[Advertisements⬇️]

AMARYAR ZAMANI CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMARYAR ZAMANI CHAPTER 4

 

”””””””””””””””””✍️✍️bayan sun gama wayar ne ta tashi ta shiga toilet, pant ta chanja ta fito kwanciya tayi ba’aɗau lokaci sosai ba bacci ya yi awon gaba da ita,sai da Meernal ta dawo tukunna ta tashe ta lokacin shidda ta wuce,bayi ta shiga tayi wanka,ta fito parlor tana fitowa ta tarar da Umma har ta gama hada ɗilkar da zata mata.

 

“ke Khadija (Miemie)zo ki zauna nasa miki wannan dilkar kinga kina chen kina shegen baccin nan har lokaci ya kure”,zuwa tayi ta zauna akan wani cushin dake gaban Umma ta zauna,ɗilkar ta fara samata,mai haɗe da turare,sai da aka gama tukunnan,ta bata wani hadin madarar shanu da kuma haɗin ci-ciɓi da zafin shi,saida ta gama ci tsaf,ta tashi bayan awa biyu,Umma ta shigo dauke da wani dan bokiti,da yake cike taf da madarar shanu,mai dan zafi-zafi,tana shigowa suka nufi toilet ,da madarar aka wanke ɗilkar ai tuni ta ɗauki walali da ƙye-ƙyeli,cikinta ya yi wani irin smooth ga santsi kamar jikin tarwaɗa,sosai take daukar ido.

 

“wowwwww,Amaryar Yaya kinga kyau da kika kara”,walaiiii ta karayi da jiki tana juyawa,sannan tace.

 

“dama ai chen ni mai kyau ce”,ta fada tana hawa kan daddumar da ke shinfiɗe gefe,Sallar magarib da isha tayi tana gamawa,ta shirya cikin kayan baccin ta masu daukar ido,kan bed din ta haye ta ja blanket,Umma ce ta shigo hannun ta dauƙe da sauran,ci-ciɓin da ta rage da tsumi a hannunta,sai kuma haɗin ƴan shila sai turiri suke da alama yanzu ta sauke su daga kan wuta,Miemie najin shigowar ta kara shigewa cikin bargon,domin bata sha’awar kara cin komai.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 

“ai nasan ba bacci kike ba dan haka tashi,dan a iya fitata bai isa ace kinyi bacci ba”,munshari ta farayi irin na wanda yaji dadin baccin nan.

 

“Meernal dauko min bulalar nan ta daddyn ku”,da sauri ta tashi ta zauna tana fik-fik da idanu,dariya ce ta kufcewa Umma ganin  yanda take zazzare idanu,mika mata kayan hannunta tayi tace.

 

“plat da cup kawai nakeson gani kuma kiyi sauri kar ya huce”,tsumin ta fara kurɓe jin zaki kamar amsa zuwa ne yasa ta ƙafa kai bata sauke cup dinba sai da ta shanye tas,sai da tagama cinye komai tukunna Umma ta dawo hannun ta ɗauke da wata ƴar karamar roba,mai dauke da haɗin zuma da kwakwa da riɗi da wasu magunguna aciki,sosai haɗin ya yi kyau a ido,da sauri Miemie ta karasa guri Umma ganin kamar kayan kwadayi ne,mika mata Umma tayi,bata jira mai zata ce ba,ta buɗe ta na murmushi,lakata tayi tasa a baki,da sauri ta furzo dashi daga bakinta,jin wani ɗaci daya gwaraye bakinta gaba daya,Umma kauda fuskar ta tayi sannan ta saki murmushi mai dan haɗe da dariya,tana cewa cikin ranta,bake uwar kwadayi ba aiko zaki ci gidan ku kuma sai kin shanye shi duka.

 

“a’a ya kika furzar kuɗi fa nasa na siya ya kikemin asara ,maza cigaba da lasa,har sai kin shanye shi”,ido ta zazzaro tana cewa.

 

“Wallahi Umma ɗaci,kuma yana da yawa”,ta karasa faɗa da hawaye a idonta.

 

“sai fa kinshanye shi kima bar ɓata hawayenki,dan bazanyi asarar kuɗina ba”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]