BABU RUWAN SO

Advertisements

_____

BABU RUWAN SO

*EDITEN BY*
*Real shaxeee?*

*WRITEN BY*
*preety xayeesherth*

*new writer*

*BISMILLAHIR,RAHMA NIR,RAHIM*

Advertisements

_____

*PAGE 1*

———————————-

Fayal ce xaune akan kujera futo war su kenan daga lectures ita da kawarta Amnah chating take yi ciki ‘kware wa Amnah ta kalle ta tace. ‘’ Fayal wai me zakicine mukazo nan nikam kitashi mutafi gida mana.‘’
magana take mata amman kaman ba da ita take ba tawani hada rai tare da bada hankalinta ga waya Da take hannun ta Amnah tasan halin kawarta ta sai tayi shiru bata kara cewa komai ba.

Wani saurayi ne yadau wanka yaci fararen kaya shiba mummana ba kuma bara ace mishi kyakkyawa ba.

Da sallamarsa yataho garesu. Amnah ce tace. ‘’ walaikumussalam.‘’ kujera ya samu ya zauna Alokacinneh Amnah ta tashi tabar gurin domin tasan halin kawarta da disga mutaneh bataso ta tsaya agabanta ta hulakanta wannan mutumin ba.

Saurayi yace. ‘’ To nidai sunana auwal Ana kiranah da Arfan kuma ni dan garin katsina ne babana ne sarkin katsina nine d’ansa nafari.‘’Duk maganar nan dayake bata dago ta kallesa ba balle tasan waye.

Yacigaba da cewa. ‘’Dan Allah ko dan iya sanin sunanki.‘’Bata dai kulasha ba sannan shikuma be gaji ba yace. ‘’ sonki nake da aure so na gaskiya.‘’ ‘Dauko eye pices dinta yi tasa akunneh Sannan ta tashi tabar gurin wanda har ta tashi ko kallon inda Auwal yake batayi ba.

Tabar shi zauneh awajen abun da tayi masa ya matukar basha mamaki irin hali da miskilanci na yarnan Ko kalloma be shita tayi mishi ba da tunani iri iri yatashi yabar wajen motarsa ya je ya hau ya bar gun aguje.

Fayal tana tashi tanufi inda sukayi paking din motarsu domin tasa Amnah na ciki
Tana zuwa ta hau Amnah da fad’a tace. ‘’ amman dai kinsa bana son irin wannan abunko kawai kinbarni dawani kato yazo yanatamin zuba kamar parrot?
Amnah tace. ‘’Nasan hula ‘kantashi zakiyi shiyasa na bar gun, har yanzu kin ki chanjaa halinki,wallayi Fayal ina kujemiki ranar da zaki fara son wanda bai ma da lokacin ki, ki tuna fa kamar yadda kikema wasu haka za,a miki,Fayal tace. ‘’ Ke dalla cen meye ma wai so hmm wallahi ni banga wani abu asoyayya ba inbanda bata lokaci dan haka ni dakika gannin nan ban da lokacin da har zan tsaya batawa akan wani banxa .‘’

Amnah takara ka da baki tace. ‘’ A bi dai ahankali domin wataran ke zaki zubda hawaye kamar yadda wasu suka zubar akanki.‘’

Fayal tace. ‘’ hmm suma wallahi suna daurawa kansu wahala ne bani na nace suxo susoni ba ai ko?
Dan haka kowa yayi takansa banzaYe wahallalu dasu,Nikam mikwomin key mutafi dan wallahi har kinsa nagaji domin nayi magana dayawa yau.‘’

 

*zamu gani shin tusa zata hura huta kuwa wane rayuwa fayal zata tsinci kanta*

PAGE 2

————————-

Fayal driving take kaman kaman bazatayi ba.
amnah tace. “Haba fayal bakiga lokaci yanata kure manah bane?
Haba Dan Allah kiyi sauri mana kinsan halin mumy fa
Duk maganar nan da Amnah take Fayar ko sauraranta batayi ba.
Amnah batagaji ba takara ka da baki tace. “magana fa nake miki inkuma baraki iya yin sauri bane ki tsaya ni nasauka na hau adedeta kawae.
Sannan Fayal tace. “oh kekam baki da hakuri kinsan dae banason yawan magana ko? hmm Kayi hakuri dai ai munkusan isa ko.?

Duk irin miskilanci da kyaliya irinta Fayal tana ragawa Amnah domin ita kadai ce tasan halinta kuma ta karance ta

Amnah tace.”shikenan amman wlh kome mah mumy tace ke ce da laifi ba ni ba.

Ahaka su fayal da Amnah sukA isa gida batare da k’ara yima wani maganah ba.

Da isarsu mai gadi yaxo yabude musu get sannan fayal tayi paking.
suka shiga cikin gida da sallamar su

Momyce zaune tana kallon Tv.

Tace. “wa,alaikumul salam.

Fayal dakinta tanufa batare da ta tsaya sun gaisa da mumy ba.
Ita kuwa Amnah taje tageshe da mumy kafin ta nufi d’akinsu.

Mumy tasan halin yarta ta shiyasa ko damuwa batayi ba da tun tana damuwa yanxu kuwa abin yaza me mata jiki sai dai kullum tana taya yartata da addu,a

PAGE 3

————————————–

Daga shigar Fayal daki har tanufi toilet ta dauro Alwalah sannan tayi sallah tana idarwa bata nufi ko ina ba sae gado..

Ita kuwa Amnah tana idar da Sallah ta nufi shashin Momy domin taci abinci sannan ta tayata aikin gida…..

Dazuwanta tace.”momy ina food dina?
Momy da dan murmushinta tace.”gashi cen a kichin
Amnah tace.”ok momy
Taje tadauko abincinta ta ci sannan suka shiga kichin ita da momy dan d’aura abincin dare.

Sunayi suna yar firarsu,,
Momy tace.”Amnah yau kuma fayal tayi wani aikine Askul?.
Amnah tace.”hmm momy wallahi bawani aiki datayi illa abinda tasaba kuma shine wai nasata tayi magana dayawa….

Momy Tace.”hmm to dai Allah ya shiryata domin narasa gane hali irin na fayal nidai da abbanta ba haka muke ba

Amnah tace.”Toh Ameeen dai momy ni abinda ma nafi jiye mata tsoro kar daga karshe tafAda tarkon wani..

Da wannan hirar suka kammala girkinsu

***********
wani saurayi na hango zaune afalo yanata murmushi nikai na dana ga irin kyansa sai da nace masha.. Allah hajiya ce tafito tana fadin.”a Amsard Yaushe ka iso ko maganah babu?
Sannan saurayin nan yad’ago” oh my hajiya yanzu na iso fa ina hutawane kinsan da jirgi yasauka a airport nina driving kai na xuwa gida shiyasa nagaji….

Hajiya tace.”owk to welcome my son yanzu tashi kaje kai wanka sai muci abinci ko?

Amsard yace.” ok hajiya nah
yanaji gidan shiru neh?
Inasu salaha da samir

Hajiya tace.”suna makaranta

Amsard yace.”oh hakane fa namanta ne yana maganar yana tafiya shashinsa.

Dashigar Amsard yashiga toilet yayi wanka sannan yayi sallar la’asar da hike yayi azahar tun amota bayan ya idar da sallar yasaka kananun kayan sa pink din riga tare da farin wandon jeans …..yafeshE jikin sa da turare sannan yanufo shashin hajiya..

Dashigarsa yatarar duk sun dawo daga skul…

Yashiga da “sallamarsa
Su sahala suka amsa tareda rungume yayan nasu

Amsard.”yace a su sahala an girma anbar fitina kenan
Sahala.Tayi murmushi

hajiya tace.”to kuxo muci abincin tunda dai duk kun dawo..

Suka nufi daining table tareda fara cin abinci

Sahala sai surutu takewa yayan nata shiko ba mai son magana bane sai dai kawai yamata murmushi

Sahala tace.”uhummm hajiya kinga yaya amsard yaki kulani ko?

Hajiya tayi murmushi tace.”kema dai kinsan halin yayannan naku shi magana ma wahala take masa keko bakya gajiya da zuba kamar parrot….

Sahala tace.”hhhhh lallai matar yaya zatasha wahala dashi wlh tab
Nidai bazan yarda da hakan ba…

Shiko Amsarda,,murmushinsa yake tare da cin abinci

Ahaka suka kammala cin abinci kowa yayi dakinsa

PAGE 4

——————————

WACECE FAYAL?

Sannan wanene Amsard???…

Fayal y’ace Wajen Alhaji Mohammed Mai zinare
Alhaji Mohammed dan garin jigawa neh sannan shi babban dan kasuwane.Abinda yasa akece Masa mai zinare yana safarar sark’wokin zinare neh daga kasashen waje.
Matarsa daya wato hajiya Amina Mata mai kirki da son yan uwanta tare da karramah mutane
Yarsu daya aduniya wato Nusaiba Mohammed wacce ake kira da fayal
fayal yarinyace kyakkyawa fara tas kamar ataba ta jini yafito kana ganinta kaga jinin fulani domin tana da wadatace ciyar suma
Sannan fayal tana da miskilanci wanda baran iya misalta muku ba ga kyaliya da rashin son magana sannan tana da wulakanta duk wani namiji da yanufe ta da kalmar so domin ta tsani wannan kalmar…

Acewarta so wahala ne dan haka batada lokacin yi…

Adalilin hali irin na fayal ne momy tadauko yar kanwarta domin taga sun dan shaku da fayal ita kadai

take sakewa fuska…

Ayanxu fayal Tacika shekarah Ashirin tana universty ajigawa karantar likitar mata take…

Wannan kadan kenan daga tarihin fayal…

WANENE AMSARD?

Amsard d’ane ga Alhaji Abubakar ,,,,,,,Alhaji Abubakar minister ne na mai ..

Suna xaune Agarin katsina..matarsa daya wato Hajiya maryam tana da mutuncinta tare da son mutane kuma yar kasuwace Tana fita kasashen waje domin siyo kaya….

yaran Alhaji Abubakar 3 Amsarda ne dansa nafari……Amsarda ba fari bane sannan kuma ba baki bane shi wankan tarwa ne Amman duk da hakan Baya hana kyahu irin na amsard fitowa asalin sunansa Abdulazeez Abubakar Ana kiransa da Amsard…

Amsard bai cika son magana ba duk da yammata dayawa nacewa suna son sa Amman hakan bayasa sa wulakantasu…

Insuka fada mai sai dai kawai yayi murmushi yace ya gode tahanyar da yake rufe ma yan mata baki kenan duk da sun san hakan zai fada Amman hakan baya hanasu cewa suna sonsa….

shiko yamakansa alkawarin bazai auri wace tace tana son sa ba sai yasamu wadda tamai….. tunda hajiyA maryam ta haifi Amsarda bata kara haihuwa ba har Amsarda yakai shekara 20…

Sun cire rai da tunani samun wasu yaran Amman duk da haka basudai nah Addu,a ba ahaka har Allah yabawa hajiya ciki ta haifi yan biyu mace da namiji sahala da sameer….

Amsarda da iyayensa sunyi mutukar farinciki

Yanxu Amsard yagama karatunsa A Ummaru Musa Yar Adu’a dake katsina sannan yakoma malesia domin masters dinsa….

ayanzu yazama cikakken medical Doctor kuma yana da asibitinsa a malesia inda yake aiki shin acen

Kadan daga cikin tarihin Amsard kenan

PAGE 5

—————————–

CIGABAN LABARIN

Abangaren Fayal tunda ta kwanta bata farka ba sai dataji ana kiran sallah magriba.

Tana tashi tanufi toilet ta dauro alwala sannan tayi sallah.

hakama su momy sun riga da sun idar da sallar su.

Har sunfara shirya abinci akan daning table.

Suna cikin shiryawa sai ga fayal ta fito tana yatsina fuska. daman wannan d’abi’ar tace.

Momy da Amnah suna ganin fayal suka fara mata murmushi.

Tare da fadin.”fayal din momy kin tashi ne?.

Alokacin fayal tadan k’akulo murmushin dole tace.” good evening mom and amnah?.

Su momy sukayi murnushi tareda fadin.”
evening fayal.

Alokacin dady yayi sallama.

Su momy suka Amsa.

Fayal tayi gudu taje gun dadynta.
Tareda fadin.”welcome dady.

Dady yace.”how are u daughter?.

Fayal.”am normal dady

Dady yace.”dax gud

Sannan momy.”tace to ai sai kuxo muci abinci ko?

Dady yayi murmushi tareda fadin.”oya daughter tashi muje.

da isar su daning Amnah tafara geshe da dady.

Ya amsa mata cikin sakin fuska.

momy tayi serving din su sukaci abinci cikin farinciki da annashuwa.

fayal Ce tafara tashi tareda fadin.”gudnight momy daddy amnah.

Momy tace.”haba dai wai harkin k’woshi?.

Kafin fayal taba momy amsa har daddy yafara magana.

“haba daughter wai ke har yanzu bazaki fara cin abinci yadda kowa yake ci bane?.

Fayal ta yatsine fuska sannan tace.”uhumm momy dadu fa naci.

Nikam byeeee tanufi dakinsu.

Bayan tafiyar fayal daki.
Dady yace.”Ni Wallahi har yanzu narasa gane irin hali na fayal.

Momy tace.”hmmm Sai dai kawai mucigaba da tayata da Addu’a domin abinnan nata bana wasa bane.

dady yace.”to dai Allah yakyauta.

Alokacin Amnah tabudi baki tace Ameeeen ni wallahi ma dady abin da yafi bani tsoro shine yadda take wulakanta maza.

INajiye mata kar taje ta wulakanta wanda batasan zuciyarsa ba.

Kokuma wataranah takamu da son wani wanda bazaiso ta ba.

dawannan hirar suka kammala cin abinci.

SAnnan Amnah tamusu sallama kowa yatafi daki.

WASHE GARI

Bayan su Fayal sunyi sallah Asuba basukoma barci bA.

Suka shiga kichin domin daura breakfast tunda yau da safe suke da lectures.
Shiyasa koma barcinma basu koma ba

*********

Abangaran Amsard mah yagama Shirinsa domin yau yanaso yaje ziyarah jigawa wajen abokinsa dake karantarwa acen universtyn.

Kamar karfe 7 Amsarda yafito yana fitowa yatarar da su hajiya da Alhaji na break fast sukuma su sahala da sameer har driver yatafi kai su skul.

Alhaji yace.”oh Amsard yaushe agari?

Amsard yasosa k’yaya tare da fadin”ina kwana Alhaji?

Ina kwama hajiya?

duka suka Amsa cikin sakin fuska.

Sannan hajiya tace.” ai tun jiya yadawo da rana. kai kuma bakanan shiyasa nabari inma suprise .

Alhaji yayi murmushi tare da fadin aiko kin kyauta dole inmiki kyauta ganin my son.

Sunfara cin abinci kenan.
Amsard yace.”Alhaji jigawa fa zan tafi ana nemana a universtyn da usman abokina yake koyarwa.

Hajiya taci”oh kai kam dai baka gajiya kuma baka zama waje daya.

Alhaji yace gashima ko yar hira bamuyi ba.

Sai alokacin Amsard yayi murmushi tare da fadin.”ai inaga bazan kai kwana 3 bama zan dawo indai nagamah.

Bayan sungama yin breakfast yamusu sallama suka mai addu’a.

yadau hanyar jigawa.

*******
su fayal sun shirya da huri domin suna tunanin yau sunada practical shiyasa suketa sauri.

Da fitowarsu Amnah tace nikam fayal bani keyn motar nan dan nasan inna biye miki sai kibatamana lokaci.

Fayal ta mika mata key din batere da tayi magana ba domin ita kanta Saury take taga sun isa skul din.

 

PAGE 6

———————————

GODIYA AGAREKU LODI LODI DOMIN KUKE DAURANI AKAN HANYA hassan atk.Real shaxee.princes dija inayinku irin totallyn nan

Amnah tuki take cikin sauri dan ita aganinta sunyi letti mah.

Amsard kuwa shima yana shiga mota yafara sauri domin yanaso ya isa kafin 10pm
Tuki yake cikin sauri.

Dadai karfe 8.00pm su fayal suka isa domin suna da nisha da makarantar .

Amnah tace.”kingama fa wai dan nayi sauri kenan nasan dakece da sai munkai 10 kafin mu iso.

Fayal ta yatsine fuska tare da jan dogon numfashi irin damwarkin nan.

Atare suka fito domin nufar inda sukaga students na zaune.

Da isarsu wajen amnah ce ta nufi wajen wata class mate dinsu tare da fadin”wai daman ba afara bane?
Tace”hmm eh wlh wai bai iso ba ashe yanada nisa.

Amnah tace”kai gaskiya amman su azabtar damu sunce mu fito da huri Amman gashi shi bai zo ba.

Takoma wajen da fayal ta tsaya domin kuwa fayal bata kula kowa askul din inkaga tayi magana da amnah take toh .

Shiyasa tun wasu nashishshige mata har sun gaji sun rage shiga harkarta domin kuwa yan kwana su take.

Da ta iso guri zakaji Anfara cewa ga yar girman kai nan tazo kowa yana fadan albarkacin bakinsa.

Wasu suce tana birgesu .

Wasu kuwa haushi take basu .

Amnah nazuwa tace.”hm wai ashema bai iso ba.

Fayal tace”what!

Duk sammakon nan dakikasa mukayi?

Alallai ma wannan mutum min ya isa.
Ai naga ba dole bane practical dinko?

To wallahi baranyi ba nafasa komawa gida zanyi.

Nina tsani wulakanci arayuwata yawani sa an ajiye mutane kaman kaji..

gashi har rana tafara fitowa mtsw.

Amnah tace.”haba fayal kinama mutane uxuri mana .

Kinsan mai yatsayar dashi kuwa?

Fayal tace”mtsw nikinga tafiyata wallahi har kai na yafara ciwo.Innaje zan turo driver yakawo miki motar.

Amnah tace.”hmmm shikenan ai .

