido ne zan kallesu Aunty….ni dai fatana ki kaini gare su yanzu…ina son sanin komai…ina son fita daga duhu zuwa cikin haske…ina son komai ya bayyana gareni kafin raina ya bar gangar jikina,ina son yin ido hud’u da manyan masoyan da zuciyata ke so kafin k’asa ta rufe idanuwa na,ki kaini Aunty,yau nake da dama tun kafin damar ta kufce min na rasa….

Sai tausayin Khaleel ya tsirgawa Aunty Kubra,taji ita ma hawayen ya tawo mata,a hankali ta karkatar da motar ta suka nufi gidan su Hamza kamar yadda Khaleel ya buk’ata.

Daddy da ke bin su a baya ganin sun sauya hanya kawai shi ma sai ya sauya,ya rufa musu baya domin bin su in da za su je,a zuciyar sa yana fad’in gara ya bisu koma ina ne,komai ta fanjama fanjammmmm…..!

*TIRK’ASHI*!!!

 

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA TAMANIN DA D’AYA DA NA TAMANIN DA BIYU

 

 

***Dai dai k’ofar gidan Aunty Kubra ta tsaya da motar ta,ta juya tana kallon fuskar Khaleel,fuskarta cike da da damuwa ta ce.

“Ga shi mun zo Khaleel,ta ya ya za mu fuskance su?”

Shi ma cikin tarin damuwar ya dube ta,a hankali ya ce.

“Shiga kawai za mu yi Aunty”

Tayi ajiyar zuciya tana jinjina kai,a hankali ta b’alle murfin motar ta fito k’irjinta na tsananin bugawa,Khaleel ma ya fito yana jan numfashi,idanuwan sa k’ur akan k’ofar gidan,zagayowa Aunty tayi gefen da yake tana kallonsa,shi ma kallonta yayi idanuwansa narai narai sannan ya ce.

“K’irjina bugawa yake sosai Aunty….Zuciyata na rawa”

Aunty tayi kasak’e,kafin kuma tayi ajiyar zuciya ta ce.

“Kayi addu’a Khaleel,in sha Allahu komai zai zo da sauk’i”

Jinjina kai yayi,ya fara addu’o’i cikin zuciyar sa,daga nan suka jera shi da Aunty suka nufi zauren gidan domin shiga.

 

 

***************

 

Da d’an gudunta ta biyo su zuwa zauren gidan tana rik’o hannayen su suna fizgewa,da sauri ta sha gaban su tana nishi,fuska babu walwala Hansa’u ta dube ta ta zabga mata harara ta ce.

“Malama matsa mu wuce,domin magana da ke bata da wani amfani wallahi”

Summaya tayi k’aramin tsaki ita ma tana hararar Hidayan,sannan cikin takaici ta ce.

“K’warai kuwa Hansa’u,gaskiya yanzu na k’ara tabbatar da cewar Hidaya bata da hankali,kuma bata san in da yake mata ciwo ba”

Hidaya ta marairaice kamar tayi kuka,tana duban su ta fara magana cikin rauni.

“Ya kamata ku fuskanceni k’awayena,menene abin fushi dan na fad’a muku sirrin zuciyata,wallahi ba laifina ba ne,kawai na tsinci zuciyata ne da tausayawa Uncle Khaleel,ga kuma tsananin soyayyarsa da take addabata kamar ta faso k’irjina,yanzu haka ji nake idanuwana tamkar su makance saboda rashin ganinsa….

Wani mugun tsaki da Hansa’u ta saki sai da ya tsorata Hidaya,cikin matuk’ar fushi Hansa’u ta dubi Sumayya ta ce.

“Sumayya ina jin kamar nayi ta dukan Hidaya wallahi,ina ji kamar nai ta kikkifa mata mari saboda b’acin ran da take saka ni,wai an ya kuwa lafiyar Hidaya k’alau?an ya kuwa bata da aljanu?”

Summaya ta keb’e baki tsananin takaici na cinta,tana dank’arawa Hidaya harara ta yi magana.

“Ai ni Sister Hansa’u ji nake kamar in shak’eta dan bak’inciki,ban da hauka da rashin zuciya duk wulak’ancin da Khaleel d’in yayi mata amma wai har yanzu yana zuciyarta bata fincike d’an iska ba! shege asararre mai kama da nunar rana! ina ganinsa mai hankali da ilimi ashe dak’ik’i ne mara hankali,an gaya masa har yanzu muna cikin zamanin da maza suke dukan mata ne da zai kama ki yayi ta jibgarki kamar jaka?daman duk soyayyar da yake ambata miki ta k’arya ce shigo shigo ba zurfi yayi miki kenan?”

Da sauri Hansa’u ta katseta da ce wa.

“Ke Sumayya ma ta duka kike,ai ba dukan ne abin ji ba,sakin wulak’ancin da yayi mata shine abin dubawa,kwana d’aya da aure,Allah dai yasa bai gama kwashe miki albarkatun jiki ba bak’in d’an iska,wallahi ni dai da zanga Khaleel d’innan a yanzu mai rabani da shi sai Allah,domin zan iya rufe idanuwa na na ci zarafin matsiyaci”

“Ya isa ! ya isheku haka!!”
Hidaya ta daka musu wata muguwar tsawa tana rik’e kanta,wasu hawaye masu zafi suka zubo mata suna bin kumatun ta,cikin matuk’ar fushi da b’acin rai take duban su tana shesshek’ar kuka ta ce.

“Gaskiya baku da kirki ! har ku tsaya a gabana kuna zagin Uncle Khaleel,shin baku san matsayinsa a guna bane?mijinah ne fa,wanda ya nuna min soyayyah! wanda ya zame min GARKUWA,saboda me dan yayi wani kuskure da ya zama k’addararsa za ku dinga aibata min shi?ni bana fushi da shi! kuma ba zan tab’a fushi da shi ba! Uncle Khaleel martabar mahaifinsa ya kare kamar yadda na kare martabar nawa mahaifin duk da baya raye,akan me za ku ga bak’insa?akan me za ku dinga zagin shi?bana buk’atar hakan,idan har za ku zo gabana ku zagar min Uncle Khaleel to gara baku zo ba”

Cikin fushi Summaya ta ce.

“Ni idan kina ambatar Soyayyar nan ji nake kamar na mutu dan takaici,Hidaya in dai haka Soyayya take to Allah ya tsinewa Soyayyah ! Allah ya kwashe mata albarka,domin bata amfaneki da komai ba tunda gashi cikin kwana d’aya da d’abbak’ata an ci mutuncinta,ashe kuwa Soyayya bata da rana,bata yi wani tasiri da amfani ba,kuma ko za ki mutu,ko za ki tsanemu ba za mu fasa zagin Khaleel ba,ba za mu fasa ambatarsa da mugu azzalumi da ya zalunci maraici ba,kuma Allah ba zai barshi ba sai ya ga sakayya da wurwuri”

Kuka Hidaya ta sake fashewa da shi,ta sa hannu ta ture su daga kusa da ita,sannan cikin kuka ta ce.

“Shikenan ku tafi ku barni,tunda ba za ku gane abin da nake nufi ba,ba za ku daina aibata min Uncle Khaleel d’ina ba! bana son ganinku Hansa’u da Sumayya ku tafi gu bani guri,kuma ni har abada zan cigaba da ganin k’imar Uncle Khaleel tare da girmama shi,saboda INA SON SA,INA K’AUNAR SA,SHINE FARIN CIKINA….!

Tana fad’in hakan ta juya ta shige cikin gidan da gudu tana kuka me tab’a zuciya,yayin da ta barsu a tsaye a wajen suna bin ta da kallon mamaki da takaici,tana shigewa a tare suka saki mugun tsaki,sannan Hansa’u ta ce.

“Za ma ki hankalta ki gane nufinmu,kuma dole ne ki cire wani Khaleel daga ranki,Khaleel d’in banza Khaleel d’in wofi,Shege mara rabo kawai”

Fizgar hannun Sumayya Hansa’u tayi suka nufi k’ofar fita daga gidan,suna kai kansu waje suka yi wata muguwar razana suka yi turus jikinsu na mugun rawa da karkarwa,wata muguwar kunya da basu tab’a ji ba ta lullub’esu,basu tab’a jin muzanta ba irin haka,ba komai ya janyo hakan ba illa Khaleel da ke tsaye yana kallon su cikin wani yanayi,ga Aunty Kubra a gefensa a tsaye ita ma sai kallon su take yi,kallon kuma da suke musu ya nuna alamar cewa sunji duk zagi da aibatawar da suke wa Khaleel d’in.

Wani mugun kwarjini Khaleel d’in yayi musu da basu tab’a gani ba,da hanzari suka sunkuyar da kansu suna jin kamar su nutse dan kunya da muzanta,shi kam Khaleel kallonsu kawai yake yi ya kasa d’auke idanu daga kansu,basu b’ata masa rai ba,illah ma jin tsanar kansa da ya k’ara yi,musamman da yaji kalamai masu dad’i da Hidaya take fad’a a kansa,tabbas yayi rashi,rashi mai girma wanda ba zai maida makamancinsa ba ma balle irin sa,wayyo rayuwa ! bai aune ba sai hawaye suka soma sintiri akan fuskar sa.

Summaya ce ta fara jan hannun Hansa’u da sauri suka bar wajen cikin tsananin kunya,Khaleel ya bi su da kallo yana kuka,har suka k’urewa ganinsa,a hankali ya dawo da kallonsa kan Aunty,ita ma hawayen ne ya cicciko idanuwan ta,amma duk da hakan sai ta girgiza masa kai alamar ya daina kuka,a maimakon ya daina sai ya sake fashewa da wani irin kuka yana ambatar.

“Aunty wallahi da gaske su Sumayya suke,wallahi na cuci Hidaya cuta ta har abada! Aunty dubi kalaman da Hidaya take ambatawa a kaina…Aunty wannan ita ce masoyiya ta hak’ik’a mai yiwa masoyinta uzuri…Aunty nayi rashi…tabbas nayi rashi mafi girma a rayuwata….

Sai ya sake fashewa da kuka,yayin da Aunty ta runtse idanuwa tana jin yadda tausayin Khaleel ke ragargaza zuciyar ta…..!

 

 

 

*************

 

Shigarta cikin gida da gudu tana kuka suka yi kacib’us da Ya Hamza da yake fitowa daga d’akinsa,da kallo ya bita yana jin zuciyarsa na bugu har ta shige parlour’n Umma tana kuka,ta wuce su Umma da Mummy da Aunty Sajida da ke zaune suna hira,ta fad’a d’aki tana gurshek’en kuka.

Cikin tashin hankali Umma ta mik’e da niyyar bin ta d’akin,sai Mummy ta dakatar da ita da fad’in.

“Barta ta sha sharafinta kawai,komai da kika gani da lokacinsa,wataran ba za ta yi hakan ba”

A sanyaye Umma ta koma ta zauna ranta a jagule duk ba dad’i,tausayin Hidayan take ji sosai a ranta.

Shi kam Hamza ya d’auki mintoci a tsaye jikinsa a sanyaye,a hankali kuma ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanu,wai shin yaushe zai samu sauk’i a zuciyarsa ne?yaushe abubuwa za su yi masa sanyi zuciyarsa ta samu salama?ko har sai ya mutu hakan zai tabbata…

Motsin da yaji shine ya bashi damar bud’e idanuwansa ya d’ago kai,nan take idanuwansa suka yi arba da Khaleel,wata matsananciyar fad’uwa gabansu yayi a tare,suka tsurawa juna idanuwa jikinsu na mugun rawa,kowa da abin da yake zuciyar sa,sun d’auki kusan minti biyu suna kallon kallo a tsakanin su kowa ya kasa furta komai,yayin da hawaye yake bin fuskar Khaleel da gudu,Aunty Kubra ce ta katse mutuwar ido biyun da suka yi ta hanyar rafka sallama a tsakar gidan.

Daga cikin parlour’n su Umma suka had’a baki wajen amsawa,Umma a jikinta taji kamar ta san muryar da ke sallama,hakan yasa ta taso ta d’aga labule don dubawa,a take gabanta yayi tsananin fad’uwa da k’arfi ganin Khaleel da Aunty Kubra a tsakar gidan su,da wani irin sauri ta fito jikinta na rawa ta zubawa Khaleel idanu cikin wani yanayi,da k’arfi kuma Umma ta ambaci sunan sa cikin wani yanayi.

“Ibraheem….!

kiran har k’wak’walwar Hidaya ya shiga,a take tayi sufa daga kan gado ta mik’e da hanzari tayo wajen window da gudu tana d’aga labule domin ganin tsakar gidan na su,jikinta babu in da baya rawa,tunda taji muryar Umma na ambatar Ibraheem to ta san Uncle Khaleel ne,take kuwa idanuwan ta suka nuna mata gaskiyar zance,Uncle Khaleel d’in ta ta gani ya juyo da hanzari yana d’aga k’afa da k’yar ya nufo Umma da ke tsaye tana duban sa,idanuwan Hidaya a kansa tana kallon wata muguwar rama da yayi ya dawo kamar tsinke,shauk’i ya d’ebeta,sai taji kamar ta shek’o da gudu ta afka k’irjinsa mai dad’i ta rungume shi,runtse idanuwa tayi tana sakin wani marayan kuka zuciyarta na harbawa.

Lokacin da Khaleel ya iso gaban Umma zubewa kawai yayi akan gwiwoyinsa,hawayensa na kwarara kamar an bud’e famfo,murya na karkarwa ya d’aga tafukan hannunsa ya had’e su guri d’aya yana rok’on Umma cikin kuka.

“Afuwan…Afuwan….Afuwan Umma…don Allah kiyi hak’uri…don darajar manzon Allah ( S A W) kiyi hak’uri Umma….

Abin da yake nanatawa kenan cikin kuka kamar ya shid’e,Umma ta rasa ma me zata ce,ta fito ne da niyyar b’atawa Khaleel rai,sai dai yadda ta ganshi gabad’aya ya gama karya mata zuciya,ji take tamkar ta fashe da kukan ita ma,Hidaya kam tsananin kukan da take yi tana kallon Khaleel tamkar ta shid’e,yanzu shikenan ita da shi sai gani sai hange daga nesa?wannan wace irin k’addara ce?”

D’aga labulen parlour’n aka yi,Mummy ta fito ita da Aunty Sajida cikin wani yanayi,a hankali ta zo gefen Umma ta dafata,Umma ta d’ago ta dubeta suka had’a idanu,sai Mummy tayi murmushi tace da Umma.

“Wannan shine Khaleel ko?D’an gidan MUDASSIR?”

Da hanzari Khaleel ya d’ago idanuwa ya dubi Mummy suka had’a idanu,gabansa yayi mugun fad’uwa da kallon da tayi masa,matsowa Mummy tayi gabansa tana kallonsa,cikin wani yanayi ta k’ura masa idanu ta ce.

“Khaleel ko…?ka san ko ni wacece kuwa?”

A hankali ya girgiza kai kafin ya maida kallonsa kan Hamza,shi kam Ya Hamza kansa a sunkuye yake,baima san halin da zuciyarsa take ciki ba,ya shagala da kallon Hamza a sanda yaji muryar Mummy na ce masa.

“Heyyyy…Ni za ka kalla ba GARKUWA ba,ni zan maka bayanin ko wacece ni ka fahimta ko?”

Dawo da kallonsa yayi kanta yana had’iyar zuciya,tun kafin ya san ko wacece k’irjinsa ke bugawa.

Murmushi tayi mai ciwo kafin ta ce.

“Wannan lokacin nake jira…kuma na san za ka zo daman…jiran da nake kenan domin na bayyana maka yadda Mahaifinka ya kashe Mahaifin Hidaya…daga nan ku bayyana gaban ALK’ALIYA domin tuhumar ku kai da mahaifinka ! yayin da zai fuskanci tuhuma akan kisan kan da yayi tsawon shekaru ! kai kuma za ka fuskanci tuhuma kan wulak’anta aure da cin zarafin Y’a mace! saboda haka ina mai farincikin shaida maka cewar ni ce MAHAIFIYAR HIDAYA WADDA TA HAIFE TA…!”

A gigice Khaleel da Aunty Kubra suka dubi Mummy cikin firgici,a dai dai lokacin kuma da ALHAJI MUDASSIR (DADDY) ya sako kan sa cikin tsakar gidan a firgice,dukkanin su suka waiwaya suna duban sa,babu wanda bai razana ba kaf cikin su,idanuwan Mummy suka yi arangama da bak’ar fuska! a take wani hawaye mai tsananin zafi suka zubowa Mummy,ta bud’e baki yana karkarwa ta ambaci sunan sa.

“MUDASSIR….!

A gigice Daddy yake kallon ta yana nuna ta hannu,cikin masifaffiyar firgita ya d’ora hannu a ka bakinsa na rawa da karkarwa yake duban Mummy kafin yayi magana a rarrabe.

“Ke….ke…ke ce…?da …daman….ki…kin…kina…nan…?”

Tana kuka amma sai da tayi murmushin takaici,sannan ta tsurawa Daddy idanu ta ce.

“K’warai ina nan Mudassir ! ban mutu ba kamar yadda ka kashe mijina! ni ma kuma kaso kasheni ni da y’ata amma Allah ya kub’utar da mu!

Ta maida kallonta kan Hamza da ke tsaye tamkar an dasa shi,ta girgiza kai hawaye na ambaliya ta ce.

“GARKUWA HAMZA yau za ka samu dukkanin amsoshin tambayoyin da kake min da kai da Hidaya,yau zan fito da ku cikin haske daga duhun da kuka afka! yau za ku san komai da ke b’oye! tabbas yau sirrin b’oye zai fito fili…..!

 

 

*RIGIJI GABJI*😳

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA TAMANIN DA UKU DA NA TAMANIN DA HUD’U

 

 

***Dukkansu zuba wa Mummy idanu suka yi,wasu na hawaye,yayin da wasu suke kukan zuci wanda yafi na fili ciwo da mak’ak’i a zuciya,Mummy ta juya a sanyaye ta shige cikin parlour’n Umma tana kuka sosai,yayin da d’aya bayan d’aya suka dinga rufa mata baya suna bin ta,babu wanda aka bari a tsakar gidan sai Daddy da ke sandare a tsaye cikin firgici da tsoro,sai kuma Aunty Kubra da ke kallonsa cikin wani yanayi mara fassaruwa.

A hankali ta taka har in da yake tsaye jikinsa na mugun rawa,k’ura masa idanuwa tayi tana kallon yadda jikinsa ke mazari,ga wani uban gumi da yake yanko masa kamar wanda ya had’iyi kunama ko maciji,wani murmushin takaici Aunty Kubra ta saki tana cigaba da kallonsa,a hankali ta nuna masa hanyar parlour’n Umma kafin ta bud’e baki cikin b’atacciyar murya ta ce.

“Ya kamata wannan zaman ya kasance har da kai aka yi shi,domin kai ma muna son jin abubuwa masu yawa daga gareka Alhaji Mudassir,dan haka wuce muje”

Kamar wata uwarsa haka ta bashi umarni! ba kuma yadda zaiyi dole yabi umarnin na ta,shi ma kuma yana buk’atar hakan a ransa,gara a warware komai ya zo k’arshe,ko da hakan na nufin zai bar duniyar gabad’aya ne.

A gaba Aunty Kubra ta saka shi har parlour’n Umma,suna shiga suka tarar kowa ya zauna,neman guri suka yi suma suka zauna,Daddy sai sab’a babbar riga yake yana share gumin da yake yanko masa,a lokacin ne kuma Hamza ya mik’e ya shige cikin bedroom d’in Umma domin fitowa da Hidaya,wadda sautin kukan da take fitarwa duk ya cika gidan,yana shiga shiga ya tarar da ita bakin window rik’e da k’arafan da ke jikin window d’in,waiwayowa tayi tana dubansa,tsayawa yayi kawai yana kallon yadda uban hawaye yake saraftu a fuskarta,tana ganinsa ta sake fashewa da wani irin kuka,sannan cikin rawar murya tace da shi.

“Ya Hamza wace irin rayuwa ce wannan?wace irin k’addara ce ke bibiyata?haka daman mutum yake ji idan wata k’addara ta same shi?Ya Hamza zuciyata za ta buga saboda k’uncin da yake damunta”

Takawa ya soma yi har ya isa gabanta in da take tsaye,hannu ya zura a aljihu ya fito da wani hankici me kyau da k’amshi ya mik’a mata,bin sa tayi da kallo tana ta faman kuka,girgiza mata kai yayi alamar ta karb’a ta share hawayen ta,a hankali ta mik’a hannu ta amsa,sannan ta fara share hawayen wasu na k’ok’arin fitowa,tana cikin sharewar tayi ya fara magana cikin murya me tsananin taushi da laushi.

“Ba zan fasa fad’a miki cewar kiyi hak’uri da k’addararki ba,sannan ki godewa Allah a bisa duk wata jarrabawa da zai yi miki,wasu suna nan da yawa a duniya jarrabawarsu tafi taki zafi,k’addararsu ta ninninka ta ki sau ba adadi amma sun yi hak’uri sun jure,saboda shi hak’uri tamkar wata madogara ce da babu yadda bawa ya iya dole sai ya dogara da shi,babu imani cikakke ga wanda ba shi da hak’uri Hidaya,bana son ki zamo daga cikin wasu irin mutane gafalallu,wad’anda lokacin da farinciki ya same su sai suyi ta murna,idan akasin hakan ya same su sai su juya baya,irin wad’annan mutanen Allah ya ambace su cikin littafinsa mai girma,cikin suratul hajji,in da ya ke ce wa.

“و من الناس من يعبد الله على حرف فإن أصابه خيراطمأن به وإن أصبته فتنة انقلب على وجھه خسرالدنياوالأخرة ذلك ھوالخسران المبين”

(Daga cikin mutane akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gab’a,idan alheri ya same shi sai ya gamsu da shi,idan kuma wata musiba ta same shi sai ya juya baya,to ya tab’e duniya da lahira,wannan ita ce hasara mabayyaniya).

“Shin Hidaya kina so kiyi hasara mabayyaniya ne?kina so ki zama cikin wad’anda suka tab’e?”

Da sauri ta girgiza kanta,sannan ta ce.

“Bana so Ya Hamza,kullum ina so na kasance mai godiya ga Allah ne,kuma mai hak’uri”

Yayi murmushi yana karb’an hankicinsa da ta kammala share hawayen ta da shi,sannan ya ce.

“Idan kuwa haka ne sai kin daina yawan kokawa a bisa k’addararki,sai kin zama Jaruma mai tawakkali,kuma sai kin k’arfafa zuciyar ki munje kinji abin da zai fito daga bakin mahaifiyarki a yanzu”

Jijjiga kai tayi cike da gamsuwa,ta juya ta d’auki Hijab d’in ta da ke gefen gado ta sanya,sannan Hamza yayi gaba,ita kuma ta biyo shi a baya cike da k’arfin zuciya.

Zuciyarta sai da taso sake karyewa,a yayin da idanuwan Uncle Khaleel suka shiga cikin na ta,da sauri ta sake aro jarumta ta afkawa ruhinta,tana son kallonsa amma haka ta kawar da kai ta samu gefe guda kusa da Aunty Sajida ta zauna kanta a sunkuye,yayin da take jin yadda idanuwan Uncle Khaleel ke mamaye ilahirin jikinta,wani irin kallo yake mata tamkar ya janyo ta jikinsa,sai dai inah! sama tayi wa yaro nisa!

Tsit kake jin Parlour’n babu motsin komai sai saukar numfashin mutanen da ke zazzaune,kowa da bitar da zuciyarsa take yi,sai da Mummy taga kowa ya nutsu,Sannan ta share hawayen ta tayi gyaran murya ta soma labarta musu labarin kamar haka.

 

 

 

 

***************

 

 

“Bani da k’warin gwiwar da zance zan tsawaita muku wannan labari a yanzu,zan bayyana muku shi ne a gajar ce,amma ta yadda kowa daga cikin ku zai iya fahimta.

” Suna na ZAINAB ,sunan mahaifina SANI. A wani lokaci mai tsawo da ya gabata,munyi aure ni da mahaifin Hidaya mai suna SULAIMAN,duk da kasancewar ba garin mu d’aya ba,ni y’ar garin (GOMBE STATE) ce,shi kuma yana garin (ABUJA),dalilin had’uwata da shi ya samo asali ne a lokacin da uban gidansa mai suna( TAUFIK’) ya turo shi garin mu domin ya duba wata ma’aikata,wadda yake son yayi irin ta ko mai kama da ita a Kaduna,saboda shi Taufik’ d’an kwangila ne,kuma mutum ne mai rik’o da gaskiya da amana,shiyasa yake samun kwangila sosai domin bashi da ha’inci da son zuciya a lamuran sa.

A ranar da na had’u da Sulaiman mun taso daga makarantar islamiyya ne,mun biyo ta jikin ma’aikatar da yazo takanas garin mu domin duba ta,a lokacin ne idanuwan sa suka yi arba da ni cikin shigar mutunci da kamala,nan take zuciyar Sulaiman ta afka cikin tsananin sona da k’aunata.

A daren ranar sai ga Sulaiman gidan mu,ya aiko yana sallama da ni,ban fita ba sai mahaifina ne ya fita domin ya ga wanene yake sallama da ni,domin ni ko zance bana yi duk da yawan masoyan da nake da su,cikin girmamawa Sulaiman ya gaida Babana,sannan ya shaidawa mahaifina wajena ya zo,sona yake yi,kuma shi aure na yake son yi,Babana ya tambaye shi yadda akayi ya sanni har ya zo gareni,sai ya shaida masa ya ganni ne d’azu da yammaci na dawo daga makaranta ,shine yayi tambaya akaina har aka kwatanta masa gidanmu shine yazo,Mahaifina yayi masa tambayoyi da dama kasancewar ya gane Sulaiman ba d’an gari ba ne,shi kuma Sulaiman yayi ta bashi amsa cikin ladabi da nutsuwa,nan Babana yace da shi ya tashi ya tafi,bayan kwana uku ya dawo.

Haka kuwa akayi,Babana bai min zancen ba ban ma san abin da ke faruwa ba,kawai bayan kwana uku sai ga Sulaiman ya sake zuwa,shi Babana ma ya manta da batun sa,kawai yace masa ya tafi ne a zaton sa ma ba dawowa zaiyi ba,ganinsa kamar ba aurena zaiyi ba,sai gashi Sulaiman yayi masa bazata ya dawo,kuma Sulaiman tun kwana biyu da suka shige ya kamata ya koma Abuja,amma ya kasa komawa saboda tsananin sona da ya kama shi,yana ji shifa yayi matar aure kawai.

A ranar ma Babana ce masa yayi akwai abin da yake yi,dan haka ya k’ara komawa bayan sati d’aya ya dawo,haka Sulaiman ya tafi duk da zuciyarsa babu dad’i,shi ko ganina ma abarshi yayi amma hakan ya gagara,kullum da tunanina yake kwana yake tashi,amma haka ya daure,ya k’ara share wuri ya zauna har tsawon sati d’aya,sai dai yayi wa Oga Taufik’ waya akan wasu matsaloli sun tare shi amma yana hanyar dawowa da zarar komai ya daidaita.

Sati na cika cif Sulaiman bai yi k’asa a gwiwa ba ya dawo gidan mu,Babana ya cika da mamaki,nan ya san cewar tabbas Sulaiman da gaske yake yi,haka nan daman yana ta istihara kan lamarina da Sulaiman d’in,sai yake jin abin ya kwanta masa sosai a ransa.

A ranar Babana ya bawa Sulaiman damar ganina,sosai hakan ya faranta ran Sulaiman,ya dinga yiwa Baba godiya da addu’a.

A ganina na farko da Sulaiman naji ya kwanta min a raina,saboda kana ganinsa kaga mutum mai addini da cikar kamala,munyi hira a lokacin duk da ban cika magana sosai ba,sai dai zantukan soyayya da k’auna da Sulaiman ya cika ni da su sun haskaka ruhina k’warai da gaske,take naji na afka kogin soyayyarsa ni ma.

In tak’aice muku daga wannan ranar sai Gombe ta zame wa Sulaiman gida,domin ba a cikakken sati sai yazo ya ganni,da Babana yaga zirga zirgar tayi yawa sai ya umarci Sulaiman da ya turo danginsa ayi maganar aure kawai,tunda mun aminta da junan mu,Sulaiman kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha don murna,sai dai kuma zuciyarsa cike take da tarin fargaba saboda k’alubalen da ke tattare da shi.

Haka ya samu Oga Taufik’ da maganar,nan take ya goya masa baya cikin murna da farinciki,saboda ba k’aramin so Oga Taufik’ yake wa Sulaiman ba,domin yaso ace yana da y’a mace,to da wallahi ita zai bawa Sulaiman ya aura,sai dai kash! shi Oga Taufik’ bai tab’a haihuwa ba,asali ma shi d’in ko mata bai da ita,duk wadda ya aura gudunsa take saboda baya haihuwa,duk da tarin dukiya da Allah yayi masa.

Sanda Oga Taufik’ yazo suka gana da Mahaifina kan lamarina ni da Sulaiman,Babana ya girgiza da jin batun da Oga Taufik’ d’in ya zo da shi,domin ya sanar da shi gaskiyar lamari akan Sulaiman babu b’oye b’oye,in da yake ce masa Sulaiman ba shi da kowa ! bai da iyaye,a gidan marayu ya d’akko shi ya raine shi har ya girma,saboda bai tab’a haihuwa ba,sannan ya sanar da shi cewar Sulaiman tun yana yaro suka yi had’ari shi da iyayen sa,cikin hukuncin Allah iyayen sa suka k’one k’urmus amma Sulaiman ko tabo bai samu ba,kamar cilloshi ma akayi daga motar,kuma an jima ana neman dangi da y’an uwan mahaifansa amma ba a samu ba,shine dalilin da hukuma ta bada shi a gidan marayu,sai daga baya Oga Taufik’ ya karb’e shi dalilin bai da d’a ko guda d’aya.

Wannan jawabi ya girgiza Babana,ya cewa Oga Taufik’ zaiyi nazari akan batun ya bashi sati biyu,Oga Taufik’ yayi godiya sosai ya bar Gombe ya koma Abuja,ya zayyanawa Sulaiman duk yadda suka yi da Babana,sannan ya dinga tausar sa akan duk sakamakon da ya fito to ya karb’a yayi hak’uri da shi,haka Sulaiman ya amsa,sannan ya dage da addu’a.

Mahaifina ya kira ni yayi shawara da ni akan maganar,na nuna masa ni dai ina son Sulaiman a haka,tun da dai musulmi ne,kuma an tabbatar iyayensa mutuwa suka yi ba wai jefar da shi akayi ba dalilin an same shi ta gurb’atacciyar hanya,jin hakan sai mahaifina ya goya min baya,duk da mahaifiyata ta so hanawa,amma da Babana ya zaunar da ita ya fad’akar da ita da maganganu masu dad’i sai ta amince ta sanya albarka a lamarin,sai dai tana ji a zuciyarta za ta yi kewata,saboda mu biyu kacal ta haifa,daga ni sai k’anwata Sajida,kuma ni ce babba,saboda suma iyayena Allah bai basu haihuwa da wuri ba.

Wannan shine tsanin Soyayyata da Sulaiman,kuma turbar da ta kaimu ga auren juna ni da shi,munyi aure na soyayya da k’auna,Sulaiman na sona nima ina son sa,cikin lokaci k’ank’ani komai ya kammala aka d’aura aure na da Sulaiman,aka kaini dank’areren gidan Oga Taufik’ da ke Abuja,wanda ya bamu part guda domin mu zauna ni da Sulaiman,kuma ya k’awata mana ko ina da kayan more rayuwa da kayan cima kala kala.

Mun yi zaman aure mai tsananin dad’i da nagarta ni da Sulaiman,baya son b’acin raina ko kad’an,yayin da nake masa ladabi da biyayya sosai da sosai,haka nan ina tsananin girma ma Oga Taufik’ wanda muke kiransa da (ABBA) ni da mijina,ko abinci zan dafa tare da shi nake dafawa na zuba Sulaiman ya kai masa,da farko ma Oga Taufik’ cewa yayi in daina wahalar da kaina ina dafa masa abinci,amma nak’i dainawa,saboda ni a uban miji na d’auke shi,uban miji kuwa kamata yayi ka kyautata masa yadda za ka kyautatawa naka mahaifin,kullum Oga Taufik’ saka mun albarka yake ni da mijina,ya kan ce muna wawashe masa takaicinsa na rashin haihuwar da baiyi ba,a kullum kuma Sulaiman bai fasa rok’on Oga Taufik’ akan yayi aure ba,ya kan ce “Abba don Allah kayi aure,zaman ka haka babu dad’i” sai Oga Taufik’ yayi murmushi ya ce,”Sulaiman kenan! tunda dai kai kayi ai shikenan,ni bana sha’awar yin auren ne,babu wacce za ta zauna dani ta san bana haihuwa,ni mata ma tsoro suke bani wallahi,duk wadda zata aureni yanzu sai dai ta aureni don dukiyata amma ba don soyayya ba”

Sulaiman ya sha zuwa yace min shifa yana so Abban sa yayi aure,sai in yi murmushi in ce”Idan da rabo zai yi”.

