[Advertisements⬇️]

THE GOVERNOR'S WIFE HAUSA NOVEL - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

*THE GOVERNOR’S WIFE*

…… MATAR GWAMNA….

*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
https://www.wattpad.com/Azi_zat?utm_source

 

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

Book one

 

*Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani iko da kuma damar fara rubuta wannan labari. Ina addu’ar Allah ya sa yadda na fara lafiya na ƙare shi lafiya. Amin*

*wannan labari zai zo daga kashi na ɗaya zuwa kashi na uku Insha Allah. Na ɗaya zai zo a kyauta yayinda kashi na biyu da na uku zai zo na kuɗi. Zuwa gaba kaɗan zan sanar da farashin da za a same shi*

*wannan labari ƙirƙirarre ne, idan yayi kamaceceniya ta wani fanni da rayuwar wani, wata ko wassu to bisa kuskure ne, ba ayi dan cin zarafin kowa ba*

01

(CONGO STATE is a fictional state in Nigeria. Jahar Congo ƙirƙirrerren Jaha ce a Nigeria)

*MAFARI*

Da ƙyar kyakykyawar matashiyar budurwa da ke riƙe da hannun Mahaifiyarta ke jan numfashi da dogon hancinta da ya zauna ɗas a tsakiyar fiskarta wanda ya ƙara ƙawata ma ta fiskar sosai. Iskar asibitin wanda ke gauraye da warin magunguna, allurai, jini, fitsari da sauran su shi ya ke yiwa mutum iso a duk lokacin da ya kusancin farfajiyar asibitin. Ansan Asibitoci da wari amma wannan warin na sa ya fita daban. Ko dan Asibitin ta gwamnati ce, oho. Rabonta da zuwa General Hospital Congo tun wani ciwo da Abba yai kusan shekaru biyar da su ka wuce.

Ba su jima da zama a wajen reception ba wata mata mai ɗauke da jaririya ta fito daga office ɗin Likita ta ce ” wai Zainabu Inusa ta shiga”

Budurwar nan ta kama hannun mahaifiyarta su ka shige ofishin Likitan.

Lokacin da su ka shigo Likitan yana ta cike-cike a file ɗin su. Ba tareda ya ɗago ba ya ce “Malama Zainabu mi ya ke damunki?”

“Ciwon ciki”

Da sauri Likitan ya ɗago fiskarsa saboda yadda muryan budurwar ya shige shi, bama wannan ba, a file ɗinsu an rubuta Zainabu Inusa matar aure ce mai shekaru talatin da takwas wannan budurwa kuwa da ƙyar idan ta haura shekaru ashirin da ɗaya.
Lokacin da ya haɗa ido da budurwar sai da numfashin sa ya tsaya na ɗan wasu sakanni. Muryar da fiskar ba baƙon sa ba ne amma wannan ne karo na farko da ya ke ganin ta gaba da gaba.

“Mu ne wanda Dr Ubaydullah Gidaɗo ya turo” ta faɗa da siririyan muryarta me ratsa zuciyar mazaje.

“Masha Allah! ke ce ƙanwar mu kenan. ya jikin Umma?”

Sai da ta yi murmushi kafin ta amsa mi shi da cewa jikin Umma da sauƙi.
Duban Umma Dr Hassan yai ya ce “Umma tun yaushe kika fara jin ciwon cikin?”
Ido kawai Umman ta bishi da shi har ya gama maganar sannan ta maida dubanta ga ‘yarta wacce ta fara ma ta bayani da yaren kurame. Dr Hassan ya sake baki yana kallon ikon Allah, sai yanzu ya gane dalilinta na iya sign language na kurame dan watarana a wani rahoto da ta naɗa ta yi amfani da shi wajen yiwa wani kurma tambayoyi. Abin ya burge mutane da dama amma yanzu da ya ke ganinta tana yiwa mahaifiyarta tafintan (interpreting) duk abinda ya ke faɗa sai tausayinta ya kama shi. Bayan ya gama sauraron bayanen ta ya ma ta tambayoyi sai ya rubuta mu su takardar scanning ya ce su je su yi su kawo ma sa ya gani.

Ba su suka bar Asibitin ba tun takwas saura minti biyar da su ka shigo har sai ƙarfe shaɗaya da minti biyu.
Lokacin da su ka fito daga Asibitin Keke daban-daban su ka hau saboda sauri da budurwar ke yi dan ta je wajen aiki yayinda Ummanta ta wuce gida.

Da gudu-gudu sauri-sauri ta shigo cikin ma’aikatar ta su, kai tsaye studio na biyu ta wuce domin yau ne za ta fara gabatar da sabon shiri da za a fara a tashar su. Ƙarfe shaɗaya da rabi saura minti huɗu ta gani lokacin da ta duba agogon hannun ta. Ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe studio ta shiga.

Zaro ido waje ta yi ganin wanda ke zaune akan kujera tareda baƙon su na mako.

Gefen C Y ta tsaya wanda ke ta faman saita Camera dan fara ɗaukan shirin.

“C Y mi yake faruwa? ya na ga Iklimah a nan”

“Sorry Sweery, Oga ya chanja ki”

“Amma…”

“We are going live in one, two, three” C Y ya faɗa yana ɗagawa Iklimah hannu.

Iklimah ta yi wani fari da ido ta fara bayani kamar haka: ma su kallon mu kuna tareda gidan Talibijin na HILL TV, inda a dai-dai wannan lokaci mu ke gabatar mu ku da sabon shiri mai suna BAƘON MU wanda ni Iklimah Jibril zan gabatar. To a yau dai mun taho mu ku da babban baƙo. Jajirtaccen Ɗan kasuwa wanda duniya ta ke damawa da shi. Baƙon na mu dai shine Alhaji Isa Madara…

Juyawa ta yi cike da ɓacin rai ta bar cikin studio ɗin. Wannan wani irin walaƙanci ne Oga ya ma ta haka.
Kai tsaye ta wuce sama inda office ɗin Ogan su ya ke.

Gaisawa ta yi da Sakatariyar sa wata mata wacce za ta iya kaiwa shekaru Arba’in zuwa Arba’in da biyar.

“Madam Deborah Oga na nan?”

“Yana ciki” ta amsa tana cigaba da latsa na’urar computer da ke gaban ta.

Wucewa ta yi ciki zuciyar ta cike da jin haushin Ogan na su.
Office ne da ya fi kowanne girma a cikin kamfanin. Mamallakin office ɗin na zaune kan kujera yana duba wa su takardu.
A ɗan ƙaramin katako da aka ajiye a tsakiyar table da ke gaban sa an rubuta *MD Adamu Ribaɗo*

“Ina kwana Sir”

“Lafiya”

“Sir na ga Iklimah ta karɓi shirin BAƘON MU”

“Eh” ya faɗa ba tareda ya ɗago ya kalleta ba.

“Sir amma ni aka ba wa shirin nan, ranan Jummu’a kai da kan ka ka jaddada mini cewa ni zan fara shirin nan, ni na tsara tambayoyi, ni ne na kira Alhaji Isa Madara…”

“Kin zo da wuri?” Yai tambayar yana ɗago ma ta ƙananun idanun sa.

“Sir inada uzuri, na yiwa C Y text tun da sassafe, kuma na zo kafin lokaci ya cika”

“So?”

“Sir wannan ba adalci ba ne, kuma…”

“Fita” ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ranta a ɓace ta fice daga office ɗin da sauri. MD ya bi bayan ta da kallo yana ƙara yabawa da wannan halitta ta Asiya.

Kai tsaye office ɗin su ta wuce wanda su takwas ke amfani da shi. Mutum biyu ta tarar a wajen ta gaishe su kafin ta wuce kan madaidaicin desk ɗinta ta zauna, ta ajiye jaka da wayoyin ta sannan ta kifa kan ta a kan desk ɗin.

Idan mutum ya ce yana son ka ka ƙi shi shikenan sai ya zama abin damuwa. Tunda ta fara aiki a wannan waje MD ke takura ma ta.

“Da wani ƙaton tumbinsa a wajen” ta furta a fili tareda jan dogon tsaki…

Yinin ranan gaba ɗaya a hasale ta ke saboda abinda MD ya ma ta. Ita gani ta ke ma da gangan yai hakan, dama tun asali Iklimar ya ke so ta yi shirin ba ita ba. Dama ƙwalele ya ke son yi ma ta…

Kusan ƙarfe biyu na rana su ka fita ɗauko rahoto chan wani ƙauye. Faɗa ne ya ɓarke tsakanin manyan ƙabilu guda biyu da su ke wajen.
Sun samu sun tattara bayanai sannan sun yi hira da mutane da dama a ƙauyen kasancewa an ɗaura labarin ne life. Faɗa ne da ya faro daga ƙona gona guda ɗaya sai abin ya zamo rikicin ƙabilanci akayita ƙone-ƙone.

*”bayan Gwamnatin Jahar Congo ta turo jami’an tsaro zuwa wannan ƙauye, ƙura ta fara lafawa, yayinda iyayen da aka yi awun gaba da ‘ya’yan su su ke cikin Alhini. Na tambayi wani jami’in tsaro wanda ya tabbatar mini da zaran sun gama bincike sun tabbatar babu hannun yaran nan guda biyar a sakawa gonar Malam Bala wuta za su sako su wa iyayen su. Muna fata dai wannan abin da ya faru zai tsaya a iya haka domin zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki. Ta ku ASIYA-SHAHIDA FARUQ BABA, tashar Hill TV”* ta ƙarasa maganar tana murmushinta mai shiga rai.

Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da C Y ya ce cut. Ba yau ta fara kawo rahoto ba amma yau tunda ta fara ta ke jin ƙirjinta na mata nauyi. Ko dan ranta a ɓace ya ke oho. Ta ɗan ɗaura hannunta a ƙirji tana jin yadda ya ke bugawa da ƙarfi. Ikon Allah! Ko ranan da ta fara tsayuwa gaban camera ta kawo rahoto shekara ɗaya da ya wuce bata ji irin wannan tsoron ba. Lokacin da ta ke kallon camera ta sani tana fiskantar duniya ne, amma yau ji ta ke kamar mutum ɗaya ta ke fuskanta, kamar wannan mutumin da ke kallonta koma wanene idonsa yana ma ta nauyi, ya saka ma ta tsoro, ya kassara duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi.
Za ka fahimci halin da ta shiga ne kawai idan har ka tuna yadda ka ke ji idan wani mutum da ka ke tsananin jin kunya ya zuba maka ido. Kana jin idon sa na yawo a ko’ina na jikin ka har hakan ya saka ma ka kasala har ma ka kasa iya aiwatar da komai, idan ma kana wani abu to ka dinga kuskure kenan.
To ko dai Ubayd yana kallon news ɗin nan ne? Ta tambayi kanta.

“You Ok?” C Y ya fargar da ita daga tunanin da ta ke yi

Ta gyaɗa ma sa kai tana murmushi.

“Ko dai saboda abinda MD ya miki ne? Yau gaba ɗaya kin yi wani iri. Babu wani spark lokacin da ki ke camera”
Yana maganar yana lanƙwasa doguwar tripod da aka ɗaura camera a kai.

“Ban san mi ya ke damuna ba, its like kamar mutumin da na ke jin kunya yana kallon program ɗin nan. I’m feeling his eyes all over me”

“Ba ma her ba, his eyes. Lallai Aseey, ko kin yi sabon crush ne” C Y ya faɗa yana dariya.

Ba yau Ubayd ya fara ganin report ɗinta ba. Infact akwai ranan da ya ke wajen ma ta ke ba da rahoto a gaban camera ɗin kuma bata taɓa jin irin haka ba. Idan ba Ubayd ba waye? Certainly not Umma da Abba saboda su kam tun ma kafin ta fara aikin sun kasance confidante ɗinta. Ta iya tuna ranan da aka ƙara mata matsayi ta zama field reporter sai da ta kira suka boosting confidence ɗinta kafin ta fara aikin.
Idan ba Ubayd ba idan ba Abba da Umma ba, to WAYE? Ta faɗa tana kallon motar su da su C Y ke faman saka kayan aikin su ciki…

 

***

GOVERNMENT OFFICE, CONGO STATE,

 

 

dif…dif…dif… ƙarar da yatsar sa ke bayarwa kenan lokacin da ya ke buga table ɗin gabansa da yatsarsa manuniya. Tunda aka fara rahoton ya ke kallo bai ɗauke idon sa ba sai da mai ba da rahoton ta faɗi sunan ta sannan aka ɗauke wajen zuwa announcer da ya ke chan studio yana ƙara commenting akan abinda ya faru a ƙauyen.
Ya bibiyi labarin ne saboda shine abu na farko mai mahimmanci da ya aiwatar a wannan shekara wanda har an kusa cin rabi cikin ta.
Mutane dayawa kallon hoto su ke ma sa. It has being a challenge lokacin da aka kira shi da gaggawa aka sanar da shi faɗan daya taso a ƙauyen Kayal ɗin. Gwamna baya ƙasar dan haka shine ya ke da damar ba da umurni a aiwatar da duk abinda ya dace gameda matsalar.
Tuni ya rattaba hannu a takarda wajen tura jami’an tsaro ƙauyen domin daidaiton lamurra a wajen. Ya ji daɗi da reporter ɗin ta yabawa Gwamna duk da dai shi da yai aikin ba Gwamna ba ne, da alama ko dai ta manta cewa Gwamna baya gari ko kuma dai ta furta Gwamna ne a matsayinsa na wakilin Gwamna ɗin.
Gidan Talabijin na HILL TV ba ta Gwamnati ba ce shiyasa ya damu da ganin rahoton daga tashar maimakon CONGO NEWS wacce ta ke gidan Talabijin na gwamnati ba lallai a yaɓawa Gwamnati baƙin fenti ba idan har ba su yi abinda ya dace ba sai ma ayi ƙoƙarin kare su.

Bai ida wannan tunanin ba wayar sa ta hau ringing. Mr Governor ya gani ɓaro-ɓaro a screen ɗin. Da sallama ya amsa wayar cikin muryarsa mai sanyi.
Daga ɓangaren Gwamna kuwa ko amsa sallamar bai yi ba ya ce ma sa maganan Albashi da zai sa hannu akai ya bari sai ya dawo tukunna.

Deputy Governor ya ce “Mr Governor nan da kwana shida fa kenan ”

“To mutuwa za su yi kafin kwana shidan?”

Bai ce mishi komai ba har ya gama magana ya kashe kiran.
Yayi tunanin ya kira ne domin yai ma sa magana akan faɗan da aka yi a ƙauyen Kayal may be ma ya yaba ma sa akan ƙoƙarin da yai wajen daƙile faɗan da wuri amma shi damuwar shi kada ya saka hannu a bawa mutane Albashinsu har sai ya dawo. Yau Albashin ya shigo daga gwamnatin tarayya, kwanan wata ya kama ashirin da bakwai idan aka ƙara kwana shida zai zama uku ga wani watan kenan, mutane za su ji jiki.
Minene amfaninsa idan har a matsayinsa na mataimakin Gwamna ba zai iya aiwatar da komai na cigaban al’umma ba idan Gwamna baya nan. Ya tabbata kenan shi hoto ne.

 

***

 

Lokacin da Asiya su ka koma office har anfara kiraye-kirayen sallar Maghriba. Tana shiga office ɗin su aka sanar da ita saƙon MD da ya ke nemanta. A gajiye ta wuce office ɗinsa, ta sani ƙorafi ne zai yi ba komai ba. Tunda a wajensa kullum ba ta iya aiki ba.

“Miye matsalar ki ne Asiya?. Today’s report was full of crap, sati biyu Gwamna baya gari amma kina ta faɗin Mai girma Gwamna ya turo jami’ai, Mai girma Gwamna ya damu da talakawansa. Give credit to whom credit belongs. Kina ganin da Gwamna Saminu Bacci ne zai tura jami’an tsaro cikin ƙanƙanin lokaci haka? I’m dissappointed in you”

Ita kwata-kwata ta manta da cewa Gwamna baya ƙasar to ko yana nan ai Deputy Governor hoto ne. Ba abinda ta taɓa jin ance yayi sai shegen yin ado kaman mace. Indai SSK ne ko mace sai albarka wajen iya ado.

Chief Editor na su da ke zaune a office ɗin ya kalli Asiya ya ce ” miya faru na ga rahoton ki na yau ba wani armashi, ba ki da lafiya ne?”

“no Sir, Ummata ce ba lafiya” Asiya ta faɗa ranta a ɓace.

“Allah ya bata lafiya”

Ta amsa ma sa da Amin. Da hannu ya ma ta nuni da ta fita daga office ɗin. Bayan ta fita Chief Editor ya kalli MD ya ce ” mutumina ka mata a hankali. The girl is good ba wanda ya fi ƙarfin kuskure”

“Idan har bama nunawa jama’a goodness na Mataimakin Gwamna kullum kallon hoto za a dinga ma sa. Wallahi da shine Gwamna da jahar nan ta fi haka cigaba cikin shekaru ukun nan. S S Kachallah mutum ne da ya san darajan ɗan Adam, he’s a man of vision and mission”

“Ni zan gaya maka halin Prof Kachallah tunda ya koyar dani lokacin ina Masters …” daga nan su ka buge da hiran mataimakin Gwamnan.

Asiya na fita daga office ɗin MD ƙasa ta koma wajen office ɗin su ta ɗau jakarta ta fito. Wani mahaukacin yunwa ke cinta ga gajiya a haka tafito daga farfajiyar gidan Talabijin ɗin. Da Ubayd na gari da shi za ta kira ya zo ya ɗauketa amma yanzu sai dai ta nemi abin hawa. Tana tsaye C Y ya fito da tsohuwar baƙar roba-roba ɗin sa.

“Ke kalar mota ce da na miki lift zuwa gida” ga faɗa yana dariya.

“Ƙaniyarka C Y, kana nufin tafiya za ka yi ka barni kenan”

Ɗan dawowa yai da baya ta hau mashin ɗin sannan ya ja suka tafi. Suna tafiyan suna taɗi saboda Clement Yohanna (C Y) akwai surutu shima kamar Asiyar shiyasa ma tasu ta zo ɗaya.

A ƙofar gidan su ya sauketa yana faɗin ta gaida ma sa da Umma.
Da sallama ta shiga gidan na su, Inna Yaha na faman jan ruwa a rijiya amma ba ta amsa sallamar ba. Ko ba ta leƙa kitchen ba ta san sai yanzu za’a ɗaura abincin dare ko kuma yanzu aka fara girkin.

Sannu da aiki ta mata duk da ta san ba amsawa za ta yi ba. Wucewa ta yi ɗakin Ummanta wadda shine ɗaki na biyu cikin ɗakuna uku da su ke jere waje guda. A kan sallaya ta samu Umman ta idar da sallah tana jan carbi, ta san ba za ta amsa gaisuwarta ba har sai ta gama azkar ɗinta shiyasa ma ta wuce wajen wardrobe ta buɗe ta fito da wata doguwar riga mai laushi, rigar guntun hannu gareta. Kayan jikinta ta cire ta saka doguwar rigan. Lokacin da ta zauna bakin gado tana naɗe wandon jeans ɗin da ta cire ne Umma ta fara mata magana da yaren Kurame inda ta ke tambayarta ya aiki, obviously ta ga rahoton da Asiyan ta kawo ɗazu a TV. Itama Asiyan ya jiki ta mata tareda tambayarta ko ta sha magani.

