[Advertisements⬇️]

MATAR POLICE COMPLETE - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA SHIMA TA NUMBER._

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 1/2_*

****************
************
******************

Wata yarinya na Hango yar kimanin shekara Tara ta na ta kokarin danewa bishiyar mangoro.

Wa su yara sa’anninta da ke kasan ta ne daya daga cikin su ke fadin, “Ke Jidda ki yi sauri fa kar Mallam Mudi ya zo , ya ganmu.”

Tsayawa ta yi da hayewa bishiyar ta joyo ta kalleta, ta galla ma ta harara kan ta ce, “Yoo ya zo ma na, ai bishiya ta kowace ba wai Dan ya ganta cikin gonarshi ba, ke Wallahi ma inna so sai na fito cikin dare na sassare bishiyar nan.”

Tsaki ta yi ta Dane saman bishiyar abinta, mangoro ta fara tsinkowa ta na mika mu su banda masifa ba abin da ta ke yi, wallahi in kuka barmin mangoro daya ya fada kasa na ga kwarzane ko dayane hum hun yara za su yi kuka Yasin.”

Ta na cikin masifar nan sai ga Mallam Mudi ya nufosu ya na yar wakarshi.

Jidda ce ta fara lura da zuwan shi hakan ya Sa ta saurin fadin, “Lantana, Indo, Ku kai min mangorona wajen IYA ga Mallam Mudi nan.”

Ai kuwa gudu su ka fara me naci ban ba ka ba, Mallam Mudi kuwa daga idon da zai yi Sai ga Jidda rashe-rashe a kan bishiyar shi.

 

Dirka tai da gudu garin binta ya fadi juyowa ta yi ta ma Sa gwalo ta ce, “Hhhh indai ni mutum zai bi ai Sai dai ya karye.” Ta na dariya ta cigaba da gudunta har ta shige gida.

Ta na shiga , “IYATAAAA ina ki ke? Ina su Lantana da Indo kar dai ba su kawomin mangorona ba.”

IYA ta fito ta na, “Oh Ni Kulu banga kowa ba agidannan tin da ki ka fita.”

Kama kugu Jidda tai ta ce, “Kambu…. To Wallahi yau da masifa akarkarar nan da alama sun manta halinane ko, na fi su iya shege, ni da wahala su da ci tab-di-jan yau sun taro bala’i.”

Fita kawai ta yi fuuu kamar wani jirgi ai ko ta na bin bayan layi Sai ga Su Shatu da Lantana, kallon su tsaya yi ta na girgiza kugu , “Ai na aza kunci gadone in malafar gidanku aradu.”

Indo ta ce, “Aa fa mun bi ta nan ne sabode kar Malam Mudi ya kama mu.”

Tsaki ta yi ta ce, “Naji to kuzo mu koma gida.”

A girme ba su girmeta ba, ajiki kam Lantana da Indo sunyi biyun Jidda Amman hakan ba ya sa Jidda jin tsoron tabasu ko yi ma su masifa inta kamama har mari ta ke ma su ,gashi bala’in tsoronta su ke, kamar mala’ikarsu.

Suna shiga gida IYA ta ce, “To ‘Ya’yan albarka mangoro a ka samo kenan.”

Harara Jidda ta galla ma ta, ta ce, “Yasin gwandama ki kama chakon bakin nan na ki Dan ba sha zakiyi ba.”

IYA ta bude baki za ta yi magana kenan Sai gashi an bankado kofar galan-galan kamar za ta fice, Mallam Mudi ne tsaye ya na huci, ya ce, “Wallahi Sai kun ba ni mangorona da kuka Sa ta.”

Jidda ta kalli shi ta ce, “Jan… Cha…. Suwaye bara yin da zasu ma Satan ma to? IYA Wallahi ki ma Sa magana ya fitan ma na agida.”

IYA ta daura hannun aka ta na fadin, “Oh ni kuluwa jikar Adam ni ban San me yar jikata ta tare ma Ku ba a garin nan kowa ya tsaneta daga Wannan ya ce ta yi kaza sai kaza to ahir din ka Wallahi tin kan natarama jama’a ka fita agidannan ko intsinema, intsinema mahaifinka kai har ma kakanka da kakan-kakan ka.”

Mallam Mudi ya San sarai IYA za ta aikata abin da ya fi hakama kan jikarta, Yanzu sai ta kala mai sharin da bai isa ya kwaci kan shi ba, hakan ya Sa shi saurin fita agidan batare da ya kara fadin uffan ba.

Jidda ce Ta kalli IYA su ka kyalkyale da dariya tare tafawa kamar wasu kawaye.

IYA ta fara mamulan baki ta ce, “Yo Yanzu dai asammin Mangoron ko?”

Jidda ta hada girar sama da kasa ta ce, “Yasin Dan fi zan millira mi ki, Ku koma Indo,da Lantana Ku dauki daya Ku raba ajiyemin saurana.”

Acikin mangoro kusan goma sha haka suna gani ba yadda su ka iya suka dauki dayan nan,domin sun San Jidda sarai intaso ma dayan kwacewa za ta yi ta ce kwalelensu ai ba Babansu ba ne ya tsinko ma ta.

Daukan daya tai ta raba gida biyu ta bawa IYA mai kwallon ta ce, “Gashinan Yasin bazaki sha da yawa ba ki ta zabgawa mutane guduwa ki cika mana gida da dauyin kashinki.”

IYA ta yi tsaki kan ta ce, “Dadinta dai duk warin kashina bai kai na ki ba ehww Ku ma in kika yi wasa sai in fadawa Babarki abin da ki ke min.”

Jidda ta zaro ido, , “tab Wannan muguwar Yi Hakuri IYATUNA mai kan tumatur shanye Wannan ma in kara mi ki, ai ni ko Birnin ma bazamu Kara zuwa ba bare ta ganni ta jibgeni.”

Suna gama kwamusar mangoron nan Su ka fara wasansu IYA na gefe ta na kallon ikon Allah ba abin Jidda ta yi ba dai-dai ba ta na mata magana za ta hauta da masifa kamar uwarta.

 

Washe gari da sassafe Jidda ta fara kwaskwarima.
Iya ta ce, “Jidda ga ruwan wanka fa nan ina dafa mi ki kinsan rabonki da wanka tin shekaran jiya.”

Jidda ta ce, “To wai dole ne yin wanka? Kinji birni sun koya mi ki Wannan iya yin yin wanka kullum ko? To nidai Wallahi ban yi datti ba, Dan haka ba wankan da zanyi kuma ma yanzu kwalliya Zan yi kan su Indo su zo mutafi kasuwa.”

Haka Iya ta ja bakinta ta yi shiru Domin tasan ko ya za ta yi da Jidda ba wankan nan zatayi ba daga karshe ma sai dai tasa ma ta kuka.

Ta na gama kwaskwarimar nan ta doko basilin ta milka ajikinta sannan ta janyo ledar kayan kwalliyarta Foundation ta fara milkawa afuska kamar ta na gini sannan ta biye shi da farar hoda, ta na shafawa ta na fadin, “Iya yau irin kwalliyar Anty Mariya zan yi, lokacin da mukaje haka naga ta na yi.”

Iya ta ma ta shiru, tsaki Jidda ta yi ta ce, “Yoo kar ma kiyi maganar mana Allah mai da koko masaki tinda so ki ke ki kurmance.”

Ta cigaba da kwalliyarta dauko bakin kwalli ta yi ta maka agirar sannan ta dau irin asalin Jan bakin nan ta maka asaman ido da baki.

Kallon kan ta ta ke amudubi ta na gyatsine fuska, “Oh Ni Jiddatu Ikon Allah, kyau iya ka kyau sai dai hassada aradu, nafi karfin mazan karkarar nan, jibi yadda bakina ya ke wani kara kyau, kai anya ma zan fita kuwa Yau Dan nasan mazan karkarar nan irin su IRO har suma ma za iya yi.”

IYA ta juyo ta kalleta ta kyalyale da dariya.

Jidda ta galla ma ta harara ta na, “Ni nasan kishi ki ke dani daman ai kuma Wallahi na fiki kyau ko Anty Mariya ma Dampol kon (dimple Queen) ta ke cemin.”

_Hhhh su Jidda Dampol kon an kashe kala_

Ta na cikin yiwa Iya masifa sai ga su Indo da Lantana, Indo ta rikye baki ta ce, “Jidda Dan Allah nima kimin irin Wannan kwalliyar kinga daman in munje kasuwa Umaru ya ce zamu hadu.”

Lantana ma ta ce, “Ni ma Dan Allah kimin irin kwalliyar da yan birni su ke yi ne fa.”

Jidda ta gara ma su harara , “ysin bazan yi aikin banza ba inna ma Ku kunyi alkawarin za Ku goyani har zuwa kasuwa?”

Da saurin su sukace , “Eh.”

Jidda ta fara ma su kwalliya anayi ana zungure ma su fuska, “ke ni dalla ki tsaya in miki Abu mai kyau duk na bi nagaji kwalliyar nan wahala gareta daga yau Indo ba zan Kara mi ki ba si ranar aurenki da umaru, wallahi fa ki tsayamin ko waskeki da Mariya kina nan da fuska kamar tuwon dawo.”

Haka ta chacchaba ma su fuska kamar tsofaffin aljanu kan ta ce, “To maza Yasin tin daga nan Lanta ki fara goyani.”

Haka kuwa akayi lantana ta goyeta abaya har kasuwa suna zuwa……

 

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 5/6_*

****************
************
******************

_Xayyeesherthul-humaerath fans group ba na ganin SHARHI fa_

_*Wannan shafin na Ku ne Ku kadai Doty hauwa Sulaiman kawar Jiddatu dompol ko tare da grannyna Mariya, Masu son farantamin dole nima na so faranta mu Ku can’t love you less*_😘😘❤️❤️

Iya ta kalleta cike da tebe baki ta ce, “Yo ai sai ki yi ta yi tinda dai ke bakin koshi ba arayuwarki.”

Tashi Jiddatu ta yi ta na saka takallemin ta tare da sude hannu ta ce, ” Nikam natafi gidan su Lantana Da Indo nasan watakil ba su ci abinci ba yanzu, zanje in tayasu ci.”

Iya ta yi tsaki ta tashi ta na, “Yo kyaji dashi dai.”

Fita tayi tana tsalle tsallenta tare wakar , “Jiddatu Tauraruwar mata nan gani nan bari dumamen mayya, Jiddatu Dompol kon.”

Hankalinta kwance ta na ta wakyenta wani yaro ta gani ahanya ya na tallen gyada ta ce, “Kai Mudi zo nan.”

Tawowa ya yi gareta.

Daffafiyar gyadace hakan ya sa fara dubawa ta na, “Wannan gyadar ta Ku ma ai duk ruwa-ruwane ka ga ni ba zan siya ba sai na dandana naji ko zan iya ci.”

Mudi ya ce, “Eh ki dandana guda biyu.”

Zaman dursham Jiddatu ta yi ta janyo mudi ma ya zauna, gyadar ta fara ci ta na to far da yawu, “Kai Wallahi Wannan ruwa-ruwa bara na gwada wa su.”

Da haka haka har ta kusan cinyewa.

Abin ka da yaro mai wayo ya ce, “Taf kin fa kusa cinyewa to wallahi ki bani kudina daman na Muttala biyarne kuma kin cinye na muttala uku.”

 

Jiddatu ta mikye ta na gyara jikinta ta ce, “Iye? Ruwa ruwan zan siya wallahi ba zan biya ko ficika ba.”

Mudi ya rikyeta kamar zai yi kuka.

Fincike shi ta yi ajikinta ta fara dukanshi ta na, “Ku ji min yaro da rainin wayo ni yaushe naci gyadar da zan biya ka zauna ka cinye abin ka za ka min sharri to Wallahi ba ka isa ba.”

Da taga yana kokarin fara rama dukan da gudu ta zura ta na yi mishi gwalo shi ko Mudi kuka kawai ya fara awajen ya tuna irin masifar ta mahaifiyarshi da zai tarar.

 

Gidan su Indo ta gutsa aguje, Innar Indo ya daka sai da ta hankade ta daga ita har turmin sai ga su akasa, maimakon ta tausayama mata ko ta ce ma ta sannu sai Jiddatu ta bige da dariya ta na, “Wayyo Allah na Ga Innar Indo a kasa, Indo fito kiga innarki tin kan ta tashi.”

Rikye ciki tai ta na dariya abinta hankali kwance.

Zura ma ta Ido kawai Innar Indo ta yi ta na, “Allah ya shiryeki Jiddatu ki Yarda ni kuma ki bige da yi min dariya.”

Tsuru-tsuru Indo ta yi domin tasan ta na yin dariya innarta ta za fara jibgarta ita ko Jidda tasan ana tabata an taba bala’i.

 

*****Mudi kuwa gida ya nu fa ya na kuka ya sanar da Mahaifiyarshi Kande masifa ai ko tuni ta fara balbalin masifarta ta ja shi gun mai gari domin tasan ko taje gun Iya sai dai ta gama masifar ta Amman ba abin da za ta iya yiwa Jiddatu.

Mai gari ya sa Mudi ya je ya nuna inda Jiddatu ta yi, ai ko ya nuna gidan su Indo.

Sallama waziri ya yi Baffan Indo ya fito a ka sanar da shi Jiddatu ake bida bai yi mamaki ba domin yasan Jiddatu ba Wanda ta bari a karkararnan.

Jiddatu na jin cewa mai gari na nemanta tasan cewa Kande masifa ce ta kai kararta ba karamin tsorata ta yi ba da ka ganta zakasan cewa a tsorace ta ke jijiyoyin wuyan nan duk awaje, Tuni ta fara fitsari tana tafiya ya na kwarara, Domin Da kyar Baffan Indo ya fito Da ita daga ban daki.

 

Suna zuwa fada ta fara kuka ta na ni fa sharri ya min na fada ma Ku sharri mudi ya min ni ko cin gyadarshi ma ban yi ba, kuma gyadar ma duk ruwa-ruwa ne, na fada ma Ku Wallahi ban ci ba mai gari ka min rai.”

Tsawa mai gari ya ma ta Wanda sai da ya sata kara yin wani fitsarin nan ta ke ya ce, “Hauwa’u waye ne wai bai San halinki ba duk karkarar nan , nasan za ki iya abinda ya fi haka ma akkala in ba akawomin kararki arana sau goma ba to za akawo sau biyar, Amman ina daga miki kafa sabida Kakarki hakan bai miki ba to wallahi yau ba Wanda ya isa ya hanani ladabtar da ke domin rigimarki ta yi yawa kowa akauyen nan bai da matsalar da ta wuce ta ki.”

Rawa jikin Jiddatu ya fara.

Mai gari ya sa aka kirawo Mai hukunci da zabgegiyar dorinarsa.

Ganin wannan dorinar ya sa ta tuna wani labari da Iyarta ta taba bata na Karyar Aljanu, sannan kuma ta kara tunawa fa ba abin da mai gari ya tsana fiye da mutuwa.

Faduwa awajen ta yi ta na birgima, ” *Diyar mu ce karku taba ma na ita duk wanda ya taba jiddatu ya tabo bala’iiiiii, masifaaaa, jaza’iiiii.”*

Mai gari ya yi tsaki kan ya ce, “Wannan ai iskanci ne Sarkin Hukunci hukunta min ita ai ni nawa aljanun ma sun fi karfin na ta.”

Jiddatu ta kara kwarara wani ihu da sai da ya ba za ilahirin karkarar ta ce, “Karku tabata in kuna so Ku tsira da rayuwarku, na fada ma Ku karku taba Jiddatu mai gari rayuwarka ta na cikin hatsari kana daf da barin duniya barin Jiddatu tai abin da ta ke so shine kadai zai kawo tsira ga rayuwarka, maigari Wallahi sai mun kashe ka Indai ka taba diyar mu baxamu lamunta ba Daren Yau za ka bar duniya, yuuuui,hiuuiu,woooo, wiii Wallahi sai ka mutu ma kawai.”

Sai ga maigari na zufa ya cire rawani tare da saukowa kasa ya na, “Dan Allah Ku yi hakuri Ku bar ni da rayuwata Wallahi ba na son mutuwa ko kadan gashi na zalinci yan karkarar nan ban nemi yafiyarsu ba Dan Allah ku yi hakuri daga yau bazan kara ko kallon hanyar da Diyarku ta bi ba bare in kulata na tuba Ku yafeni.”

maigari Hadda guntun hawaye ya na rokon Jiddatu ta barshi da rayuwarshi.

Wata irin dariya ta fara ta fasa ta na fadin, “karaso nan na ce ma ka zo.” Cikin tsawa ta ke maganar.

Jiki asanyaye ya karasa gareta kai akasa.

Shafa kan shi ta farayi sannan ta dago da fuskarshi ta na ja mi shi gemu ta ce, “Wuiii wiii Allah ka zaunar da tsohon nan aduniya har sai lokacinsa yayi, Amman da zaran rana daya ya taba mana diyar mu ko da kuwa bata mata rai ya yi ba makawa wannan ce ranar shi ta karshe aduniya.”

 

Jiki na rawa ya ce, “Insha Allah hakan ma ba zai faru ba nidai Dan Allah Ku bar ni da raina.”

Kwatsam sai ga Iya burun-bururun sai masifa ta ke ta na fadin, “Wallahi Yau sai in tsinewa maigarin nan, in tsinewa babanshi, in tsinewa kankanshi kai har ma da kakan kakanshi wai mu za agwadawa iskanci atabamin jiki azauna lafiya, to wallahi sai in sallah in roki Allah ya sa adaina ruwa agarinnan na shekara guda.”

Da sauri maigari ya isa gareta yana, “Iya Wallahi ba mu mata komai ba mutanenta ne sukazo yanzu ki tayani ba su hakuri.”

Kallo Daya Iya ta yiwa Jiddatu tasan cewa wannan iya shegene kawai daya daga cikin Wanda ta ke koya ma ta.

Tsaki ta yi ta na, “Yo ai kai ka ja daman mu har ma za akoya mana iskanci ne ai sai dai mu mukoyar in ka na son zaman lafiya to ka fada wa yan garin nan kaf su fita harkar jikata ko ko nai Addu’ar rashin ruwa.”

Daura hannu ya yi akan shi ya na fadin, “Wa innahu sulaimanu wa innahu sulaimanu Ashe dangin Aljanu mu ke tare da su ni kam dai Dan Allah Ku yafemin nadaina daga yau andaina wallahi.”

Iya ce ta karasaga Jiddatu ta na tafo ma ta yawo tare da surutan da ita kan ta batasan me ta ke fadi ba.

Jiddatu ta yi wata attishawa ta na fadin, “Dan Allah kar Ku dakeni ni banci ba fa.”

_*hhhhhh lallai ma Jiddatu ku ga iya shege tamkar ba ita ba.*_

Iya ta kafta ma ta I do ta na fadin, “Yo ma ba na tsine ma su ba, tashi abinki kinji mu tahi gida.”

 

Suna tafiya mai gari na binsu ya na Jiddatu ta yafe mishi, wayencewa ta yi kamar batasan me ake ba ta ce, “Iya wai menene? Ni fa ba na son ganin tsohon nan kice mi shi ya tafi.”

Iya ta ce, “Maigari karkaji komai ai ka tsira tafi kawai tin kan ta birkice.”

Da gudu maigari ya bar wajen ya koma fada ya hana haki sai zufa fifita kawai ake yi mishi ya na hamdalal Allah ya taimake shi.

Jiddatu da Iya na shiga gida…….

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 3/4_*

****************
************
******************

Kan su shiga ciki Jidda ta ce, “Ke tsaya in sauka anan, bari kiga yadda za mu na tafiya, kun San ni dai ban son raini, Dan haka dole muna tafiyar yan matan birni, bari kuga Yadda Mamana a birni ta ke tafiya.”

Tafiya Jidda ta farayi tana harde kafa kamar agwagwa sai wani rangwada ta ke tana fari da ido abin ka da mutum kamar tsinke ta na tafiyar kaman za ta fadi,

Ta cigaba da fadin, “muna daga daki ni da Iya muna lekyota in fada mu Ku har wani rangode kai ta ke fa.”

Indo ta ce, “Ke kan kinji Dadi Mamanki yar birni, Jidda mu ma yaushe za ki kai mu gidanku na birni.”
Jidda ta yi tsaki, “Tab ni ai bazan kara zuwa ba, bayan dukana Mama ta ke ga masifa tab Ni ko bikin Anty Mariya ma ban zuwa duk yan gidan fa masifaffu ne.”

Lantana ta ce, “ni kam dama nice ai tuntuni zan koma can da zama.”

Jidda ta ce, “Ai sai kuyi ta yi ni nan ya fi min dadi, kunga kuzo mu fara tafiyar nan tin kan na manta.”

Su Ku fara shiga kasuwa, wajen wani mai goriba Jidda ta tsaya tana kifta mi shi ido.

Abin ka da Dan karkara anga yan mata mai kwalliyar yan birni tuni ya birkice sai kallonta kawai ya ke.

Ita kuwa Jidda kara wani rankwashewa ta ke tana, “Gaskiya Gorubar nan za ta yi zaki fa, bara in fara dandana Wannan muji.”

Daya ta dauka ta fara ci ta ce, “Kai Gaskiya da zaki sosai Indo, lantana kuma ku zo Ku zabi na Ku.”

Da sauri su ka karaso su ka dauko daddaya ita ko Jidda ban da Wanda ke hannunta sai da ta kara diban manya guda uku.

Nan fa Mai Goriba hankali shi ya fara dawowa seti ya ce, “To Yan mata kudin fa.”

Jidda ta kyakyale da dariya kan ta ce, “Kudi kuma? Ai ka kalli rabonka, tinda ka kwalla min Ido ai ba a banza za ka kalli kwalliyar Dompol kon ba.”

Mai goroba ya ce, “Dan Allah Ku ba ni kudin ba nawa ba ne na ajiya ne fa.”

Da ido Jidda ta yi ma su Indo magana sannan afili ta ce, “Ku je gun IYA Ku karbomin kudin in bawa Wannan mayyen.”

Su ka tafi abin su.
Ita ko ta kara dumbuzan guda biyu ya zama shida kan ta zura aguje, ba abin ya bita ba azo a kwamushe sauran kawai hawaye ya fara ya na, “Allah ya isa Wallahi ni dai ban yafe ba , Wannan yarinya akwai mugunta Allah zai sakamin.”

Jidda da su Indo ko na labe ban da dariya ba abinda su ke yi mi shi.

Jidda ta ce, “yauwa Ku zo muyi gaba abin mu saura Addu’Ah Dan na jima ban sha ba wallahi.”

Sai ga Umaru na washe baki ya ga masoyiyarsa da kawayenta, da sauri ya karaso garesu shi da abokinsa Adam.

Lantana sai wani fari ake da ido anga masoyi.

Ta na saurin domin karasawa garesu, Jiddatu tai ma ta wata tsaya, “Dalla chan ki tsaya ya karaso wawiya kawai Ki ja ma sa aji mana haka yan matan birni su ke, na alama yau in mu ka koma gida sai na koya mi ki soyayya yadda naji yayata na yi intana waya.”

Lantana dai ba da son ranta ba ta tsaya har su Ummaru su ka karaso.

Ummaru ya ce, “Ah Su Jiddatu manya kenan Yau anshigo gari, .” kawar da kai Jidda ta yi ta na, “Eh fa munzo gaisuwa ne.”

Lantana ta ce, “Wato shine jiya ka ki zuwa ko?”

Ummaru ya ce, “Haba Lantana kema kin San dai anfara shirye-shiryen bikin mu dole sai na kara dagewa da noma.”

Adam ya ja Ummaru gefe, “Kai nikam dai fa ina son Wannan Jiddar nan ta min wallahi gashi yanayin ta na yan birni.”

Ummaru ya kama baki, “tab wai Jiddatu ka ke nufi ko Indo? Ai in fada ma kaf kauyen nan ba Wanda ta ke kulawa, Amman gwada sa’ar ka dai.”

Su dawo
Adam ya ce, “Jidda Dan Allah ko za mu iya magana?”

Da Murmushinta ta Amsa da Eh suka ja gefe.

Adam na Sosa Kai ya ke fadin, “a Gaskiya kin min matukar kyau tinda nake akarkarar nan ban taba ganin mai kyau kamar ki ba.”

Wani irin dadi Jidda ke ji har cikin ranta kara kallon kanta ta ke tana wani fari da Ido harda juyawa irin ya ma kara ganinta da kyau sosai.

Ya cigaba da fadin, “da ya ke kinsan ni natafi birni Neman kudi Yanzu ma maganar auren Ummaru ne yadawo Dani, Dan Allah ko zaki so ni Wallahi ni dai na mutu aso da kaunarka.”

Tini ran Jidda ya baci ba abinda ta tsana fiye da mutum ya ce ma ta wai yana sonta, can kuma sai ta kyalkyale da dariya ta ce, “Amman kaban kunya na aza kawai zakata yabon kyau na ne sai ka bige da wai ka na sona? To ahir din ka ni ko mai maigarin garin nan ma bai isa ya ce ya na sona ba bare kai, kagan ni nan ni Jiddatu kyau iya ka kyau to ka kiyayeni da Wannan rashin kunyar ta ka, yara ba ko kunya wai ka na so na?”

