[Advertisements⬇️]

AMARYAR ZAMANI CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMARYAR ZAMANI CHAPTER 2

 

✍️✍️Hannun shi ta kama tana dan wasa dashi a hankali a hankali,kallon ta ya yi da rinnanu idanunshi,hada ido sukayi,alama ya yi mata da taɗai na,murmushi tayi,  a haka har suka gama rabon,i.v d’in .

 

“Sweetheart a fara kai su A.A gida, ni gidan Umma Maryam zaka kaini”,ta fad’a tana kallon fuskarshi,bayan sun sauke su A.A ya juya da motar dan kaita gidan Umma Maryam ɗin, ƴar ya tsarshi babba tasa cikin bakin ta fara tsotsa,wani irin taka birki kake ji,ƙuuuuuuuuuu,wani irin fisgota ya yi kan cinyar shi ya fara kissing d’inta,a zafafe,martani tashiga mai da masa,oooooh ni wannan lamari Allah ƙyauta ,AMAREN ZAMANI sai a hankali zalamar su tayi yawa,wai fa tunkafin auren kenan wannan in akayi  auren sai dai su haɗiye juna,sai da suka gaji dan kansu sannan suka saki juna,kan kujera tana mai da numfashi,shima numfashin yake mai dawa a hankali,kallonta ya yi ya ga yarda ta rufe idon ta tana mai da numfashi,dariya ce ta ƙwace mishi yace,”yadai AMARYAR ZAMANI,wai har kin gaji ne kike mai da wannan Uban numfashin kamar warda tayi gudun fanfalaƙi”,cewar Abdul yana maida kansa ga tuƙin da ya fara.

 

 

“hmmmmm a ba gajiya nayi ba kawai dai na barka ne ka sarara,ko a ci gaba ne”,ta fad’a tana kashe mishi idon daya,sai kace wata tsohuwar kilaki na fada cikin raina,kallon ta ya yi ciƙe da mamakin maganar da ta faɗa,kwata_kwata bai yi tsammanin wannan maganar zata fito daga bakin Miemien ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 

“aaaaaa lalle Yarinyar nan wuyan ki iya isa yanka,duk ranar da na kama ki zaki gane baki da wayau”,dariya kawai tayi tana ayyana wani abu ayya na wani abu a ranta,haka suka cigaba da firar event din da za’ayi a bikin,bayan su isane bai ɓata wani lokaci sosai ba ya tafi,cikin gidan ta nufa tana cewa.

 

“Ummana kina ina gani na karaso”,da sauri Meerlas Ƴar Umma wadda ba za ta wuce sa’ar Miemien ba ta fito taba cewa.

 

“Amarya kinsha mai sai yanzu kike zuwa?”,kallonta Miemie tayi da murmushi tace.

 

“eh Wallahi sai yanzu ,rabon i.v muka je duk na gaji,yawwa jiya ba nace kizo muje ba mai yasa bakizo ba”,ta faɗa taba ƙwaɓe fuska zatayi kuka.dariya Meerlas tayi tace,”oooh yau ni na haɗu da AMARYAR ZAMANI,ke yanzu wannan ƴar maganar ce zata sa ki kuka,lalle Yaya Abdoul ya bani da shagwaɓa”,ta faɗa tana kara ƙyalƙyalewa da dariya,binta Miemie tayi da gudu ,zagaya parlorn suka ringayi,Meerlas nayi mata dariya,Umma ce ta jiyo hayaniyar su ta fito,da sauri ta riƙo hannun Miemie tana cewa.

“ƙyeleta ki zo muje na yi miki farfesun kaza mai daɗi kuma karki sake ki b….

 

 

muje zuwa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]