Ƙarfe bakwai da rabi da minti takwas bayan ta idar da sallan Isha Cornflakes ta haɗa da madara ta fara sha tanayi tana danna wayarta. Kiran Ubayd ne ya shigo wayarta amma har ta katse ba ta ɗauka ba saima tsaki da ta yi. Bayan ya jera kira biyu ba a ɗauka ba sai a na ukun ta ɗauka amma ba ta yi magana ba.
“My Aseeya” ya faɗa da murya mai sanyi.
Tasirin da sunan yai ma ta ne ya sa ta yin guntun murmushi.

“Tuba na ke ranki shi daɗe. Na san na yi laifi amma a bani dama na faɗi uzuri na”
Still shiru ba ta ce komai ba

“Mine kina ji na?”

“Mine”

Asiya ta ɗan jinginar da kanta jikin gadon Umma sannan ta ce “ni mi zan ce tunda Matan Lagos sun ɗauke mun kai. Yau tun da sassafe da muka yi waya ba ka sake waiwaya na ba sai yanzu. Na san ka kalli report ɗina na yau amma ko ka kira ka tambayi lafiyata, you dont even care ko na dawo lafiya ko ban dawo ba, kawai kai…” haka ta yi ta rantings har sai da ta gaji da kanta ta yi shiru, a lokacin ne kuma Ubayd ya samu damar lallaɓata dan ya san halin kayan sa indai tana kwarwa to ba a katseta har sai ta gama.
Bayan ta karɓi haƙurin sa ne suka bige da hiran masoya ba ta ma ji shigowar ƙaninta Aliyu ba sai kawai gani tayi ya ɗauke kofin cornflakes da ke gabanta ya fara sha. Tana ma sa magana da hannu amma inaa bai kulata ba sai ya ma koma gefe ya shanye cornflakes ɗin tas.
Bayan ya gama kuwa ya dangwarar mata da kofi a wajen yai gaba. Shigowan Umma ɗakin ne ya sa ta yi sallama da Ubayd akan za ta kirashi anjima.
Da hannu Umma ta gaya ma ta cewa ta je ta samu Abbansu a falo yana nemanta.
Sanda za ta wuce falon Abban ta kula da Inna Yaha da ke ta kwaran-kwaran a kitchen tana rabon abinci, babu wuta kuma torchlight da ta ke amfani da shi ya dafe ba haske sosai. Ba ta taɓa gajiya da mamakin halin Inna Yaha.

Asiya ta yi sallama bakin ƙofar falon Abba. Abba ya ce ta shigo.
Abba dattijone da kallo ɗaya zaka ma sa ka san ya doki shekaru sittin da biyu zuwa da biyar. Fari ne sosai a lokacin ƙuruciya amma yanzu ya fara dafewa, fiskarshi da kanshi yana yalwacce da gashi wanda kusan ya riga ya zama fari gaba ɗaya sai tsilli-tsillin baƙi da ba za a rasa ba.

Bayan ta gaisheshi ne ya ke tambayarta gameda ƙauyen da su ka je yau ɗauko rahoto. Bayan sun yi alhinin abinda ya faru tare ya sanar da ita musabbabin kiranta da yai. Magana ce akan admission da ƙaninta ya samu a Congo University wanda ya dage akan ba zai zauna a hostel ba sai dai ya dinga jeka ka dawo, shawaran Asiya ya tambaya ko dai ya siya ma sa babur kaman yadda Habib ɗin ya buƙata ne?.

Abba ya jima da retire har yanzu kuɗin pension ɗin sa su ke lallaɓawa. Ba dan Allah yayi ita da Umma suna sana’a ba da abubuwan ba za su zo da sauƙi ba. Ubayd ma yana nasa ƙoƙari akan mahaifinsa sosai.
Bikinta da na Faty da za ayi Abba ke yiwa taru dan haka maganar siyan Babur bai taso ba. Za ta yiwa Habib magana, gigin samartaka ke ɗibanshi yana ji yanzu ya gama sakandare zai shiga Jami’a.

Bayan ta bar wajen Abba ɗakin su ta koma inda Umma ke faman tura tuwon da aka miƙo ma ta. Sau ɗaya ta kalli tuwon ta kauda kai. Ga abinci ba za ayi da wuri ba gashi ba zai taɓa yin daɗi yadda ya kamata ba.
Kafin ta kwanta sai da su ka sake yin waya da Ubayd sannan ta kira Queen Bee su ka yi maganar Salon ɗin su…

*Mi za ku ce gameda Asiya-Shahida?*

 

*THE GOVERNOR’S WIFE*
…… MATAR GWAMNA….

*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

Book one

 

02

***

 

A chan wani ƙaton gida da ke GRA wasu manyan mutane ne guda huɗu ke zaune a wani katafaren falo daya amsa sunan falo saboda girma da kuma irin kayan alatu da aka zuba a ciki.
Ɗaya daga cikin su wanda kusan shi za a kira da babban su ya kalli wani da ke sanye da farar shadda da farin hula ya ce “Kachallah kana ganin za mu samu abunda mu ke buƙata a wajen sa?”

Kachallah ya ce “inada yaƙinin haka Yallaɓai. Shi mutum ne mai biyayya”

Wani mai baƙin suit ya tari bakin Kachallah da cewa “inada shakka akan wannan”

“Mr Paul mi kake so ka ce, ba dai kana nufin za a rusa tsarin wannan gwamnatin ba…”

“Mr Paul, Alhaji Kachallah wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran lokaci dan haka zamu cigaba da saka mishi ido kafin lokacin ya cika. Ko mi ka ce Yallaɓai?”

Yallaɓai ya kalli Mutumin da yai magana sannan ya maida dubansa ga Alhaji Kachallah da Mr Paul. A hankali ya fara shafa gemun sa yana yi yana murmushi. Murmushin Yallaɓai na da ma’anoni daban-daban amma a wannan lokaci dukkan su sun yarda cewa yana nufin su kwantar da hankalin su ne, wato akwai nasara a dukkan tsare-tsaren su.

 

***

LADIES HALAAL SALON & SPA waje ne da ya amsa sunan sa, domin kuwa dukkan abubuwan da ake gudanarwa a wajen suna ƙoƙarin tafiya da tsarin da bai kaucewa tsarin musulunci ba. Waje ne da Asiya-Shahida, Queen Bee da Alhaja Oyiza su ka buɗe saboda samawa mata wajen kula da jikin su. Ma’aikatan wajen dukkan su mata ne. Cikin ayyukan da su ke gudanarwa a wajen akwai wanke gashi, drying da kuma stretching, suna gyaran farce (menicure and pedicure). Ana kitso da kuma ƙunshi sannan watanni biyar da su ka wuce da su ka dawo sabon shagon su da ke anguwar GRA suka fara gyaran jiki da spa treatment a wajen (wanda ya haɗa da body, hair and foot massage, facial treatment da sauran su)

Shigowar Shahidah sashen da ake yin gyaran gashi da kitso ya sa wajen yai wani irin tsit. Precious da ke yiwa wata mata kitson wig ta tsaya da kitson tana kallon Shahida jikinta na ɓari.

Matar ta ɗan ɗago ta ce “ya ki ka tsaya?”

Tunda ba sa saida gashin wig kenan matar ce ta zo da abinta. Shahida ta faɗa a ranta.
Precious ba ta san ma Shahida na cikin shagon na su ba da ba za ta yi gigin fara yiwa matar nan kitson wig ba. Ta san dokar shagon su amma wannan matar Comissioner ce, duk da ta hannun Queen Bee ta zo ta tabbata za ta raɓi maiƙo a jikin matar, shiyasa da matar ta nuna kitson wig za a mata ba ta iya yi mata musu ba.

Shahida ta ƙaraso gaban matar sannan ta kalli Precious ta ce ” ina bawa mutane dama ɗaya tak a rayuwa, na ƙarshe kenan da za ki sake taka mana dokan wannan shago. Ki maida mata kuɗinta ta bar mana waje”

“Malama ban gane mi ki ke cewa ba. Da alama ba ki san ko ni wacece ba ce”

“Duk wanda ya shigo wannan waje domin a masa wani abu a nan to sunan sa customer. A dalilin an ɓata miki lokaci za a maida miki kuɗin ki dan haka ki wuce wajen da su ke yin irin wannan kitso a ƙarasa miki a chan”

“What nonsense” matar ta faɗa a fusace tana miƙewa tsaye.

“Idan kin fita ki ɗan ɗaga idon ki sama za ki ga sunan wannan waje. Saka gashin wig baya cikin services na mu”

Daga haka Asiya-Shahida ta bar wajen. Tana jin matar tana ta zage-zage amma ko ajikinta. Ta yiwa matar farin sani. Habiba sunanta a ƙasan layinsu ta taso. ta tsula bariki sosai kafin ta auri kwamishinan ilimi shekaru uku da suka wuce.

Dole ta yi magana da Queen Bee ta jawa Precious kunne tunda ita ta bata aiki. Idan irin haka ya cigaba da faruwa Salon ɗin su zai zama babu wani banbanci tsakaninsa da sauran gama gari…

**

Shahidah na zaune tana zanawa Amarya Layla lalle a hannu ta ji matan da ke wajen sun saka ihu.

Basma ta ce “Jennifer ƙara mana volume mu ji mi ya ke cewa”
Kafin ta gama maganar ma ta riga ta ƙara volume ɗin.
Muryan daya doki kunnen Asiya ne ya sa ta jan dogon tsaki ba shiri.

“Yanzu dan Allah saboda wannan wawan ku ke ta ihu”

Banza su ka yi da ita suka cigaba da yaba mutumin da ke magana a cikin TV.

“Ki ga idon sa dan Allah, ko idon kaɗai Allah ya bashi wallahi an zuba ma sa baiwa” wata daga cikin ƙawayen Amarya da ake wa Lalle ta faɗa.