Haka rayuwar mu ta kasance cikin jin dad’i,duk wata hidima ta Oga Taufik’ a hannun Sulaiman take,babu wanda ya san sirrin Oga Taufik’ sama da mijina Sulaiman,haka nan babu mutumin da Sulaiman ya fi so a duniya irin Oga Taufik’,domin ko hira nake ni da shi bai da zance sai na Abban sa da yabon sa,ya kan rok’e ni akan nima na cigaba da girmama masa Abban sa da yi masa hidima.

Wata ranar Asabar lokacin watan mu shida da aure,ina kwance ina baccin rana saboda yadda nake jin kasala sosai a jikina,sakamakon shigar ciki k’arami da na samu,sai ga Sulaiman ya dawo gida katsahan,ina d’an baccina amma sai da ya tasheni da wasannin sa ya wartsakar da ni,sai da na wanko idanuwana a toilet na dawo gare shi sannan nake tambayar sa me ya dawo da shi gida a dai dai wannan lokacin?

Sai yake ce min “Zainab Abbana ne zaiyi bak’i abokanan aikin kwangilar sa,kuma gida za su zo su ziyarce shi,shine ya ce min in je restaurant in siyo musu abinci da abubuwan sha da za a tarbe su da su,ni kuma sai nake ganin tunda gaki ai babu abin da ba zaki iya ba,yanzu so nake ki tashi muje ktcheen muyi girki kala kala domin mu fitar da abbana kunya ko?”

Jijjiga kai nayi ina murmushi,duk da ko ktcheen din bana son dosa saboda abin da ke cikina baya son k’amshin ktcheen,amma haka na daure muka shiga ni da Sulaiman muka fara harhad’a abubuwan da zamu buk’ata,nan da nan muka fara girki Sulaiman na tayani da yanka abubuwa,yana ta min dariya ganin nasa yanki na d’aure hancina dalilin bana son k’amshin abincin,a haka har muka kammala,Sulaiman na ta azalzalata wai muyi sauri saboda bak’in daga Kaduna za su tawo,kuma yanzu dab suke da isowa.

Ko awa d’aya bamu yi da kammalawa ba sai ga Abba yayi wa Sulaiman waya kan cewa bak’in fa sun iso,ganin kayan da yawa sai Sulaiman ya umarceni da na sanya hijabina na tayashi d’aukar wasu kayan domin mu kai,haka kuwa akayi,ya d’auki basket d’in da na jera abinci,ni kuma na d’auki wanda na jera drink da su ruwa,muka nufi sashen Oga Taufik’ (Abba).

Bak’in su biyu ne kacal,har k’asa na durk’usa na gaishe su,Abba yana ta fara’a yana nuna musu ni a matsayin surukarsa matar d’an sa,ganin abincin da yawa kala kala nan Abba ya fahimci ni ce na girka,nan ya dinga yiwa Sulaiman fad’a wai ya wahalar da ni,shi dai Sulaiman dariya yake kawai,Abba ya min godiya sosai,abokanan sa ma suka yi min godiya,wad’anda na rik’e sunan su sosai a raina,lokacin da naji Abba na fad’awa Sulaiman sunan su,wato ALHAJI MUDASSIR DA ALHAJI MAUDE.

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA TAMANIN DA BIYAR DA NA TAMANIN DA SHIDA

 

 

***Mummy ta cigaba da ba su labari da ce wa.

“Wannan shine gani na na farko ga Alhaji Mudassir,da kuma aminisa mai suna Alhaji Maude,wad’anda dukkansu y’an kwangila ne,kuma sun zo wajen Oga Taufik’ ne domin ya bud’a musu hanya,su cigaba da samun kwangilolin da za su samu kud’i sosai.

Zama mai dad’i da armashi ya cigaba da wanzuwa tsakani na da mijina,har zuwa lokacin da Allah ya saukeni lafiya na haifi d’iya ta mace,wato Fad’imatul Hidaya,zan iya ce muku Oga Taufik’ ya fimu farinciki da murnar samun wannan haihuwa,shine yayi komai da ake wa mai jego da jaririya,gata dai mun sha shi fiye da in da bakwa zato,kyautattuka kuwa Oga Taufik’ yayi mana su har sai da muka gaji da amsa,saboda shi yana da yawan kyauta da sadaka,haka nan duk lokacin da zai fitar da zakka yana yin ta yadda Allah yake so,shiyasa arzik’in sa yake hab’aka kullu yaumin.

Sai da Hidaya tayi wata shida sannan muka san ita sikila ce,wani dare da ta dinga kuka ta hanamu barci,musamman idan na tab’a k’afarta sai ta tsandare da ihu,hankalin mu ya tashi,washe gari kuwa da wurwuri muka nufi asibiti da ita,anan aka yi mata gwaje gwaje,daga baya aka sanar da mu cewar ita d’in sikila ce.

Muka shiga tashin hankali,saboda mun sani lalurar sikila babban ciwo ne mai matuk’ar wahala,amma da muka yi tunani muka ga ai Allah ne mai d’ora cuta kuma shine mai yaye wa,kuma ba kanta farau ba haka nan ba kanta k’arau ba,sai muka fallawa Allah kawai,muka shiga addu’a da nemar mata magani.

Wata rana muna zaune ni da Hidayan,lokacin shekarar ta biyu har da watanni,tuni bakinta ya bud’e ta fara magana,shiyasa na zaunar da ita ina koya mata karatun Suratul Fatihatul kitabi,nan da nan naga tana d’aukewa,hakan ya faranta raina Allah Allah nake Abbanta ya dawo na bashi labarin Hidaya ta iya karatu.

Da ya dawo sai na lura da ba shi da walwala sosai,sai naji hankali na ya tashi,nayi masa dukkan abin da ya kamata nayi masa,abinci ma kad’an ya ci yace min ya k’oshi,na d’auke na mayar ktcheen,ina dawowa sai na tarar suna ta labari shi da Hidaya yana dariya,na zo na zauna gefen su ina kallon sa,sai ya waiwayo ya kalleni da murmushi kan fuskarsa yana d’ora Hidaya kan cinyarsa ya ce da ni.

“Mummyn Hidaya yaushe Hidayana ta fara iya karatu baki min albishir ba?”

Ni ma nayi murmushi na langab’e wuya nace.

“Ina ta so ka dawo na fad’a maka,to kuma na ganka ba yadda na saba ganinka ba shiyasa nayi shiru da bakina dan kar na dame ka”

Ya girgiza kai yace min.

“Ai wannan abun farinciki ne bai kamata ki b’oye min ba,bakiji yanda naji dad’i ba wallahi,ai gobe zanwa Abba albishir cewa amaryarsa ta iya karatun alk’ur’ani”

Nayi dariya kawai,yayin da ya cigaba da kallon Hidaya yana fad’in”Princess d’ina sake karanta min in ji”

Ita kuwa ta tak’ark’are tana karanta masa Fatiha,shi kam yana ta jin dad’i.

Sai dare da muka zo kwanciya nake tambayar sa dalilin canjawar yanayin sa d’azu,da dai kamar ba zai fad’a min ba sai kuma ya janyoni jikinsa sosai yana gyara min kwanciya,sannan yayi ajiyar zuciya ya ce da ni.

“Wato a rayuwa wasu mutanen ba sa tsoron Allah Zainab,ha’inci da son zuciya yayi wa wasu katutu a zuciya,rashin imani ya yawaita,d’azu Abbana ya kirani,da naje sai na iske shi cikin damuwa,shine hankalina ya tashi na tambaye shi damuwarsa,sai yake shaida min cewar akwai aminan sa guda biyu da suke harkar kwangila da su,ina jin ma ai kin san su,wad’anda suka tab’a zuwa nan gidan lokacin kina da cikin Hidaya har kika yi musu girki,to shine fa yake shaida min cewar baya jin dad’in aiki da su,saboda suna da son zuciya,yana nemo musu kwangiloli ya basu saboda ya fisu hanyoyi na samun kwangiloli ko a wajen gwamnati ma,to amma duk lokacin da hakan ya faru ba sa yin aiki da gaskiya,ayyukansu ba sa yin k’arko,su kan fi maida hankali akan abinda za su samu fiye da aikin da za su yi,yace min a kwanakin nan ya sama musu wata kwangila daga gwamnati mai tsoka,duk don ya kyautata musu ya hana kansa ya ba su,kuma ya rok’e su suyi aiki mai nagarta,amma basu yi hakan ba,kwata kwata a kud’in da aka basu ko kaso goma cikin d’ari basu kashe ba,su dai burin su su azurta kan su ba suyi aiki mai kyau ba,Abba yace min hakan sai da ya janyo masa matsaloli daga gwamnati,shine yake neman shawarata akan ko dai ya daina nemo musu kwangiloli ta b’angaren sa,ya barsu su nema da kansu,ni kam take na bashi shawarar cewar hakan ne ya kamata,kawai ya daina nema musu tunda sun cika zuciyarsu da mugunta,kuma yayi musu gargad’i sau ba adadi amma sun k’i dainawa,take Abba ya amince da shawara ta,yace min zai kira su gobe ya fad’a musu abin da ya yanke a kansu”

“To kinji dalilin b’acin raina har na dawo gida,saboda ni bana son huld’a da irin wad’annan mutanen da basu san kowa ba sai kansu,gara Abba ya fita sabgarsu saboda kar su dinga janyo masa zargi da b’atanci gun jama’a da abokan huld’ar sa”

Ajiyar zuciya na sauke mai k’arfi,ina jinjina maganar a raina,tabbas gara Abba ya fita harkar su,tunda ba za su gyaru ba,nan na cigaba da kwantarwa da mijina hankali,har bacci yayi nasarar d’auke mu mai dad’i.

 

 

 

*****************

 

Lokacin da Abba ya kirawo Alhaji Mudassir da Alhaji Maude sun tsorata da jin batun sa,domin sun san kusan shine silar arzik’in su,ya bud’a musu sosai a harkokin su,hakan ya sa suka rud’e suka gigice,suka rasa yadda za su yi,nan sukai ta rok’on Abba akan ya basu dama ta k’arshe in sha Allahu za su gyara.

Da yake Abban yana son cigabansu sai ya hak’ura,ya sake basu dama suka cigaba da harkokin su,sosai suke samun kud’i mai yawa,Abba ya fad’awa Sulaiman cewar sun rok’i a basu dama ta k’arshe kuma ya basu,Sulaiman yace shikenan babu damuwa Allah ya sa su rik’e alk’awari.

Tafi tafi aka cigaba da buga harka,har Hidaya ta fara girma ta kai shekaru biyar kan ta shida,don har an sakata a school,kuma ta tashi da basira sosai,gashi mun yi sa’a lalurarta bata cika tashi sosai ba,saboda Oga Taufik’ yana k’ok’ari wajen siya mata magani akan kari,d’awainiya yake da Hidaya sosai,haka nan son da yake wa Sulaiman shine ya shafi Hidaya.

Ba zan manta wata rana da Hidaya ta zo na d’aya ba lokacin da suka yi exam,Abba dan murna sark’ar gwal ya siya mata,ni ma kuma ya siya min dank’areriya mai kyau,yace saboda ni na d’ora Hidayan akan turba ta gari,ni ce nayi mata foundation mai kyau har take k’ok’ari a makaran ta.

Ana cikin hakan kawai watarana muna zaune sai Abba ya kira Sulaiman,da hanzari ya tafi amsa kiran,da ya dawo min gabad’aya ransa a jagule yana ta masifa har na tsorata,saboda na san Sulaiman yana da hak’uri bai cika fushi ba,da k’yar ma ya sanar da ni cewar ai abokan Abba ne halin tsiyarsu ya motsa,sun aikatawa Abban babban laifi,kuma daman ai ance mai hali baya fasa halin sa.

Nan na tattaushe shi na kwantar masa da hankalu,sai yake ce min shidai ya fad’awa Abban sunyi na farko kuma na k’arshe,ba za a sake basu wata dama ba kuma.

An yi hakan da kwana biyu sai Sulaiman yake bani labarin wai sun same shi har office d’in sa,wato Alhaji Mudassir da Alhaji Mauden,akan ya lallab’a Oga Taufik’ ya basu wata damar,saboda sunga shine mashawarci a gareshi,shine na kusa da shi sosai,take Sulaiman yak’i yarda da batun su,yace ba ruwansa ba zai saka baki ba,domin dai suna cutar da Abban sa saboda sunga yana da hak’uri,shine fa sukai fushi suka dinga zagin Sulaiman d’in suna aibata shi,suna ce masa matsiyaci d’an tsuntuwa wanda bai gaji arzik’i ba,sun so su had’a kaine yadda za su bawa Sulaiman kud’i mai yawa dan a cuci Abba,amma Sulaiman ya gaza hakan ya fatattakesu duk da sun girme masa,take Alhaji Mudassir ya furta wata magana cikin fushi,domin cewa yayi.

“Kai Sulaiman baka isa ka ja damu ba,ko shi marik’in naka yayi kad’an balle kai k’aramin k’waro wanda bashi da ko sisi,kuma mu zuba da kai mu gani,wallahi sai munga bayanka daga kai har uban gidan naka tunda ka ja da mu”

Tunda Sulaiman ya bani wannan labari sai na kasa nutsuwa,tsoro ya cika raina fal,har ma Sulaiman d’in ya dinga mun dariya wai na cika tsoro,babu abinda zai faru basu isa suyi komai ba,mu dogara ga Allah kawai.

Da naji haka sai na share batun,washe gari aka yo min waya daga gida Mahaifina ba lafiya,hanakali na a tashe na tafi GOMBE,ni da Hidaya babu Sulaiman,saboda aiki yayi masa waya yace min zai zo daga baya ko nan da kwana biyu ne ya duba Babana,da naje ma sai na tarar Baban ya samu k’warin jiki sosai,ya dinga murnar ganina da y’ar jikar sa.

Kwanana biyu ina ta jiran Sulaiman shiru bai zo ba,sai gashi ya kirani a waya wai in yi hak’uri aiki ne ya masa yawa,ya nemi in bashi Baba a waya na bashi suka gaisa,yayi masa ya jiki tare da bayar da hak’urin rashin zuwan sa,Baba yace babu komai ai ya ji sauk’i ba sai ya zo ba,sannan yayi masa godiyar d’awainiyar da yake da su,haka nan yace a yiwa Oga Taufik’ godiya ma .

Washe gari sai Baba yace na haad’a komatsaina na koma d’akina bai ga amfanin zamana ba na bar mijina shi kad’ai,ba da son raina ba na kama shirin tafiya,Babana ya zaunar dani ya dinga min nasiha kan zaman aure da biyayya wa miji,yace in yi hak’uri zan ci riba,haka Ummana ma tai tayi min Nasiha,na nemi ta bani Sajida mu tafi tayi min hutu amma Ummana ta k’i,tace min in bar mata d’iyar ta tunda gashi nan ni ma na samu tawa,ba zai yiwu in had’a biyu in barta ba ko d’aya ba,tilas haka na hak’ura nayi sallama da su cikin yanayi mara dad’i da kewarsu,na bar Gombe na dawo Abuja.

Kwatsam kawai sai ganina Sulaiman yayi,ya sha mamaki sosai saboda baiyi tunanin zan dawo kusa ba,nace masa ai Baba ne ya koroni,ya dinga dariya yana shiwa Baba albarka,wai Baba yayi masa dai dai daman kewarmu yake ni da Hidayan sa,a ranar har b’angaren Abba naje na gaishe shi tare da kai masa tsarabar Gombe,Abba ya dinga murnar ganinmu tare da sa albarka,ni dai nan na fito ma na bar Hidaya a wajen sa tana ta ba shi labarin Gombe yana dariya.

A washe gari kawai sai muka tashi Abba ba lafiya,babu k’afa babu baki babu ido,ma’ana baya iya tafiya,haka nan baya gani kuma baya magana,ya zama dunkun dukumanu,batun tashin hankali ma baki yayi kad’an wajen zayyana shi,a haka muka kwashe shi zuwa asibiti,duk wani gwaje gwaje an masa amma aka kasa gano lalurar da take damun sa balle a bashi magani,sai uban drip da kullum suke sanya masa.

Abba duk ya rame saboda wahalar da yake sha,shi kansa Sulaiman yayi bala’in rama,kullum cikin kuka yake da neman hanyoyin da zai nemarwa Abba magani amma an rasa,tunaninsa gabad’aya ya toshe ya rasa mafita.

A haka aka sallami Abba daga asibiti muka dawo gida babu wani cigaba,da muka dawo ne ma hankalina ya kai kan in dinga karanta masa alk’ur’ani da ayoyin karya sammu ko sihiri,take kuwa muka fara ganin alfanun abun,domin idanuwan Abba sun bud’e yana gani,sai dai ba magana,amma yana iya motsi har ya karb’i abinci me d’an ruwa ruwa.

Wata rana da ba zan manta da ita ba muna zaune muna karantawa Abba alk’ur’ani,da ni da Sulaiman,sai Hidaya ma ta zo ta zauna ta na karatun,Abba yaji dad’i sosai har ya dinga hawayen jin dad’i,sai da muka kammala sannan ya d’ago hannun sa ya kirawo Sulaiman,Sulaiman ya tashi ya je gareshi,ba bakin magana amma haka ya dinga nunawa Sulaiman godiyarsa gare mu,sannan ya nunawa Sulaiman wata akwatu y,ya nunar masa ya d’auko masa ita.

Sulaiman ya d’auko ya kai masa,sannan ya d’aga shi ya jingina da gadon,sai ya nuna wa Sulaiman yadda ake bud’ewa ya umarce shi kan ya bud’e masa,take kuwa Sulaiman ya bud’e,sai ga tarin takardu kala kala sun bayyana.
Takardun filaye ne da na gidaje,da dai kadarori da dama,ya raba su gida uku,sannan ya umarci Sulaiman da ya bashi biro da takarda zaiyi rubutu.

Sulaiman ya tashi ya binkito takarda da biro ya kawo,shine ya rik’ewa Abban hannu yayi rubutu saboda yadda jikinsa yake wani irin rawa,Abba yayi rubutu kamar haka.

*D’ana wannan sune kadarorin da na mallaka,ka sani cewar ni ma maraya ne mara uwa da uba tamkar kai,bani da d’a haka nan bani da jika,haka nan bani da d’an uwa na kusa sai y’an uwa na nesa,to ga dukiyata nan na rabata gida uku,ka d’auki kaso d’aya na mallaka maka,kaso d’aya kuma a bawa dangina na nesa,ragowar kaso d’ayan kuma a rabawa mabuk’ata wato marasa k’arfi ko kuma marayu,saboda ni na san tawa ta zo k’arshe,na bar wannan wasiyya ne saboda inaji a jikina mutuwa zanyi*

Da Abba ya gama rubutun sai yayi wa Sulaiman alamar ya karanta,Sulaiman yana karantawa sai ya fashe da kuka,hawaye yayi ta malala akan fuskar sa,na matso ina tambayar sa abin da ya faru,sai ya mik’o min wannan takarda nima na karanta,sai nima na fashe da kuka,mukai ta kuka Abba na girgiza mana kai alamar mu daina kuka,yana ta shafa kan Sulaiman,kuma shima hawayen yake yi.

Da dare yayi sai Sulaiman ya umarceni akan in tafi part d’in mu ni da Hidaya mu kwanta,shi zai zauna wajen Abba domin ya kwana da shi,haka kuwa aka yi,na d’auki Hidaya muka wuce sashen mu,kafin mu tafi ma sai da Abban ya nemi in kawo masa Hidayan gabansa,da na kai masa ita ya d’ora hannu a kanta yayi shiru alamar addu’a yake mata,sai da ya kammala sannan yayi min nuni da na d’auketa,haka na d’uketa jiki a salub’e muka bar sashen na sa.

Cikin dare wajen k’arfe d’aya da rabi Sai ciwon k’afa da k’irji ya hana Hidaya bacci,tai ta kuka har tana shirin fita daga hayyacin ta,hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi,ina tsoron fita in nufi sashen Abba a wannan daren,tilas na janyo waya ta na kira Sulaiman ina kuka na shaida masa halin da muke ciki,nan take Sulaiman yace min gashi nan yanzu zai zo tunda Abba ya samu bacci.

Can kuwa sai gashi ya fad’o d’akin a rud’e,ya zo ya karb’i Hidaya daga hannuna,ya tambayeni na bata magani?cikin rud’ewa na girgiza kaina alamar ban bata ba,saboda gabad’aya na rud’e ma,ya umarce ni naje na d’auko na kawo masa,ya bata maganin ina kallo tana ta kuka tana cewa”Abbana k’afa na ciwo zata cire”lallashinta ya dinga yi cike da tausayawa,bayan tasha maganin sai ya dinga yi mata addu’a yana shafawa a k’afar ta ta,cikin ikon Allah sai ta samu salama har bacci ya kwashe ta a jikinsa,lumshe idanu yayi ya jingina da allon gado yana shafa bayanta,a haka baiyi aune ba kawai sai bacci ya kwashe shi shima,saboda a kwanakin baya samun bacci dalilin lalurar Abba,ni kuma ganin yayi bacci sai na kasa tashin sa ya koma gun Abba,a ganina gara na barshi ya d’an huta ya rama baccin da bai samu ba a kwanakin,nima rab’awa nayi gefen su na kwanta,nan da nan nima baccin ya kwashe ni.

Kiran assalatu ne ya tayar da mu,Sulaiman ya farka yana salati sannan ya dube ni yana tambayata wai ya akayi har bacci ya kwashe shi anan?bai koma wajen Abba ba?bai ma tsaya jiran amsawa ta ba ya mik’e yana kwantar da Hidaya gefe guda sannan ya fice daga d’akin da sauri ya nufi sashen Abba.

Har na shiga toilet zan d’auro alwala kawai naji dawowar Sulaiman a firgice yana k’wala min kira,da hanzari na fito a lokacin har Hidaya ta farka a firgice saboda k’arar muryarsa ta razanata,nan da nan ta fashe da kuka,bai bi ta kan Hidayan ba ya nufo ni a gigice yana fad’a min wai yaje sashen Abba amma bai ganshi ba,baya in da ya barshi a kwance,kuma shi dai ya san Abba ba iya mik’ewa yake ba balle ace tashi yayi da kansa,kuma duk ya duba sashen amma ko mai kama da shi bai gani ba,nan da nan nima na rud’e,muka fita muka fara binciken gidan a wannan asubar,amma duk in da muke tunanin ganin Oga Taufik’ bamu ganshi ba,sai gashi muna kuka da idanuwan mu duk mun firgice,musamman Sulaiman da kamar yayi hauka dan rud’ewa da gigicewar da yayi,sai nice ma nace ya kamata muje wajen mai gadin get d’in gidan mu tambaye shi ko ya san abin da ya faru,da gudu Sulaiman ya kwasa yayi bakin get,yayin da na rufa masa baya,muna zuwa muka ga mai gadin a sheme a k’asa a sume,ga kuma alamun duka nan a gefen fuskar sa,ga kuma get a bud’e han hai,wani irin tashin hankali ya rufto mana da bamu tab’a tsammani ba,shikenan shigowa akayi aka sace Oga Taufik’ kenan?kafin ka ce me Sulaiman ya fad’i ya suma,Zuwa wayewar gari kuwa tuni zan ce ya cika gari cewar an nemi Oga Taufik’ an rasa,ma’ana dai ba a san in da yake ba.😭

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

BABI NA TAMANIN DA BAKWAI DA NA TAMANIN DA TAKWAS

*SADAUKARWA GA* 👇

SA’ADATU TIJJANI D’AHEER
RUMAISA GWARZO
AMEERA ABUBAKAR
KADIJA D’ANGUDE
SAFIYA UBA WADA
NANA AISHA
MOMYN IFFAH
SADIYA Y’AR AMANA
FA’IZA GOMBE

DA SAURAN SU

*Kuna bawa GARKUWA BIYU Hak’k’insa na Sharhi yadda ya kamata,godiya nake muku tare da Jinjina*🥰🤝👍

 

 

***Gida ya cika taf da mutane y’an jaje,haka nan ga police da suka zo bincike akan lamarin,kuma sunyi wa mai gadi tambayoyi sosai bayan ya dawo hayyacinsa,in da ya sanar da su cewar shi dai bai san komai ba,abin da ya sani shine, Ya kulle get kuma ya dawo wajen zamansa ya zauna,can gyangyad’i ya fara d’ibansa yaji alamun kamar ana bud’e get d’in ta waje da mukulli,da sauri ya zabura ya mik’e ya nufi bakin get d’in,sai ya lura ashe bai sa sakata ba,ya kai hannu kenan zai sa sakatar kawai yaji an turo k’ofar get d’in da k’arfin tsiya an doka masa ita a fuska,yayi baya ya fad’i,wasu mutane suka shigo da bai tantance ko su wanene ba,suka murk’usheshi suka shak’a masa wata hoda da ta fitar da shi daga hayyacinsa take ya suma,daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba har zuwa safiya da ya farka yaji ana batun ba a ga Oga Taufik’ ba.

Mai gadi yana bayani yana kuka da sharar hawaye,y’an sanda suka d’auki bayanansa sannan suka zo kan Sulaiman shima,da farko ma kasa magana yayi saboda halin da yake ciki,duk wanda yaga Sulaiman a lokacin dole ya tausaya masa,yayi kuka yayi kuka har hawayensa ya k’afe,burinsa yaga Abbansa kawai,abinda yake dad’a tayar masa da hankali rashin sanin wane hali Abban yake a halin yanzu,da k’yar ya iya bud’e baki yayi wa y’an sanda bayanin da suke so,bayan haka y’an sanda sun dudduba gidan tare da d’aukar bayanin komai da komai,sannan suka ce mu jira su za su gudanar da bincike kuma in sha Allahu za a dace.

Sai yamma lik’is y’an jaje sun fara bajewa sai ga Alhaji Mudassir da Alhaji Maude a gigice sun zo,suka samu a gaba har da kukansu na munafunci,suna tsinewa duk wanda wa sace Oga Taufik’,shi dai Sulaiman ko kallonsu bai yi ba ma har suka gama maganganunsu na rainin hankali,sai kuma suka koma yiwa Sulaiman yarfe,wai da alamun tambaya a kansa,saboda shine yake kula da shi har ya kwana da shi,to yana ina har hakan ta faru?to in ma shi ya b’atar da Oga Taufik’ dan ya cinye dukiyarsa to yayi gaggawar fitowa da shi,in ba haka zai fuskanci masifa da bala’i a rayuwar sa,Ina zaune a gefen Sulaiman ina jin duk cin mutuncin da suke masa,hawaye na zubar mana ni da Sulaiman amma basu daina ba,haka suka gama rashin mutuncinsu sannan suka mik’e suka fice suna ta yab’awa Sulaiman bak’ak’en maganganu.

Sai da suka fita sannan Sulaiman ya mik’e da hanzari zai bi su,na mik’e na rik’e shi ina had’ashi da girman Allah akan ya rabu da su ya tura musu aniyarsu,amma Sulaiman ya fizge jikinsa daga nawa,ya dubeni a haukace yace min.

“Zainab wallahi ba zan k’yalesu ba,basu isa suci bulus ba,sai na bisu na mayar musu da amsoshin maganganun da suka yi a kaina”

Ina ji ina gani Sulaiman ya fice ya barni a gun a tsaye,yana fita ya hango su sun nufi motar su za su shiga sai shewa suke yi suna tafawa,Alhaji Mudassira na cewa.

“Wai shikenan Maude kana nufin mun gama da babin Taufik’ kenan?”

Alhaji Maude ya k’yalk’yale da dariya ya ce.

“K’warai kuwa Mudan,har duniya ta nad’e ba za a sake jin d’uriyar Taufik’ ba,saboda kurciya me dogon zango na sa akayi masa”

Suka sake kwashewa da wata mahaukaciyar dariya,shi kam Sulaiman ilahirin jikinsa rawa yake da jin zantukan su,daman yana zargin su! gashi kuwa zarginsa ya tabbata daga jin kalaman da suke furtawa,hannu ya sa aka ya rafka wani salati tare da ambatar”Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”.

A gigice suka waiwayo suka zubawa Sulaiman ido ganinsa a bayansu,domin su basu ma san yana bayansu ba,kuma sun tabbatar yaji duk maganganun da suka furta,matsanancin tsoro ne ya kamasu,suka fara waige waige dan ganin ko wani yaji maganarsu bayan Sulaiman,ganin babu kowa a wajen sai suka saki ajiyar zuciya suka fad’a motar su suka fizgeta suka bar harabar gidan,suka bar Sulaiman tsaye a wajen a sandare yana zubar da hawaye.

Shiru shiru bai shigoba hakan yasa na biyo shi dan ganin meke faruwa,tunda na ganshi yana kuka naji hankalina ya tashi,jansa nayi har cikin gida na zaunar da shi,na rik’e hannayensa a rud’e ina ta tambayar sa dalilin kukan da yake,Sulaiman ya kasa magana,illa jikina da ya fad’o ya dinga wani irin kuka kamar zai had’iyi zuciya,ganin halin da yake ciki ban san lokacin da nima na fashe da kukan ba,Hidaya ma ganin muna Kuka sai ita ma ta zo ta rungume mu ta fara kukan,haka muka kasance cikin kuka babu mai rarrashin wani a cikin mu.

Sai dare sannan na samu Sulaiman ya fara nutsuwa,shima sai da muka d’auki alk’ur’ani ni da Hidaya muka dinga karantawa,har muka kammala,lokacin ne ya janyo Hidaya jikinsa yana jin dad’i ya dinga sanya mata albarka,Hidaya kuma ganin Abban ta ya fara warewa sai ta shiga yi masa surutu da tambayoyi irin na yarinta,har ya dinga murmushi yana tambayat wai yanzu shekarar Hidayan nawa?take na bashi amsa da cewar ta shiga shekara ta takwas a wannan watan.

Sai da Hidaya tayi bacci sannan Sulaiman ya iya fad’a min abinda yaji su Alhaji Mudassir suke tattaunawa akai,take hankalina nima ya tashi,nace yanzu menene abinyi?Sulaiman ya ce min.

“Gobe zan kai wa y’an sanda report akan abinda naji,duk da dai bani da wata sheda akan hakan,amma na tabbatar idan suka tsaurara bincike za su tarar da abinda nake gaya musu,Zainab wallahi tunda Abba ya fara rashin lafiyar nan nake zargin mutanen nan,ashe kuwa sune azzaluman da suka aikata komai,shin daman Zainab a duniya sakamakon alkairi da sharri mutane suke saka shi?babu abinda Abba bai wa mutanennan na kyautatawa ba,amma ga da abin da suka saka masa,lallai na yarda d’an adam butulu ne Zainab,kuma sharrin mutum yafi na sharrin tsohuwar mota,amma in sha Allahu k’arshen zaluncinsu ya zo,gobe da wurwuri zan tafi police station na kai report d’in su”.

Ni dai azabar mamaki ta cikani,lallai mutum mugun ice ne,sharrin mutum na da yawa,haka muka dinga tattaunawa da Sulaiman a daren nan,har za mu kwanta bacci ma sai naga ya mik’e,ya tafi ya d’auko wannan jakar da Abba ya bashi mai d’auke da kadarorinsa,dawowa yayi ya dank’amin jakar,sannan yace min.

“Zainab ki ajiye wannan jakar a hannunki,ki kula da ita sosai,na zab’i in damk’a miki ne saboda ni na san rayuwata za ta iya shiga garari a hannun wad’annan azzaluman mutanen,duk da Allah ya fi su,amma dai gara ki barta a gunki ki kula da ita sosai,na san duk wani abu da suke hank’oro ba zai wuce dukiyar Abbana ba,kuma babu rabonsu a cikinta,domin bai ambace su cikin wad’anda za a raba da su ba”

karb’a nayi ina jinjina batunsa,yace min in tashi in je in yi mata b’oyo na musamman,haka na tashi jikina a salub’e,shima sai naga ya tashi ya fice zuwa d’akin sa wai zaiyi wanka zafi yake ji.

Da na shiga bedroom d’ina sai na rasa in da zan b’oye wannan jakar,nai ta kallen wurare da dama a d’akin amma na rasa inda zan saka ta,duk inda idona ya kai sai naga ai jakar bata dace da wurin ba,a hankali sai naja jiki na nufi Vantlation d’in cikin d’aki na jakar na hannuna,ina zuwa na tsaya ina kallon k’asan gurin,siminti ne shimfid’e a wurin ba tayel ba,kawai sai naji zuciyata ta amince da gurin a matsayin in da zan b’oye jakar.