Tsalle tai ta Zungure ma sa kai tai ta ce, “Dama wasa kaje kayi ya fi ma danni in yaro ya karamin Zane shi zan wallahi.”

 

Adam kawai tsayawa yayi yana kallonta domin agirme dai yasan ya ba Jidda shekara goma ko fi ma Amman har ta na zungure mi shi kai.

Tsaki tai ganin ya tsaya kallonta ta ce, “Ke Lantana Soyayyar nan ta isa haka anfa zuwa siyan Addu’ahn ma sai wani makon Yanzu yunwa na Ke ji muje gida.”

Sallama Lantana ta yiwa Ummaru shi ko Adam ya yi suman tsaye.

A komawa Indo ce ta Goya Jidda har gida suna shiga ta baje,” IYA ina tuwona ni wallahi yunwa nakeji in banci ba ina ganin mutuwa zan yi.”

Iya ta fito, “Ina kan ki fita ki ka karya Jiddatu malmala uku fa kika cinye, wai Dan Allah ina zaki kai ci ne? Ni naga ta kai na Ke gashi ba kiga ba Amman sai bala’inci.”

Harararta Jidda ta fara yi, “Ai dadinta ma Dai Babana Ke kawo abincin nan bare amin gori.”

Iya ta ajiye mata tuwon masara miyar kuka malmala daya.

Jidda na gani ta kurma ihu kambu, “Dan Wannan tuwon Wallahi ni ya min kadan ki karamin.”

Iya ta ce, “Saura fa malmala biyu ne kadai kuma kinsan yau har rana daman nayi mana.”

Jidda kawai ta fashe da kuka ta na rikye ciki, “Wayyo Iya za ta kasheni da yunwa, wayyo cikina shikenan shikenan zan mutu da yunwa.”

Kuka ta Ke tana bori tare da suruntai.

Kan kace miye iya ta diri mata tukunyar tuwon gabanta.

Tana gani ta tashi tana share hawaye ta ce, “Indo Ku tafi gida sai na gama cin abinci kwa dawo.”

Fita kawai su ka yi domin sun San koda sun zauna Jidda ba sammusu tuwon nan za ta yi ba.

Fara cin tuwon nan tai ba kwakkwotawa kai kace bata taba cin abinci ba cikin dakiku kadan Jidda ta cinye manyan malmalayen tuwo guda uku.

Tana cinyewa ta ce, “IYAtuna Dan Allah ki daura ma na wani abincin kan anjima kin San cikina da jin yunwa.”

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 7/8_*

****************
************
******************

Su ka tintsire da dariya , “Iya Taji kunji min Fitinanniya wato kina sane da labarin jummala mai Jinnun karya.”

Jidda ta ce, “Eh mana ai nikam ma Yau dole ki kara bani labari domin kare kai na ko wataran ma za akara hakan.”

Iya ta tabe baki , “Ja’ira kawai ai ina ganinki nasan cewa wannan iya shegenki ne kawai.”

Jiddatu ta ce, “umm nikam dai Wallahi yunwa na ke ji Iya.”

Iya ta ce, “Aiko ban ko daura sanwa ba na fito kenan aka sanar dani halin da kike ciki.”

Nan take Jiddatu ta baje awajen tana bori, “Ni Wallahi yunwa nake ji kuma mutuwa zanyi in banci abincin nan ba, wayyo hanjin cikina suna magana wallahi Iya kinji ko magana suke Wallahi Yunwa nakeji kaman cikin zai fashe hanjin su fito.”

Iya ta dafa hannu aka ta na fadin, “ki rufamin asiri Jidda karki mutu wallahi in kika mutu bin ki zan yi ko mahaifinki ban mai son da na ke yi mi ki ba kiyi hakuri kinji ki bawa hanjin cikinki hakuri yanzu zan dafa miki taliyar birni (indomie) ko Leda biyu ai ya isheki ko?” Iyatu na maganar ta na goge guntun hawayenta.

Jiddatu ta gyara zama ta na, “Yauwa sun tsaya ma yanzu ki dafamin ko da Leda uku dai zanyi maneji dashi kin San tsutsar cikin nan nawa da hanjin kwashewa su ke, kuma ki daina kuka bazan mutu ba kinji mutuwa ma tare zamuyi.”

Jiki na rawa Iya ta tashi ta na shekan majina ta ji yar lelenta na maganar mutuwa tuni ta dafa ma ta indomie.

Tana gamawa kuwa Jiddatu ta langwabe sai da Iya ta bata abaki.

 

Da daddare Iyatu zaune da Jiddatu tare da su indo da lantana anzo hirar dare.

Jiddatu ta tintsire da dariya, “Wayyo Allah na Wallahi yau Baku ga maigari ba harda fitsari fa, lokacin da ya cire rawanin shi saura kiri in sa dare sai na wayance da ihu.”

Indo ta ce, “Haka Baffa ya zo yana fadawa Inna ai wallahi na so ma ina wajen daman gashi mugu aj gwanda da ki ka mishi hakan ma.”

Lantana ta ce, “Hhhh wayaga mai gari na fitsari f
Indon nan ya yi zuru-zuru kamar magarya.”

Jiddatu ce ta katse su, “Ai Wallahi da ace ya sa andakeni ko? Daga shi har mai hukuncin sai na rama in nemo wannan abin kaikayin in sa ma su ajiki.”

Iyatu ta ce, “Ai ko ba Ku da wayo irin namu na yan da kinga ai ni naso ma ki bari ya Dan tabaki kan daga baya ki tsere kinga daga nan zamu hada ma su damurmurar Dana sani.”

Jiddatu ta shekye da dariya, “Kai Amman dai Allah shiryaki Iyatuna Wallahi kin San salon mugunta da ace azamanin fir’auna ki ka zo dole Ku sasanta.”.

Iya ta gyatsine fuska kinci gidanku sai dai Wannan masifaffiyar uwartaki Amman ba ni ba.”

Jiddatu ta fara hararar Iya, “Ni dai wannan ba Uwata ba ce bayan ma ba ta so na, yauwa Iyatuna kawo kudin tsiren ma nasan yanzu Mallam Audi ya fito.”

Iya ta lalubo gefen zaninta ta Ciro wata fatakakkiyar naira Dari ta ce, “Gashinan ki ce mishi acikamin kulli kuma gashasshe mai zafi za abani.”

Jiddatu ta tashi tana yauwa Indo da lantana Ku tashi mu je dagan sai Ku huce gida kun ga dare ya yi kar amaku masifa kun San fa ina sonku.

Washe baki su ka yi dukan su adole yau Jiddatu ta ce ta na son su.

Suna zuwa wajen Mallam Audi Jiddatu ta ce, “Mallam Audi abani tsire Amman wai yaji kuli fa inji Iyatuna.”

Mallam Audi ya ce, “Ah Yan mata Jiddatu kenan yau kece da wuri haka?”

Murmushin dole Jiddatu ta kakalo ta na, “Amman fa Iya ta ce sai na dandana naji ko na yau ne domin jiya kwananne ka ban.”

Mallam Audi ya ce, “Yoo ai ba matsala ga yanka daya nan ki gwada.”

Mika ma ta yayi, tafara ci, girgiza kai take kamar wata mai cin abinda ya fi komai dadi aduniya chan sai ta ce , “Gaskiya ne Mallam Audi Yasin sai da kunnena ya amsa fa, naman nan ya ba da kala sosai fara zuba min dai, Amman fa naman na ya yi wallahi.”

Magana ta cigaba da yi tana kara daukan wani shi ko hankalinsa ya yi gaba yana ta zuba ma ta harda sa gyara, mika matan da zai yi kawai ya ga ai ta cinye tsinke guda Babba ke wajen, tana ganin ya lura da hakan cafkan Wanda ya kulle ma ta atakarddan ta yi gudu mai na ci ban ba ka ba, bin ta ya ke shima ya na haki, sai da ta bari sun shiga wani lungu mai shegen duhu ta labe aciki, shims ya na zuwa ya shige, Jan kafarshi ta fara tana katuwar murya, “Yeeeeeeeeee Ina kuke Ku fito ga nama nan mun samu har gida Yau akwai walimar dare daga ji zai yi tsoka.”
Ihu ya fara ya na, “Dan Allah kuyi hakuri Wallahi ban San cewa Wannan gidanku ba ne na tuba Ku yafemin Ku sakeni Dan Allah.”

Kara kankameshi Jiddatu da su Indo ke yi shi kuma ya na kokarin kubucewa ai ko da kyar ya yi nasarar subucewa aguje ya fita alungun ya na, “Yau ni naga jaraba wallahi nikam na yafe maganar tsiren ma akan na rasa raina.”

 

Ya na fita suka fara dariya kan suka fice daga lungun

Suna fita Jiddatu ta lalubo wani karami, ki ince figagge daga cikin tsiren ta mikawa Indo, “Gashinan tin da kece Babba ki raba mu Ku nikam natafi gida.”

Lantana ta ce, “Ayya Jidda ki Dan kara mana karami ne fa.”

Jidda ta ce, “Iyee kwadayi ko? Lallaima yaran nan kun iya samun waje maimakon kuce min kun Gode sai kuce wani in kara ma Ku, to kwaddayayyu Wallahi bazan Kara ba kuma kucemin kun gode.”

Ba yadda Suka iya haka suka ce ma ta sun gode.

Ta washe baki, “Yauwa yaran kirki maza atafi gida dare ya yi saura kuma gobe Ku ki zuwa yimana wanke-wanke sharar gida, kuma karku manta zamuje makarantar allon yamma fa.”

 

Sai da ta gama tsattsayar ma su tare da kafa dokoki kan ta bari su ka tafi.

 

NA SAN MA SU KARATU ZA SU SO SANIN WACECE JIDDATU TO KU GYARA ZAMA DARAM DOMIN YANZU ZA KU SAN ASALIN JIDDATU.

 

JIDDATU ‘Ya ce ga Alhaji Ibrahim hamshakin Dan kasuwa da ke zaune agarin kano tare da Mahaifiyarta Hajiya Zainab, Jiddatu ita ce ‘ya ta uku wajen iyayenta kuma ita ce ta karshe, Babar Yayarta Mariya mai shekara 20, sai Hamza mai shekara 18 sannan Jiddatu da ta ke da shekara 9 aduniya, Iya mahaifiya ce ga Alhaji Ibrahim mahaifin Jidda,Wanda Iya tinda aka Haifi Jidda ta daura son duniyar nan ga Jidda, mussaman ma da taji ansa sunanta, Iya na son rayuwa da Jidda Amman ba ta son zaman birni ko kadan hakan ya sa ta nemi da abata Jidda su dawo kauye tin bayan suna, da kyar Alhaji Ibrahim ya rarrashi mahaifiyarshi kan cewa ta bari sai Jidda ta kai yaye, aiko Jidda na cika Wata bakwai Iya ta kasa hakuri ta zo ta tayar da masifa kan dole sai anbata Jidda, daga Alhaji Ibrahim har Hajiya zainab ba su so ba Amman ba yadda suka iya haka su ka tattara komai na Jidda aka danka ma Iya ta tafi da ita chan kauye.

 

Kwata-kwata ba shiri tsakanin Jidda da mahaifiyarta domin bata jin dadin irin rikon da Iya ke yiwa Jidda hakan ya sa da zaran ta yi Abu Hajiya zainab ba ta iya hakuri sai ta tanka.

Ita kuwa Iya da taga ana yiwa Jidda masifa ta gwammance su daina zuwa.

Akwai lokacin da akayi Hutu Alhaji Ibrahim ya tattaro iyalansa domin yin Hutu wajen mahaifiyarshi, Amman kwana daya sukayi iya ta koresu sabida kawai Mama ta daki Jidda akan ta ki yin wanka, kuka iya ta fara ana ma ta bakin ciki za a kashe ma ta Jika, ta dinga masifa hadda hada ma su kayansu su koma garin su ai ba ita ta gayyace su ba Dan haka baza atakura ma ta yar jikarta ba, haka su ka komo kano ba da son ran su ba.

 

Jiddatu Yarinyace karama kimanin shekara shida, rigimamiya, ga tsokana ga tsoro sannan ga bala’in ci.

Jiddatu kyakkyawace dai-dai gwargwado, chocolate in color sannan kullum fuskarta cikin murmushi ta ke hakan ke kara bayyanar da Dimple din da ke fuskarta wadda yayarta ke ma ta ikirari da Dimple Queen,ita kuma ta ke fadin (dompol kon), Jiddatu ta tsani wanka arayuwarta duk da cewa bata son kazanta Amman ta fannin wanka fa sai anyi daru kan Jiddatu ta yi.

Wani abin mamaki duk abun nan na Jiddatu ta na da kwakwalwa fiye da yadda ake tsammani ta na zuwa makarantar boko da islamiya na kauyen duk fitinarta ba ya hanata iya karatu ko fahimta domin har mamaki ake, hakan yasa wani lokacin ma ko ta yi Abu malaman kan kokarin kawar da kai,yanzu ta na aji hudu na matakin primary kuma tun da ta fara zuwa makarantar nan daga islamiya har boko na daya ta ke zuwa bata taba zuwa na biyu ba ma bare na uku, su Indo da lantana kuwa kullum su ne na karshen aji.

Abu daya kullum maganar Jiddatu daya ne ita fa *MATAR POLICE* da wannan Kalmar ma kadai ta kan iya kwatan kanta in ta yi laifi abin ka da yan kauye akwai tsoron jami’an tsaro.

Ko wanene wannan police din? Ku biyu ni domin sanin wanne Wannan jarumin na Dompol kon🤣

Kadan kenan daga cikin labarin Jiddatu wadda ta adabi karkarar.

 

_GASKIYA BA NA GANIN SHARHI KO DAI LITTAFIN BA YA MA KU NE?_

_GARABASA GA DUK MAI SON SIYAN *JAMEEL (Nafseen)* da *MATAR POLICE* DUK MAI SON DUKA BIYUN MAIMAKON BIYAN 400 ZAN BAR MA KU 300_

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 9/10_*

_*🥳🥳🥳Har Yanzu ba afara wannan somin tabi ne, karku gaji Ku cigaba da bibbiyata domin wannan daban ya ke da wa’inda kuka karanta abaya, salon sa da ban haka ma tsarinsa da ban🥳🥳*_
****************
************
******************

Washe gari..

Jidda da Iya sunyi sallar asuba, nan fa Jidda ta janyo tea plask din da Babanta ya kawo ma su domin ajiyan ruwan zafi sabida Jiddatu, katon kofin da ke gefen plask din ta dauko ta zuba ruwan shayin tam da kofin sannan ta zuga uban sugar, da ta kafa kan ta ajikin kofin sai da ta shanye tas kan ta ce, “Alhamdulillah.”
Sannan ta yi wata shegiyar gyatsa.

Wannan ka’idar Jiddatu ne da zaran tayi sallar asuba sai ta sha shayi wani lokacin ma harda dumame, duk ranar da bata sha ba kuwa akwai masifa agidan shiyasa Iya ta ke kokarin tanadar komai do min ta San in Jidda ta birkice ba za ta ga da kyau ba.

 

Ta shi tayi zata fita.

Iya ta ce, “Oh ni Hauwa kulu, yanzu Dan Allah ke ko komawan barcin nan ma da yan zamani ke yi bazakiyi ba sai kin fita kofar gida kin addabi jama’a.”

Murguda baki ta yi, “Ni to ina ruwana barcin Daren ma dai Dan ya zama dole ne da Yasin bazan ba, ni natafi kawai ki min dumamena kan na dawo.”
Ta fice abinta ta na tsalle-tsalle.

Iya ta tabe baki, “Allah dai ya shiryamin ke.”

 

Jiddatu na fita ta zauna Adan wani karamin dutse da ke kofar gidan.

Rami ta yi awajen tana carafke.

Chan sai ga masu tafiya gona na fitowa.

Wani tsohone yazo hucewa Dan babur din sa irin na da ya ji, jiki ko a Ido ma ba kadan ba bare kuma kaji irin sautin da ya ke badawa.

Ta shi tayi ta na kyakyalle Dari, “Ah Baba ina kwana?”

Ko kallonta bai ba domin yasan halin Jidda sarai.

Dariya ta cigaba da yi ta ce, “Wuta sallau, wuta , wuta Yasin kaf karkarar nan ba abin hawa kamar na ka, wuta sallau.”

Shi dai sauri kawai ya ke ya ga ya bar wajen.

Sai ga wani manomi ya zo wucewa da fatanya.

Jidda ta tashi ta karasa gabanshi tsalle ta yi ta taba, kan shi, ta kyakyalle da dariya, “Tab ji kan ka kamar na agwagwa?”

Tsorota manomin nan ya yi, ya ce, “mi ye akaina? Kar dai wani Abu ne ya zurmamin.”

Dakewa Jiddatu ta yi, ta ce, “Eh mana, ai inaga sai na bubbuga ma ka, kan nan in ba haka ba zurmawa zai yi daman gashi ya fara zama irin na agwagwa.”

Zama ya yi ya ce, “Dan Allah ki gyara min kai na Wallahi zan baki ko me kike so.”

Jiddatu kamar za ta yi dariya ta damke, “To shikenan Amman fa da zafi kuma in kayi kuka nikam zan bar ma haka.”

Da sauri ya ce, “Kimin Dan Allah bazan yi ba.”

Hannu Jidda ta dunkule ta maka ma sa duka atsakarka, sai dai ya yi guntun kwalla, Amman ya daure, kara maka mishi wani dukan ta yi, sannan ta dibo kasa ta dinga watsa mishi akai harda laka, bai San lokacin da fitsari ya fara fito mi shi ba.

Dariya ta fara ta na to she bakin ta kardai ya gane, ta ce, “To Kawu na gyarama ba sai ka ba da komai ba ka tafi kawai Dan Allah na yi ma.”

Ya ce, “to nagode Allah mi ki albarka ‘ya ta.”

Tafiya ya yi, nan fa Jidda ta fara lekyen kan shi tana kyalkyale dariya, hadda rikye ciki, ,”Wallahi yan kauyen nan ba su da wayo.

 

Zata shiga gida kenan sai ta hango wani mai rake na tawowa, tsayawa ta yi ta na son sha gashi ba ta da kudi, nan ta ke ta tuna da Ahlam din kuchakar kishiya yadda ta yi wa baba mai rake.

Dariya ta yi ta karasa gareshi ta na, “Mai rake in ba rake mutuwa ta zo ta tafi da kai.”

Da bai kulata ba Amman da ya ji maganar mutuwa ya tsaya, “Ta Allah ba ta ki ba insha Allah ba dai yanzu ba.”

Jiddatu ta ce, “To Wallahi ka bani raken nan ko in ma ka Addu’ar mutuwa, kasan fa ni da kakata in mu ka yiwa mutum Addu’ar mutuwa, mutuwa ya ke.”

Nan fa cikin mai rake ya duri ruwa, da sauri ya ce, “Haba Jiddatu Dan Allah kar Ku min zabin Wanda ki ke so aciki.”

Ta karkarewa Jiddatu ta yi ta kwashe manyan ciki guda uku ta ce, “Shikenan Baba nikam ma zan ma ka Addu’ar gadin duniya.”

Ya ce, “Aa tab nidai kawai kimin Addu’ar kar in mutu yanzu Amman gadin duniya ai ya fi karfina.”

Da dariyar ta ta ce, “shikenan jeka abinka baba kar ka damu.”

Washe baki ya yi yaci gaba da tafiya ya na, “Tab Allah ya taimakeni yanzu ba da ban ba ta ba da mutuwa zan yi, tab aradu sai natara kudi na je birni ko da sau dayane, wannan yanzu shikenan za ta min Addu’a kar in mutu Yanzu ai gwanda da ma na biyo tanan daga yau kullum zan biyowa ta hanyar nan ina bata raken ta na min Addu’a.”

Ita ko Jidda sai dariya ta ke, “wato dai duk tsofin kauyen nan ba sa son mutuwa, hhhhh ni ko na sami abin yi ai kenan.”

Kallon raken hannunta ta yi ta na, “Yau zan sha dadi kuma Yasin ba zan samma iya ba.”

Zama tayi ta fara sha sai da ta shanye guda daya kan ta lekya daga zaure ta na, “IYA kin gama ne inshigo? Iye, Iya kin gama nafara jin yunwa fa ni wallahi yunwa na ke ji.”

Iya ta ce, “To uwata ai ba ni nace ki zauna awajen ba ko? Gashinan ki zo ki ci ai.”

Jidda ta gyara daurin zaninta ta dammare sauran raken ajiki kan ta shiga.

Ta na shiga ta ci karo da malmalar tuwo biyu.

Ihu ta fara ta na tsalle, “Ni Wallahi tuwon nan ya min kadan Iya na fada miki ni yamin kadan me naci bare na bawa ‘ya’yan cikina, ko hanjina ma ai bazai samu ko loma ba.”

Ta daura hannu aka ta na kurma ihu.

Iya ta ce, “Ke matsalata da Ke wallahi kwata kwata ba ki da hakuri, yanzu ina ga sauran nan na ije mi ki in kin cinye wannan din kya kara.”

Washe baki Jidda ta fara ta na, “Yauwa Sowaty Iya ta kin san ma miye sowaty? Sunan da Mama Ke cewa baba ne fa wai Sowaty (sweety) kin ga daga yau nima haka zanna ce mi ki, tin da dai ke kadai ki ke sona.”

Zama ta yi ta fara cin abincin sai labari ta ke bawa Iya na abin da ta yi, Iya ko sai dariya ta ke tana jin dadi.

 

Ta gama ci kenan sai ga Indo da lantana.

Hararsu ta fara ta ce, “Ina yanzu Ku ke zuwa ko? Dan kunga Yau ba boko shine bazaku zo da wuri Ku tayani aikin ba ko? Kai nama daina Hausa daga yau turanci irin na Anty zan na yi, Oyoo You Indo, You Lanta landwon (nildwon),”

 

Tashi ta yi taje ta dauko bulala .

“As forom tode zan ga who you sa’a is, in gaya ma Ku ni Ina pale (play) da Ku ne?”

Jiki na rawa su Indo su ka yi nildwon.

Iya ta ce, “Haba ke kuwa Jidda ki ma su uzuri daga Nolnol dinnan.”

Jidda ta kyakyalle da dariya , “Hhh Iya ke baki iya Abu ba kina cewa za ki yi Landwon ake cewa ba nolnol ba.”

Iya ta ce, “Oho ko ma miye dai ki ma su uzuri.”

Jidda ta hadda rai, “I rantsuwa You kunci sa’ar Iyatu bor if you kara it agan yasin I wol dagargaza if and if.”

Tsayawa ta ma su ta kara da , “Oya sanda of kuma Ku ce min Sorry Madam.”

Ta shi sukai jiki ba kwari , “Sorro Madam.”

Dariya ta yi, taji dadi yau sai zazzaga turanci ta ke, “Iya Wallahi fa na gama iya turanci Yanzu kam Anty Mariya ba ta isa ta min dariya ba sai dai ma in koya ma ta.”

 

Iya ta ce, “Ai kuwa dai nima nagani su kam ai basu iya komai ba daman sai iyayi.”

Jidda ta koma ga Su Indo ysn kan I Bude Eyis dina Afara wanke wanke da sharar gidannan.

Da sauri suka tashi su ka fara, kamar uwarsu ko ince Jidda ma ai tafi iyayensu iko da su.

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 13_*

****************
************
******************

Mallam ya’u na magagin barci ya bige wajen kunnen ya na, “Wai kudajen nan ba za su bar mutum ya yi barci ba ne, wannan wani irin bala’i ne?”

Ya gyara juyi sannan ya cigaba da barcin sa.

Su kuwa lantana sun diba karas iyaka son ran su da Jidda ta ga sun gama diba nuni ta ma su da su fara gaba ita kuwa ta kafa kan ta dai dai kunnen mallam ya’u.

Ta ce, “Yau sai muncinyeka, mun dagargaza namanka za mu cin yeeeeee kaaaa.”

Murya abankare kamar tsohuwar aljana.

Jin maganar ya ke kamar amafarki chan ya ga dai ba sarki sai Allah sai cunkumarshi Jidda ke yi, gashi ya kasa bude ido ya make awajen.

Jidda ta kara fadin, “Sai muncinyeka Wallahi, Yau sai namanka ya shiga tukunyar kasa.”

Azabure Ido rufe mallam ya’u ya zura aguje ya na, “Innalillahi wallahi su suke ganin mu ba mu, mu ke ganin su ba.”

Jidda kuwa yadda ta ga yana gudu ban da dariya ba abin da ta ke yi har da rikye ciki.

Tashi ta yi ta nufi wajen su Indo da lantana ta karbe karas din ta na fadin, “Muje gidan Iya sai in ba Ku na Ku, kwa wuce gida.”