“Allah ya shiryeku gaskiya. Mutum tsohai-tsohai da shi ku dinga wani drooling akan sa kaman wasu ƙwailaye”

“Ke dai ‘yar baƙin ciki ce Asiya. Allah ya isan ma SSK ɗin mu za ki kirashi tsoho”
Kafin ta yi magana kuwa Asabe ta ce “ni kin san Allah yanzu haka idan da za ace na zaɓi tsakanin SSK da kuma Ubayd ɗinki Asiya Wallahi Tallahi SSK zan zaɓa”

Asiya ta fusata ta kaiwa Asabe duka Asabe ta kauce tana yi ma ta dariya. Ranan har Asiya ta gama yiwa Amarya Lalle ba ta dena diri ba. Hayaƙi ne kawai bai fito daga bakin Asiya ba saboda yadda ta dinga faɗa akan an haɗa masoyinta Ubayd da SSK…

 

**

 

“Gashi nan ai ya ƙi biyan albashi ya bar mutane da yunwa. Idan ka yi magana kuma a fara ganin baƙin ka mtsww”

“Mine kina da abun dariya Allah. Tunda mu ka zauna a nan ba hiran da mu ka yi sai ta SSK. Ki rage ƙiyayyar ki gareshi please. Abun ya fara yawa”

“Amma Ya Ubayd…”

“Yanzu dai a ajiye maganar sa a gefe tukunna. Albishirin ki”

Asiya ta haɗe rai ta juyar da fiska gefe.

“My Aseeya haka zan tafi gida ba tareda kin min murmushinkin nan mai sanyaya min zuciya ba”

“Ka je SSK ya maka murmushin tunda ka damu da shi”

“Mi zan yi da murmushin ƙato bayan inada kyakykyawar budurwa a kusa da ni”

“Dama ina so na miki maganar gida ne amma tunda kinyi fushi shikenan”

“Dan Allah an gama gyara kitchen ɗin?” Ta faɗa cike da excitement.

“Wagga Bafulatana ba ta da kunya samsam”

“Eh ɗin” ta faɗa tana murguɗa ma sa baki.

“Kinga ɗan bakin nan da Allah zai kaimu wata biyar da kwana shauku da na jima da maganin sa”

Asiya ta yi saurin sunkuyar da kai tana rufe bakinta da tafin hannu tana murmushi cike da jin kunyarsa.

“Na rufe bakin ko?, gara ma ki sani a matse na ke wallahi. Abba dai ya cuceni daya saka bikin nan da nisa haka. Tunda Mustafan Faty bai gama shiryawa ba da anyi namu bikin idan ya so sai ayi na su daga baya”

“Ya Ubaydu wai ka je inji Abba” muryan ƙaninsa Musa ya doki kunnen sa.

“Musa kana so in zaneka ko? Za ka faɗo kanmu ba sallama sai kace wani dabba”

Musa ya fece daga wajen da sauri tun kafin Ubayd ya damƙeshi dan ya san halin yayan na sa sarai.

“Barin je wajen Abba”

“Idan ka je ka kai ma sa ƙorafin ka ƙila ya chanja ra’ayi”

“Ahaf ashe ba ni ɗaya na matsu ba kenan”

Ba ta amsa ma sa ba ta wuce ɗaki da sauri.

Murmushi yai mai daɗi yana addu’ar Allah ya kai shi lokacin da Asiya Shahidah za ta zama mata a gareshi.

Asiya na shiga ɗaki ta faɗa kan gado. Murmushi ta ke yi tana jin tsananin shauƙin son Ubayd. Ba za ta ce a matse ta ke ba amma harga Allah ba ta so aka saka bikin su wata shida ba, ta ɗauka wata uku ko huɗu Abba zai sa. Koda yake duk dalilin Mustafah wanda zai auri Faty aka kai bikin da nisa saboda ya ce bai gama shiri ba. Suma ɗin cikin wata shida kam sun gama shirya komai.

Ƙaran shigowar notification ta ji a wayarta da ke gefen gado, da sauri ta jawo wayar dan ta san ba zai wuce saƙon favourite poet ɗin ta ba ne wato KaSaSa. Ai kuwa tana buɗewa taga saƙon email ɗin daga KaSaSa ce. Tunda ta subscribing a website ɗin ta koyaushe ta ɗaura sabon poem za ta gani a email ɗinta.

Ta karanta poem ɗin ya fi sau biyar kafin ta miƙe ta je ta ɗauko littafinta da ta ke rubuta duk poetry na KaSaSa a ciki, ta rubuta sabon poem ɗin da aka turo. Idan Ubayd ya zo sallama dole ne ta karanta mishi poem ɗin dan ya taɓa zuciyarta sosai. A zuciyarta ta ce Allah ya zubawa KaSaSa baiwar kalamai.

 

***

Motoci guda biyar ne su ka shigo wani katafaren gida, irin gidajen nan ne da ƙusosin gwamnati da manyan ‘yan kasuwa kaɗai ke iya mallakan su a wannan ƙasa, shi ɗan talaka sai dai ya gani kawai ya buɗe baki ya cika zuciyar sa da buri sannan ya kaɗa kai yai gaba, amma gidan yafi ƙarfinsa.

Motocin sun tsaya ne a farfajiyan gidan. Motar da ke tsakiya wacce ta fi kowanne kyau wani bodyguard ya buɗe ya fito daga gaban motar da sauri sannan ya buɗe ƙofar baya.
Ƙafafuwansa da ke sanye da designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior ne suka fara sauka ƙasa kafin sauran jikin ya biyo baya. Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo takwas a ma’unin meter (1.8m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da ta shahararren ɗan film ɗin ƙasar India (Bollywood) wato Amitabh Bachchan.
Baƙi ne sosai irin baƙin da ya fi kama da na larabawan ƙasar Sudan. Sai dai na shi baƙin ya haɗu da hutu da jin daɗi sai ya zama har wani sheƙi ya ke yi yana ɗaukar ido. Idanunsa sun fi ko ina ɗaukar hankali a jikin sa. Fari fat da ɗigon baƙi wanda yai kamar an ɗiga baƙin tawada a cikin ruwan madara. Zara-zaran gashin ido da kuma gira da ke cike da baƙin gashi su suka haɗu suka ƙara ƙawata manyan idanunsa. Baƙin saje da ya haɗe da fiskarsa zuwa gemu da gashin baki suka bawa fiskar kyau da kamala.

A zahiri kallon yaro ake ma sa saboda kyaun jikinsa da ke ɓoye shekaru ,da kuma yadda akoda yaushe ya ke shiga irin ta Matasa. A ranakun Jummu’a da lokutan zuwa wajen taro na musamman kawai ya ke shiga irin ta Malam Bahaushe, amma fiye da rabin shigar sa shiga ce ta mutanen ƙasar waje. Ba abun mamaki ba ne ka ga SSK sanye da Tshirt da jeans a office tun ma kafin ya shiga siyasa har zuwa yanzu kuwa da su ke kan Gwamnati.
Kasancewar ya samu sa’ar karatu da wuri ya amshi Phd ɗin sa yana shekaru ashirin da bakwai ne yayinda ya kai matsayin Professor a shekarun sa talatin da biyar, kusan shekarun da ake ɗiba ma sa kenan idan an kalleshi wanda a zahiri an zaftare ma sa kusan shekaru goma kenan cikin shekarun sa.
Yanzu ma SSK na sanye ne da riga mai dogon hannu kalar sararin samaniya, irin yadda sama ke kasancewa a ƙarshen yammaci kafin dare kamar wajajen ƙarfe biyar da rabi zuwa shida ɗin nan, musamman a lokacin sanyi. Wandon jikin sa ta jeans ce kalar light blue, yana sanye da agogo da kuma zoben azurfa a yatsarsa ta tsakiya da ke hannunsa na dama.

Tuni bodyguard ya amshi jakar hannunsa bayan ya sara ma sa yana ƙame jiki tareda faɗin “Excellency”

Mataimakin Gwamna kenan *Professor Saifuddeen Sa’ad Kachallah* ingarman namiji mai cikar zati da haiba wanda a yanzu ya ke riƙe da jahar saboda Gwamna baya gari.

Kai tsaye cikin gidan sa ya wuce wanda ya gina da halaliyarsa tun ma kafin ya shiga siyasa dan ya ƙi komawa gidan gwamnati. Daga falon farko ba kowa sai dai yana iya jiyo hiran matarsa a ɗaya falon da wasu matan. Ya haura matattakala da zai kai shi sama inda ɗakunan gidan su ke. Ɗakin ƙaramin ɗan sa ya fara leƙawa. Yaron ɗan kimanin shekaru shida na zaune akan gado yana buga game a laptop ɗin sa. Sa’ad Saifuddeen Sa’ad Kachallah kenan wanda kowa ke kiransa da Junior. Ya kissing goshin yaron yana tambayarsa ko yayi homework ɗin sa yaron ya amsa da eh. Ya shafa kan yaron sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Bai leƙa sauran ɗakunan yaran na shi ba saboda kwana uku da su ka wuce su ka tafi hutu. Babbar ‘yar sa Nana Khadija ta tafi gidan ƙanwar matarsa yayinda Aisha da su ke kira da Mahira ta tafi wajen Dadda wato kakar sa.

Wanka SSK yai sannan ya sanya farar jallabiya ya fito saboda kiran sallah da ya ke jiyowa daga masallacin kusa da gidan sa.

Hajiya Bilkisu na zaune a falonta tareda wasu mata guda uku. Ɗaya matar Comissioner ce, ɗaya kuma matar wani Senator ce, sai ɗayar kuma tsohuwar comissioner of Health ce wato Dr Madam Helen Audu.