Ajiye jakar nayi na fita na koma store d’in mu na d’akko guduma,sannan na tawo da ruwa a kofi,sai na dawo na kulle d’akin na wuce Vantlation d’in,tsugunawa nayi daga gefe nasa guduma na fara fasa k’asan gurin sosai da k’arfi,sai da naga yayi rami sosai nasa hannu na fito da k’asar wajen,sannan na saka wannan jakar tayi dai dai a wajen,sai kuma na mayan da k’asar na dandab’e,nasa ruwa na k’ara dandab’ewa,ma’ana na binne jakar kenan,da na gama komai sai na janyo k’ofar vantlation d’in na kulle,na nufi toilet na wanke hannaye na,sannan na fito parlour.

A dai dai wannan lokacin da na kammala komai sai ga Sulaiman ya shigo,ya dube ni yana tambaya ta.

“Kin adana jakar inda ya dace ko?”

Na gyad’a kaina tare da cewa.

“Na adanata inda babu wani mahaluk’i da ya isa ya ganta”

Jinjina yayi min tare da murmushi,sannan ya ce min.

“Allah yayi miki Albarka Zainab,Na gode”.

Naji dad’in addu’ar sosai a zuciyata,na amsa ina murmushi,sai ya dubeni ya sake cewa.

“Kije kiyi wa Hidaya addu’a a d’akinta,ni zanyi wasu salloli ne”

Na amsa tare da mik’ewa na fice zuwa d’akin Hidaya da ke jikin na mu d’akin,dan akwai k’ofa ma cikin d’akinmu da zata kaika d’akin Hidaya kai tsaye ba sai ka bi ta parlour ba,ina wucewa shi kuma ya shimfid’a darduma ya tayar da Sallah.

Da na je na dawo sai na tarar har lokacin sallolinsa yake ta yi,na zauna ina jiran ya kammala mu kwanta,amma shiru da yayi sallama sai ya kabbara wata har na fara hamma bacci na d’iba na,hakan yasa na kashingid’a ina ta kallonsa,idan yayi sujjada ya kan d’au tsawon lokaci bai d’ago ba,a haka har bacci ya kwashe ni yana ta sallar sa.

Har bacci na yayi nisa sosai sai naji Sulaiman na bubbugani yana tashina,na bud’e idanuwana da suka zama k’ananu saboda bacci ina dubansa,sai naji yana cewa.

“Zainab tashi kinji,motsi nake ji kamar ana shigowa gidannan fa”

Nan da nan na wartsake,na nemi baccin na rasa jin abinda yace,a firgice na mik’e zaune,muka yi kasak’e muna jin alamar motsin tafiya sosai,a tsorace muka sake duban junan mu,kafin muyi wani yunk’uri muka ji an banko k’ofar d’akinmu da k’arfi an shigo.

Wasu mutane ne za su kai kimanin su biyar,sanye da bak’ak’en kaya da mask bak’ak’e sun b’oye fuskokin su,wata irin tsawa d’aya daga cikinsu ya daka mana,sai da y’an hajin cikinmu suka kad’a take muka durk’ushe a k’asa ganin manya manyan makamai da bindigogi a hannun su,wani irin matsanancin tsoro ne ya kama mu,yayin da muke ta ambatar “La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimina”

Babbansu ne ya k’yalk’yale da wata irin dariya kafin ya dubi Sulaiman,cikin kakkausar murya ya nuna shi yace da shi.

“Kai k’aramin d’an iska k’aramin k’waro,kai har ka isa ka ja da manyan alhajoji kamar Alhaji Mudassir da Alhaji Maude?to uban gidan naka ma mun gama da babinsa balle kai k’aramin matsiyaci,yanzu muna so ka fara fito mana da duk wasu kadarori da Alhaji Taufik’ ya mallaka,domin mun san cewar suna hannunka,idan kuma ba haka ba kasan ya yadda ake sara rake?to billahillazi haka za mu sassaraka mu feraye naman jikinka”

Tashin hankali kenan wanda yafi k’arfin tunanin mu,take na nemi hawaye ma na rasa tsabar bala’in da ya same mu,addu’a kawai nake bankawa a zuciyata Allah ya rabamu da sharrin wad’annan mutane azzalumai,ganin Sulaiman yayi shiru bai amsa musu ba yana ta dai kallonsu,sai wani da ke gefe ya d’aga bindigar sa ya kwad’awa Sulaiman a gefen kansa da k’arfi,wata irin k’ara Sulaiman ya saki ya fad’i kwance a k’asa jini ya fara zubowa ta kansa,cikin matuk’ar tashin hankali na nufe shi a razane na kamoshi jikina ina kukan da babu hawaye,sai ihu nake cikin gigicewa har ban san lokacin da na dinga k’unduma musu zagi ba,Marin da aka gaura min shine ya tsayar da maganata,saboda azabar da ta ratsani kamar wadda aka saukewa guduma a kumatu,jikin gigicewa Sulaiman ya rungumoni jikinsa yana hawaye,take ya fara rok’on su da cewa.

“Dan Allah na rok’e ku kar ku tab’a min matata ! duk abin da za ku yi min ni na fanshe ta kuyi a kaina,amma don Allah ita mace ce kar ku tab’a min iyali na,komai za ku yi to kuyi a kaina na amince”

Wata dariya dukkan su suka bushe da ita,kafin babban na sau ya sake magana cikin shakiyanci.

“Eh lallai soyayya ruwan zuma! tabbas akwai k’auna a tsakani,to babu laifi tunda soyayya gaskiya ce,kuma muma walidan mu ita suka yi har aka samar da mu,za mu k’yale matarka darajar soyayya,amma fa kai wallahi ko ka bamu abinda muke so ko ka bar duniya a yanzu ba da b’ata lokaci ba”

Har zanyi magana domin d’auko musu jakar sai naji Sulaiman ya zuro hannunsa na baya ya kama hannuna da k’arfi ya matsa alamar in yi shiru,sannan ya dube su har lokacin jini na fita ta goshinsa,yace musu.

“Babu mahalukin da a duniya yasan inda na b’oye abinda kuke nema,ko matata bata sani ba,ni kad’ai na sani,kuma na rantse da ubangijina ba zan fad’a muku ba, ba zan baku ba,sai dai ku kasheni har lahira,na san cewa daman kwanaki na na duniya ne suka k’are,amma ba zan taimakawa azzalumai irinku ba”

A haukace Babban nasu yayi ball da Sulaiman yana dukansa da wata sanda,ihu na saka nayi kansa ina tunkud’e shi ina cewa”Ka daina dukar min mijina,kar ka kashe min mijina,zan ….”

Katseni Sulaiman yayi da mugun sauri ya fizgo hannayena,bai damu da dukan da ake masa ba ya tsura min idanu cikin firgici ya ce.

“Idan har kika yi magana ba zan tab’a yafe miki ba Zainab,ki barsu suyi duk abinda za su yi,komai yana da farko kuma yana da k’arshe,idan sun kasheni suma za su je inda na tafi,ba za su tab’a dawwama a duniya ba”

Inaji ina gani a gabana suka cigaba da dukan Sulaiman,wani irin duka da har ya fara fita daga hayyacin sa,ni dai kuka kawai nake mai cike da firgici,ba don maganar da Sulaiman ya fad’amin ba da tuni na basu abinda suke so,jin hannun Sulaiman nayi yana janyo ni da alamar magana yake son yi min amma muryarsa ta kasa fita tsabar wahala,da hanzari na ture na kusa da shi da yake dukan sa na matsa jikinsa,kunnena na kai dai dai bakinsa ina kuka sosai,sai naji yana ce min.

“Zainab duk wuya kar ki basu wannan jakar,idan har kika basu sun ci nasara a kanmu,kuma na san ko na basu ko ban basu ba kasheni za su yi,gara suyi nasara guda d’aya,bana son su samu nasara guda biyu,Zainab ki rik’e mana y’ar mu da kyau,ki kula da tarbiyyarta da lalurarta,ke kad’ai kika rage mata yanzu da danginki,kinga ni dai bani da dangi,Abba ne kawai dangina kuma a yanzu shima babu shi,nima kuma zan tafi,don Allah Zainab ki rik’e amana kar ki bari azzalumai suyi nasara a kanki Zainab….

Iya nan maganarsa ta tsaya saboda fizgata da akayi daga jikinsa akayi cilli da ni gefe,a lokacin ne kuma wayar Ogan na su tayi k’ara,d’agawa yayi yana fad’in.

“Hellow,ALHAJI MUDASSIR”

Banji maganar da akayi masa daga can ba,sai dai naji ogan na bada amsa da cewa.

“D’an taurin kaine wannan shegen mutumin yak’i bamu abinda muke so fa”

Yayi shiru yana sauraren abinda ake cewa,sai ya kwashe da wata muguwar dariya.

“Hahaha! kar ka damu ALHAJI MUDASSIR,yanzu za mu aika da shi BARZAHU kamar yadda ka umarce mu,suma iyalin na sa za mu yi abinda ya dace a kansu” ya sake bushewa da dariya sannan ya kashe wayar ya mayar aljihu.

Ni dai matsanancin kuka nake ganin har Sulaiman ya daina motsi,ina kallo ogan na su ya sa mutane guda biyu suka zo suka d’aga Sulaiman da ya gama fita daga hayyacin sa,suka mik’ar da shi tsaye,ni kuma ya umar ci d’ayan da yazo ya rik’eni,ina fizge fizge amma haka ya rik’eni gam ya toshe min baki na,Lokaci guda naga Ogan ya fito da wata zabgegiyar wuk’a sai k’alli take yi tana d’aukar ido,zaro idanuwa nayi ina shirin sume wa a sanda naga ya nufi gaban Sulaiman da ita ya tsaya,sannan ya sa hannu ya d’ago kan Sulaiman da k’arfi ya dube shi,cikin wata kakkausar murya ya nuna masa wuk’ar da ke faman k’yalli ya ce.

“Za ka bamu ko ba za ka bamu ba?”

Sulaiman da ya kasa magana ya girgiza masa kai alamar ba zai basu ba,bakinsa na motsi yana ta kallona alamar salati yake yi da shahada,wani mugun murmushi Ogan yayi kafin ya d’aga wuk’ar ya sokawa Sulaiman a k’irji da k’arfi😭Wani irin ihu na saka duk da bakina a rufe yake sai da gidan ya amsa,fizgo wuk’ar yayi ya sake luma masa a cikinsa😭 take wani irin jini yayi tsartuwa ya fara malala a k’asa,a lokacin tuni rai ya bar gangar jikin Mijina Sulaiman😭,sun kashe min shi😭,duhu ne kawai ya mamaye min idanuwa na,sanda na riski muryar Ogan na su na magana da alama waya ya buga.

“ALHAJI MUDASSIR mun cika aikin ka ! a yanzu haka ran Sulaiman ya tafi Lahira…!

Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba😭

 

 

 

 

 

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA TAMANIN DA TARA DA NA CASA’IN

 

*SADAUKARWA GA MUTANE GUDA BIYU*👇

GAREKI MISS FLOWER KE CE TA FARKO,MARUBUTA NA GODIYA DA YABAWARKI GARESU,ALLAH YA BAR ZUMUNCI,MU MA MUNA K’AUNARKI SOSAI🥰

TA BIYUN KUMA BAN SANKI BA,AMMA SAK’ONKI YA ISO ZUWA GARENI TARE DA SAURAN MARUBUTA,KAMAR YADDA KIKA CE NICE A FARKON FARI,TO NIMA NACE KE CE A FARKON FARI 😅KUMA INA NEMANKI DOMIN KI KARB’I TUKUICIN K’AUNA,HASSANA D’AN LARABAWA NA MIKI SON SO FISABILILLAH,KUMA MUNA GODIYA SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.🤝🥰

 

 

***Ruwa suka yayyafa min na farfad’o,a lokacin bani da buri illa nima su kasheni domin nabi Sulaiman d’ina,hakan yasa na dinga kallon gawar Sulaiman da ke kwance,ina rok’onsu akan nima su kasheni kawai na shirya mutuwa,Ogansu ya sake fashewa da dariya yana kallon wuk’ar hannunsa sannan ya dube ni ya ce dani.

“A cikin tsarin mu babu aika ki lahira a yanzu y’ammata,ki bari idan buk’atar hakan ta taso ba ma sai kin rok’emu ba,da kanmu za mu aika ki lahira domin ki bi d’an masu taurin kai”
Daga nan ya juya ya dubi mutanen da suka rik’e Sulaiman,ya umarce su da su d’auki gawar Sulaiman suje su sakata a motar da suka zo da ita,duk fizge fizge na akan su bar min mijina kar su fita gawarsa k’in saurarata suka yi,suka d’auke shi jini na yarari suka fice da shi akan idanuwa na,wannan shine gani na k’arshe da Sulaiman d’ina.

Akwai ragowar mutum d’aya a cikinsu wanda na lura shi tunda suka zo baiyi magana ba,kuma baiyi motsi ba yana k’ame yana kallon dukkan abinda ke faruwa,sai a lokacin Ogansu ya dube shi yayi masa sigina,Sannan ya juya ya fice ragowar d’ayan ya bishi a baya,daman su biyar ne.

Shi wanda aka yiwa siginan shine ya k’araso gareni inda nake tsugune ina wani irin kuka na tashin hankali,yana zuwa gabana ya dubeni ya ce min “Tashi” yanayin muryar da yayi amfani da ita babu fad’a da tsawa,sai naji kawai dan karan kaina na bi umarninsa na tashi tsaye,kallon fuskarsa nake ina kuka,amma da yake akwai mask a tasa fuskar bana ganin komai sai idanuwan sa,nuna min d’akin yayi sannan ya sake ce min.

“Ki duba d’akin nan ki d’auki duk abinda za ki d’auka kizo mu tafi”

Na cigaba da kallonsa kawai,to ina zamu tafi?ina za su kaini?tambayoyin da nake wa zuciyata kenan babu mai bani amsa,sai naji kawai ban tsorata ba,gara na bisu in ma kashenin ne suyi zan fi son hakan ma,me zan zauna nayi a duniyar da babu Sulaiman a cikinta?

Juyawa nayi nabi ta k’ofar da ke cikin d’akina zuwa d’akin da Hidaya take,Allah sarki baiwar Allah duk abinda ake ita baccin asara take,ana can an kashe mata mahaifi tana bacci,yana biye da ni har inda take kwance,ban san abinda ya k’arfafa min zuciyata ba kawai dai naji na daina jin tsoro zuciyata ta dake sosai,sai naji hawayen ma ya k’afe min illa azabar suya da k’irjina yake yi.

Yana ta kallona har na d’auki Hidaya duk girmanta na sab’a a bayana,na d’auki zani na goyata,sannan na tsaya ina kallonsa,sai naji ya sake ce min.

“Y’arki kawai za ki d’auka?ki sake dubawa dai idan da wani abin da za ki d’auka,amma ki hanzarta kada lokaci ya k’ure mana”

Nayi duru duru na rasa me zan d’auka,gani nake babu wani abu da zai min amfani,amma da na tuna da maganar Sulaiman akan na kula da d’iyar mu,kawai sai na juya na d’auko wata jaka,na d’ibarwa Hidaya y’an kayayyakinta da takalma,sai kuma idanuwana suka fad’a kan Sark’ok’in gwal d’in mu da Abba ya siya mana ni da ita,suma na d’auke su,sai kuma wani littafi da biro da na d’auka,duk na had’a a cikin jakar yana tsaye yana kallona.

Karb’ar jakar yayi ya rik’e,sannan ya nuna min hanya na wuce ya biyo ni a baya har zuwa waje,ina ta kallon gidan da nayi rayuwa a cikinshi tsawon shekaru,muna zuwa harabar gidan na kalli inda mai gadi yake sai naga ban ganshi ba,k’ila shima sun kasheshi ne,sai dai naga ragowar mutanen da suka fara fita suna shisshiga mota,sai Ogansu ya nufo mu ya tsaya dab da mu,cikin wata kakkausar murya yace da wanda ya fito da ni.

“Ka aikata abinda aka umarceka,kar ka sab’a mana k’aidar aiki,idan har aka samu matsala kaima ka san sauran”

Jijjiga kai yayi yana sara masa,sannan ya nuna masa wata mota yace ita za mu shiga,agaba mutumin ya sanya ni ina goye da Hidaya a bayana,so nake na tambayesu gawar Sulaiman amma bakina ya b’ame,haka aka bud’e min k’ofa na shiga bayan motar na zauna,sannan wnnan mutumin ya shiga gaban motar ya tayar ya figeta muka bar harabar gidan.

Muna fita ya tsayar da motar,banyi aune ba naga ya juyo ya busa min wata hoda,take kaina ya juye,ban san lokacin da wani bacci mai nauyi ya d’auke ni ba.

 

 

 

*****************

 

 

Bud’e idanuwa na nayi a hankali,sakamakon wani abu da naji an fesa min wanda ban san ko menene ba,a hankali muka had’a idanuwa da mutumin da ya d’akkoni a mota,sai a lokacin naji Hidaya ma ta farka tana ta motsi a bayana jin na matseta,kuma daman ni ba goyata nake ba kasancewar ta girma sosai,idanuwana a kansa na tsura masa idanu,sai naga ya sa hannu a aljihun rigarsa ya fito da biro da takarda yayi rubutu a jiki,sannan kuma ya d’auko wata envelope ya had’a da takardar hannun na sa ya mik’o min,hannu na kai na amsa,ban san me yasa nake masa ladabi kan duk abinda ya umarceni ba,ina karb’a naga ya fita daga motar sannan ya zo ya bud’e min ta inda nake zaune, “Fito”abinda yace da ni kenan bayan ya bud’e min k’ofar,a hankali na janyo jikina na fito Hidaya na a bayana tana ta k’ok’arin na saukota,lek’awa yayi cikin motar ya fito min da jakar da na zubo kayan Hidaya ya mik’o min,nan ma na karb’a babu bakin magana,sai naga ya koma cikin motar ya zauna bayan ya rufe k’ofofin,kafin in ce me har yaja motar da gudu ya bar inda nake.

Motar na bi da wani irin kallo har ya b’ace a wajen na rasa tunanin me k’wak’walwata take,nidai na san tuni hankalina ma ya gushe daga jikina tun sa’ar da aka kashe min Sulaiman akan idanuwana,nafi minti goma ina kallon in da yabi da motar na kasa d’auke idanu,kukan da Hidaya ta soma shine ya ankarar da ni na dawo hayyacina,a hankali na sakkota daga bayana ina kallonta,sai lokacin wani hawaye ya sake zubo min,shikenan an mayar da ni bazawara!sannan an mayar min da y’ata marainiya! rungumeta nayi a k’irjina na fashe da wani irin kuka mai cin rai,ita ma Hidaya ta rungumeni tayi luf a jikina,kiran Assalatu da naji an fara yi shine ya ankarar da ni ashe fa talatainin dare ne a lokacin,gurin yayi tsit babu motsin kowa,hakan yasa na ja gefe d’aya daga wani loko na ajiye jakarmu a gefe,sannan na zauna na d’ora Hidaya akan cinyoyina na cigaba da kuka ina salati,Hidaya kam luf tayi a jikina ta kwantar da kanta,sai bacci ma ya sake kwasheta.

Muna wajen har gari ya waye rana ta fara fitowa,da yake ina daga d’an loko babu wanda ya ankara da mu,sai da rana ta dallewa Hidaya idanu sannan ta farka tana muttsike idanuwa,ni ko dama babu alamun wani barci a idanuwana,hankalina yana ga gawar Sulaiman,ko ya suka yi da ita oho,Allah masani.

Hidaya ce ta fara kukan yunwa,dan lokacin kusan goma na safe ne,hakan yasa tilas na mik’e jiri na kwasata,na k’ara sab’ata a bayana na d’au jakar na rik’e a hannuna na fito daga lokon da muke,har lokacin kuma wannan takarda da envelope da wannan mutumi ya bani suna hannuna,mun fito daga lokon na kama waige waigen in da zan samarwa Hidaya abin da zata ci,tunda shi yaro bai san hak’uri da yunwa ba,ni kuwa ko yunwar ma bana ji,a haka na dinga tafiya ban san ina nake tsoma k’afata ba,dan ban ma san a ina nake ba a halin da nake ciki.

Cikin ikon Allah na b’ullo wata kwana na dinga jin k’amshin suyar wainar k’wai,ashe me saida shayi ne a wajen,hakan yasa na tsaya a gefe duk ga maza nan akan benci sun jeru masu zuwa su siya,sai lokacin na tuna ai ban d’akko kud’i ba,banda ko sisi a jikina,hankalina ya tashi na rasa ya zanyi,me shayin ne ma ya lura da ni ya k’ura min idanu kamar zai cinyeni,sai kuma yace da ni.

“Hajiya lafiya kuwa?ko wani abin za a baki?”

Daurewa nayi cikin wata irin murya nace.

“Don Allah taimako nake nema,shayi da bread za ka sammin zan bawa y’ata tana jin yunwa gashi bani da kud’in siya mata”

K’are min kallo yayi,ya kalli suturar jikina ya tabbatar me tsada ce,sai dai daga gani bana cikin nutsuwata,hakan yasa ya b’ata rai kamar yaga kashi sannan yace min.

“To angaya miki ni kayan Shayin zuwa nake a sammin balle nima nazo nayi ta sanwa mutane?dalla malama wuce kibawa mutane guri kayana na kud’i ne ba na alakoro ba,ke ni gabad’aya ma ban yarda dake ba”

Hawaye ne ya tawo min,har na juya zan tafi sai naji wani daga cikin mutanen da ke zaune ya kirani,na juyo na dawo,sai ya kalli me shayin ya ce.

“Haba Rabilu,taimako fa ta nema,idan ba zaka taimaka mata ba bai kamata ka muzantata ba,kuma duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimaka masa in dai da zuciya d’aya yayi,kuma in dai don zatin Allah yayi,dan haka ka had’a mata shayi ka bata bredi ta bawa y’ar ta ta ,ni kayi min lissafi da kud’i na sai na had’a na baka”

Godiya nai tayi wa mutumin,sannan na ja gefe na zauna kan wani dandamali,har aka had’o min shayin aka mik’o min tare da bread,na karb’a na sakko Hidaya kan cinyata na fara bata,nan da nan kuwa ta karb’a taci bread ta sha shayi ta k’oshi tayi gyatsa,ni ko ko sha’awa bai bani ba ma,ko ruwa bana jin zan iya kaiwa bakina,mutumin da ya siya mana shayin yana zaune har Hidaya ya dinga yiwa wasa,na sake yi masa godiya sosai sannan na mik’e,ya zaro kud’i a lokacin ban san ko nawa ba ne ya mik’o min wai na siyawa Baby abincin rana,kamar ba zan amsa ba sai kuma na amsa na sake yi masa godiya na wuce Hidaya na d’aga masa hannu,mutanen wajen suka bini da kallo,a haka har na fita daga layin na shiga wani layin,sai na had’u da wani d’an mata shi haka yana motsa jiki,na tsaya na tambaye shi shin nan ina ne?sai ya tsaya yana kallona kafin yace min.

“Nan tudun wada ne”

Na tsaya nayi kasak’e,ya sake kallona yace min.

“Ko baki gane ba ne?Nan fa unguwar tudun wada ne,cikin jihar KADUNA”

Sai mamaki ya kamani,kenan wannan mutumin a daren jiya da ya d’akkoni daga Abuja kaduna ya kawoni kenan?godiya nayi wa matashin kafin na wuce shi ma ya bini da kallo.

Ina ta tafiya har nazo wani layi da babu hayaniya sosai,lokacin sha biyu na rana har ta wuce,na fara gajiya gashi na rasa in da zan dosa,hakan yasa na tsaya cak ! sai kuma idanuwana suka fad’a kan wani kango da ke gefena,sai kawai naji zuciyata ta aminta da shiga cikin kangon na fake kafin in san abin yi,ganin kangon a bud’e yake hakan ya sa na turmutsa kaina rik’e da Hidaya da jakar kayan ta.

Muna shiga na samu wajen zama,na sauke Hidaya,sai ta k’ara matsowa jikina ta kwanta,kafin wani lokaci bacci ya sake d’auketa,ni kuwa ina zaune dangwargwar tunani da sak’e sak’e ya cika zuciyata,kawai sai na d’akko wannan takarda da wannan mutumi ya bani na bud’eta,sai naga rubutu kamar haka a jiki

 

*Ba wani ba ne ya umarcemu da mu kashe mijinki illa Alhaji Mudassir,kuma shine yace bayan mun kashe shi ke kuma mu b’atar da ke yadda ba za a sake jin d’uriyarki ba ke da y’arki,a yanzu haka ni aka bawa kwangilar b’atar da ke,amma sai naji wani abu mai kama da tausayinki,dan haka na kawo ki kaduna,abinda yasa na kawoki kaduna kuwa shine,nan ce mahaifar Alhaji Mudassir,ina so ke da y’arki kuyi rayuwa a garin ta yadda zaku san komai nasa,duk da yanzu baya garin yana Abuja,ta haka ne zaku iya d’aukar fansar abinda yayi muku a tsawon rayuwarku,ko kuma ita y’arki ki barta ta rayu a kaduna ke kiyi nesa da ita,amma ki bar mata sak’o wanda ko da ta girma zai zame mata jagora wajen gane wanda ya kashe mata mahaifinta,saboda shi Alhaji Mudassir yafi saninki a kanta,muddin yasan kuna wannan gari zai iya lallab’owa kuma ya sa a kashe ku,dan haka kisan yanda zakiyi ki bar kaduna a yau domin zai iya bibiyarki,amma ita y’arki ki barta a kaduna*

Nayi kuka sosai bayan kammala karanta wannan takarda,sai naji a zuciyata na aminta da duk abinda wannan mutumi yace min,tabbas ba abinda nake ji a zuciyata sai son d’aukar fansa,hakan yasa naji a zuciya zan rabu da Hidaya,zan barta gidan marayu ko dan watarana burin zuciyata ya cika,bud’e envelope d’in nayi,sai naci karo da hoton Alhaji Mudassir,na dinga kallon hoton ina kuka ina jin matuk’ar k’iyayyar wannan mutumi a zuciyata,a haka na bud’e jakar nan na zaro biron da na sako da littafin,na yagi paper na fara rubutawa Hidaya takardar cikin kuka,bayan na gama sai na had’a ta a cikin envelope d’innan tare da hoton Alhaji Mudassir,sai kuma na yagi wata paper nayi rubutu da zummar zanje gidan marayu na Kaduna in faki ido,ko a k’ofar wajen ne na ajiye Hidaya da kayanta in tafi in barta,k’ark’ari dai na san zanyi kewa,na rasa ubanta ita ma na rasa ta,amma zan bita da addu’a,saboda nidai zuciyata ta k’ek’ashe akan d’aukar fansa,kuma Hidayan nake so ta d’aukar min fansar bayan ta girma.

A wannan kangon muka wuni,har Hidaya ta farka ta cigaba da wasanninta,kuma bata ce min tana jin yunwa ba,ni kuwa halinda nake ciki ma ya isheni,musamman da Hidaya ta tambayeni Abbanta sai na b’oye fuskata na dinga kuka,ita kam sai ta cigaba da wasanninta tana tsalle tsalle,burina na nemi ruwa nayi alwala nayi sallah,amma bani da nutsuwar da zan iya yin sallar,so nake duhun magariba kawai yayi in samu in fita daga kangon in kai Hidaya gidan marayu ni kuma na wuce duk inda Allah ya nufe ni da zuwa,ina kwance lamo cikin mawuyacin hali har Hidaya ta gaji da wasan ta zo tana cewa in tashi mu tafi,ni kuwa ko mik’ewa na kasa yi,nan ta lura da bushewar da bakina yayi,shine ta ce zata fita ta samomin ruwa,ina niyyar hanata fitan ma amma tuni ta ruga ta fice daga kangon ta barni kwance nan,wanda dalilin fitar ta ne gamuwar ta da HAMZA,wanda ya zame mata GARKUWA.

A lokacin da naga Hamza kallo d’aya nayi masa kawai naji ya kwanta min a zuciyata,sai naji ina ma dai zai iya rik’e min Hidaya duk da dai shima ba wani girma ne da shi ba,amma tun lokacin na fahimci shi yaro ne mai matuk’ar hankali,kuma Allah yayi masa wata baiwa da shi kansa bai san yana da ita ba,shiyasa lokacin da na bashi takardar da zai kai gidan marayu ina kallo ta fad’i daga hannunsa lokacin da zai cusa a aljihu,kafin ya ankara na janyeta na b’oye,na san ba zai tab’a iya kai Hidaya gidan marayun ba idan ba wannan takarda tunda ita ce shaida,tilas zai rik’e min Hidaya da shi da iyayensa,sai gashi kuwa yayi mata rik’o irin wanda ma ban tab’a zata ba,lallai Hamza ya cika GARKUWAR HIDAYA.

Mummy ta sauke ajiyar zuciya tana kallon mutanen da ke sauraren ta,a hankali hawaye ke cigaba da kwarara a idanuwan ta kafin ta bud’e baki don cigaba da magana.

 

 

 

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA CASA’IN DA D’AYA DA NA CASA’IN DA BIYU

 

 

 

Ban bar wannan kangon ba sai da duhun magariba yayi,sannan na daddafa cikin k’arfin hali na fito,babu komai a tare da ni sai sark’ar gwal d’ina da na d’auka a cikin kayan Hidaya na k’ulle ta a bakin zani na,sai kuma kud’in da wannan mutumin ya bani akan na siyawa Hidaya abincin rana,a haka na fito ina walagigi har zuwa bakin hanya wajen titi,sai a lokacin na tsaya na tambayi wani mutum in da zan sami motar da zata kaini Gombe,yace min ai dole sai naje tasha,a tak’aice dai wannan mutum shine ya sakani a hanya har zuwa tasha,nayi masa godiya sosai,sai dai kuma wani jidalin babu motar da zata tashi a daren wai sai zuwa safiya,haka na hak’ura nayi kwanan tasha,dan ma naga da mutane sosai,da sassafe kuwa mota ta d’aga damu zuwa Gombe,wannan kud’i da mutumin nan ya bani su suka zame min GARKUWA,domin da su na samu na biya kud’in mota.

A maimakon da na isa Gombe na samu salama sai na tarar da wani tashin hankalin,mahaifina ya rasu ana shirin kaishi makwancinsa,ana ta neman wayata da ta mijina an rasa,take na fad’i a tsakar gidan mu na suma tsabar tashin hankali.😭

Kwana na biyu ban san in da kaina yake ba,nasha wahala matuk’a da gaske a lokacin,na dinga ciwo kamar ba zan kai labari ba,abubuwa biyu suka had’e min,rashin miji da rashin mahaifi lokaci guda,in ban da Allah waye zai maka wannan?ganin halin da nake ciki shiyasa Ummana bata tambayeni Hidaya da mahaifinta ba,har sai da aka d’auki kwana tara da rasuwar mahaifina,lokacin mutane sun baje y’an zaman makoki,na rame na k’ok’ale tamkar allura,ko mik’ewa tsaye nayi jiri nake ji sai an rik’eni,bana iya ci balle sha,kullum kuka nake me soya k’irji da zuciya.

Ranar kwana goma da zuwa na Gombe Ummana ta sameni har d’akinta in da nake kwance ina sana’ar kuka na,ta zauna ta d’agoni ta tasheni zaune,sannan ta tsura min ido ta dinga lallashina da kalamai masu dad’i tare da yi min nasiha da hak’uri akan rashin mahaifina,sannan ta tambayeni shin ina mijina?ina Hidaya?kuma ya akayi na zo Gombe a ranar ?kamar ina da masaniyar mahaifina ya rasu?haka ta dinga jeromin tambayoyin da suka sake tayar da hankalina,na dinga wani irin kuka me tayar da hankali da ban tausayi,har ita ma nasa ta fashe da kukan ,tana ta rok’ona akan na fad’amata abinda ya faru,domin wannan kuka da damuwar da nake ta shallake hankali da tunani,da k’yar na iya bud’e baki cikin kuka na fayyacewa mahaifiyata dukkan abinda ya faru,abu d’aya na b’oye mata,shine barin Hidaya da nayi a Kaduna,sai nace mata wad’annan mutanen sun tafi da Hidayan da gawar mahaifinta,kuma ban san in da suka tafi ba,saboda na san in dai na fad’amata Hidaya na Kaduna tilas zata ce sai an karb’o ta,shiyasa nace mata haka,sannan na k’ara mata da cewa mutanen sun ce muddin na bibiyesu ko na fallasa su gun hukuma to nima sai sun kasheni,kuma sai sun k’arar da kaf zuri’ata dake doron k’asa,dan haka na kiyaye. Wannan bayani da nayi wa mahaifiyata ya sakata cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa,tayi kuka mara iyaka tare da mamakin yadda mutanen duniya suka lalace,zalunci da mugunta ya mamaye zukatan al’umma,wanda mumini na k’warai ba zai tab’a aikata wannan mummunan aiki ba,haka muka had’u muka dinga kokawa da jajantawa juna.