Haka kuwa akayi Yau anci sa’a ta ba su guda bibbiyu sai washe baki su ke.

 

Bayan Sati daya an sa bikin Lantana su Indo amare an dage sai shirye-shirye ake.

Ta dage wai zatayiwa Lantana dilka yadda taga anyima wata abirni.

Ka sa ta samu ta kwaso irin lakarnan, da Jan kurkur, sannan lallai, ta kwaba.

Lantana, “ki zo in mi ki abin nan wallahi Dan inna tashi ba yi zan ba.”

Da sauri lantana ta fito daga ban daki ta na, “Kiyi hakuri Jidda gani nan.”

Kan kace miye yan mata manya da yara ancika agidan Iya ana ganin gyaran jikin yan birni.

Ita kuwa Indo sai gurzawa lantana jiki ta ke tana masifa, “duk anbi an cikawa mutane gida ni Wallahi na tsani irin haka yara kamar ya’yan Aljanu.”

Iya ta ce, “Ai ke abun jin dadi ne ma azo kallo kinga nan gaba kya fara na kudi ma.”

Jidda ta ce, “Tab ai aradu ko yanzu ma angon lantana sai ya biya ni, ai an hana aikin banza.”

Cikin Ikon Allah kuwa a cabe-caben har fuskar lantana ta Dan yi kyau har cikin ma ya Dan yi luwai-luwai, kai kaji ihu agun yan kauye ai sun sami mai gyaran jikin yan birni.

Lantana kuwa sai wani botsewa ta ke tana matsewa, ana gama ma ta akayi wa Indo.

Jidda ta ce, “ni kam ba sai na yi ba, inna ma Ku ma shikenan.”

Ana gama wa aka siyo bakin lallai ita da kanta ta Kara caccaba masu kafa da hannu, har ma da sarkan wuya.

Sai da Jidda ta yi kwana biyu ana dangwalawa cikin Lantana da Indo laka da lalle, kuma in za a fita sai ta sa su dauko zani arufa har kai wai Ido kadai za su na lekowa ba ason rana ta ta ba.

Daren Yau sa lallen Ummaru da lantana, Jidda an dage manyan kawayen Amarya sai ummaru ya ba da kudin sa lalle.

Haka kuwa dolen shi sai da ya ba da naira Dari kan Jidda ta bari iyayen ummaru su ka sata lalle.

Adaren ranar Lantana da indo agidan su Jidda su ka kwana.

Washe gari tun asuba Jidda ta sa Lantana da indo wanka aka dandasawa lantana kwalliyar yan birni mai kama da aljanu, ita kuwa kwaskwarimarta ta fama ta yi sannan ta dauko kayanta mai kyau ta sa ko kwalliyar ba tai ba ta ce, “yan kauyen nan da raini nasan ina kwalliya afuska za su fara jeruwa da warin hammatarsu wai suna sona, gwanda ma na zauna haka ko na tsira, Dompol dinnan ma kadai ya isa ya razana su.”

Ta kyalyale da dariya kan ta tashi ta na” yauwa lantana ki ga ni fa yadda za ki na tafiya daga yau irin na manyan Mata, daura hannu za ki yi akwankwason ki kina tafiya kamar taliyar yan birni, kinga indai ki na mishi haka to fa ba zai kara aure ba, nima ranar da mukaje birnine naga ana fada a Talabijin.”

Lantana ta ji maganar rashin karo kishiya tuni ta ta shi ta na kwaikwayon Jidda.

Kiransu akazo yi kan cewa angwaye sun dawo daga daurin Auren.

Wani mayafi Jidda ta dauko Wanda babanta ya aiko ma ta da shi ta lullube Lantana.

Suna fita antaro ana kallon Amarya mai irin adon yan birni.

Shi dai Adamu abokin ummaru hankalinshi na kan Jidda ita kawai ya ke kallo.

Ta na sane da shi suna hada ido za ta galla mishi harara tuni ya ke kawar da kan shi kasa.

Jiddatu ta ce,”Ummaru Amman zaka bar mu MU cigaba da zuwa makaranta da lantana ko? Kasan dai saura shekara daya mu gama.”

Ummaru ya San halin Jidda sarai hakan ya sa shi saurin amsawa da Eh.

Yamma ta yi amfara zuwa daukan Amarya Jiddatu ta rankwashi kan Lantana “wawiya kin ki kiyi kuka ko? Ai ace mi ki Mara kunya ko kukan ya ki zuwa ki kakalo na karya.”

Haka ba yadda lantana ta iya ta fara kukan karya ta na ihu.

Sunje har an wuce gidan ba a sani ba, tuni lantana ta cire ido amayafi ta na fadin, “An wuce gidan fa gashi cen wance da ke da dakalin ne.”

🤣🤣🤣amaren zamani.

_*Karku manta fa har yanzu ba mu shiga birni ba🥳🥳🥳karku bari shiga birni ya kubuce ma ku, maza Ku hanzarta domin fara biyan 200 din Ku kacal*_

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 11/12_*

****************
************
******************

Sai da suka kammala gyaran gidannan tsaf kan Jidda ta bari su ka je gida domin cin abincin rana tare da shirin islamiya.

Ko da suka dawo tana nan ta na gilu-gilu lokacin Islamiya har ya fara kurewa, ga shi suna jin tsoron mugun malaminsu, ba abin su yi magana ba Jidda ta hau su da bala’i, kwaskwarima ta fara yi sannan ta dauko kayan kwalliyarta, “Ku zo nan kuna YI da kan Ku duk abin da na YI kuma Ku yi.”

Da sauri kuwa Su Indo da lantana ansami garabasar kayan kwalliyi akafara, tuni ma sun manta da maganar sun makara.

Jidda na gamawa ta kalli Indo tare da dafka wani hamshakin tsaki ta ce, “Dilla chan Ke ba a kan gira ake sa kallin ba saman gashin ne wawiya kawai.”

Karfa ta yi ta kara chaba mata girar da eye-shadow .

“Woo kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa kamar yau aurenki, aradu in anzo bikin ki za aga tsiya a kauyen nan.”

Karasa maganar ta yi cikin dare ta ce, “Ku tashi muje kan wannan masifaffen malamin ya fara.”

 

Tafiyarsu su Ke su na ta dariya duk Wanda ya kalli Jidda su ka hada Ido sai ta galla ma sa harara tare da murguda baki.

 

Suna isa makaranta Malam ya yi suman tsaye ya ce, “lallai ma wato yau ba iyaka makaran Ku ka tsaya ba hadda kwalliyar Aljanu?”

Jidda ta fara murguda baki, “Ni dai Wallahi ban yi kwalliyar Aljanu ba Ehee, ni nasan ma haushi ka Ke ji matarka ba ta iya ba.”

Mallam ya ce, “Ni kike maiwa da martani ko? Zan nuna mi ki ba ta iya ba kuwa, daga Ke yar yan korar na ki sai na yi maganinku yau.”

Jidda ta ce, “Tab ni Wallahi an hana dukana kuma in ka dakeni za ka gani.”

A fusace Malam ya dauko dorina domin ba Yau Jidda ta saba yi mi shi rashin kunya ba, ya na kyalletane sabida karatun ta.

Dukan su ya farayi suna kuka, mussaman Jidda ban da kararta ba abinda ake ji, Iya da ke gida ma sai da ta jiyota.”

Tuni Iya ta zagaro kafa ko takalmi ba bu bare mayafi.

Jidda kuwa ta kidime”Wayyo mallam zai kasheni shikenan mallam zai kasheni, mallam Wallahi kashi na Ke ji ka barni na je na yi nadawo sai ka cigaba, mallam zan yi agun wallahi gashinan zai fito mallam, mallam zai fito.”

Shi ko mallam kaman ana Dada tinzirashi ya cigaba da dukanta.

Yan makaranta kuwa ban da dariya ba abin da su Ke.

Iya ta shigo cikin masifa, “Wai wannan wani irin bala’i da masifa ne yarinya kowa ya na hassada da ita duk kun bi kun tsaneta son ko kowa kin Wanda ya rasa.”

Ta fisge Jidda awajen mallam ta cigaba da fadin, “Gani nan sai ka hadamu ka daka ai ko in tsinemaka, in tsinewa kakan kakanka, ban da mugunta irin taka wannan yarinyar nawa ta ke yaushe ta kai duka wannan ko goyo abayama ba ta zarce ba bare amata duka da wannan tsimagiyar, kana nan da hanci kamar fantekar da ta yi wata ba waiwayeta ba, ba ki kamar tuwun dawan da ya shekara, to wallahi ahir din ka da jikata karkasa in maka baki domin gadon mu kambun ba ka.”

Shi dai Mallam tunda Iya ta fara magana ya ja bakin shi ya yi tsint tare da saukar da kai kasa domin yasan ba abin mamaki ba ne Iya ta mai tijara cikin dalibansa ya gode ma da abin ya tsaya iyaka masifa ban da mari Dan in taso sai ta rama ma ta.

 

Cikin shagwaba da gulma Jidda ta ce, “Iya kuma fa na fada mishi kashi nkeji ya bar ni nayi Amman ya ki.”

Iya ta dubeshi tare da zungure mi shi kai, “Kai baka kashin ne ko ko ba kasan yadda ya ke matsin mutum ba, nan nan naga kana yaro kullum in ka zo gidana wasa sai kasani aikin kashi ga kashinka da uban wari, yo ai ko ubanka ma lokacin ahe haka ya ke gadone abin.”
Ta kyalyale d dariya.

Yara na son yin dariya Amman ba yadda suka iya suka gimtse.

Jiddatu ta ce, “To Iya ki tafi ni nama daina jin kashin ya mana karatun kawai.”

Iya ta ce, “Shikenan yar lelena,kai kuma Audu ka ke ko mudi, ahir dinka ko kallon banza ban so akarayiwa Jidda, maza ka ma su karatu jikin lumana kasan ba mu son tashin hankali, Ah to.”

Ta fice ta na kanun maganganunta, “Yo in ban da tsiyama har an iya ayi mana kallon banza sai inyiwa mutum baki ya ba ce aradu
, Ni fa tausayin yan kauyen nan ma na ke, kar in tafi komai ta barbare,da tuni na koma birni,Amman su ba sa ganin hakan, Oh ni Baba Kulu.”

 

Iya na tafiya mallam ba yadda ya iya haka ya cigaba da ma su karatu ko hada Ido ya yi da Jidda saurin kawar da kai ya ke yana fadin, “A uzubillahi.”

Ita kuwa Jiddatu sai kallon shi ta ke tana kyakyalewa da dariya.

Ana cikin karatu ta katse, “Mallam zan yi kashi.”

Kawar da kan shi ya yi daga I donta ya ce, “To jekiyi.”

Ta kara da cewa, “Kai baka jin kashin ne?”

Ya ce, “Eh.”

Ta ce, “To ai shikenan ni dai zanje na yi kuma in ka na ji kaje ka yi karka ma na tusa a aji.”

Yara suka tintsire da dariya sai da ya ma su tuzuren dole kan su ka kumshe dariyar.

Kuwa Jidda fita tayi ta yi wasanta son ranta kan ta dawo ajin.

Mallam Addu’a ya ke kawai lokacin ta shi ya yi ya kadasu gida.

Jidda sai kakale-kakale ta ke daga tace zata sha ruwa, sai ta zatayi fitsari.

Daga karshe dai lokaci bai ma yi ba mallam ya kadasu gida ya ce antashi, Jidda kuwa sai murna daman abin da ta ke so kenan ahanya su lekya gona su diba karas.

 

Tafiya su ke Jidda ban da tsokanar mutane ba abinda ta ke yi.

Indo ta ce, “Laa Jidda kin ga fa Mallam Ya’un ya na barci dadin ma diban kenan.”

Lantana ta ce, “ai kuwa kin ga shikenan ma diba son ran mu.”

Jidda ta ce, “Ku Je Ku diba ni zan tsaya anan inna tsokanarshi.”

Tsinke ta dauka ta karasa wajen shimfidar mallam ya’u dai-dai kunnenshi ta tura ahankali……….

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 14/15_*

****************
************
******************

Rankwashi Jiddatu ta kaiwa lantana
Ta ce, “Mara kunya kawai, ni daman so na ke in Dan ba tsofin nan wahala Amman kin wani kofsa wawiya kawai ai sai mu shiga.”

 

Su kuwa tsofin da ya ke sun San halin Jidda sarai kawai shigewa gidan su kai ba tare da sunce kala ba.

Ko zama ba su yi ba ana ajiye Lantana tsoffafin su ka bar indo da Jidda.

Jidda ta ce, “Yauwa ki saurareni in mi ki fada ehee ban da rawar kai, kuma karki Yarda ya rainaki Wallahi, kina sa shi aiki, kamar irin wanki da sharar tsakar gida, kar ki kuskura ki na washe ma sa baki kalan ya rainaki kin San haka mazan su ke fa hmm na fada mi ki nidai, sannan yadda na ga Mamana na yi dare na yi kiyi kwaskwari ma ki chanja kaya, ita dai kam wanka ta ke Amman ni kwaskwarima zannayi Dan wanka zai na kodar min da jiki, ke ma in kinga zaki iya wankan to Shikenan ki na yi,kuma zan zo ma in koya mi ki girkin yan birni, sannan fa in kin gashi karkina zama ba hijabi kin tuna abin da mallam ya ke fada mana amakaranta? Yauwa sai ma me zan ce miki? In him ki dinga irin kwalliyar nan da na koya mi ki kinji.”

Ita kuwa Lantana sai bin Jidda da Ido kawai ta ke.

Indo ta ce, “Kin manta baki tuna mata maganar tafiyar nan ba.”

Jidda ta ce, “Yauwa wannan tafiyar da na koya mi ki haka fa zaki na mishi kina Dan fari da ido, hhhh haka ake yasin.”

Ta ce la na Dada mantawa ma kawo kunnenki kiji Lantana ta kawo kunnenta suna gama magana kawai naga sun birke da dariya.

Angwaye su ka yi sallama da sauri Jidda ta rufewa Lantana fuska da mayafi.

Suna shigo Jidda da indo su ka amsa.

Ummaru ya ce, “Ah Hajiya Jidda Ikon Allah.”

Hararshi ta yi ta ce, “Kai dai kaji da shi, sai wani washe baki ka ke ko kunya.”

Adamu ya ce, “To mallama Jidda amana Addu’a.”

Gyara zama tayi tare da murtuke fuska kamar wa ta babbar ma ta ta ce, “To bismillah da fatiha, ta kammala da fadin Ammen kan ta cigaba, ” To Allah ya sanya alkairy, Allah ya sa kar ka mata kishiya, Allah sa kana tayata aiki, Allah rabaku da dambe kamar yadda Innar lantana da babanta ke yi, Allah ba Ku ‘ya’ya dozin-dozin.”

Amsawa su ke da amin kawai, Jidda ta ce, “To maza asallame mu muyi gaba.”

Adam ya ce, “Gashinan awajena in mun fita zan Baku.”

Har sun tashi za su fita Jidda ta je dai-dai kunnen lantana ta ce, “Ni dai karki manta aragemin sauran tsire da kifi har ma da lemun kwalbar da asuba za mu zo karfa, sannan kar ki manta da abin da na fada mi ki dazu.”

Har sunje bakin kofa ta kara juyowa ,”karki manta fa.”

Lantana ta daga ma ta kai.

Su na fita Jidda ta fara Harar Adamu ta na murguda baki , “Ni ka sallame mu kawai mu yi gaba mu na da abin yi fa.”

Har da juya mi shi baya.

Ciro dubu daya ya yi ya ce, “to gashinan.”

Karba ta yi tana washe baki, “Ah lallai ka ce kai ma Alhaji ne kamar babana to mungode.”

Adam ya ce, “Ah tsaya ma na kiji.”

Gwalo ta mi shi ta na tafiya tare da fadin, “Sai da Safe Dan samrayi.”

Ba ason ran Adam ba haka Jidda ta tafi ta bar shi tsaye awajen.

 

Jidda ta ce, “Indo ga kudin nan ki tafi dashi kawai da safe in zamu tafi boko kya mana chanji, yauwa karki manta da asuba za mu je cin tsiren Lantana.”

Dariya Indo ta yi kan ta ce, “Shikenan ina idar da sallah zan zo yasin.”

,,,,,, haka kuwa akayi Jidda na idar da sallah ta sha ruwan shayin ta na fama sai ko ga Indo.

Iya ta ce, “Ina za Ku je haka?”

Jidda ta ce, “Gidan lantana ma na cin tsiren amare kalan mu bari aje a cinye.”

Iya ta daura hannu a ka , “Oh ni Ibrahim ya haifo min wadda ta fi ni iya shegeni, ni ko zamanin mu mu kan bari hantsi ya fito kan muje Amman fa Ku da duku-duku haka? Ku bari garin ya Dan washe mana.”

Jidda ta murguda baki , “Mu ina ruwan mu walle sai munje in ma ba su tashi sallah ba ma tashesu kin san lantana da shegen barcin tsiya.”

Iya ta ce, “Yo ai Shikenan ni dai aragomin tsiren.”

Jidda ta ce, “Tab walle cinye kayanmu za mu yi naga ke ma lokacin da Kakana ya ke Raye ai kinci kuma Baki rage min ba.”

Iya ta yi shewa, “Lallai ma Jiddatu yo shi kakan na ki ma da bai kawo tsire ba sai kosai.”

Jidda ta galla ma ta harara , “andai ji kuma ysin ba zana ragoma ki ba.”

Fita suka yi suna zuwa kuwa ko Sallah su lantana da ummaru ba su yi su na ta barci, kwankwaso kofar galan-galan din ne ya farkar da ummaru, azubure ya je ya bude kofar ganin Su Jidda kafe ne ya sa shi suman tsaye.

“Wato ma ko tashi sallar ba kuyi ba yanzu ai kwayi ni matsamin in shige.” Cewar Jidda.

Abin ya matukar batawa ummaru rai Amman ba yadda ya iya haka ya nufi massallaci.

Suna shiga Jidda ta fara dukan Lantana, “Dallah ki tashi wawiya ko sallah daga ke har mijin na ki ba Ku yi ba, ni tashi ki ba mu tsiren mu da sauran lemon kwalba.”

Ta shi Lanta ta yi ta na mitsika Ido ta daga filon ta ta mikawa Jidda.

Jidda ta sake baki, ” kambu Dan wannan za Ku rage ma na.”

Lantana ta ce, “Jidda Wallahi wannan din ma da dambe da kwatan ma Ku fa sai ci ya ke ya ma fi ni ci.”

Jidda na ci ta na, “Amman lallai wannan Ummaru ya Iya shege sai mun gyara ma sa zama wa to ko kunya ma.”

Indo ma naci ta na, “Amman yau za ki shirya mu je boko ko?”

Jidda ta ce, “Ai dolen ta ma Yanzu ki tashi ki yi sallah, in kin gama komai za mu biyo mi ki mutafi bokon.”

Lantana ta tashi ta na, “To ni kayan boko na ma na gida.”

 

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 16/17_*

****************
************
******************

 

Jidda ta ce,”Ai sai ki tafi dana jikinki kawai.”

Sannan ta tashi.

Indo ta ce, “Mu kam mun tafi muje mu shirya, Yau fa in aka tashi za mu zo nan mu yi girki.”

Lantana ta ce, “To daman ni ban ma Iya girkin ba kwa koyamin.”

Jidda na fita tana fadin, “Ai ko za mu koya mi ki irin na yan birni ma.”

Lantana harda tsalle ta na murna za ta koyi girki,irin na yan birni ma.

 

Kamar yadda Jidda ta ce ko haka akayi Ummaru na shigowa ya ga Lantana na kokawar fita.

“Ah’ah Amarsu ina za kije yanzu ko kin manta cewa amare ba sa fitane bare ma in za su fita sai da izinin mai gida ko?”

Lantana ta tabe baki za ta yi kuka, “Ni Wallahi zan je, ni Wallahi in ba ka barni na je ba, ba ma ruwana da kai, kuma kai ba Angona ba ne, kuma fa in ban je ba su Jiddatu ba za su zo su koyamin girkin yan birni ba.”

Ummaru ya ce, “Dan Allah ki yi hakuri kar ki sa a zata wani abin na ke mi ki, yi shiru za ki je, ai ko Dan girkin birni ma na barki ki je, kin ga yau na fadawa su Adamu da Mustapha har ma da Lawandi su zo, su kwashi girkin yan birni.”

Lantana ta yi tsalle ta na, “Yauwa Angon lantana, shiyasa na ke son Ka fa.”

Ummaru ya ce, “Allah ko?”

Lantana ta ce, “Eh ma na irin Son yan birni ma na ke ma, me ma suke cewa? Kamar Jidda ta koyamin Yauwa, Lilivi lovi yoh.”
Ta karasa fada ta na rufe fuska.

Ummaru ya sa hannu a kirji, “Aradu har kin sa na ji kifiyar so da kaunarki ta cekeni a kirji, yanzu to fa ko wanka bakiyi ba ko sai kin dawo ne.”

Ta na wani fari da Ido ta ce, “Eh mana.”

Ummaru ya ce, “To ai karki tafi da yunwa bara in karbo ma na shayi da burodi mu ci ko.”

Lantana ta ce, “Yauwa daman rabona da burodi tin ran Sallah da Jidda ta sammana.”

Cikin Murmushi Ummaru ya ce,”yau kam zakici har ma sai ya ginsheki.”

Zuwa ya yi, ya siyo ma su, kan kici me lantana har ta kusa cinye biredin.

Ummaru dai ya siyo Abu Amman ya fi karfin shi haka ya yi hakuri har su Ka kammala.

Lantana ta tashi , “To ni natafi Ka gyara gidan Ka yi wanke-wanken ko?”

Ummaru ya ce, “Angama Amarya Amman mu je in fara rakaki ko?”

Lantana ta ce,”To mu je.”

Suna fita sun fara tafiya kenan sai ga su Jidda da Indo.

Indo ta ce,”Yauwa sai mu hice makarantar ai daman gidan ki mu Ka nufa.”

Ummaru ya ce,”To ai hikenan mu je in Dan taka ma ku. ”

Jidda ta galla mi shi harara, “To bayan ma ko rikye ma ta hannu ba kayi ba wannan ai kauyancine.”

Ta yo gabansu ta daga hannun Lantana da na Ummaru ta hada ta na, “Yauwa kunga yanzu kowa ya ganku ya San amarene.”

Sai da suka isa kofar skul din kan Ummaru ya jiyo da niyar komawa gida.

Da karfi lantana ke magana, “Kar Ka manta da wanke-wanke fa kaji ko.”

Ummaru ya ce,”Yanzu ma kuwa Amarya.”

Suna shiga ana dukan wa inda suka makara Jidda ta ce, “Lallai Yau in malamin nan ya ta ba ni zai ga masifa.”

Indo ta ce, “Allah sarki ita kam lantana Yanzu ba mai dukanta kamar yadda ba a dukan su Sha’awa.”

Jidda ta ce,”Mu ma din Wallahi ba Wanda ya isa ya dakemu ai inko ya dakemu aradu yau sai ya cire wannan bujen wandon na shi batare da ya sani ba. ”

Suna cikin hakan kuwa Maman buje ya ce, “Ah Amarya Lantana har andawo makaranta ne? To ma za shige aji ki barni da wa’innan shirmammun.”

Lantana ta tashi ta shige aji, sai ga Zainab ta zo.

Zainab wata yarinyace sa’ar Jidda Amman kwata-kwata ba sa jituwa da Jidda, mussaman Zainab yadda ta ke nuna ma su gadara ai ita budurwa Malam buje ce, hakan ya sa ta zuwa makaranta a duk lokacin da ta so domin tasan ba dukan letti ake ma ta ba, ita kuwa Jidda kullum abin na tsaya ma ta arai ta dauki alwashin wataran sai ta yi maganin Zainab, Abu daya ke ba ta tsoro tasan ba ta da karfi kar azo ita ba ta daka adaketa.

Kallon Zainab ya tsaya yi yana wayancewa kan ya ce,”Ah’ah Zainabu yau an makara kenan? Ya akayi hakan ya faru Dan nasan ba halinki ba ne.”

Marairaicewa Zainab ta yi ta ce, “Wallahi Malam cikina ke ciwo shiyasa Yanzu ma da kyar na tawo.”

Daga ma ta gira ya yi kan ya ce, “Ayya sannu to maza huce ki shige aji.”

Jidda ta yi kwafa.

Ta na fadi aranta yau insha Allah ko ma miye zai faru sai na yi maganin yarinyar nan.

Murmushi ta yi da ya baiyana afili.

Sannan Malam buje ya fara doka.

A na zuwa kan Jidda ta tsere aguje sai da suka zagaya makarantar nan kaf kan Jidda ta tsaya kan lokacin ma ya gaji, Dan mugunta kuwa sai da ya ma ta bulala daya.

Shige wa aji ta yi ta na ma sa gwalo, “Ai ko ba komai dai wani ya ji ajikin shi, hhh mallam mai buje kawai.”