Fayal ta.”figa mota aiko duk tabade mutanan gurin da kurah.

Mutane suka fara cewa.”tir dai da hali irin naki

Ita kuwa batama san mai suke ba tayi tafiyarta.

ita kuwa Amnah ta koma wajen wata yar ajinsu Khadija suka zauna.

 

Fitar fayal keda wuya Amsard yashigo makarantar.

Da shigowarsa usman yazo yashiga dashi ciki.

Khadija kawar amnah tace”kai Amnah gaskiya yayarnan taki batada hakuri gashi daga fitar ta har ya iso.

Amnah tace.”hmm wlh haka take ni bansan wani irin hali fayal kedAShi ba.

Suna cikin hira akazo kiran mutane domin shiga bayan kowA yashiga.

Amsard yaga wajen mutum daya babu yace”wa usman gurin waye wannan?

Sannan usman yayi bincike akaga ashe wajen fayal ne.

usman yazo Yafadawa Amsard fayal ce.
dakuma dalilin tafiyarta.

Ran amsard yayi mutukar baci domin yatsini mace mai girman kai.

Acewarsa matan mesukedashi da hardasuyi girman kai.

 

Yayi murmushi yacewa usman kabarni da ita i will teach her a lesson

DAMUGANI KOWANI MATAKI AMSARD ZAI DAUKA AKAN FAYAL??

 

PAGE 7

————————————

INAKIKE MY SOUL BAN MANTA DAKE BA KUMA BARAN TABA MANTAWA DAKE TARE DA AMSARD DINA NA GASKIYA INA MUTAKAR ALFAHARY DAKU NUSAIBA MUHD AUWAL AND DAN MATASHI NAH

GODIYA GAREKU MASOYA WANNAN LITTAFI INAJIN DADIN BADA HADIN KANKU GARENI ANA MATUKAR TARE.

Da isar fayal gida ta tararda momy adaki tana duba wasu takardu .

Tashiga da sallamarta.Domin ita kanta tasan bata da gaskiya yau.

Momy tana raga mata aduk abinda take amman banda ta fannin karatu.

Dan haka take tsoro.

Momy tadago tare da fadin”wa alaiku mul salam

Fayal tayi sauri domin nufa dakinta momy ta dakatar da ita.

“ina zaki kuma?
Faya tace”fa…….

Momy tace”tsaya banason wannan maganar banzar taki mekika dawo yi?

Fayal tace”momy shifa lecturern da akace daizo yamana yaki zuwa.

Momy ta nufasa hadi da cewa”hmmm naga yanzu ma 10:am tayi.

Fayal nifa nagaji da rashin hakurinki.

Wai ke ko karatun ma barakiyi hakuri ba dan kisamu?

duk maganar nan da momy take fayal takasa dago ido domin tasan bata da gaskiya.

Momy tace”ki huce kibarmin gida kikoma inba haka ba kuma kema kinsan sauran wallahi.

Atake fayal ta juya domin komawa skul.Amman ba dan ranta yaso ba .

Dan haka ma ahankali take driving kamar wata mara laka ajiki.

 

Abangaren su Amsard kuwa yace”sufara

Yayinda aka fara practical gadan gadan .

Kowa adaliban yanajin dadin yanayin practical din domin yana musu yadda zasu fahimta.

Gashi duk yan matan shige masa jiki suke.

PAGE 8

————————————–

Sunata shigewa Amsard jiki da tambayoyi shiko sai dai yayi murmushi sannan yabasu Amsa.

Domin Amsard yana da hakuri sose Amman in aka kuresa bara ataba jin dadi bah.

Fayal ta iso skul kamar yadda tasaba fuskar nan ayatsine amman nayau kam daban ne domin yatsinar yau tafi ta kullum.

Duk da haka bayasa kyahunta yaragu sai dai karuwa.

Tafiya take kamar bazata taka kasa ba.

Tana isa tashiga cikin lap din dazuwanta bawanda yakulata.

Sai masu gulma,Wasu nacewa yau anrage girman kan kenan.

Wasu ko ce suke oh tir dai anyi ba ayi ba miye amfanin dawowar.

Kowa na fadan albarkacin bakinsa.

Ita kuwa Amnah cewa take. “Fayal ga wajen kinan.

tukun tajuyo tanemi waje tazaune daidai da dawowar Amsard domin yaje yadauko abune Amotarsa.

Yaga fayal shikansa saida yace. “Masha Allah azuciyarsa.

Amman afili yace. “ke lafiya zaki shigo mana waje bakiga muna aiki bane?

Fayal batamasan yanayi ba domin ko kallonsa batayi ba bare har tasaurari maganarsa.

Amsard abin yamatukar bata mai rai dan haka yayi magana da tsawa”keee get out of my class!

Fayal tajuyo arazane domin ita arayuwarta bawani namiji daya taba daga mata murya bare tsawa.

Shiyasa tajuyo arazane domin inba dan yamata tsawa ba da saidai inyagaji da maganarsa yatafi yabarta.

Fayal.”tace what!!!!!!

Amsard yace.”i said get out of my class .

Aji yayi shiru domin yau fayal tagamu da gamota wasu sai dariya suke aboye.

Dan haka fayal tamike ta tashi domin baran ajin.

Jiki asanyaye domin ita abinma mamaki yabata.

sukuwa sauran yan ajin suji mamaki dasukaga fayal tayi shiru bata kara magana ba ta tashi ta tafi.
Duk ji da kan nata yau ina yake?‘’

 

Fayal tana isa mota tafara kuka ba kakkautawa domin ita gani take ayau anmata tozartar da bata taba tsammani ba.

Amsard yaji mamaki datakasa bada hakuri bare yaji tausayinta tayi .

Yacewa usman. “Lallai kuna fama da yan girman kai amakarantar nan wlh indai zanyi sati amakarantar nan sai na gyarama kowa zamansa.

Usman yace. “Hmm ai wlh indai fayal ce tafi hakama ninaji mamakima da bata fadama wata bakar magana ba.

Amsard yace”hmm ai wallahi kaima kasan banason raini da ta fadamin wata bakar magana .Da daga yau barata kara wulakanta wani namiji ba.

 

usman.Yace”hmm kai dai bari kawai .

Fayal kuwa tana nan amota takasa tukin ma balle taje gida sai kuka take tare da mamakin abinda Amsard yamata

 

PAGE 9,10

——————————–

Amsard yaciga ba dayiwa student bayani.

Amman acikin zuciyarsa tunanin fayal yake.

Oh afili kuma yace”oh wai nikam ma ina ruwana da ita.

Miye damuwata ai ita tawa kanta.

Mtws.

Usman yace”yadai amsard naji kaman kana magana.

Amsard da baima san maganar zuci ta fito fili ba.

Yayi murmushi sannan yace” aa no bakomai.

Ahaka sukagama practical dinnan Amman Amsard yarasa me yasa yake tunanin fayal.

Duk yadda yaso yabari amman yakasa.

Awata zuciyar kuwa cewa yake inaga dai tausayinta nake.

Yanata sake sake azuciya.

su amnah sun fito kenan ta hango motarsu.

Dan haka ta nufa wajen domin ita atunaninta driver ne yazo daukanta.

Tana zuwa taga abin mamaki abin da bata zato.

Fayal ce zaune tazuba uban tagumi tana kuka.

Arikice Amnah tashiga tare da fadin”yaya dai fayal lafiyan ki kuwa kike kuka haka?.

Fayal takasa magana saima wani kukan dayagara tawowa.

Bashiri amnah tafara driving .

Gudu take akan titi domin jikin fayal yadau d’umin zazzabi tafara.

Fayal rawar sanyi take matuka.

Domin yau tayi kukan da bata tabayi ba tunda tazo duniya .

Niko nace wace take ganin magana aikin wahala ne inaga kuka?
Hmm.

Da isarsu gida Amnah tashiga domin sanar da momy.

Momy tafito arikice domin shiga da fayal cikin gida.

Ita kuma Amnah takira family doctorn su domin yazo yaduba jikin fayal.

Kafin likita yazo har momy tafara d’uma ma fayal jiki da ruwan zafi.

Har zazzabin yafara sauka.

Sai ga doctor Abdulrahman ya iso.

Isowarsa keda wuya yashiga dubata .
Sannan yasa abata koda tea ne tasha yamata allurar barci.

yana mata kuwa tasamu yin barci.
Bayan doctor yatafi ne momy tafara”Tambayar Amnah wai meyafaru ne?

Batare da bata lokaci ba Amnah tama momy bayanin yadda komai yakasance.

Momy taji dadin abin nan ba duk da tasan laifin yartace Amman bataji dadin hakan da amsard yamata ba.

Allah sarki uwa da y’a kenan.

Momy tace”hmm to dai Allah yashiryamin ke fayal bansan ya zanyi dake ba sai dai mucigaba da addu’a .

Amnah tace”Ameen momy.

bara nayi sallah sai indaura mana abinci.

Momy tace”ok nima bara nayi sai mushiga kicin din tare.

Suka tashi domin sallah bayan sun idar suka nufa kichin domin daura abinci.

Fayal barci take Amman ganin abin da yafaru take acikin idonta.

Afirgice tafarka tare da fadin”wai ni yau wani zai wulakanta!!!!!

 

Wallahi wallahi sai sai na rama abin da yamin.

Yanzu zan fara asalin wulakanci tunda da ance INayi nikumA banga hakaN ba.

DAn hakA yanzu da afara.

Hmmm niko nace kome da afara?
Sai kubiyo ni Aysherth(preety xayeesherth)
Domin sannan me za afara cewAr fayal.

Bayan su momy sun kammala girkinne suka fito .

Fitowarsu keda wuya sukaga fayal zaune afalo.

Da alamu dai tunani take.

ko tunin me take? ohoo dai.

Amnah ce tafara magana”fayal kin tashine?
Ya jikin?

Sannan momy tace” sannu fayal.Ya jikin dai?.

duk maganar nan bata dago ba sai daga baya ta yatsina fuska tare da fadin dasauki.

Tun daga nan bata kara cewa komai ba.

Suko su momy da hike sunsan haka halin fayal yake sai abin bai damesu ba.

sabida hakan yabi musu jiki.

Tafiya sukayi suka fara jera abinci adainin.

Bayan su kammala ne sukace da fayal tazo taci abinci.

taje tazauna Amman tunani take.
Har yanzu abin yaki bace mata a ido .

Niko nace ai ke kikajawa kanki.

anzuba mata abinci amman takasaci.

Momy ta lura da hakan Amman tashareta.
SAi Amnah ce ta ka da baki tace.”fayal bazaki ci abincin bane?

FAyal”ta yatsine fuska.
Sannan tace na k’woshine fah.

Sai alokacin momy ta bude baki tace”wallahi indai yau bakici abincinan ba sai dadynku yaji abinda kika aikata askul .

Kinsan dai inasane dakomai ko?

Fayal ta girgiza kai tare da fadin “aa danci.

Ahaka faya ta chacchakula abincinan tabari wai adole taci.

Domin ita dama asalinta cin abinci wahala yake mata.

Suna gama ci FAyal taje tayi sallar la’asar sannan takoma gado.

****
Abangaran amsard kuwa sun koma gidan usman dake jigawa .

SUNa isa yatarar da matar usman phertymerh sai fara”ah take.

Dasauri tazo ta karba jakar mijinta tanamai sunnu da zuwa.

Amsard kuwa murmushi yake.Domin usman da pherty na birgeshi.

Pherty tace”ah kacemin yau munada babban bakwo agidannan .

Amsard yace”oh sai yanzu kikaganni ?
Bayan kingama karban mijinki?

Pherty tayi murmushi sannan tace”hmm ai kasan halin naku ne sai ahankali inmuka sake sai amana kari.

Amsard da usman suka sheke da dariya .

sannan Amsard yace”ashe dai anajin tsoronmu.

pherty tace”ai dole munma wallahi harda gudU.

Shidai usman ba abinda yake musu banda dariya.

Pherty tace”gwandama ogana fa ashe tunda kai har yanzu ko budurwar ma babu.

Antsaya anamin bakin cikin samun kawa.

*PAGE* 11,12

Pherty tace”hmm bara nakawo muku abinci
Baran ma kai gauro”.

Amsard yayi murmushi tare da fadin”ai sai nabaku mamaki domin inna tashi hudu zan jera”.

Usman yace”,kaga nima nasamu damar kara daya.Daga karshe yakarasa da dariya”.

Pherty tagallawa usman harara tare da fadin”kanku dai akeji tayi tafiyarta”.

Usman yace”kaga har nakashe mata baki”.

Dukansu suka sheke da dariyar mugunta.

Bayan wasu yan mintuna sai ga pherty tadawo dauke da abinci.

Tafara zuba musu tuwon shinkafa ne sai drinks din abarbA.

Bayan ta zuba ne tace”oya su malam gauro azo aci abinci kai kuma honeyna ga namu nan”.

amsard yace”aiko indai hakane kuci kayanku tunda ni wareni za’ayi kuma in baki kama kafa dani ba sai nasa ankaro miki biyu.”

pherty tayi dariya sannan tace haba yayana nasan barakamin haka ba.
Kumama ni wasa nake ga abincin ku nan kuci”.

Usman da amsard suka saka dariya tare da cewa” dole amana biyayya”.

pherty dai dariya take domin tasaba da zolayar sa.

Sai da sukaci suka k’woshi sannan Amsard yace”bara yatafi hotel domin aceb zai kwana”.

Usman yace”kai haba abokina mu kwana anan mana ga dakuna anan “.

Pherty mah tace”haba ya amsard ka tsaya anan mana”.

Amsard yace”kwaji dashi dai domin nasan azuciyarku kunata sauri natafi neh”.

Pherty da usman suka fashe da dariya.

Sannan usman yace” baka dai son kwana ne kawai”.

AmSard yaCe”hmm wallahi inada wani aikine kuma nafison nasami nutsuwa nikadai”.

Pherty tace”kodai za agun yayata kuma kawatace?.
amsard yace kedai sai ahankali nalura damuwar ki kawace kawai kuma kinkusa samu na huta”.

Pherty tayi dariya sannan tace “aiko da ka huta sosemah”.

usman yace”gobe dai ka fito da huri to damin mukarasa da sauri”.

Amsard yace”insha Allah kuwa .

Usman ya”Allah yasa”.
Tare da fadin Ameen dukansu”.

Sannan sukayi sallama cokin farinciki da begen juna.

Da fitar Amsard yanufa hotel domin sai sukayi sallah tun askul.

**************

Aban karaen fayal kuwa har yanzu tana nan da kudurinta azuciya.
Sai kitse kitse take ta hanyar da zata rama abin da Amsard yamata.

misalin karfe bakwai na dare dadyn fayal ya iso gida .

Dashigowarsa yaga momy da Amnah neh kadai afalo .

Bayan yayi sallama sun amsa suka masa sannu da dawowa.

Sannan yaduba Amnah yace “ina kawartaki neh ko yauma yan abun sun motsa ne?

Amnah dai tayi murmushi sannan tace” tana daki”.

sannan momy ta kwashe duk abinda yafaru tsakanin fayal da lecture ran su .

Kwatakwata dady bai ji dadin abin da yar tasa ta aikata ba.
DAn haka yace”amnah ta kira masa fayal .

Bayan taje kiranta ne suka tawo tare.

Fayal tageshe da dadynta sannnan yafaramata magana”.

fayal gaSkiya yau banji dadin abin da kika aikata ba.
kinsan dai karatu ba abin wasa bane ko?.
Banaso inkarajin wani makamancin hakan yafaru “.

Fayal ta sunkuyar da kanta domin jin fadan dadynta.

sai da yamata fada meshiga jiki sannan ta d’ago tace” masa ta godE tare da alkawarin insha Allah barata karaba”.

Dadynta yaji dadin hakan sannan yasamusu Albarka ita da Amnah .

sannan sukaci abinci tukun kowa yakoma daki domin kwanciya.

*WASHE GARI*

da safe amsard yafara shirin tafiya skul .

Su fayal ma sun shirya.

Atare suka isa skul motar su fayal nagaba ta Amsard kuma abaya .

Fayal takinta take yadda tasaba kamar ba titi tahau ba.

AMsard yanata horn Amman duk da haka fayal ta kara gudun motarsu ba .

Ran Amsard ya matukar baci dan haka yatsaya da tukin domin ganin kosuwaye zasu fito amotar nan.

Tsayuwarsa kedawuya yaga anyi paking .

*WA zai gani?*
*WAni mataki zai dauka?*

*PAGE* 13,14.

———————————————————

Fitowar Fayal kenan daga mota .
Tana yatsina fuskar nan kaman yadda tasaba.

Amsard kawai tsayawa yayi domin abin mamakima yabasa”wato ma abin yarinyar nan har yakai haka!.
Yake fada azuciyarsa.

ita kuwa batamasan dawani abayanta ba tafiyarta take cikin isa da k’asaita.

Amsard yafito shima sannan yanufa wajen usman.

Dazuwansa bayan sun gesa da usman sai yace”usman wai dama haka yarinyar nan take?.
Ita yar wayema wai agarin nan?.”

Usman yanunfasa sannan yace”hmm daga maganar nan take nagane wa kake nufi
Domin nasan inba fayal ba ba wace zata nemi b’atama rai”.

Haka take kuma wallahi karkayi tunanin wai iyayen ta ne suka goyamata baya domin wulakanta mutane.

Aa ba haka suke ba domin su kullum fatan ta gyaru suke domin su kansu basa ganewa halayenta “.

Karkaji mamaki innacemaka bata da samari domin ita aganinta soyayya bakomae bace bace wahala .
Batasan cewA *BABU RUWAN SO* ba ita tadaukesa amatsayin shirme”.

Amsard ya nunnfasa tare da fadin”hmm A lallai wannan tacika miskila duk miskilancin dasu momy sukecewa inadashi insuka wannan yarinyar sai sun sara mata.
Domin komai nata nadaban ne .
Amman insha Allah ni nadau Alkawarin sai na chanja mata hali kai dama rayuwarta ta gaba daya”.