“Yanzu dai ina so komai ya tafi dai-dai gobe, kar ya zama saboda first lady ba ta nan sai mu kasa gudanar da taron yadda ya kamata”

“Hajiya Bilkisu kar ki ji komai, ai abinda ki ke yi a wannan jaha ko firstlady albarka” inji matar senator

Bilkisu ta yi ƙasaitacciyar murmushi ta ce “indai akan cigabar jahar nan ne dole na yi ƙoƙari wajen ganin komai ya tafi dai-dai”

Madam Helen ta ce “Hajiya Bilki ni zan wuce”

“Nagode Mommy, sai mun haɗu goben” Hajiya Bilki ta faɗa da sigar girmamawa saboda Madam Helen ta girme ta sosai, idan ba ta yi sittin ba to za ta kusa kaiwa hakan.
Bayan tafiyar Madam Helen da kusan minti shabiyar sannan sauran matan su ka tafi sai a lokacin Hajiya Bilkisu ta samu damar sauke nannauyan ajiyar zuciya tana tararradin yadda gobe zai kasance. Wannan ne karo na farko da za ta gudanar da babban taro ita kaɗai. Taro ne na matan Gwamnonin Arewa wanda tun kafin tafiyar Firstlady aka tsara shi, ita ne ta kawo shawaran kuma Firstlady ta amince da shi sai dai rashin Firstlady a gari ya sa aka yi tunanin ɗaga taron har sai ta dawo amma Hajiya Bilkisu ta nuna ba sai an ɗaga ba za ta wakilci Firstlady a wajen taron.

Bayan tafiyar matan nan ta lalubo wayar ta ta cigaba da bibiyar yadda za a sauki baƙin gobe ba tareda an samu matsala ba.

Lokacin da ta samu nitsuwa ta haura sama ɗakinta ta wuce ta yi wanka ta saka kaya sannan ta fara sallah, ta haɗa sallar La’asar, Maghriba da Isha wanda zirga-zirga bai sa ta samu yinsu akan lokaci ba.

Ƙarfe goma da kwata ta shiga ɗakin mijinta wanda ke kishingide akan gado yana danna waya yana murmushi.
Zuciyar Bilkisu sai da ya kusa bulloƙowa waje saboda tsallen da yai, kamar walƙiya ta zo ta ɗauke wayar hannunsa tana huci tana duba abinda ya sa shi irin wannan murmushi haka. Shafinsa ne da ya ke rubuta poems ya ke dubawa, ba mamaki yana dariya ne saboda yadda mabiya shafin ke alaƙanta shi da mace.
Saƙon wani fan ɗin sa ta gani da ya ke cewa shi a duniya ba macen da ya ke so kamar KaSaSa.

“Darling har yanzu ba za ka ce mu su kai namiji ba ne ba mace ba” sai kuma ta yi saurin gyara maganarta da cewa “gara su cigaba da yi maka ganin macen, kafin yanzu mata su dinga damunka da waya”

Mayar ma sa da wayar ta yi tana murmushi ” My Darling ka san ina kishin ka dayawa”

Bai ce ma ta komai ba ya cigaba da duba saƙonnin masoyan na sa.

“Ka ci abinci?” ta tambaya lokacin da ta kwanta gefen sa.

“Na leƙa ɗakin Junior ya riga yayi bacci, i guess tare ku ka ci dinner kenan”
Still bai amsa ma ta ba.

Ta sani idan SSK yana harkan rubuce-rubucen sa baya taɓa ba da hankali a wani abun daban, shiyasa ta haƙura da maganan ta manna ma sa kiss a kumatu tareda faɗin goodnight ta ja bargo ta kwanta. Gobe babban rana ce a gareta shiyasa dole daren yau ta samu isasshen bacci.

A wajen SSK ba komai ya hanashi kula matar ta sa ba sai ganin cewa ɓata lokaci ne a gareshi ya faɗa ma ta kuskurenta. Shi ba ma’abocin yawar magana ba ne hakan ya sa tun farkon auren su ya ke ɗagawa Bilkisu ƙafa, sai dai maimakon abubuwan su ragu sai ya zama ƙaruwa kawai su ke yi.
Irin rayuwar da yai buri idan yai aure ba ita ce rayuwar da ya ke yi yanzu ba.

A wassu lokutan yakan yi tunanin idan da Misturah ya aurah abubuwa ba za su zo ma sa haka ba. Kafin ya faɗa soyayyar Misturah ta kasance abokiya a gareshi wacce ya ke iya gayawa damuwar sa, wacce ya ke iya neman shawara a gurinta kuma ya samu shawara mai kyau.
Duk da sun taso gida ɗaya babu wannan kusancin tsakanin sa da Bilkisu. Har yau da su ka kusan cika shekaru shabakwai da aure ba zai ce ya gama sanin halin Bilkisu ba haka nan itama yanada yaƙinin ba ta san wanene Saifuddeen ba. Suna rayuwa ne tareda shamaki kamar labule a tsakanin su. Tun kafin ya zama Mataimakin Gwamna baya samun kulawar daya dace a wajen Bilkisu sannan daga shiga gwamnati abubuwa suka sake taɓarɓarewa.
A lokutan dayake cikin ƙunci ya ke buƙatar nitsuwa daga matar sa. A lokutan da kansa ya ɗau zafi daga harkokin gwamnati ya ke buƙatar samun mafaka a wajen matar sa. A lokutan ne za ka ga Bilkisu ta shagalta da harkokin siyasa ko kasuwanci.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tunda ta sako maganar taron matan Gwamnoni da za ayi baya tunanin ta sake saka shi a lissafinta. Idan har ta tuntuɓeshi to tana neman shawara ne bisa jadawalin da ta tsara na abubuwan da za a gabatar ranan.
SSK ya juya ya kalli Bilkisu da ta ke gwarti alamun baccinta yayi nisa kenan.

Kafin ka yi aure duk irin waɗannan ƙananan abubuwa ba ka saninsu sai kun zauna tare na wani lokaci.
Akwai lokutan da idan zai kwanta sai ya saka auduga ko earbud a kunnensa saboda yadda Gwartin Bilkisu ke hana shi bacci, a hankali har jikinsa ya saba da hakan.

Aure sai da haƙuri, abunda ake gayawa sabbin ma’aurata kenan. Alokacin ba sa gane me ake nufi da haƙuri har sai sun kwana biyu da aure.

A farkon auren su yayi haƙuri da lokutan da zai shiga banɗaki yaga Bilkisu ta jefa pant mai haɗe da pad cike da jini a loundary basket ɗin su. Ko kuma a lokutan da ta ke fama da mura ka ga tissue papers da ta face majina da shi a kan gadon su. Ba zai taɓa mantawa da ranan da ya shiga banɗaki tsantsin majina da aka fyace a ƙasan tile ya ɗebeshi ya faɗi ƙasa ba. Yayi haƙuri da kasancewarta ba ta girki saboda a gidan su bata yi, duk da kuwa girki na cikin abubuwan da ke taɓa ma sa zuciya. Girkin Misturah na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka shi faɗawa soyayyarta tun bai shirya hakan ba.

“Saif wannan pepper soup ɗin yana narka zuciyar namiji yana saka mishi nitsuwa. Inada yaƙinin koma mi yake damunka idan ka ci wannan peppersoup ɗin za ka samu sanyi” abinda ta faɗa kenan lokacin da ta miƙa ma sa ɗan ƙaramin food basket da ta riƙo ma sa.
Misturah ta yi gaskiya domin ranan da ya sha wannan peppersoup ɗin ya samu nitsuwa.

SSk ya kai hannunsa ya shafa gashin wig da ya ɗan bulloƙo ta gefen hular baccin Bilkisu.
Yayi haƙuri da kasancewarta mai saka gashin wig duk da kuwa warin gashin na tada ma sa hankali.
Namiji na son mace da za ta fahimceshi, ta saurari maganar sa. Sai dai Bilkisu ba ta ɗaya daga cikin irin matan nan.
Sau dubu Bilkisu za ta yi iƙirarin tana tsananin son shi tana kuma kishin sa, hakanan kuma sau dubu ba za tayi abubuwan da zai cire shamakin da ke tsakanin su ba, har ta samu damar mallake zuciyarsa.

A lokutan kaɗaici he find solitude in poetry, shiyasa ya ke ɓoye kansa da sunan KaSaSa wanda acronym ne na sunansa.

SSK yai murmushi ganin Bilkisu ta maki kanta tareda sosa tsakiyar kan.

Duk wani mulki daya ke da shi ya tsaya a bakin ƙofar gidan sa ne, a cikin gida shi mijin Bilkisu ne, Abban Nana, Mahira da kuma Junior.
SSK ya muskuta ya jawo Bilkisu jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, rabon daya samu nitsuwar miji da mata daga gareta kusan sati biyu kenan.

“Darling na gaji” ta faɗa cikin magagin bacci

“Kar ki damu ba abinda zan yi” ya furta a hankali wani abu na sukan ƙirjinsa…

 

***

“Kina jina? zan turo miki kuɗin idan na dawo daga office. Ya jikin Muttaƙa?

Tana saƙale da waya a kunnenta yayinda ta ke ƙokarin ɗaura agogo a hannunta.

“Sumayya ki tabbatar Ale bai san da kuɗin nan ba. Kuɗin maganin Muttaƙa kuma ki tabbatar an siyi duka magungunan shi”

Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta wuce inda Umma ke ƙoƙarin raba abun kari. Kunun gyaɗa ta yi da ƙosai da kuma soyayyen dankalin Hausa.

“Umma zan wuce” ta faɗa da yaren kurame

Umman ta amsa ma ta da cewa ta tsaya ta ci abinci.

“Zan makara Umma, amma ki haɗa min kunun da dankalin in tafi da shi office”

Murmushi Umman ta yi sannan ta fara neman inda za ta zubawa Asiya kunun.

Minti shida kacal ta ƙara aciki ta fito ɗauke da jakarta da kuma ledan da Umma ta ba ta. Motar Ubayd na jiranta a ƙofar gida dan haka tana shiga ya ja motar da gudu. Gaisawa su ka yi a tsanake ta cigaba da duba wayarta tana bitar report ɗin da ta haɗa jiya.