Tunda Jidda ta shiga ban da tunanin abin da za tayiwa Zainab ba abin da ta ke, ai ko sai lokacin Break ya yi, da sauri cikin yatsine Zainab ta ta so za ta huce Gaban Jidda da gangan ta ta ke wa Jidda kafa.

Karaf Jidda ta tashi nan ta ke ta wanke ta da mari, Zainab ta ce, “Kambu ni ki Ka Mara? Ni sa’arkice.”

Ganin Jidda ta ga Zainab ba ta da niyar ramawa ya sa ta cigaba da dokanta ta na, “Eh din andake ki din ni sa’arkice da zaki takana ki huce kamar kin taka dutse ko hakuri ba za ki ban ba.”

Kamar ta sami jaka dukanta kawai ta ke ta inda ta so.

Zainab kuwa raguwa tuni anfara kuka hawaye da majina ne kadai ke gangarowa daga fuskarta.

Ita ko da taga tana kuka nan ta ke karfi da kwarin gwiwa ya kara zuwa ma ta, tana dukan tana, “Yara sai shegen raini ai daga yau na ga wadda zaki karawa rashin kunya, gwanda ma ki kiyayeni ke kin San karfi na kowa? Ko shi mallam bujen ma kawai ina raga mi shi ne Amman in kuka kai ni makura sai na ma Ku targade akumatu Wallahi.”

Dakyar Ko aka kira Malam buje ya kwaci Zainab a hannun Jidda.

 

Urs Xayyeesherth
[11/15, 4:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://chat.whatsapp.com/KZgI9wMaXS23wEuzgd0ntQ

_*Group di na na zallan mata ne Dan Allah kar namijin da ya shiga, sannan in kin San bakya SHARHI ke ma karki shiga*_

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 18/19_*

****************
************
******************

Jidda sai nishi ake ana wage baki adole yau ta yi duka abin da ba asaba ba.

Zainab kuwa baki ya mutu ko Ido ba ta so su hada da Jidda domin tasan yau ta maku, ko ina Jidda ta samu kawai dabga ta ke ita ko ajikinta.

A na tashi su ka nufi gidan Lantana.

Suna zuwa lantana da dauko kwanan garar da aka kawo ma ta ta ce, “Yauwa Jidda ina shinkafa za a dafa?

Jidda ta daga mata gira, ” Eh ma na shinkafar nan ma ta turawa kuwa. ”

Lantana ta ce,”To yanzu indo ki kunna ma na wutar ni sai in yi dakan kayan miyan.”

Aiko da kyar wuta ta kunnu, kayan miya kuwa andaka su fatso fatso.

Lanata ta ce,”Jidda mun gama.”

Tashi Jidda ta yi ta na ya mutsa fuska, “Yauwa dauko robar manjan afara zubawa, ki dauko waccer katuwar tukunyar, wadda ta fi kowacce girma fa.”

Jiki na Rawa Lantana ta dauko ta mikawa Jidda.

Da Jidda ta fara zuba manjan nan sai da ya yi Rabin galan din kar ta bari, “Gashi nan, kin San Anaso manja ya ji sosai shinkafar ta yi ja ta fi kyau, yauwa dibomim ruwa cikin karamin bokitin nan.”

Ko bari manjan ma ya soyu ba ayi ba aka zabga uban ruwa acikin tukunya, kan nan aka sa fatso-fatson kayan miya.

Jidda ta ce, “Yauwa yanzu ba bare magi guda ashirin azuba, ba zamu sa gishiri ba Dan yan gayu ba sa gishiri a abinci, Yauwa Indo in kin zuba magani ki rufe ruwan ya tafaso kan azuba shinkafar,Lantana ki Auno ma na mudu Daya.”

Lantana ta ce, “To, kiji fa har abincin ya fara kamshi.”

Jidda ta ce,”Ai kadan ma kenan sai ma mun gama dafawa zakiga yadda zatayi.”

Jidda ta karbi shinkafar,Indo ta ce, “Laa Jidda ba Wanke ba fa?”

Jidda ta galla ma ta harara “ni banson rashin kunya to bara Awanke din ba wayace miki yan birni na wanke shinka? To yasin rage dadin ta ake in an wanke Dan haka ba wankewan da za ayi haka za asa.”

Lantana ta ce, “Laa Jidda kaman fa naga su Inna Sai sun cire datti kan ma ake dafawan.”

Jidda ta yi tsaki , “To ai sai ku yi tunda ni zaku koyama girkin in kukayi wasa Wallahi sai in tafi in bar ma Ku girkin nan danma kunci sa’a ina farinciki yau na Zane zainabu Amman da wallahi ba wadda zan koyawa girkinma.”

Lantana ta ce, “Aa ki yi hakuri Jidda ni nama tuna fa haka kawai Inna ke sawa na ta ba ji ma tana cewa In anwanke shinkafa gardinta ake rage wa .”

“eh mana ba ki ga ba wanke taliya ba? Ai shiyasa ita tafi dadi.”cewar Jidda.

Indo ta wage ba ki, ” Au ahe hakane.”

Jidda ta bude tukunya, “Oh ga hutar naci fa Amman ruwan nan ya ki tafasa, Indo za ki cigaba da fifitawa nikam nagaji wallahi.”

Chan Jidda ta Kara budewa ruwan bai tafasa ba, tsaki ta yi ta ce, “Wallahi haka za azuba sa tafaso tare ma, tin da dai ya fara zafi ai Shikenan ta ma fi sauri, ni dama nasani ai da tin dazu da aka zuba ruwan na sa shinkafar atare.”
Lantana ta ce, “Wallahi kuwa.”

Zuba shinkafar ta yi sannan ta dunga juyawa da ludayi, “Bara na ji ko maganin dai ya ji, ta dandana , ” Kai Indo salam Wallahi kara bare guda goma muji.”

Da sauri indo ta kara bare maganin aka zuba.

Jidda ta dandana, “Ah yauwa Yanzu kam ya ji magi arufe ke kuma Lanatan kan girkin ya karasa kije kiyi kwaskwarima in mi ki kwalli ki sa kayan nan na sallanki.”

Lantana ta ce, “Yauwa na ma tuni haka gwaggo ta ce min ina ado.”

Jidda ta ce, “Eh ma na.”

 

Nan fa Lantana ta yi kwaskwarima aka caccaba ma ta fuska.

“Kai Lantana ya naga kinaso ki fini kyau ne aradu daga yau bazan kara mi ki kwalliya ba.” Cewar Jidda.

Lantana ta ce, “Tab nikam ai nasan ko me zanyi baxan kamoki kyau ba.”

Jidda ta ce, “Allah to ba ni mudubin nan ma in kara ganin Dompol di na.”

Kallon kanta ta ke tana wani yatsina fuska, da wani harare harare ta na daga gira.

“Gaskiyarki ne Lantana Gaskiya ni mai kyau ce, kyau iyaka kyau ysn ko makiyi Dompol kon ta zarce kowa, Laaa Indo dubamin abincin nan ki gani.”

Indo tana dubawa ta ce, “Laaa Wallahi ta fara yi kin ga ta fara kwoyaye Asama fa.”

Jidda ta ta so tana, “Yauwa yanzun nan zai karasa tinda ki ka kwayayen ai shine tafasan daman bara na Kara dandanawa inji.”

Ta na dandanawa, “Wooo Gaskiya yau abincin nan fa zai ta fi da mutane.”

Lantana ta ce, “ai ko daga jin kamshin ma.”

Lantana an zauna an harde kafa daya kan daya.

Jidda ta ce, “Indo Kamar fa yamma ta Farayi jeki mokotannan ki jiyo ma na karfe nawa ne?”

Indo ta ce, “To.”

Jidda aka cigaba da juya abinci kamar an sami masa.

Indo ta shigo , “wai karfe uku.”

Jidda ta ce, “Tab Gaskiya Lokaci ya kure, bara abincin nan ya karasa yanzu za mu huce gida.”

Lantana ta ce, “Amman kwa tsaya kuci ai ko Ku tafi da shi ko?”

Jidda ta ce, “Aa mu kam yadai yi ai na bakine gobe maci dumame ni yunwa ma nakeji zanje in ci tuwo na agida.”

Lantana ta ce, “To shikenan.”

Jidda ta kara dubawa, shinkafa tana nan ta yi tsumburun-burun, kana juyawa kana jin karar kasa, ga ruwa kamar gwate, abin dai ba kyan gani.

Jidda ta ce, “Yauwa ya ma yi daga gani, Yanzu ki dauko kwanuka ki zuba ma su ni kam mun tafi sai goben.”

Jidda na isa gida tq bajewa Iya ta na jin yunwa ai ko sandaren dumamen tuwonta malmala uku nan ta ke ta cinye kan ta fara bayani, “Ashe daman ina da karfi na ke bari ake rainani Daga yau wallahi dukan yara zan nayi in suka kawomin raini, ai yau na yi maganin Zainabu.”

Iya ta ce, “Iye karki cemin wannan zainabun mai fantekar fuska.”

Jidda ta kyalyale da dariya, “Yo ina wata bayan ita ai yau sai da nasata kuka wallahi, hhhh da kyar mallam buje ya karfeta.”

Iya ma ta kyalyale da dariya, “Yo ko ke fa ai ni naso ma ki mata targade akumatu domin kina ganin yarinyar nan zaki San ta yi gadon rashin kunya wajen uwarta, lokacin da uwarte ke budurwa haka akayi ta fama da ita ga shegen fitsarin kwance sai da akamatq Aure ta daina fa.”

 

Jidda ta kara kyalyalewa da dariya, “Amman dai anyi babbar banza ina jin ma zainab din na Dan tabawa Dan in tazo makaranta zaki Dan dinga jin bashi bashi.”

Iya ta ce, “Ai ba musu hakane ma.”

******
Su Jidda na fita kuwa sai ga Ummaru da abokan shi.

Ummaru ya ce, “Ah lallai gida ya bime da kmashi ina abincin na mu.’

Lantana tq ce, ” Ku nemi wajen zama yanzu zan kowo abincin.

Ta na kawowa……

 

Urs Xayyeesherth
[11/15, 4:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

14 November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 20_*

****************
************
******************

*_MY GROUP MEMBERS🙁ARADUN ALLAH ZA KU SHA MAMAKI IN NA FARA SHARA_*

Ummaru ya ce, “Yauwa Amarya.”

“Ah mu yi muci kan akira sallar Dan lokaci ya yi.” Cewar Adam

Yusuf ya ce, “Eh kam danni na zaku inci girkin Amarya.”

Ummaru ya ce, “To, toh bara abude, Amman fa yusuf ban da hadama Dan nasan ka Yanzu sai ka wawishe mu muna nan gawo.”

Dariya Yusuf ya yi kan ya ce, “To ai Shikenan bismillah.”

Ummaru ne ya bude kwanon ya na, “Yaw….
Kalmar da bai karasa ba kenan ganin abin da ke cikin kwanon.

Adam da yusuf su ka zaro ido.

Da karfi ummaru ya kwallawa Lantana kira, ” Ina kike ne?”

Ta zo ta na, “Kar dai har kun gama ai akwai saura atukunya in za Ku karama.”

Ummaru ya daga kwanon ya na, “Miye wannan Dan Allah? Na ga Abu kamar gwate?”

Lantana ta raunana fuska, “Girkin yan birni ne Jidda ta mana kuci Wallahi da dadi.”

Ummaru ya ce, “Aa nikam wannan abincin yan birnin ya fi karfinmu.”

Lantana ta daka tsalle ta na kuka , “Ni Wallahi sai kunci ai kai ka sa mu dafa kuma wallahi sai ka ci nikam.”

Ganin ihun ya yi yawa ne ya sa Adam magana, “Shikenan ki yi hakuri za mu ci lantana Yanzu ma kuwa.”

Dariya ta yi ta na, “Yauwa ko kufa.”

Tare su kai loma yayinda suka fara karo da samudawan Kasa, tare da bala’in zakin magani.

Nan ta fe ummaru ya fara kwararo amai.

Adam kuwa aguje ya fice.

Yusuf ko uban yan kwadayi, wularshi bai dauka ba shima ya fice adari.

************Washe Gari da Sassafe Jidda na tsaye kofar gida, kwatsam ta hango motar babanta, da gudu ta karasa ta na bin motar, tsayawa ya yi ya daga glass din ya ce, “Haba Mamana Kina mace Amman kina bin mota da gudu, sau nawa ina mi ki fadan ki dai na wasan banzan nan.”

Sunkuyar da kai ta yi tana wasa da yatsunta cikin shagwaba ta ce, “To ai ni ina murna ne Fa Baba.”

Murmushi Alhaji Ibrahim ya yi kan ya ce, “Amman dai kin San zan karaso ko? Ba ma wannan ba shigo mu karasa kofar gidan.”

Jidda ta washe baki “to abudemin kofar.”

Bude ma ta yayi ta shiga kan ya rufe kofar.

“Baba na ga kazo kuma fa muna da komai ba abin da ya kare yasin in ma Iya ta fadama haka to wallahi mu na da komai fa karya ta ke.” Cewar Jidda.

Alhaji Ibrahim ya ce, “Iye Mamana kakar ta ki ce ta ke karya ko?”

Jidda ta ce, “To ai ke kacemin ba kyau karya kuma wallahi muna da komai fa.”

Alhaji Ibrahim ya ce, “Oh ni kam to yanzu dai ni nazo daukanku ne za mu koma Chan garin kano sai ki cigaba da karatunki acen ko?”

Nan ta ke Jidda ta hada rai, “Tab ni wallahi ba zani ba kalan inje wannan matar ta ta dukana? Tab ni fa MATAR POLICE ce kuma Kaka Iya ta ce min ba a dukan matan yan sanda.”

Alhaji Ibrahim ya ce, “Mamana ban San yaushe za ki girma ba Wallahi yanzu mahaifiyar ta ki ce muguwa ko?”

Jidda ta tabe baki, “Umm to bayan batasona kullum fa dukana ta ke, kuma ma Iya ta fadamin wai batasona ta tsaneni daga kai sai Iya ne fa kadai ma su sona.”

“A’a Mamana kar inkara jin kin kara fadan haka, Mamanki ta fi kowa sonki kuma ba ta tsaneki ba wawancin da kike ne bata so ke ma kin sani kir ki kara Fada kinji.” Cewar Alhaji Ibrahim.

Jidda ta ce, “Umm Amman ni dai bazan je gunta ba.”

Alhaji Ibrahim ya fita tare da zagayowa ya bude wa Jidda kofa ya na, “Yanzu dai zo mu shiga ciki.”

Azuciyarsa kuwa ya na fadin, “Insha Allah yau sai na kawo karshen zamaku akauyen nan nikam nagaji.”

Suna shiga Iya ta washe ba ki, “Iyee Ashe Ironane ahanya daman tinda naji sautin mota jikina ya ba ni cewa kai ne abin ka da kauyen ya tattara matsayita nasan ba wani mai mota sai kai ne ke shigowa.”

Durkusawa Ya yi tare da fadin, “Ina yini Iya fatan mun same Ku lafiya.”

“Lafiya lau Wallahi ya mutan gidan jarababbu fatan an barsu lafiya?”

Murmushi ya yi azuciyarsa ya na fadin, “Oh mai hali dai ba ya fasawa.”

Afili kuwa ya ce, “Suna lafiya ku ma suna gaidaki.”

Tabe baki ta yi, “Ni awa ai ban kai agaidani ba wannan masifaffiyar matar da in anbarta ma dukana zatai.”

Shiru ya yi kawai kasancewar ya rasa abin cewa domin mahaifiyarshi kiris ta ke jira ta fara zubar masifa kamar fanfo

ya na ganka wani iri ne ba gwari ince dai lafiya Dan na ga lokacin zuwan ka ma bai ba watan yau ya cika 10 kuma kai sai karshe ka ke zuwa.”

Kai Akasa Alhaji Ibrahim ya ce, “Lafiyar kenan dai da bata wuce na zo Neman alfarmar ki Yarda in tafi da Ku birni ba insha Allah ba abin da zai…..

Ba karasa ba ta ce, ” Dakata Iro wato ta zigokan ko? Duk wata hanya da za abi a rabani da Jidda nemota ake ko ince ma kashemin ita akeson yi da duka, to wallahi tun huri ka kiyayeni ka tashi ka fitan min agida.”

 

Alhaji Ibrahim ya ce, “Aa Dan Allah Iya ina so ki fahimceni, ke kan ki kinsan ba uwar da zata haifi ‘ya ace ba ta so yana yin Jidda ne ya banbanta da na yan uwanta.”

Ta shi Iya ta yi tsaye tare da tabe baki ta ce, “Magana dai ta fito wato ni ban Iya raino ba ko? Ku na so kuce na lalata ma Ku tarbiyar ‘ya ko? Wai ni ka ke fadawa Magana Iro.”

Fashewa da kuka ta yi ta na face majina da saman zaninta ta ce, “Allah sarki Mallam Ado ka zo kaga yau Dan ka na fadamin magana, ko kai da kake mijina ba ka fadan magana ba sai shi da aka ashirce shi.”

Jidda ta yi tsit ta kalli wannan ta kalli wancen.

 

Alhaji Ibrahim bai San lokacin da shima hawaye ya fara kwararo mi shi ba ya ce, “Ki yi hakuri Iya ki yafemin ban da niyar saki zubda kwalla, zan tafi insha Allah daga yau bazan Kara maganar komawarku birni ba.”

Ya tashi zai fita.

Iya ta ce, “Allah raka ta ki gona.”

Jidda ta ce, “………

😅😅 *Yanzu aka fara, yawan comments yawan typing🥰🥰*

Urs Xayyeesherth
[11/15, 4:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

15November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 21/22_*

****************
************
******************

*GARABASA GA MUTANE UKU DA SU KA FI KOWA YIN SHARHI ZA SU KARANTA HAR KARSHEN LITTAFIN NAN KYAUTA BATARE DA SUN BIYA KO SISI BA*

“Baba ka tsaya, ka daina kuka kaji, Zamu koma Amman sai in ka Yarda Mama da Uncle ba za su ka ra dukana ba.”

Baba na share kwalla ya ce, “Insha Allah Mamana ba mai taba min ke, kin San dai ina sonki ko?”

Murmushi Jidda ta yi kan ta karasa gaban Iya ta ce, “Kaka Iyatuna ki Yarda mu koma kinji kinga ai Baba na son mu in ita bata son mu, kinji kar Baba ya ta kuka mu Yarda mu koma kinji.”

Iya ta ce, “Ni fa ba inda za ni Ehewe ina nan garin daram dam da ke.”

Jidda ta tashi ta fadawa Iya magana akunne nan ta ke su ka kyalkyale da dariya.

Iya ta ce, “Zan koma Amman ba Dan kai ba kuma ba Dan shedaniyar matarka ba illa Dan farincikin Jidda, domin farincikinta ta fiyemin komai hatta nawa ma, indai zan ganja cikin walwala to tamkar ni ce, Dan haka za mu koma.”

Alhaji Ibrahim ya ce, “Alhamdulillah Na gode Iyaa, yanzu za mu Iya tafiya?”

Iya ta galla mi shi harara ta ce, “Kwajiyemin zumudi ai a bari dai inyi sallama da yan gari ko? Dan haka sai gobe, in ka ga za ka Iya kwana to in kuma bazaka Iya ba ka tafi mu zo da kan mu.”

Alhaji Ibrahim ya yi saurin fadin, “A’a Iya zan ma jira Ku ai ba matsala.”

Nan fa tinda Jidda ta fice agidannan ban da bazawa agari za su koma birni ba abin da ta ke fadi agari kowa na jin hakan za su yi Hamdala aransu domin Allah ya ta ba su ka kaikyayin da ke addabarsu.

Lantana da Indo kuwa kuka su ke hakkun domin ji su ke kamar za arabasu da farinciknsu, Jidda ta ce, “Ku dalla Ku daina kuka zanna zuwa ina dubaku fa in kawo ma Ku kayan birini, kayan abincin dadi har ma da na sawa kunji, Yauwa Lantana Ku zo ma muje ayi tsokanar karshe.”

Indo ta ce, “Nikam dai fa ba na so ki tafi ga bikina fa watan gobe ni ko irin kwalliyar Da kikewa Lantana ba ki taba min ba.”

Jidda ta ce, “Dalla chan ai zan zo zan fadawa Babana ya kawoni, ni dai damuwata yanzu mu yi tsokanar karshe kinga gobe da safe za mu tafi.”

Lantana ta ce, “To ko dai kasuwa za mu shiga ne?”

“dilla can kin manta yanzu ke matar Aure ce in mu ka shiga kasuwa ummaru zai gan mu fa kuma kin San za ayi Fada.”

Lantana ta ce, “umm Shikenan to Yanzu ina za mu je?”

Jidda ta ce, “Yauwa muje gonar Malam bala mai kan tabarya hhhhhh wayyo Wallahi goshin mutumin nan dariya ya ke ba ni.”

Indo ta kyalyale da dariya, “Ai Wallahi ni goshin sa ma kadai na ke son ja fa.”

Lantana ta ce, “Ai ko mu rufawa kan mu asiri Dan naji Ummaru na cewa ciwon hauka ya kama Malam balan fa in akaje gonarshi bugu ya ke.”

Jidda ta ce, “Ku ji ma fa sallah ake kira in ban koma gida Yanzu ba Baba zai min Fada kin San yazo, gobe da safe kan mu tafi sai kuzo gidan kunji.”

Lantana ta ce, “To Shikenan.”

Indo ta ce, “to muje in raka kan na wuce gidan.”

Su ka tashi sai da Indo ta raka Jidda gida kuwa kan ta tafi, Jidda na shiga gida.

“Mama tun da kika ci abinci fa kike fice agidan nan sai Yanzu.” Cewar Alhaji Ibrahim.

Jidda ta shagwabe fuska, “Umm Baba fa na je sallama da Kawaye na ne.”

Gudun kar ya takura Iya ta tunzura ya sa shi fadin, “Allah dai kyauta to.”

Iya ta ce, “Ameen Uban kanzagi.”

Jidda ta ce, “Iya ina shinkafar kince ita zaki dafa da daddare.”

Iya ta ce, “Yoo gatanan ki diba na bar mi ki atukunya.”

Sai da Jidda ta makare cikin roba kan ta zauna ta cinye tas, Baba kawai tsayawa ya yi kallon ikon Allah ba halin magana, mamaki ya ke da irin ci na Jidda.

 

****Washe gari da sanyi Safiya Iya ta fara tattara kayan su harda su tukwane.

Baba ya ce, “Iya akwai komai na girki agidan ba sai kin dauka ba.”

Harararshi ta yi Tare da fadin, “Ni to zan tafi da nawa ina fadama ba abin da zan bari agidannan gwandama ka ji ehee kalan mu je ana raina mu akan abincin Da Jidda za ta ci? Bar ni na tafi da komai nawa.”

Haka Baba ya yi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Jidda ma ko ta na nan tana hada tarikicenta.

Sai da suka kwashe komai kaf su ka yi wanka, ganin baba ya sa Jidda yin wanka ba musu.

Sun fito za su tafi Iya ta ce, “Ayya mai gari nasan zai yi kewarmu ka bi da mu ta gunshi mu ma sa sallama.”

 

Mai gari na ganin Jidda da Iya sai da gabanshi ya fadi ya ce, “Hajiya Iya ba dai wani laifin aka ma Ku ba.”

Dariya Iya ta yi ta ce, “Aa fa maigari sallama na zo yi ma za mu koma birni da zama.”

Wata irin ajiyar zuciya maigari ya yi wadda sai da ta bayyana azahiri.

Ya ce, “Ayya Yanzu dai za Ku tafi ku bar mu kenan Amman da Jidda zaki tafi?”

Iya ta ce, “Eh Wallahi tausayinka kawai na ke na tafiyar nan ta mu shiyasa na zo ma sallama.”

Wani irin dadi maigari yaji aranshi fal farinciki azahiri kuwa kukan munafurci ya fara kakalowa, “Ai Wallahi ko ni ne abin tausayi nasan kaf garin nan sai ya yi rashin ki, Allah sarki Hajiya Iyatu kamar in bi Ku Wallahi.”

Nan ta ke ma Iya ta fara kuka ta na goge majina da bakin zani ta ce, “Allah sarki Anya ma zan Iya tafiyar nan ko ni kam na fasa tun da dai ka ke kuka.”

Da sauri mai gari ya share hawayen tare da Jan majina ya durkusa gabanta tare da fadin, “aa ba za ayi haka ba nikam na hakura Wallahi na yafe mu je ma in rakaku.”

Maigari ya kalli ya Fada ya ce, “Maza Ku hanzarto mu raka Hajiya Iyatu.”

Haduwa sukayi duka suka nufi hanyar rakiyar Su Jidda, Lantana da Indo sai kuka ake za arabu da Aminiya.

Jidda ko sai washe baki ta ke tana, “Lantana karki damu in kin haihu ai zan zo suna da bikin Indo.”

A haka dai har su ka isa Motar sai da maigari ya tabbatar andaina hango motar su Jidda kan ya ce, “Alhamdulillah Nagode wa Allah, Allah raka ta ki gona yanzu ba ni ba jin batun mutuwa.”