Usman yayi murmushi sannan yace”anya kuwa abokina baka fada ba?”.

Amsard ya sheke da dariya sannan yace “haba kai kam usman me zanyi da ita kawai dai inaso na nuna mata *BABU RUWAN SO* ne.
Sabida takiyaye wulakanta masu sonta”.

Usman yace”aa fa dai kar azo daga baya akamu kuma”.

Amsard yayi murmushi’sannan yace kadai ka tsaya kaga dramar nan .
Domin yanzu za,a fara”.

usman yace”toh shikenan fatan alkairy nakewa abokina”.

Amsard yacewa usman”yagode sannan yakarasa maganar dacewa su tashi su tafi domin fara aikinsu”.

ita Kuwa fayal tine taje tasamu waje tazauna sai alokacin Amnah kecewa”fayal kinsan kuwa dazu wannan lecturern abayanmu kuwa kikaki matsa me”?.

Fayal ta dago sannan taja dogon tsaki tare da cewa”ai gwanda haka indai ko shine yanzu yafara ganin abubuwa kala kala sai randa yabar makarantar nan zai rabu da jarabawata”.

Amnah batasan sanda ta shek’e da dariya ba sannan tace”lallai ynzu kinaso ki taro wanda yafi karfinki, anya ma kin kallesa Da kyau kuwa?.

Fayal tace”toh uwar kalle kalle ni me zan kalla ajinkisa me yake dashi”.

Amnah ta karAshekewa da dariya sannan tace”amman gaskiya zanji dadin wannan dramar taku .
Za,asha kallo awanga makaranta.

Fayal tace”kyaji dashi dai nikam wlh duk akan mutumin nan kwanann sai magana nake mtsww”.

Ita dai Amnah dariyar ta take domin taga tun ynzu yar uwarta ta tafara magana inaga in aka fara dramar?.

Hmmm kallo nagaba kubiyoni danjin yadda zata kaya.

Amsard ya usman sun shiga domin fara practical.

Shigarsu keda wuya kawai Amsard yaga fayal azaune .

Abin yabasa mamaki azuciyarsa yace”toh yar girman kai yau anzo kenan.

Sunfara practical dinsu cikin nutsuwa ita kanta Fayal sai dataji farinciki tanata tunani ashe fa jiya tayi missing sose,wata zuciyar kuma tace sai me? mtsw”.

Suna kammalawa fayalce tafara fita aiko da amsard yaga haka sai yayi sauri yabita.

Tashiga mota tanajiran amnah .

Shiko Amsard yana zuwa yahau motarsa sannan yasha gaban tata.

Fayal tace”owk wato mutumin nan adole shima so yake ya rama abinda name dazu ko?
Alallai naga alamon cewa bai san wacece fayal ba,
Amman yaro kakusan sanin ni wacece yadda inma kaganni barakaso karasawa inda nke ba balle ka kalleni”.

Tana maganar nan Amnah nashiga motar aiko ta figa motar da gudu.

Amsard yana ganin haka shima yafara gudu.

Fayal tayi tayi yadda zatayi ta huce Amsard Amman takasa gashi daman ita ba iya gudu sose tayi amota ba.

Aiko ananne ranta yakara baci batasan sanda ta figi motar da mugun guba.

Aiko karaf sai gashi tayi gware da motar Amsard .

Amnah tun tana magana tana ta”haba fayal kiyi ahankali mana ko kibani nayi driving din.

Duk magiyar nan da Amnah tayiwa fayal Amman bata saurareta ba hasalima batasan me take BA.

Aiko amnah naganin sunyi karo da mota ba abinda take fada sai” innalillahi-wa’inna -illaihir-raji’un”.

Ita kuwa fayal ko numfashima batayi bare motsi.

Shiko Amsard yabuga kansa ajikin madubin mota kansa sai zubar jini yake.

Amnah gaba daya tarasa ta yadda zata fara dominga fayal nan kwance ko motsi babu .

 

*PAGE* 15,16

————————————————————-

Dasauri Amsard yafito amotarsa domin duba motar su fayal.

Yna zuwa yaga Amnah sai kuka take tana salati.

Dasauri yataimaka mata suka fito da fayal .
Sannan yakaita motarsa domin daman shi ba abin da yasami motar tasa sai dai kansa dake zubar da jini.

Tuki yake Amman duk hankalinsa baya jikinsa gabadaya ya rikice kawai tuk’i yake.

Da isarsu asibiti akazo domin awa fayal taimakon gaggawa .

Sannan shima Amsard yaje aka me treatment din kansa.

Ita kuwa Amnah ba abinda yasameta dan haka ta kira momy awaya domin sanar da ita halinda ake ciki.

Aikuwa da fadarta momy tace”gatanan zuwa “.

Bajimawa sai ga momy ta iso adaidai wannan lokacin kuwa fayal ta farfado.

Momy tashiga dakin tasamu fayal da Amnah tace”wai ya akayi haka neh?.

Amnah tabude baki zatayi magana fayal tamata alama datayi shiru.
Aiko Amnah tayi tsit domin tasan halin fayaL.

Fayal tace”uhymm momy wata motace abayan mu tana gudu nikuma kinsan ban iya gudu ba shine fa kawai mukaci karo”.

Momy tace”hmm toh shikenan dai Allah yakyauta abinma yazo da dan sauki”.

Amnah tace”Ameeen”.

Fayal kuwa tayi dogon numfashi domin ta tsira da kyar dan tasan in momy tasan gaskiya bazataji da dadi ba.

Doctor yazo yaduba su sannan yace” ga takardar sallamarsu nan angama komai”.

Momy tace”toh ai ban biya ba “.

Doctor yace”ai wanda yakahosu ne yabiya”.

Momy tace”owk ko zan iya ganinsa?.

Doctor yace”a’a ai ankirasa wai yana sauri shiyasa ma bai tsaya muku sallama ba”.

Momy tace”owk to mungode Allah yabiya”.

Suka kare dacewa”Ameeen”.

momy ko dady bata kira ba suka tattara suka nufa gida domin fayal ta dan warware.

Shiko Amsard yana tafiya ashe managen sa na chan malesia ne yakirasa domin wani aiki na gaggawa wanda dole sai da shi abin zai tafi dai’dai.

Su fayal na tafiya Amota Amman kwatakwata hankalinta baya jikinta gaba daya tunanin irin wulakacin da zatawa Amsard take.

Batama jimamin jikinta sai wani jarabar datake tarawa.

Ita aganinta ma wato ya rainasu ne da har zai biya musu kudin asibiti.

Watomah yadaukesu matsiyatane ko?.

Hmmm duk dai wannan maganar datake ta zuciya ce dan haka babu me bata Amsa.

Amsard sauri sauri yake yakira usman yace masa”su hadu a airport domin ko katsina bazai koma ba malesia kawai zai huce” .

Shiyasa yace”yazo yakarba motar .

Aiko nanda nan sai ga usman yazo.

Usman yace”kaiiii Amman gaskiya banji dadin abunnnan ba nida naketa shirin kallon dramar miskili da miskila”.

Amsard yayi murmushi sannan yace”oh yaro ai kabar dadi tun yau mukafara dramar kuma gashi kayi missinh” .

Usman yace”oh haba dai abokina bani labari mana”.

Amsard yaduba agogon hannunnsa sannan yace kaga yanzu jirginmu zai tashi kabari sai munyi waya koma hadu a whatsApp.

Kuma ma ai ba dadewa zanyi ba karka damu kakusa zama drectorn dramar mu”.

Usaman yashek’e da dariya hade da cewa”lallai kam toh adawo lafiya actor na actress”.

Shima Amsard yayi dariya sannan yace”toh sai na isa kajini ko?.

SUKa gesa tare da yin sallama.

Amsard yahau jirginsu suka tashi.
Yayinda shima usman yahau motar domin komawa gida.

SU fayal sun isa gida adai dai lokacin da daddy yadawo .

Fayalce tafara fitowa tare da Amnah data rike mata hannu.

Daddy abin ya razanasa domin bai san meke faruwa ba kuma gashi yaga yarshi ba dai dai ba.

DAddy yace”fayallllllllll kala….. sai da yaja numfashi sannnan yakara cewa”fayal kalau kuwa?

 

*PAGE* 17,18

———————————————————————-

Daddy yazo yatallafawa fayal domin shiga cikin gida.

Suna shiga ya kwantar da ita akan kujera domin ko bed room basu karasa shiga ba afalo suka tsaya.

Bayan yan wasu daki k’u ne daddy yaja numfashi sannan yacewa momy”wai ya akayi ne? meyafaru?”.

Momy itama sai da taja mufashi sannan ta kwashe duk abinda yafaru ta fadawa daddy.

Daddy yadanyi murmushinsu na manya sannan yace”kice ma abin yatsageta kennan kuma gashi ansamu dan albarkan yaro .
Domin na tabbatar da wasu ne guduwa zasuyi”.

Momy tace”wallah kuwa ninaso ma nagansa domin namasa godiya amman ba dama”.

Daddy yace”ai nima inason ganinsa insha Allah duk randa Allah yayi zan gansa sai name halallaci kamar yadda yamin”.

Ita dai fayal jinsu take Amman zuciyarta cike take da bak’in ciki .

Ita kuwa Amnah suna zuwa tayi kichin domin daurA musu abinci.

???????????

Amsard ya isa malesia lafiya da isarsa bai nufi ko ina ba sai Amsard special hospital .

Yana isa managen sa yazo yamasa bayanin komai.

Ashe wata yarinya aka kawota sunyi hatsari gaba daya namomin kafarta sun fita sai jijiyoyi kawai ake hangowa.

Sannan kuma yar Nigeria ce ankasa aikin ananne aka turasu malesia.

Batare da bata lokaci ba Amsard yaje yayi wanka sannan yayi sallah yana idarwa yaci abinci sannan yasaka kayan aikinsa.

Sukaje domin farawa yarinyar nan aiki.

Batare da bata lokaci ba yafara aikinsa cikin zafin nama da kwarewa.

Aiko aikin nasu da alamon nasara aciki domin kosu yan malesia sai da suka jinjina masa.

*KATSINA*
Gidan su Amsard.

Sahalace tabiyo sameer da gudu tana fadin”uhymmm hajiya momy kice yabani abuna”.

Sameer yayi sauri ya dane ajikin hajiya momy yana fadin”uhymm hajiya momy nawane fa ba nata ba “.

Hajiya momy tayi murmushi tare da fadin”kai sameer fa kaine babba kabawa yar kanwarka Aro mana”.

Sameer yace”uhumm to gashi kuma in bro Amsard yasiyomin kayan wasa bazan baki ba “.

hajiya momy tace”oh kun tunamin mah bara nakirawosa.

Domin yacemin zai koma malesia Yau.

Momy taceWa sahala tadauko mata wayarta domin ta kira Amsard.

Sahala tadauko sameer yace”ai shi zai kira Amsard tindama bros dinsa ne”.

Sameer yakira Amsard har sau ukku bai dauka ba.

SAhala sai dariya take masa.

Momy tace”rabu da ita sameer dina inaga aiki yake kuma ma nasan inyadawo zai kiramu”.

Haka dai hjy momy tata fama da rigimarsu sahala.

Har daddy yadawo sannan tasamu sauki suka koma kansa.

??????
Amnah tagama abinci sannan tayi sallah aka taimakawa fayal ma tayi sannan suka zauna domin cin abincin.

Daddy sai jan fayal yake da magana Amman samm taki .

shiko da hike yasan halinta bai damuba domin yasan koda lafiyarta kalau ba sakewa zatayi ba inaga bata da lafiya.

Dakyar fayal tadan chakali abinci sannan suka tashi sukayi sallah .
Kowa yayi bed room dinsa.

??
Abangaren AMsard kuwa sai yanzu yasami kansa .
Bayan yayi sallahne yaduba wayarsa yana dubawa yaga missed call din hjy momynsa.

AIKO batare da bata lokaciba yakirata .

Sameer ne yafara dauka suka gesa sannan yabawa sahala suka gesa.
BAyan su gama masa shirmensa ne suka bawa momy wayar .

DASuka gesa hjy momy tace”dazu kar dai har kunfara aikine?”.

Amsard yafadawa hjy momy duk abinda yasami yarinyar nan

Hajiya momy ta matukar tausayawa yarinyar nan.

 

SUKayi sallama sannan kowa ya kwanta.

*PAGE* 19-20

——————————————————————

*WASHE GARI*

su fayal suntashi da huri domin tafiya scul
Domin daman yau ne zasu gama practical dinsu.

Bayan sun kammala komai sunyi wanka sannan suka shirya cikin shiga iri daya bak’a doguwar riga tare da farin gyale farin takalmi da farar jaka.

Amnah ce kadai ta tsaya yin kwalliya duk da dai bame yawa tayi ba itako fayal daman ba yi take ba iyaka karshen kwalliyarta shine tashafa farar hoda da farin manbaki.

Amman duk da haka kyanta kara fitowa yake sai kaga kamanma intayi kwalliyar muni zatayi.

Bayan sungama shirine sukayi breakfast karfe takwas daidai sannan suka nufi mota domin fayal jiki yayi sauki sose kaman ba ita bata jiya ba lafiya.

Amnah ce ke driving dinsu itako fayal sai tunanin abinda zatawa Amsard yau take.

Da isarsu makaranta akace musu ae yau lecturern bazai samu damar zuwa ba yayi tafiya so dole sai yadawo sucigaba.

Dan haka ynzu zasu cigabada lectures ne.

Ita dai fayal bataso haka ba domin kuwa yau taxomasa da tsarabar rashin mutunci ita practical dinma bai dame taba akan shirinta daya baci.

 

Fayal tacewa Amnah”kinga fa mutuminnnan baida mutunci fa”.

Amnah tace”haba fayal yanada uxurine fa”.

Fayal taja tsaki sannan ta huce ajinsu.

Sannan Amnah tabi bayanta.

 

????????
*malesia*

Amsard ne zaune adakinsa yafito DAga wanka yashirya cikin kananun kaya bak’in wando bluen riga sannan yasaka glass dinsa na likitoci.

Ankawo masa abincinsa sannnan yaci .

Bayan yagamane yadauko wayarsa yakira usman.

Bayan sun gesane usman yace”yauwa yallabe bani labarinku kai da madam”.

Sai da Amsard yaja numfashi domin shi harma yamanta dawata wai fayal.
Sannan yace”kai dai baka mantuwa wallah”.

Usman yasheke da dariya sannan yace”eh din naji nidai abani labari”.

Amsard yakwashe duk abinda yafaru tsakaninsa da fayal yafawa usman.

*PAGE* 21,22

——————————————————————-

Bayan yagama fadawa usman abin dayafaru tskaninsune.
Usman yace”oh Allah dai yakiyaye gashi yanzu baka da numberta balle muji yajikin”
Yakarasa maganar tare da dariyar mugunta.

Amsard yace”kai kama sameni wallahi yaushe zan karba number wannan jaririyar ai kabari kawai sai na nuna mata *Babu ruwan so* alokacin ne zata nemi numberta kai yarma dani gabaya”.

Usman yakara dariya sannan yace”kaiiiii oga adaiyi magani awannan miskilancin naka”.

Amsard yace”hmm usaman kennan karka damu kabi dramar nan asannu zatazo karshe bakaji yadda bature yake cewa *wonder shall never end* ba dan haka karkayi mamaki daga karshe”

Usman yace”toh shikenan oga Allah dai yaba da sa’a dawasa wasa hakan yazama gaskiya yatashi daga drama”.

 

Amsard yace”kai dai baka da damuwa wallahi gwara kai ma bara natashi domin zamu shiga aiki”.

Usman yace”toh yaushe zaka dawo neh?

Amsard yace”wallahi daga zuwana har aiki yamin yawa Amman karka damu inaga jibi nazo”.

Usman yace”owk Allah yakaimu”.

Amsard ya amsa da “Ameeeen”.

 

Sukayi sallamah sannan kowa yayi wajen aikinsa .

 

????????????

 

Lectures akema su fayal Amman ita gaba daya hankalinta baya jikinta sai tunani take .

Ita kadai sai yatsina fuskarnan take .

Abinda akasaba bara adaina ba dai.

Tun 8 suka shiga lecturers Amman sai 4 akabarsu sufito domin sallah hada azhar da la’asar sukayi.

Fayal sai mita takeyi akan anki bari su huta itako Amman sai dai ta kalleta domin ita tariga tasaba da hali irin na fayal.

Aiko suna idarwa ba abarsu sunci komai ba suka koma lectures .

Gaba daya sun galabeta sai wajen 6.10pm suka fito wasu masallacinma har Anfara kiran Sallah.

Suna fitowa suka nufi motarsu domin komawa gida bashiri Fayal tamikawa Amnah key din motar domin acewarta tagaji bazata iya komai ba.

 

Aiko Amnah gudu take Amotar domin ita kanta tagaji ga azababbiyar yunwa Anhanasu ko cin abinci.

 

Suna isa megadi yabude musu get suka shiga sannan Ammnah tayi paking fayal ko daukan jakartama batayi ba tashige gida .

 

SAi Amnah ce ta dibomusu dukansu.

 

Fayal tanashiga tayi sallama tageshe da momy daga nan bata kara cewa komai ba tayi cikin dakinsu.

 

sannan Amnah tashigo da sallamarta bayan sun gesa da momyne .

Momy tace”sannu da alama yau practical din yabaku wahala”.

Amnah tace”ai bama practical din mukayi ba domin lecturan bai zo ba.
kinsan mun kwana biyu ba lectures shiyasa yau muka dadde”.

MOmy tace”owk toh sannun ku nima yau aiki yamin yawane wallahi sai yanzu nashigo naga bakwanan gashiba abinci”.

Amnah tace”to bara nadaura mana momy”.

Momy tace”kema fa kingaji da kin huta kawai anyi ordering “.

Amnah tace”A’a momy kinsan fayal batacin abinci waje bara kawai nayi”.