Ummana ta k’ara bani hak’uri tare da min nasiha akan gara mu hak’ura kar muce za mu d’au wani mataki,tunda ba k’arfi garemu ba,ga yadda k’asar ta mu ta zama manya suna taka talakawa yadda suke so kuma babu yadda za a yi,idan ma muka ce zamu shigar da k’ara bamu da wata babbar shaida,reahe ma zai iya juyewa da mujiya,idan baka iya kama b’arawo ba shi sai ya kama ka caraf,gara mu barwa Allah komai zaiyi sakayya lokacin da bamu zata ba,tashin hankalinta d’aya ne wato bamu san halin da Hidaya take ciki ba,ko tana raye ko tana mace Allah masani,kullum zancenta baya wuce na Hidaya tana addu’ar duk in da take in tana raye Allah ya cigaba da kare ta,kuma Allah ya bayyanata.

Ni da yake na san Hidaya na raye bana damuwa da hakan,sai dai kullum ina mata addu’a,ban tab’a mantawa da ita ba,haka nan mahaifinta da Oga Taufik’ kullum sai nayi kuka idan na tuna su da rayuwar da muka shimfid’a mai dad’i,yau komai ya wargaje dalilin azzalumai,ba mijina,ba mahaifina,babu y’ata sanyin idaniyata a tare dani,sai inji wani bak’inciki kamar na mutu,sai in tuna da wad’anda basu da kowa,wad’anda suka tashi a gidan marayu basu da dangi,sai in ga ashe ni Allah yayi min lud’ufi ma da ya barni da uwata ina ganinta ina jin dad’i,ga y’ar uwata Sajida ma akusa dani,sai in godewa Allah abisa jarrabawar da yayi min,Amma tabbas a lokacin nan na shiga tashin hankali mara misali,babu ranar da zata fito ta wuce ban zubar da hawaye ba,abinda yake sanyaya min raina kawai shine yawan mafarkin Hidaya da nake,cikin rayuwa ingatacciya da kyawun yanayi,wannan kad’ai ya kan sani naji farinciki mara misaltuwa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin k’alubale,kwana bayan kwana,sati bayan sati,wata bayan wata,shekara bayan shekara,har aka d’auki wasu shekaru kafin na fara manta wasu Abubuwan da suka faru da ni,amma ban tab’a mantawa da Sulaiman da d’iyata Hidaya ba,da kuma Oga Taufik’kullum ina musu addu’a,rayuwa dai muna yin ta kadaran kadahan,mu ba masu k’arfi bane amma akwai rufin asiri,abin da mahaifinmu ya mutu ya bari shi muka dinga juyawa da jalautawa muna rufawa kanmu asiri da shi,a lokacin ne kuma mane ma auren Sajida suka fara bayyana kasancewar ta girma sosai har tayi candy,sai Ummana tace min nima ya kamata na fitar da miji nayi aure zamana haka baida wani amfani,nan fa hankalina ya tashi sosai domin banga ta in da zan iya wani aure ba a halin da nake ciki,duk da Sulaiman ya mutu amma shine kawai a raina,na dinga kuka ina ce mata nifa ba zan yi wani aure ba har abada,ganin tashin hankalin da na shiga sai Ummana ta rabu da ni da zancen fito da miji,akayi bikin Sajida aka gama aka kaita gidan mijinta nan Gombe a unguwar Arawa.

Bayan bikin ne nake fad’awa Ummana ina son komawa makaranta domin na rage zaman gida da yawan tunani,Umma ta bani k’warin gwiwa sosai,sai dai tunaninta ta ya ya zan dinga samun kud’i ina biya a makaranta?tunda bamu da wani k’arfi?a lokacin ne na d’auko sark’ar gold d’ina da na tawo da ita,na cewa Ummana ita zan siyar nayi hidimar makaranta,ragowar kud’in kuma sai mu ja jari mu kama sana’a,haka kuwa akayi,muka saida sark’a kuma tayi daraja sosai da sosai,wani d’an uwan mahaifina Kawu Muttak’a yayi min cuku cuku har na samu shiga jami’ar GOMBE domin cigaba da karatuna,wanda na d’auki b’angaren shari’a a matsayin abin da zan karanta,ko domin cimma wani k’uduri na wa.Ragowar kud’in kuma muka fara sana’ar sayar da abinci a cikin gida,Umma ta d’auki ma’aikata guda biyu suna taya ta aikin,nima duk randa bani da lakca ina zama ayi da ni,da yake Umma mai tsafta ce kuma ta iya abinci sosai nan da nan muka samu kasuwa sosai da sosai,abinci har k’arewa yake ayi ta zuwa nema.

Cikin lokaci k’ank’ani Allah ya sakawa sana’ar mu albarka,sai gashi mun tara kud’i mai yawa,harkar karatuna kuma na tafiya yadda ake so,na dage sosai karatu nake ba da wasa ba,kullum Hidaya na raina,ina jin sha’awar zuwa Kaduna domin na binciki halin da take ciki.

Wata rana kawai na tashi da son ganin Hidayan,zuciyata sosai take azalzalata akan son ganinta,ji nake in banje Kaduna a lokacin ba kamar wani abu zai faru da ni,hakan ya sa na samu Ummana na tsarata akan cewa Za mu yi wata tafiya a makaranta zuwa Jami’ar Kaduna, Jami’ar Kaduna ta gayyaci Jami’ar GOMBE domin k’arawa juna sani akan wasu abubuwa da suka shafi harkar karatu,Umma ta amince sannan ta bini da addu’ar samun nasara da kiyayewar ubangiji.

Na shirya nayi wa Umma sallama na fice sai tasha,na nemi motar Kaduna na d’ane,direba ya kwashi mota ya dinga falfala gudu,ni dai bakina d’auke da addu’o’i kala kala har muka isa Kaduna lokacin kusan k’arfe d’aya na rana,da na sauka daga mota sai na d’akko nik’ab d’ina a cikin jaka na d’aura,kamar me gudun kar na had’u da wanda ya sanni,cikin ikon Allah ban manta da sunan unguwan Tudun wada ba,sai gani a cikinta ina bin layi layi har na zo kan layin da kangon nan yake,wanda muka zauna ciki randa na bawa Hamza Hidaya,sai naga kangon ma tuni har an gine shi ya zama gida, dan ma dai ina da gane guri shiyasa ban b’ata ba.

Na d’an jima ina tsaye ina k’arewa gurin kallo kafin na cigaba da tafiya na b’ulla wani layin,sai lokacin naji zuciyata na tambayata wai shin ma ina zanga Hidayan?tunda ba sanin gidansu Hamzan nayi ba,shin ma har yanzu Hidayan tana hannun Hamzan?kuma shin har yanzu Hamzan suna wannan garin cikin wannan unguwar?ina zan gansu?take k’wak’walwata ta shiga yi min wad’annan tambayoyin .

Ina tsaye daga gefe nake wannan tunanin,wallahi kamar an ce min kalli d’aya gefenki kawai na juya,me zan gani?Hamza ne da Hidaya suke tafe,yana rik’e da jakar ta ta makaranta da alama ko islamiyya zai raka ta,suna tafe suna hira fuskokinsu da murmushi,Hamza ya k’ara girma sosai,Hidayana tayi girma ta k’ara kyau fes da ita kamar ba mai lalura ba,ban san lokacin da Hawaye ya kwararo min ba,kamar na ruga da gudu na isa wajensu,amma k’afafuwana suka gaza hakan,ban san me zance musu ba idan naje gare su,kwata kwata ma ban shirya hakan ba,ba zan tab’a iya manta kamannin Hamza ba balle y’ar da na haifa a cikina,ta gabana suka wuce lokacin Hidaya na dariya k’ila wata maganar Hamza ya fad’amata,kuma a lokacin da suka zo dab dani naga Hidaya tana waige waige k’ila ko wani yanayin taji a jikinta,da naga haka sai nayi hanzarin juya baya har suka wuce,sannan na juyo na cigaba da kallon bayansu har suka k’urewa ganina,hawaye sosai na dinga zubarwa a wajen,nafi k’arfin rabin awa kafin na share hawaye na na matsa d’an can gaba kusa da wani mai siyar da manja da man gyad’a,yana zaune a rumfarsa ta langa langa,nayi masa sallama ya masa yana tasowa da hanzari ko yayi zaton mai zan siya,sai na gaishe shi,sannan na tambaye shi dan Allah ina neman gidan su Hamza,an ce min a layin nan yake,sai ya tambayeni Hamzan babbane ko k’arami?nace masa babba ne dan har ma ya fara zama saurayi,sai yayi murmushi yace min .

“HAMZA GARKUWAR HIDAYA za ki ce min kawai Hajiya”

Nace masa “Au haka ake kiransa?”

Ya jijjiga kai da fad’in.

“K’warai kuwa,idan ba haka kika ce ba ba lallai a gane ba,saboda akwai Hamza da yawa a layin nan har da yara,amma kina cewa GARKUWAR HIDAYA to za a shaida shi ”

Sai nace masa “Ayya ! to me yasa ake kiransa da hakan,wacece kuma Hidayan?”

Sai naga ya kalleni sosai kafin ya kuma murmushi yace min.

“Da alamun dai ke ma baki san Hamzan sosai ba ko Hajiya?dan duk wanda ya san Hamza to dole ne ya san Hidaya, ita Hidayan kuma k’anwarsa ce,dalilin kiransa da GARKUWAR HIDAYA kuma saboda tsananin sonta da yake da kareta,baya barin kowa ya tab’a ta,ya zame mata GARKUWA SOSAI,ko yanzu ma basu dad’e da wucewa ta nan ba ya tafi rakata makarantar islamiyya,da alamun dai ke bak’uwa ce baki ma san su Hamzan sosai ba ko”

Nan da nan na girgiza kai ina fad’in.

“Tabbas ban san su ba,kwatance akayi min aka ce idan naje gidan su Hamzan na shiga na fad’i gidan da nake so a kaini to za a kaini,yanzu dai gidan su Hamzan za ka taimaka ka nuna min”

Babu b’ata lokaci kuwa ya d’aga yatsan sa yana nuna min gidan da ke d’an can nesa da mu kad’an,nayi masa godiya ina kallon k’ofar gidan,na zaro d’ari biyar na bashi,ya dinga yi min godiya,sannan na wuce shi kuma ya koma runfarsa ya zauna.

Ta k’ofar gidan su Hamzan na wuce,na jima a tsaye ina kallon gidan da Hidaya take rayuwa a ciki tamkar a gidan aka haifeta,nayi kuka sosai ina jinjina k’addarar da ta rabani da gudan jini na,kamar na shiga gidan haka na dinga ji,sai kuma na taurara zuciyata kawai,ina ji ina gani na wuce daga k’ofar gidan na koma bakin titi na nufi tasha,take na samu motar da za ta tashi zuwa Gombe ana jiran mutum d’aya,ba tare da jinkiri ba na haye direba ya d’aga da mu zuwa Gombe,zuciyata cike da raunin ganin Hidayata,sai dai cikin farinciki nake da murna matsananciya ganin yanayin da ta samu kanta na kulawa wanda ko ni sai haka,zuciyata kuma ta k’ara girmama HAMZA GARKUWA,tare da k’ara jin wata k’aunarsa mai girma ta mamaye ni.

Tun daga lokacin sai na samu kwanciyar hankali sosai,kuma daga ranar ne duk lokacin da naji mararin ganin Hidaya na kan tsara Ummana na tawo Kaduna kawai don na ga Hidaya,na kan lab’e tare da rufe fuskata,wataran na ci sa’ar ganinta ko za ta tafi makaranta ko kuma ta dawo,wataran na ganta a shagon da ke jikin gidan nan na sai da wayoyi da yin chaji,wataran ma har naje na dawo bana cin karo da ita,sai dai duk da hakan na kanji dad’i saboda na san tana samun kulawa sosai.

A haka shekaru suka dinga ja har na kammala karatuna na fito da babban kwali,haka nan na dinga ziyartar wurare daban daban dan k’ara ilimi akan harkokin shari’a,har kuma lokacin burina na na a raina na ganin bayan Alhaji Maude da Babban mak’iyina wato Alhaji Mudassir,wanda kaf fad’in duniya bani da mak’iyin da ya fishi.
Lokacin Hidaya ta girma sosai,kuma ina da yak’inin sak’on da na bar mata ya kusa isa gareta,duk da na san zata ga bak’ina sosai akan gujemata da nayi,amma na san wannan ita ce hanyar da yafi kamata na bi,domin cimma k’udurina.

A ranar da Hamza ya ganni a airport tabbas ni ya gani,shi ban san abin da yaje yi ba,amma ni zan yi tafiya ne zuwa wata k’asa akan harkar Shari’a,wanda gwamnatin Gombe ta d’auki nauyi na saboda k’wazon da nake da shi a harkar,wannan tafiya da nayi ita ce musabbabin da na daina jin labarin ku ko bibiyar lamarinku,har aka yi shirin aurar da Hidayan ba tare da na sani ba,tunda yawanci abubuwan da suke faruwa da ita ina sanin wasu,ta hanyar zuwan da nake da kuma wasu hanyoyin da nake bi don bincike akan ku.

Mun d’auki lokaci mai tsawo a tafiyar,domin kwana na biyu da dawowa garin Gombe kawai na dinga jin wata muguwar kewa wadda ban tab’a ji ba,zuciyata na azalzalata kan naje naga Hidaya,saboda wasu irin mafarkai da nake da ita,kullum na ganta a mafarki sai na ganta tana kuka sosai tana mik’o min hannayen ta domin na kama,sab’anin baya da duk lokacin da zanyi mafarki da ita na farinciki ne,zan ganta tana walwala da nishad’i,amma yanzun mafarkina ba haka yake nuna min ba,nan na tabbatar k’ila ko tana cikin damuwa ne ko b’acin rai,shiyasa hankalina ya gaza kwanciya.

A firgice na tashi saboda wani mugun mafarki da nayi da Hidayan,kuka nake sosai ina ambatar sunanta har ban san lokacin da Ummana ta taso ta zo gareni ba,ta rik’eni ganin ina zabur kamar zan ruga da gudu,addu’a ta dinga yi min har na samu nutsuwa,sai kuma na dinga kuka kafin na tashi da hanzari in ce mata ni Kaduna zan tafi,cikin tsananin mamaki take tambayata me zan yi a kaduna a tsohon daren nan?wajen wa za ni a kaduna?wa na sani a can?cikin gigita nake ce mata ni wajen Hidaya zan tafi,y’ata zanje na gani,so nake na san halin da take ciki kawai a yanzu,Umma cikin tsananin mamaki ta kamoni ta zaunar da ni,tana tambayata wai Hidayan da shakara da shekaru ba a tab’a jin d’uriyarta ba ta ya ya na san cewar tana kaduna,waye ya fad’a min?ko dai a mafarkina na gani?Sai lokacin na fara dawowa hayyacina na tuna she fa Umma bata san Hidaya na kaduna ba,ashe fa na b’oye mata komai,to amma yanzu ba zan iya b’oyewar ba,bayyanawa a wannan muhallin ita tafi dacewa da ni,a hankali na bud’e bakina na fad’awa Ummana komai da ya faru cikin kuka matsananci,ban tab’a sanin Ummana tana da fushi sosai ba sai lokacin,domin har marina tayi,ta rufe idanunta ta dinga min fad’a kamar ta cinyeni,wai ni mahaukaciyar ina ce da akan wannan dalilin na banza da wofi zan rabu da y’ata,a wane garin mahaukatan na tab’a ji an yi haka?kai ranar naga fushin Umma wanda ban tab’a gani ba,ta dinga kuka sosai tana fad’in ban kyauta ba na cutar da Hidaya,ni ma na dinga kuka ina kawo mata uzurina akan hakan,saboda na tsorata da su Alhaji Mudassir na san komai za su iya aikatawa,ranar dai haka muka kwana cikin kuka,da assssuba kuwa Umma ta d’auki waya ta kirawo mijin Sajida akan tana son ya kawo Sajida a lokacin tana son ganinta,yace shima har ya shirya zai yi wata tafiya shi da ubangidan sa da asubar, za su yi sati biyu ne a tafiyar ,amma bari ya kawota ita da yara sai ya wuce kawai,haka kuwa akayi,yana kawo su ita da yaran ta shi kuma ya wuce ya tafi,Umma ta zayyanewa Sajida komai,hankalinta ya tashi itama har da kuka tana min fad’an abin da na aikata,ni dai hak’uri na ba su akan duk abin da ya faru,sai kuma Umma tace tilas mu tashi mu nufi Kaduna a wannan asubar dan zuwa mu gano Hidaya,kuma tilas in bayyana mata kaina.

A wannan Asubar muka tawo Kaduna ni da Sajida,Umma ta dage sai ta bimu muka tausheta akan ta zauna tare da yaran Sajida mu kad’ai ma mun isa muje,da k’yar ta yarda ta bi mu da addu’a,shine fa muka dira Kaduna a wannan ranar kuma da wuri,saboda muna zuwa tasha muka samu motar da za ta tafi Kaduna ba da b’ata lokaci ba,

Ba k’aramin mamaki Hamza da Mahaifiyarsa suka shiga ba a lokacin da suka yi arba da ni cikin gidansu ina bayyana musu kaina,Hamza yayi kukan farinciki da murna yana kallona,da na nemi ganin Hidaya sai aka sanar dani jiya aka d’aura mata aure tana gidan mijinta,take kuma Umman Hamza ta bawa Hamza umarni kan yaje ya tawo da Hidayan da mijinta domin su ganni,shine Sajida ta bishi suka tafi,take kuma suka je suka tarar da abin da ya fallasa komai.

Umma ta sauke Numfashi tana kallon mutanen falon kowa kukan jin labarinta yake yi,yayin da Hidaya ta mik’e da hanzari ta nufeta ta fad’a kanta tana wani irin kuka tana kiran Abban ta,Khaleel kam k’urawa mahaifinsa ido yayi cike da tsantsar tsana da k’yama,Mummy har shid’ewa take saboda tsananin kuka,kafin ta d’ago kai tana rungume da Hidaya ta kalli Daddy ido cikin ido,wanda yake had’a uwar zufa cike da mad’aukakin tashin hankali mara misali,cikin tsana da k’yama ta ce masa.

“ALHAJI MUDASSIR,yau k’aryarka ta zo k’arshe! k’ila Allah yayi nufin tona asirinka ne shiyasa ya had’a auren d’an ka da y’a ta,kuma ya raba auren a dai dai lokacin da komai zai fallasa,kaine ka aikata komai! kaine ka kashe min mijina ! kaine ka sa na rabu da y’ata ta cikina tsawon shekaru! wannan duk sharrinka ne ! don haka na shirya tsaf domin yin shari’a da kai,duk da cewa d’anka Khaleel LAUYA NE,to zan gani zai bi bayanka ne ko zai bi bayan GASKIYA,ko a yanzu burina na farko ya cika,domin kuwa na tabbatar kud’in nan da kuke hank’oro har yanzu baku same su ba,suna in da na b’oye su tsawon shekaru,in da babu wani mahaluk’i da ya sani da ga ni sai ubangiji na,a yanzu kuma nake fatan burina na biyu ya cika,wato ganin bayanka da kai da azzalumin abokin ka wato MAUDE,dukkan abubuwan nan da suka faru kaine silar su MUDASSIR,kai ne ka kashe min MIJINA ka rabani da shi,bud’e baki kayi magana ko ba kai ba ne……?” Mummy ta k’ara she da daka masa wata muguwar tsawa.

Take Daddy ya mik’e a firgice ya rik’e kansa ya fashe da wani irin gigitaccen Kuka yana fad’in.

“Ni ne…..Tabbas Ni ne….Wallahi Ni ne na ……! 😳

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA CASA’IN DA UKU DA NA CASA’IN DA HUD’U

 

*Hassana D’an Larabawa Fan’s,ina godiya gareku da sharhin ku akan wannan littafi tare da addu’o’i na fatan alkairi da nake samu daga gareku,Allah ya bar zumunci ya saka da alkairi,ku cigaba da hakan ni kuma in sha Allah zan cigaba da faranta muku,Na gode masoyana* 👏😅🥰

BARKA DA JUMA’A 😍

 

***Kafin ma Daddy ya k’arasa maganar da yake tuni Khaleel yayi wuf ya mik’e cikin tsananin tashin hankali da gigita ya rik’o kafad’un Daddyn sa,idanuwansa na zub da hawaye masu zafi da k’una,kallon Daddyn yake cikin fitar hayyaci numfashin sa na sama sama tamkar zai d’auke,k’ok’arin magana yake amma ya gaza hakan,tuni idanuwansa suka soma shirin k’ak’k’afewa,sai gashi yana niyyar zubewa k’asa,babu wanda ya fara isa gareshi sai HAMZA,ya taro shi da hanzari yana zubewa a jikinsa,a tare suka kai k’asa Hamza na rungume da Khaleel d’in yana ambatar sunan sa da k’arfi yana tallafo fuskar sa domin ya kalleshi.
“Khaleel….” abin da yake ta ambata kenan,yana k’ok’arin Khaleel d’in ya bud’e idanuwan sa da suke lumshewa za su rufe,”Open your eyes Khaleel,don Allah ka bud’e idanuwanka ka kalleni nan kaji…..Hamza ke magana…Hamza abokin ka..!” a wani slow Khaleel ya fara bud’e idanuwan ya zuba su a fuskar Hamza ya k’ura masa idanu,sai kuma ya sake lumshe idanuwan wasu hawaye suka kwararo masa tamkar ruwa,Hamza ne ya saka hannuwansa yana tare hawayen Khaleel,tare da girgiza masa kai,cikin taushin murya ya sake ce masa.

“Ka daina kuka,kayi hak’uri da K’addarar ka”

Runtse idanuwa Khaleel yayi,da k’yar ya iya d’aga hannu ya rik’o hannun Hamza ya runtse cikin nasa hannun,sai kuma ya fara magana a hankali wadda bata fita sosai,amma shi Hamzan yana jin abin da yake cewa.

“K’addara ko…? Tabbas haka ne,na had’u da k’addarori masu zafi a rayuwa ta,ciki kuwa har da fushin da Abokina Hamza yake da ni,wannan ma k’addara ne ko?”

Girgiza kai Hamza yayi sannan ya ce.
“Hamza baya fushi da Khaleel, wata ajiyar zuciya Khaleel ya saki mai k’arfi tare da kwararowar hawaye,sannan ya k’ok’arta ya d’ago da taimakon Hamza ya mik’e zaune,duk hankalin mutanen parlour’n a tashe yake,wasu ma har sun mimmik’e tsaye ganin fad’uwar da Khaleel yayi,musamman da Hidaya ta zabura tana kuka ta isa gaban Khaleel d’in da Hamza ta tsuguna,idanuwan ta akan Khaleel d’in,had’a ido kawai Khaleel yayi da Hidaya,sai ya fashe da kuka ya sa tafukan hannayen sa ya rufe fuskar sa,cikin kwararar hawaye da rauni yace wa Hidaya.

“Don Allah kiyi min afuwa…kiyi hak’uri…wallahi kunyarki nake ji ko idanuwa bana son had’awa da ke…hak’ika da ni da mahaifina mun cutar da ku…mun gigita duniyar ku….mahaifina ya kashe miki mahaifin ki…wayyo Allah na …! Sai ya fad’a kafad’ar Khaleel yana wani irin kuka na tashin hankali yana dafe k’irjinsa da ke barazanar tarwatsewa.

Kowa na cikin palour’n kukan tausayin Khaleel yake yi,Hidaya kam ji take kamar ta janyo shi jikinta ta rungume shi,daren su na jiya na dawowa k’wak’walwarta da tarin soyayya da k’auna da ya gwada mata,kuka take sosai yayin da ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana jin ina ma mutuwa ta zo ta d’auke ta da wannan bak’ar rana da take gani a idanuwan ta.

Khaleel dai kuka yake mara misali,yayin da Hamza ke hawaye yana bubbuga bayansa alamar rarrashi,can Khaleel ya d’ago cikin hawaye ya dubi Hamza ya ce.

“Kaine fitilar da ke haskaka min gabana Aboki,duk wani duhu da zan fad’a k’ok’arin ka shine kaga ka fito da ni cikin haske,sannan kana yawan fad’a min girman iyaye da zaburarwa akan yi musu biyayya,wani lokaci kuma da ya sud’e kayi min nasiha akan GASKIYA,har ma kace min tana da matuk’ar amfani a duniya da lahira,domin ana shigar da masu yin gaskiya gidan aljanna,har kace min an tambayi Annabi ( S A W) menene aikin y’an aljanna?sai Annabi ya ce “GASKIYA” ,kuma kace min GASKIYA tana kub’utar da duk wani mai yin ta daga halaka,haka nan GASKIYA tana sa nagartar zuciya,tana gadarwa mai yin ta nutsuwa da kwanciyar rai,tana kub’utar da mai yinta daga afkawa cikin fitintunun rayuwa,ta kan zamewa mai yinta tushen aikata ayyukan alkairi,tana korewa mai yinta siffantuwa da munafurci,tana datar da mai yinta wajen hasashe da hangen nesa,tana k’arfafa hujjar mai rik’o da ita da kuma yinta,mai yinta yana samun yabo da kirari da kyakkyawan ambato daga mutane,duk wad’annan abubuwa mutum ba zai tab’a samunsu ba sai yayi rik’o da GASKIYA,Aboki ina so ka fito da ni Haske,shin Shin Mahaifina zan zab’a a wannan gab’ar ko kuma bayan GASKIYA zan bi?”

Hamza ya lumshe idanuwan sa,maganganun Khaleel sun tab’a ruhinsa,ya bud’e baki zai magana kawai suka ji muryar Daddy cikin kuka yana cewa.

“D’ana Khaleel kar ka bi bayana,ka bi bayan GASKIYA,domin ita za ta tseratar da kai,nima zan bi bayan GASKIYA,kuma ita za ta yi min jagora wajen sanar da ku dukkan wani abu da kuke son sani daga gareni,kuma na rantse da ubangijina zan fad’i GASKIYA,don haka kowa ya bud’e kunnuwan sa ya saurari wannan labari.

 

 

 

*******************

 

Na kasance mutum mai son zuciya da son abin duniya,wannan hali na wa munyi tarayya akansa ni da Abokina Alhaji Maude,domin shima haka yake,ko in ce har ya fini,duk abin da za mu yi bamu fiya saka Allah da GASKIYA a lamarin mu ,wannan shine ya janyo duk wasu ayyuka da za mu gabatar babu imani a cikin su.

Alhaji Taufik’ yayi mana komai a rayuwa! duk wani abu da muke tak’ama da shi ta silar sa muka same shi,bawan Allahn nan ya kan hana kansa wani abun domin ya bud’a mana mu samu,amma maimakon mu tsayar da GASKIYA da AMANA a lamarinmu sai muka k’i,muka dinga bin son zuciya muna aikata b’arna kan duk wata kwangila da yake nemo mana,yayi mana uzuri babu adadi,kullum nasiha yake mana a k’ok’arin sa na mu zama mutanen kirki,amma muka shafawa idanuwan mu toka muka k’i saurarensa da Gasgata shi,ko ni na so nabi tsarinsa sai Maude ya dankwafeni,akan gara muyi abinda muke so,ko domin mu zo mufi Alhaji Taufik’ d’in kud’i,tunda yayi mana zarra nesa ba kusa ba.

Babu wani mutum da ya tsaye mana a rai irin SULAIMAN,domin mun gane cewar da shawarwarinsa Taufik’ yake amfani,shiyasa a lokacin har Taufik’ d’in yake neman d’aga mana jan kati domin fatattakarmu cikin sha’aninsa,akan hakan muka nemi Sulaiman domin mu janyo ra’ayinsa ya goya mana baya,sai ya nuna mana cewar shifa ba zai bi bayan K’ARYA ba,bayan GASKIYA zai bi,wannan ta sa muka k’ara k’ullatarsa,musamman ni da na fito masa da tsanata a fili,sab’anin Maude da ya b’oye muguntarsa a zuciyar sa.

A wancan zamanin abubuwa sun cigaba da tafiya ne ba yadda muke so ba,tunda kuwa babu dad’ewa da Taufik’ ya zare hannuwansa daga lamuran mu sai gashi mun fara fuskantar matsaloli,komai ya fara rincab’e mana,abubuwa suka fara yi mana zafi,babu ta in da muke samun kwangiloli Taufik’ ya toshe mana duk wata k’ofa da zamu dinga samu,hujjarsa kuwa ita ce,bama yin aiki da GASKIYA,kuma duk abinda za mu samu cikin aikin da za mu yi kusan haramun muke ci,to shi yana karemu daga cin haram ne saboda haram ba zai cecemu a lahira ba,gara mu rasa a duniya da muyi asarar lahirar mu,wanda mu duk bamu fuskanci abinda yake nufi ba,idan ma mun fuskanta to mun take Gaskiya,gani muke kawai Hassada da bak’inciki yake mana,baya son cigabanmu ne.

Watarana Alhaji Maude ya kirani akan shifa ya fara gajiya da ganin Taufik’ a doron k’asa,ya kamata mu san yadda zamu salwantar da rayuwarsa mu shafe babinsa,nan da nan na bashi goyon baya,sai dai na cewa Maude kar a kashe Taufik’,ni duk zaluncina ba zan iya kashe mutum ba,a dai san yadda za a yi kawai a b’atar da shi a doron k’asa,amma ban da kisa,nan Maude yayi wani murmushi,yace min na bar komai a hannusa shi zaiyi maganin abun.

Kwana biyu da hakan na samu labarin Oga Taufik’ ya kwanta rashin lafiya,wadda ya zama baya ji baya gani balle tafiya,ina jin wannan na san aikin Maude ne,ashe kuwa hakane,dan kirana yayi yana shek’a dariya yana ce min “Mudan mutuminka fa ya zama dukunu,kuma saura kad’an na k’are masa gudu” nima na shek’e da dariya sannan nace masa”Hakan ma yayi Maude,amma dai ba kashe shi za a yi ba ko?dan bana son kisa ya shigo lamarin mu,hakkin rai ba k’aramin abu bane”sai Maude ya ce min”Kar ka samu damuwa ba kashe shi za a yi ba,kurciya me dogon zango zan sa ayi masa,nan da kwanaki k’alilan za a manta da tarihin wani Taufik’ gabad’aya” Muka kwashe da dariya muka tafa muna jin dad’i.

Kwanaki k’alilan da hakan kawai naji zancen an sace Taufik’ ,ma’ana an neme shi an rasa,ina shirin kiran Maude a waya sai ga wayarsa ta shigo,da hanzari na d’aga ina tambayar sa abinda ke faruwa,sai ya shek’e da dariya yana fad’in”Mudassir na gama cika aiki,ka shirya yanzu zan zo na d’auke ka mu tafi gidan Taufik’ yin Jaje,domin kurciya me dogon zango ta tabbata a gareshi” Wani irin dad’i ya mamayeni,na dinga shek’a dariyar murna,nan Maude yake ce min idan mukaje gidan mu dinga nunawa kamar Sulaiman ne ya b’atar da Taufik’,domin shi ya kamata mu lik’awa sharrin tunda duk shine sanadin da yasa Taufik’ yayi fushi damu,tunda da shawarar Sulaiman yake amfani.

Aikuwa hakan ce ta tabbata kamar yadda Zainab ta fad’a,tabbas mun fad’awa Sulaiman bak’ak’en maganganu a ranar,mun bi shi da sharruka kala kala akan muna zarginsa da sace Taufik’,muka yi muka gama yana zaune yana kuka baice mana uffan ba,sai da muka juya muka fito muna dariya da hirar yadda aka yiwa Taufik’ kurciya me dogon zango,ashe bamu sani ba Sulaiman na bayanmu kuma duk yaji abin da muka tattauna,wannan ya saka mu cikin tsananin tashin hankali da tunanin wace mafita garemu?domin komai zai iya faruwa idan muka yi sake.

Muna tafe a mota sai zufa nake yi,Alhaji Maude ne yake tuk’a motar amma shi sai na lura hankalinsa ma a kwance yake,cikin wani irin yanayi na fara fad’a masa cewar ni dai nayi danasanin abin da muka yi,yanzu gashi tun ba a je ko’ina ba asirinmu yana neman tonuwa,nan Maude yayi wani murmushi mai kama da na mugunta,sannan ya ce min” Haba Mudassir kar ka bani kunya mana,wannan d’an abin ne zai tashi hankalinka?kawai dan wannan k’aramin alhakin yaji sirrin mu?ka zuba idanu ka gani shima a yau d’innan zan sa a gama min da shi,domin ba zai kai labari ba”

A tsorace na dubr shi ina fad’in “Ba dai kashe shi zaka yi ba ko?nifa na fara tsorata Maude,gara mu ajiye makamanmu wallahi,idan ma asiri kasa aka yi wa Taufik’ aka neme shi aka rasa to gara kaje ka sa a warware shi kawai ya dawo,gara mu hak’ura kawai saboda zuciyata ta fara rawa akan aikata wad’annan munanan ayyuka,iya rashin Gaskiyar mu da hassadarmu ta ishemu ba sai mun had’a da salwantar da rai ba Maude,mu fa musulmai ne,kar muje mu rasa imaninmu gabad’aya”

Nan da nan naga fuskar Maude ta sauya,hankalinsa ya fara tashi saboda ina neman in mana sakiyar da babu ruwa a wannan lamari,take ya sauya fuska ya fara karantomin dad’in baki,wai idan har na bijire a wannan gab’ar to k’arshen mu yazo,domin Sulaiman zai iya fallasa mu ga hukuma,kuma idan akayi bincike tilas a gano mune muka shirya komai,a likacin ne za mu kwashi kashinmu a hannu,dan haka na maida hankali kawai muyi abinda ya kamata,in yaso daga baya sai mu tubarwa Allah kawai,haka Maude ya isheni da dad’in baki har na aminta da maganarsa,yace min in bar komai a hannunsa,shi dai yayi min alk’awarin babu kisa alamarin,tunda bana so,amma zai bi duk hanyar da zai bi domin ganin komai ya wakana cikin sauk’i,a haka muka rabu,yaje ya saukeni a gidana shi kuma ya wuce domin tsara yadda zai tunkari lamarin.