Tafiyar minti shabiyu ya kaisu ma’aikatar su ta yiwa Ubayd sallama ta shige ciki yayinda shima Ubayd ya wuce Asibiti.

Tana shiga office ɗin su ta printing report ta wuce da shi office ɗin Editor I.

“Weldone Shahida” ya faɗa lokacin da su ka gama duba report ɗin tare wanda kusan gyaran da ke ciki kaɗan ne.
Tana komawa office ta samu sauran colleages ɗinta suna hiran taron da za ayi yau a jihar ta su. Da SSK da matar sa Bilkisu duk babu wanda ke burge Asiya a cikinsu.

“Shahida kin san wa za’a tura yau?”

Shahida ta girgiza kai tana cigaba da latsa laptop ɗinta.

Mike ya sake cewa ” Shahida ina tunanin Abigail za a tura fa gashi har yanzu ba ta iso ba”

“Mike kar ka dameni dan Allah. Idan ba ta zo ba MD zai iya bawa wani ai, ko kai ko Usman”

Ta sani magana ya ke son gaya mata akan kada ma ta sa ran MD zai bari ta je ta covering report ɗin wajen taron da za ayi na matan Gwamnoni. Ba ta san mi ta tsarewa Mike ba a wannan office ɗin. Tun tana bautar ƙasa kafin a ɗauketa aiki yake sa mata ido cikin lamurranta.

Ta cigaba da aiki tana yi tana shan kununta.

CY ya shigo office ɗinsu da sauri. “Aseey ki je office ɗin MD yanzu-yanzu”

“Miya faru?” Ya ɗaga mata kafaɗa ya fita da sauri.

Ta yi saurin kurɓan sauran kunun daya rage sannan ta goge bakinta da tissue ta fice daga office ɗin da sauri tana lura da yadda Mike ke binta da mugun kallo.

Ba ta da ikon yiwa MD musu lokacin daya sanar da ita cewa itace za ta kawo rahoton wajen taron da za ayi yau.
Lokacin da za ta tafi ya ce “Asiya bana son shirme”

“Ok Sir”

Ta sani Abigail yai niyyar tura wa saboda Abigail ta fita gogewa a wajen aiki. Tunda aka buɗe gidan talabijin ɗin ta ke aiki da su kusan shekaru shahuɗu da suka wuce kenan. Rashin Abigail Manji ne ya sa MD ya waiwayeta. A wajen CY ta ke jin labarin wai Abigail tayi tafiya, jiya da daddare mahaifinta ya mutu a chan ƙauyen su.

Ba su kaɗai ba ne ‘yan jarida da su ka zo ɗaukan rahoto kusan kowanne gidan jarida sun aiko da wakilan su. CY ya fito da kayan aiki ya shiga saita camera ɗin.

***

Chief of staff (COS) ne ya shigo ofishin mataimakin Gwamna da sauri hannunsa riƙe da ipad.

“Your Excellency za ka so ganin wannan”

SSK ya karɓi pad ɗin daga hannun COS ya danna kan video dake screen ɗin.

Yar jarida ce a gaban hall ɗin da ake taron matan gwamnoni tana bada rahoto.

“Kaman yadda al’umma su ka shaida irin almabazzarancin da akayi a wajen wannan taro wanda ake iƙirarin anyi shine saboda talakawa. Ko ta ina talaka zai anfana da mawaƙan nan Wizkid da Patoranking da aka ɗauko daga Lagos domin matan Gwamnoni su shaƙata da waƙoƙin su?. Yayinda matar mataimakin Gwamna wato Hajiya Bilkisu S Kachallah take magana akan yadda za a gina gidan marayu, talakawa na nan suna alhinin rashin albashi, rashin ruwa ga uwa uba malaman makarantar firamare da ke yajin aiki tun sati uku da suka wuce har yanzu Gwamnati ba ta waiwayesu ba.
Na zanta da wasu matasa inda su ka bayyana mini cewa taron da Hajiya Bilkisu ta yi wani farfaganda ce kawai da ke son ɗauke hankalin talakawa daga matsalolin da su ka sha mu su kai…”

Tsaida video ɗin yai ya miƙawa COS ipad ɗin

“Your excellency kana buƙatar mu tuntuɓi gidan talabijin na Hill TV ne?”

“A’a”

COS na fita daga office ɗin SSK ya ɗau waya ya kira commisioner of finance…

*THE GOVERNOR’S WIFE*
…… MATAR GWAMNA….

*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

Book one

 

*bayan kwana biyu ina muku barka da dawowa cikin labarin. Saboda wassu uzuri ba ku jini ba sai yau. Insha Allah daga yau za a cigaba kamar yadda na tsara. Nagode*

 

03

“Aseey we are dead” CY ya faɗa lokacin da suka shiga mota za su koma office.
“Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi”

“Dama kin fi kusa da MD ai”

“Kai ka san wannan”

Lokacin da su ka isa office Asiya ta ɗauka MD zai ma ta faɗa amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo.

Awa ɗaya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma’aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma’aikata kowa ya ji alert ɗin albashinsa.
Mintuna kaɗan bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa.
Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo.

Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin..

***

Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office ɗin MD. Tana gama karantawa ta wuce office ɗin sa da sauri.

“Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor”

“Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director”

“Sir???”

“Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs”

Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne.

“Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya ɗaukan mataki mai tsauri akan ki”

Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba.

“Shikenan Sir, nagode” daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta.
Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta ɗau jakarta ta bar station ɗin…

 

Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta. Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan.
Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne?

Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop.
Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd godiya.

“Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?”

“Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci”

“Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faɗa”

“Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba”

“Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi”

Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce ɗakin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan.

***

Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru.

A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba.

Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi.
Ya ƙara da cewa ” ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba”

Yallaɓai yai murmushi ya ce “Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya”

“Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya”

“Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi”

Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce “ni zan wuce”

Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa.

“Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse…”

Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu.

Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan…

 

***

 

Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa,
Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa.

“Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu” ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu.

“Hansa’u kenan”

“Hajja idan na girma ina son zama kaman ki”

Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa’u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana’a tunda ta ƙi auruwa. Hansa’u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce ‘yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba.

“Hansa’u Malamin Junior ya zo ko?”

“Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje”

“Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita”

“Hajjan mu a kawo mana tsaraba”

Hajiya Bilkisu ta ɗan yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta.

Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi.

Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar ‘ya’yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha’awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji.

Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu.

Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi.
Tun Bilkisu na ɗaukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi.
Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya a fusace dan ganin su waye su ka fita mutunci a wajen first lady ɗin, lokacin da ta juya first lady ce ke saukowa ƙasa biye da ita kuma Hajiya Hadiza matar Senator da Hajiya Kaltume matar Commisioner.

Hajiya Bilkisu ta bi su da kallon mamaki. Saboda waɗannan matan First lady ta zaunar da ita na tsawon awa uku.

“Ba ki tafi ba?” First lady ta faɗa da mamaki

Hajiya Bilkisu ta buɗe baki cikin kaɗuwa.

“Bilkisu Kachallah. Ashe ke ce ake ta damun First lady wai tana da baƙuwa”

Hajiya Hadiza kenan da wannan magana.

“First lady saboda waɗannan kika shanyani kaman kayan wanki” ta yi maganar tana nuna su.

“Tabbas saboda su kuwa. Bilkisu na ji duk abinda kika yi tun kafin na dawo amma ki sani ba zan lamunci hakan ba. Taron matan Gwamnoni aka ce za ayi ba na matan mataimakan Gwamnoni ba. This is the last time da za ki sake haɗa taro idan bana gari”

 

“Sai da muka gaya ma ta ta bari ki dawo kafin ayi taron nan amma ta ƙi. Wallahi matar Gwamnan Ekiti sai da ta gasa mana magana a wajen taron nan, kin san yarabawa ai”

“Ni! Ni ki ke wa munafurci Hadiza?”

Hajiya Hadiza ta juya kai tana tura baki.

“Ki tsaya iya matsayinki Bilkisu sai a samu zaman lafiya” First lady ta faɗa a fusace

Hajiya Bilkisu ta haɗiyi wani abu daya tokare mata maƙoƙoro.

“Nagode First lady. Dama na zo yi miki barka da dawowa ne amma na ga alama ba ki cancanci gaisuwar ba. Mu kwana lafiya”

Hajiya Bilkisu ta juya da sauri ta fice daga gidan.
A cikin mota danne ƙirjinta ta yi saboda yadda ya ke bugawa yana sukanta. Ba ta iya ɓacin rai ba dan tana farawa zuciyarta ke fara ciwo. Shekarun baya ance tanada hawan jini shiyasa ta ke kaffa-kaffa da duk abinda zai ɓata ma ta rai.

Bayan ta koma gida ba wanda ta kula ta wuce ɗakinta ta sa key sannan ta kwanta akan gado har lokacin ba ta cire hannu a ƙirjin ba dan ji take idan ta cire zuciyarta zai iya bugawa. Ƙarshe ta tashi ta ɗauko maganinta ta watsa a baki ta haɗiye zuwa minti shabiyar maganin ya fara aiki dan bugun ƙirjinta ya fara raguwa.

Idan ba ƙaddara ba da First lady da Hajiya Hadiza da ita Hajiya Kaltumen dukkan su babu sa’anta cikin su. Idan ba muƙami da mazajen su ke riƙe da shi ba babu wadda a cikin su ta taka ƙafarta wajen gata da daraja. *Bilkisu Sani Kachallah* ce fa. Waye bai san tarihin ahalin gidan Kachallah ba. Familyn Kachallah su ne da Jahar Congo gaba ɗaya.

Bilkisu Kachallah ba za ta iya tuna lokacin da bacci ya ɗauketa ba. Ta dai farka tsakar dare ta ganta kwance da kayan jikinta sai alokacin ta tashi ta cire kayan ta saka na bacci sannan ta dawo kan gadon ta zauna dan bacci ya washe a idonta, tunani kala-kala ta zauna yi har Asuba.