Momy tace”oh Amnah kincika san sisternnan taki “.

Amnah tayi murmushi.

MOmy tace “to dai Allah yayi muku Albarka kuma Allah yakaramiki hakuri da juriyar zama da fayal”.

Amnah ta Amsa da Ameeen .

SAnnnan ta tashi tashiga daki tacire kaya tasa wasu tayi sallah tukun tashiga kichin.

Batare da bata lokaci ba ta fere doya sannnan tawanke tukun tasa atukunya ta daura agas .

BAyannnan tayi gretin din kayan miya tafara soyawa ba mai bayan yadan soyu tazuba kwai.

 

Kafin tagama miyar har doyar tayi dashike agas neh.

Bayan takammala doya da miyar sos ne tukun ta hada musu fruit salat.

Tana kammalawa anakiran sallar isha tuni taje tayi wanka sannan tadawo domin shiryamusu abinci a dainin.

????????

Amsard yana cikin aiki chuku chuku har yanzu dai anata fama akan kafar nan duk da alamun sun fara samun nasara.

 

*PAGE* 23.

————————————————————————-

sai karfe 10pm su amsard suka samu fitowa daga dakin ofireshon .

Suna fitowa yanufi gidansa sannan yayi wanka tukun ya gabatar da sallah.

Yana idarwa yanufi kicin domin shi inba girkin hajiya momy ba gwara yayi da kansa inkaga Amsard yaci abincin waje to fa ba yadda ya iyane.

Dan haka bai damu da gajiyar dake jikinshi ba yafara aiki .
yadaura sanwar wake sannan yadaura shinkafa adayan gefen gas din .

sannan yakoma yafara gretin din kayan miya.

Batare da bata lokaciba shinka far nan suka tafaso dan haka yasauke su duka sannan ya wanke .
Ya zuba su a abin tsamewa .
Yadibo kayan miyannnan yasa atukunya asoyasu sose da manja sannan yazuba su kayan dan’dano .
Bayan yazuba ruwan yatafasa sannan yasa su shinkafa da waken nan.

 

yatafi fallo domin huta wa bai fi 40minit ba aiko yafara jin kamshi alamun abincinsa yadahu
Yaje yasauke sannan ya samo plet yasa .
yakoma falo.
Sannan yake firish dinsa yadauko drinks na lakaseraH
Yazauna dominci.

Arayuwar Amsard acikin abinci ba wanda yakeso fiyeda dafa dukan shinkafa da wake.

Adrinks kuma lakaserah.

Shiyasa ba ya kyashin yima kansa girki komai dare.

 

*PAGE* 24,25.
———————————————————————–

Amsard yagama abincinsa yaci kuma sannan yayi lafila tukun ya kwanta barci.

Suma su fayal sunci abinci tukun sukaje kwanciya.

Anan ne fayal take ta tunin Amsard dayaki zuwa azyciyarta tace kodai ma tsoro yajine yace zai tafi wajen aiki ana nemansa tana ta tunani dai iri iri daga karshe kuma tace”toh ma ina ruwana dashi mtsw”.

Batasan maganarma tafito fili ba sai ji tayi Amnah ta shek’e da dariya .
Sannan tace “aiko da ruwanki tunda kina tunaninsa”.

Rain fayal yabaci dan haka taje dogon tsaki sannan ta kwanta.

Sai tajima ita kanta haushin kanta take.

****WASHE GARI******
????????

Da Asusuba Amsard yatashi yayi sallah sannan yayi wa kansa breakfast .
Yayi wanka sannan yashirya tukun yayi break kafin 7 har ya kammala komai nasa sai tafiya asibity.

Da isar sa asibity akasanar masa Da ai feshen din sa ta farka .

Aiko yayi farinciki da jin hakan .
Batare da bata lokaciba yaje yaduba sannan yamata tambayoyi tukun yakoma office dinsa.

 

yau gaba daya fayal ta tashi jiki ba kwari ita kanta batasan meke damunta ba ita dai kawai taji jikinta ba kWAri .

Dan haka tanayin wanka ta zumbula doguwar riga sannan ta dauko hijab da glass dinta tasa .

Ko breakfast dinma takasa yi su momy sun tambayeta menene Amman sai dai tace musu bakomai.

Tun suna tambayarta har suka gaji sukayi shiru.

Ahaka suka tafi skul itada Amnah .

Fayal sai faman tsaki take wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.

Ita kuwa Amnah me zatayi banda kallo .
Azuciyarta kuwa cewa take”da alamu kinkusa chaza hali mu huta dan inAga kinkusa fadawa tarko”.

Afili kuma tayi murmushi abinta.

Fayal ko sai sake yamutsa fuskarnan take ga tsaki.

 

Ahaka suka isa skul ba mai wa wani magana .

duk da dai daman hakan dabi’ar fayal dince .
Amman nayau din yafi nakullum.

Sun isa skul wajen 8 dan haka har anfara lectures ma Amnah tashiga sannan tace”excuse sir”.

Sai da yabata izinin shiga tukunna tashiga .

Ita kuwa Fayal batama fito amotar ba sai ynzu duk da tasan sunyi letti Amman ko ajikinta .

Tafiya take kamar bazata taka kasa ba .

TaNa zuwa tashige lecture room din ko sallama babu.

Shiko lecture yace”tafita mai a aji tabari sai takoyo sallama tukun tadawo.

 

Aiko hakan ko ajikinta Dan hakama yasa tacigaba da tafiya kamar wadda kwai yafashe mata aciki.

kowa yakoma da kallonsa gareta ahaka har tabar ajin.

 

shiko lecturern sai da yazabga tsaki sannan yace”wallahi duk mace me irin wannan halin tausayima ni take bani gwara ku gyara halayenku ku huta.

 

Sannan yacigaba da lectures dinsa.

 

Amnah azuciyarta kwatakwata bataji dadin abin da fayal tayi ba domin koda yaushe infayal tayi wani Abu kanta yake dawowa sai yan ajin sutamata habaici.

Itakuma batason hakan
Shiyasa kawarta guda dayace akaf makarantar.

 

Fayal tana fita tayi mota tabude baya ta kwanta abinta ita har taji makarantar tafitan mata akaima.

KOMai yasa?
Ohooo Amsar da taba kan ta kenan.

Ahaka har tafara barci abinta.

?????????????????????

Amsard yaga yau ba aiki sose a office dan haka yafara shirin komawa nigeria gobe.

MIsalin karfe 2 Yakira usman yafada mai insha Allah gobe zai dawo .

SAnnan usman yace”toh Allah yasa nidaman na zaqu kadawo aciga ba da drama domin naga mutuniyar ma amota ita kadai
DA alama dai yau ma ankuma da wani kenan”.

Amsard yace”hmmm ai wannan yar sai dai Allah yakyauta Amman fa karka damu nakusa saita ta”.

USman yasa dariya sannan yace”toh nidai kullum inama fatan sa’a “.

Amsard yayi dariya shima sannan yace”kadai ji dashi ageshemin da uwargida”.

USman yace”aiko zataji domin nafara bata labarin dramar ku”.

Amsard yace”kace kasani a faifai kenan”.
Usman yasa dariya.

SAnnan AMsard yace”nidai sai anjima inashiri ne”.
Sukayi sallamah.

*PAGE* 26,27.

—————————————————————-
Bayan usman sunyi sallama da Amsard .

Sai Amsard yacigaba da shirinsa nakoma wa nigeria.

 

Abangaren fayal kuwa tun karfe 9take barci sai 1 tafarka daidai da fitowar su Amnah kenan.

Amnah nafitowa ta hango motarsa abin yabata mamaki dan batayi tunanin ganin fayal ayanzu ba.

Batama ga abin mamaki ba sai da taga fayal da alamun tashi daga barci.

Azuciyarta tace”ikon God”.

Niko nace sai kallo.

tana zuwa tace”fayal lafiya kuwa”.

fayal ta yamutsa fuska har kungama kenan?

Amnah tace “eh wlh lecture usman ma yasanar damu insha Allah jibi zamu cigaba da practical dinmu”.

Fayal tace”kwaji dashi dai”.

Amnah tace”hhhh ai shiyasa kikaga mun fito da huri yau yasin da sai 6 inaga har sai kingama kumburah ma’.

Fayal taja tsaki sannan tace”ni kishigo mutafi ko malama”.

Ita dai Amnah dariya take da dariyarta tashiga mota suka nufi hanyar gida.

Sun isa gida bakowa dahike momy ta tafi aiki shikuma dady yayi tafiyama.

Dan haka suna isa fayal tayi sallah tukun tadawo kichin domin daura abinci.

Duk irin halin fayal na kyaliya hakan baisa iyayenta sun sakalta ta ba .

Aduk sanda momy zatayi girki sai ta tabbatar da su fayal da Amnah na wajen.

Dan haka fayal tashiga kichin domin musu girki .

shinkafa da wake dafa domin itama shine abincin datafi so arayuwarta.

Tana kammala momy tadawo dan haka suka hadu a dainin domin cin abinCi.

Ananne momy tace”yadai maganar practical dinnaku gashima naga yau kun dawoma da huri”.

Amnah tace”umm momy wai jibi zamu cigaba kinsan gobe sunday shiyasa kawai akabari sai monday inAga yau me practical din zai dawo shiyasama yau bamu jima a lectures ba”.

Momy tace”owk su fayal ansha aiki ko maganar ma baza amin ba”.

Fayal ta yamutse fuska sannan tace”hmmm momy”.
Daganan bata kara cewa komai ba .
Sukuwa momy da Amnah suna hira sunacin abincinsu.

Itakuwa Fayal yadda batason yin magana haka bataso nakusa da itama su cika yi dan Haka da anfara cin abinci taga su momy sunfara bude dandalin hira sai tayi sauri tabar wajeN.

Toh yau mah haka tayi tayi tatashi tabar wajen.

Dashike sunsaba da halinta hakanma baya damunsu.

Fayal tana shiga daki Tadauko wayarta tafara game.

Domin datayi magana gwarah tata karatu ko game.

Suko su momy sai dasukaji sunyi nak tukun Amnah ta kwashe kayan da tA bata tatafi wanke’wanke .

Sai momy afalo dake danna wayarta.

Megadi yashigo da sallamarsa.
Momy ta Amsa.

Sannan me gaji yace”wai wani ne yace nakira masa fayal”.

Shikansa asanyaye yake maganar domin yasan halin ta sarai.
Bayau akasaba zuwa wajenta ba tana hulakanta mutane .
Amman duk da haka kaman karuwa masoyanta suke.

Sai da momy taja dogon nufashi.
Domin ita kanta tsoron yartata take.

Sannan tace”waye ke kirinta?.
Megadi yace”wani ne yazo amota yana waje “.

MOmy tace”owk kace tana zuwa”.

Megadi yace”toh sannan yatashi yatafi jikinsa asanyaye.

Momy takasa motsi sai tunanin yadda zata bullowa yartata take.

Daga karshe dai kawai ta yanke shawarar zuwa tasanar mata.

Momy nashiga ta tarar da fayal kwance tana game awaya.

TAyi sallama sannan fayal ta dago tukun ta Amsa.

MOmy tace”fayal “.

Fayal ta dago.
Tukun momy takara da cewa dadynki ya aiko wani dan abokinsa kije ku gesa”.

fayal ta yatsina fuska sannan tace momy ni wallahi agajiye nake kawai Amnah taje su gesa”.

DAkyar momy tajawo hankalin fayal dataje su gesa tukun tayarda.

Momy tabar dakin gaban ta sai faduwa yake.
Azuciya kuma tana addu’ar Allah yasa adace yau”.

FAyal tadauko hijjabinta harda daukowa Amnah likaf tasa.

Tana fita!.

 

*PAGE* 28.

———————————————————————-

fayal ta fito tana fitowa ta hango wani saurayi Tsaye tare da abokinsa sai washe baki suke.

Taja dogon tsaki tukun azuciyarta tace”hmm shirme”.

Tafiya take kaman bazata karasa garesu ba.

Hakanne ma yasa basusan da fitowarta ba.

Sai da ta isa dai dai wajensu tukun suka ankarah.

Saurayin nan ne yafara magana dace”hajiya bako sallama ne?.

Abokinsa yace”kokuma tayi bamuji ba dai ko?.

Saurayin yace”oh hakane fa ashe kanata jana da hira ne”.

Suka sheke da dariya dukansu .

Ita kuwa fayal abin ya kona mata rai taja dogon tsaki.

 

Tukun saurayin yafara dacewa”toh hajiya nidai sunana ibrahim Anakira da khaleel ni dan kasuwa ne kuma ina karatune har yanzu Kuma ni dan garinnan neh”.

Yakara jan numfashi sannan yace”naganki ne wallahi Askul dinku nikuma naga bai kamata namiki magana acen ba shiyasa naxo nan”.

 

Agaskiya inasonki sokuma na aure.

Khaleel sai washe baki yake waishi adole Amsa yake jirah.

Duk maganar nan yake itA fayal ko ajikinta ita haushinsa nema yakamata.

Gawata dariya dayake kamar anmasa kyauta.

Duk azuciyarta take ta fadin hakan.

Abokin khaleel yace”kodai kunya hajiyar tamu take neh”.

Shiko khaleel har yanzu dai washe baki yake.

Sai Alokacin fayal tadago ta kare musu kallo sannan taja dogon ciki tafara tafiya.

 

Shikuwa khaleel da Abokin sa tsayawa kawai sukayi suna ganin ikon Allah.

Tafiyarta take hankalinta kwance kamar ba abinda yafaru .

Sai da tashiga cikin gida tukun abokin khaleel yace”kaga dai abinda nke gujemaka kenan ko?

 

Sai da akace kar muzo kowa yafadamana halinta Amman kai kaki yarda wai adole sai ka gwada sa’arka toh ai kuwa yau ga sa’arnan kazo gun wadda ko kalloma bamu isheta ba”.

 

Shidai khaleel yakasa magana domin har ynzu abin mamaki yake basa.

 

*PAGE* 29,30.

———————————————————————–

Bayan shigar fayal gidane .
Su khaleel kuma suka tafi.

****WASHE GARI*******

Amsard yakammala shirinsa tsaf domin tahowa nigeria.

Yagama komai sannan ya yatafi domin hawa jirgin safe.

yazuwa kuwa ba ajima ba suka kammala kome jirginsu yatashi.

Wata yar budurwace ta nufo inda Amsard yake .

Tana isa tace masa”excuse sir”.

Tukun Amsard yadago yakalleta .

Tace”can i sit pls”.
Cike da shagwaba take maganar.

Shikuwa yarasama me zaice mata kawai sai ya girgiza kai.
Alamun eh .

Aiko tana ganin haka tayi saurin zama kusa dashi.

sai magana take me da turanci Amman yaki kullata .

Domin shi Amsard yatsani macen data fiye iyayi.

Baima san tanayi ba duba jaridar hannunsa yake.

Gashi kana ganinta kasan jinin hausawace amman tazo taname wani yare.

 

Sunfi minti goma ahaka sai daga karshe taga dai ba sarki sai Allah tukun tace”haba oga magana fa nake tun tuni kaki kulani”.

Akara na biyu kenan daya dago tukun yace”au daman kin iya hausa neh?
AI nazata daga turanci sai turanci”.

Budurwar nan tayi murnushi tukun tace”Ai kaine nake tunanin bakajin hausa shiyasa nama turanci”.

Amsard yace”owk”.

Budurwar nan takara dacewa”sunana zubaidat Amman anakirana da zuby
Sannan kuma ni yar asalin jigawace Amman ina karatu A malesia”.

 

Amsard yace”owk barkanki dai”.

 

Zuby takara dacewa”inbazaka damuba inaso nazama sistern ka”.

Amsard yamata shiru.

takara dacewa”pls kuma me sunanaka?

Amsard yace”sunana Amsard kuma ni dan garin katsinane nima karatune yakaini malesia sannan nafara aiki”.

Zuby gaba daya tabawa Amsard hankalinta sai dataga yatsaya da magana tukun .

Tace”wooow Amman gaskiya sunanka yamin dadi kamar yadda kake da kyau hakama sunanka yake.

Toh pls kayarda nazama sister ka mana”.

Amsard”yace owk”.

 

Zuby takuma cewa”toh kadan bani numberka mana dan Allah”.

Amsard yace”owk sannan yafadamata ta rubuta sai da takirasa taga yashiga tukun ta katse .
Sannann tace”toh kayi save mana”.

Amsard baice mata komae ba yayi saving tukun yacigaba da karanta jaridarshi.

 

Zuby ta lurah dacewa Amsard bai son magana sose shiyasa tun tana jan sa da hira har tayi shiru tabarshi.

 

Ahaka har suka iso nigeria zuby ta tsaya tukun tame sallama tare da yafadamata a inda yasauka zatazo domin tasamesa.

Amsard yamata kwatance makarantar su fayal tace “aiko gobe zatazo insha Allah”.

Aha sukayi sallama kowa yayi hanyarsa.

Abangaren su fayal kuwa yau ana hutu tunda sukayi sallahr asuba ita da Amnah suka koma barci sai wajen 12.30 suka tashi.

 

Suna tashi kuwa sukayi wanka tare da sallar azahar tukun suka fito geshe da momy.

Amnah ce tafara fita .
Tana fita tahango momy naduba takardu ahannnunta.

Amnah tageshe da momy .

MOMy ta amsa cikin sakin fuska .

Sannan fayal tafito ta geda momy.

Momy ta Amsa.

Sannan momy tace”toh tunda sai ynzu Allah yayi kuka tashi ai sai ku daura girki”.

FAYal ta hada rai kaman zatayi kuka.

Amnah tace”uhymm momy yunwa fa nakeji nidai”.

Momy tace”aiko zakuyi bayani tunda bani nace kuta barci ba”.

Fayal tace”uhumm momy”.

MOMy tace”toh kudan ban tausayi dai ga abinci ku cen kuje kuci”.

FAyal tayi murmushi tare da fadin”owk momy”.

AMnah ma tawashe baki tare da tashi domin zuwa cin abincin.