Allah shine shaidata,kuma nayi alk’arin fad’in GASKIYA, duk da na san cewar ba lallaine ku aminta da abinda na fad’a ba ko wanda zan fad’a yanzu,amma ni dai na san GASKIYA zan fad’a,ko da za ta kasance min kalami na k’arshe da zanyi a rayuwata.

Daddy ya Numfasa cikin zubar da k’walla mai zafi,ya kalli Mummy da tunda ya fara magana idanuwanta na kansa cikin wani kallo na muguwar tsana,ba Mummy kad’ai ba kowa ma Daddyn yake kallo,shi kam Daddy cigaba yayi da kallon Mummy kafin ya sake bud’e baki ya cigaba da cewa.

“Zainab….Na rantse da Allah ba ni nasa aka kashe Mijinki ba…ba ni na kashe Sulaiman ba…hasalima ni ban san Sulaiman baya doron duniya ba…ban san an kashe Sulaiman ba duk tsawon wannan lokacin…
Na san duk wannan sharrin Alhaji Maude ne ya k’ullashi,ya aikata wannan abun da sunana domin ki tsaneni Zainab,domin duniya tayi Allah wadai dani,domin ba tun yau ba na fara fuskantar Maude ba don Allah yake sona ba,abotar da muke yi ba don ALLAH da GASKIYA da AMANA ya d’auketa ba,sai don shima ya cimma wani k’uduri na sa a kaina.Wallahi Zainab a washegarin da kika ce an kashe Sulaiman da kaina na samu Maude akan ya ake ciki?sai yace min in kwantar da hankalina angama komai,daga Sulaiman har iyalensaya sa an musu kurciya me dogon zango,ban tab’a fahimtar wannan yaren na sa na KURCIYA ME DOGON ZANGO ba sai yau,ashe abinda yake nufi ya kashe Sulaiman,kuma na tabbatar shima Taufik’ ya sa an kashe shi ne,tunda har wa yau ban k’ara jin labarinsa ba,duk kuma lokacin da na cewa Maudw ina son ganin Taufik’ domin na nemi afuwarsa sai dai yayi dariya ya share zancen baya bani amsar komai akan hakan,ashe ni ban sani ba Maude ya kashe Taufik’ da Sulaiman,kuma yayi amfani da sunana wajen fad’in ni na aikata hakan,innalillahi wa inna ilaihir raji’un…Tabbas Maude ya ci amanata…sannan ya ci amanar abotar mu….!

Daddy yana zuwa nan ya fashe da wani irin kuka,fad’i yake “Wallahi Zainab ba ni na kashe miki Sulaiman ba…ban san me nayi wa Maude ba da ya nana min wannan sharri me girma haka…me yasa yayi min haka bayan ni na rik’eshi Aboki…ashe shi ba da zuciya d’aya yake zaune da ni ba…yanzu wannan shine sakayyar abotar da muka yi ni da shi kenan?”

Kafin kowa yayi magana HAMZA ne ya fara mik’ewa tsaye,idanuwan sa na zubar da hawaye ya dubi Daddy,sannan ya d’aga d’an yatsansa sama yayi magana da babbar murya,kowa ya zubawa Hamza idanu suna jin abinda yake cewa.

“Na rantse da ubangijina,Abota ta k’warai da tasirinta ga mutum tana tabbatuwa a gareshi muddin an ginata akan GASKIYA NE,ayoyi da yawa a cikin alk’ur’ani sun bayyana mana wajabcin rik’ar abokan k’warai da yin watsi da miyagun abokai,a ko yaushe mutum mai hankali ya kan gujewa miyagun abokai kamar yadda ake gujewa zaki saboda ya san babu alkairi a tare da shi,kuma duk wanda ke zama da miyagun abokai to ya had’u da tab’ewa,bisa ga misali,Daddy kalli fad’in Allah mad’aukakin sarki inda yake cewa.

“و يوم يعض الظالم على يديه يقول يليتنى اتخذت مع الرسول سبيلا. يويلتى ليتنى لم أتخذ فلانا خليلا. لقد أضلنى عن الذکر بعد إذ جاءنى وکان الشيطن للإنسن خذولا.”
Fassarar ayar(Ranar da azzalumi zai rik’a cizon yatsansa yana cewa”kaicona ! ina ma na bi hanya tare da manzo! kaicona ! ina ma da ban rik’i wane aboki ba?hak’ik’a ya b’atar da ni daga bin Alk’ur’ani bayan ya zo min” kuma shaid’an ya kasance mai tab’ar da mutane ne).

Sannan Manzon Allah (S A W) ya tsawatar mana akan zama da miyagun abokai.Kamar hadisin da aka karb’o daga Abu musa Allah ya yarda da shi ya ce: Hak’ik’a Manzon Allah (S A W) ya ce: “Kwatankwacin zama da abokin k’warai da miyagun aboki kamar zama da mai sayar da turare ne da zama da mak’eri,shi dai mai sayar da turare ko dai ya sammaka,ko ka siya,ko kuma kaji k’amshi.shi kuwa mak’eri ko dai ya k’ona maka sutura,ko kuma ka ji k’auri” Bukhari da muslim ne suka rawaito shi.
Duk abubuwan da suka faru da kai Daddy babban tushensu shine rashin samun Aboki na gari,tarayya da mugun aboki ya janyo maka fad’awa cikin wannan yanayi,abota ta k’warai daga mutanen kirki take,masu hankali da nagarta wad’anda za su dinga taimaka maka akan GASKIYA kuma suna nuna maka ita,kai ne ka zalunci kanka Daddy,domin ubangiji ba mai zaluntar bayinsa ba ne.

“من عمل صلحا فلنفسه.و من أساء فعليھا .و ما ربك بظلم للعبيد”

(Duk wanda yayi aiki nagari ,to kansa ya yi wa,wanda kuma ya munana kansa yayi wa,ubangijinka ba mai zaluntar bayi ba ne).

Gabad’aya mutanen da ke zaune sun had’a baki ne wajen fad’in “ALLAHU AKBAR” tare da jinjinawa Hamza wajen fad’in GASKIYA.Sai Hamza ya cigaba da magana yana kallon kowa.

“Ni na gasgata Daddy…kuma kuma ina son ku gasgata dukkan abin da ya fad’a..na hangi tarin GASKIYA cikin idanuwan sa da kalamansa..magana ta k’arshe shine,za mu sa ayi bincike ta b’angaren Shari’a akan Alhaji Maude,kuma zai shiga hannun hukuma nan ba da jimawa ba,domin abi kadin duk wani abu da ya aikata,ni nayi Alk’awarin zan d’auki nauyin komai a hannuna”

Da hanzari Khaleel ya mik’e ya iso gaban Hamza ya kama hannuwansa ya rik’e,girgiza kansa yayi sannan yayi magana ya ce.

“Tun lokaci mai tsawo kake amsa Sunan GARKUWAR HIDAYA ABOKI,don Allah nima ka bani wannan damar ko sau d’aya,ni ma ina so na amsa sunan GARKUWAR HIDAYA ko sau d’aya ne”

Sai Hidaya ta taso ta tsaya a gabansu, cikin kuka take duban Ya Hamza da Uncle Khaleel,tayi magana cike da rauni.

“Uncle Khaleel kana so ka zama GARKUWATA kamar yadda Ya Hamza ya zama ko?”

Da sauri ya amsa mata da “Tabbas ina so” yana kwararar da hawaye.

Sai ta sunkuyar da kanta k’asa ta ce.

“To ina so duk inda Alhaji Maude yake ka sa a kamo shi,da duk wani mai hannu cikin kisan Mahaifina da Alhaji Taufik’,a gurfanar da su gaban shari’ah,sannan ka tsaya min a matsayinka na LAUYA har mu samu nasara a yanke musu hukuncin da ya dace da su,muddin ka aikata haka to tabbas ka zama GARKUWAR HIDAYA”

Kafin ma Khaleel yayi magana sai suka ji muryar Daddy cikin tabbatarwa yana ce wa.

“Ni kuma zan baka goyon baya D’ana Khaleel,domin cikawa Hidaya burinta,duk da na sani har da ni cikin wad’anda hukunci zai hau kansu,amma na zab’i GASKIYA kuma ita zan bi,k’ila ita ce aikin da zan yi wanda zai zame min kaffarar laifukana na baya…!

Sai Khaleel ya matsa jikin mahaifinsa ya rungumeshi,take suka fashe da kuka mai cin rai,yayin da ragowar mutanen da ke zaune kowa ke kuka hawaye na zuba.

 

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA CASA’IN DA BIYAR DA NA CASA’IN DA SHIDA

 

*SHAFIN YAU ME YAWA NE,IDAN KUNJI DAD’INSA TO KUYI SHARHI ME MA’ANA*👇😉

 

***Ranar haka ta kasance musu babu Wanda ya samu nutsuwa a cikinsu,kowa da abinda ya addabi zuciyar shi,Daddy yayi nadama sosai,har yake ji a zuciyarsa ina ma bai san Alhaji Maude ba,ina ma bai biyewa son zuciya ya aikata abubuwan da suka faru a baya ba,da yana da yadda zaiyi da ya goge tarihin baya,amma babu yadda zaiyi,alk’alami ya riga ya bushe.

Kwana biyu da hakan Mummy da Aunty Sajida suka yi shirin tafiya Gombe,kuma tare da Hidaya za su tafi,hakan yasa Umma da Hamza su ma suka ce da su za a yi wannan tafiyar,ko domin suje suga kakar Hidaya,amma Umma ta k’udure a ranta ko sunje Gombe tare da Hidaya zata dawo,zata rok’i Mummy alfarmar ta bar mata Hidaya a wajenta,ko domin sabon da tayi da ita,duk da tana ji a zuciyarta anya idan ta aikata hakan tayi adalci kuwa?kamata yayi ta bar Hidaya da mahaifiyarta su zauna tare,ko domin dad’ewar da suka yi ba tare da juna ba,ta san dole ne za su yi mararin juna,kuma za su so kasancewa tare da juna a koyaushe.

A motar Hamza suka yi tafiyar,shine zai tuk’a motar yayin da Hidaya ke zaune a gefensa,sai kuma Umma da Mummy da Aunty Sajida da ke zaune a gidan baya,Khaleel ya so ya bisu,abubuwa biyu suka yi masa shamaki,na farko yana son zama domin kammala bincike kan Alhaji Maude da kuma shigar da k’ara da yake son yi a kotu,na biyu kuma nesanta kansa da yake so yayi da Hidaya,domin tabbas ganinta yana tayar da hankalinsa ba kad’an ba,wani irin sonta yake ji a cikin zuciyarsa,kuma ita ma ya lura tana jin soyayyar shi a ranta,sai dai Soyayyar ba zata yi musu amfanin komai ba,wannan dalilin ya sa ya hak’ura da bin su,illa fatan alkairi da ya bisu da shi.

Cikin ikon Allah suka isa garin Gombe,suka tarar da tarba mai kyau daga kakar Hidaya,domin kamar ta goya su,ta rik’e Hidaya k’am a jikinta tana hawayen jin dad’i da murna,sai ga dangi na nesa da na kusa duk sun hallara domin ganin Hidaya,sai ga Hidaya na kuka sosai,kukan ganin danginta,kukan godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana mai matuk’ar muhimmanci a tare da ita.

Kwanansu uku a Gombe,sunji dad’in garin sosai saboda karamcin mutanen garin,haka Aunty Sajida da yaranta suka dinga zagayawa da Hidaya da Umma cikin gari gidajen y’an uwa da abokanen arzik’i,tabbas Hidaya taga gata,kuma taji dad’in hakan,ta samu kanta cikin walwala sosai,duk da akwai abinda yake mintsinin zuciyarta,wato soyayyar Khaleel da ke addabarta,duk dare ba ta iya bacci sai tunaninsa da kuka,gashi ba ganinsa take ba,ko muryarsa ma bata ji,har gwada kiran wayarsa take ko domin taji muryarsa amma kullum wayar bata shiga,mamaki ya kan baibayeta ,burinta ta samu Ya Hamza ta tambayeshi dalilin da yasa bata samun lambar Uncle Khaleel d’in.

A kwana na biyar ne da zuwan su Hidaya ta shiga d’akin da aka sauki Hamza da sallamar ta,fura Mummy ta dama masa shine ta bawa Hidayan ta kai masa,zaune ta tarar da shi da waya a kunnensa yana magana fuskarsa d’auke da murmushi mai k’ayatarwa,ajiye furar tayi ta nemi gefe ta zauna tana kallonsa,ambatar sunan Khaleel da yayi shine ya saka ta zabura jikinta na rawa alamar murna,ta tsurawa Hamza idanu tana wani irin murmushi mai kyau,cikin azarb’ab’i da saurin magana ta ce.

“Lah ! Ya Hamza da Uncle Khaleel kake magana?Don Allah Ya Hamza ina son jin muryar shi,bani shi mu gaisa”

Sanya mata ido kawai Hamza yayi ganin yadda jikinta ke rawa duk ta wani firgice,sai mik’a masa hannu take tana yarfewa alamar ya bata wayar,lumshe idanuwa yayi ya sauke ajiyar zuciya kafin cikin sanyin murya ya ce wa Khaleel.

“Khaleel ga Hidaya a kusa da ni,bari na bata wayar ku gaisa”

Daga can Khaleel ya d’auke wuta gabansa na tsananin fad’uwa,ambatar sunanta kad’ai sai da ya sanya shi cikin wani yanayi,ya san yana jin muryar ta to sai ta tono masa mikin da ke zuciyarsa,k’ila ko bacci ba zai samu a daren ba,hakan ya sa cikin sauri yace wa Hamza.

“Aboki wani aiki ya taso min yanzu na hanzari,idan nace zan tsaya gaisawa da ita zan b’ata lokaci,kawai mik’a min gaisuwa ta zuwa gareta tare da fatan alkairi” yana fad’in hakan kafin ma Hamza yayi wani yunk’uri tuni ya kashe wayar sa,ya bar Hamza da waya a kunne yayi sakato da shi.

Hidaya na jiran ya mik’o mata waya sai gani tayi ya sauke wayar ya ajiye ta gefe yana sauke numfashi,bin shi da ido tayi alokacin da shima ya d’ago kansa suka had’a idanu,ganin yadda take kallonsa sai ya d’an lumshe idanu yana shafa kansa ya ce.

” Ya kashe wayar” Zaro idanuwa tayi,sai ga hawaye sun cicciko idanun,kautar da kai Hamza yayi yana cewa,” Amma ya ce min in gaisheki…kuma yana miki fatan alkairi..wani d’an uzuri ne ya taso masa da ya hana ganawarku a yanzu”jijjiga kai Hidaya tayi Hawayen na sakko mata,ta sanya bayan hannunta ta goge,sannan ta mik’e a hankali domin barin d’akin,har ta kai bakin k’ofa taji muryar Hamza ta kira sunan ta.

“Hidaya” tsayawa tayi cak kafin ta waiwayo duk jikinta a sanyaye, ” Zo nan kinji” abinda yace da ita kenan yana gyara zamansa kan daddumar da yake zaune,takowa tayi a hankali ta iso gabansa,sannan ta tsuguna kanta a sunkuye tana wasa da yatsun hannun ta idanuwan ta cike da hawaye.

Kallonta yake sosai kafin ya k’ara ambatar sunanta,ta d’ago idanuwan ta ta jefa cikin na sa,saiga hawaye yarrrrrr sun biyo kuncinta,k’irjinsa yayi wata irin harbawa,har ga Allah baya son damuwar wannan baiwar Allah,cikin muryar jimami da rauni ya ce mata.

“Me ya saka ki kuka?ko wani abu na damun ki ne?”

Girgiza kai tayi hawaye na yarari a fuskarta,sai shi ma ya girgiza kan,ka na ya sake cewa.

“Ah ah Hidaya,tabbas akwai abinda yake damun zuciyarki,kawai dai ina tunanin kin sauya min matsayi ne,kin canja ni a matsayin wanda kike fad’awa damuwarki har ya baki shawarar da ta dace ko?Hidaya duk wani yanayi da zaki shiga ina fuskantar sa,kin sani tun kina yarinya na gama karantarki,ko motsi kika yi na kan gane abinda yake nufi,yanzu ma fuskarki da yanayinki sun karantar da ni damuwar da kike ciki,da zaki taimaka da kin fad’a min,k’ila akwai wani abu da zan iya taimakawa da shi domin kawar da damuwar”

Kawai Sai Hidaya ta fashe da kuka jin maganganun Hamza,ta sanya kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka me had’e da shesshek’a mai tab’a zuciya,to ita yanzu me zata ce masa?bud’e baki za ta yi ta fad’a masa cewar Soyayyar Khaleel ce ke addabarta?ko ce masa za ta yi tunanin Khaleel ke damun ta?ko kuwa kewar Khaleel na neman hallakata?duk ciki babu wanda zata iya kallon tsabar idanun Hamza ta fad’a masa,domin ita kanta ta san akwai babban shinge tsakaninta da Khaleel,wani shinge mai matuk’ar girma da zai hana wanzuwar komai a tsakaninsu.

Kukan da take sosai yake tab’a ruhin Hamza,yayi shiru yana sauraren ta tare da runtse idanuwan sa,ta d’auki tsawon lokaci tana ta kuka ba tare da ya dakatar da ita ba,ya barta tayi abinta ta k’oshi,a ganinsa kukan zai yaye mata wata damuwar,shiyasa baiyi k’ok’arin hanata ba,sai dai shima yana jin tamkar ya fashe da kukan,saboda raunin da zuciyarsa tayi,sai da yaji ta d’an tsagaita sannan yayi magana cikin sanyin murya.

“Hidaya kiyi hak’uri…kiyi hak’uri…kiyi hak’uri…ita rayuwa daman haka take,ba ko yaushe mutum yake jin dad’i a cikinta ba,akwai tarin k’alubale da k’addarori da jarrabawa,hak’uri da juriyar da mutum zai yi matakin nasara ne,taki damuwar kawai kika sani Hidaya,amma wallahi da zaki san damuwar wasu to tabbas za ki ga taki k’arama ce akan ta su,na san zaki ta cewa shi wannan Hamzan kullum bashi da magana sai ta Hak’uri,to kar kiyi gajen hak’uri ki dai k’ara hak’urin,wallahi duk wanda yayi hak’uri ya had’a da addu’a ba zai tab’a tab’ewa ba Hidaya,tashi kije,kuma ki cigaba da hak’uri da addu’a”

Share hawayen ta tayi,sannan ta mik’e a hankali ta fice,maganganun Ya Hamza na yawo a kanta,har ta fice idanuwan sa a kanta,sannan ya lumshe idanuwa yana d’an sakin wani murmushi k’arami,a ransa yake cewa”Hidaya kenan ! damuwarta kad’ai ta sani,bata san damuwar da ke ran wasu ba”bud’e idanuwan sa yayi ya k’urawa sili ido,a hankali ya furta cewar.

“Allah ka magancewa duk wani musulmin duniya damuwar da take ransa….!”

 

 

 

****************

 

Kwanansu Bakwai da zuwa Gombe suka yi shirin komawa Kaduna,ko dan saboda aikin Hamza da yake ta fashin zuwa,dan ma ya d’auki uzuri a wajen aikin shiyasa bashi da wata damuwa,Umma ta kasa yiwa Mummy magana akan tana so Hidayan ta bisu,ita ma kuma Mummyn bata yi mata zancen ba,hakan yasa Umma da Hamza ne kawai ke shirin komawa babu Hidaya da zata zauna na wani d’an lokaci domin shak’uwa da danginta da kuma mahaifiyar ta.

Har bakin mota suka yi musu rakiya,godiya dai da fatan alkairi Umma da Hamza sun sha a wajen dangin Hidaya har kunya suka dinga ji,haka nan sun samu alkairai masu yawa wasu ma k’in karb’a suka yi saboda yawan abubuwan,sai ga Hidaya na kukan rabuwa da su,shi Hamza ma kasa tsayawa yayi yaga kukan ta ya shige mota ya zauna,sai Umma ce ta dinga lallashinta ita ma har da nata hawayen,ta dinga lallab’ata akan tayi hak’uri ba dad’ewa zata yi a Gombe ba,da zarar komai da Khaleel yake yi ya kammala dole su tattaro su dawo Kaduna ko domin fuskantar Shari’ar da ke gabansu,hakan ya sa Hidaya ta rage damuwarta har tayi murmushi,Umma taji dad’i ta rungumeta,daga nan kuma suka saki juna Umma ta zagaya ta shiga mota,sai Hidaya ta matsa inda Hamza ke zaune b’angaren tuk’i ta d’an lek’a shi,yana zaune wayarsa na hannunsa yana danne danne,sai da ta ambaci sunansa sannan ya waiwayo a hankali ya amsa yana duban ta,sai tayi k’asa da kanta tace masa.

“Ya Hamza Allah ya tsare hanya,Allah ya sauke ku lafiya,don Allah a mik’a min gaisuwata zuwa ga Uncle Khaleel kafin na dawo”

Murmushi me kyau ya sub’uce masa,ya tura wayarsa cikin aljihu ya jinjina kai yana fad’in.

“Sak’onki zai isa in sha Allah,amma banji kin ambaci Hansa’u da Sumayya ba,ko su kin manta da su ne?”

B’ata fuska tayi tana marairaicewa kafin ta kalleshi tace,” To ai su fushi nake da su Ya Hamza,munyi fad’a na daina kula su ma”

Hamza ya d’anyi dariya,har sai da Hidaya ta k’ura masa idanu saboda kyawun da taga ya k’ara a idanuwan ta,jerarrun hak’oransa farare tas sun bayyana sai d’aukar ido suke,cikin dariyar ya ce.

“Da alama sun miki wani laifi kenan?to ina neman musu afuwa da yafiya,kiyi hak’uri ki yafe musu”

Sai ta jijjiga kai tare da matsawa daga jikin motar,domin ta basu damar tafiya,a hankali tana kallonsa ta ce,” Sun ci darajarka Ya Hamza,wallahi da zan jima ban k’ara duban wata yarinya a cikinsu ba”
Dariya ya sake yi yana k’ok’arin tashin mota da hannu d’aya,d’aya hannun kuma ya d’ago shi yana mata jinjina irin ta sarakai,fuska a washe yake ce mata “Sannu Babba,Allah dai ya k’ara Girma” Maganarsa ta bawa Hidaya dariya,take kuwa ta fashe da dariya tana rufe fuskarta,Umma ma na gefe zaune kusa da Hamza tana murmushi,har Hamza ya tashi motar yana murmushi suka soma tafiya,yayin da Hidaya take ta d’aga musu hannu murmushi d’auke akan fuskarta,sai Hamza yake ta jin dad’i akan ya tafi ya barta cikin nishad’i ba cikin damuwa ba.

 

 

 

***************

 

Cikin ikon Allah kwanakin da suka shud’e tuni Khaleel ya kammala shirye shiryen komai da had’a bayanai,kuma har an shigar da k’ara kotu,in da Mummy ta so jagorantar Shari’ar,amma Hamza ya ce ta bari wani Alk’alin yayi,saboda ita dole zata kasance lamba ta farko wajen bayar da shedar duk wasu abubuwa da suka faru a zamanin na baya da ya shud’e.

Rana d’aya Alhaji Maude da Alhaji Mudassir suka samu takardar sammaci daga kotu,take kuwa Maude ya kira Daddy yana zayyana masa wai an kawo masa sammaci daga kotu,Daddy da ke jin haushinsa sosai yace masa shima ya samu sammacin,dan haka sai suyi shirin shiga kotu kawai,domin a bajeta a fai fai,ya kashe wayar ya bar Maude da waya a hannu baki a sake.

Ana saura kwana d’aya shiga kotu,sai ga tawagar mutanen Gombe sun iso,Mummy ce da Aunty Sajida,sai kuma Mahaifiyar su,tare da Hidaya da tayi wani mugun kyau kamar wadda taje k’asar waje,jikinta har wani shek’i yake yi tayi b’ul b’ul da ita,duk da bata yin k’iba amma ta murje sosai,har k’ofar gida mota ta kawo su ta dire,suka firfito suna sakko da kayansu,Hidaya murna duk ta cika ranta,ko tsayawa kwasar kayan baya yi ba ta ruga domin shiga gidan da d’an gudunta.

Lokacin ne Hamza da Khaleel ke k’ok’arin fitowa daga cikin gidan,Khaleel na korawa Hamza bayanin yanda Shari’ar za ta kasance a gobe,suna sanyo kansu cikin zauren Hidaya ma na shigowa da d’an gudunta,su za su fito ita kuma za ta shiga,saura kad’an su zabga karo suka ankara suka yi baya da sauri idanuwan su a waje,ita ma ja baya tayi tana sauke wani irin numfashi kafin ta d’ago kanta idanuwan ta su fad’a cikin na Uncle Khaleel,take taji wani irin abu ya tsirga mata,musamman da taga yayi wata muguwar rama yayi duhu,duk ya sauya mata saboda ta d’auki tsawon lokaci bata ganshi ko ta ji muryar shi ba,a k’alla kuwa za a yi wata biyu kan na uku,domin a yanzu mutuwar auren su suna cikin wata na uku ne,wani irin kallo suke wa juna tamkar za su had’e,Khaleel na had’iyar wani yawu me d’aci da ya cika bakinsa,kai gaskiya ya tafka babbar asara,rashin Hidaya a gareshi ba k’aramin gib’i ba ne,shi kad’ai ya san halinda zuciyarshi take ciki.

Abin da ya d’agawa Hamza da Khaleel hankali bai wuce ganin Hidaya da suka yi ta dafe kanta da hannu d’aya ba,d’aya hannun kuma ta rufe bakin ta tana wani irin yunk’uri,cikin firgita Hamza ya dubeta a rikice yana fad’in ” Ke lafiya..?me ya sa m….

Kafin ma ya kai k’arshen maganarsa sai gani suka yi Hidaya tayi k’asa ta durk’ushe,take ta fara kelaya wani irin amai na tashin hankali tana yunk’uri kamar ta amayo y’ay’an hanjinta,matsowa suka yi gareta dukkansu suna sunkuyawa zuwa gareta cikin tashin hankali,sannu kawai suke jera mata yayinda ta kasa amsawa sai yunk’uri take tana kelaya amai,tuni hawayen wahala ya wanke fuskarta saboda rad’ad’in da take ji a k’irjinta na yunk’urin da take yi,a lokacin ne kuma su Mummy suka k’araso cikin zauren,sai suka tsaya turus suna duban Hidaya da ke durk’ushe tana amai,ga kuma Hamza da Khaleel tsugune gabanta sai jero mata sannu suke yi.

Hamza ke tambayar Mummy a rikice”Wai daman Hidaya bata da lafiya ne?” Aunty Sajida ce ta bashi amsa da cewa”Lafiyar ta k’alau muka tawo wallahi” Mamakinsu bai wuce yadda aman yak’i tsayawa ba,sai wani irin yunk’uri take yi ga juyawar da kanta ke yi,wani irin jiri take ji kamar za ta kife a wajen,ganin haka sai suka tsorata sosai,Khaleel yace gara a tafi asibiti a duba halin da take ciki,irin wannan mugun amai lokaci guda akwai tashin hankali.

Aunty Sajida ko hutawa bata yi ba ta rik’e Hidaya da idanuwan ta ke lumshewa tsabar wahala,suka yi waje,yayin da Hamza da Khaleek suka rufa mata baya,Khaleel ya janyo motarsa cikin rawar jiki,ya bud’ewa Aunty Sajida bayan motar suka shiga ita da Hidaya sai jera mata sannu yake yi,shi da Hamza suka shiga gaban motar,nan da nan Khaleel ya figi motar cikin hanzari suka nufi asibiti.

Ita dai Umma sai ganin su Mummy tayi kawai,ta tare su cikin murna da kulawa,sai da suka zauna take tambayar Ina Hidaya da Sajida?nan Mummy take fad’amata dukkan abinda ya faru yanzu daga zuwansu,take hankalin Umma ya tashi ta fara neman hijab wai za ta bisu asibitin,sai da Mummy ta dinga tausarta akan tayi hak’uri ta zauna tunda sun tafi,ta tabbatar ba za su jima ba yanzu za su dawo,kuma in sha Allahu Hidayan za ta samu lafiya.

*********

Zaune suke a gaban Likitan suna jiran jin bayaninsa,bayan zuwan su an d’auki jinin Hidaya da fitsarin ta domin a gwada,Sannan kuma an jona mata drip saboda yawan aman da tayi,tana kwance a d’akin da aka jona mata ruwan bacci ya kwasheta cikin wahala,yayin da Aunty Sajida take lura da ita,su kuma suna can office d’in likita zaune suna jiran sakamakon ya fito dan sanin abinda yake damunta.

Cikin lokaci kad’an kuwa sai ga shi an kawowa likitan sakamakon,ya karb’a ya sanya glass d’in sa yana dubawa,take suka hangi fuskarsa d’auke da tarin murmushi mai k’ayatar wa,su kam a rikice suke,har rige rigen tambayarsa suke yi wai shin me yake damun Hidayan?

D’agowa yayi yana murmushi,kafin ya dube su yana fad’in” Alhamdulilla” Sannan ya zarce da cewar ” Wanenw mijin na ta a cikin ku?” Sakato suka yi suka rasa abin da za su ce,Sai Khaleel ne yayi k’arfin halin magana”Ni ne mijinta Doctor,wani abu ne ya faru?me yake damunta ne? ya k’arasa da jero masa tambayoyi,Hamza ya bi Khaleel da kallo kawai,Sai Likita ya mik’owa Khaleel hannu ya kama hannun Khaleel d’in yana girgizawa cike da fara’a,murya a sake ya ke cewa.

“Congratulation….Ina taya ka murna matarka tana d’auke da cikin wata Uku…shine ya sabbaba mata shiga cikin wannan yanayi”

A take Khaleel ya zabura ya mik’e cikin d’imaucewa da gigicewa idanuwan sa a warwaje yake kallon Likita da kuma Hamza……!

 

 

************

 

A firgice Aunty Sajida ta juya jin an turo k’ofar d’akin da k’arfi an shigo,Khaleel na ya shigo da sauri ya nufi in da Hidaya ke kwance tana baccin wahala,yana zuwa ya zube gaban gadon ya kwantar da kansa gefen da take kwance tare da fashewa da wani matsanancin kuka,sai surutai yake cikin gigicewa da d’imaucewar k’wak’walwa.

“Ki yafe min matata hak’ik’a nayi nadamar abinda na aikata…kuma zan kasance cikin nadama har lokacin da zan bar duniya…shikenan ba zan cigaba da rayuwa da ke ba?ba zan kasance muhalli d’aya tare da ke da tsatsona da ke jikin ki ba?hak’ik’a na tafka asara…na san abinda zai fito daga jikinki ba zai tab’a yafe min wulak’anta masa mahaifiya da nayi ba…tabbas Allah mai hikima ne da basira cikin dukkan abin da ya tsara…
Sai ya sake fashewa da kuka yana cigaba da surutai kala kala,Aunty Sajida dai a tsorace take,ta tsurawa Khaleel idanu k’irjinta na bugawa,juyawa tayi ta dubi Hamza da shima ya shigo d’akin jikinsa a sanyaye,idanuwansa cike suke da tarin k’wallar tausayin Khaleel,har gaban gadon yaje ya sunkuya ya d’ago Khaleel d’in ya mik’ar da shi tsaye,hannu ya kai yana share masa hawaye tare da girgiza masa kai,wani hawayen ya sake kwararowa Khaleel,ya bud’e baki cikin kyarmar murya ya cewa Hamza .

“Aboki ya zanyi?”