Jidda da Iya kuwa tunda suka shiga mota ban da barci ba abin da su ke sai da aka kusa isa garin kano su ka farka.

Kamar jira Jidda ta ke asauka ta na fita ta fara tsalle-tsalle ki cibis ta bangaje wani Matashin saurayi.

Ko juyawa ta kalle shi ba tai ba bare ta bashi hakuri.

Hakan ya sa shi saurin shan gabanta tare da kwalla ma ta wani hamshakin mari, ya cigaba da tafiyar shi.

Kuka ta fara ta na, “Allah ya i San min wallahi mugu kawai azzaalumi mai kan tabar…

 

Urs Xayyeesherth
[11/19, 2:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

16November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 23/24_*

_*Free pages na daf na karewa wa inda ba su biya ba su hanzarto domin biya tare da samun cigaba akan lokaci*_
****************
************
******************

Tabarya, kuma sai Allah ya sa ka min.”

Ta na ta tsine-tsine dawowa ya yi, ya tsaya ya kare ma ta kwallo da kyau jikin shi ya ba shi cewa wannan yar uwar shi ce, duk da kasancewar bai San ta ba kuma bai taba ganinta ba sai yau, tsanarta ya ji kawai ya shiga ranshi nan ta ke domin in akwai Abin da KHALEEL ya tsana bai wuce rashin kunya ba,bayan ya gama kare ma ta kallo, wani hamshakin tsaki ya yi sannan ya ya juya da niyar tafiya.

Ita ko Jidda kan ta akatsa ko kallon fuskarshi ma ba tai ba bare tasan waye har sai da taji takun tafiyarshi na barin wajen kan ta murguda baki tare da dogon tsaki kan ta ce, “Aikin banza duk da ban ga fuskarka Amman zan ganeka da wannan zoben hannun na ka, kuma wallahi sai na rama Marin da ka min, mugu kawai duk gida anbi antara mugaye kawai, kuma duk sai na gyara ma Ku zama.”

Iya ce karaso tana fadin, “Jidda wai ina ki ke ne? Daga zuwa naji kin fara un-uni kar dai wani ne ya ta ba min ke?”

Jidda ta ce, “Wani ne fa wai Dan natakashi ba da Sanina ba shine ya mareni, kuma fa ni ban sani ba.”

Iya ta ce, “Lallai ma suna so daga yau in fara tsine ma su kenan ko? Gida duk anbi antara azababbu mugaye agida to wallahi ba zata sabu ba.”

Mama da Mariya sun fara jin kwaroroton Iya hakan ya sa su saurin fitowa.

Mama ta durkusa , “Ina kwana Hajiya.”

Kau da kan ta gefe tai tare da amsawa kamar me shan magani.

Mariya ta ce, “Ah Hajiyar mu an iso kowa sai ya San da zuwanki.”

Iya ta ce, “Ba dole ba daga zuwa har an taba min abar so na.”

Mama ta ce, “Iya Kiyi hakuri yanzu dai mu shiga ciki.”

Iya ta ja Jidda su ka yi gaba fuuu.

Mama ta tsaya ta na fadin, “To Allah ga mu gareka, Allah ne kadai ya San yadda zaman gidannan zai kasance.”

Mariya ta ce, “Mama Kiyi hakuri ai anyi mai wuyar tunda suka Yarda su ka dawo komai zai yi dai-dai.”

Mama ta ce, “to mu shiga kar wani abun ya biyo baya ni ban San ma waye yadaketa ba tunda dai duk antafi makaranta, Uncle ma ya na kasuwa KHALEEL ne kadai ya fita yanzu.” Ta na maganar har su ka shige ciki.

 

Iya zaune akasan kafet Jidda kuwa ta Dane kan kujera ta na kwance ga kafa duk datti kamar an kwato ta daga filin dambe.

Kawar da kai Mama ta yi kawai daga baya kuma wani tunani ya zo ma ta tace, “Jidda ko gaisuwa ba bu? Ko ba ki ganni ba ne?”

Jidda ta murguda baki tare da fadin, “Ni ai bakyasona ni bazan gaisheki din ba ni ke ba mamana ba ne, Kaka ta fi sona tinda ita bata dukana.”

Dan takaici Mama ba ta Iya kara fadin uffan ba, sai zuwa ta dauko abinci da tayi.

Ajiye ma su foodflask din tayi gaban su sannan ta dauko flat da cokali.

Da sauri Jidda ta sauko ta bude flask din ta na ganin abinci jallop din shinkafa ce taji nama da kifi akalla mutane biyu zuwa uku za su ci su koshi.

Jidda ta fara ci tana, “Iya kice fa ta kawo mi ki naki abincin ke ma kin San yunwa na ke ji, wannan ma da kyar ya isheni.”

Iya ta ce, “ai kinga irin matsalar da na ke jiye ma na kenan anzo abincin ma ba za a ba mu ishasshe ba sai an mana rowa, maza zainabu in za a Iya atashi adafamin nawa abincin yanzu in kuma da sauran na Ibrahim ki ba ni shi ya nemi wani abincin.”

Mama ta ce, “Iya ki kalli abincin da ke cikin flask dinnan fa? Wallahi ko namiji ma da kyar za asamu mai Iya cinye abincin nan bare wannan yarinyar.”

Iya ta rikye baki , “Abu yanzu ni ki ke fadawa maganar nan iye? E sabida ke kin saba da yiwa ‘ya’ya mugunta ai ba za ki ba su abinci ishasshe ba to ni ba na haka kinga abincin nan? To tas Jidda za ta kare shi kuma atanadan ma ta na anjima ma.”

Iya na jin sallamar Alhaji Ibrahim ta fara kukan munafurci, “Zainabu yanzu ni zaki ce ba zaki bawa abinci agidannan ba? Ni za ki hana abincin da ‘Dana ya fita ya nemo, ni za ki ciwa zarafi, daman nasan ni ba so na kike ba daman ai da kina da dama da tuni kin illatani.”

Mama tsayawa ta yi kawai ta ma rasa abin cewa, Iya sai da ta tabbatar baba ya ji komai kan ya na shigowa ta kara fashewa da kuka.

Tsawa Baba ya yiwa Mama tare da fadin, “Wannan wani irin iskancine? Mahaifiyar tawa za ki bari da yunwa da ace ta ki ce ni zan mata haka ko ko? Ke za ki mata haka? Kin nunamin cewa mahaifiyata ba komai ba CE awajenki ko.”

Durkusa wa Mama ta yi ta ce, “Ayi hakuri akasi aka samu, bara na dauko abincin.”

Dauko abincin Baba ta yi ta ajiye wa Iya agabanta dagowan da zatayi sai hawaye, Jidda na ganin hawayen nan ta kyakyalle da dariya, “Hhhh Katuwa na kuka.”

Da sauri Mama ta bar falon, Mariya ma ta bi sahun bayanta ta na kuka.

Iya ta ce, “Munafukan banza munafukan wofi mu har agaya mana munafurci mu da mu ke namu akasan rafin maliya ma da gangun kifaye, an koyawa ‘ya ma munafurci kai wannan lamari dole in gyara ma Ku zama agidannan.”

Baba ya ce, “Adai kara hakuri Hajiya ki ci abincin sai ki yi wanka Kiyi sallah.”

Iya ta ce, “Sallar dai ko? Ai naga na yi wanka da safe kan mu tawo ko ance ma ni ma agwagwace kamar waccer MATAR ta ka? To bazan ba kuma ba mai sani dole, ba gwanda ni ba ma ina wankan sau daya arana mahaifinka kan ya bar duniya sai ya yi wata bai sa ruwa ajikin shi ba, wani lokacin da dambe zan je in fadawa kakanka ya zo ya taimaka a mishi da girmanshi.”

Jidda ta kyalkyale da dariya, “Ashe su kaka dai antaba Kazan ta.”

Iya ta ce, ‘Sosai ma Yo ai Wannan kadan ma kikaji.”

Baba ya San In Iya ta fara zuba ba kakkautawa hakan ya sa shi gaggawan fadin, “To adai yi hakuri, ni bara na shiga masallaci in kun gama in gyara dakin tin jiya kuma nasa ankai kayan da kukazo da su.”

Iya ta na sharban loma ta ce, “To to Masha Allah.”

Da sauri Baba ya fice afalon ba inda ya fara nufa sai Dakin Mama wadda suna zaune da Mariya ban da kuka ba abin da suke.

Da sallamarshi ya shiga ya ce, “Farincikina, dole ki yi hakuri, ban da wata mafutar da ta wuce wannan, ke kan ki kinsan halin Hajiya tunda ma bare yanzu da tsufa ya kamata, magaifiyata ce dole mu yi hakuri da ita mussaman akan Jidda da ba wanda ta bari ni kai na ma da na ke danta ba ta barni ba, bare ke da kike matata, yi mata biyayya ya zama dole agareni ko da ba na so Indai ba zarce ka’idar musulunci ba ya wajaba akaina, dawo da su gidannan ba karamin jahadi bare Wanda ke da kanki ki ka kara karfafamin gwiwa domin inganta rayuwar ‘yar mu, kin ga kuwa hakuri tare da kau da kai akan lamarinsu ya zame ma na dole, mussaman Jidda sai munyi kokarin janta ajiki, Mariya ina so daga yau ko fita za kiyi kunayi tare, kan asan makarantar da za a sata.”

Mama ta share hawaye ta na fadin, “Ni lamarin Hajiya ba ya da muna ko kadan wallahi, damuwata Jidda ne da bata daukeni abakin komai ba illa wadda ta tsana abin nan na min zafi wallahi, inda wadda na Ke so aduniya bayan Jidda ne wallahi, ita ce ‘ya ta karshe wadda na daura buri na duk a kan ta Amman kaddara ta shiga tsakanin mu .”

Baba ya ce, “Ki daina fadin hakan insha Allah komai zai huce, Yauwa dazu na ga KHALEEL da mu ka iso Allah ya sa dai lafiya ko?”

 

Mama ta ce, “Hmm to za ace Lafiyar kenan, matsalar dai ta Hajara ce, har yanzu ita fa bata shirya haihuwa ba gashi shi kuma ya kasa hakuri da son ‘ya’ya, kuma shi ya na sonta ba zai iya ma ta kishiya ba, na rasa ta inda zan fuskantowa lamarin.”

Baba ya ce, “Yanzu irin case din da ake ta fama da su kenan wallahi Allah dai ya kyauta bara na je sallah, kuma kuyi sannan Ku koma falon kar abarsu su kadai.”

 

Urs Xayyeesherth
[11/19, 2:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

18 November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 25_*

****************
************
******************

Washe gari.

Jidda da Mariya zaune afalo Mariya na chatting, sai ga sallama.

KHALEEL ne ya shiga cikin Uniform din sa na Police Rai abace ya zauna yana, “Mariya ina Mamane?”

Mariya ta dago ta kalle shi tare da fadin, “Ah Yaya Khalil kai ne? Ai ko Yanzu Uncle ya fita, Mama kuma tana dakinta.”

 

Kallon agogon hannunsa ya yi cike da takaici ya ce, “Owk wato ba zai Iya jirana gaba ai ya kyauta bara na je na sami Mama daman ni gun ta na zo.”

Jidda ko tana gaban TV kallon Tom and Jerry ban da kyakyala dariya ba abin da ta ke.

Wuce wa Khalil ya zo yi kwatsam ya taka igiyar TV ya dauke.

Tsaki Jidda ta yi tana, “Wannan ai Iskanci ne kawai mutum ya na kallo anzo an kashe, Allah ya isana wajen da aka tsallake ban ga ni ba.”

Mariya ta ce, “Ke Jidda miye haka ba ki da kunya ko?”

Murguda mata baki Jidda tai ta ce, “To ni waya ce ya ta ba min kallo na.”

 

Kamar zai yi gaba ya dawo baya ya kare ma ta kallo ya tuna da abin da ya hadu su ajiya tsaki ya yi tare da karasowa gaban ta, bakinta ya riko da hannunsa ya na, “Ke ba ki da kunya ko? Ko dai makauniyace ke? Wawiya kazamiya kawai, ki fita a idona Tin ka saki agaba.”

Jidda na kokarin yin kuka ya kara bige bakin ya na, “Ni ban ma San me ya kawo wannan sharar gidannan ba, Mariya anya ko wannan ba yar tsutuwa Mama ta jajibo ma na ba ko?”

Mariya ta kyakyalle da dariya Yaya Khalil adai yi hakuri abar ta haka in ka shiga ka tambayi Mama.

Tsaki ya yi ya sake ta tare da tashi domin tafiya.

Da gudu Jidda ta mikye tana, “An Fada din wallahi Allah ya isan min mugu mai kan mangoro bakin gwanda kawai gatun banza da wofi kuma kai ne kazami ba dai ni ba.”

Abin ya matukar bawa KHALEEL haushi tafiya ya yi kawai ba tare da ya waigo ba.

Ya na shiga ya sami Mama ta sa Qur’ani agaba tana karatu.

Sallamarsa ce ta katseta ta amsa tare da kokarin rufewa, “Ah KHALEEL har ka iso anji asibitin an cire ko?”

Cike da takaici Khalil ya ce, “Ina fa Mama ni kam na hakura kawai duk sanda taso ganin ‘ya’yan ta je acire.”

Mama ta ce, “To shikenan Amman ya naga ranka abace ko wani abun ne kuma?”

KHALEEL ya numfasa kan ya ce, “Wata yarinyace wallahi, wai ma wacece ne yarinyar nan tin jiya fa zan fita ta takeni ni ko na maketa.”

Mama ta yi tsaki kan ta ce, “Jidda ce wallahi, ni nasan ba mai aikata wannan lamari sai ita.”

Khalil ya ce, ” Jidda dai Auta Mama? Kar kice Min itace ta zama Mara kunya haka?”

Mama ta ce, “Hmm ka manta ne kai kafi kowa sanin damuwata bai huce halin da Jidda ke ciki ba, gashi andawo da itan ma ni naga kamar abun karuwa ya ke, Yanzu za ta yi abu ka yi magana Hajiya Iya ta fara tsine ma ka.”

KHALEEL ya ce, “Ai ko ni Wallahi Indai zan zo gidannan to sai na gyarama Jidda zama daga ita ma har ita Hajiya Iyan.”

Mama ta yi murmushi ta ce, “Khalil ai da ka taba Jidda gwanda ka rufama kan ka asiri ka taba koma waye, yau ka ga Hamza na School, Uncle kuma ba ya zama tunda Alhaji ya fara tafiye- tafiyen nan wace makaranta ka ke ganin yadace akayi ta duk da tafara a kauye dai Amman yakamata amaidata baya kasan karatun chan da nan ba daya ba ne bare bana jin cewa ma ta na wani kokartawa.”

KHALEEL ya ce, “Zan sa aduba ko ta su Ameera ne asata.”

Mama ta ce, “yauwa hakan ma ya fi.”

 

KHALEEL ya ce, “Bara na koma office ni kam Dan nasan yanzu za kiji anfara kirana.”

Mama Ta yi dariya, “ai kuwa dai kai kam ba ka da hutu in ka bar office kamar komai ya tsaya sai ka dawo sun ta damunka da kira kenan.”

Khalil ya ce, “Bari kawai Mama.”

Jidda na labe tana jin KHALEEL zai fito ta shiga kicin da sauri ta dibo mangyada.

Dai dai kofar fita ta je ta kwarara mangyadan da ya ke golden ne mutum ba zai lura ba.

Ya fito kenan aka fara kiranshi awaya tsaki ya yi, ya kalli wayar ya ce, “An fara kenan.”

Kara sauri ya yi domin fita ya na yiwa Mariya magana, “Ki min magana A WhatsApp ina so mu yi wata magana.”

Kan Mariya ta amsa sai ga Khalil tim akasa.

Jidda ta kyalkyale da dariya tare da shige wa ciki.

Ba karamin buguwa KHALEEL ya yi ba domin ya ma kasa motsawa da sauri, Mariya ta kira Mama su ka fito.

Urs Xayyeesherth
[11/19, 3:56 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

19November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 26/27_*

****************
************
******************

 

Iya ma da saurinta tana, “Munafukan banza Munafukan wofi to nima sai na ga abin da karewa buzu nadi, e ankira mahaifiya tazo ni kuma ko oho to gani nima.”

Ganin KHALEEL dumus akasane ya sa Iya yin shiru.

Mama mika mi shi hannu, ta ce, “Sannu to wai ma mai ya kawo danko wajen nan ne ikon Allah, Mariya ko yau Laure ba tai mopping ba ne?”

Mariya ta ce, “Aa na ga ni tun safe ta yi ma kan ta daura breakfast.”

Da kyar KHALEEL ya tashi jiki duk ya yi tsami.

Mama ta ce, “Anya zaka Iya driving din ma ko?”

Ya tsina fuska ya yi ya ce, “Ah zan kokarta insha Allah na ji kaman targade ne ma na yi akafar , zan biya agyara kan na shige gida.”

Iya ta ce, “Sannu Dannan kaji, mutan gidan ne sun San salon mugunta kusufa-kusufa sai hakuri.”

Mama da Mariya kawai kawar da kai su ka yi.

KHALEEL ya ce, “Ayya Hajiya ai ba komai sauri na ke ma ban sami damar shigowa na gaisheki ba.”

Iya ta ce, “Ayya ince kai ne Dan Yayan Zainabu ko?”

KHALEEL ya ce, “Eh ni ne.”

Iya ta ce, “Naga kama kam in kaje kace ma Hajiya mun zo gari fa, yakamata ta zo ta gan mu.”

KHALEEL na kokarin dingisa domin shiga mota ya ce, “To.”

Jidda ce ta fito ta na kyakkya dariya har da rikye ciki ta ce, “shikenan wani ya zama gurgu, hhhh Dan gurgu zo inma jagora.”

Cije baki Khalil ya yi tare da kawar da kai cike da jin radadi ya bude kofar motar ya shige.

Mama ta ce, “Jidda ke dai Allah ya shiryaki ni ina shakku ma in ba ke kika zuba mangyada agun nan ba.”

Karaf Iya fara surfa bala’i , “Ku jiye min
Iskanci abin har ya kai ga sharri? Yaushe mu kazo gidan da har za ace ta San ta dibo wani mangyada ta zuba ma sa, to ahir din Ku walle ban son takura na fada ma Ku daga ke har yar korar yar ta ki.”

Janyo Jidda ta yi tana, “Maza zo mu shige, kinji yar albarka.”

Jidda ta bi Iya ta na waigowa tare da yiwa Mama gwalo.

Suna shiga Daki Jidda ta kyakyalle da dariya, Iya ta ce, “Kaniyarki kinji ko ai tunda na ga idonki nasan ke ki ka zuba mi shi mangyada kina ganinsa da Kayan Yan Sanda fa to walle in ya zo tafiya da ke ni ba ruwana ban koya mi ki haka ba tam.”

Jidda ta shagwabe baki, “Umm ni fa shine dazu yatabamin kallona kuma ya matsemin baki, gashi ya ce min kazamiya ni kuma bazan Yarda ba ai ni ba kazamiya ba ce.”

Iya ta ce, “kyaji dashi dai ni dai in yazo tafiya da ke ba ruwana tunda dai ke baki jin magana.”

 

Jidda ta fita tana, “Ni dai Wallahi duk wanda ya ta ba ni sai na ta ba shi ni ina ruwana da mutane.”

 

*****Sai da KHALEEL ya je aka gyara mi shi targade kan ya nufi gida.

Da sallamarshi ya shiga Hajara na zaune ta na aiki da system din ta, ta amsa da cike da Murmushi.

Da kyar ya karaso sannan ya zauna.

Hajara ta ce, “Soulmate ya na ga kaman da kyar ka ke tafiya Office din fa?”

Numfasa KHALEEL ya yi kan ya ce, “Hmm Wallahi targade na yi agidan Mama.”

Hajara ta ce, “Ayya Sorry Sannu ka ji.”

“Yauwa Dan Allah ki taimaka min da ruwan zafi mana.” Cewar KHALEEL.

Hajara ta bata rai tare ta ce, “Ayya Soulmate aiki fa na ke, bara dai na kira Jummai ta kawo ma.”

KHALEEL ya ce, “Haba Hajara Yanzu Dan Allah ki na nufin aikin ki ya fini mahimmanci ne? Ace komai sai dai mai aiki ta min Amman ke kwatata bakya kishina kullum ki fita aiki nima na fita shikenan burinki, kin ma fita aikin bai wadatar ba agidan ma bazaki ajiye kiji Dani ba? Haba Dan Allah.”

Tashi ta yi ta na, “Soulmate! Kai kam ai daman kiris ka ke jira ka farawa mutum masifa nikam dai aiki na ke Yanzu, wannan masifar sai tasa na ma manta inda na ke bara na haura sama in turoma Jumman sannu kaji Allah kara sauki, Love you.”

Tafiya ta ke tana waka abinta hankali kwance, shi ko KHALEEL ta kai ci ne ya kudumemasa akirji tun abin baya dumunsa har ya fara damunsa domin lamarin Hajara kullum cigaba ya ke daga tace ba za tai wannan ba sai wancen ita dai son duniya da karya kawai ta sa agaba.

 

Kan mu yi nisa nasan masu karatu za su so sannan wanene KHALEEL.

KHALEEL dai da ne ga Alhaji Muhammad tare da mahaifiyarshi Hajiya Maryam wadda ta kasance Yayace ga Hajiya zainab mahaifiyar Jidda,shine Dan sa na fari Wanda tunda su ka haifeshi Allah bai kara ba su haihuwa ba sai bayan shekara a shirin da su ka sami Yan Biyu Amira da Amir wa inda su ke sa’anni ne ga Jidda.
Asalin Sunan KHALEEL Ibrahim ana masa lakabi da KHALEEL ne domin Sunan mahaifinshi yaci, Tun ya na karami ya ke da sha’awar zama Dan sanda Wanda mahaifinsa ya dauki aniyar cika ma sa burinshi har Allah ya yi kuwa, sai da ya fara aiki kan Allah ya hada shi da Hajara, ya na matukar son ta ita ma ta na son shi har Allah ya sa su ka yi auren soyayya, Amman matsala daya da Hajara kwata-kwata ba ta da lokacin KHALEEL kullum cikin aiki da yawon biki na yan karya yan uwanta, ko daga cokali ba ta yi agidannanta hatta daki sai dai mai aiki ta gyara, girki ma ko ita batama Iya ba bare ta yi, sannan tasa aranta cewa ita sai ta cika shekara biyar da yin aure kan ta haihuwa dan ita ba za ta haihu Yanzu tai saurin tsufa ba, duk irin son yara na Khalil dole Hajara ta sa shi ya ajiye agefe, sannan ta raina danginsa ko biki ko suna Indai ba na danginta ba ko bata zuwa

KHALEEL mata shi ne kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa ya na kokari wajen ibadarsa, ya tsani rashin kunya da raini arayuwarsa,hakan ya sa ko kannnensa ba ya wasa da su bare wasu, ya na da mutukar zurfin ciki in kika ga furta Abu to ya kai shi makura ne ya rasa hanya, kuma wannan dinma sai dai ya sanar da Mama kadai wadda ta kasance uwar dakinsa, ya shaku da mama fiye da mahaifyarsa domin ita ta raine sa tin yana karami,tare da Uncle Wanda ya kasance yaro ne Dan tsuntuwa da Alhaji Ibrahim ya tsinta ya mai dashi tamkar Dan shi, amman uncle ya sa wata mummunar niya azuciyarshi ba ya ga nin alkairin da aka mai,,, makusar Khalil Daya ya na shaye-shaye tare da bin matan banza , Wanda zan Iya cewa ya na da halaka da Matar shi Hajara domin kulawar da ba ya samu daga gareta.

KHALEEL ya na matukar Son hajara hakan ya sa bai da niyar Karin Aure ko kadan aransa ya gwammace da bin mata tare shaye-shaye, tun ya na gudun matan da kawo mishi hari har ya kasance shi da kan shi ya ke Neman su domin biyawa kan shi bukata.

Kadan kenan daga cikin tarihin KHALEEL.

CIGABAN LABARIN

**************abun ka da namiji har KHALEEL ya ware kwana biyu, Mama ta kirashi domin ya zo ya kai Jidda makaranta.

Tunda Jidda ta ji cewa za a ka ita makaranta ta ke murna Amman da aka mata maganar wanka sai ta fara kuka.

Har Khalil ya zo anata fama da Jidda ta ki yin wanka, fincikarta ya yi kawai ya shige da ita Toilet ya fara ma ta wankan, Ihu ta ke tana, “Wai ana dole ne ni to ka bar ni zanyi da kai na mugu kawai ruwan fa na zafi wayyo Allah Iya na kizo ki kwaceni ZAI kasheni Wallahi.”

Ko saurarenta KHALEEL bai ba sai da ya ma ta wanka tsaf sannan ya fito daga toilet din ya na, “In kuma ki ka tsaya wasa Wallahi man ma sai na shafa miki in sa miki kaya, office fa zan tafi kina batamin lokaci ana jirana…..