FAYal ma tabi bayanta.

SUNa zuwa kuwa sukaga AShe dambu momy tamusu.
DAman tasan Amnah dason dambu shiyasa take yawanyi.

AIkuwa AMnah tana gani tace”woooow sannan tajuya gun momy da gudu turungumeta tare da fadin “nagode momy nah”.

Momy tayi murmushi tukun tace”u ar wlcm my daughter”.

SAnnan AMNah takoma sukafara cin dambu sai washe baki take tana ta surutu itakuwa fayal sai yatsina fuskar nan take tana ci kaman dolE.

DUK DAtanaso amman bata nunawa.

Itakuwa Amnah sai zakan abinta take.

*PAGE* 31,32.

———————————————————————–

Fayal ce tarafara tashi tabar Amnah tanacin abinci
Haka kawai taji tana farincikin da ita kanta batasan dalilinsa ba
Ahaka ta wuni cikin farinciki wadda ko su momy sai da abin yabasu mamaki.

Kawai binta suke da ido
Sai kallo.

Amsard ya iso jigawa karfe 4.00 ina isowa yakira usman awaya domin yazo yadaukesa.

Batare da bata lokaciba kuwa Usman ya iso
Yana isowa Amsard yahangosa dan haka yasa yakarasa wajen sa.

Amsard nazuwa yace”a lallai usy kanaji dani naga saurinka fah”.

Usman yayi murmushi sannan yace”ba dole naji dakai ba tunda kakusa angwancewa”.

Amsard yadan daki bayan usman sannan yace”kai ko baka da dama gwara kai nikam muje kasaukeni amasaukina insamu inyi wanka dan wallahi nagaji”.

Usman yayi dariya sannan yace”owk oga muje”.

Usman ne ke driving dinsu cikin kwanciyar hankali yanata jan amsard da surutu .
Shiko Amsard sai dai yayi murmushi
Amman duk da haka usman bai bar magana ba sabida yasaba da halin abokin nasa.

Ahaka har suka isa hotel din da amsard ke sauka tukun sukayi sallama tare da fadin cewa gobe sa hadu a skul cewar Amsard.
Usman yace”owk”.

Amsard nashiga dakinsa yayi wanka sannan yayi sallah tukun aka kawo masa abinci yaci.

****WASHE GARI*****

Fayal tunda tatashi sallar asuba bata koma barci ba tana ta shirin skul tare da girka breakfast .

Ita tayi musu komai nakaryawa sai da ta kammala ma tukun Momy tafito domin daurawa aiko da mamakinta taga har fayal ta gama komai.

Taji dadi sose domin tana ganin yarta takusa dawowar rayuwa kamar takowa.

Momy tace”sannu fayal”.

Fayal tayi murmushi tukun tace”morning momy”.

MOmy tace”morning daughter.

Sannan fayal tace”momy bara naje natashi Amnah tayi wanka nimA nayi sai muyi breakfast din”.

Momy tace”owk”.

Fayal taje tatashi Amnah tukun tashiga wanka bayan ta fito neh Amnah ma tashiga tayi.

Bayan sun kammala shirinsu tsab tukun suka nufi falo domin yin breakfast.

Sai dasuji duk sunyi da dam tukun suka tashi domin tafiya skul
Suka mawa momy sallama tamusu addu”a sannan suka tafi mota.

Dasuka shiga mota Amnah ce ke driving ita kuwa fayal sai murmushi take tana tunani.

Amnah tadago ta kalleta abin yabata mamaki azuciyarta tace”oh kome yasami fayal ne ? ohoo tabawa kanta Amsa sannan takara dacewa Allah yasa dai lafiyarta kalau”.

 

Abangaren Amsard ma tuntuni yagama shirinsa nazuwa skul .

Yana fitoWa yahau motarsa domin jiya daddare usman yabadaa motar aka kawo masa .

A dai dai Amsard dasu Fayal suka iso school.

Amsard ne yafara fitowa ya shiga ciki.

Sannan su fayal suka bishi abaya
amsard yana shiga yaga usman har angama shirya kome kawai shi ake jirah.

Su fayal ma sun shigo.

Batare dA bata lokaci ba kuwa akafara practical .

Sunfara tun wajen 8 amman gashi har 3 basu gama ba duk kowa yagalabaita.

Dan haka Amsard yace suje suyi sallah sai adawo .

Amsard da usman suka tafi masallaci sukayi sallah aiko suna idarwa usman yace”kai oga yamaganar dramar nan tamune ?.
Amsard yayi murmushi sannan yace”dadina dakai zumudi Amman karka damu yau za afarah”.

Usman yagyara zama da darisa sannan yace”dakyau”.
Amsard yace to ai sai katashi mutafi ko?.
Usman yatashi domin komawa.

Suna tafiya tare kamar bazasuyi ba sai dariya usman yakewa Amsard.
Ahaka har suka isa.
Suna shiga akacigaba da aiko ba tsayawa domin Amsard yarike wuta akan dole sai sun kammala yau.

Ai ko sai karfe 6.00 suka gama.

Amsard yahango fayal zaune Amota tana jiran Amnah taje karbo wani book dinta.

Amsard yataka asannu har motarsu yama fayal sallamah ta Amsa.
Tadago takallesa tukun ta sunkuya.

Amsard yace”yajikin naki fatan kinsamu sauki dai ko?.

Fayal tace”dasauki jiki Alhmdlh”.
Amsard yace”ko zan iya samun numberki?.
Fayal ta tsinci kanta dason bada numberta
Batare da bata lokaciba tafada masa .

Sannan yayi saving
Amsard yace”toh nagode malamah fayal”.

Fayal sai dataji wani tsigar jikinta natashi sabida yarda yafada sunan.

Murmushi kawai tamai shima yamata sannan yatafi.
Yana tafiya Amnah ta isa taga hucewarsa dan haka take ta tunanin kardai fayal ta wulakantasa neh ahaka har ta isa motar.

Tana shiga kuwa ta ga fayal sai wannan murmushinfa take nayanzuma har yafi nada ita dai abin yaKara kule mata kai kenan.

Shikuwa Amsard yana karba ya nufi inda usman yake domin yalabe ne yaga me zai wakanah.

Yana zuwa usman yace”yana kanata murmushi ne kodai andace ne?.

Amsard yace”da alamu yar nan har tafara fadawa tarkona”.

Anan amsard yama usman bayanin komai .
Aiko usman yayi farinciki da jin haka domin burinsa kenan.

 

Abangaren fayal kuwa har ynzu dai murmushinan take amnah sai da tagaji da kallon ikon Allah tukun tafara tuki.

Ita kuwa fayal har ynzuma batasan wai amnah kallonta take ba domin tunaninta yayi zurfi.

Ahaka har suka isa gida.

 

Amsard yabi usman gidansa sai da sukayi sallahr magriba da isha sannan suka shiga ciki wajen Ameenah.

Ameenah tayi farinciki da ganin amsard abokin tsokanarta.

*PAGE* 33,34.

—————————————————————-
Amnah tanayin pakin fayal ta fito da gudu ta shiga gida tare da murmushi afuskarta.
Tana shiga ta ga momynta afalo da guda ta karasa tare da rungumeta tana oyoyo momynah.

Tsabar mamakin da momy taji takasa rufe bakinta atsaye take kyam
Sai da fayal din ta kara dacewa’ umm momy miyafaru naga kina mamaki?

Momy tayi murmushi sannan tace”lafiya kuwa fayal?.
Faya tace”uhumm momyna lafiyalau tana fada tana tafiya harta shiga daki.

Sai ga Amnah tashigo taga momy sai murmushi take.

Bayan tayi sallama momy ta amsa takara daceWa”momy naga kema kina murmushi kodai kinga abinda nagani ne?.
Momy tace”hmm kedai bari kawai yau da alamun sa’a agidannan “.

Amnah tayi murmushi sannan tace”uhumm momy ai kawai kibari wannan ma kadan neh”.

Momy tace”hmm toh dai Allah yasa hakan alkairi ne”.
Amnah tace”Ameeeen “.
Sannan ta nufa dakinsu.

Amsard suna shiga Ameenah tafara tsokanarsa tana” ango an iso kenan ya kawartawa?.
Amsard yayi murmushi tare da cewa”hmm gaskiya keda mijinki baku da damuwa naga alamah”.

Usman yayi karaf yace”aiko muke da damuwa domin kuwa damuwa ita ce muga mun aurar da kai”.
Ameenah tace”yes my honey kasan wannan da kauyene rabu dashi ai yanzu bamu da matsala tunda kakusa fadawa tarko”.

Shide Amsard dariya ma suke basa domin gani yake abin ba me yuhuwa bane.

Ameenah takawo wa su amsard abinci sai da sukayi nak kafin Amsard yatashi ya nufi masaukinsa.

Fayal tunda tashiga daki barci take har Amnah tagama girkin dare Amman sai da aka fara kiran sallah fayal tatashi.

Yau da dady zai dawo da daddare shiyasa Amnah ta yi girke girke.
Aiko ana idar da sallar magriba sai ga motar dady.

Fayal ta fita daguda ta taro dadynta shiko dady sai dariya yake ahaka suka shiga gida .

Sai da dady yayi wanka yayi sallah tukun akazo wajen cin abinci.
Har yanzu fayal murmushi yake shiko dady yakasa hakuri sai da yace”ya naga gidan yakara haske ne sai dariya fayal take?.
Momy tace”hmm kema kagani dai da alamu addu”ar mu tafara aiki kenan”.

Ita dai fayal bata fasa murmushinta ba .

dady yakara da cewa”wallahi har kyanki yafito my daughter dakika fara murmushi”.

Momy tace”fada mata dai”.
Amnah ma dai sai fara”ah take domin ita kanta tafison ganin fayal ahaka.

Sai wajen karfe 9 kowa yatafi daki ya kwanta.

???washe gari???

Su fayal sun kammala komae sun tafi skul.

Amsard yana tashi da safe yashirya domin komawa katsina.
Sai da yakira hjy momy yasanar mata tukun yakira usman sukayi sallamah sannan yahau motarsa domin yanufi katsina.

karfe 9 dai dai ya isa domin gudu yke amotar hjy momy taji dadin ganinsa haka ma Alhaji .
Anmasa abinci kala kala iri iri yaci ya kwoshi sannan yke sanarwa wa da hjy momynsa yayi kewar abinci ta.

Ita dai hajiya murmushi take sannan tace”ai ankusa adaina kewata da abinci na in nasamu sirika.

Amsard yayi murmushi tare da sose kyaya tukun yaci gaba da cin abincinsa.

Sai ga su samir da sahala nan sundawo daga skul.

Samir yace”oyoyooo sweet br nah”.

SAlaha tace”uhumm ysn br dina ne ba naka ba”.
Amsard yace”kudai bazaku girma ba tu kuzo nan”.

Suka karasa wajensa sannan suka geshe sa bayan ya amsa sahala tace”br my tsaba fa?

Amsard yayi murmushi yace”karki damu little sister tsarabar ki na nan”.

SAmir yace”uhymmm nifa br”

Amsard yace”haba ai kasan kai muna tare”.

Momy tace”kwJI dashi dai”.

Ahaka su Amsard suka yini cikin farinciki agidansu .

Ahaka har dare yayi.

sai 6 su fayal suka koma gida daga skul.
Bayan tayi sallah
Sunci abinci tana kwance akan gadon ta sai kallon wayarta takeyi.

Aikuwa sai ga kira yashigo mata .
Mezata gani?.

SAbuwar ce tashigo mata.

WAye yakirata???
Shin zata daga ko bazata daga ba????.

 

Sai kubiyoni danjin yazata kayah.

 

*PAGE* 35

—————————————————————-

Fayal bata daga sabuwar number awayarta wani lokacinma ko tasan number ba dauka take ba bare wadda batasani ba.

Awannan lokaci kawai sai ta tsinci kanta dason daga wannan number.

Dan haka ta amsa tare da sa wayar akunnenta.
Tayi shiru .

Abangaren amsard ma shirun yayi domin ya tsinci kansa asabon yanayin da bai taba shiga ba.

Dan haka dukansu sukayi shiru nadan mintuna .

Sai chan Amsard yayi jarumta yace”Assalamu alaiki”.

Fayal sai da taji wanni iri ajikinta na sabon yanayi .
Itama dakyar tayi dagiya sannan tace”wa”alaika salam”.

Alokacin Amsard yaji yasamu kwarin gwiwa dan haka yakara da cewa”Yakike? ya gida? ya aiki?.

Fayal batasan sanda dariya ta subuce mata ba tsabar tambayoyin da taji ya jero mata.

Aiko Amsard yanajin haka shima yafara tayata dariya.

Sai da tasha dariya iya shanta sannan tace”yooo irin wadannan tambayoyin har ina?.

Amsard yace”har zuciyAr fayal manah”.

Sai da faya taji wani zir azuciyarta sannan tayi karfin halin cewa”toh duk dai lafiya”.

Amsard yace”ai haka akeso .
Yau kunyi lectures ko?.

Fayal tace”eh wallahi gashi duk mungaji “.

Amsard yace”hmm to Allah yahuta gajiya”.

Fayal tace”Ameeeeen”.

Sai kuma duka sukayi shiru kowa yakasa maganah.

Sai chan amsard yKuma cewa” to sai anjima malama fayal”.

 

Alokacin fayal taji duk walwalarta ta dauke domin bata gaji da jin muryArsa ba.

Dan haka tace,,,,,,,,,,,,,,,,,,

*PAGE* 36,37.

————————————————————————-
Dan haka tace”owk ba matsala sai anjimah”.

Sukayi sallama acikin nutsuwa.

Bayan sun kammala wayar Amsard yaji gaba daya yanayinsa ya chanja .
Sai wani farin ciki yake wanda shikansa bai san meya jawo hakan ba .
Shidai kudurinsa akan fayal da bannne yanzu kuma yaji yanayinsa daban ba irin wanda yatsara ba.

Kome yasa hakan,ohoo
Yake tambayar kansa.

Abangaran fayal ma jitayi farincikita na karuwa amman ita ayanzu tafara tantamar kardai so ne yakamata .
Azuciyarta tace”aa fa kawai yana burgeni neh”.

Niko nace zama kiyi bayani.

Tundaga ranar kusan kullum misalin karfe 8 nadare amsard yake kiran fayal awaya su gesa bayan sun gesa haka dukansu zasuyi shiru na yan mintuna sannan suyi sallama kowa kuma yana begen juna.

Duk da basu da wata hirar dasuke tabukawa awayar amman haka bai sa Amsard yadaina kiran fayal awaya ba
Haka kuma itama fayal duk sanda bataga kiransa ba takan shiga damuwa.

 

Yanzu gaba daya fayal ta chanja tafara sakewa da mutane amman duk da hka dai bata dai na wannan yatsinar fuskarba kuma rashinson maganar nan ma na nan sai dai tadan ragu.

Momy da dady tare da Amnah bakaramin farinciki sukeba sanadiyar ganin fayal cikin walwalah.

Shiko Amsard har yanzu dai miskilancinsa na nan amman kuma bai baryiwa mutane murmushin nan dayasaba ba.

Yauma dai kamar kullum fayal da amnah sun gama shirinsu tsaf domin tafiya skul.

Yau kam amnah batajin dadi sose dan hka fayal ce tayi driving dinsu.

misalin karfe 8suka isa
Suna zuwa kuwa ana shiga lectures
Dashike yau lectures din safe suke dashi kadai hakan yasa suka fito karfe 2.

Suna fitowa Fayal tace ma amnah”inaso muje zan siyo wani story book kinga yau mun fito da huri”.

Amnah tace”owk toh muje nima naduba”.

Sukaje wani shagon littafai.

Fayal tana zuwa tafara dube-dube bataga littafin da takeso ba.

Chan kuma taga Amnah tazo tace”nikam kinga nina sami nawa fadamin sunan wanda kikeso natayiki nemah”.
Fayal tace”muga nakin”.
Amnah ta bata

 

Aiko fayal nakarba taga an rubuta true love story
Fayal tace”woow toh ai wannan nake nima”.
Amnah takasa magana dan mamaki wadda ta tsani jin kalmar love ma wai itace me cewa tana neman love story!

Ita dai kawai kallon fayal take

Fayal takara da cewa”muje nima kidauko min ko”.

Sai alokacin amnah tace”owk to rike wannan ni bara nadauko wani”.
Amnah taje tadauko sannan ta biya .

Suka koma mota sannan suka kama hanyar gida.

Wajen karfe 3 suka isa gida suna zuwa sukayi sallah sannan fayal tashiga kichin domin daura abinci.

Ita kadai take aikin domin amnah tana dan zazzabi.

Dan haka ta yanke hukuncin daura musu indomie suci kawai daga baya sai ta daura girkin dare.

Aiko tana kammala indomien tadaura girkin dare sannan tadawo sukaci ita da Amnah.

Sai wajen karfe 6 sannan ta kamala girkin dai dai da dawowar momy da dady.

tana gama taje tayi wanka tukun dukansu sukayi sallah magriba .

Sannan suka ci abinci
SAi bayan sallar isha kowa yatafi daki.

FAyal nashiga daki tafara karanta littafinta
Tana karantawa tana kallon agogo .

 

TAga har karfe 9 amsard bai kirata ba.
Tun tana boye damuwarta harta fara bayyanata.

Tayi kwokarin mayar da damuwar amman takasa .
Dan haka ta yanke hukunci kiransa kawai.

Tadauko wayar zata kira takasa.
Taga abindai ba yi dan haka ta dan nah kirah.

Takira wayarsa akashe taki shiga kwatakwata.

Duk da haka bata daina kira ba har wajen 10 amman yaki shiga.

tacigaba da kira har wajen 12 sannan taga tashiga.

 

Tashigan tana ringin amman ba adauka ba.
Sai da takira wajen sau 9 ba adaga ba ata goman ne taci sa a aka daga .

fayal tace”assalamu alaikum”.