Hamza ya ce “Godiya ga Allah za ka yi ,ba kuka ba,murna ya kamata kayi Khaleel domin mun samu k’aruwa a lokacin da bamu yi zato ba”

Sai Khaleel ya sa kansa a kafad’ar Hamza hawaye na tsiyaya,cikin tabbatarwa ya ce wa Hamzan “Ina murna Aboki,tabbas ina jin duk duniya yau babu wanda ya kaini farinciki,domin na samu abinda ban tab’a tunanin zan samu a rayuwata ba,kuma na sameshi ne daga wacce nake matuk’ar so da k’auna,sai dai kuka ya zama dole a gareni Aboki,k’addara ta rabani da ita a lokacin da yafi dacewa ace ina tare da ita,ko domin in bata kyakkyawar kulawar da ta dace akan nauyin da na d’ora mata,Aboki na zalunci yarinyar nan,ban kyauta mata ba,ya zanyi?don Allah ka fad’amin ya zanyi?

Rungumeshi Hamza yayi k’am yana runtse idanu,yana jin kamar tausayin Khaleel zai kasheshi,jin muryar Aunty Sajida suka yi cikin rud’u tana fad’in “Wai menene ya faru ne?menene ya faru Hamza?”

Hamza ya zaunar da Khaleel gefen gadon da Hidaya ke kwance,saboda jin da yayi jikin Khaleel d’in na rawa sosai,Khaleel ya jingina kansa jikin bangon d’akin idanuwansa kan Hidaya yana kallon yadda take sauke numfashi,ya dinga kallon lafaffen cikinta yana mamakin wai akwai ajiyarsa a ciki,tabbas Allah mai hikima ne,bai san lokacin da wani kukan ya b’alle masa ba.

Shi kam waiwayawa yayi ya dubi Aunty Sajidasannan yayi k’asa da kai yayi magana A hankali.
“Aunty Doctor ya sanar da mu cewa Hidaya na da juna biyu,ma’ana tana d’auke da cikin Khaleel na wata uku”

Dafe k’irji Aunty tayi tana salati,ta juya tana kallon Khaleel da ke kuka sai taji mugun tausayinsa wanda bata tab’a ji ba,hawaye ya kwararo mata,bata ma san lokacin da ta dubi Hamza ta jefa masa wata tambaya ba a d’imauce.

“Hamza kaine malami…wai shin babu ta yadda za a yi a gyara auren Khaleel da Hidaya su koma ne?Wallahi tausayinsu nake ji,yana son matarsa ita ma tana son mijinta,k’addara ce kawai tayi musu shigar sauri,wallahi tunda suka rabu bata da sukuni ko a Gombe bacci ma bata iya yi sai yawan tunani da kuka,wataran ma idan ta samu baccin sai dai kawai kaji tana ambatar sunansa kamar mai mafarki alamun dai shine a ranta,ka duba Hamza idan da akwai wani hadisi ko aya da suka yi bayani akan irin wannan sakin da yadda za a gyara shi don Allah ka taimaka,kar yaran nan su rasa hankalinsu domin damuwar tayi yawa” ta k’arashe maganarta da kuka sosai.

Hamza yayi shiru,kafin ya d’ago idanuwansa da suka sauya launi suka yi jajir,hawaye ya kwanta a cikinsu,a sanyaye ya ce wa Aunty Sajida.

“Ni ba Malami ba ne Aunty,sai dai na kasance d’alibi mai neman sani musamman akan harkar addini,na karanta Alk’ur’ani da sauran litattafai na musulunci,tabbas a gabana kuma a gabanki Khaleel ya saki Hidaya,kuma ba saki d’aya yayi mata ba saki uku yayi mata,har maimaitawa ya dinga yi a lokacin,to akwai malamai da suka rabu gida biyu akan irin wannan sakin, wad’ansu suna cewa wanda ya saki matarsa saki uku a kalma daya ko majlisi daya to saki daya ne yake afkuwa.

Wannan shi ne ra’ayin da aka samu daga Ibn Abbas, kuma ita ce fatawar irinsu Ibn Taimiyya da dalibinsa Ibnl Kayyim da sauransu.

Amma abin da jumhur na malamai suka tafi a kai shi ne, idan mutum ya saki matarsa da irin wannan siga to ta saku saki uku, ba zata sake halatta gare shi ba har sai ta yi tabbataccen aure kuma mijin ya d’and’anta, kamar yadda Allah madaukaki yake fada:
*”فإن طلقها فلا تحل له من بعد حتى تنكح زوجا غيره، فإن طلقها فلا جناح عليهما أن يتراجعا إن ظنا أن يقيما حدود الله”*

(Idan ya sake ta (saki na uku) to ba ta sake halattuwa a gare shi har sai ta auri wani mijin ba shi ba, idan kuma ya saketa (shi mijin na biyu) to babu laifi a kansu su yi kome…….).

Wannan k’aulin dukkanmu akansa muke,kuma shi muke bi,Khaleel ya saki Hidaya saki uku,dan haka ba zata sake halatta a gareshi ba har sai bayan ta auri wani mijin ya d’and’ana zumarta,daga nan ne kuma idan sun rabu da mijin,to ta halatta a wajen Khaleel,a wannan lokacin za su iya komawa auren su.

Aunty ta share hawayenta ta cigaba da duban Hamza,tabbas ta gamsu da bayaninsa,to amma tunda akwai mafitar da ya fad’a ko ita za a gwada?shiyasa ta sake cewa Hamza.

“Na fahimta Hamza,to amma tunda akwai mafita me zai hana mu sami wani ya auri Hidayan, ko bayan ta haihu ne,in yaso ko wata d’aya tayi sai ya saketa ta dawo hannun Khaleel d’in ko?ina ga hakan zai fi ko dan mu ceto rayuwarsu Hamza”

A tsorace Hamza ya dubeta,cikin mamaki yace .

“Aunty Auren KISAN WUTA kenan fa”

Ta jinjina kai tare da cewa “Eh shi nake nufi Hamza,ai wai dan mu ceto rayuwar wad’annan masoyan”

Hamza ya ce.

“Mu ceto rayuwar su ko mu k’ara dilmiyar da su cikin halaka? Aunty Sajida bud’e kunnuwanki kiji ni.

Auren kisan wuta d’aya ne daga cikin lalatattun aure da addini ya haramta, Manzon Allah (S.A.W) Ya la’anci wanda yake yi da wanda aka yiwa, a cikin fad’in sa Annabi (S.A.W) ya ce:

*”لعن الله المحلل والمحلل له”*

(Allah Ya la’anci mai halattawa (Auren kisan wuta) da wanda aka halattawa)

Idan aka yi shi to matar ba ta halatta ga duka mazan, na farko da na biyun.

Ko da daga baya mijin ya canja niyyarsa daga auren kisan wuta sai dai ya saketa a sake sabon aqadi, idan kuma ya sadu da ita to sai ta yi cikakkiyar idda ta jini/tsarki uku ga wacce take ala’ada, ko wata uku ga wacce ba ta yi.

Idan kuma mijinta na farko yana son mayar da ita to sai ta sake yin wani auren da shari’a ta amince da shi kuma mijin ya kwanta da ita, idan ya saketa ta yi idda to sai ya shiga zawarci a sake sabon aqadi.
Wallahu a’alam.

Don haka Auren kisan wuta ba abune me kyau da addini ya yarda da shi ba,babu kyau aikata shi,babu wata hanya da za su bi tilas suyi hak’uri da k’addararsu,kamar yadda duk wani mutumin k’warai yake wa Allah biyayya akan jarrabawar da ya d’ora masa.

Take Aunty Sajida ta sake gasgata Hamza,ta tabbatar Hamza d’an baiwa ne,bawan Allah ne na gari wanda baya bin son zuciyarsa sai abinda Allah da manzonsa suka umarce mu….

 

 

***************

 

Lokacin da suka koma gida su Umma suka ji Labarin Hidaya na da ciki ba k’aramin kad’uwa suka yi ba,sun tausayawa Khaleel da Hidaya sosai a bisa wannan babbar k’addara da ta afka musu,ita kanta Hidayan tunda taji labarin tana da juna biyu ba k’aramin firgita tayi ba,ta yi kuka ta gode Allah,tausayin Khaleel na cin zuciyar ta,Khaleel kuwa ranar sai da ya sha maganinsa na ciwon zuciya,jin yadda k’irjinsa ya rik’e sosai,kowa dai ya tausaya musu,sai dai ta wani b’angaren ana murna da samun cikin da Hidayan tayi,a matsayin kyauta daga Allah.
Khaleel ya cigaba da k’arfafa zuciyar sa saboda Shari’ar da za su fuskanta a washegari,daren baiyi bacci ba sai salloli da addu’a kan samun nasarar ubangiji akan shari’ar,bashi ba ma hatta Hamza da ragowar mutanen gidan babu wanda yayi cikakken bacci a wannan daren,sun rayashi da salloli da addu’o’i bisa rok’on ubangiji kan samun nasara,saboda ita shari’a sab’anin hankali ce sai an had’a da addu’a.

 

 

*************

K’arfe Goma sha d’aya na safiyar washegari sun hallara a Kotu,inda Daddy da Alhaji Maude ke tsaye wajen amsa tambayoyi bisa ga manyan Laifukan da suka aikata,aka fara bata kashi tsakanin Lauyan da ke kare Alhaji Maude da Lauya Ibraheem Khaleel mai kare b’angaren masu k’ara,shi kam Daddy ma bai d’auki wani Lauya ba,ba tare da kuma b’ata lokaci ba ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su,amma Alhaji Maude yak’i amsawa ya k’aryata cewar shi bashi ne ya kashe Sulaiman da Taufik’ ba,sharri kawai Mudassir yake masa,cike da k’warewa Khaleel ya dinga jerowa Alhaji Maude tambayoyi wad’anda suka firgitashi ya dinga inda inda,Alhaji Maude ji yake tamkar ya shak’e Khaleel ya mutu,aka kirawo sunan Mummy nan da nan ta fito,ta bayar da shaida akan dukkan abinda ta sani,sai lauyan Alhaji Maude yayi mata tambaya akan cewa a labarinta da takardar da wannan mutumi ya bata ai sunan Alhaji Mudassir ta gani,to ya akayi ta jingina kisan akan Alhaji Maude,anan ne Mummy tayi shiru tana tunanin amsar da zata bayar,take alk’ali ya d’aga shari’ar zuwa wata Uku masu zuwa,kuma yayi umarni a tafi da Alhaji Maude da Daddy gidan ajiya a ajiye su har zuwa lokacin da kotu za ta cigaba da zama,kuma alk’ali ya bada umarnin a kamo mutanen da ake zancen sune suka yi kisan,haka nan yayi umarnin a tafi da Mummy da jami’an tsaro domin a binciko wannan jakar kud’i da ke b’oye tsawon shekaru,da wannan aka tashi daga zaman kotu na wannan rana.

Y’an sanda na shirin tafiya da su Daddy sai Khaleel ya nemi yana son yin magana da mahaifinsa,da k’yar ma suka yarda dan dai sunga Lauya ne,suka koma gefe guda suka tsaya,Khaleel ya dubi mahaifinsa cikin rauni ya ce.

“Daddy kayi hak’uri da duk abinda zai faru,gara ka karb’i hukuncinka tun a duniya kafin a je lahira”

Daddy ya jijjiga kai cike da k’aunar d’an sa ya ce” Na shiryawa hakan Khaleel,kuma zan baka duk wani goyon baya dan ganin ka samu nasara a wannan shari’a in Allah ya yarda”

Khaleel yayi murmushi sannan ya ce “Na gode Daddy,yanzu ma wani taimako nake son kayi min,zan baka wata y’ar na’ura y’ar k’arama ce sosai dan girmanta ko rabin d’an yatsa baiyi ba,zaka sakata a aljihunka kullum ka kasance tare da ita,a duk lokacin da zaka yi magana da Alhaji Maude ya kasance ka latsa ta,za ta d’auki dauki duk wata magana da za ku yi,wannan shaida ce me k’arfi da muke son mu sameta a wajenka,domin na tabbatar Alhaji Maude zai nemeka da maganar,kuma ina so ka biye masa domin kuyi ta,ta nan za mu samu wasu abubuwan da za su taimaka mana”

Daddy ya dafa kafad’ar Khaleel ya saki murmushi,sannan yace masa “Kar ka samu damuwa Khaleel,ka bani na’urar,kuma in sha Allahu za ka samu duk wasu bayanai da kake so a tare da ni”
Khaleel ya d’auko na’urar ya dank’awa Daddy a b’oye,Daddy ya karb’a ya zura cikin aljihunsa,sannan suka rungume juna kamar ba za su rabu ba,a lokacin ne y’an sanda suka k’araso domin sun gaji da jira suna so su tafi da Daddy,ba tare da b’ata lokaci ba Daddy ya saki Khaleel tare da yi masa kyakkyawan murmushi,y’an sanda suka saka shi a gaba har zuwa wajen motar su,sai lokacin Daddy ya juyo ya kalli Aunty Kubra da ke gefe tana hawaye,ya girgiza mata kai ya ce mata.

“Kiyi Hak’uri Kubra” Iya abinda yace mata kenan aka kad’ashi cikin mota,take motar ta tashi aka wuce da Alhaji Maude da Daddy.

 

 

************

A washe gari ne kuma jami’an tsaro da Mummy da Khaleel da Hamza suka nufi Abuja,tsawon shekarun nan gidan Alhaji Taufik’ yana nan inda yake,babu abinda ya tab’a shi,yana dai k’arkashin kulawar gwamnati ne,sai dai gidan sosai yayi k’ura da datti ta inda sai da suka sa face marks suka rufe bakin su da hancin su,ko ina k’ura da datti da yana da k’wari kala kala,a haka suka turmutsa suka shiga har cikin d’akin Mummy wanda ta barshi tsawon shekaru,Mummy bata tsaya ba har sai da ta dangana da su cikin vantlation d’in da ta bunne wannan jaka.

Mutum biyu ne suka hau fasa gurin,yayin da su Mummy suke tsaye a gefe suna kallo,cikin mintoci sai gashi an hak’o wannan jaka a inda aka binneta,mamaki sosai su Hamza da Khaleel suka shiga lokacin da suka yi arba da jakar,suka kalli Mummy suna jinjina mata,yayinda ganin wannan jaka ya tonowa Mummy mikin da ke zuciyarta ta dinga zubar da hawaye mai tsananin zafi su Hamza na lallashin ta.Sai da suka kammala komai jakar tana hannun ma’aikata sannan suka kulle gidan suka dawo Kaduna a ranar.

Abubuwa sun cigaba da faruwa na farinciki da akasin haka,inda Hidaya ke cikin wani irin yanayi,sai dai ta fawwalawa Allah komai ta mayar da hankalinta kan rainon abinda ke cikinta,dan ma bata wani laulayi sosai sai d’an abinda ba za a rasa ba,haka Khaleel yake daurewa zuciyarsa yana zuwa ganinta da duba halinda take ciki,duk da kullum idan ya ganta baya samun nutsuwa sai sunyi kuka sun zubda hawaye,har cikin ta ya isa wata hud’u da kwanaki a lokacin da ta fara zuwa Awon ciki a asibiti,duk wani nauyinta kuma Khaleel ne ya d’auke,baya barin Hamza da Umma suyi mata komai,tuni kuma su Mummy suka koma Kaduna ko domin aikinta,Aunty Sajida kuma ko domin mijinta da yaranta,sai dai ba a cikakken sati biyu su kan zo Kaduna domin a ga juna a sada zumunci,amma ita Hidaya tana Kaduna wajen Ummanta,bata koma Gombe ba.

Khaleel yana zuwa ganin Daddynsa,da shi da Aunty Kubra,har ma da Hamza da Umma,Hidaya ma ba a barta a baya ba,kuma duk lokacin da suka je indai Daddy yaga Hidaya ya dinga hawaye kenan yana bata hak’uri,har sai ita ma ya sakata hawayen,Daddy yana tausayawa Khaleel da Hidaya akan rabuwar su,gashi sun samu k’aruwa a lokacin da zama ya haramta a gare su.

Lokaci na ta tafiya har wata uku ta cika cif,ana shirye shiryen komawa kotu domin zama na biyu,saura kwana uku su shiga kotun Khaleel ya ziyarci gidan Umma domin ya ga lafiyar Hidayan,sai ya tarar Umma bata nan,Hamza ma baya nan sai Hidaya kawai a gidan,tana zaune a tsakargida tana wanke wanken kwanuka,Sallamar Khaleel ta sa ta juya tana amsawa cikin fara’a sannan ta zarce da cewa.

“Sannu da zuwa Uncle Khaleel”
K’arasowa yayi gabanta ya tsuguna yana janye kwanukan,sannan ya kalleta yana d’an b’ata rai ya ce “Ba na hanaki yawan aikace aikacen nan ba?kina fama da kanki amma ba zaki dinga hutawa ba,ni fa idan na ganki kina aiki hankalina tashi yake yi Hidaya”

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k’asa,sannan ta ce “Babu fa wani abu da yake damuna Uncle Khaleel,haka ma Ya Hamza sai yai ta hanani yin komai,kuma a asibitine ake ce mana mu dinga motsa jikinmu,saboda idan haihuwar ta zo mana zamu samu sauk’i sosai”

Jijjiga kai yayi ya gamsu da bayaninta,sai ya sanya hannu a ruwan wanke wanken yana taya ta,tana ta cewa ya bari kar ya b’ata jikinshi amma yak’i,har tattare hannun rigar yayi ya cigaba,sai da ya kammala mata sannan ya bari,a hankali ta mik’e daga kujerar da take zaune da k’yar,saboda cikin ya soma girma sosai yayi tsini kamar ta kusa haihuwa,da yake Hidaya siririya ce bata da k’iba sai cikin yake rinjayarta,sai a dinga ganin kamar yayi mata nauyi,ita kuma bata jin wani nauyi sosai,yanzun ma da ta mik’e kallonta kawai Khaleel yake yi yana jin tausayin ta,sai faman ce mata yake “Sannu …sannu da ibada kinji Hidaya..Allah ya saukeki lafiya ya rabaku lafiya” Kunya ta kamata,sai ta sunkuyar da kai tana amsawa cikin zuciyarta,ta fara kwashe kwanukan tana kaiwa ktcheen,yayinda Khaleel ya sanya tsintsiya yana share wajen da suka yi wanke wanken.

Kusan ranar a gidan ya yini,yana ta tayata aikace aikacen gidan,da zarar ya ga zata yi wani abun sai ya karb’e yace shi zaiyi,sosai ranar tayi musu dad’i kamar kar ta wuce,suna ji a zukatansu ina ma suna da aure,da kulawar da za su bawa juna sai ta ninka haka sau ba adadi,haka Khaleel ya isheta da zancen Babyn da zata haifa masa,har yana cewa idan ta haihu karb’an babyn zaiyi dan ya dinga ganinsa yana jin dad’i,tunda ya san cewar ita aure za ta yi,wannan maganar ita ta b’ata ran Hidaya ta dinga kumburi har da hawaye,wai akan me zaice za ta yi aure?ita ba wani aure da za ta yi,hakan yasa ya dinga bata hak’uri har ta sakko suka cigaba da hirar su,sai da ta kammala girkin dare da yamma da taimakon Khaleel,sannan tayi shirin shiga wanka domin taji dad’in jikinta,sai Khaleel yaji a ransa da suna da aure fa shine zai mata wankan ma,da hanzari ya kawar da wannan tunanin daga ransa,hawaye ya ciko idanuwan sa amma ya shanye dan kar Hidaya ta gani.

Da za ta shiga wankan sai Khaleel ya karb’i mukullin d’akin Hamza yace zai bud’e ya zauna a can har ta gama shiryawa,kuma zai jira Hamzan ya dawo domin akwai abinda za su tattauna da shi,Hidaya dai tana bashi mukullin ta shige ta tafi domin yin wanka,shi kuma ya bud’e d’akin Hamzan ya shige abunsa,yana shiga kan gadon Hamza ya fad’a ya kwanta rigingine yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwansa,ya jima a haka kafin ya bud’e idanuwan yana gyara kwanciyar shi,sai idanuwansa suka kai kan wani littafi k’arami mai kyau,d’auka yayi yana kallon littafin,bai san ko na meye ba amma yaji a zuciyarsa yana son ya ga abinda ke ciki,hakan ya sa ya bud’e littafin yana daga kwance ya fara duba shafin farko,ba rubutun kowa ba ne a jiki illa rubutun Hamza,hakan ya sa ya fara bin shafin farko yana karanta abin da ke jiki,a take ba da shiri ba sai ga Khaleel ya mik’e a matuk’ar razane,idanuwansa kamar su fad’o k’asa ya cigaba da karanta abinda ke cikin littafin shafi bayan shafi,cikin lokaci k’ank’ani sai ga Khaleel yayi rud’ewar da ya jima baiyi irinta ba,zuciyarsa kamar ta faso k’irjinsa ta fito,hawaye ya b’alle masa kamar an bud’e famfo,kuka Khaleel ke yi sosai har bai san lokacin da gaban rigarsa ya jik’e da hawaye ba.
Bai kai k’arshen littafin ba yaji kansa na juyawa,ba zai iya cigaba da karanta abinda ke rubuce ba,hakan ya sa ya ajiye littafin inda ya ganshi sannan ya mik’e cikin layi da cushewar tunani zai fice daga d’akin,waiwayowa yayi yaga takarda da biro akan bedside drawer,sai ya sunkuya ya d’auka yayi rubutu kad’an a jiki ya nannad’e,fitowa yayi daga d’akin Hamzan har lokacin hawaye ne ke sintiri kan kyakkyawar fuskarshi,yasa mukulli ya kulle d’akin,sannan ya nufi parlour’n Umma ya lek’a,baiji motsin Hidaya ba,hakan yasa yayi zaton ko har lokacin tana wanka bata fito ba,ajiye mata takardar yayi kan kujera,ya d’ora mata mukullin kan takardar yadda zata gani,sannan ya fice ya bar gidan ma gabad’aya zuciya cike da rauni.

Sai da Hidaya ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar shadda,sai taga cikinta ya k’ara fitowa sosai,hakan ya sa ta d’auko hijab ta sanya ta rufe jikinta,sannan ta fito parlour’n.
Da mukullin d’akin Hamza ta fara cin karo,ga kuma takarda a k’asan mukullin,hakan yasa ta sanya hannu ta d’auki mukullin ta ajiye gefe,sannan ta d’au takardar cikin mamaki ta warware tana dubawa.

*Ko da kin fito kin tarar bana nan ba wani abu bane,na samu kiran gaggawa ne shiyasa na tafi bamu yi sallama ba,kiyi hak’uri*

*UNCLE KHALEEL*

Iya abinda ta gani kenan,ta sauke ajiyar zuciya ta d’an lek’a tsakar gidan tana duban d’akin Hamza,sai kuma ta saki labule ta koma parlour’n tana zama kan kujera zuciyarta cike da sak’e sak’e,bata jima da zama ba kuma taji muryar Umma na sallama alamun ta dawo……!

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
pls

08080049548

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA CASA’IN DA BAKWAI DA NA CASA’IN DA TAKWAS

 

*** Ranar da aka yi zama na biyu a kotu sai da Hidaya ta razana da taga Khaleel,saboda wata irin rama da taga ya sake yi,idanuwansa kuwa sanye suke da glass ba a ganin k’wayar idanuwan kwata kwata,shi ba gwanin sanya glass bane ma ,amma ranar ya sanya domin b’oye idanuwansa,hatta Hamza sai da yayi masa tambaya akan ramar da yaga yayi,kawai murmushi yayi yace masa bayajin dad’i ne,ya taya shi addu’a kawai.

A ranar an cigaba da gabatar da shaidu ne akan shari’ar,inda ba a samu wata cikakkiyar shaida daga Alhaji Mudassir ba,saboda duk tsawon wannan lokacin Alhaji Maude ya k’i yarda suyi magana balle ya samu wani abin daga gareshi,ta b’angaren Mummy dai an samu shaidar wannan jaka da ta binne wadda Alhaji Taufik’ ya bawa Sulaiman,shi kuma ta b’angaren Alhaji Maude an kamo mutanen da ake zaton su ya tura suka yi kisan,kuma har da su akayi zaman kotun,dukkansu suna tsaye a b’angaren tuhuma,kuma duk wata tambaya da akayi musu sun dage ne akan su dai Alhaji Mudassir ne ya saka su aikata kisan,amma babu ruwan Alhaji Maude a ciki,hakan ya faranta ran Alhaji Maude,ya tabbatar shine ke da nasara akan shari’ar domin Mudassir bai da wata gamsasshiyar shaida da zai bayar,shi kam Daddy rud’ewa yayi sosai,domin dai ya san bashi ne ya aikata hakan ba,shi kansa Khaleel shari’ar ta fara bashi tsoro,da farko yana ta hango nasara,amma a yau duk jikinsa yayi sanyi sosai,daga nan ne Alk’ali ya d’aga shari’ar zuwa wata d’aya mai zuwa,kuma rana ta k’arshe da zai yanke hukunci,dan haka ya umarci kowane b’angare na masu k’ara da wanda ake k’ara da su gaggauta samo shaidu k’warara da manyan hujjoji wanda kotu za ta yi la’akari da su,a take Alk’ali ya buga guduma kowa ya mik’e tsaye.

Bayan mutane sun firfito waje ne aka sake fito da Alhaji Maude da Daddy da wad’annan mutane da aka kamo,za a wuce da su gidan Ajiya kafin ranar da za a dawo kotu,anan ne Khaleel ya sake neman alfarmar magana da mahaifinsa wanda da k’yar ya samu suka yarda suka basu minti biyu suka koma gefe tare da wani d’an sanda da ke rik’e da bindiga,tun kafin ma Khaleel yayi magana Daddy ne ya fara dubansa ya ce.

“D’ana kana cikin damuwa ko?domin na lura duk lokacin da kake cikin yanayi na damuwa ka kan rufe idanuwanka dan kar a gane yanayin ka,to amma ni naji a jikina akwai damuwa a tare da kai,ga kuma rama da naga ka kuma yi sosai,me yake faruwa da kai ne?don Allah ka taimaka ka rage wannan damuwar,in dai don wannan shari’ar ne in sha Allahu mu ke da nasara,Allah ba zai tab’a tab’ar da GASKIYA ba,domin kullum GASKIYA ce a gaba da K’ARYA Khaleel.

Murmushi Khaleel yayi hawaye na tawo masa amma ya shanye,ba zai iya misalta damuwar da ke ruhinsa ba,tabbas yana cikin damuwa mara iyaka,sai kawai ya ce wa Daddy “Babu abinda yake damuna Daddyna,kawai dai bani da lafiya ne shiyasa kaga yanayi na ya sauya,amma na fara jin afuwa ma a jikina”

Daddy ya rik’o hannun Khaleel yana masa sannu,sannan ya ce “To kaje kaga likitanka mana,bana son a samu matsala har ciwonka ya tashi,kaga dai abinda ke gabanmu akan shari’ar nan” Sai Khaleel ya jinjina kai da fad’in “In sha Allah babu abinda zai faru sai alkairi” sannan ya zarce da cewa “Daddy Kayi k’ok’ari ka samu wani abu daga Alhaji Maude ko mutanen da za a had’aku da su a yau,saboda bamu da wata cikakkiyar hujja da za mu gabatar,amma tunda akwai wannan na’ura a tare da kai to na san za ta yi mana amfani sosai muddin kuka yi magana kai da Alhaji Maude” Daddy ya fara bawa Khaleel amsa sai wannan d’an sandan ya matso yana fad’in “Lokaci ya cika” sannan ya sanya Daddy a gaba suka wuce zuwa mota,yayinda Khaleel ya bisu da kallo zuciyarsa a jagule.

Tun daga lokacin su Khaleel suka maida addu’a aikinsu,sosai suke kaiwa Allah kukansu akan ya basu nasara da sa’a akan shari’ar,wata d’abi’a kuma da Khaleel ya shigo da ita shine d’auke k’afa daga gidan su Hamza,kwata kwata ya daina zuwa ganin Hidaya,sai dai ya kan yi mata aike da dukkan abinda ya san tana buk’ata har ma wanda bata buk’ata ba,Umma har cigiyarsa take amma Khaleel ya kasa zuwa kullum sai yace abubuwa sun masa yawa,duk sai Hamza yake jin sa cikin wata matsananciyar damuwa da kewa,hakan ya sa yaje ya samu Khaleel akan ya fad’a masa dalilin sauyawar sa,amma Khaleel ya ce shifa babu komai,kawai yanayin rayuwa ne ya kawo hakan,tilas Hamza ya hak’ura ya barshi ba dan ya so hakan ba,sai dan yayi iya yinsa amma Khaleel d’in ya kasa fad’a masa damuwar sa.

 

*************

 

*RANAR ZAMAN K’ARSHE A KOTU*

 

Dukkan wanda zai halarci kotun a ranar ya wayi gari ne da fargabar abinda zai afku,Nasara ko rashin nasara?hakan ya sa kowa jikinsa yake a sanyaye,dan tun safe Hamza ke jin matuk’ar fad’uwar gaba mai girma,har ya kasa yin shiru ya fad’awa Umma,sai tace ya dinga addu’a zaiji sauk’in abinda yake ji,shi ma Khaleel haka ya samu kansa da fad’uwar gaba sosai,sai da Aunty Kubra ta dinga k’arfafa masa gwiwa sannan ya d’an saki ransa.

Hidaya kuwa an so hanata zuwa kotun ma saboda yadda cikinta yayi wani irin girma kamar cikin wata tara,alhali cikin wata bakwai ne kacal,da k’yar take iya d’aga k’afa saboda girman cikin hakan yasa Ya Hamza yace tayi zamanta a gida ba sai taje ba,sai ta fara rok’onsa har da kukanta wai ita dai yayi hak’uri ya bari ta je taga yadda za a yankewa Alhaji Maude hukunci a gabanta,har Mummy sai da tasa baki tace “Hidaya me yasa bakya jin magana ne,tunda Hamza yace ki zauna a gida to ki zauna mana,yanzu a haka zaki shiga kotun da wannan d’irmemen cikin?ke ana guje miki wahala amma bakya ganewa”ganin Mummy nayi wa Hidaya fad’a hakan yasa Umma ta saka baki ta ce” Don Allah Zainab ku rabar min da y’ata haka,tunda tana son zuwa kuma zata iya to ku barta taje mana,ai gara mu tafi da ita da a barta a gida ita kad’ai” sai Mummy da Hamza suka yi shiru ganin Umma ta goya mata baya,ita kam Kakar Hidaya dariya ta dingayi tana tsokanar Hidaya da mai raguwar zuciya,wai ita ba jaruma ba ce tunda abu kad’an ke sanyata kuka,sai Aunty Sajida ce ke kare Hidayan tana cewa”To ai yawan kuka shine yake nuna mutum yana da cikakken imani a zuciyar sa”

A lokacin da motar su ta tsaya a harabar kotun dai dai lokacin ma motar Khaleel ta tsaya,Hamza ya fito ya bud’ewa su Umma k’ofa suka firfito,a lokacin Khaleel ya k’araso gare su shi da Aunty Kubra,ya tsuguna yana gaida su Umma,su Mummy suka amsa yayinda Umma tace “Ba zan amsa gaisuwarka ba Khaleel tunda ka gujemu,yaushe rabon da na ganka?”ya sunkuyar da kai yana shafa wuyansa yana d’an murmushi yana bawa Umma hak’uri,ta d’an yi dariya tana fad’in “To shikenan na hak’ura,amma sai kayi min alk’awarin za ka dinga zuwa ina dama maka kunun gyad’a ka dinga sha ko dan ka maida jikinka,wannan ramar da kake yi tayi yawa Ibraheem,sai k’arewa kake kamar ruwan aski” Dariya yayi sannan yace wa Umma in sha Allah zai dinga zuwa.

Bayan su Umma sun gaisa da Aunty Kubra sai suka d’unguma suka wuce cikin kotun,sai a lokacin Hamza ya zagaya ya bud’ewa Hidaya b’angaren da take zaune,ta sako k’afafuwanta waje tana kumbura baki wai ya manta da ita cikin mota bai bud’e mata da wuri ba,harararta yayi yana fad’in “Sai ki fito ko” da k’yar ta yunk’ura ta iya fitowa daga motar tana kwab’e fuska.

Tana fitowa Khaleel ya bita da wani irin kallo yana mamakin yadda cikinta yayi girma sosai,ko dan ya jima bai ganta ba ne?ita ma kallonsa ta dinga yi kamar ta fashe da kuka,Uncle Khaleel d’in ta duk ya zabge ya k’are,wanda bai masa cikakken sani ba ba lallai ya shaida shi ba tsabar ramar da ya kwantsama,hakan ya sa ta tsura masa idanu kawai tana kallonsa,sai shine ya kawar da shirun ta hanyar duban Hamza yace masa.

“Aboki haka Hidaya tayi nauyi daman?”

Hamza ya harari Hidaya saboda haushin da ta ba shi,sannan ya juya yana rik’o hannun Khaleel ya ce.

“Eh fa,amma da yake yarinyar nan kunnen k’ashi ne da ita nace mata ta zauna a gida kar tazo shine har da kuka,ita kuma Umma ta goya mata baya”

Khaleel yayi murmushi kawai sannan ya ce.