*_MY GROUP MEMBERS LAST WARNING KO A GYARA KO IN DAINA DAGA YAU AM SERIOUS🤷‍♀️_*
[11/24, 10:58 AM] Xayyeesherth: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

21November 2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 28/29_*

****************
************
******************

Hajiya Iyatu ana jin tsoro da kyar aka Iya cewa, “Ayya D’ana adan barta ta shirya da kan ta.”

KHALEEL ya ce, “To.”

Wata irin shegiyar dafaffiyar doguwar Riga Jidda ta sa, ko hijabi babu sai wani fingilin Dan kwali ta fito ta na, “Na gama.”

Wata irin tsawa KHALEEL ya ma ta wadda sai da ta ra zana ya ce, “wannan wani irin kaya ne? Dalla jeki cire kuma ki dauko hijabi ba na son iskanci fa.”

Murguda mi shi baki ta tsaya yi, “To ai ni sauran kayan sallah na ne.”

KHALEEL ya ce, “Kin san Allah ko ki chanja kayan nan ko na baki mamaki ta ke awajen nan.”

Komawa daki ta yi ta na un’uni daga karshe sai ga ta fito cikin wata atamfa mai Dan kyau dai-dai gwarwado, Amman ba hijab.

Cikin fushi KHALEEL ya ce, “Ina hijabin?”

Tebe baki Jidda ta yi, “Ni ban da shi.”

Kallon Mariya ya yi ya ce, “Ki ba ta Aron hijabi ta sa Dan bazan tafi da mai sufar slinda tsirara ba.”

Da sauri Mariya ta dauko ta na, “Amman fa ya mata yawa nasan har kasa zai kai mata ma.”

KHALEEL ya karba ya mi ki mata, “Eh tasa hakan.”

 

Fita sukayi KHALEEL na sauri ya shige wajan driving ita ko ta tsaya chak kallonta ya yi sannan ya ce, “Bazaki shiga ba ne ko sai na mammakeki awajen kazamiyar banza da wofi.”

Murguda baki ta yi ta ce, “Ni dai ba kazamiya bace kuma ni ban Iya budewa ba.”

Tsaki ya yi yana, “Bagidajiya sai rashin kunya Amman ba abin da aka Iya.” Fincikarta ya yi ya bude kofar ya na hankadata kamar mai tura kura.

Zama ta yi tana, “Allah ya isan min wallahi, kuma sai na fadawa Babana, mugu kawai.”

Kallonta ya yi sannan ya ce, “In baki min shiru ba wallahi yanzu zan Ciro bindiga in harbeki haba yarinya sai ka ce yar Aljanu.”

Tunda Jidda ta yi maganar bindiga ta ta gama razana hadda rikye baki ta kasa motsawa, ji tai cikinta ya fara murdawa, sai tusa bumbubum da karfinta ga bala’in wari.

 

Tsaki KHALEEL ya yi ya na, “Miye haka wannan wani irin iskanci ne da salon kazanta.”

Da ya yi kokarin to she hancinsa da hannunsa ya ga dai abin ba da sauri ya nemi waje domin yin parking ya fice ya na rikye ciki,ba iyaka hanci ba, har cikin cikinsa ya Ke jin warin tusar Jidda da ke kokarin galabaitar da shi.

 

Ita ko Jidda ban da dariya ba abin da take hadda ya rikye ciki.

Ga KHALEEL da kyankyami duk ya bi ya tsargu ban da yawu ba abin da ya ke zubarwa.

Tunawa Yayi da turaren da ke cikin motar da sauri ya koma ya feshe motar da turaren kan ya shiga ya zauna, “Wallahi in kika Kara min tsinanniyar tusarnan sai na jefarki waje, kazamiya kawai ke bazaki Iya cemin zakiyi tusa ba in tsaya ki fita kawai Dan iskanci sai ki min amot….

Ba karasa ba kawai shima sai ga tusa wadda ta fi ta Jidda ma kara illa banbanci da ita ba tai wari ba.

Kyakyallewa da dariya Jidda ta yi ta na, ” Wayyo garde ya yi tusa, hhhhhh kai meyasa baka fita ka yi awajen ba? Ai da ka gwada fita mun gani.”

Har cikin ranshi ba karamin kunya ya ji ba, Amman ya daure tare da fadin, “Ki min shiru ko na harbeki Wallahi.”

Azuciyarsa ya na mai takaici tare da fadin, “Ni dai na hadu da jangwamgwam ko na yi shiru sai tasan yadda ta yi sani yin magana dole Anya wannan yarinya ba Aljana ba ce in ma ko ba aljana bace to tana da aljanu ajikin Amman zan yi maganinta insha Allah.”

 

Suna isa kofar makarantar da sauri ya bude ma ta kofa ya na, “Maza ni ki yi sauri duk adalilinki na makara wajen aiki.”

Jidda ta chuno baki ta na, “Eh dai eh dai na ji dadinta ma ni dai ni karamace Amman kai kato da kai kana tusa.”

Tsaki ya yi kawai, ya cigaba da tafiya.

Suna shiga office din da ya ke headmastern ya abokin Khalil ne ya ce, “Ah abokina ai na zata ma ka fasa kawotan ne sai gobe.”

Khalil ya girgiza kai”Aa dai gata nan ko play class amaka ta Dan zubin kauyece.”

Dariya Umar ya yi, “Lallai abokina ba ka da dama kana ganin katuwar budurwa ka ce asata a ajin wasa, ba ma nan ba, ya naga kaman Ku daya ta ma fi kama da kai fiye da Amir da Amira ko daman yan uku ne?”

Tsaki ya yi, “Aa fa ni ka bar hadani da kwailar nan, yar Mamanace.”

Karaf Jidda ta ce, “Ni Wallahi na fishi kyau kaf garin mu ma ansan ni kyakkyawace shi da ya ke tu………

Mari ta ji ya sauka afuskarta , gudun kar ta mai baram barama ya sa shi saurin marinta domin karshen maganar ba ta huce na tusa ba.

Kuka ta fara ta na, ” Mugu azzalumi kawai, ni Allah ya isana.”

KHALEEL ya ce, “Iyee rashin kunyarki har anan ma ko lallai zanyi maganin…

Bai karasa ba wayarsa ta fara ringing ya na dagawa ya yi saurin dagawa Umar hannu zan tafi kawai ka yi abin da ya dace.

 

Ko da Umar ya sa aka ma ta interview ya ji matukar mamaki domin ba yadda ake tsammani ba ne, hakan ya sa shi kai ta ajinsu Amir da Amira kawai primary three.

Ko da ya kai ta bancin su Amira ya ajeta ya na, ” To Amira ka kawarki nan kuma yar uwarki.”

Da sauri Amira ta ce, “Ke ce Jidda ko? Daman Yaya da Mama sun fadamin za akawoki makarantar mu.”

Jidda ta ce, “Eh mana Amman yayankin nan mugu ne fa, ni wallahi na tsaneshi ko yanzu ma sai da ya mareni.”

Amira ta ce, “Laa Yaya Khalil din? Ni dai ba ruwana.”

Malami na shigowa kowa ya mikye ya gaidasa ban da Jidda da ke zaune hankali kwance.

Lekowa ya yi ya na wace gwanarce zauna ba ta shi ba, cikin harshen turanci.

Wata baiwa Jidda na jin duk abinda za afada ma ta da turanci amsa ce dai ba ta Iya ba dawa ba.

Ta yike tasan da ita ya ke cewa ta yi, “Na me Na Jidda I no go tsayawa walle, sabida in Our gari an ce ba kyau.”

 

Tsabar salo na turancin Jidda daga yan ajin har malamin ban da dariya ba abin da suke, daga karshe ma kawai cewa ya yi kowa ya zauna.

Lokacin yin drowing ne ya yi, shi su ke da a time table hakan ya sa Malam Ahmad yin drawing din kuliya, tare da rubutu a kasa THIS IS A CAT.

Bayan ya gama rubutawa Ya ce, “Wacece ko waye zai karanta min? Jidda ta Riga kowa daga hannu, hakan ya sa Uncle Ahmad zabanta ya ce, ” Oya Jidda muna saurarenki.”

Da karfin ta cike da karfin gwiwa ta ce, “This is a kuliya, mis mis kuliya.”

Ilahirin Ajin ba su San sanda suka tsinci kan su da yin dariya ba, Jidda kuwa tsalle ta yi ta na, “Yeee to atafamin mana, mu fa a garin mu ana tafawa.”

Uncle Ahmad cikin dariya ya ce, “Oya clap for her.”

Tun daga ranar Uncle Ahmad ya ji Jidda ta shiga ranshi komai ta yi kawai birgeshi ta ke.

Ko da aka tashi driver ne ya zo ya dauke su, Amira ta ce, “Jidda ina gidan mu zakije?”

Jidda ta ce, “Aa ni akai ni gidanmu bazani gidanku yayanku mai tusa, yata dukana ko ya harbeni ba. ”

Haka kuwa akayi Jidda aka fara kai wa gida kan aka kai su Amira da Amir.

Jidda na shiga gida kuwa ta tarar da Mumy (Hajiya maryam) ta zo suna ta hira da Hajiya Iya.

Mumy ta ce, “Kakata andawo kenan, ya baki bi su Amira da ba, ai da anjima driver ya dawo da ke.”

Jidda ta ce, “Ni Um-un bana son gidanki Wannan Yayan dukana ya ke, dazu ma ya min wanka fa tab.”

Murmushi Mumy ta yi ta ce, “Ayya Sorry Kakata ki yi shiru kinji ko, in kara dukan ki ni zan rama miki da kai na.”

Jidda ta ce, “Yawwa, ni yunwa Nakeji iyatu abincina, wayyo cikina.”

Mumy ta ce, “Je ki gun Antynki Mariya ki karbo abincin ina jin ai ta kammala.”

Da gudu Jidda ta shige kicin , “Anty Mariya Yunwa na ke ji mai aka dafa.”

Mariya ta ce, “Taliyace ga tanan in zuba mi ki ne?”

Nan ta ke ba magana Jidda ta baje a kicin din kasa ta fara kuka, “Wallahi bazan ci taliyar ba, ni tuwo zanci ni innaci taliyar zukyemin jini ta ke, wayyo Allah na.”

Da sauri Iya da Mumy su ka nufi kicin ba shiri, hatta Mama da ke daki ma sai da ta fito, sun zata wani Abu ne ya same ta.

Suna shiga Mariya ta ce, “wai ba za ta ci taliyar ba.”

Iya ta fara surfen masifa, “Ai daman wannan salon mugunta ne kawai ace safe taliya rana taliya taya abinci zai zauna acikin mutum to Wallahi tun wuri adafa ma ta tuwo yanzun nan ko kuma ni na shiga kicin din in dafa.”

Da sauri Mama ta shige ta na, “Bara in daura Mariya ki min jajjjage.”

 

Jidda kuwa tashi ta yi ta fice waje abinta.

Ta na fita ta ga yaron makota na wasa ta ce, “Kai zonan.”

Yaron ya zo da akalla bai zarce shekara biyu ba.

Ta ce, “Mamanka ta ma wanka kuwa ?

Ya ce, ” Aa.”

Nan ta ke Jidda ta fara tubeshi ta kai sa gaban famfom da ke kofar gidan ruwan sanyine sosai Amman ta tasa yaron mutane gaba tin bir ta na jikashi.

KHALEEL ne ya zo wuce wa amota daga office zai je wani aiki.

Hango Jidda ya yi tana ta faman dirzan jikin Dan mutane, kaman zai wuce sai kuma ya tsaya.

 

Urs Xayyeesherth
[11/24, 10:58 AM] Xayyeesherth: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

24November 2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 30/31_*

****************
************
******************

Dago glass din Motar ya yi, ya kalleta sannan ya fito.

Ya na fitowa saukar rankwashi kawai Jidda ta ji a kanta, tun kafin ta dago kai ta ga waye ma ta fara, “Allah ya Isa na Wallahi, mugunta kawai.”

Dagowa ta yi suka hada ido da KHALEEL ta yi saurin kawar da kai ta na, “Yaron nan fa ya ce min Mamanshi ba tai mai wanka ba shine na Ke mi shi.”

KHALEEL ya ce, “Ke din ma kin Iya yiwa kan ki ne bare Dan wasu? Kuma bakya ganin ana sanyi ne? Na Lura Ke kam dai mahaukaciya ce, Shashasha.”

“Ni dai ba mahaukaci….

Kan Jidda ta karasa magana sai ga mahaifiyar yaron nan ta fito ta na kumfar masifa.

Banda iskanci A sanyin ki jikamin yaro da ruwa, wannan ai iskancine ba yarinta ba.

Ta na karasowa ta maka wa Jidda Mari afuska, Jidda ta ce, ” Mugu Azzaluma kawai.”

Nan fa ran MATAR nan ya kara baci hakan ya sa ta saurin harzika tare da Fara jibgar Jidda.

Ban da Ihu ba abin da Jidda Ke yi.

Ta fara , “Yaya Dan Allah ka ce ma ta, ta barni haka Wallahi daga yau bazan kara mi shi wanka ba, ni ba ma ruwana da shi.”

Kallonta KHALEEL ya yi,tare da yin dogon tsaki, ko kala bai ce ba ya yi wajen motarshi ya bar wajen nan ta ke.

Mata kuwa sai da ta jibgi Jidda son Ranta kan ta kyaleta, ba shiri da gudu Jidda ta shige gida ta na haki.

Mumy ta ce, “Kakata ina kikaje ne haka tun dazu an gama tuwon Amman an dubaki ba a ganki ba?”

Jidda ta ce, “Umm ni ma ban San inda aka kai ni ba kawai gani nai nadawo.”

Ta shi ta yi ko wanke hannu ba tai ba zata fara cin tuwon.

Mumy ta ce, “Aa dai aje awanke hannunku.”

Ta shi tayi tana tsallenta ta shige toilet ta wanke kan ta fito ta fara zakar tuwo.

Tunda ta fara cin tuwon nan Mumy Ke ganin ikon Allah har sai da Jidda ta take tuwon nan tsaf abincin da mutane uku za su iya ci Amman ga yarinya nan yar shekara Tara ta cinye tas.

Ta na gamawa Mumy ta ce, “Sannu Fa Jidda, Yawwa Hajiya Iya wai ya maganar yan Jigawane Malam Adamu?”

 

Iya ta tabe baki , “Yoo ina nasan ma yadda ya ke mutumin da ya manta da mu gabadaya, ina so Ibrahim dai ya zo ya kira min shi asalularsa asanar da shi Maganar Auren Mariya in ya yi niya yazo shi da iyalan na sa.”

Mumy ta ce, “Ah yakamata kam ya zo gaskiya.”

 

Malam Adam ‘Dana ga yar uwar Hajiya Iya kasancewar Iyayensa sun rasu tun yana yaro hakan ya sa Iya ta Rainasa tare Alhaji Ibrahim,Malam Adam ya na da matukar son abin duniya arayuwarshi ya dage sai ya yi kudi ya zarce Ibrahim, duk da kasancewar shima ya na da rufin asiri dai-dai gwargwado Amman ya fi hange kan na Dan uwansa,hakan ya sa ko waiwayen Hajiya Iya ba ya yi bare kuma Alhaji Ibrahim.

 

Mama ce ta fito daga daki ta na, ‘Yawwa Mumy daman Alhaji ya ce inya dawo daga tafiya za mu je siyayyen kayan bikin, kin ga kwanaki na ta tafiya gashi mu ne dangin Amarya kuma dangin ango.”

Mumy ta ce, “Hakane kam Uncle dai kam ai ya yi sa’an uban gida, ya rainesa kuma ya bashi kyautar ‘ya, kin ga ai sai mu tafi duka da ni, da Ke, da mariyar, har ma Da Hajiya Iya, kin San yaran yanzu da su ake zuwa siyayyen komai na zamani ya chanja.”

Karaf kuwa Iya ta ce, “Ai kuwa dai, ni fa lokacin Aurena, ko Iya hada ido da iyayena ba na iyayi, Amman yanzu Ku tsabar rashin kunya ma naga da yaran kuke shawara, gaskiya duniya ta zo karshe, ko gobe ko jibi sai ku Iya jin ance tashin alkiyama ne.”

Mumy ta ce, “Hajiya Iya gobe talata jibi laraba fa kuma ai Ran juma’a ne za ai tashin alkiyama.”

Iya ta ce, “Au ki na so ki cemin ba ma juma’an ba ne yanzu? Lallai to ni azatona ma ai yau juma’an ne duniyarce duk kun bi kun rikitata.”

 

Dariya Mumy ta yi ta tashi ta na fadin
, “Wai yaushe ne Alhajin zai dawo?”

Mama ta ce, “Ina jin gobe ma insha Allah.”

“To Allah ya kai mu, bara kiga na huce gida nasan su Amira kadai ne agida sai dije mai aiki.”
Cewar Mumy da ke kokarin fita daga gidan kenan.

Mama Ta tashi za ta bi ta Iya ma ta tashi za aje ayi munafurcin ba to muje tare kanwa uwar gami.

*******WASHE GARI

Dassafe Mama ta sa Jidda ta shirya domin driven su Amira na hanya zai zo ya kai su skul.

Sabon uniform din da aka dinka ma ta,ta kalla kawai sai ta fara kuka , “Ni Wallahi bazan sa wannan dangalallen guntun sket din ba, ai ni ba yar iska ba ce, Wallahi bazan sa ba.”

Iya ta ce, “Ina bayanki walle Dan haka ke ba yar iska ba ce ba Wanda ya isa ya saki ki sa wannan danalallen skilen kamar mai tallan jikinta, kalan ma ki fita ace mi ki karuwa, to Wallahi ahir din ki Zainabu Jidda ba za ta sa ba ah to na dai Fada mi ki, ki ma fice min da gani tun kan na tsine mi ki na tsinewa kankan kakarki.”

Ba yadda Mama ta iya da Hajiya Iya haka ta fita, sai wata shawarar ta zo ma ta, ta kira Baba ta sanar da shi, ya ce ta kai wa Jidda wayar.

Da ke Mama tasan halin Iya ta na shiga ta ce, “Hajiya wai Gashi za Ku gaisa da babansu.”

Da sauri ta fizge wayar ba ni naji Dana.

Ta kafa ta akunne kamar zata manne awajen Baba ya gaisheta ta amsa sai washe baki ake, ya ce, “Ah ya na ji kamar muryar Jidda ne ko ba ta je makaranta ba ne yau.”

Iya ta ce, “Ina fa zataje makaranta bayan ankawo ma ta kaya wani irin na yan iskan zamanin fir’auna.”

Baba ya ce, “Ayya Iya Kiyi hakuri ta sa ba kayan yan iska bane uniform ne, na yara kuma haka ake yin sa, Amman inna dawo za asan yadda za ayi.”

Iya ta ce, “To shikenan ba ra dai mu gani.”

Ta mikawa Mama wayar, Mama na fita.

Iya ta ce, “ai in sun San wata ba su San wata ba, ni dai bazan barki da shigar iskanci ba dauko ki sa ki ga wani Abu.”

Da Jidda ta sa uniform din nan ba karamin kyau ya ma ta ba tamkar Dan jikinta akayi.

Nan ta ke Iya ta dauko wani tsohon zanin leshinta ta ce, “Yawwa matso nan in daura mi ki, tunda su yan iska ne ai mu ba ma biye ma su ba.”

Haka Jidda ta fito ga uniform ga zani daurin kirji, zama ta yi ta zabga uban kwalliya kamar me tafiya tashi, sannan aka sa sandal da safa, tafiya ta farayi kamar wadda kwai ya fashewa aciki adole ita ta yi kyau.

Mama na ganin Jidda daga sama har kasa Dan takaici bata San lokacin da ta fara dariya ba, Mariya ma na fitowa ta fara zabga dariya harda rikye ciki.

Iya ta ce, “Iskancin banza iskanci wofi, mu za agayawa iskanci ai mun nuna ma Ku mun fi Ku iyawa ne.”

Mama dai tai tsit.

Mariya ta ce, “Dimple Queen ina zuwa haka? Kamar mai zuwa tashe Amman dai ba makaranta za ki ba ko?”

Jidda ta murguda wannan bakin da ya sha Dan Jan baki kamar manja ta cigaba da tafiya ta na rankwasa ta ce, “Makaranta ma na ai ni ba yar iska ba ce.”

Ta na fita sai ga driven ya zo, shi kan shi sai da yayi dariya ganin shigar da Jidda ta yi, Amir da Amira ma ban da dariya ba abin da su ke.

Ita kuwa Jidda ko ajikinta ga ni ta ke ta yi shiga tare da kwalliyar kera sa’a.

Suna shiga Makaranta ban da kallon Jidda ba abin da ake ana dariya Amman ita hakan fa ko ajikinta, malamai sun yiwa Principal magana Amman ya ce abarta.

Fita break aka yi Jidda da Amira su ka fito waje suna cin abinci.

Wata yarinya ta zo wucewa kawai ta taka wa Jidda kafa, Jidda ko na tashi ta wasketa da Mariya nan ta ke yarinyar ta fadi aka sa.

Jidda ta ce, “Laaa Amira yasin Aljanune da wannan yarinyar fa kin ga ta fadi.”

Amira ta ce, “To kin ga mu tashi ba ruwanmu.”

Jidda ta ce, “Tab Wallahi ni sai na mata magani Hajiya Iya ta koyamin yadda ake rukiya.”

Amira ta ce, “To nidai ba ruwana Wallahi.”

Jidda ta kama kunnen yarinyar ta na gwaranci, ba abin da bata, har A,b,c,d da 1,2,3 ma sai da suka sami damar shiga.

Chan dai jikin Jidda ya fara Duran ruwa taga yarinya ba ta da niyar farkawa, chakulkulu ta fara ma ta ta na, “Wallahi Ku saketa na Fada ma Ku Ku saketa in ba haka ba kakata za ta tsine ma Ku.”

Ashe daman yarinya iskancine tana jin an fara chakulkulu ta fara motsawa.

Da guji Jidda ta bar wajen sai da zanin ta ya fadi akasa tsabar gudu wai ajanune Ke bin ta abaya.

Ita ko Amira ban da dariya ba abin da ta ke…

Haka Jidda ta koma gida, ba zani, Iya na ga ni ta fara salati da sallallami, “Ni kuluwa na shiga hamsin ya na ganki tsirara?”

Jidda ta gwalalo ido, “Aljanu na gudunwa shine su ka zaremin zanin ni ban ma San ya fadi ba sai da muka koma aji.”

Iya ta kyalkyale da dariya, “Ke ki ka San shakiyancin da ki ka yi dai, Babanki ma ya dawo tashi muje.”

 

________Bayan kwana biyu.

Tun ranar da KHALEEL ya rankwashi Jidda bai kara zuwa gidan ba ko ince ba su kara haduwa ba sai yau da yake weekend ne kuma bai da aiki a office, Hajara ya dauko daga wajen salon kasancewar motar ta ta sa mi matsala, hakan ya sa shi cewa ta rakashi ya gaida Mama kan su wuce gida da kamar ba za ta yarda ba, da kyar dai ta yarda su ka shiga.

Ya na shiga ya Tarar Mama na fama da Jidda ta tsefe kan ta ta ki yarda fir, wai ai satin kitson biyu kuma sai ya yi wata kan ta tsefe.

Da shigarsu Tsawa KHALEEL ya ma ta, nan take Jidda ta fara fitsari awajen tana kuka, Iya na ganin Jidda na kuka itama ta fara, da sauri ta tashi ta shige daki ta kwaso kayansu ahargitse ma ta kulle azaninta, kuka ta ke bilhakki da gaskiya,ga kaya aka da ta daura ta fito ta na, “ke kina mata shima ya zo ya na mata ni na gama lura da Ku in ba kashemin ita kukayi ba bazaku taba jin dadi ba, yau zan bar ma Ku gidannan daga ni har ita sai Ku ta yi,” in ta yi magana daya biyo sai goge majina da saman zani, ana kara kakkalo wani hawayen.

Janyo Jidda ta yi tana , “Muje.”

Daga Mama har KHALEEL summan tsaye su kaj awajen har ma sun ka sa motsi bare magana.

Hajara kuwa Jan gefe ta yi tana danna wayarta hankali kwance.

Suna fita sai ga Baba ya shigo Mama ta kirashi awaya, da ya ke bai yi ni sa ba.

Ko kallonsa Iya ba tai ba ita dai yau sai sun koma kauye.

Jidda kuwa ta ji dadin zaman birni har ga Allah bata son komawa.