***

Shahidah na bacci wayarta ya hau ƙara. Ta sa hannu ta jawo wayar da ke gefen gado saura kaɗan ya faɗo ƙasa.

“Hello” ta faɗa da muryan bacci

“Mine kin tashi kuwa? Na kusa isowa fa”

“Ka manta anyi suspending ɗina jiya”

“Subhanallahi! Ok ok barin zo in gaida Abba sai na wuce office…” ai bai ƙarisa bama Asiya ta kashe wayar saboda baccin da ke cinta.

Da sassafiya Bilkisu ta shirya ta sauko ƙasa. Daga wajen dining room wanda ke haɗe da babban falon ƙasa ɗan ta Junior ya ƙwala ma ta kira “Mommy” ta juya da sauri tana maƙalawa fiskarta murmushin bogi wanda ya ɓoye ɓacin rai da ta ke ciki.

“My boy”

“A’a Nana yaushe kika dawo. Zunairah ya Maman ki?” Ta jera maganar tun kafin ta iso wajen su

“Mommy ina za ki sani kuwa. Jiya ina miki magana haka kika shareni kika wuce sama. Daga baya na je na yita buga ƙofar ki amma shiru ba ki buɗe ba”

“Sorry Dear, jiya na gaji ne dayawa”

“Miyasa Junior ke cin abinci shi ɗaya ina Hansa’u?”

“Hansa’u” ta ƙwala ma ta kira da ƙarfi

“Mommy Airah ce ta aiketa ta kawo mata boiled egg”

“Ok girls barin fita, idan Daddyn ku ya tashi ku ce ma sa na tafi Kachallah House”

Bayan tafiyar Hajiya Bilkisu sai ga Hansa’u ta fito da wani bowl ɗauke da ƙwai guda uku ta ajiye a gaban Zunairah.

Zunairah ta zaro ido ganin ƙwai da ɓawonsa a jiki sai tiririn zafi ya ke

“And what is this? N Luv kinga shirmen wannan crazy old fool ɗin ko?”

Nana ta kalli Hansa’u ta ce ” yanzu Hansa’u ita ki ke so ta cire ɓawon ƙwan kenan?”

“Ke ce ki ka ce na kawo shi kwili-kwili (quickly-quickly) kuma na ji Hajiya na kira shiyasa na kawo shi haka nan”

“Dalla je ki ɓare ƙwan ki kawo” Nana ta faɗa da tsawa.

Hansa’u ta ɗauke kwanon ta koma kitchen da sauri.

 

Hajiya Bilkisu da ta fito ba ta wuce ko’ina ba sai Kachallah House. Da ta shiga gidan ba ta wuce sashen kowa ba sai sashen mahaifinsu wanda ya ke gefe da asalin cikin gidan, a nan ya ke karɓan baƙin sa a nan kuma ya ke duk wasu harkokin sa. Sashen ya ƙunshi falo guda ɗaya da dining room sai manyan ɗakuna guda huɗu. Ba kowane ya sani ba amma ita Bilkisu ta san akwai falon sirri a gidan wanda Mahaifinsu ke karɓan baƙi na musamman inda ake yin meeting na tsakar dare a ciki.

Shekarunta shabiyar lokacin da ta gano ɗakin, ta je duba wani littafi a library ɗinsa ne hannunta ya danna wani switch a jikin bango sai gashi carpet ɗin wajen ya ɗage. Ba tareda tsoro ba ta leƙa wajen daya buɗe ɗin sai taga matakala ce a wajen. Ta sa ƙafa ta fara taka matakalar har ta nitse ciki dan falon underground ne. Ta san turawa na yin ɗaki ko basement a cikin ƙasa amma ba ta taɓa tunanin sashen mahaifin na su na da irin wannan ba. Falo ne Babba da ya sha kayan alatu fiye da ɗaya falon sai ɗakuna biyu wanda tayi-tayi ya buɗu ya ƙi buɗuwa shiyasa ma ta haƙura ta fito ba tareda ta ga abinda ke ciki ba.

Ta ci sa’a Baban na su na nan dan lokacin ne ma ya ke ƙoƙarin karyawa ga tulin abinci kala-kala da aka ajiye ma sa wanda aƙalla mutum shida za su iya cin abincin su ƙoshi sarai.

“Bilkisu” ya kira sunanta da mamaki.

Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe bakwai da minti arba’in da bakwai.

“Lafiya dai ko?”

“Lafiya Baba”

Bayan ya tambayi lafiyar mijinta da ‘ya’yanta sannan ya tambayi mi ke tafe da ita da sassafen nan dan yasan haka kawai Bilkisu ba za ta nemeshi ba.

“Saifu ne zai miki kishiya?”

“Baba idan kishiya ce ai da sauƙi. Baba tambaya na zo yi”

Alhaji Sani Kachallah ya suɗe romon kan rago da ke shirin gangarowa zuwa gwiwar hannunsa. Wani lokaci idan Mahaifinsu yai wani abun kamar wani faƙiri wanda ba shi da gata ko kaɗan. Yanzu miye na suɗe hannu?. Ta yi saurin kauda wannan tunanin a ranta ta maida hankalinta zuwa abunda ya kawota.

“Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?”

Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata.

“Wace tambaya ce kuma wannan?”

“Baba dan Allah ka amsa min tambayata”

Alhaji Kachallah ya kalli idon ‘yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce ” idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba”

“A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?”

Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe ya ɗaura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido.

“Babu yadda za’ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka ɗaura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar ma su zuwa sun yi nisa sosai”

“Bilkisu!”

“Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and…”

Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi.

Bayan fitar Bilkisu daga falon, Alhaji Kachallah ya faɗa kogin tunani. Ta ina zai fara? Akwai gaskiya a hasashen Bilkisu dole ne ya san yadda zai yi ya shawo kan matsalar tun kafin lokaci ya ƙure a juye ma sa baya.

***

“Miyake faruwa naga kwana biyu ba kya fita”

SSK yai maganar yana zama gefen gadon Bilkisu tareda kissing goshinta.

“Ba na jin fitan ne kawai. Ina buƙatar hutu ne ma”

“Nima ina buƙatar hutun nan Allah. Inaga tunda Gwamna ya dawo why not mu je UK hutu ko da na sati biyu ne?”

“Its a good idea gaskiya. Muna buƙatan hutun nan sosai” ta yi maganar tana murmushi.

SSK bai jima da fita daga ɗakinta ba wayarta ya hau ruri. Madam Bintu ta gani a jikin screen ɗin hakan ya sa ta faɗaɗa murmushinta. Ta yi saurin ɗaukan kiran tana faɗin ” mutanen Turkiyya kin shigo kenan”

Daga ɓangaren Madam Bintu ta ce “na shigo jiya da dare zan shigo wajen ki anjima”

“To sai kin zo”

Ƙarfe biyar da rabi sai ga Madam Bintu a gidan ta. Hansa’u ta kira ta kawo musu abin taɓawa.

“Har yanzu ba ki rabu da wannan matar ba bayan shirmen da ta yi kwanaki”

“Bintu tausayi ta ke bani Allah. Besides yanzu ta iya aiki sosai ba kaman farkon kawota ba sai dai ba a rasata da shirme kam. Most importantly tana sani dariya and that’s help alot ga mu ma su hawan jini”

“Ok” ta faɗa tana ƙarewa Hansa’u kallo. Gani ta ke kaman idon matar na mata kama da wacce ta sani amma ta rasa gano ko wacece.

Bayan Hansa’u ta bar wajen Madam Bintu ta tambayi Bilkisu yadda taron matan Gwamnoni ya kasance dan lokacin da aka yi taron ba ta ƙasar.

“Ba abunda zan ce miki Bintu sai dai in ce kawai taro yayi kyau. Kuma za a sake wani taron nan ba da daɗewa ba”

Madam Bintu ta kalli Hajiya Bilkisu cikin rashin fahimta, maimakon ta mata ƙarin bayani sai kawai ta fashe da wata ƙasaitacciyar dariya.

 

**
A chan gidan Yallaɓai kuwa Chief of Staff (COS) ɗin Gwamna ne a gaban Yallaɓai yana ma sa bayani mai mahimmanci wanda ya sa Yallaɓai nitsuwa na ban mamaki. Har ya gama bayanin Yallaɓai bai ce komai ba sai ma murza gemunsa da ya fara yi a hankali.

Ba kasafai ya ke samun ma su taurin zuciya irin ta KACHALLAH ba. Shekaru da dama an taɓa yunƙurin aikata irin wannan abu sai dai kuma komai ya zo ya chanja a ƙurarren lokaci.

“Ka haɗa meeting da Kachallah cikin satin nan” Yallaɓai ya faɗa bayan yayi dogon nazari.

COS yai murmushin gefen baki dan ya san yanzu liyafa za ta cigaba. Ya ƙwallafa rai sosai akan Gwamna Saminu Bacchi sai dai cikin shekaru uku da yai a kan mulki sun samu saɓani sosai domin lokacin da idon Gwamna Saminu ya buɗe da kuɗi sai ya zamana yana ƙoƙarin take duk wata hanya da su suke yagan rabon su, yanata wawure komai shi kaɗai da iyalin sa ba dan Yallaɓai ya tsayar ma sa ba wasu abubuwan haka za su dinga wuce shi.

Saifuddeen Sa’ad Kachallah daban ya ke da Gwamna Saminu, kuɗi ba za su ruɗe shi ba. SSK ya gaji arziƙi irin arziƙin da ko da ba zai yi wani aiki ba zai isheshi ci da iyalen sa har iya karshen rayuwar su ba tareda sun yi talauci ba.
SSK shine mafita a gareshi da shi da KACHALLAH.