Adaya bangaren akace”wa alai salam”.

sai da fayal taji numfashinta yafara daukewa domin muryar mace taji awayar .

meyasami amsard?
Shin wacece tadaga wayar?

Sai kubiyoni domin jin yazata kasance.

 

*PAGE* 38,39.

————————————————————————-

Fayal takasa maganar da hajiya momy taji shiru sai tace”me wayar bai da lafiya neh yana barci kuma yanzuma nina kunna wayar”.

Sai alokacin fayal tace”ayyah ina hini?.

hjy momy tace”lafiya lau”.

Fayal tace”toh ya mejikin?

Hjy momy tace”dasauki inya tashi ma zan fada masa kin kirah”.

Fayal tace”owk sai da safe “.

Ahaka sukayi sallama.

gaba daya daren ranar fayal takasa barci sai tunini take tarasa me yake mata dadi daga tace wannan sai tace wanchan.

Gaga karshe kuma tace”toh kodai sonsa nake?

Ta tambayi kanta sannan takara dacewa”aa shakuwace kawai”.

Ahaka sai wajen karfe 3 nadare tukun fayal tasamu damar yin barci.

Shiko Amsard dama tun safe yatashi da matsanecin zazzabi hakan yasa momy takira family doctorn su yadubasa yamasa allurai shiyasa tunda yasamu barci bai farka ba har cikin daren.

Momy nagama waya da fayal ta tsinci kanta cikin farinciki mara misaltuwa domin ita aganinta yanzu danta har yasamu lokacin kula wata budurwa da har zata kirasa.

Dama alokacin tazo dubasa ne sai ta kunnah wayar domin tasan za ane mesa aiko tana kunnawa taga kiran fayal yashigo.

Dan haka tana gama waya da fayal ta nufi dakinta domin kwantawa.

*WASHE GARI*

Fayal takasa tashi sallar asuba sana diyar rashin barcin datayi jiya dan haka sai da Amnah ta tasheta tukun tayi sallar .

Amman gaba daya jitake bata da lafiya ga tunanin amsard fal azuciya.

Dan haka tana idarwa tashiga wanka tayi kozataji dadin jikinta sannan takoma barci.
Dayike yau weekend ne.

Amnah tazo kiranta suyi breakfast kawai taga sai rawar sanyi take abin yarazana Amnah dan hKa tayi gaggawar kiran momy aka kira doctor .

Batare da bata lokaci ba doctor ya iso yadubata tabata magani da allurai sannan tasha tea sai ta koma barci.

Abangaren amsard kuwa yau yatshi da kwarin jiki .

yau duk su sahala da sameer na gida .
Dan haka suna tashi suka nufi dakinsa .

Sai rigima suke masa shiko da hike ba me magana bane inyayi daya biyu sai yamusu murmushi.

 

Anacikin haka hjy momy tashigo dauke da breakfast din Amsard.

hjy Momy tace”toh ba za dai abar min da ya huta ba ko?.

Sahala tace”uhumm hjy momy nikadaice fa yarki”.

Sameer yace”tab ni ne kuma ma nitafiso”.

Sai alokacin Amsard yace”bawani nan dukanku ba ya”yan hjy momy bane ku ya’yan Alhaji neh”.

 

Tuni sahala tafara shagwaba ita adole itace yar hjy momy.

Ita kuwa hjy momy sai dariya take musu tana farincikin ganin iyalenta cikin walwalah
Daga karshe tace”haba auta aike ta da bance
Kai kuma sameer aikasan kai yayanta neh dan haka kaci girma”.

Samer sai murna shi adole yayan sahala ne.

Suko amsard da hjy momy sai dariya suke musu.

hjy momy tace”in kutashi muje ga breakfast dinku chan kai kuma son ganaka nan kaci”.

SAmeer yace”ai nima ance yayan sahala ne toh sai akaimin daki irin na bros”.

 

Amsard yace”a lallai ma sameer wato kanmu daya ko?

 

Dukansu suka sa dariya sannan suka fita.

 

Abangaren fayal kuwa sai wajen karfe 2 ta farka tasamu tayi wanka sannan tasha kosta.

 

Amsard sai alokacin dayagama kome tukun yadauko wayarsa yana duba wa aikowa sai gashi yaga kiran fayal DAtayi jiya yaga andauka dan haka Yace”kar dai momy ce tadauko”.

 

 

YANata sakye sakye azuciyarsa.

DAi dai da lokacin da fayal tadauko waya

TAfara kiran amsard
Tana kira kuwa taci sa,a yashiga bajimawa ya dauko.

tare da yin sallamah

FAyal sai da taji wani farinciki tare da annaushuwa najin muryarsa datayi.

 

*PAGE* 40
————————————————————————-

Fayal ta amsa masa sallamarsa tare da fadin”ina hini?
Ya jiki?.

Sai da amsard yayi murmushi sannan yace”lafiya jiki kuma dasauki”.

Fayal tace”toh sannu
Amsard yace”yauwa ashe hjy momynace tafadamiki bnda lafiya ni sai ynzu ma dauko wayar shine naga kiranki”.

Fayal tace”hmm eh”.

Amsard yace” yanaji kema kaman baki da lafiya?.

Fayal tace”eh wallahi dan zazzabi nake”.

Amsard yace”ayya ashe dukanmu daya ne to Allah dai yabamu lafiya”.

Fayal tace”Ameeen”.

Sannan sukayi sallamah cikin nutsuwa tare da farinciki.

suna gama wayar nan fayal taji kamar ba ita ke rashin lafiya ba gaba daya ta ware walwalarta ta dawo .

 

Ba shiri ta dauko book dinta tacigaba da karantawa.

Sukansu su momy sai da sukayi mamakin warware wartah.

Amsard suna gama waya da fayal ya kira usman awaya.

Duk da sunyi waya da ranA amman hakan bai sa sun fasa ta dare ba sai Da sukayi kamar yadda suka saba.

 

washe gari

 

Jikin amsard dana fayal yakara sauki sose.

Misalin karfe 2 na ranah usaman yakira amsard awaya.

Amsard nagani yadauka cikin farnciki tare da masa sallamah.

Usman ya amsa sallahma .

Bayan sun gesa usman yke cewa”ya dramar nan neh anya tana tafiya daidai kuwa?

Amsard yace”hmm kedai kabari kawai ashe mu mun mata mummanan kallo ne ba haka take ba yarinyr tana da saukin kai fa” .

Usman yace”ba wani nan kawai kai dai ka fada tarko neh”.

Amsard yasa dariya tare dacewa”Allah magNar gaskiya nke fadama kuma maganar tarko kam nafada daman inaso nakiraka musan nayi”.

Usman yace”Alhmdlh wallahi naji matukar dadi to yanzu ka fada mata neh?.

Amsard yace”a’a wallahi ni tsoro nkeji”.

Usman yace”haba dai saikace ba namiji ba haba mutumina karka badamu mana”.

Amsard yace”hmm bazaka gane band”.

Sai da usman yatabbatar da amsard ya gamsu zai yi abin da yace sannan yasamu sukuni.

Dazasuyi sallamah amsard yama usman alkawarin insha Allah zai mata magana yau da dare.

*PAGE* 41,42.
————————————————————————-

Bayan Amsard yagama waya da usman

Gaba daya amsard yakasa sukuni sai tunanin yadda zai bullowa fayal yake.

Wani lokacin yace yafasa
Sai yaga kuma baza iya hakan bA.

Sai sakye skye yake azuciyarsa.

Fayal kuwa taNa kammala akin ta tadauko wannan littafin tacigaba da karantawa.

Labari ne na soyayya acikin wannan littafi
Soyayyace Me danko wace takusa zuwa dai dai data su fayal.
Hakan yasa fayal take jin dadin labarin domin atunanin ta indai son amsard ne yakamata toh wannan littafin zai taimaka mata wajen gudanar da soyayyarta ita da amsard.

Tunda dai ita batasan yaso yakeba
Hasalima bata daukesa wani abu arayuwaba.

toh amman yanzu Allah yadaura mata ya zatayi?.

 

Bayan an idar da sallar isha misalin karfe 8 daidai.
Amsard yana kwance akan gadonsa

Hakama fayal.

Amsard ne yadauko wayarsa domin kiran fayal.
Ya rike wayar ahannunsa kusan minti biyar yakasa kira duk yana kara nazari akan abin da zai fadamata.

Daurewa kawai yayi ya danne sunan princess dayake dasunan yayi saving din number fayal.

 

Fayal tana zaune sai tunanin amsard yake domin taga lokacin kiransa yayi amman shiru .

Aiko itama sai taga sunan prince nakiranta alokacin.

 

Abin mamakin anan kuma abin tambAyar shine;
Taya akayi fayal da amsard sukayi saving din suna iri daya?.

Toh gaskiyar dai itace ba wanda yasan wani yayi saving da princess ko prince kawai tsabar *Babu ruwan so* neh yasa hakan .

Fayal tadaga wayar da saurinta tare da yi massa sallama da zakakkar muryarta wadda akullum ita ke kara rikita Amsard.

Sai da yace”Masha Allah azuciyarsa
Sannan ya amsa sallamr cikin nutsuwa”.

Fayal ta tsinci kanta da cewa”ina hini?

Amsard yace”lafiya .
An hini lafiya yan mata?.

SAi da fayal taji wani shokin sannnan tace”lafiya lau yayanah”.

Awannan lokacin shikanshi Amsard sai da yaji shokin sannan yace”har nasamu wannan mukamin ne haka?.

 

Fayal tace”hmm ai harma yafi haka”.

Amsard yace”aiko naji dadi kuma nagode”.

Fayal tace”ur ar wlcm”.

Amsard yace”hmm dama magana nakeso muyi yau”.

Fayal tace”owk toh inaji”.

Amsard yace”dama,dama,damah”.

Fayal sai farinciki take domin atunaninta zaice yanasonta neh

Dan haka tayi karfin gwiwar cewa”hmm inaji”.

Amsard yace”daman ina…..

*PAGE* 43
———————————————————————–
Amsard yAce”daman so nake nafada miki gobe Dan zo jigawane”,

Fayal taji wani farinciki ya maimaye zuciyarta hakan yasa takasa hakuri sai da tace “Amman dai zakazo gidanmu ko”.

Amsard yace”hAba dai ninasa Nazo banga kanwata ba”.

Fayal tace”yauwa yayana har naji dadi wallahi ai nazata ko gidanmu bazaka leko bane”.

A haka su fayal sukasha hirarsu har tayauma tafi ta kullum sukansu mamakin hakan suke.

Suna gama wayar nan amsard yakasa barci sai tunanin karyar da yama fayal yake yanzu fa yazama dole yaje jigawa gobe.

Daga karshe ya yanke shawarar zaije goben *INSHA ALLAH*
Kafin yakwanta sai da yakira usman yasanar masa yadda suka kaya da fayal .

Usman yaji dadin jin hakan Dan haka shima yakara masa gwarin gwiwa akan yazo kawai.

Abangaren fayal ma takasa barci sai murna take da tunanin wani irin tarba zatawa amsard.

A haka har barci yakwasheta.

 

*washe gari*

Amsard yana tashi da asuba bayan yayi sallah yayi wanka tukun yaje yasanarwa momy akan yau zaije jigawa.

Momy tamasa addu”a sannan sukayi sallama yakira alhajima yasanar masa domin alhaji baya gari.

Misalin karfe 8 daidai Amsard yadau hanya.

Abangaren fayal ma kuwa tun da ta tashi da asuba batakoma ba .
Tarasa INA zatasa kanta Dan farinciki hakan yasa tayanke hukunci fadawa amnah yau zasuyi bako.

Amnah tayi matukar mamakin jin wannan zanchan abaki fayal hakan yasa tayi saurin sanarwa da momy .
Momy mah tayi mamaki matuka Amman farincikinta yafi mamakinta yaw a.

Hakan yasa tasa akiramata fayal domin Susan yadda zasu tarbi bakon nasu dakyau.

Batare da bata lokaciba fayal da amnah suka shiga kichin domin daurawa bako abinci.

 

Misalin karfe 12 amsard ya isa jigawa yana isa ba Inda ya nufa sai gidansu usman .

Usman da Ameena sunyi matukar farincikin ganin amsard.

Anmasa tarba me kyau
Sai dai baici abincin sose ba.

Hakan yasa Ameena race”wato ni baza aci abinci na soseba ko?
Sabida ynzu an min kawa toh shikenan Nima sai narama”.

Usman da amsard suka shekye da dariya sannan amsard have”da kin ishemu akan anki miki kawa ynzu kuma anmiki Amman kin ishe mutane da surutu”.

Usman yace”kwaji dashi dai kanku akeji keda yay an naki.

Ameenah tace” aiko ba aji kanmu ba tunda munkusa samun amaryar”.

Amsard dai dariya yake abinsa.

***************************
Tun safe sai yanzu su fayal suka kammala girki.
Hakan yasa taje tayi wanka sannan tayi sallah tadauko wata rigarta wadda momy tasiyomata daga dubai pink Colo CE da adon farin bit da ston ajiki sai gyalenta fari shikuma me adon pink ga takalminta fari shima dai adon pink ne ajiki.

Batare da bata lokaciba tasa kayan ta bazan iya misalta muku kyaun datayi ba domin kayan kamar dan ita akayi sa yamata dam ajiki .

Batayi wata kwaliyaba illa hoda da man baki datasa Amman hakan bai hana fito da kyahun data kara ba.

Tadauko turarenta ta fesa sai tashin kamshi take wadda inbawai kasantaba zaka zeta sabuwar amaryace.

Tana zaune Kennan tagama kome amnah tashigo tare da fadin woow my soul kinga Kyan dakikayi kuwa wannan ai sai ki zaburar da bakon.

Fayal dai murmushi take domin ita kanta tasan tayi kyau.

 

*************************
Usman yace”kaga mallam tashi muje muyi sallah sai mu huce gidansu amaryar tamu.
Inmuka biye ta amena sai mukai LA”asar anan.”.

Ameenah race”aa gwara kutafi nikam nasan kawata NATA zuba I do.

Sai dusu amsard sukayi sallah sannan suka dau hanyar gidansu fayal

Dashike daman jiyan fayal ta turamasa address din.

Batare da bata lokaciba suka isa .
Amsard yakira fayal yasanar mata sannan suka Shiga da motar ciki.

Amnah CE tafito domin shiga dasu ciki ananne taga abin mamaki wato amsard.

Haka tadaure tamayar da mamakinta tamusu iso izuwa falo.

Suna Shiga taje takawo musu girkin da akamusu.

Sannan suka gesa takoma ciki.

Usman yace”toh sarauniyar sai taja mana ajine kafin tafito.

Bai rufe bakinsaba sukaji anyi sallamah

*PAGE* 44.

————————————————————————
Fayal ce tashigo da sallamarta.

Usman ne ya amsa domin amsard mah yatafi da kallon fayal sai da usman yadan tabashi sannan yayi saurin cewa”wa’alaiki salam”.

Fayal tace”ina hininku?
Ya hanya?

Amsard yace”lafiya lau hanya alhmdlh ya muka sameku?

Usman yace”kai oga adai bari nima mugaisa ko nifitama zanyi sai kuta hirarku”.

Fayal tace”hmm haba dai dan kawai mundan gesa to kaima ai gesuwarka ta dabnce dan haka ina hini y hanya ?

Usman yayi murmushi sannan yace”lafiyalau kuma ga saukon gesuwa kafin nafita daga hajiyata wai tna gesheki”.

Fayal tace”aiko nagode kuma ina amsawa”.

Amsard yace”to baban surutu ansamu waje”.

Usman yayi dariya sannan yace”hmm nikaga ma tafiya inkun gama nazo muyi sallamah”.

Ai amsard yanajin cewar usman zai fita yarike yatashi tare da fadin ai wallahi ka tsaya ko muje tare” .

Usman yasa dariya tare da cewa”kai dai kam ko ?

Yacewa fayal bari nadan me magana yanadan zuwa”.

Fayal ma dai gabanta faduwa yake ta kakulo murmushin dole tare da fadin toh.

Usman yaja amsard waje.

Amsard yace”wallahi ni tsoro fa nakji dan Allah ka tsaya kafada mata da kanka”.

Sai da usman yayi dariya iya sonsa sannan yace”haba abokina ai ba”a haka toh ma wai kana tsoronnata za ayi soyayya?.

Kaga ka cire kome azuciyar kayi abu kamar namiji ba mace ba yanzu inaso kakoma zaka iya insha Allah”.

Amsard har yatafi yadawo tare da fadin”toh me zance mata?

Usman yace”kai dai kaje baxaka rasa abin fadaba ni na fadama “.

Haka amsard yakoma jiki ba kwari yana zuwa yama fayal sallamah

Ta amsa cikin sakin fuska.

Amsard yace”yau wai saura kun wata nawane ku kammala skul?

Fayal tace”saura wata daya inga kome da kome”.

Amsard yace”owk”.

Dukansu sukayi shiru nakusan mintuna goma.

Amsard yaga shirun yamasa yauwa hakan yasa yace”kanwata”.

Jiki asanyaye Fayal tace”Na”am”.

Amsard yace”nazo miki da wata magana bansa ko yazata zo miki ba jikiji dadinta ko akasin haka duk bansan amsa ba.

Abinda nasani dayane yazamemin dole nafada ko dan samu sukuni azuciyata.

Amman kafin nan inAso na tambayeki
Abu daya itama sai kinyi hakuri domin bansan ko zakiji dadinta ba.

Amsard yaja numfashi sannan yace”shin anmiki miji agidane ko aa?

Fayal ta girgiza masa kai domin tunda yafara maganarnan kanta akasa yake takasa dagowa su hada ido.

Amsard yace”toh gaskiya bazan boyemiki ba naji dadin jin hakan.

Amman kuma ga wadda nake nema agareki.

Amsard yace”fayal
Yadanyi shiru sannan yakara dacewa”fayal inasonki”.

Sai da gaban fayal yAfadi.

Sannan yakara dacewa”so kuma na aure inkin amince”.

