[Advertisements⬇️]

AMARYAR ZAMANI CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

👰🏼👰🏼AMARYAR ZAMANI👰🏼👰🏼

 

SHORT AND BRIEF  STORY

 

LABARI/TSARAWA DA RUBUTAWA

_SALMEERT (AUTAR MAMA ƳAR LELEN  ROYAL)

 

 

SADAUKARWA GA DUKKAN MUSULMAN DUNIYA BAKI DAYA

 

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

INA ROƳON ALLAH YARDA NA FARA RUBUTA LITTAFIN NAN ALLAH LAFIYA  YASA NA GAMA LAFIA

 

 

“””””””””””””””””””✍️✍️Wata Ƙyaƙyawar Yarinya da baza wuce shekara goma sha biyar ba zuwa sha shidda na gani a wani shagon saloon sai yanga take ,tana iyayi da yauƙi,shiga nayi don inga iya gudun ruwanta,wata naji tana cewa,”kaiiii ƙawata amma fa gaskiya kinyi kyau sosai ,jifa yanda kike ƙyalli tun kafin auren wannan in aka ɗaura killan touching light xaki zama killan saboda ƙyalli”,wani farrr naga tayi da idon tana jujuyawa saman kujerar ,tana wani munafiƙin murnushi ,”kedai bari ƙawata Wallahi na ƙagara wannan sati dayan ya yi ya ƴaraso a ɗaura a kaini gidan my Abudul”,ta fada taba wanni lumshe ido,ai sororo nayi ina kallon ikon allah ,cikin raina na furta ya Illahi yanzu  wannan yar Yarinyar take fadin wannan maganganu,wata daga cikin Yaran tace “ke Miemie ba kunya bare tsoron Allah har kike cewa haka”,kallon ta tayi tana ɓata rai tace “ke A .A  mai kike nufi ne ko ban isa auren bane” , ta faɗa tana jujuya wani fikikin jikinta ,wanda da alama ma ko ƙwari kashi  bata gama yi ba,cikin rana nace wannan a tatsi mage ko a kashe,wadda aka kira da A .A tace,”hmmmmmmm zakici Uban ki Yarinya bake kince aure kike so ba ƴar ficiciya dake”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 

wata daga chen baya tace ,”mudai namu mu taimako da ruwan zafi “,ta faɗa tana ƙyarƴyacewa da dariya duma dariyar sukayi,amma banda Uwar gayyar,Miemie ce tace “nidai yanzu tunda an gama ku tashi muje kusan na kira sweetheart dina nace yazo ya kaimu mu gama wannan rabon i.v dinnan yau daga chen Hajiya tace ma wai na wuce gidan ,Umma Maryam wai kuma na zaina a chen”,ta fada tana kwabe fuska,tashi sukayi duka ,ta biya kuɗin saloon din da akayi musu suka fito ,fitowar su ya yi dai_dai da fakawar wata haɗaɗiyar mota ƙirar  BMW ,da sauri Miemie yace “kuyi sauri ga sweetheart chen fa yazo”,daya daga cikin su ce tace “wake Miemie wannan rawar kan da kike yi na mai nene ?”,kallon ta Miemien tayi tace ,”ke ƙyele ni kinsan irin son da na keyiwa,Yaya Abdurrahman kuwa,tuk kamin ace za”a hadamu aure nake jin soyayyar shi cikin zuciyata dan haka ƙyele ni nayi rawar kan nawa”,kallom ta nayi da mugun tausayi domin bata san aure ba shi yasa take yi masa irin wannan rawar kan,fitowa daga mota ya yi yana jiran karasowar su ,wow gaskiya guy din ko ni sai da na ƙyasa domin ya haɗu sosai ,suna ƙarasawa gurin shi ta fada jikin shi tana mishi kukan shagwaɓa ,da kallo su A.A suka biya domin abin nata yafi karfin su,da sauri yadan janye ta daga jikin shi yana cewa ,”mai nene kuma ya faru baby”, shagwaɓa ta shiga yi mishi tana diddara kafafuwa da sauri ya buɗe mota yasa ta ciki yacewa sh A.A suma su shiga ,suna shiga yaja motar,a kasalance domin duk ta saukar mishi da kasala da kuma wani mugun feelings

 

 

muje zuwa.

 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]