[Advertisements⬇️]

AFRAH CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Siririn tsaki ya k’ara saki a karo na biyu, yayin da ya k’ara bararaje wa a kan kujeran da aka tanada musu dan zama. Bini bini yakan duba agogon hannun shi na kamfanin Rolex, sai kuma ya maida hankalinshi kan abin da a ke gudanar wa dangane da meeting in da suke yi.
Maganar dai d’aya ce wanda akeyi yinta akan lack of security na k’asarmu. So tari yakanyi Allah wadai da irin wannan meetings in Sabida ba abinda ake tsinanawa a wajen sai maganganun da ana barin wajen toh fa sun shud’e kenan. Sai su zama kamar ba a yi su ba.
Abin na d’aya daga cikin abubuwan da suke k’ara harzuzk’a Umar kenan. Ace za ayi abu kuma ak’i aiwatar wa duba da yanda k’asarmu ta lallace wanda sai dai addu’a ace kuma za a sa ma yan ta’ada ido suyi ta yin kansu ai ba magana baci. Duba da lokacin da aka sace yan makarantar dabci, wai ace a yi yarjejeniya da su. Kuma wai har su da kansu zasu dawo da yaran ba tare da an kamasu dan gurfanan da su gaban shari’ah ba toh ai shi a ganinshi anyi biyu Babu kenan, ba wan ba k’anin. Wanen kenan