 

*SHIN YA KUKE GANI? YA DACE ACE JIDDA DA IYA SU KOMA KAUYE, KO KUWA ZAMAN BIRNIN DAI ZAI FI??? MAJORITY CARRY D BOTH*

Urs Xayyeesherth
[11/26, 10:03 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

26November2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 32/33_*

😂 *ARADU KAMAR AN TOFE LITTAFIN NAN YAWANCIN FANS DIN SA OUT OF 100% , 80% MA SU SUNA AISHA NE😂 ABIN DA MAMAKI FA TAKWARORINA NE MASOYA, WANNAM FEJIN SADAUKARWA NE GAREKI NAMESY AYSHA SHU’AIB, TARE DA AYSHATUL-HUMAERA, DA KE MA AISHA🤣DA AYSHER🤣BAN MA SAN YANDA ZAN BANBANTAKU BA WALLE😂KAWAI DA MA DUK WATA MAI SUNA AISHA INA YIN KU IRIN SOSAI DINNAN🥰🥰*

****************
************
******************

😂😂 *NA LURA MASOYAN DOMPOL KON BA SA SO TA KOMA KAUYE, DAMAN GWADA KU NAI AI ZAMAN BIRNI YA ZAMA DOLE GA JIDDA, TUNATARWA DAI FREE PAGES NA DAF DA KAREWA DAN HAKA DUK WADDA TA SHIRYA SIYA TA MIN MAGANA*

Baba ya durkusa gaban Iya ya na, “Dan Allah ki yi hakuri ko me aka mi ki daga yau basa a kara ba,in sha Allah, ki ya fe ma na.”

Iya ta ce, “To ban da fitsara da iskanci ga ta tsarkin yan tsafta za ta addabarmin diya wai sai tai kitso, ana dole ne? Na ga ita kan ta lokacin da ta aureka a yar gajarta ta ke, ga kai kaman hammatar yan iska, ai ko gwanda jiddan ma ta gajemu tai gashi sak kamar na yan indiya, shine ake bakin ciki ko, hnmm za asha mamaki fa agidannan.”

 

Mama ta karaso” Hajiya Dan Allah ki yafemin na tuba, bazan kara ma ta magana akan komai ba.”

 

Iya ta kada kai tare da fadin, “Yoo ina ma kika ganmu bare ki kara tursasata yin wani abun, na Fada ma Ku fa ba abin da zai hanani barin gidannan Yau.”

 

Daga Mama har Baba ba su San sanda hawaye ya fara zubowa daga idanunsu ba, mussaman Baba da ya San Iyah za ta Iya rabuwa da kowa ma indai akan Jidda ne.

Janyota tai suka cigaba da tafiya ta na hama min masifa, KHALEEL da ya tsaya kallon ikon Allah ne ya yi saurin shan gabansu.

Shima durkusawa Ya yi kamar yadda Baba ya yi, “Hajiya Dan Allah ki yi hakuri, ba za akara takurawa Jidda ba, ai ni na za ta ma kitson kan na ta ya kai shekara ne ba a tsefe ba, da nasan sati biyu ne ma ko magana bazan yi ba.”

 

KHALEEL na magana hanjin cikin Iyahtu na motsawa domin duk a tsorace ta ke gudun kar ya dauko bindiga ya ce zai harbeta cikin sauri ta ke fadin, “Yawwa Dan Albarka daman nasan da ka sani ai bazaka tabamin jikalle ba ko? To Yanzu dai ina bakazo da bindiga ba?”

KHALEEL ya fahimci tsoron bindiga karara afuskar Iyah hakan ya sa shi fadin, “Aa Amman na barta amota ko in dauko mi ki ne?”

Ta na ji ya ce ta na mota ta yi wata irin ajiyar zuciya da ya kai karshen maganar kuwa
Wani irin zaro ido Iyah tai tare da fadin, “A’a A’a Dan Allah ka bar ta ni inna ganta ai suma zan, na yarda za mu koma Amman fa kama Mamanku magana in ta kara tabamin ‘ya Wallahi sai taga baje kolin iskanci agidannan, in mu ka fita ba ma zamu koma kauyen ba duniya zamu shiga.”

KHALEEL ya ce, “Ba ma za ayi hakan ba insha Allah.”

Mika hannu ya yi zai karbi daurin kayan, Hajiya Iyah ta ce, “O’o bar ni inshiga da kayana.”

Jan Jidda tai su ka koma ciki, ta na shiga ta ga Hajara zaune ban da danna wayarta ba abin da ta ke Iyah ta kalleta tare gyatsine baki, “To fa wannan mai zubin tabaryar daga ina?”

Jidda ta kyakyalle da dariya su ka shige dakin su .

 

Mama da Baba suna ta yiwa KHALEEL godiya domin sun San in ba dan KHALEEL ba yau ba Wanda ya isa ya hana Jidda da Iyah barin gidannan.

 

Murmushi kawai KHALEEL ya yi ya na, “Bara na je na kira Hajara mu tafi nasan ta gaji da jirana yanzu.”

 

Suna shiga Mota Hajara ta fara banbamin masifa,” in ban da wulakanci ka tafi ka bar ni zaune kamar ka Shanya wake?”

KHALEEL ya ce, “Am So Sorry Madam baki ga case din da ya tashi ba ne, yakamata in tsaya in gyara tunda har da ni aka bata.”

Hajara ta ce, “ai shisshiginka ya ja ma, to ma wai wannan yarinyar daga ina? Ga shi ma na ga kaman kuna kama duk da dai ban wani tsaya kallonta ba.”

KHALEEL ya ce, “Hmm kanwata Autar Mama.”

Tsaki Hajara ta yi, “Ka ji da shi dai in ma Matar ka ce.”

Dagowa KHALEEL ya yi ya kalleta, “Haba Hajara mai zan yi da kanwata kuma? Kanwar ma Jidda, Allah ya sawake Wallahi kin chuceni ma, ko da wata ce awaje banjin zan Iya kara mi ki kishiya bare wannan yar shilar me nasama ya ci bare ya ba na kasa.”

Dariya Hajara ta yi, “Yoo waya sani Abu aduhu Ai sa an laluba akan San na kwarai,hhhhhh ni ko ma zan so ace an baka wannan yar shilar ko na huta.”

KHALEEL ya ba ta rai, “Stop it, Sweety ba na son irin wannan wasan kin fi kowa sani tam.”

Duk kasancewar KHALEEL ya san wasa Hajara ta ke Amman ran shi ya matukar baci tun da ta dangan ta shi da Jidda kuma ma amatsayin ma ta, tsanar Jidda ne karara ya shiga ran shi, jima ya ke kwata-kwata ba ya son kara ganinta domin ya tsani yarinyar maganar ta ma inda hali bai son akara a inda ya ke.

1wk ltr

Jidda zaune afalo ban da tsalle-tsalle ba abin da ta ke yi, Hamza ne ya shigo da Sallamarsa da gudu ta je ta rungumesa , “Oyo yo Yayana.”

Mamaki Hamza ya yi ganin Jidda agidan na su.

“Ah Jidda yaushe Ku ka zo?”cewar Hamza.

Jidda ta ce, ” Tab ai mun jima tun kwanaki fa har ma Baba ya sani makaranta, Yawwa Yaya Hamza ka dawo Dan Allah za ka goyani?

Hamza ya rikye baki, “Kin gan ki Yanzu ai kin zama katuwa inna goyaki Mama za ta yi Fada, kin ga ma fa yunwa na ke ji, ya na ji gidan shiru, ina Anty Mariya da Mama?”

Jidda ta ce, “Anty Mariya ta je rabon ankon bikinta kuma ta ki tafiya da ni, Mama da Kaka kuma kowa ya na dakinsa.”

Hamza ya ce, “Owk shikenan Yanzu dai bara na Je nai wanka na yi alwala, inna yi sallah ma gaisa.”

Hamza na shiga daki Uncle ne ya shigo da sallamarshi, ko kallonsa Jidda ba ta yi ba, domin ta tsani mutum nan haka kawai batare da tasan dalili ba.

Ya ce, “Jidda ina Mariya.”

Murguda ma shi baki ta yi, “Ta tafi anguwa nima ban sani ba ma.”

Kallonta ya yi kawai ya cizan bakin sa ya wuce daki.

Kwanan KHALEEL wajen bakwai bai leka ko gidan Su Mama ba, sai da ta kirashi awaya ta ji lafiya kan ya yanke shawarar zuwa, Amman azuciyarsa ba abin da ya ke Addu’a illa Allah ya sa kar ya hadu da Jidda domin Dan ita ya kauracewa gidan ko kadan ba ya son ganinta ga yanayinta ya ki ficewa daga idanunsa ko ya yarufe ita kawai ya ke hange.

Ita kuwa Hajara ta sami abin yi, ta na ganin sa zata fara angon Jidda ikon Allah, ma su kitso duk bayan wata guda.

Kamar kullum dai yau ma shigarshi ya yi cikin Kanikinsa na yan sanda, ya yi matukar kyau ban da tashin kamshi ba abin da ya ke.

Hajara ta kalle shi tare da fadin, “Ango agaida Amarya Dan nasan wannan wankan sai Jidda ikon Allah.”

Ko kallonta bai yi ba sai tsaki da ya jefar ma ta ya fice.

Driving ya ke ahankali kamar Wanda bai son Zuwa in da za shi bare ma amsar hakane ba son zuwa ya ke ba.

 

A haka har ya isa dai-dai get din gidan hamdala ya yi azuciyarsa da Allah bai sa ya fara karo da Jidda ba, bude ma sa mai gadi ya yi sannan ya je ya yi parking awajen da aka tadana domin yi.

Fitowar da zai yi ko ba wadda ya fara tozali da ita illa Jidda, tsaye ta yi daga daga da kwakwar manja daga bakinta har hannunta.

Kallonshi ta yi ta na washe baki, ya yi kokari domin kawar da kan shi, a zuciyar sa kuwa ya na fadin, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Wucewa ta zo yi gaban shi ta, taka mi shi kafa, zafin zuciya nan ta ke ya wasketa da mari, ita ko Jidda kyankyame shi ta yi, ta shafe shi da manjan da ke hannunta duk uniform din ya baci.

Bai Ankara ba kawai sai ga ni ya yi ta zura aguje ta na mai gwalo kallon jikinsa ya yi kan ya lura da abin da ta mai, shima bin ta ya yi aguje tamkar yaran da ke wasan kasa.

 

Urs Xayyeesherth
[11/27, 10:25 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

27November 2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 34/35_*

😂 _*Salon fa ya chanja Amman Jidda bazata taba chanja wa, kurumin Ku yanzu aka fara*_🥰🥰
****************
************
******************

Ya na bin bayanta Jidda ta shige dakin Hajiya Iya, tsaki Khalil ya yi, ya kalli jikinsa cike da takaici ya nufi dakin Mama.

Ya na shiga Mama ta ce,”Subhannallah KHALEEL miye ne ajiki uniform din ka na ga kamar manja?”

KHALEEL ya ce, “Hmm yarinyarcen Ma na ina wata bayan ita.”

Mama ta ce ,”Jidda ba, na sani za ta aikata fiye da hakan ma, sorry ka je bangaren su Uncle da Hamza ka sa wani kayan, ka kawo uniform din Mariya ta wankema A washing machine Yanzu zai bushe ka samu ka tafi.”

“OK to Ashe fa Hamza ya dawo biki, lallai yaron nan ma ba ya son zaman makaranta.” Cewar KHALEEL.

Mama tai Murmushi ta na, ” kai ma dai kasan Hamza ba zai yarda ayi bikin nan ba shi ba.”

KHALEEL ya ce, “Ai kuwa hakane bara na je in cire tun kafin mayun nan su fara addabata da kira.”

Bangaren su Hamza ya nufa domin cire uniform din ya na cirewa kuwa ya bai wa Hamza ya kawo ma Mariya shi ko ya zauna ya danna wayarsa.

 

Jidda ce ta fito daga Dakin su domin zuwa wajen yayanta tafiya ta ke ta na mita , “Ni wallahi sai ka goyani Yau dinnan tin da ka dawo kullum sai dai katamin wayo nikam dai yau bazan yarda ba wallahi sai an goyani.”

Da karfin ta ya bude kofar ta Fada dakin tana tsalle tsalle, alamar mutum dai ta hango hakan ya sa ta rufe Ido tare da yin tsalle ta Dane bayan KHALEEL. ”

Abin ya matukar ba shi Mamaki ya zata hamza ne ya shigo, ita ko Jidda sai kara kankyameshi take ido rufe ba ta ma San waye ba.

Fisgota ya yi daga bayan shi ya sauketa kasa nan ta ke Jidda ta wangale ido.

Abin da tagani ne ya sa ta suman tsaye, KHALEEL daga shi sai singileta da gajeran wando, kara kallonsa ta yi sama da kasa, hadda murza hannu a ido domin kara tabbatar da cewa ba mafarki ta ke ba, ta ga dai KHALEEL din ne kuma ayadda ta gan shi, nan ta ke ta zura aguje.

Ta bar KHALEEL tsaye ya na mamaki azuciyarsa ya ke aiyanawa, “Anya kuwa yarinyar nan ba yar iska ba ce? To in ba haka ba miye na zuwa ta haye bayana hadda rungumeni?” Chan dai sai ya tuna wani Abu tsaki ya yi, ya na , “Allah ya kyauta.” Sannan ya cigaba da danna wayarsa.

Jidda ko na fita ta shige dakin Iyah ta na haki, “Wallahi Dan iskane, ba kaya fa ya zauna adakin, tab Wallahi shima Dan iska ne,nikam dai ba ruwana dama ban gan shi ba.”

Iyah ta ce, “ke dalla fadamin waye ne? Wai waye ne?”

Jidda ta ce, “Yaya KHALEEL fa, ina shiga dakin su Yayana na gan shi ba kaya.”

Iyah ta yi wani hamshakin tsaki kan ta ce, “Yo daman ke sai yau ki ka sani? Ai daman Dan iska ne, Dan haka ma daga yau kar in kuskura in kara ga ni kina mai dariya ko washe bakin nan, kalan ya je ya iskantamin ke, ni fa ma nagama ganoshi son ki ya ke Wallahi.”

Jidda ta ce, “Kambu ni dai Wallahi ba na son miji me tusa, tab me zan yi dashi ma, kullum ya na cika min daki da wari, kuma ya na zama min ba kaya tab ni dai ba ruwana.”

Hajiya Iyah ta ce, “Ai ko ma kina son shi ni kam dai ba na so , wa inda ma suke kisa tab, ai sai ya hada dani da ke ya kashe, gaki ke me Sarar cewa ke MATAR POLICE ce to Yau kin ga ni daman na Fada mi ki duk yan sandan nan fa yan iska ne ah to ni dai ba ruwana.”

Jidda ta gwalalo ido, “Ni fa Yanzu na daina son Dan sanda, daman akauyene na ke Fada Dan kar su rainani Amman yanzu kam nadaina ba ruwana da mai tusa Wallahi.”

Hajiya Iyah ta tabe baki, “Ohon ma ki dai, ki na ganin shi ya na zare ido sonki ne ni naga alama, azamanin mu na da in saurayi na son budurwa za ki gan sa kullum idon nan azare kamar sabuwar gujjiya.”

Jidda ta kyalkyale da dariya, “Tab wayaga mai idon gujjiya ni kam no me no you, aradu, hhhhhh, ba ni ba hi, turanci ma fa na mi ki.”

Iya ta ce, “Ni dai kam ba ni waje ki ga, Gobe za mu tafi siyayyen Mariya.”

Jidda ta tabe baki, “Nikam dai na tsani wannan Uncle din mijin Anty Mariya Wallahi, ba na so ya aureta mugu ne.”

Iyah ta ce, “To ai ita dai ina ta na son sa? Dan haka baki isa ki hana komai ba.”

 

Washe gari da sasaafe su Mama da Hajiya Iyah su ka kintsa domin tafiya siyayyen kayan auren Mariya, har ma da Baba, da ita kan ta Amaryar.

Anzo za atafi kenan Mumy ta zo amotarta, Jidda ta ce itakam ba zata bi su Mama ba, ita Motar mumy za ta bi, haka kuwa aka yi.

Baba ke driving, Hajiya Iyah na gaba, Mama da Mariya kuma abaya.

Motar mumy kuwa daga driver sai Jidda Da mumy abaya.

Tafiya su ke cikin kwanciyar hankali da nishadi, har su ka isa wajen.

Komai Mama ta samo sai ta mikawa Jidda, ita ko sai murna ta ke tana amshewa Mama ta ma manta da cewa siyayyen Mariya akaje Jidda kawai ta ke zakulowa kaya tamkar itace amaryar.

 

Sai da suka gama siyayya tsaf har sun kusan isa gida, karaf Babbar Mota ta hau kan Motar su Mama.

Ba karamin hatsari akayi awajen ba, nan ta ke, Baba da Hajiya Iyah, Mariya Allah ya dauki ran su, illa Mama da ke da sauran numfashi, duk da kasancewar itama ba asa ran cewa ba za ta rayu ba.

 

Inalillahi-wa’inna-ilaihir-raji’un kalmar da Mumy ke iya furtawa kenan.

Ganin Gawawwaki akasa kwance nan ta ke Jidda ta sume awajen lamari ya Dada rinchabewa.

 

Mumy ta rasa inda za ta sa ranta hakan ya sa tai saurin kiran Dady, da KHALEEL awaya.

Da ya ke kasuwar ba nisa gareta ba nan ta ke Daga Dady har ma KHALEEL da yan office din su suka hallarci wajen, Mama aka fara yiwa taimakon gaggawa sannan aka dauketa aka nufi da ita Asibiti, Jidda ma asibitin da aka kai Mama aka kaita, Hajiya Iyah ko da Mariya, da Baba gida aka nufa da su domin yi ma su sutura akai su makwancin su.

 

Har sai washe garin da aka kai binne su Hajiya Iyah kan Mama ta fara farfadowa, kamar amafarki Jidda ta ji motsin Mama, nan ta ke itama ta farka, Ta na farka wa ta tuna da abin da ya faru nan ta ke kwalla ya faru zubo mata tana fadin, “Iyata, Babana, Antyna,duk sun ta fi Mama, Mama ki ce su dawo Dan Allah, in ba su dawo ba nima mutuwa zan yi in bi su.”

Mama ta kalli Jidda tare da rikye ma ta hannu ta ce, “Mamana kin San ina son ki ko?”

Jidda ta daga ma ta kai, “Amman ki dawo min da Iyata da Baba kin ji Mana Dan Allah.”

Mama ta yi Murmushi kan ta ce, “Mamana sun tafi kenan ba za su dawo ba, nima zan bi su, ki yafemin kinji, nima na yafe mi ki, ki rage tsokana kinji, ki zama yar kirki jiddana.”

 

Jidda na kuka ta ce, “Dan Allah Mama ke ma kirki tafi ki tsaya, mamana ki tsaya Dan Allah.”

Mama ta ce, “Yayanki Hamza da Mummy na nan har ma da Yayanki KHALEEL, ina son ki Jidda.”

Kuka kawai Jidda ta ke ta ma rasa abin fadi.

Mama ta fara salati nan da nan Allah ya dauki ranta, dai dai lokacin Da mumy ta shigo kenan.

Kuka kawai daga Mumy har jiddan su ke, sai da Khalil da Hamza su ka zo suka fara rarrashinsu.

 

Jidda ta fita ahaiyacinta gaba daya har akayi ukun su mama da Baba.

Mumy ce ta dauketa ta dawo da ita gidanta, shi kuwa hamza ma ya koma makaranta.

Uncle kuma ya na nan ya na surkullen da zai yi ganin cewa an ba shi Jidda ya aura domin ya yi alwashin ba zai tashi abanza ba, batare da yaci gadon Alhaji Ibrahim ba.

 

Jidda ta ma daina magana kwata-kwata arayuwarta sai ciwo da ta ke faman yi ko makaranta ba ta samun damar zuwa , abincin ma da ta ke kururuwar ci ba dama bata ma son ga ni bare ta ci.

 

Zaune ta ke ta kifa kan ta akan kafafuwanta karaf sai ga sallama sak irin muryan Babanta.

Nan ta ke Jidda ta, tashi taje ta rugumeshi ta na kuka.

Mumy da Dady na fitowa….

Urs Xayyeesherth
[11/28, 11:50 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

29November 2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 36/37_*

****************
************
******************
Suka tarar da Alhaji Adamu ne, Dan Uwan Alhaji Ibrahim da mu kai bayaninsa abaya.

 

Dady ya ce, “Alhaji kai ne agidan na mu?”

Alhaji Adamu ya washe baki, “Eh Wallahi ni ne, zuwa ya kamani, banji rasuwar ta su ba ai sai jiya cikin dare, hakan ya sani gaggawan zuwa.”

Dady ya ce, “Ayya kai ya yi zafi Wallahi, shiyasa ma ni kai na ban sami damar kirinka ba, ga wajen zama nan bismillahi.”

 

Alhaji Adamu ya zauna tare da kakako hawayen gulma, “Allah sarki Jidda, Yanzu saura min ke kadai sai Hamza adangina, ba Hajiyarmu, ba Ibrahim da iyalinsa, wannan lamari ya matukar tadamin hankali.”

 

Dady ya zauna kusa da shi ya na fadin, “haka Allah ya tsara lamarinsa Wanda ba Wanda ya isa ya kauce ma sa, Abu daya yanzu kawai suke bukata daga garemu Addu’a.”

Alhaji Adamu na face hancin ya na, “Hakane kam shiyasa na zo in tafi da diyata ko da ta dinga dibemin kewa ta zauna Chan cikin yan uwanta, ina ganin hakan zai fi, shima hamzan zan biya ta makarantarsu in sanar da shi komai ake ciki, daman munyi alkawarin aurawa ya’yanmu Juna, kuma Alhamdulillah ga Jidda nan insha Allah sai mun cikawa Hajiya Iyah burinta, zan tafi da Jidda in aura ma ta yayanta Sulaiman.”

 

Tun da Alhaji Adamu ya fara jawabi ya zo gabar Dauke Jidda nan da nan gaban Momy ya fadi, domin har ga Allah ta San cewa ba abin da Alhaji Adamu ya shirya illa mugunta da son rai.

Dady ya ce, “To Ina ganin ai anzama daya, bai kamata ka raba mu da Jidda ba a yanzu tunda ga Yayar mahaifiyarta, da kuma Yayanta ina ganin ai ba matsala, maganar aure kuma ai kana da iko a kanta ko da ma ba Dan ka bane ka isa ka badata bare danka to Amman aganina Jidda tai yarinta da aure a yanzu kam dai, yakamata ace ka bari ta Dan kara tasowa yanzu fa take cikin shekara ta Tara, to me za aurar, ita ba girman jiki ba, bare ace.”

 

Sai da Alhaji Adamu ya numfasa kan ya ce, “Alhamdulillah naji dadi ka ce inada iko da ita, Dan haka ba fa zan barta ba, sannan ba fa zan bar maganar auren nan ba.”

Tsabar takaici Mumy batasan sanda hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta ba.

 

Dady ya kalleta sannan ya kau da kai izuwa duban Alhaji Adamu ya ce, “Alhaji Dan Allah ka tsaya mu yi magana ta fahimta, ina ganin bai kamata ace wannan maganar har ta zama Babba ba, ka dubi yar uwar mahaifiyar ta mana, kaga irin halin da ta shiga, da zaka taimaka da ka bar mana Jidda har lokacin da zakai ma ta auren.”

 

Tashi Alhaji Adamu ya yi, yana kwallawa Jidda kira,”Ke Jidda ina kike fito za mu tafi, inna biye ta mutanen nan zasu batamin lokaci. ”

Mumy ce ta durkusa gareshi ta na, “Dan Allah Alhaji kar ka min haka, wallahi ina yiwa Jidda So fiye da ‘ya’yan da na Haifa domin ita din tamkar yar uwata daya tilo da na rasa ne Dan Allah karka rabani da ita.”

Fitowa Jidda ta yi da gudu Alhaji ya rikye mata hannu tare da tsaki ya ja ta suka bar gidan.

Ahanyar fitansu su kai kicibis da KHALEEL ya na shigowa.

Abin ya bawa KHALEEL mamaki Amman ya basar, Jidda ce ta kalli Khaleel tare da yi mi shi gwalo.

Kallonta ya yi, ya yi tsaki tare da kau da kai, kan ya nufi cikin gidan.

KHALEEL na shiga ya tarar da Mumy na kuka Dady sai faman ba ta hakuri ya ke.

Karasawa ya yi yana, “Lafiya dai kuwa?”

Mumy ta ce, “KHALEEL sun rabani da Jidda Dan Allah ka kar bomin ita, wallahi jinta na ke tamkar yar uwata.”

KHALEEL ya ce, “Haba Mumy akan wannan yarinyar zaki tada hankalinki? To miye ma yata tafiyan da ita ai sai me, mu daman ba nema mu ke ba, ni wallahi daman ma na tasan….

Cikin tsawa Mumy ta dakatar da shi, “ba ita ka tsana ba ni ka tsana, domin duk abin da kayiwa Jidda kamar kaiwa Amir da Amira, Yanzu yarinyar nan abar tausayice ba abin da take bukata fiye da taimako, wannan mutum ban da son duniya ba abin da ya sa agaba, ni nasan ba Dan Allah ya ke son komawar Jidda da hamza garesa ba, dukiyarsu kawai ya ke so, ni dama ace dukiyar zai ci kadai da sauki in zai bar ma na su, Amman ni nasani cewa Jidda wahala zata sha itace abar tausayi, domin ni nasan ya tsaneta, sanadiyarta su ka fara samun matsala da Hajiya Iyah.”