“To meye abin fushi Aboki,ai gara ka barta ta zo taga k’arshen shari’ar ko?”

Hamza ya waiwaya ya dubi Hidaya ya ce.

“Kalli fa Khallel,kalli yadda take d’aga k’afa da k’yar,haka kawai salon ta wahalar mana da d’an mu ko y’ar mu” Sai Khaleel ya fashe da dariya,Hidaya ta bishi da kallo ganin kyawun da dariyar tayi masa,sai taji yana cewa Hamza ” Au wai kai ta jaririnka kake ma ko Aboki?ni kam ta ita nake,domin ita ce bana son ta wahala ba jariri ko jaririya ba”

D’an k’aramin tsaki Hamza yayi yana fad’in “daman ai bakin ku d’aya kai da ita” Khaleel ya cigaba da dariya yayin da Hidaya ke wa k’eyar Hamza gwalo ganin Khaleel ya goyi da bayan ta.

A tsakiya suka saka Hidaya suna takawa a hankali suka nufi cikin Kotun,yayin da Khaleel yayi k’asa da murya ya ce wa Hidaya.

“Ki tayani addu’a yau burina ya cika,ina son yau suna na ya tashi daga Ibraheem Khaleel ya koma GARKUWAR HIDAYA.

************

 

Bayan Alk’ali ya shigo an mik’e an yi gaisuwa kowa ya zauna,a lokacin ne lauyoyi suka fara mik’ewa suna gabatar da kansu gaban mai girma mai shari’a,kotun tayi tsit mutane dank’am ta cika tayi taf,daga nan ne kuma shari’a fa ta fara d’aukar d’umi in da kowane b’angare ke k’ok’arin bayar da hujjar da za a gamsu da ita,yayin da Khaleel ya isa gaban Alhaji Maude ya tsaya,Alhaji Maude ya bishi da wani kallo na tsana a yayinda Kaleel d’in ke ce masa “Alhaji Maude ka ce ba kaine ka sa aka kashe Sulaiman ba,kuma ba kaine ka b’atar da Oga Taufik’ ba a wancan lokaci,amma alamu da dama sun nuna kana da hannu dumu dumu a cikin aikata hakan,me yasa ka tsaya jayayya da kotu ka kasa amsa laifinka?kana son ka bawa kotu wahala ne ko me?”

Alhaji Maude ya ce “Kamar yadda na fad’a a baya yanzu ma haka zan fad’a,ba nine na sa a kashe Sulaiman ba,kuma ai ko da aka tambayi wad’anda suka yi kisan sun fad’a da bakinsu cewar Mudassir ne ya saka su,dan haka Alhaji Mudassir ke da alhakin kisan ba ni ba”

Sai Khaleel ya juya ya kalli Alk’ali ya ce.

“Ya mai shari’a,Alhaji Maude kawai yana so ya wahalar da kotu ne,amma tabbas shine ya sa akayi wannan kisan bi sa ga wata k’wak’k’warar shaida da zan bayar a yanzu”

“Objection my lord” abinda Lauyan Alhaji Maude ya fad’a kenan yayin da ya mik’e tsaye cikin huci,sannan ya zarce da ce wa” Ya kamata Lauyan masu k’ara ya daina tabbatar da cewar Alhaji Maude shine ya aikata hakan,tunda har yanzu zargi ake yi ba a tabbatar ba, Na gode”

Alk’ali ya tsawatar wa Khaleel,Sai Khaleel ya bayar da hak’uri da fad’in zai gyara,daga nan kuma ya nemi da a bashi dama domin ya gabatar da hujjar sa ta k’arshe,wadda yake ganin ita ce za ta kawo k’arshen komai akan shari’ar,Alk’ali ya ce da Khaleel “An baka dama barrister Ibraheem Khaleel”

Matsawa yayi kusa da Daddy ya karb’i wannan na’urar,sannan ya kaita gaban Alk’ali a matsayin hujjar sa,kotu tayi tsit yayinda alk’ali ya danna wannan na’ura,bayan tayi shuuuuu na tak’aitaccen lokaci sai ga magana ta fara fitowa,in da muryar Daddy ke magana tana cewa.

“Yanzu Maude amanar da ke tsakanina da kai ya kamata kayi min haka?me nayi maka a rayuwa kake neman mak’alamin sharrin da bani na aikata ba?a dalilin me za ka ce nine na sa aka kashe Sulaiman?bayan tun a wancan lokacin ka san ni ne nace maka bana son kisa ya shigo cikin lamarin”

Maganar Daddy ta tsaya,sai dariyar Alhaji Maude ta fito da k’arfi hahahahahaha, kafin kuma a jiyo muryarsa yana mayarwa da Daddy raddi da cewa.

“Kai Mudssir har kayi k’warin wuyan da za ka ce za ka ja dani ?ni zaka tonawa asiri saboda kana tunanin d’anka Lauya ne zai kare ka?to bari kaji in gaya maka,duk yadda kake tunani na na shallake hakan wallahi,kuma Alk’awari nayi yadda naga bayan Taufik’ da Sulaiman kaima sai naga bayanka,daman ni ba son gaskiya nake maka ba,dan haka ka shirya kaima sai ka bak’unci lahira kamar yadda Taufik’ da Sulaiman suka bak’unta,nine da nasara a wannan shari’ar,wannan Alk’awarina ne Mudassir” ya sake fashewa da dariya.

Sai ga muryar Daddy cikin Kuka yana cewa.

“To me yasa ka zab’i aikata hakan?me yasa kake so kaga bayana?me nayi maka?

Alhaji Maude ya ce “Babu abinda kayi min,kawai ganinka ne bana so na dinga yi a duniyar,dan haka nake so ka kauce ka bani wuri,kuma tabbas nine na sa aka sace Taufik’,kuma na sanar da kai cewar Kurciya me dogon zango na sa akayi masa,da yake kai me tosasshiyar k’wak’walwa ne sai ka kasa fahimta tun a wancan lokacin,abin da baka sani ba tun a daren bayan na sa an sato shi da hannuna na kashe shi,kuma muka je muka cillashi cikin teku ta yadda halittun cikin ruwa za su cinyeshi ba za a sake jin d’uriyarsa ba,haka nan nine na sanya aka je aka kashe Sulaiman,shi ma da hannuna na jefa gawarsa cikin teku bayan sun kawo min gawarsa,kuma nine na sa a b’atar da iyalin Sulaiman,amma sai nayi matuk’ar mamaki da naga sun bayyana a yanzu,hakan yasa nayi tunanin wanda na bawa aikin b’atar da su ne baiyi dai dai ba,kuma shima ina nan zuwa gareshi sai nayi masa hukunci kan abinda ya aikata,sai naga bayansa bayan naga bayanka,dan haka ka k’ara sani Mudassir,nine da nasara a wannan shari’ar,domin baka da wata hujja da zaka gabatar gamsasshiya da za ta k’waceka,kana gani zan yi free,kai kuma a yanke maka hukuncin da ya dace da kai”

Iya nan maganar ta tsaya sai dariyar Alhaji Maude dake tashi cikin na’urar,b’angare d’aya kuma kukan Daddy na tashi.

Alk’ali na kammala ji sai kotu ta d’auki hayaniya da surutai,yayinda Alhaji Maude ya tsorata ya firgita ya gigice,banda gumi babu abinda yake yi.

Alk’ali ya tsawatar tare da buga guduma,kotu tayi tsit kowa na mamakin wannan dambarwa,Zuciyoyin su Mummy K’al kamar madara saboda jin dad’in abinda ke faruwa,yayin da Alhaji Maude da lauyansa da mutanen da suka yi kisan suka yi tsuru tsuru kamar mage a kwali,sunyi matuk’ar tsorata da wannan gundumemiyar shaida da Khaleel ya bayar,Lauyan Maude bak’inciki kamar ya kashe shi,ya akayi Alhaji Maude ya saki baki ya dinga kwarara jawabai har haka? Ni kuwa a zuciyata nace Hakkin rai ne ,dan hakki ba zai tab’a barinsa ba.

A lokacin ne Khaleel ya matsa gaban wad’annan mutane guda biyar,sannan ya dube su ya ce.

“To ga dai maganar da oganku Alhaji Maude yayi,ya tabbatar da shine ya kashe oga Taufik’,kuma shine ya sanya kuka kashe Sulaiman,da ragowar k’ulla k’ullar da kuka aikata,shin har yanzu kuna kan bakarku na cewa ba laifin Alhaji Maude ba ne?ko kuwa za ku bi hanyar GASKIYA ku bar dokin K’ARYA? ya rage ruwanku ku fad’i gaskiya domin ku tsira daga la’antar da Allah mad’aukakin sarki zai sanya a kanku,domin Allah da kansa yake ce wa a cikin littafinsa mai girma.

“فنجعل لعنت الله على الکذبين”

(Sannan kuma mu sanya tsinuwar Allah akan mak’aryata).

Duk wata shaida da zaku bayar a halin yanzu to ina baku shawara da ta kasance gaskiya ce.

“واجتنبوا قول الزور”

Allah ya ce (ku nisanci fad’ar shaidar zur).

“و لا تکتموا الشھدة,و من يکتمھا فإنه ءاثم قلبه ,والله بما تعملون عليم”

( Kada ku b’oye shaida,duk kuwa wanda ya b’oye ta,to hak’ik’a shi mai kangararriyar zuciya ne,kuma Allah masanin abin da kuke aikatawa ne).

Ku sani cewar wannan rayuwar za ta k’are,za ku je gaban ubangijin ku kuna masu tab’ewa idan har kuka b’oye gaskiya,kar ku d’auka za ku dawwama ne,wallahi duk wani abu da yake doron k’asa mai k’arewa ne.

“کل من عليھا فان ,و يبقى وجه ربك ذو الجلل و الإکرام”

(Duk wanda yake kan doron k’asa mai k’arewa ne.fuskar ubangijinka ce za ta wanzu,ma’abocin girma da d’aukaka).

Yanzu zab’i guda biyu ke gareku,imma ku fad’i gaskiya ku tsira gurin ubangijinku ku samu aljannan mad’aukakiya,imma ku fad’i k’arya kuje kuyi wata irin rayuwa ta danasani bayan mutuwar ku,tun kafin ma kuje gaban Allah ku fara had’uwa da fitinar k’abari,ku had’u da azaba,kafin Allah ya tashi duk wad’anda suka mutu a k’aburburan su,Allah ya tara bayinsa domin yin hisabi a gare su, ku da kuke tunanin Alhaji Maude zai ceceku babu abinda ya isa yi a wannan rana domin shi ma ta kansa yake, kuma a ranar ne kowa za a nuna masa aikin da yayi imma na alkairi ko na sharri,daga nan kuma a fara hisabi,muminai su karb’i littafin su da hannun dama,kafirai da munafukai su karb’a da hannun hagu,Allah ta’ala yana ce wa.

“ووضع الکتب فترى المجرمين مشفقين مما فيه و يقولون يويلتنا مال ھذا الکتب لا يغادر صغيرة و لا کبيرة إلا أحصھا ووجدوا ما عملوا حاضرا ولا يظلم ربك أحدا”

(Kuma za a aje littafi,wannan lokaci za ka ga masu laifi a tsorace saboda halin da suke ciki.kuma suna cewa,”Kaicon mu! wane irin littafi ne wannan ?baya barin k’aramin laifi da babba sai ya lissafa su.Kuma suka samu abin da suka aikata a halarce,Kuma Ubangijin ba zai zalunci wani ba).

Daga nan sai hawa kan sirad’i,gada ce da take k’ark’ashin Jahannama,wannan gadar ta fi gashi sirantaka,kuma ta fi takobi kaifi,muminai za su wuce ta kan wannan sirad’i kamar walk’iya,wasu kamar iska,wasu kamar ingarman doki,wasu su tsira su kub’uta,wasu kuma su kukkuje a wuta,har na k’arshe su zo da jan ciki.

Haka y’an aljanna za su shige cikinta suna masu murna da farinciki,Allah zai kora y’an wuta zuwa jahannama jama’a jama’a (Allah ka kiyashe mu 👏😭)
Ya ku bayin Allah kuji tsoran Allah ! ku sani mafi darajar mu a wajen Allah shine mafi tsoran sa,duk wanda aikinsa ya dak’ilar da shi to dangantakarsa ba za ta ciyar dashi gaba ba.Ku sani Allah yana lissafa muku ayyukanku da kuke yi,dan haka duk wanda ya samu alkairi to ya godewa Allah.Wanda kuma ya sami kishiyar wannan to kar ya zargi kowa sai kansa”

Tunda Khaleel ya fara jawabi kotun tayi tsit,masu kuka na yi,wato masu k’ara jin imani a zuciyar su kenan,sai ga wad’annan mutane guda biyar sun fashe da kuka matsananci,yayin da nan take suka zab’i fad’ar GASKIYA domin su tsira daga azabar Ubangiji ranar lahira,a take kuma suka yi bayani akan cewar tabbas Alhaji Maude ne ya saka su aikata wannan d’anyen aiki,kuma ya umarcesu akan su mak’alawa Alhaji Mudassir alhakin abun,Mai girma mai shari’a ya sauke numfashi bayan ya kammala jin jawaban su,sannan yayi shirin yanke hukuncin da ya dace da shari’ar,Zuciyar Alhaji Maude kamar ta fito dan bak’inciki,bai tab’a tunanin talala Mudassir yayi masa ba,bai tab’a sanin ya d’auki maganganun da suka yi ba,wata tsanar Mudassir ta sake linkuwa a ransa,yana ji a zuciyarsa ko me za a yi ba zai bar Mudassir ba sai yaga bayansa,zuciyarsa ta taurara k’warai da gaske.

Alk’ali yayi jawabai Sosai,sannan ya gabatar da hukunci kamar haka:

Alhaji Mudassir an yanke masa hukuncin d’aurin shekaru goma gidan yari tare da aiki mai tsanani,bi sa ga yadda aka had’a baki da shi wajen cutar da Oga Taufik’ da Sulaiman.

Mutane guda hud’u daga cikin mutane biyar d’innan an yanke musu hukuncin d’aurin rai da rai,saboda da su aka had’a baki wajen kisan Oga Taufik’ da Sulaiman.

Sai ragowar mutum d’aya daga cikinsu wanda da hannunsa ya kashe Sulaiman,shi kuma da shi da Alhaji Maude an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya,saboda sune suka yi hukuncin da hannunsu.

Sannan yayi hukunci akan dukiyar da Oga Taufik’ ya bari,akan a nemo danginsa na nesa domin a raba ta kaso uku kamar yadda yace,danginsa suna da kaso d’aya,su Mummy da Hidaya na da kaso d’aya,sai kuma kaso d’ayan a kai gidan Marayu.

Kotu ta d’auki kabbara da wannan hukunci da aka zartas,yayin da Hidaya ta d’aga murya da k’arfi ta mik’e tsaye ta ambaci sunan Khaleel tana hawaye,ya waiwayo yana dubanta fuskarsa cike da murmushi,sai ta d’aga masa hannu tayi masa jinjina,sannan ta fad’a da k’arfi kowa yaji,ta ce “Lallai yau ka amsa sunan GARKUWAR HIDAYA,Uncle Khaleel a yau kaima ka za ma GARKUWA TA”

A d’imauce kowa ya maida hankalinsa b’angaren da Alhaji Maude yake,ganin ya fizge bindigar hannun d’an sandan da ke kusa da shi ya ture shi k’asa,sannan ya saita Alhaji Mudassir da bindigar yana faman nishi kamar kumurci,dukkan mutanen da ke wajen mik’ewa suka yi cike da firgici,Mai shari’a ya dinga bawa Alhaji Maude umarnin ya ajiye bindigar hannunsa,kar yayi harbi da ita a kotu yake,amma Alhaji Maude ya cigaba da zare idanu yana kallon Daddy da ya d’aga hannu sama,take Alhaji Maude ya fara magana cikin tsawa.

“Duk wanda ya motsa sai na harbeshi,yau k’arshenka ya zo Mudassir,za ka fara mutuwa kafin ni na mutu,wallahi ba zaka rayu a duniya ni na mutu ba,yadda ka tonamin asiri nima sai naga bayanka kafin kaga bayana” Ya sake saita bindigarsa saitin da Daddy yake ,Alk’ali na magana amma inah ,Alhaji Maude niyyar harbi kawai yake,a dai dai lokacin da yake niyyar d’ana kunamar bindigarsa Hamza da Khaleel suka fara takowa suna nufo in da Daddy yake,Alhaji Maude yayi magana cikin kakkausar murya.

“Duk wanda ya matso inda yake tare zan harbe ku,dan haka ku barni na aiwatar da abinda nayi niyya” a lokaci d’aya Hamza da Khaleel suka nufi Daddy suna shirin tureshi saboda kar harbin ya same shi,a lokacin ne kuma Alhaji Maude yayi harbin ,k’arar harbin da ta gigita kotun,ganin mutum d’aya daga cikin mutane uku ya fad’i alamar shi harbin ya sama,sai ga Hidaya ta k’wallara wata irin k’ara da ta sake hargitsa mutanen kotun,take kuma ta fad’i rub da ciki akan cikin ta kafin ma a taro ta……😭

Shin wa harbin ya samu? Alhaji Mudassir? Khaleel? ko Hamza? 😭😭😭

 

 

 

 

 

 

 

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

 

BY HASSANA D’AN LARABAWA ✍️

 

BABI NA CASA’IN DA TARA DA NA D’ARI

*GA DUK WANDA YA KARANTA SHAFIN NAN TO YAYI MIN AFUWA*👏👇

 

***K’arar wani harbin ne ya sake gigita kotun,sakamakon wani d’an sanda da ya harbi hannun Alhaji Maude da ke k’ok’arin sake yin wani harbin,ganin harbin da yayi ba Daddy ya sama ba,take bindigar hannun Alhaji Maude ta fad’i k’asa,yayinda hannunsa ke wani irin karkarwa yana ihu saboda azabar da ta ratsashi,kafin me y’an sanda sunyi kansa sun dak’ume shi.
Khaleel kam a jikin Hamza ya fad’i sakamakon shi harbin ya samu a daidai kafad’arsa ta hagu,tuni jini ya fara wanke jikinsa har ma da jikin Hamza da ke rik’e da shi,wani irin ihu Hamza yake yi yana jijjiga Khaleel wanda bai tab’a yi ba,Daddy ma rik’o Khaleel yake yi yana wani irin kuka da ihu yana ambatar sunan sa,amma Khaleel mirgina kai kawai yake a k’irjin Hamza yana ambaton Allah,kafin kuma Numfashinsa gabad’aya ya d’auke ya sandare a jikin Hamzan,ganin haka take Daddy ya fad’i ya suma a wajen,Hamza kam da ya d’imauce ihu kawai yake yana fad’in “Khaleel d’ina ka tashi,please ka bud’e idanuwanka,Jama’a don Allah ku taimaka min…
Gabad’aya Hamza neman rasa hankalinsa yake yi.

Can gefe ma Fad’uwar da Hidaya tayi akan cikinta sai ga jini ya b’alle mata,kuma ita ma a take ta suma,su Umma na kanta sai kuka suke yi ganin bata numfashi,kowa ya rud’e ya gigice ,dan wasu tuni suka shige k’ark’ashin kujerun da ke kotun saboda razanar da harbin ya haifar musu,yayinda da yawa mutanen da ke cikin kotun sai da suka yi fitsari a wando tsabar tsoro.

A take aka d’ebi Khaleel da Hidaya aka yi asibiti da su, har ma da Daddy da yake kan kulawar y’an sanda Aunty Kubra kuka take kamar ranta zai fita,abubuwa duk sun cab’e mata,ga rashin miji na tsawon shekaru da zata yi,ga kuma k’addarar da ta samu Khaleel,wanda shi zata kalla ta dinga jin dad’i tunda babu fuskar mahaifinsa a kusa da ita.

Likitoci sun karb’i Khaleel da Hidaya da hanzari,in da aka nufi wani b’angare da Khaleel domin cire masa harsashin da ya huda kafad’arsa,Hidaya kuma akayi emergency da ita dan ceton rayuwarta da abinda ke cikinta,sai dai abin ya ci tura,domin Hidaya na cikin matsanancin halin da ko dai a rasata ko a rasa abinda ke cikinta,Lokacin da Likita yayi musu bayanin halinda ake ciki dukkansu kuka suka saka,Hamza ya fad’i k’asa cikin tsananin tashin hankali ya d’aga hannayensa sama yana wani irin kuka idanuwansa tamkar su zazzago,fad’i yake.

“Allah kaine Allah,ina rok’onka ka tak’aita min duk wata k’addara da jarrabawa da za ta sameni a yau….Allah ka ceto min ran Hidaya da Khaleel…Allah ni mai hak’uri da biyayya ne akan duk abinda za ka d’ora min…kuma ba ka d’orawa bayinka abinda ba za su iya d’auka ba…ina rok’on ka Allah kasa kar wannan rana ta zama mafi bak’i a duniyata da rayuwata…wad’annan mutane guda biyu bayan mahaifiyata bani da tamkar su…Allah kai ka had’ani da su har ka sanya min k’aunarsu a ruhina..k’auna mara yankewa…k’auna mai girma…Ya Allah ka basu lafiya….

Sai ga Hamza yana shirin kifewa a k’asa tsabar kuka da tashin hankali,Umma ta taroshi tana rik’eshi jikinta tana kuka,Hamza ya cigaba da kuka yana fad’in.

“Ummana Hidaya da Khaleel…bana so na rasa su…don Allah Umma…

Ya kasa k’arasa maganar saboda abinda ke tokare k’irjinsa.

Mummy kuka,Aunty Sajida kuka,ita kam y’ar tsohuwa kakar Hidaya tafi kowa gigicewa da ganin wannan tashin hankali,sau biyu tana tsula fitsari a wando,yanzun ma tana lakure a gefe jikinta na tsuma sai zare idanu take tana kuka.

Lokacin ne Doctor ya fito ya nemi ganin mutum d’aya wanda ya fi kusanci da Hidaya,ma’ana mijinta ko mahaifinta ko mahaifiyarta,take Mummy ta bishi,saboda Hamza ko iya mik’ewa tsaye ya kasa,Likita ke wa Mummy bayani akan tasa hannu domin a yiwa Hidaya C S a ciro babyn,idan ba haka ba rayuwarsu tana cikin hatsari,take Mummy ta sa hannu tana rok’on likita kan ya taimaka ya ceto rayuwar Hidaya,ita kad’ai ta haifa kuma bata rayu da ita ba,yanzu ne lokacin da za su yi rayuwa tare ya taimaka ya ceto rayuwar Hidayan,likita ya cewa Mummy “Hajiya zan yi iya yina,sauran kuma zan barwa Allah saboda rayuwar Hidaya a hannunsa take”

Nan take aka fara shirin shiga da Hidaya (Operation room),wadda ke cikin wani yanayi na rai kwakwai mutu kwakwai,su Umma kan su da suka ji C S za a yiwa Hidayan hankalinsu ya dad’a tashi ne,amma da likita ya dinga yi musu nasiha nan take suka fara dawowa nutsuwar su,suka fara ambaton Allah da kai kukansu gareshi.

Hamza ma ganin ana shirin shiga da Hidaya d’akin tiyata sai ya fara k’arfafa zuciyarsa,take kuma ya tuna da halin da Khaleel ma yake ciki,take ya mik’e jikinsa na mazari,Umma ta rik’o shi tana ambatar “Ina za ka Hamza?” Cikin wata irin murya yayi magana yana dubanta da idanuwansa da suka jirkice “zan je gun Khaleel ne Umma…ku ku zauna anan ni bari na tafi gun sa” Aunty Sajida ce ta share hawayenta ta jinjina kai tare da duban Hamza ta ce “Mu tafi tare Hamza,su Umma sai su zauna anan a jira hukuncin Allah,can d’in babu kowa sai Aunty Kubra da Y’an sanda” hakan ya sa Umma ta saki hannun Hamza,suka wuce suka nufi b’angaren da Khaleel ya ke.

Sun tarar da Aunty Kubra na zaune tana kuka,nan take sanar musu an shiga da Khaleel d’in d’akin tiyata domin cire harsashin da ke jikinsa,tace musu ita ta tsorata saboda tana ganin kamar Khaleel ba zai tashi ba,nan Aunty Sajida ma ke fad’awa Aunty Kubra halinda Hidaya da d’an cikinta ke ciki,hankalinsu duka ya k’ara tashi suka cigaba da ambaton Allah suna zub da hawaye,Hamza kam jikin garu ya jingina kansa yana jin kansa na juyawa kamar ya mace,tabbas yana cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa.

An d’auki lokaci mai tsawo kafin a kammala aikin cirewa Khaleel harsashin,daga nan kuma likitoci suka yi abinda za su yi sannan suka yi masa allurar bacci aka dawo da shi d’akin hutu aka shimfid’e shi tamkar matacce,har kuma lokacin basu bawa kowa damar ganin Khaleel d’in ba.

A can b’angaren Hidaya an yi aiki cikin nasara,in da aka cirowa Hidaya baby boy me matuk’ar kyawu da d’aukar hankali,su kansu likitoci sunyi mamaki da suka ga yaron tuk’ek’e mai girman gaske,wanda wasu yaran y’an wata tara ma basa yin girma irin wannan,amma sai gashi shi d’an wata bakwai(bakwaini)yayi wannan girman,ikon Allah kenan.

Bayan sun gamawa Hidaya komai ita ma aka gangaro da ita d’akin hutu,likita ya tabbatarwa su Umma lafiya k’alau take sai dai sun mata allurar bacci dan ta samu hutu,Lokacin da aka kawo musu jaririn sunyi matuk’ar murna duk da suna cikin wani yanayi na tunanin halinda Khaleel ke ciki,Allah kenan mai yadda ya so,Khaleel ya samu k’aruwa a lokacin da yake cikin wani yanayi.

Mummy ce ta kira wayar Aunty Sajida take sanar da ita haihuwar, “Alhamdulillah” kalmar da Aunty Sajida ta fad’a kenan wadda ta sanya Hamza bud’e idanuwan sa ya zuba mata su don neman k’arin bayani,haka ma Aunty Kubra ke kallonta,sauke wayar tayi ta ce musu.

“Allah ya sauki Hidaya lafiya,an samu yaro Namiji,da Hidayan da jaririn duk suna cikin k’oshin lafiya”

Wani irin lumshe idanuwa Hamza yayi,hawayen dad’i ya tsiyayo masa,take ya godewa Allah da fad’in “Alhamdulillahi ala kulli halin”sannan ya zarce da fad’in “Allah ya tashi kafad’arka Abokina,ka bud’e idanuwanka kaga wani arzik’i mai girma da ubangiji ya azurtamu da shi”

Aunty Kubra ma tayi murna sosai duk da har lokacin hankalinta a tashe yake.

 

 

 

*************

 

Kusan lokaci d’aya Khaleel da Hidaya suka farka, a lokacin ne kuma likitocin suka bayar da umarnin ganinsu, ta b’angaren Khaleel akwai Hamza da Aunty Kubra da Aunty Sajida,lokacin da suka shiga d’akin da hanzari Hamza ya isa gadon da Khaleel ke kwance,an nannad’e kafad’arsa da bandeji in da aka ciro harsashin,idan kaga Khaleel dole ka tausayawa yanayin da yake ciki,Hamza na zuwa hannun Khaleel d’in ya kamo yana k’ank’amewa kamar zai had’iyeshi,Khaleel ya bi Hamza da wani irin kallo yana runtse idanuwansa saboda azabar da yake ji a sassan jikinsa musamman k’irjinsa,Sannu suka dinga jerawa Khaleel gabad’ayan su,gyad’a kai kawai yake yi bakinsa ya kasa furta komai,kuma maganar yake son yi,Hamza ke tambayar Khaleel shin ko yana jin ciwo sosai ne a fad’awa likita?Khaleel ya jinjina kai yayi magana a hankali wadda sai da Hamza ya kai kunnensa dab da bakin Khaleel d’in sannan yaji abinda yake fad’a.

“Ina jin ciwo Aboki,musamman a cikin k’irjina,amma likita babu abinda zai iya yi min,domin yayi dukkan wani k’ok’ari da zai iya”

Aunty Kubra ce ta matso sosai tana tambayar Hamza abinda Khaleel ya ce,Hamza ya fad’a mata,sai ta kama sharar hawaye tana fad’in “Allah ya baka lafiya Khaleel,ubangiji ya tashi kafad’un ka”

Jin Khaleel na janyo hannun Hamza sai Hamzan ya sake matsawa sosai jikinsa yana tambayarsa “Kana son wani abu ne?” Khaleel ya d’an yamutsa fuska jin kafad’arsa kamar ba a jikinsa take ba,sannan ya cewa Hamza “Ina Hidaya…?” Wani d’an murmushi ne ya sub’ucewa Hamza a yayin da yake fad’in ” Hidaya tana tare da su Umma,a yau kuma Allah ya sauketa lafiya an samu lafiyayyen Namiji,duk da har yanzu banga yaron ba saboda ina tare da kai” Wani kyakkyawan Murmushi Khaleel ya saki duk da ciwon da yake ji,ya k’urawa Hamza idanu yana fad’in “Alhamdulillahi,Allah na gode maka da ka azurtani da babban arzik’i” sannan ya ce wa Hamza “Aboki cikin Hidaya wata bakwai ne fa bai isa haihuwa ba ko?” Hamza ya sake damk’e hannunsa ya ce “Halin da taga ka shiga ne ya sababba mata shiga yanayi mara dad’i,shine dalilin da yasa aka yi mata C S aka ciro jaririn dan kar a samu matsala,amma duk suna cikin k’oshin lafiya a yanzu haka”

D’aga idanuwa Khaleel yayi yana ta hamdala ga Allah,daga nan kuma ya dubi Aunty Kubra yayi magana,lokacin muryarsa har ta fara washewa dalilin farincikin da ya samu kansa ciki, “Aunty don Allah a kawo min jaririn mana na ganshi,idan zai yiwu har da Hidayan ma,ina jin kamar nayi tsuntsuwa na gansu wallahi”

Sai Aunty Kubra ta d’anyi murmushi,sannan ta juya Aunty Sajida ta bi ta a baya suka fice suka nufi b’angaren da Hidaya take.

 

*************

 

“Don Allah Umma ku sanar da ni gaskiya idan Uncle Khaleel ya mutu…idan kuma bai mutu ba ku kaini na ganshi….

Abinda Hidaya take ta ambata kenan tana daga kwance,hawaye na tsiyayo mata ta gefen fuskarta,Umma ta kai hannu ta share mata hawayen sannan ta rik’o hannunta guda d’aya tana matsawa a hankali ta ce.

“Me ya sa kika kasa yarda da abinda na fad’a miki?Khaleel yana nan da ransa bai mutu ba Hidaya,kin san ai ba zanyi miki k’arya ba”

Cikin kuka Hidaya ta kuma cewa “Na san ba zaki fad’a min abinda ba haka yake ba Ummana,to amma idanuwana sun kasa manta yadda naga Uncle Khaleel ya fad’i sanda aka harbe shi,don Allah Ummana ki taimakawa numfashina ki kaini naga Uncle Khaleel”

Umma ta dafe kanta,magiyar da Hidaya take mata ta raunata zuciyarta,sai Mummy ce ta matso tana shafa kan Hidayan kafin tayi magana a hankali.

“Ke Hidaya d’ago kanki ki kalleni”Hidaya ta d’ago tana kallon Mummy sai kuka take,Mummy ta girgiza mata kai ta ce “Kiyi hak’uri kinga d’inki ne a jikin ki fa,ko kin manta Haihuwa kika yi?tsaga jikinki fa aka yi aka fito da jariri,kiyi hak’uri bari a kawo miki yaron da kika haifa ki gani kinji”

Girgiza kai Hidaya tayi,hawaye na tsananin zuba ta ce da Mummy “ah ah ni ba shi nake son gani ba Mummy,idan kuna so na kwantar da hankalina na daina kuka to ku kaini wajen Uncle Khaleel,ganinsa kawai zanyi sai ku dawo dani don girman Allah Mummy”

Suka rasa yadda za su yi da Hidaya,gabad’aya ta tashi hankalinsu ta addabesu da rigima da kuka da magiya,ita fa kawai Uncle Khaleel take son gani,a dai dai lokacin ne su Aunty Kubra suka shigo d’akin suka tarar da wannan rigima ta Hidaya,da k’yar ta amsa sannun da suke mata tana kuka,suka karb’i jaririn a hannun Ummansu Sajida suna dubansa cike da murnar samun sa,kyakkyawan jariri fari tas da shi har wani ja yake,Aunty Kubra ta rungumeshi jikinta tana hawaye.