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Fitowa yayi daga bak’ar audin da a ka parka ta wajen parking lot in gidan su.
A estate duk family in suke, estate da kakanshi ya ginashi kuma duk yaran shi suke zama a wajen daga kan matan har maza.
Gidaje ne manya manya mansions din nan ne wanda yake zagaye da shukoki da manya manyan bishiyo.
Tafiya ya farayi da tak’ama da issa duk sojojin wajen suna sara masa. Tafiyar minti uku yayi kafin ya isa ga kofar shiga cikin gidansu Wanda a ka basu shida cousins din shi wanda basu da auren.
Shiga yayi ciki, ya fara tafiya ta cikin long hallway in da yake kalar fari da ratsin ruwan gwal Wanda hotuna flowers ne a jere a wajen da kuma wasu waiting chairs da a ka aje a wajen masu k’ira royal amma costumized ones. A yanda yake tafiyan nan nashi har ya isa wajen elevatorn da zai kai shi part in shi. Danna wani dan circular bottom yayi yana jira ya bud’e ya shiga. Yana ko bud’e wa ya shiga, sai ya danna floor din da yake kafin ambin ya fara tafiya.
Bayan yan sakonnin ne abin ya tsaya, fitowa Umar yayi, kafin ya fara tafiya yana fuskantar inda b’angaren sa ye ke. Masu aiki ne birjik suna aikin su yayin da duk in da yawuce suna kwasar gaisuwa, ba laifi yana amsa musu duk da dai in ka ga yanayin shi ka san yan cikin b’acin rai ko da’ike daman haka fuskar tashi take kamar wanda aka aiko ma da sak’on mutuwa. Kullum a hade ba za ka tab’a cewa yasan wani abu wai shi dariya ba.
Yayi tafiya mai dan nisa kafin ya iso barinshi. Black double doors ne a wajen wanda duk haka kalar k’ofo!in suke a gidan na su sai dai kowa da inkiyanshi manne a jiki k’ofar. Tura shi ya yi jita a bud’e bai yi mamaki ba sabida yasan ya sa kanwar shi Abida yi mashi gyara . Sabida shi bai yarda wani dan aiki ya shigar mishi d’aki ba .
Tun daga bakin kofa ya fara cin karo da abin da ya k’ara harzuk’a shi wato jin kamshi turaren da aka fesa wanda shikuma ya ma tsani k’amshin, wannan kuma na nuni da ba Abida ce taiyi mishi gyaran d’akin ba.
I’m going to deal with this girl ya fad’a a zuciyar shi yayin da ya dumfari parlourn shi wanda yake sai ka shiga sannan ka samu k’ofar shiga d’akin shi. Ko da shigan shi hankalinshi bai kawo mai akwai wani acikin ba sai da ya ji wata tsiririyar murya kamar wacce aka tatse tayi magana.
” Welcome back ya Umar “.
Tsayawa yayi yayin da ya d’an juyo fuskar shi, dara daran sexy eyes in shi suka sauka akan kyakkyawar fuskar ta. Kallon rashin sani yake yi mata yayin da ya d’aga gira d’aya. Shi a rayuwar shi ba ya da son hayaniya kuma duk zafinshi in dai macece ce toh bai tab’a daga mata murya k’illa ko Sabida irin sabon da yayi da mummyn sa ne oho.
Kallon shi ita ma tayi tana jiran taga ko zaiyi mata magan duk da dai tasan bai da suturu. In dai har kaga surutun sa toh sai in yana wajen maman sa. Irin kallon da yake mata ne yasa tasha jinin jikin ta.
Bayan yan sakonnine ya juya da fuskar shi izuwa d’ayan gefen yayin da ya fara takawa zuwa d’akinshi, kamar bai masan da ita a wajen ba. Ita kuwa tana ganin haka sai ta furzar da isa kafin ta saki ranta ta zauna zaman jiran ya fito.
Tun tana jira taga ko zai fito, taga har ya kwashi mintuna ashirin ba alamun shi , sai ta dan jingina da head rest in kafin kace me sai barci ya dauk’e ta, daman ta wahala sabida gyaran da tayi.
Shikuma goggon naku, yana gama abin da ya ke yi, ya fito ya same ta jigine tana barci baice komai ba ya fita daga part in shi. Sai da yayi tafiya minti biyar kafin ya isa gidan su. Shiga yayi cikin hallway in dayake painted in rich gold. Katon chandelier ne yake fara ma mutum iso, sai kuma spiral staircase in da yake colourn fari da ratsin gold a jikin rail in. Kan staircase in kuma white and black lush carpet ne shimfid’e a kasan. Hawa yayi ta staircase in kafin ya bi ta wani narrow way da zai kashi da part in mahaifiyarshi. Tura kofar yayi da sallama a bakin shi , mummy da ke zaune a kan wata shegiyar royal chair ta amsa yayin da ta juyar da ganin ta daga tv izuwa ga danta dake k’arasowa ciki..
” Abul khair ” ta kirashi da nickname in shi sabida sunan babban tane da shi.
“na’am mummy ya gajiya ” ya fa’da yayin da yake durkusawa domin ya zauna a k’asa, gefen kafarta .
D’ora kanshi yayi a kan cinyanta, itakuma ta fara caressing kanshi. Lumshe ido yayi yana jin dad’in caress in yayin da ya fara magana kamar haka.
” mummy ” ya kira sunan ta a sanyayye.
” na’am Abul khair. ” ta amsa mishi tana duban d’an nata, sanyin idaniyan ta.
” ina Abida ” ya tambaye ta.
” mai ya faru. Mai taima kuma yau ” ta tambaye shi sabida tasan d’an nata da sanyi indai akan mace ne. Shi a gurin shi mata basu cancanta ana d’aga musu murya ba koda kuwa duk abin da suka ma mutum. A wurin shi a lallaba su ya fi, sabida shi d’aga muryan ma ke kawo raini kuma yanda bazai so ko uban da ya haife shi yaringa d’aga wa mummyn murya ba, toh shi ma bazai yi wa wasu haka ba.
” mummy I asked her to clean up my room amma shine zata sa wata, watan ma a complete stranger ” ya ambata yayin da yake sassauta muryar shi wanda take nema ta fi normal voice in shi karfi, hakan kuma ke nuni da haushin da yake ji.
Baran in ya tuno da wadda ya gani zaune a ciki falorn shi. Shi a rayuwar shi baya son yawan shishigi.
” Ayya kayi mata uzuri, ta tashi da niyar yi amma aka kirata aka ce mata suna da fixed lecture, kuma ka ga dai dole ta je ko ” tayi reasoning da shi.
” kuma da kake ce wa stranger ba fa kowa bace illa yar Ummanka Hauwa “.
D’ago idanun shi yayi yana kallon mamar shi da mamaki. Umma matar Abul bait ce, yayan mahaifinshi , kuma Banyan mahaifiyar shi ba wanda yake so kamar Umma. Ya san dai Umma na da ‘yaya shida, hud’u maza, biyu mata amma bai zata tana da ‘yar da takai kamar shekarun Abida ba koma ta girme mata da dan shekaru ba .
Bai sake cewa komai ba sai dai shirun da ya ratsa wajen, yayin da uwa da dan duk sukayi Shiru suna enjoying silence din.


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]