Fayal tayi shiru sai faman bugu da zuciyarta takeyi.

Amsard yace”amsar ki nAkeji jira
Fatan ban batamiki rai ba.

Fayal tace”…….

*PAGE* 45
———————————————————————–

Fayal tace”a’a ni baka batamin rai ba”.

Amsard yace”toh ina sauraranki”.

Fayal ta girgiza kai alamar ta amince tare da shiga cikin gida da gudu.

Amsard yayi murmushin farinciki tare da fadin Alhamdulillah Allah nagode maka.

Su momy da amnah nazaune sai ga fayal tashigo da gudu.

Momy ce tace”lafiyanki kuwa fayal?

Fayal ta sunkuyar da kai tare da ce”eh momy wai kije ku gesa zasu tafi”.

Tace”owk kice musu ina zuwa”.

Fayal ta shagwabe fuska tare da cewa momy nifa ba zan iya komawa ba cemin yayi wai fa………
Ko me ta tuna sai tafasa fada.

Amnah kuwa me zatayi banda dariya wayaga su fayal wai yau har anyi hira da saurayi kuma anajin kunyarsa.

Momy tace”oh toh Allah dai yakyauta amnah jekice musu ina zuwa”.

Amnah tace”toh momy da dariyarta ta tafi.

Shiko amsard yakira usman yashigo suna zaune akan fayal zata dawo suyi sallamah.
Sai ga sallamar amnah nan tashigo.

Suka amsa mata cikin sakin fuska sannan tace”musu momyn tana zuwa “.

Usman yace”owk fayal dinfa?

Amnah tace”tana ciki”.

Usman yace”toh bara nabaki sako ki bata”.
Usman yadauko wannan turaren da suka siyo ya mikawa amnah.

Amnah takarba dai dai da shigowar momy.

Alokacin Amsard yakara wata karamar rikicewar sabida ganin momy da yayi.

Tuni ya durkusa kasa yakasa dago kansa .

Shiko usman abin dariya ma yabasa amman haka yadaure shima yadurkusa ya geshe da momy ta amsa.

Sannan amsard ma yagesheta ciki ciki waishi adole kunya yakeji.

Ita kanta momyn dariya yabata amman haka ta daure ta amsa.

Sunyi gesuwar mutunci sannan sukayi sallamah amnah ce ta rakasu har mota tana tsokanar amsard akan shi kunya fayal kunya saga ya za ayi zamamnan.

Shidai amsard murmushi kawai yake.
Shi kuwa usman sai da da zigata yake.

Ahaka sukayi sallamah cikin nishadi.

 

Su na shiga mota usman yacigaba da dariya kamar fanfon dariya ba kakkautawa barin ma da amsard yace”me ai guduwa fayal tayi.

Aiko anan yabude sabon babin dariya.
Tun amsard nabiye masa har yafarajin haushi .

Hakan yasa usman yayi shiru tare da cewa”Allah ya huci zuciyar ango”.

Shidai amsard bai kulasa ba driving dinsa yake.

 

Chan Amsard yace”usman Dan Allah kafadawa Alhaji su zo suneman min aure”.

Usman yace”kai bazaka iya fadaba ai kai kakeso bani ba ehee”.

Amsard yace”please be seriouse ka taimakeni wallahi inaso ayi aurern nan da hurine kaga takusa kammala project dinta”.

 

Usman yace”oh ni yanzu wallahi kafara bani mamaki wanda bai da lokacin kansa ma bare na mace amman ynzu wai aure kakeso?

Amsard yace”eh din to haram neh”.

Usman yayi dariya sannan yace”halak neh”.

Amsard yace”to zakamin abinda nabukata ne ko aa?

Usman yAce”nina isaaa
Ai kamman anyi angana ango daman burin mu kenan”.

Amsard yace”kaji dashi dai muje nasauke ka agida na huce gida domin nace yau zan koma”.

Usman yace”owk”.

 

Suna isa usman yasauka.
Amsard yace”ageshe da ameenah”.

Usman yace”zataji sai munyi waya ko’.

Amsard yace”ok”.

Sukayi sallamah amsard yadau hanyar komawa katsina.

Abangaren fayal kuwa
Tunda tashiga daki takwanta sai farinciki take.

Tana ta tunani wai yau itace take soyayya kuma har tasan miye so .

Ikon Allah kennan.

Tana cikin tunanin nan amnah tashigo tare da fadin”watomah har turaren dakike sawa yasani shine yasiyomiki ko?

Fayal tace”haba dai aiko tana fada taga ashe *orchid of love* neh
Turaren da take sawa.

Azuciyarta tace”oh ya akayi yasan turarenah?.

Ohooo waye yasani
Sai kubiyoni domin sannin yadda yasan hakan.

Haka fayal ta hini cikin farinciki.
Haka shima amsard tuki yake cikin farinciki.

Sai misalin karfe tara ya isa katsina.

Adai dai lokacin kuwa fayal ta shirn kiransa awaya domin masa barka d gajiya.
_PAGE_ *46*

————————————————————————-

Fayal tadauko wayarta ta danna prince.

Shigar Amsard gida kenan yana geshe dasu momy sai ga kiran fayal yashigo.

Alokacin amsard yaga kira yayi murmushi sannan yacewa su momy” ina zuwa”.

Momy da alhaji kawai murmushi sukayi domin sunfara gano inda dan nasu yanufa kuma suna farinciki da hakan.

Amsard yashiga dakinsa sannan ya amsa tare da fadin”Amincin Allah yatabbata agareki ya kyakkayawa”.

FAyal tace”tare dakai wanda yafi fure kyau”.
Amsard yace”wo wane ni anan sahun?

Fayal tace”ke awanda yafi nan mah”.

Amsard yace”idan baku kenan ko?

Fayal tayi murmushi tukun tace”abar maganar kawai .
Ya ka isa gida lafiya?

Amsard yace”lafiyalau.

Fayal tace”ya gajiyar hanya?

Amsard yace”Alhamdulillah”.

Sannan yace”wato kika gudu ko amsa babu ko?

Fayal tace”hmm bazaka gane bane”.

Amsard yace”niko zangane indai anganar dani”.

Fayal tace”owk shikenan nakusa ganar dakai ai”.
Amsard yace”ke ko?
Kin cika wayo .

Fayal tace”aikai ka koyamin”.

Amsard yayi dariya
Sannan yace”toh abani amsa ta yanzu”.

Fayal tafara shagwaba “uhumm uhum uhumm nidai Aa ba yau ba”.

Sai da Amsard yaji jikinsa duk yamutu.

Sannan yace”uhumm uhumm nimah”.
Kuma shikenan sai kin amsa min maganata kafin mukara waya” .

Fayal tace”uhumm sory zan fada fa”.

Amsard yace”owk to inaji”.

Fayal tace”kasan miye?

Amsard yace”Aa”.

Tace “uhummm bakome to”.

Amsard yace”ai bazako ki fada din ba ko? Kodai bAkya sonane?.

Fayal tace”uhumm Aa fah”.

Amsard yace”toh fada inaji”.

Fayal tace”toh karufe fuskarka”.

Amsard yasheke da dariya sannan yace”au yanzu sai na rufe ido ? Toh kunyarwa kikeji?

 

Fayal tace”uhumm kai manah”.

Amsard yace”to inadai innarufe zaki fada?

Fayal tace”eh”.

Amsard yace”promise?

Fayal tace”yess ”

Amsard yace” owk toh na rufe” .

Fayal tace”yauwa”.

Amsard yace”kifada mana”.

Fayal tace”.
*PAGE* 47.

————————————————————————-
Fayal tace”na amince!”

Tana fadar hka kuwa takashe wayar wai ita adole kunya takeji.

Amsard yayi matukar farincikin jin hakan.

Hakan kuma yasashi kiran usman awaya.
Bayan sun gesa amsard yake cewa”ya maganar fadawa Alhajin ne?

Usman yace”oh mutumina ba hakuri toh yanzuma ina hanyar katsina ne domin nazo nasanarw da alhaji.
Nasa nabaka mamakine hakan yasa ban fada ba”.

Amsard yace”woow amman gaskiya ka kyauta kuma Naji dadi”.

Usman yace”toh nidai karka dameni sai na iso kawai”.

Amsard yace”a iso lafiyA”.

Sukayi sallamAh

Usman yashiga tunani wai yanzu har amsard ne yake iya damuwa akan mace!
Abinda da ko kallo basu ishesa bama!

Oh ikon Allah kennan
Gaskiya wanda baisan so ba bai iya farawa ahankali ba.

Da wannan tunanin usman yacigaba da driving.

 

Afannnin fayal kowa farincikinta kara karuwa yake sai murna take moy da dadyma sai farinciki suke barin dadyma yaji dadin jin labarin zuwan amsard.

Misalin karfe 1usman ya isa katsina ba inda yahuce illa gidansu amsard.

 

Usman yana isa cikin gida yashiga batare da bata lokaci ba.
Aiko yana shiga yaga su sameer n wasa dayake weekend ne kowa nagida .

Suna ganinsa sahala tashiga ciki da gudu tana hjy momy ga yah usman nan yazo.

Hjy momy tace”wo kice yau munyi babban bakwo agidan namu”.

Tafito shiko sameer tuni yayi dakin amsard yasanar dashi.

Atare amsard d momy suka fito palo.
Momy nafadin a lallai yau munyi bAbban bakwo”.

Shiko amsard sai washe baki yake.

Usman ya geshe da momy.
Ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayar ya iyalen?.

Usman ya amsa dacewa”suna lafiya”.

Hjy momy tace”toh sahala adaukowa yaya abinci ko?.
Sahala tace”owk momy.

Sahala taje tadibowa usman da amsard abinci atare sukaci.

Sai da suka gama sannan sukatafi massallaci sukayi sallah .

Bayan sun dawo neh usman kecewa “hjy momy ina Alhaji ne?

Momy tace”aiko ynzu yadawo daga sallah yana daki”.

Usman yace”toh bara naje mu gesa” .

Momy tace”toh abokin naka yaraka ka mana”.

Usman yace”toh suka tashi shida amsard.

Suka shiga dakin dady bayan sun gesa ne sai amsard yace”yana zuwa”.

Zai fita sai usman yace”ka dan cewa momy tazo zAmuyi magananeh”.

Amsard yace”,ok”.
Yana fita sai yakira momy sannan ya nufi dakinsa.

 

Momy na shiga usman yace”toh daman alhaji sanadiyar zuwana ba nakome bane illa muna neman alfarma da aje jigawa nemawa abokina aure”.

Hjy momy tayi saurin cewa”wani abokin naka?!

Usman yayi murmushi sannan yace”amsard”.

Alhaji da hjy momy atare sukace”Alhamdulillah”.

Alhaji yakara dacewa”gaskiya naji dadin jin wannan kalmar daga gareka dole nabaka tukwici”.

Hjy momy tace”kodai nina basa”.

Usman yayi murmushi sannan yace”alhaji zan turoma da number baban yarinyar sai asa ranar zuwa”
.

Alhaji yace”hakanma yayi”.

 

Sannan usman yace”bara naje muyi sallamma nakoma domin banson nayi dare”.

Alhaji yace”ah tsaya ga tukwicin ka motace wadda jiya aka kawomin daga dubai .

Bansan me zAnbaka ba ga key din ayi hakuri da wannan “.

Usman yakasa rufe baki anacikin hakan momy tace”niko kabani account no dinka zan turo maka da million daya”.

Usman yace”woo momy ‘alhaji bansan dame zan gode muku ba”.

Sukace bakome ai munsan kafi karfin hakan ma awajenmu.

Cikin farinciki sukayi sallama sannan yaje yasami amsard domin yin sallam
ah.

*PAGE* 48.

————————————————————————-
Yana zuwa yacewa”amsard toh mallam nidai nagama nawa sauranmu shan biki”.

Amsard yace”waa! Gaskiya ka kyautamin angon Ameenah amman dai su Alhaji sun ji dadin jin hakan ko?.

 

Usman yace”sosema kuwa ga alalominan ma hjy momy tamin kyautar kudi alhaji kuma mota”.

Amsard yace”woo mutumina natayaka murna Allah yasanya alkairy”.

Usman yace”Ameen sannan yakara dacewa yauwa katuromin address din gidan sai naturawa alhaji”.

Amsard yace”owk”.

Usman yace”toh ango nizan huce kasan mutuniyr sai ahankali itaga nakai cikin dare d matsala”.

Amsard yace”oh ni karkamin wani iyayi muma munkusa shiga daga ciki dai muhuta”.

Usman yace”oh kaji dashi dai nikam nayi nan”.

Sai d amsard yaraka usman yashiga motarsa sannan yadawo gida.

 

Amsard nashigo gida yatarar da hjy momy da alhaji afalo fuskarsu tacika da farinciki .

Yashigo da sallamarsa sannan yazauna akasa yakasa dago kai waishi adole kunya.

Hjy momy ce tafarada cewa”oh su amsard yanzu dai angirma anbar shirmen kin kula mata”

Alhaji yace”kedai kam kincika zolaya kyabarsa yahuta dai ko?.

Hjy momy tace”lallai kam tunda nakusa samun suruka”.

Alhaji yace”yauwa zanma alhaji babba magana anjima in usman yaturomin da adreess din sai ashirya tafiyar kuma kafada mata ta sanar da yan gidan za azo”

Amsard yace”toh tare da sosa kyeya kansa akasa”.

Ahaka ranar gidansu amsard yakasance cikin farinciki.

Dadddare lokacin wayar su amsard yayi.
Amsard baima kira fayal ba amman yanashirin kira kafin yakira har fayal tariga kira.

Amsard nagani yayi murmushi sannan yadasa akunnennsa tare da fadin amincin Allah yatabbata ga sarauniya “.

Fayal tace”tare sarkin sarakai.
Dafatan anhini lafiya”.
Amsard yace”lafiya lau dafatan itama sarauniyata tahini cikin lafiya tare da farinciki”.

Fayal tace”Alhamdulillah”.

 

Amsard yace”,yauwa kifadasu dady su alhaji zasuxo inaga nan da jibi”.

Fayal tace”mezasuyi?

Amsard yace”zasu rabamune”.

Fayal tace”haba dai?
Dan Allah?

Amsard yayi dariyar data ishesa sannan yace”matsoraciya to wasa nake ‘.

Fayal tace”toh mezasu zo yi”.

Amsard yace”nemamin auren sarauniyata”.

Duk da fayal tasan amsard ba kallonta yakeba amman sai data rufe fuska?domin kunya.

 

Sannan tace”uhumm har naji dadi”.

Amsard yace”yau fa saikincemin i love u inba hka ba bazanyi barci ba fah”.

Fayal tace”uhumm nifa kunya nkeji”.

Amsard yace”au daman in anajin kumyar har fada ake?.

Fayal tace”ehmana”.

Amsard yace”toh nidai yau saikin fada fa”.

Fayal tace”toh”.

Amsard yace”yauwa fada”.

Fayal tace”ni aa”.

Amsard yace”au bakyasonA kennan?

Fayal tace”a’a fa zan fada.
*PAGE* 49.

————————————————————————-
Amsard yace”,owk inaji”.
Fayal tace”,uhummm 1.
Uhumm 4.
Uhumm 3.

Amsard yace”,mekenan haka?

Fayal tace”abinda kakeso mana nafada kayi tunani zaka gane”.

Amsard yace”aa nidai kimin bayani”.

Fayal tace”toh 1 mean i.
4 mean love. 3 mean you.

Kaga in aka hada i love you kenan’.

Amsard yace”wooooooooow!
Nakasa rufe baki bansan yadda kalmar nan take da dadiba sai yau
Gaskiya naji dadi kuma nagode sarauniyata”.

Fayal tace”uhummm toh nima sai kafadamin”.
Amsard yace”toh ai nawa me sauki ne indai wannan kalmarce har sai kingaji daji dan haka
*I LOVE YOU I LOVE YOU I LOVE YOU*
Sai da yafada sau uku da karfi sannan fayal tace”wAyyo Allah kunnenah zai fasamin kunne jama’a akawo agaji”.

Amsard yasa dariya taredacewa”i love you baby princess”.

Fayal ma tayi dariya sannan tace”toh dai Allah yashiryamin kai”.

Amsard yace”Ameeeen matar”.

Fayal tace”au har nazama matar?
Amsard yace”eh mana ai har andaura asama saura nakasa”. Fayal tace”a lallai ne ango”.

Amsard yace”yauwa amaryar mukwana lafiya “.

Fayal tace”owk byeee
Misss you”.

Amsard yace”miss you too”.

Sukayi sallamah cikin nishadi da begen juna.

Fayal bata kwanta barci ba sai da tatashi amnah domin sanarmata abinda ke faruwa.

Fayal tace”amnah amnah amnah kitashi”.

Amnah tace”uhumm fayal menene?.

Fayal tace”tashi kizauna muyi magana”.
Amnah ta tashi tareda cewa”toh inaji”.

Fayal tace”wai afadawa su dady da momy yan uwan amsard dasuzo jibi”.

Amnah tace”woow harkinsa nadaina jin barci dagaske?

Fayal tace”ehmna dagaske nake miki”.

Amnah tace”gaskiya naji dadi da safe ni zan farawa momy albishir “.

Fayal tace”umm to mukwanta sai da safe “.

Amnah tace”owk byee amaryar mu”.

Fayal tace”kyaji dashi dai”.

Amnah ta yi murmushi sannan ta kwanta .

 

Abangaren amsard kuwa suna gama waya da fayal yaje yadauro alolah domin yin lafilah.

Ya roki Allah dayasa alkairy ne haduwarsa da aurensa da fayal.

Sai da ya idar yagabatar sa addu”o insa sannan yakwanta barcinsa.

Washe gari

*PAGE*50
——————————————————————————————————————————–
Washe gari tunda safe Alhaji ya fito ya kira hajiya momy yace ” Kishirya zamuje gidan Alhaji babba”.

Tace “to Alhaji” tashiga ciki ta kimtsa sannan ta fito suka fita.