Ganin kukan da Hidaya ke yi ya fara yawa kar ya tab’a mata aikinta sai Kakarta tace a tambayi likita idan zai yuwu ko a gadon marasa lafiya ne sai a turata a kaita ta ganshi domin dai hankalinta ya kwanta,haka kuwa aka yi,shi kansa likitan ya tsorata da kukan da Hidaya take tana numfarfashi,hakan yasa ya bayar da umarnin wasu nurses su d’auko gadon da ake tura marasa lafiya a d’orata a kai sai a kaita,take kuwa suka aikata umarnin likita aka d’auko gadon aka d’ora Hidaya,sai lokacin Hidayan ta ji farinciki a zuciyarta.

Su Aunty Kubra ne suka fara yin gaba rik’e da jaririn a hannunsu,wanda yayi luf da shi cikin shawul yana baccinsa,suna shiga d’akin da sauri Hamza ya mik’e ya taro su ya karb’i jaririn fuskar sa cike da annashuwa yana ta hamdala,wajen Khaleel ya nufa yana rik’e da shi ya haska masa shi yana cewa “Ga kyauta daga Allah ya iso Khaleel” duk da bala’in da Khaleel yake ji a k’irjinsa da kafad’arsa hakan bai hanashi sakin murmushin da ya jima baiyi ba,cikin wata irin murya yace wa Hamza”Aboki d’ora min shi a k’irjina” Hamza ya zaro idanu yana girgiza kai ya ce “Yanzu fa ka gama ce min zuciyarka na ciwo,ta ya ya za a danne k’irjin da ba shi da lafiya?” Khaleel ya lumshe idanu ya ce “Ko ya ya dai taimaka ka d’ora min shi Aboki,ko sau d’aya ne muji d’umin juna ni da shi” Sai Hamza ya rausaya kai,ya matsa a hankali ya d’ora jaririn a k’irjin Khaleel,take Khaleel ya lumshe idanuwan sa hawaye ya tsiyayo,hawayen murna,hawayen godiya ga sarki Allah! mai kyautar abin da babu wani bawa da ya isa yayi maka idan ba shi ba.

A lokacin ne aka shigo da Hidaya cikin d’akin ana tura ta a gadon,su Umma gabad’aya suna biye da ita,har gaban gadon da Khaleel yake aka kai Hidaya,sai lokacin Hamza ya k’araso kusa da ita yana duban ta d’auke da tausayi akan fuskarsa,a hankali yake mata sannu,ta amsa da “Yawwa Ya Hamza” sai kuma ta waiwaya tana duban Khaleel da ke amsa sannun da su Umma ke masa,ta k’ura masa idanuwa take kuka ya b’alle mata,sai Khaleel ya juyo ya tsura mata ido kafin ya girgiza mata kai alamun ta dena kuka,a hankali yace mata ” To menene abin kuka kuma?ke da za ki yi farinciki Allah yayi mana babban arzik’i da ba kowa yake samu ba,ki daina kuka kinji Hidaya,komai da kika gani muk’addari ne daga Allah,duk wasu abubuwa da suke ta faruwa a rayuwar mu tuni daman Allah ya rubuta sai sun faru,yanzu dai kinga jaririn na mu ko?”

Tana shesshek’ar kuka tace” Ni ba shi nake son gani ba,baban shi nake son gani daman” Sai Khaleel yayi murmushi yana nuna Hamza da baki sannan ya ce “To ai ga baban na shi can fa” duk suka juya suna kallon Hamza wanda ke murmushi yana sunkuyar da kai.

Khaleel ya sake ce wa Hamza “Aboki d’an matso min da shi,ka sa kunnensa saitin bakina ina so in mishi hud’uba ne” Aunty Kubra ta ce “Hakan na da kyau,bari naje k’ofar asibitin nan naga akwai masu sayar da dabino da zam zam sai na siyo kayi amfani da su”

Bata jima ba kam ta dawo da su a hannun ta,Hamza ya matsar da jaririn Khaleel yayi masa hud’u ba,sannan ya tauna dabinon ya sanya masa a baki,sai ga jariri yana mulmul da baki,Hamza yayi dariya yana fad’in “Kalle shi wai shima daga zuwanshi duniya ya san zak’i…ko da yake gado yayi,mamanshi ma haka take da son zak’i” ya fad’a yana duban Hidaya,ita kam hankalinta gabad’aya na kan Uncle Khaleel”

Khaleel ne ya ce wa Hamza “Aboki zo ka d’auke takwaran ka ka bawa su Umma shi” Hamza ya k’ura masa idanuwa ya ce “Takwarana kuma?” Khaleel yayi murmushi ya lumshe idanu ya ce “Eh takwaran ka mana! Sunansa HAMZA ,da sunan nayi masa hud’uba”kafin Hamza ya ce komai sai Khaleel ya cigaba da magana “Ka san me ya sa na saka masa suna HAMZA? saboda ina son ya d’auko komai na ka,kyawun ka…ibadarka…kirkinka…addininka…halayyarka…ililiminka…ladabinka…biyayyarka…tauhidinka…nagartarka…mu’amalarka…kyawun zuciyarka…iliminka…da komai na ka Aboki…na tabbatar idan ya kasance haka zanyi alfahari da shi…zai zame min ولد صالح wanda ko bayan ba raina zai dinga tunawa da ni yana min addu’a”

Sai Hamza ya fashe da kukan murna,kowa na d’akin godiya yake wa Khaleel domin tabbas jajirin yayi dace da suna mai Kyau,Hidaya kanta murna take yi mai yawa,domin burinta kenan ta samu d’a ta saka masa suna HAMZA,girman sunan da darajar da yake da shi a gareta ba zai lissafu ba.

 

Sai bayan sallar isha’i ana shirin mayar da Hidaya d’akinta sannan Khaleel ya ce da su Umma don Allah yana son yayi magana da Hidaya da Hamza su kad’ai,sai su Umma suka fita suka basu guri,Hamza ya janyo kujera ya zauna a tsakiya,ga Khaleel kwance kan gadon sa,ga Hidaya ma kwance kan gadon da aka kawota,Khaleel ne yayi gyaran murya ya dubi Hidaya yayi mata wata tambaya.

” Me ya sa kika aureni?”
Shiru tayi ta k’ura masa idanuwa kawai,domin bata san amsar da za ta bashi ba,hakan da ya gani sai ya lumshe idanu ya ce “Ni na san a tarbiyyar da Aboki ya baki ya d’oraki a kan fad’ar gaskiya komai d’acin ta,don Allah Hidaya kar ki min k’arya,kar ki fad’i wani abu dan naji dad’i,fito min da gaskiyar ki ki fad’a min me ya sa kika amince da ni har kika aureni?”

Hawaye ya tawo mata,tabbas Khaleel ya d’aureta da jijiyar jikinta,sai ta zab’i fad’ar gaskiyar kawai tunda ita yake son ji,hakan ya sa ta sanyaya murya tace “Saboda Ya Hamza,domin ka kasance Zab’insa a gareni” Khaleel ya runtse idanu sosai wani abu ya soki k’irjinsa,sai Hidaya ta cigaba da magana tana ce wa “Amma Uncle Khaleel daga lokacin da na aureka naji soyayyarka da k’aunarka ta shiga raina,a lokacin da na fara sonka a lokacin kuma rabuwa ta riskemu bamu zata ba” Sai Khaleel ya bud’e idanuwansa hawaye ya sakko masa,a take yace wa Hidaya “Kin san wani abu?har yanzu bakya sona,kina dai k’aunata kuma kina tausayina,amma so na soyayya ba ni kike wa shi ba ABOKINA kike wa” Take Hamza ya zabura cikin zare ido da gigicewa yake duban Khaleel,bakinsa har rawa yake wajen fad’in “Meye haka Khaleel…wace irin magana ce wannan?ta ina wannan maganar mara tushe balle makama ta b’ullo?yanzu har zafin ciwo ya sa ka fara irin wannan sambatun Khaleel…?don Allah…
D’aga masa hannu Khaleel yayi yana dakatar da shi,cikin wata irin murya ya ce.
“Dakata Aboki babu abinda za ka fad’a min domin na san komai,kullum kai ne me d’oramu a tafarkin gaskiya akan me kake so kayi k’arya a yanzu domin naji dad’i? duk abinda zaka fad’a ba zan tab’a yarda da kai ba Aboki,abin da baka sani ba na san komai,na san son da kayi wa Hidaya,a ranar da naje gidanku baka nan na shiga d’akinka anan ne na ci karo da (diary) d’inka wanda sirrinka ke ciki,ka gafarceni Aboki domin na d’auka na karanta abinda ke ciki,ban tab’a jin tashin hankali irin na ranar ba,domin naga tsantsar So da K’auna da ka nunawa Hidaya a ciki,nayi danasanin shigowa rayuwarku da raba soyayyarku mai girma,me ya sa kayi min haka?me ya sa baka sanar da ni kana sonta ba?me ya sa ka bani ita na aura alhali kana sonta?Hamza wace irin zuciya ce da kai?wane irin so kake min da ka zab’i farinciki na akan na ka farincikin?”Khaleel ya fashe da wani irin kuka,Hamza kam dafe kansa yayi yana jin kamar ya fad’i,sirrin da yake ta b’oyewa yau gashi ya bayyana,shi ma kukan ne ya kufce masa ya matsa yana rik’e hannun Khaleel,hawayen sa na d’isa a hannun Khaleel d’in kafin ya bud’e baki ya ce.

“Ka na ji ko Khaleel..wannan ba komai bane,ba Hidaya ba ko dukkan abinda na mallaka kake so wallahi zan baka,ai mutum na gari baya manta alkairi,menene baka yi min ba a rayuwa Khaleel?duk wani abu da ka san zan ji dad’i ya d’aga darajata kayi min shi,Khaleel ban da mahaifiyata da tayi ta k’ok’ari a kaina bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya kaika tallafata a rayuwa,sai kuma dan ka nuna kana son abinda nake so na hanaka?sai nabi son zuciyata na so kaina?ba haka zuciyata take ba Khaleel,ni ina sowa d’an uwana musulmi abinda zan sowa kaina na alkairi,wallahi Khaleel da zuciya d’aya na bar maka Hidaya,tabbas na san na sota so mara adadi,amma da na fallawa raina hak’uri sai Allah yayi min jagora wajen mantawa da komai,banyi hakan da wata manufa ba sai dan ka samu abinda kake so Khaleel,kuma daman Allah ya nufa kaine mijin Hidaya ba ni ba,tunda komai da yake faruwa da sanin Ubangiji ne Khaleel”

Khaleel ya damk’e hannun Hamza yana kuka sosai,a hankali ya girgiza kai yana cewa ” Na sani aboki kai mutum ne mai kyakkyawar zuciya da tsantsar imani,kuma hak’urin ka shi ya kaika matakin nasarar da za ka mallaki Hidaya a halin yanzu” Da sauri Hamza ya dubeshi,sai ya jinjina masa kai tare da fitowar hawaye,sannan ya cigaba da cewa “Babu wani d’a namiji da ya dace da rayuwar Hidaya fa ce kai,Hidaya taka ce aboki,shigar sauri kawai nayi maka,amma da yake ita d’in ba matata ba ce sai Allah yayi nufin raba auren da wuri,ka lura da kyau akwai abinda Allah yake nufi da rabuwata da Hidaya Aboki,a yanzu Hidaya bata da wani miji sai kai,ni daman babu wani zama da yayi ragowa tsakani na da ita,domin ni tawa ma ta k’are,wallahi Aboki ciwon da nake ji a zuciyata ba lallai na k’ara kwana d’aya a duniya ba,rok’ona a gareka ka auri Hidaya ka rik’eta da jaririn da ta haifa maka,domin d’anka ne,duk in da aka je HAMZA NE UBAN HAMZA, GARKUWA NE UBAN GARKUWA,rok’ona na biyu gareka shine ka kula min da Mahifina,na san k’ila Allah ba zai sake had’a fuskokinmu ba,ka fad’a masa naji dad’i da ya karb’i hukuncinsa tun a duniya,kuma ina addu’a da fatan hakan ya zame masa kaffarar dukkan laifukan da ya aikata,ka kasance mai yi masa nasiha,domin tabbas Daddy zai yi rashi,zai rasani bayan ya rasa mahaifiyata,bayan Daddyna na sani babu wanda zai kaika kukan rashina Aboki,sai dai kayi hak’uri,Khaleel d’inka ba mai tsawaicin kwana ba ne,Dan Allah Aboki ka auri Hidaya,ka aureta domin ka cigaba da zama GARKUWARTA,naji dad’i da komai ya zo k’arshe,rok’ona a gareku kar ku manta da ni,ku dinga sanyani a addu’arku ko zan samu salama cikin k’abarina”

Kukan da Hamza da Hidaya ke yi yayi yawa,har su Umma da ke waje suka fara jiyo wa,hakan yasa suka shigo da hanzari suna tambayar abinda ya faru,Hamza ya kife kansa kan gadon da Khaleel ke kwance zuciyarsa tamkar ta fito,kuka yake wanda bai tab’a yin irinsa ba,Umma ta nufi Hidaya tana rik’eta ganin tana yunk’urin mik’ewa,cikin tashin hankali Hidaya ke rusa kuka tana cewa da Umma “Umma Uncle Khaleel ne ya saka mu kuka,yana ta cewa mutuwa ziyi kuma ya san ba zamu jurewa rashinsa ba,don Allah Umma kice masa ya daina fad’a domin na san idan ya mutu Ya Hamza ma binsa zaiyi?to ni kuma ya zanyi Umma?ni kad’ai zan zauna a duniyar kenan duk GARKUWATA sun k’are?

Hawaye ya zubowa Umma na tausayin su gabad’aya,a hankali take rarrashin Hidaya,yayin da su Mummy ke gefe kowa yana sharar hawayen tausayi,Khaleel kam hannu yasa yana shafa kan Hamza da ke kife ya jingina da k’irjinsa,a hankali kuma ya rufe idanuwansa yana ta cewa “Kayi hak’uri Aboki….kayi hak’uri Aboki…kayi hak’uri Aboki”

Har wajen goma na dare suna d’akin kafin likita ya zo ya bayar da umarnin mayar da Hidaya d’akinta saboda allurori da magunguna da zai bata,haka aka fita da Hidaya na kuka sosai,babyn ma ya farka yana ta kuka alamar yunwa yake ji,Umma da kanta ta fito da Nonon Hidaya aka sanyawa babyn a baki,nan da nan ya kama yana sakin ajiyar zuciya,Hidaya ta runtse idanu tana jin tausayin d’anta da soyayyarsa a zuciyar ta,bayan ya gama sha likita yazo ya bata magunguna sannan yayi mata allurar bacci,Umma ta ce da su Mummy su koma gida ita da Aunty Sajida da kakar Hidaya,ita za ta kwana da Hidayan,yayin da Hamza zai kwana da Khaleel shi da Aunty Kubra,shima kuma Khaleel d’in an masa allurar bacci ne dan ya samu sauk’in ciwon da ke addabarsa.

 

Sai can cikin dare Hamza na zaune kujerar da ke gefen gadon Khaleel d’in ya kifa kansa, hannunsa sark’e cikin na Khaleel d’in,ba bacci yake ba zuciyarsa ce kawai babu dad’i,Aunty Kubra kam tana zaune sai gyangyad’i ke kwasarta,Hamza ne ya ji tamkar ana jijjiga hannunsa,da hanzari ya d’ago kansa yana duban Khaleel sai yaga jikinsa na rawa kamar wanda ake jijjigashi da k’arfi,a tsorace ya mik’e yana rik’o shi yana ambatar sunansa,Khaleel juya kai kawai yake azaba ta isheshi,da k’yar ya fizgo magana cikin nishi kamar numfashinsa zai fice” Aboki zuciyata ciwo,danna min k’irjina zai tsage” Hamza ya rud’e ya rasa ya zaiyi,ya k’walawa Aunty Kubra kira ta farka a gigice ta tashi ta nufo su,ganin yadda Khaleel ke yi sai Aunty Kubra ta rud’e ta fashe da kuka tana ambatar “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un….shikenan Khaleel haka zaka yi mana? Hamza ya gigice har bai san lokacin da ya rik’e hannun Aunty Kubra ba,yana ce wa “Menene Aunty?Me zai mana?don Allah menene?” Aunty Kubra ta kuma fashewa da kuka ta ce” Wallahi Hamza Khaleel mutuwa zaiyi,an tab’a yin mutuwa a gabana,duk wasu alamu da na gani sun tabbata a yanayin Khaleel yanzu” Hamza ya girgiza kai kamar mahaukaci yana duban Aunty Kubra” Ba mutuwa zaiyi ba…Khaleel ba zai tafi ya barni ba Aunty…

Aunty Kubra ta katseshi “Shikenan Hamza bari naje na kirawo likita,kai kuma zauna a wannan kujerar kai ta fad’a masa kalmar shahada,amma ni dai na tsorata da Khaleel” tana fad’in hakan ta fice da sauri,yayin da Hamza ya juyar da idanuwansa yana duban Khaleel da ke wani irin nishi da k’arfi idanuwansa a warwaje ya damk’e hannun Hamzan sosai,sai Hamza ya sake fashewa da Kuka yana ambatar “La ilaha illallahu muhammadur rasulallah ( S A W).

 

**********

 

Kamar wadda aka tasa daga barci firgigit ta farka,ta d’aga kanta tana duban Umma da ke bacci kan daddumar da ke shimfid’e,a hankali ta yunk’ura ta mik’e zaune tana cije leb’e,ta sanya hannu ta matsar da jaririn da ke gefenta sannan ta zuro k’afafuwanta sa sauko daga gadon,kamar me koyon tafiya haka ta dinga salallab’awa a hankali dan kar ta tashi Umma har ta fice daga d’akin ta nufi d’akin da su Khaleel suke.

Tun daga k’ofar shiga take jin muryar Hamza na kalmar shahada,da sauri ta tura k’ofar d’akin ta afka tana nishi,Hamza ya d’ago yana kuka ya dubeta sanda ta k’araso idanuwa warwaje take cewa “Ya Hamza me ya faru?” jikin ne ya tasar masa?” gyad’a kai Hamza yayi kafin ya sanya hannu ya janyo ta kusa da shi,a hankali cikin kuka ya ce mata”Ke ma ki dinga fad’in abinda nake fad’a” take suka had’a baki suna ta maimaita kalmar shahada suna kuka,tun Khaleel na wani irin nishi me k’arfi da juya kai har ya fara sassautawa,a k’arshe sai ga bakinsa ya kama ambatar kalmar da su Hamza da Hidaya ke nanata masa,ya fad’a kusan sau hud’u sai kuma idanuwansa suka yi sama yana damk’e hannun Hamza sosai,daga nan jikinsa ya fara saki har rai ya k’arasa ficewa daga jikinsa 😭a wannan tsakiyar dare na ranar Alhamis,a lokacin ne kuma Aunty Kubra da likita suka shigo d’akin da hanzari.

Hamza bai san mutuwa ba,amma yana ganin yadda Khaleel yayi ya tabbatar ya rasa shi kenan😭,Khaleel ya tafi ya barshi,k’asa kawai yayi ya durk’ushe yana jin ina ma shima ya mace,Hidaya ta bishi tana damk’ar kafad’arsa tare da girgiza shi tana cewa “Ya Hamza menene ne?ya naga Uncle Khaleel ya daina motsi?” Hamza cikin sark’ewar numfashi ya ce .
“Mun rasa shi Hidaya,yau munyi rashin Khaleel…daman ya fad’a mutuwa zaiyi muna ganin kamar k’arya ne ashe gaskiya ya fad’a…Khaleel d’ina ya tafi ya barni mutuwa ta rabani da shi….😭

Take Hidaya ta sulale a jikin Hamza sumammiya,shi ma Hamzan idanuwansa suka fara lumshewa yana shirin kifewa Aunty Kubra da likita suka taro su cikin tashin hankali.

 

***************

 

Ni Hassana D’an Larabawa hannuna yayi kad’an wajen rubuta matsanancin halin da Hamza da Hidaya suka kasance dalilin rasuwar Khaleel,damuwa tai damuwa😭,kewa tai kewa😭,idanuwa sun koka😭,zuciyoyi sun raunana😭,sai dai ya za a yi da hukuncin ubangiji? wanda shine ya halicci Ibraheem Khaleel kuma ya karb’eshi a lokacin da yake so.

A safiyar Juma’a ne kuma da aka wayi gari aka tawo da gawar Khaleel tsohon gidan su na garin Kaduna,anan aka shirya shi,har da HAMZA cikin masu wanke gawar Khaleel, da shi aka shiryashi cikin likkafaninsa,yana kallonsa akwance babu motsi,babu magana,babu murmushin da kullum yake masa,babu mai ambatarsa da kalmar Aboki,sunan da tun ranar da Allah ya had’asu Khaleel d’in ke ambatarsa da shi,amma a yau komai ya k’are,Hamza yana gabatar da abubuwa ne kawai amma ba a cikin hayyacinsa yake ba,kuka kuwa sai da ya zama da k’yar idanuwansa ke bud’uwa,addu’a kam da samun yabo idan yana yawa to zaiwa Khaleel yawa,kowa yabonsa yake domin Khaleel mutum ne mai alkairi da zama lafiya da mutane.
Ana shirin sallatar gawar Khaleel sai ga y’an sanda guda uku sun rako Daddy,duk wanda yaga Daddy da halin da ya shiga dole yayi kuka,musamman da ya fara cin karo da Hamza sai ya rungumeshi yai ta kuka yana fad’in “Ba ni aka yiwa mutuwa ba kai aka yi wa mutuwa Hamza,sai dai kayi hak’uri,amma na san rashin Khaleel zai cigaba da tab’a ka har ranar da za ka bishi” Daddy har gaban makarar da aka saka Khaleel yaje ya tsuguna,yayi masa addu’o’i masu yawa tare da fatan shigarsa k’abarinsa cikin sa’a da tarar da alkairi,har ya dinga surutai wad’anda ke k’ara karya zuciyar mutane suna kuka,musamman da ya ce “Ban tab’a ganin d’a mai biyayya kamarka ba Khaleel,tun kana yaro nake amfani da dama ta nake tank’waraka yadda nake so,baka tab’a bijire min ba sai biyayya a gareni,ko iya wannan ta isa ta shigar da kai Aljanna,bana jin d’acin rayuwar da zanyi a gidan yari kamar d’acin rashinka,na yafe maka Khaleel kuma ina maka fatan samun rahamar ubangiji” Daddy ya dinga kuka hawaye na sharara,sai ga y’an sandan da suka rakoshi suna sharar hawayen tausayi.

Bayan an wa Khaleel Sallah sai aka d’aukeshi domin kaishi gidan sa na gaskiya,da Daddy da Hamza sune suka saka Khaleel a cikin k’abarin sa aka binne shi😭,aka yi addu’o’i sannan aka fara watsewa,Hamza yana ji kamar kar ya tafi,shikenan fa rayuwar,duniya ba matabbata ba,Allah kasa mu cika da kyau da imani👏😭

Daga Mak’abarta sai y’an sanda suka wuce da Daddy,daman an masa alfarma ne dan zuwa jana’izar Khaleel,nan ma Hamza yayi kuka yana tuna wasiyyar Khaleel kan kulawa da mahaifinsa,kuma ya d’auki wannan alk’awari muddin yana da rai zai kula da Daddy tamkar mahaifinsa da ya haifeshi.

Ita kam Hidaya har lokacin tana asibiti cikin mawuyacin hali,Aunty Sajida ke lura da ita,babyn sai kuka yake yi kamar yana da masaniyar mahaifinsa ya rasu,ranar da ya zo duniya ranar ya rasa mahaifinsa,sai dai ba zaiyi maraici ba,tunda akwai Hamza a filin duniya.

A can gida tare da su Umma da Mummy aka cigaba da zaman makoki,Hamza ya kasa hankalinsa biyu ne daga gida zuwa asibiti gano halinda Hidaya ke ciki,idan ya karb’i takwaransa Hamza yana zubda hawayen rashin mahaifinsa Khaleel a kusa da shi,Allah sarki Khaleel,ya tafi ya bar zukata da kewa idanuwa da zubda hawaye😭.

Allah ne kawai ya rubuta da kwanan Hidaya a gaba,amma ta sha wahala matuk’a da gaske kafin komai ya daidaita,kullum haka take sanya Hamza a gaba da kuka har ma ya rasa ya zaiyi,lokacin zuciyar Hamza ta zama tamkar ta mata,shima kukan yake a kullum,Umma ta rasa yanda za ta yi dasu musamman idan aka rasa me rarrashin wani a tsakanin su,sai su sanya Hamza k’arami a gaba suyi ta kuka,a rasuwar Khaleel Hamza ya had’u da lalurar hawan jini saboda tsananin damuwa har sai da ta kaishi ga kwanciya a asibiti kamar shi ma zai mace,nan da nan Hidaya ta fara nutsuwa ganin shi ma za ta rasa shi,a ganinta idan ta rasa Khaleel ta jure ba zata iya jure rashin Hamza ba,mutuwar Hamza tamkar mutuwarta ne.

Har Khaleel yayi watanni hud’u da rasuwa basu dawo cikin hayyacinsu sosai ba,duk juma’ar duniya kuma sai Hamza ya shirya ya kaiwa k’abarin Khaleel ziyara tare da addu’o’i na musamman,da har ya fara zuwa da Hidaya,amma ganin tashin hankali da kukan da take yi sai yake barinta a gida yaje shi kad’ai,Hamza k’arami na ta girma da wayo,k’aunar da Hamza ke masa ba za ta lissafu ba,kusan ma shine me rainonsa da kulawa da shi,ko ya yaji yayi kuka yanzu hankalinsa zai tashi ya dami Hidaya akan ta ba shi Nono,shi kansa yaron yayi sabo da shi ta yadda idan bai ga Hamzan ba sai yayi ta kuka yana neman sa,shak’uwa ce mai girma a tsakanin su.

Hamza yana ziyartar Daddy akai akai domin duba lafiyarsa,idan yaga halinda Daddy ke ciki yana jin k’unci a ransa,sai dai babu yadda zaiyi,kullum yaje suka ga juna sai sun yi kukan tunawa da Khaleel,kuka ya zame musu jiki,Aunty Kubra ma ta jima kafin ta dawo nutsuwarta,ba k’aramin duka mutuwar Khaleel tayi mata ba,Su Alhaji Maude tuni aka zartas musu da hukuncin su,duk da hakan zuciyar Hamza bata yi sanyi ba,dan bai da wani mak’iyi da ya wuce Alhaji Maude wanda shine sanadi ko kuma silar mutuwar Khaleel,duk da babu wanda yake mutuwa sai lokacinsa ya yi,kaf dukiyar Khaleel Hamza k’arami ne ya ci gadonta,domin Daddy yace ba zai karb’i komai ba shima ta sa rabin dukiyar ya mallakawa Hamza k’arami da Hidaya da Hamza babba,rabin kuma ya barwa Aunty Kubra da y’ay’anta guda biyu,a ganinsa babu wata rayuwa a gabansa ta jin dad’i,yana fatan ma kafin ya cika shekaru gomansa na gidan yari Allah ya d’auki rayuwarsa ya huta.

 

************

Shekaru biyu suka shud’e bayan mutuwar Khaleel,lokacin tuni Hidaya ta yaye Hamza k’arami,a lokacin ne kuma sai ga uban masoya sun fara tuttud’owa domin auren Hidaya,nan da nan hankalin Umma ya tashi ta samu Hamza tayi masa fata fata,tace idan ba zai auri Hidaya ba to wallahi zata bawa wani dama ya fito,zai rasata a karo na biyu,domin zurfin cikinsa yayi yawa,Hamza ya dinga bawa Umma hak’uri yana hawaye ,wai daman yana jira ne Hidayan ta yaye Hamza,kuma yana so yaji idan har lokacin tana son sa,mamaki ya kama Umma har ta ce masa “Da man Hamza soyayya na tsufa ne?ai sai dai masoyan su tsufa,wallahi babu wani namiji da Hidaya za ta so tamkarka har duniya ta nad’e”

“INA SON TA UMMANA,INA MATUK’AR K’AUNAR TA” Hamza ya fad’a kansa a sunkuye,hawaye na saraftu saboda tunawa da Khaleel da yayi,Allah sarki rayuwa…

A wannan lokaci ne aka d’aura auren HAMZA DA HIDAYA,wani aure mai cike da tarihi da zukata ba za su mantaba,rana mafi daraja da soyuwa a zukatan ma’auratan,domin sun fitar da rai da ita sai gashi Allah ya nufe su da ganinta,lallai hak’uri da k’addara da jarrabawa mataki ne na nasara a rayuwa,dole sai an jarrabeka sannan za ka ji dad’i,ko a yanzu ma cikin wata jarrabawar suke ta rashin Khaleel a kusa da su…
Ranar da suka kasance inuwa d’aya makwanci d’aya an tafka soyayyah,soyayya mara iyaka! soyayya mai tsayawa a zuci! wata irin soyayya da bata da misali! a ranar Hidaya ta tabbatar da maganar Khaleel da ya ce ba shi take So ba,Hamza take so,shi dai tana masa k’auna da tausayawa ne,amma so na soyayya kam Hidaya Hamza ta tattarawa,to yau dai ga Hidaya da Hamza sun samu cikar burinsu,amma duk da hakan basu tab’a manta Khaleel ba,babu ranar da zata fito ta wuce basu yi zancensa ba,Khaleel na shan addu’a wajen wad’annan bayin Allah,a haka suke ta rainon Hamza har ya girma sosai ya kai wasu shekaru,Hidaya ta bayar da kwangilar gina makarantu da asibitoci da k’ungiya ta taimakon marayu duk k’ark’ashin sunan Khaleel,domin ya zame masa sadak’atul jariya zuwa makwancin sa.Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali da nagartacciyar soyayyah.

 

**************

Ni HASSANA D’AN LARABAWA na ajiye alk’alami na tare da ajiyar zuciya da sakkowar hawaye a idanuwa na,bayan na kammala rubuta tarihin rayuwar HIDAYA,labarin da ya shiga zuciyar mutane suka so shi sosai,domin akwai Darasin rayuwa da abubuwa da dama da mutane za su d’auka.

Bayan kammala rubutun littafin GARKUWA BIYU da wasu shekaru Hidaya ta samu cikin Hamza,da lokacin haihuwa yayi ta haifi y’an biyu mace da Namiji,macen ta ci sunan Umma namijin kuma sunan Marigayi Khaleel,Shekaru goma cif da mutuwar Khaleel a lokacin ne Daddy yayi free ya fito daga prison,gabad’aya ya sauya tsufa ya sakko masa,duk kammaninsa na baya sun sauya kuma baya gani sosai sakamakon yawan kuka da yake akan tunawa da D’an sa Khaleel,watansa d’aya da fitowa shi ma ya rasu sakamakon ciwon da yayi ta fama,wannan mutuwa ma ta hargitsa su,sunyi kuka har sun godewa Allah,amma suna wa Daddy zaton rahamar Ubangiji,tunda ya tuba ya bi hanyar dai dai.

Rayuwa ta cigaba da mik’awa Hidaya da HAMZA GARKUWA NA FARKO, tare da y’ay’an su,a gefe ga su Umma da Mummy da su Aunty Sajida da Aunty Kubra.

 

*K’ARSHE….!*

WANNAN SHINE K’ARSHEN LITTAFIN GARKUWA BIYU WANDA NI HASSANA D’AN LARABAWA NA RUBUTA,INA ROK’ON RABBANA YA BANI LADAN ABINDA NA RUBUTA DAI DAI,SANNAN YA GAFARTAMIN KURA KURAN DA KE CIKI,ALLAH KASA WANNAN LITTAFI YA AMFANI DUK WANDA YA KARANTA SHI,GA DUK WANDA YA KARANTA YA AMFANA DA SHI INA ROK’ON ADDU’A GAREKU YAN UWA AKAN WATA BUK’ATA TAWA,KUYI MIN ADDU’A ALLAH YA BIYA MIN ITA,NAGODE MASOYANA TABBAS DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA DOMIN IDAN BABU KU TO BABU HASSANA D’AN LARABAWA,GA DUK ME NEMAN K’ARIN BAYANI KO WATA SHAWARA AKAN RUBUTUNA K’OFA A BUD”‘E TAKE ZAI IYA NEMA NA AKAN LAMBATA KAMAR HAKA 08080049548,SAI KUMA MUN SAKE HAD’UWA DA KU CIKIN LITTAFIN (BAHAGON LAYI SABON SALO) KO KUMA SABON LITTAFINA DA ZAN FARA MAI SUNA……. IDAN RABBANA YA BANI IKO DA DAMA AKAN RUBUTAWA BAYAN NA HUTA,SHIMA LITTAFIN NA SA SALON DABAN YAKE,LABARIN GASKE NE DA YA FARU MAI TSAYAWA A ZUCIYA DA WATA IRIN RAYUWA,KU DAI KU CIGABA DA BINA TARE DA JIMIRIN KARANTA RUBUTU NA,INA GODIYA GAREKU MASOYA,TABBAS NA GA K’AUNA A GARKUWA BIYU 👌😅💃🏻🥰

 

 

 

Comments
Share
Vote
pls

 

 

 

 

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]