 

KHALEEL ya yi shiru ya ma rasa abin fadi.

Dady ya ce, “ni ban damu da maganar Hamza ba daman maganar Jidda ne ya dameni kuma ma na aure Yanzu, ki jibeta yar karamar yarinya kawai abata ma yarinya karama rayuwa.”

Mumy ta ce, “Hmm kai ma ka Fada dai, Yanzu yazama dole mu nemo mafitar da zamu bi domin taimakon yarinyar nan karta Fada Ga mummunan yanayin da ke bibiyarta.”

Dady ya ce, “Wannan ya zama dole in sha Allah zan yi iyaka bakin kokarina.”

 

************Alhaji Adamu Ba inda ya nufi Da Jidda sai cikin garin Katsina inda iyalansa su ke da zama.

Tunda daga shiga cikin gidan Jidda ta fara fuskantar sabuwar rayuwa, mai cike da al’ajabi tare kaddara.

MATAR gidan ce zaune wadda ake yiwa lakabi da Ammie ta taso ta yiwa Jidda wani mummanan kallo tare da fadin, “Alhamdulillah ,Allah dai ya yi wai kishiyar Tsohuwa ta haihu.”

Alhaji Adamu ya kyalkyale da dariya, “Ai fa kam lamari ya tabbata ko ince ya kusa, domin wannan shine farko.”

Karewa jidda kallo tai sama da katsa tai tsaki tare da fadin, “Ke Fatima, zo ki dau yar shilar nan Ku bata abinci ta ci, sannan ta na gamawa daman washing machine din mu ya sami matsala ki Ciro ma ta wankin nan ta yi.”

Fatima ta ce to tare da kallon Jidda da harara ta ce, “Mu je.”

Sai da Ammie ta lekya tare da tabbatar wa su Jidda sun shige cikin kan ta fara magana kasa-kasa, “Fatan dai ka kwamuso mana dukiyar?”

 

Dariya ya yi yana, “Ke kin cika azarzababi walle, yaushe Yanzu zan fara maganar kudi, ke baki San komai kan tsari ake ba ne? So na ke sai na Aurawa waccer matsiyaciyar yarinyar sulaiman, shi kuma hamza yadawo kan afara maganar dukiya, in ba haka ba ina farawa yanzu ai za su gano mu, su fahimci inda mu ka dosa, Yanzu ma ba ki San yadda na sha fama da mutanen nan ba ne Wallahi.”

Ammie tayi shewa ta ce, “hihi na dai kusa zama Hajiyar gaske, Wallahi ni har ma na zaku ayi ayi aure.”

“Ke dai kiyi shiru kawai akan maganar auren nan ma sai da na ya fito karyar cewa munyi alkawarin aura wa ya’yanmu juna, ni dama na tsani yarinyar da ta sa Iyah ta fita sabgata ni mai zai kani gareta in ba kaddara ba, hmm Wallahi ana samun kudin nan sakesu zamuyi subi duniya, Chan ta matse ma su, daga ita har Dan uwan na ta ba damuwata ba ne.”
Cewar Alhaji Adamu.

Ammie ta ce, “Ai fa kam shiyasa tun yau ma zata fara aikatuwa, kaga ma bara na shiga daga ciki in taci abinci Yanzu zata fara duty.”

Dariyar mugunta Alhaji ya yi ya na, “Hajiya ba ki da dama.”

Ta na shiga ciki ta tarar da Jidda ta yi tsili-tsilli da ido ta ci abinci bai isheta ba tana Neman kari Amman tsoro ya ha na ta magana.

Tsawa ta ma ta ta na, “Ke nan gidan fa ba na lalaci ba ne, na Fada miki, kima daina wani zare min ido, Inda cen kin saba iskanci agidan Ku to nan ba zan dauka ba, Dan haka maza tashi kije ki wanke min kayan nan tas, kuma ba na son ganin datti ko kadan ajiki.”

Ko da Jidda ta ga wankin sai da gabanta ya fadi, ba abin da ya zo ranta sai Iyah, lokacin da ke ma su wanki.
Nan take kwalla ya fara kwarara daga idanunta.

Tsawa tare da Mari alokaci daya Ammie ta kai ma ta, “ba ki isa ba fa dole sai kinyi wankin nan wallahi agidannan ko da zaki kai tsakiyar dare ne, to yazama dole ki yi na Fada miki, maza ki fara.”

Haka Jidda ta fara sabar wankin nan ba yadda ta iya ban da hawaye ba abin da ke zubowa daga idanunta.

Urs Xayyeesherth
[11/30, 7:39 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

30November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 38/39_*

_*Karku Manta daga wannan saura free page dayane za a shiga na kudi, in aka yi posting 40 shikenan nadaina posting a ko ina sai payment group Wanda tuna nafara sambada wa inda suka biya*_

****************
************
******************

Ta na gama wankin nan yunwa kamar za ta kashe ta.

Kallon Fatima tai da ke ta danne-danne waya ta ce, “Anty Fatima na gama yunwa na ke ji Dan Allah.”

Dalla ma ta harara Fatima ta yi ta ce, “Dalla matsamin anan wawiya kawai, sai shegen ci kamar kaza naga dazu ki ka gama cin abincin nan dai ko?”

 

Shiru Jidda tai ta zauna daram awajen da ta gama wankin ta fara kuka.

Ihu ta ke tana, “Wayyo Allah Iyah na, Iyah na Dan Allah ki zo ki taimakeni, Wallahi yunwa na ke ji Zan mutu.”

Ammie ce ta tawo bijigin-bijigin ta na, “Fatima wannan wani irin iskanci ne nake jin ihu ana kuka.”

Fatima ta ce, “Ammie Wai ta gama wankin Yunwa ta ke ji, kuma fa kina gani kan ta fara na bata sauran abincin da Yaya Sulaiman ya rage.”

Kallon Jidda, Ammie tai cike da takaici, ta karasa gareta tare da fadin, “Daman an kawo ki ne Dan kici abinci an Fada miki? To daga yau ma ki sani nabari a rana sau daya zakina cin abinci agidannan, kuma duk zan kori yan aikin mu ke zakina komai girki ne dai kawai mai aikin za ta na yi, ina Ita Hajiya iyar ta gama sangartaki? To za mu gani, mu zuba mugani ni da ke agidan nan.”

Kuka kawai Jidda ta ke ta ma rasa abin fadi.
Dare na yi Jidda ta rasa wajen kwanciya, cikin tsawa Ammie ta mi ka mata taburma, ga sanyin tais ga gari sanyi, ba abin luluba, abin tausayi, da ka ganta za kasan cewa ta na cikin maraici.

Haka Jidda ta kwana da yunwa
Washe gari da asussuba Ammie ta tasheta tai sallah za ta koma Ammie ta ce , “A’a ai yarinya yanzu za ki fara aikin ki, ki fara share kaf gidannan sannan kuma kiyi mopping, ki wanke toilet, ina son ganin gidannan ta-tas kan na farka daga barci karfe 9 na ba ki awa uku kenan .

Da sanyin asubar nan kowa na barci haka Jidda ta fara zabgar aikin nan ba ji ba gani, tun tana kwalla har hawayen ma ya gaji yadaina fitowa.

Ta kammala kenan, ta zauna domin hutawa nan taji an zuba ma ta ruwan sanyi, bude idon da zatayi Sulaiman ne tsaye ya na, “Yar shillar Amaryata MAZA tashi ki fara aikin lada, ga wanki chan ki wanke mun su tsab domin fita wajen ball zan yi.”

Tashi Jidda tai ta dauki kayan ga yunwar jiya ga ta yau, ta fara wankin nan.

Ta kammala wajen karfe sha biyu na rana, Sulaiman na shigowa ya yi ma ta wata irin tsawa, “Wannan wani kalan iskanci? A haka kikeso na sa kayan duk jurwaye? To MAZA ki tashi ki kara wankemin har sai ya fita tas.”

Ya na gama maganar ya tafi ya na wakarshi hankali kwance hadda fito.

Jidda na kuka haka ta kara sabar kayan nan ba ita ta gama ba sai wajen karfe hudu.

Zama tai atakure ta na tagumi, yunwa ta Riga da ta gama cin ta, Jidda ta ci abinci ma ya aka kaya bare ba ta ci ba, da ka ganta zakasan cewa tana cikin wani hali, abinka da Mara jiki nan da nan sirantarta ta kara fitowa fili.

 

Chan anjima sai Ga Fatima nan ta turo ma ta plate din wata ya mishasshiyar shinkafa, wadda ba ta fi loma biyar ba, ko da Jidda ta kalli shinkafar nan sai da tai guntun hawaye.

Fara ci kawai ta yi tamkar wadda ba ta ta ba cin abinci ba, maimakon ta koshi sai yunwar ta karu, ruwa kawai ta dunga durawa har cikin ta ya fara kullewa kan ta bari

***Tun da Jidda ta koma gidan Alhaji Adamu ban da bauta ba abin da ta ke, ta gama fita a haiyacinta, ba zama bare Hutu, sai aiki.

Mumy kuwa ta na nan cikin damuwa hankalinta ya gama fita a kan ta domin jikinta ya ba ta cewa Jidda ba ta cikin yanayin walwala.

Dady ya na ta faman nemo mafitar da zai kwato Jidda.

*****A kwana a tashi Jidda na cikin sati uku da zuwanta gidan Alhaji Adamu.

Da sassafe ta fito ta na shara Fatima ta fito Jidda ba ta lura ba ta watsa ma ta shara, nan Fatima ta fara jabga ihu ta na kuka,” wayyo Allah Ammie na kinga za ta kasheni, ta watsamin shara. ”

Da sauri Ammie ta dauko Bulala ta fito , “Ke Wai wace irin yar iskar yarinya ce? Bakin ciki kikemin da ita ko? To yau sai naci uban ki agidannan Wallahi.”

Dukan Jidda ta farayi da bulala ba ji ba gani, tun tana ihu har tai shiru.

Nan ta ke Ammie na dukanta har tayi barci awajen.

 

Urs Xayyeesherth
[12/1, 9:04 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

1December2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_LAST FREE PAGE 40_*

_*KAMAR YADDA NA FADA DAGA WANNAN ANDAINA POSTING AKO INA SAI PAYMENTS GROUP WANDA YA IYAKA WAN INDA SUKA BIYA ZAN SAMBADA ACIKI, SANNAN INSHA ALLAH LITTAFINA BA ZAI TABA FITA BA IYAKA ADADIN MUTANEN DA SUKA BIYA IYAKA SU ZA SU KARANTA🥰 KO BA KOMAI YAU ZAN GA MASOYANA DA MA NA JIDDA DIMPLE QUEEN*_

****************
************
******************

Jidda na cikin barci tai mafarkin Hajiya Iyah , “Jidda me ki ke yi na haka? Jidda me yasa ki ka yi sanyi aka rainaki? Jiddatuna ki tashi ki tuna labaran da na ke baki, ki kwaci kan ki daga gidan nan,Jidda ba na son zamanki agidannan ki tashi ki koma Chan wajen Mumynki in ba haka ba Jidda daga ni har Iyayenki ba za mu yafe mi ki ba, Jidda ki tashi na Fada mi ki ,ki tashi Yanzu.” Cewar Iyah

Afirgice Jidda ta farka dai-dai lokacin da Ammie ke zuwa tashinta, ta mikye kenan sai ga Ammie da ruwan sanyin nan kamar yadda ta saba.

Kallon Jidda tai tare da watsa mata, “Munafuka duk da kin tashi sai na watsa mi kin, shegiyar yarinya kawai ba ni waje, kuma maza ki yi sallah afara gyaran gida, Dan yau za a daura mi ki aure da Sulaiman ki tabbatar kin gyara ko ina.”

 

Maganar Aure da Jidda taji ne ya rikita ma ta kwakwalwa nan ta ke, ta kara tuno mafarkin Hajiya Iyah.

 

Fara gyaran gidan tai kamar kullum Amman adai dai lokacin da ta zo mopping wa ni hamshakin Murmushi ne ya bayyana daga fuskarta, azuciyarta ta na fadin, “Wallahi sai dai akasheni Amman Yau sai na yi abin da naga dama agidannan kuma na gudu.”

Shiga kicin tai ta dibo mangyada tare da zubawa acikin ruwan Mopping din, har ta kammala ba Wanda ya farka agidan abin ka da yan Hutu.

Jidda na gamawa ta sulale tare da barin gidan.

Ko da ta fita asanyin asuban nan mai gadi bai farka ba, bare ma ya San da fitarta ko ya hanata.

 

Tafiya kawai Jidda ta ke cikin daji ba ta San inda ta ke shiga ba bare tasan inda ta ke fita.

Yunwa ta gama cinta gabadaya ta gigice da kyar ta ke tafiyar ma.

****Karfe Tara dai-dai Ammie an dau wanka ana tafiyar kwalisa, sa kafar da za tai kan tais nan take tajita akasa, kwallawa Fatima kira tai ta na ihu, Fatima ma na sa kafa ta ji ta dim, sai kuka, Alhaji Adamu na jin hakan fitowan da zai sai gashi shima a kasa tim.

Ammie na kuka, Fatima na kuka Alhaji kuwa ya yi tsiru-tsiru da ido ya na kallon kowa daya bayan daya, radadi ya ke ji inda hali zai yi kukan Amman ba dama.

 

Dakyar su ka sami damar janye cikinsu su ka koma daki.

Ammie ta fara masifa ta na kwallawa Jidda kira ta kira ya fi sau Dari, Amman ko alamar Jidda ba ta ji ba bare motsinta.

“Shedaniyar Yarinya na San ba Wanda zai yi wannan aika-aikan sai Ita Wallahi, kuma yau inna kamata sai ta manta garin su, Wallahi sai na ci uwar yarinyar nan, ji kina kamar wadda aka ma duka nasan dole in yi zazzabi.”

 

Sai ta kira ma su aikin su kannan aka gyara gidan.

Ko da Ammie za ta fito, nemo zukyekiyar Bulalarta ta yi ta cigaba da masifa ta na ke waye gida adole ta na Neman Jidda.

Daga karshe ta ga ba alamar Jidda agidan, nan ta ke hankalinta ya tashi tana yiwa Alhaji magana ya fito, aka tambayi mai gadi ya ce shi bai San inda Jidda ta ke ba, domin ko fitartama bai ji ba.

Daura hannu ya yi akai ya na, “Wayyo Allah na, na shiga uku wannan jarababbiyar yar za ta ja min masifa, in dai ta tafi ta chuceni Wallahi, shikenan an gama dani, kai Wallahi ma sai na nemota ko ina ta shiga ba gudu babu ja da baya sai na Aura ma ta Sulaiman.

Firgar motarshi ya yi nan ta ke ya fice.

Ita ko Ammie sai hamami ta ke, ” Ni Wallahi akawomin ita ma in ci uban shegiya yadda tasani ciwon jikin nan nima sai na sa ta.

A bangaren Mumy da Dady kuwa sunji labarin cewa za ayi auren Jidda da Sulaiman hakan ya sa su yin asuban ci domin su riski auren, su dakatar.

Suna cikin tafiya kamar wasa Mumy ta hangi wata yarinya ya she akwance ga dukkan alamu ma ta fita a haiyyacinta.

Mumy ta ce, “Alhaji tsaya mu duba yarinyar chan.”

Dady ya ce, “Kin San dai mun makara kar fa a daura auren nan.”

Mumy ta ce, “Ayya wannan yarinyar ma ga dukkan alamu ta na bukatar taimako tamkar Jidda, mu tsaya mu taimaketa, watakil in mun taimaketa mu ma Allah ta ji kan mu ya kufuto mana da Jidda.”

Suna fita Mumy na zuwa ta tatarar ai Jidda ce kwance, numfashi ma da kyar ya ke fita, kana taba jikinta sanyi karara, da alamun sanyi ya gama shigar ta.

Kuka Mumy ta fara ta na, “Wallahi Jiddatu ce, Ita ce, Alhaji Dan Allah ka taimakeni kar Jidda ta mutu numfashin ma da kyar ta ke iya yi.

Nan ta ke Dady ya sa Jidda amota su ka shiga gari domin Neman wani asibitin da ke kusa.

Cikin sa’a kuwa suka hangi wani karamin asibiti, suna shiga aka farayiwa Jidda taimako har Allah ya sa ta farfado cikin ikon sa.

Amman likita ya sanar Mumy da Dady cewa, ” Nemoniya wa to ciwon sanyi ya Riga ya ma ta shigar sauri, ta indai in ba a tsaya ma ta ba zai iya halaka ta, sannan yunwa ta fara cin jikinta tana bukatar kulawa ta mussaman a yanzu dai kam.

Mumy ta yi kuka sosai domin jin hakan ta ke har cikin ranta.

Jidda ko sai kallon Mumy ta ke tana kyalkyallewa da dariya, in Mumy ta kalleta tai Murmushi ta ma rasa abin fadi.

Mota suka shige da niyar komawa gida.

Mumy ta ce, “Alhaji shin me ka ke ganin ya dace mu yi a yanzu?”

Girgiza kai kawai Dady ya yi, “Ni nasan me zanyi abin da na ke gudu ya zama dole ne inyi domin in taimaki marainiyar Allah, kar ki CE min za ki ja da hukunci na domin sai bayan na aikata zakiji bayani, Yanzu dai ki saurareni zuwa safiyar gobe kawai in sha Allah komai ma ya zo karshe.”

Mumy ta yi shiru kamar yadda mai gidanta ya umarci da tai hakan.

Suna isa gida Jidda na ganin Amira sai dariya da murna hadda tsalle kamar wadda akayiwa allura.

Wanka Mumy ta ma ta sannan ta hada ma ta tea da indomie Jidda na zama ta fara cin abincin nan kamar mayya ko na bakinta bata bari ta ke kara sa wani.

Mumy na kallon Jidda sai kwalla.

Ita ko Jidda intaci taci sai ta dago ta kalli Mumy ta ma ta gwala tana, “Ni Wallahi ba zan sammaki ba.”

Dan dole dai sai Jidda ta sa Mumy dariya.

Ko da dare ya yi, Mumy daukan Jidda ta yi, suka nufi dakinta domin ta ce ba za ta rabu da da ‘yarta ba.

Dady ko sai dariya ya ke, Amir ya ce, “Mumy katuwa da ita bazaki bari ta kwana dakin Amira ba?”

Mumy ta ce, “Aa din Ku bar min abata.”

******Washe Gari da asussuba Dady ya na fita massalaci, dawowan da zai yi gida sai da ya kira KHALEEL ya zo.

Zama sukayi afalo ya sa aka kira mi shi Mumy da Jidda.

Dady ya ce, “To Yanzu za Ku ji, hukuncin da na yanke, kuma ba na son amin jayayya daga ke har ‘Dan ki domin kamar yadda Jidda ta ke ‘ya agareki nima haka Jidda ta ke ya agareni, kamar yadda ki ke da iko da ita, nima ina da iko da ita, so na gama yanke hukunci ko ince nama yanke , asafiyar yau ban shigo gidannan ba har sai dai na Daura AUREN JIDDA DA KHALEEL A masallaci.

Nan ta ke KHALEEL ya mikye tsaye sai kwalla, ” Dady Dan Allah me zanyi da wannan yarinyar? Dady aduba agani dai ni kam dai anga…

Tsawa Dady ya ma sa ya na fadin, “Na aura ma ka Jidda, kuma ba rabuwa sannan kasani yau Jidda ba inda zata kwana sai agidanka na fadama.”

Mumy ta ce, “Alhamdulillah nasan cewa daman bazaka taba yanke hukuncin da bai dace ba, Na gode sosai Alhaji Allah kara girma.”

 

Dan takaici Ma KHALEEL hanyar fita ya nufa.

Mumy ta ce, “Ka dawo, nace ma ka dawo,ga Jidda nan ka rikyemin ita amana, Wallahi Wallahi in ka rabu da jidda bazan taba yafe ma ka ba, nafadama.”

Jidda na zaune kawai bin duk mai magana ta ke da baki, damuwarta kai tai abin da za akomar da ita wancen gidan, domin tasan duk muguntar KHALEEL ba dai zai hanata abinci ba.

Kuma daman ita babbar damuwarta ba ta huce na ciki, in taci ta koshi shikenan.

Tunda KHALEEL ya fita ma ya kasa komawa gida Office ya nufa hankali Tashe, shi ba ma ta Hajara ya ke a yanzu ba, tsanar da ya yi Jidda ke dawainiya da shi.

 

Misalin karfe hudu na yamma Mumy ta shirya Jidda cikin bakar doguwar Riga tare da golden din bols da golden din gyale, simple makeup ta ma ta, Wanda ba karamin kyau ta yi ba, kiran KHALEEL mumy ta yi awaya tana fadin, “Ga mu nan fa mun gama in zaka tafi gida ka biyo mu tafi tare.”

 

Ba yadda KHALEEL ya iya haka ya biyo gidan kuwa.

Mumy ta bude baya za ta shiga Jidda ta bita.

Mumy ta ce, “Iye KHALEEL fito ka budewa matarka gaba ta zauna maza.”

Jidda ko ajikinta ta lura ranshi abace ya ke yana bude ma ta ta shige da sauri tare da yi mi shi gwalo.

Suna isa Hajara ta dawo daga wajen aiki kenan.

Mumy ta ce, “Yawwa daman ke na fi bida a yanzu, zauna ko.”

Zama Hajara tai tana mai kallon Jidda cike da Mamaki.

Mumy ta nuna Jidda tare da fadin, “abokiyar zamace akayi miki gatanan, kuma ‘ya ta, dage ke har shi yadda kuka bi da ita haka itama zata bi da Ku, kunsan da hakan domin yarinyace, ko da yake mijin na ki ba son ta ya ke ba, to Amman ni fa ina sonta kuma ba na son abin da zai sameta dai dai Dana lokaci gudu, Dan haka KHALEEL ka ji nan adakinki Jidda za ta zauna, sannan ba ta da lafiya ga magungunanta nan in dare ya yi abata, maganar abincin na San ba Ku da matsala ni zanyi mai aikin ma magana kan na tafi.”

Kallon Mumy Hajara tai cike da gyatsina fuska ta yi tsaki tare da tashi ta na fadin, “Me zan kisa agun wannan yar shilar? Shi kan shi ma baya gabana bare ita mtsw.”

Ta haura stairs abinta.

Mumy ta yi Murmushi ,”to ka dai ji, ni dai akulamin da ‘ya ko asami matsala Jidda ta shi muje dakin.”

Sai da Mumy ta kai Jidda dakinta, Jidda na ta tsalle tana murna kan Mumy ta fito ta sami KHALEEL, “Kasan Allah yau adakin nan zaka kwana domin kuwa nasan halinka sarai, karka kuskura ka ce zaka bar Jidda ta kwana ita kadai.”

Daga wannan maganar Mumy ta fice daga gidan.

Dare na yi mai aiki ta kawo ma Jidda abinci, ta ci ta koshi son ranta kan ta haye kan gado tuni barci ya yi awon gaba da ita.

KHALEEL na shigowa ya yi tsaki tare da mata tsawa wadda sai da ta sa ta farka wa.

“Dalla sauka min agado chan kasa zaki kwana, ko da ni kike so in kwana akasan?”

Jiki asanyaye Jidda ta kwanta akasa.

Kamar KHALEEL zai ce ta dawo sai wata zuciyar ta ayana ma sa da ya kyalleta.

Cikin dare kamar amafarki Jidda na fitar da wani irin numfashi, ga shi ta kyankyame jikinta waje daya da alamar cewa sanyi ke damunta.

KHALEEL na gani ba wadda na tuno sai Mumy hakan ya sa shi saurin dagata daga kasan ya mai da ta kan gado, da sauri ya dauko maganin ta ya ba ta, ya lullubeta zai sauka kan gadon ya ji Jidda ta kyankyame ma sa jiki.

Ba yadda ya iya haka ya kwanta akan gadon nan.

Kallon fuskarta ya ke zuciyarsa na ayyana ma sa, “Ashe yarinyar nan kyakkyawace haka.”

Can kuma sai ya yi saurin kawar da kai tare da daina kallonta.

KHALEEL ya tashi sallar asuba ya nemi Jidda ciki da waje ya rasa ga Mumy ta kira waya abata za ta gaisa da yarta.

KHALEEL ya gama duba ko ina agidan nan ya rasa Jidda zama ya yi kasan bishiyar da tsakar gidan har gari ya yi haske ya ma rasa inda zai sa ransa.

Ya tashi da niyar kirin Mumy ya Fada ma ta halin da ake ciki daga kan da zai yi sai ga Jidda Asama bishiya.

 

_*HHHHHH AMARYA MAI HAWA BISHIYA*_

_*TO ALHAMDULILLAH YAU DAI ANZO KARSHEN FEJIN KYAUTA DUK MAI SON CIGABAN ZA TA IYA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 08103080717*_

Love you oll lodilodi

URS Xayyeesherth

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]