***

“Wallahi an cuceni Ya Ubayd. MD mugu ne wallahi”

Ubayd yai murmushi ya ce ” ni kam ya min dai-dai, dama daurewa kawai na ke yi amma kullum aka nunaki a TV sai na ji kamar zuciyata za ta fashe”

“To ta Allah ba taka ba. Sai an maidani reporting unit”

“Ina kishin ki Asiya na haƙura ne kawai saboda babu yadda zan yi amma Allah idan ki ka shigo gidana ba za ki sake bayyana a TV ba, ko dai ki tsaya aiki a bayan fage ko kuma ki haƙura da aikin”

“Ya Ubayd you are joking right”

“I’m not Asiya. Gara ma ki saba da inda aka kai ki yanzu”

Sati ɗaya da suspension ɗin ta aka kirata akan ta dawo. Yau ta fara fita aiki amma duk ta ji ba daɗi ba ta son ɓangaren da aka kaita ko kaɗan.

“Ya Ubayd ba haka mu ka yi da kai ba baka ce za ka rabani da aikina ba”

“Ba rabaki zanyi da aikin ki ba na dai ce bayan munyi aure ba ƙaton da zai sake ganin ki a TV yana ƙare miki kallo especially with irin shigan da ki ke yi” yai maganar da ɗan ƙarfi

Asiya ta miƙe daga kujeran da ta ke zaune ta ce “ba ka isa ba kuwa”

Ta wuce ta barshi a wajen baki buɗe.

Washegari ko jiran sa ba ta tsaya yi ba ta hau keke ta wuce office…

 

***

” na gaya miki babu kuɗi a ƙasa, duk wani abu da zamuyi yanzu mutane za su yi magana. We need this year to work on something saboda campaign da za a fara nan da watanni huɗu ma su zuwa”

Gwamna Saminu Bacchi kenan yana ƙoƙarin lallashin matar sa.

“Kana so ka ce min ba ka da kuɗin da zamu celebrating 8years anniversary na mu?”

“Ba wai ba kuɗin bane amma kuɗin campaign ne”

“Kar ka gaya min magana dan Allah. Uban me Saifuddeen Kachallah ke da shi da zai iya celebrating 15yrs anniversary na su a tsakiyar teku shekaru biyu da suka wuce. Na je party ɗin fa. Sati biyu aka yi a cikin jirgin ruwa wanda komai da komai da mutanen ciki su ka yi yana wuyan sa”

“Sha’awanatu. Saifuddeen Kachallah millionaire ne tun kafin mu hau gwamnati ko mi zai yi ba wanda zai zargeshi amma ni…”

“Ba zan yadda ba fa. Dole ne ayi anniversary party namu a Italy. Wallahi kai ka ke sawa ma Bilkisu Kachallah tana raina ni. Ina matar Gwamna amma ko motan da ta ke hawa tafi tawa”

“Yanzu kinsan ya za ayi ne? Za mu yi party amma a nan Nigeria. Bamu jima da dawowa daga ƙasar waje ba idan muka sake fita mutane za su yi magana…”

“Wai ina ruwanka da mutane ne. Kai fa Gwamna ne. Gwamnar jahar CONGO wancan tafiyar Asibiti ka je wannan tafiyar kuma yana cikin yiwa iyalinka hidima ne”

” Amma Sha’awa…”

Daga haka Gwamna Saminu Bacchi ya haɗiye sauran maganar sa saboda haɗe bakin su da Sha’awanatu ta yi.

Washegari da safe Gwamna ya tashi da wani irin ciwon kai da ciwon ƙirji, ciwon ne ma ya tashe shi daga bacci tun ƙusan ƙarfe huɗun Asuba.

Wasa-wasa har ƙarfe shida jikin ba sauƙi duk da kuwa ya sha magungunan sa.

“Za mu wuce Asibiti ne ko a kira maka likita?” First lady ta tambaya cike da fargaba.

“Ki kira Likita” ya faɗa da ƙyar saboda yadda ƙirjinsa ke takure.

Bai kai awa ɗaya ba saiga likitan sa ya iso koda ya duba shi cewa yai jinin sa ne ya hau sosai idan akwai wata damuwa da ke ransa to yai ƙoƙarin kauda ita dan abunda ya sa a ransa ka iya jawo ma sa bugawar zuciya.

Shi dai ya sani bai sa komai a ransa ba. Ba a fara campaign ba balle ya ce shine ke ɗaga ma sa hankali. To kodai Barasar daya kwankwaɗa jiya da dare ne? Duk da likitan sa na chan Germany ya hana shi shan barasa. Duk da kuwa ya san ba zai iya dena sha ba, sai dai ya rage sha ba kamar da ba.

Allura da Likitan ya ma sa ya taimaka ma sa sosai dan har ya samu yayi bacci. Lokacin da ya farka kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe.
Sha’awanatu ta taimaka ma sa yai wanka ta kawo ma sa abinci har kan gado amma bai iya ci ba sai shayi kawai ya sha.

Ƙishirwar giya ce ta dameshi dan duk da yana jin jiki yayi amanna idan ya ɗan kurɓi kaɗan zai samu sauƙi. Fita yai daga ɗakin Sha’awanatu ya wuce na sa ɗakin a nan ya fito da kwalbar giya ya kwankwaɗa ya girgiza kai ya sake kurɓan kaɗan sannan ya mayar da sauran ma’ajiyar sa.
Shiryawa yai ya fita saboda akwai meeting da zai yi da wasu contractors ƙarfe biyu na rana.

“Yanzu yadda baka da lafiya haka za ka fita?”

“To ya za ayi dole ne mu yiwa talakawa aiki”

“To. Amma ka dai yi tunani akan abinda na ce”

Dariya Gwamna ya fara yi sai kuma ya dafe ƙirjinsa saboda yadda ya ji ƙirjinsa na suya kaman an saka masa wuta.

“Your excellency jikin ne?”

Kafin ta ƙarisa maganar Excellency ya kai ƙasa.

“Your excellency, miya faru? Ƙirjin ka ne?”
“Waye a nan? a kira likita. Excellency… Saminu…Saminu ka tashi”

Lokacin da aka garzaya da Gwamna Asibiti ya riga ya cika likita ya ce zuciyar sa ce ta buga (cardiac arrest)…

***

Mataimakin Gwamna na zaune a office Chief security officer ya kira shi, kiran da ya ɗaga ma sa hankali sosai dan kuwa a kiɗime ya fice daga office ɗinsa ya wuce Asibiti.

Mummunan labarin da aka gaya ma sa a waya shi ya tarar a wajen domin kuwa Allah yayiwa Gwamna Saminu Bacchi rasuwa.

A chan Kachallah House kuwa Alhaji Sani Kachallah ne ke waya da mijin ‘yar sa wato Saifuddeen wanda ya jaddada ma sa mutuwar Saminu Bacchi.

“Mi aka ce ya kashe shi?”

“Baba ba zan iya cewa komai ba yanzu”

Alhaji Sani Kachallah ya ce “ba komai zan kiraka anjima”. Yana kashe wayar ya shiga kiran numbar Yallaɓai.

A chan gidan mataimakin Gwamna kuwa Bilkisu Kachallah ce zaune a falo tana cin gasashshiyar kifi da soyayyen dankalin turawa haɗe da lemo mai sanyi.

“Hansa’u, Hansa’u ” Hansa’u ta fito da gudu.

Miƙo min remote ina son kallon news.

Hansa’u ta miƙa ma ta remote ɗin Bilkisu ta chanja channel daga Zee world zuwa Congo news…

***

Asiya Shahidah na zaune a sabon office ɗinta tana aiki akan computer abokin aikinta Ɗahiru ya shigo office ɗin da sauri.

“Shahidah kin san labarin dana ji kuwa daga fitata a office ɗin nan?”

“Miya faru?”

“Yanzu Abigail ta ke kawo rahoto cewa Gwamna ya rasu”

“Wani Gwamnan?”

“Gwamnan Congo mana”

“Innalillahi! Dan Allah?”

“Allah kuwa”

Asiya Shahidah ta miƙe ta bar office ɗin da sauri…

 

Kusan awa ɗaya da rasuwan sannan Mataimakin Gwamna kuma acting Gwamna ya bada sanarwan mutuwar Gwamna Saminu Bacchi.

*”Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’oun. Haƙiƙa dukkan mai rai mamaci ne. Muna yiwa Jahar Congo ta’aziya bisa rasuwan Mai girma Gwamna Alhaji Saminu Bacchi wanda Allah yai wa rasuwa yau shabakwai ga watan Nowamba. Haƙiƙa wannan jaha ta yi babban Rashi”* hawayen da ya zubo ma sa yai saurin sa hankerchief ya goge sannan ya cigaba da bayani
*” Insha Allahu za ayi jana’izar sa a gidan gwamnati da ƙarfe biyar na yamma”*

Asiya Shahidah da ke kallon news ɗin a talabijin da ke office ɗin su CY ta ce “Ikon Allah har da kukan munafurci kaman bai ji daɗin abinda ya faru ba, Shege. Ai yanzu kam jahar nan ta shiga uku a hannun wannan Wawan”

A ɓangaren Yallaɓai kuwa yana gama kallon bayanan da SSK yai ya danna remote ya kashe T V sannan ya kai duban sa ga Kachallah ya ce

“To kyan alƙawari dai cikawa. Ina fata Saifuddeen zai bamu haɗin kai”

“An gama Yallaɓai”

Yayinda wasu ke cikin baƙin ciki da rasuwan Saminu Bacchi wasu kuma na nan suna planning yadda za a juya Gwamnati.
Duniyar kenan. Tunma kafin a sa shi cikin ƙasa har an riga an cire shi daga lissafi.

Da ‘yan siyasa za su dinga tunawa da cewa akwai ranar da dukiya ko matsayi ba zai amfanesu ba ƙila da za su tausayawa talakawan su.

 

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]