Ashe duk abun nan da ake amsard yana jinsu yanata murna azuciyarsa. Suna fita shima ya fito falo ya zauna dan yakira fayal.
Kafin ya fito da wayarsa naji tana ringing yana fiddo ta yaga princess ce nan yaji wani sanyi aransa, ya daga tareda fadin.
” Aminci, karamci, halacci da mutunci sukara tabbata agareki ya saraunmiyar kyawawa” Saida fayal taji wani sanyi batasan lokacin data lumshe idoba.

Tace ” tareda kai habebe na. Fatan rabin raina ya tashi cikin koshin lfy ”

Amsard yace ” ina lfy kanwata daman yanzu nake shirin kiranki”

Fayal tace” ai naji hakan azuciyata shiyasa nace bari narigaka”

Amsard yace” gaskiyane Masoyiyata Ammanfa yau kin dan ban mamaki”

Fayal tace “uhum uhum yayana menayi uhum ”

Amsard yace” uhum uhum kalamanki sukaban mamaki ashe kanwar tawa gwanace a kalaman soyayya ”

Fayal tace ” uhum yayana ai soyayyarka ce tasani nazama haka domin banma san yanda akai naji ina furtasuba”

Amsard yace” Lallai kanwata kice naci gari? “.

Fayal tace “sosaima.”

Amsard yace ” gaskiya naji dadi babyna.”

Ahaka sukayi sallama zuciyar kowa cike da shaukin kaunar junansu.

A bangaren su Alhaji da hajiya momy kuwa. Sun isa gidan Alhaji babba. Sunkuwa yi sa’a Alhaji babba baifitaba. S Suna shiga Alhaji babba yataso da murna yace ” Alhaji kaine yau agudanmu ba ko waya Allah dai yasa lfy”

Alhaji yace ” wlh kuwa Alhaji ai abundake tace damu yafi qarfin waya”

Alhaji babba yace” to to zauna zauna Allah yasa lafiya”

Alhaji yace” wannan tafiyar ta dankace Alhaji. Nazone mu tattauna don danka amsard yasamu mata”

Alhaji babba yace ” Alhamdulillah kai amman gaskiya nayi murna sosai kace amsard angirma kai masha Allah ”

Alhaji yace ” to yanzu halinda ake cikima so nake muje neman auren nasa a jigawane, yaushe kake ganin yakamata muje”

Alhaji babba yace “ai ba abun jinkiri nan gobe goben nan zamuje insha Allah. Asanar dasu kawai”

Ahaka sukayi bankwana akan gobe insha Allah zasuje jigawa neman auren amsard.

A bangaren usman kuwa yana isa gida. Ya yi sallama Amina ta taso da gudu tatarbesa cikin murna tace “honey katafi kabarni inata zullumi fatan kadawo lfy.”

Usman yace ” lfy kalau uwargidana nazo miki da Albishir abokina ankusa angwabcewa. Kuma Dadynsa yabani sabuwar mota hajiya momy kuma tabani one million boron Albishir.”

Amina tace” kai Alhamdulillah gaskiya nima naji dadi matuqa kace su yaya amsard ankusa zama ango”.

A bangaren su fayal kuwa. Dasafe amnah tatashi tacewa momy “yau inada Albishir da zan baku keda Dady.”
Momy tace “Kaii harkinsa nafarajin dadi dagaji Alkhairi ne. To fadamin”

Amnah tace” noooo mommy sai mun je yin breakfast zakiji ”

Momy tace ” to shikenan ”

Bayan su momy da amnah sungama hada kayan breakfast. Momy takira Alhaji suzo an shirya breakfast.

Sun zo an zazzauna amman fayal bata fitoba dady yace “wai ina fayal dita? ” Amnah tace “tana daki.”
Dady yace” jeki kiramin ita tazo mu karya”

Amnah tace “to dady”

Amnah tatashi tanufi dakinsu tana zuwa tatarar da fayal sai dariya take tana wayarta da amsard.
Amnah ta kalleta tace” ohni su fayal har an zama yan gari a birnin love. Toki taso muje dady nakira muyi breakfast ”

Fayal tace ” to ganinan zuwa. ”
Tai sallama da amsard tatashi suka tafi. Suna shiga ta zauna inda tasaba zama akan dining set ta gaishe da dady da momy.

Suka amsa cikin farin ciki. Dady yace” ina kika shige ne ko barci ake? ”
Fayal tace”a a dady kawai ina zaunene. ” tafada tana kallan Amnah tana mata alamar tayi shiru karta tonata. Amnah tai shiru kawai tana murmushi.

Kusan mintuna 10 dafara cin abincisu sai amnah tace ” dady da momy albishirinku”.

Sukace” goro atare suna dariya”
fayal najin haka tai zunbur tamike ta ruga ciki tana rufe fuska domin tasan me Amnah zata fada. dukkansu suka fashe da dariya.

Amnah tace” dady zakuyi baqi gobe ”

Dady da mumy sukace” baki kuma Suwa zasu zo mana?”

Amnah tace “dady su Abban amsard ne zasu zo neman auren Fayal”
Dukkansu cikin farinciki sukace “Alhamdulillahi kaiii masha Allah. Allah yakawomu lokaci Kaii gaskiya munji dadi”

Momy tatashi dagudu tashiga ciki tana kiran fayal fayal zozo manaaa ‘yataaaaaaa.

*PAGE* 51

————————————————————————

Fayal tana shiga daki ta kwanta .
Momy nashigowa taga fayal akwance.
Momy tace”ah wai kwantawa kikayine aibakiga ta kwanciyaba tunda dai kinsan gobe muna da baki ko?.

Fayal ta girgiza kai alamar eh.

Momy tace”toh kuzo keda amnah kushiga kasuwa kusiyo duk abinda kukasan da”abukata domin bana son aikan auwalu shirme yamasa yawa”.

Fayal tace”toh momy”.

Sannan tashi tashiga toilet tayi wanka amnah ma tazo tayi.

Batare da bata lokaci dukanninsu suka shirya sannan suka nufi market domin cefane.

 

Sunyi cefane sose wanda ko wani gidan bikinma ba ayinsa.

Sai misalin karfe 4 suka dawo gida .

Suna shiga momy suka tarar ta kira momyn amnah suna magana akan zuwansu amsard.

Dagudu fayal takarasa gun momy tare dafadin”wayyo momyna mun gaji wallahi”.

Momy tacewa momyn amnah”kingama ka ya”yan naki sun dawo “.

Momyn amnah tace”toh ageshemin da amare kuma ahuta gajiya sai goben ko”.

Momy “tayi dariya sannan tace”owk amare dasuji eh sai goben kizo da huri fa”.

Momyn amnah tace”insha Allah”.

Anan sukayi sallamah

Momy ta kalle fayal da amnah tace”a lallai kungaji dan naga har wani baki kuka kara” .

Fayal tace”uhym ba amnah bace take ta siyan kayayyaki ” .

Amnah tace”ehdin ai hakanma bamu gama ba komawa zamuyi”

Fayal tayi dariya sannan tace”ai ynzu kam kinyi kadan yarinya”.

Momy tace”um ba surutu ba kutashi kuyi wanka sai kuyi sallah maza azo afara rage aiki”.

Amnah tace”owk momynmu”.

Dukansu sukatashi .

Kowa yayi wanka sannan sukayi sallah aka dukufa wajen aiki.

 

Abangaren amsard kuwa sai farinciki yake .
Hjy momy kuwa tasashi agaba sai tsokanarsa take shiko amsard baki ba abin magana ba sai dai yayi murmushi.

 

*washe gari*

Da huri su Alhaji babba suka shirya shida amininsa domin zuwa jigawa.

 

Fayal suna kichin sai aiki suke sai ga kiran prince yashigo ai tuni fayal tazura daki da gudu”

Momy tace”toh Allah dai yakyauta wataranma kuma agabanmu za ayi ko kunya ba aji ba tunda yanzu ma anfara yin wayar”.

Amnah tasa dariya sannan tace”momy kenan”.

Sunata aikinsu suna fira sai ga momyn amnah ma ta isa akacigaba da aiki.

Fayal tana zuwa daki ta amsa wayar tare da fadin”Assalam alaika”.

Amsard yace”wa’alaiki salam .

Fayal tace”good morning honey”.

Amsard yace”morning my princess.
Fatan ranar nan tamiki kyau kamar yadda fuskarki take”.

Fayal tace”da ikon Allah mijin kirki
Da fatan dake da”azo domin ina bukatar ganin kyakkayawar fuskar sarkinah”.

Amsard yace”uhumm bayan sunce baza azo dani ba uhumm ni kuka ma zanyi”.

Fayal tace”uhummm haba sarkina karkayi kuka kayi hakuri kaji kasan me kyau baya kuka”.

Amsard yace”uhummm ni a”a sai nayi fah’.

Fayal tace”uhummm uymmm toh muyi tare uhummmm uhummmmm”.

Amsard yace”wayyo rufamin asiri sarauniyata karkiyi kuka ai inwani ne ma yazubarmin da hawayenki sai na zubarme da idonma gaba daya”.

Fayal tace”toh promise bazakayi kukan ba”.

Amsard yace”i promised sarauniyata.

Fayal tace”tanx my sarki.

Alhaji yasa sahala takira amsard tazo tasami amsard nawaya tace”yaya alhaji yana kiranka”.

Amsard yamata alama da hannu da nufin yana zuwa.

Amsard yacewa”fayal byeee sarauniyata alhaji nakirana”.

Fayal tace”owk byeeee miss you take care”.

Amsard yana zuwa alhaji yacemasa gasu alhaji babbanan sun iso kazo kai zakayi musu jagora zuwa jigawan.

 

Amsard yaji dadin jin hankan sose amman haka yaboye azuciyarsa gudun kar ace yayi rashin abin.

 

Abangaren fayal kuwa suna gama waya taje kichin aiko ta tarar momyn amnah ta iso.

 

Momyn amnah tasa fayal agaba sai tsokanarta take.

Fayal kuwa takasa magana gashi amnah da momy sai dariya suke mata.

*PAGE* 52.

————————————————————————-

Amsard ne ke tuka su
Sunyi nisa atafiya sannan yashiha gidan mai domin kara me amotar alokacin ne yama usman text cewa”muna hanya fa dani akazo inmun kusa dan ma magana muhadu agidan su fayal din”.

Alokacin daya tura text dai dai da gama sa man da ake hakan yasa suka cigaba da tafiya su Alhaji babba kuwa sai hirarsu suke amota .
Insuka ma amsard magana sai dai yayi murmushi in nabada amsa ne sai yabAsu.

 

Su momy sun kammala kome hakan yasa sukaje suka kara wanka kowa yaci gaye sannan suka fara shirya abincin acikin flas da dish.

Adai dai wannan lokacin su amsard suka iso .
Usman ma ya iso domin amsard yakara masa text din.

 

Usman ne yafara shiga yasanar wa da dady sun iso dama shima dady yakira dadyn amnah suna xaune jira kawai su amsard su iso hakan yasa yace”a madallah kushigo mana “.

Su Alhaji babba suka shigo sunyi gesuwa ta mutunci sose da dady kamar sun san juna hakam ba karamin dadi yamusu ba .

Bayan sun gesa ne dady yasa akaturo amnah .
Amnah tana zuwa yace “yauwa damuyi maganene kikai shi bakwon nako dayan falon kwa gesa achan”.

Amnah tace”to tare da fadin muje to”.

Amsard da usman suka bita tashiga dasu falo.

Sannan ta koma ta sanarwa da momy akan akai musu abinci.

Amnah tace”momy fayal takai wani karamin falo ni dan kai na dady .

Momy tace”owk”.

Aka kira fayal takai abinci .

Fayal tace”uhumm momy nifa kunya nkeji”.

Momy tace”a basu sanki ba ma”.

Fayal tafara shagwaba aiko momyn amnah tace”maza dauka kikai amnah kema dau naki.

 

Ba musu dukansu suka dauka domin sun san halin momyn amnah atsaye take.

 

Abangaren su alhaji kuwa
Alhaji babba yanemawa amsard auren fayal kuma dadyn amnah yabasu tare tabbacin ba bata lokaci za ayi bikin.

Sunyi farinciki sose ana cikin hakane amnah takawo musu abinci suka fara ci cikin nishadi.

 

 

Fayal tana zuwa kawai taga abin mamaki wai amsard ne zau ne dan ita ko ganin usman m batayi ba.

Ta sake baki kawai tana kallonsu.

Amsard sai murmushi yake mata.
Usman yace”yadai amaryar mu ki karaso mana.”.

Sai alokacin fayal tagane ashe ba amsard vane kadai.

 

Tayi murmushi tare da ajiye basket din abincin.

Sannan tazauna tana fadin”sannun ku dazuwa”.
Usman yace”yauwa amaryar mu”.

Fayal ta ce”ina hininku”.
Amsard yayi sauryn cewa lafiya lau” .
Usman yace”kai mallam adai bary na amsa ko?

Amsard yace”aa barni mallam gwara na amsa abina”.

Fayal tace”uhumm wato da kacemin barakazo ba ko?.

Amsard yayi murmushi sannnan yace”,ai surprise nakeso namiki neh”.

 

Fayal tace”ysssn zakayi bayani amman dai ga abinci kufara ci”.

Fayal ta zuba musu abincin tare da musu bismillah.

Usman yace”toh nidai akwoshe nake uwargida tacikamin ciki da abinci.

Fayal tace”haba dai kaci mana banda fulako fah’.

Usman yayi dariya sannan yace”ai kigodewa Allah akwoshe nake da sai nacinye abincin nan duka.

Fayal tayi dariys tare da fadin lallai kam.

Amsard yace”uhumm nito kizo muci “.

Fayal tace aa nifa nakwoshi.

Amsard yace”,uhummm uhummm ni wallahi sai kinzo danci”.

Fayal tace”uhymm ni aa kaci”.

 

Usman yabude baki tare da fadin”laaaaaa agaban nawa?
Toh bara nabarku .

 

 

Amsard da fayal suka sheke da dariya atare .
Domin sun sunmanta ma dashi awajen.

 

Niko nace kwaga masoyan asa….

 

Amsard yace”au mallam daman kana nan nsh”

Usman yace”ai baka tuna dani ba kam.

Ahaka sukata zolayar juna har sukaci abincin.

Su alhaji sun tsayar da auren nan da karshen wata .

 

Sukayi sallama tare dasaawa akira musu amsard da usman dasu koma gida.

Fayal tunda taji maganar tafiya tafara shagwaba akan amsard ba zai tafi ba.

Usman yace”yoooo kwana nawane?
Ai munkusa hutawa da wamnan shagwabar”.

Dakyar amsard yalallaba fayal ta hakura.

*oh su fayal anzama yar love*

Suka rabu cikin farinciki da begen juna.

*PAGE* 53.

————————————————————————

Su amsard suka kama hanyar komawa jigawa.

Ita kuwa fayal tana komawa momy amnah tasa ta agaba tana da anki zuwa amma tunda akaje aka hango ango an labe.

Fayal takasa zama dan kunya.

 

Ahaka rayuwarsu fayal da amsard takasance arana sai suyi waya sau goma ko fima .

 

Yau yakasance saura kwana biyu biki.
Dan haka gobe sa lalle kuma za ayi kamu.

Amsard tuni ya iso jigawa gidan usman ita kuwa AmeenAh tuni takoma gidan su fayal domin shirye shirye da hike fayal bata da wasu kawaye Ameenah da Amnah ne sai kuma kawayen amnah na skul da suka gaiyata.

 

 

Washe gari
Anata chukuchukun biki
Lokacin tafiya kamu yayi.
Fayal tasaka jan doguwar riga tare da golden din rosil da takalmi tare da pos dinta.

Sukuwa kawayen amarya golden din kaya suka da jan dan kwali.

Amsard ma jan kaya yasa tare da golden din takalmi da hula.

Abokanansama golden din kaya sukasa

Agaskiya abin nasu yatsaru ba sai nabata lokaci wajen muku bayani ba.

Anfara kamu lafiya sannan akasa fayal a lalle tare da amsard .

Ankira amsard da fayal suyi rawa fayal ta kame kam
Shiko amsard yabawa mutane mamaki.
Yadunga tikar rawa sai vedio akemasa wasu kuma na masa manni.

Ahaka aka kammala cikin farinciki.

 

Washe gari yakasance daurin aure dan haka dun bun mutane sun sheda aure fayal da amsard.

 

************

Rayuwa suke cikin farin ciki da zaman lafiya tare da annashuwa.
Kowa yana kyautatawa juna akullum suna gundun bacin ran junan su .

Anacikin haka fayal tasamu ciki.
Tasamu kulawa agurin amsard kamar yadawo da cikin jikinsa yake.

Ita kuwa fayal ansamu damar shagwaba sai wadda ta karu.

Anacikin haka fayal ta haihu lafiya tasamu yarta mace.

Wace akasamata sunan hjy momyn amsard
Ana kiranta da *ASHNAH*

 

*ALHAMDULILA NAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI TAKEN ‘BABU RUWAN SO’ BANSAN IYA YAWON GODIYA DA ZAN NUNAMA D’UNBIN MASOYANA BA, NAGODE KWARAI DASO DA KAUNAR DA KUKA NUNA MA LITTAFINAN, ALLAH YABARMU TARE……..**THANKS ALOT ALL MY FANS…..LOVE YOU SOOOOO MUCH*?*Godiya ta musamman ga duk ‘yan group d’ina, dakuma ‘yan uwana writers nagode sosai Allah yasaka da alkairi da zumunci da san da kuka nunamin.*_*Jinjina Gareku ‘ yan Zamani Writer’s Association nagode kwarai Allah ya kara d’aukaka*_My fans sai kunjini a sabon novel d’ina nan gaba me taken *KUCHAKAR KISHIYA*

*Ur”s preety xayeesherth*?

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

KHAIREEYAH CHAPTER 13

Advertisements _____ Bayan tayi addu’a ta kwanta, wayar tane yafara ringing, wata number tagani wanda …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *