[Advertisements⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 88 BY AZIZA IDRIS GOMBE - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 88 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

mushi, sannan ya ce, “Shi kenan

hankalinki ya kwanta?” Ita ma murmushin ta

yi a kunyace. Take Dr. Yusuf ya san

lamarin nasu ya wuce basaja.

Haka yana ji yana gani suka fice a ofishin din

ka na ganinsu, ka ga wadanda suke

matukar son juna, daga kallon da suke yiwa

juna, zuwa yadda suke magana da juna

kadai ya isa shaida. Ajiyar zuciya ya yi, ya

daga aikin da ta mika na Project din da

suka bari.

A bangarensu kuwa, tun suna tunanin abin na

dan lokaci kadan ne za ta daina,

amma gadan-gadan! Wannan cikin sam baya

son kamshin Zaid, sai daga baya suka

fahimci ba turaren bane ma baya so, shi karan

kansa ne, daga nan kuwa ya nisanci

shisshige mata da yake yi, sai in ya kama dole.

Wataran sai ya yi kamar zai riketa

yadda ya saba zama kusa da ita, sai ya tuna.

Har tausayi yake ba ta, amma ba

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

yadda ta iya. Haka dole suka raba sabogoginsu.
Wannan al’amari ba karamin damun Zaid ya yi
ba, amma dole ya hakura saboda ya
san halin da take shiga, muddin hakan ta faru,
sai ta yi kwana guda tana jinya.
Da abin ya isheta ne, take fadawa Takiyya a
waya, “Ke kawas, kin taba jin haka?
Ace gaba daya fa sai na dauko dauriyar duni-
yar nan na ke iya zama da shi mu yi
hira, ki duba dai wannan al’amarin, muddin
aka ce kuwa ga shi ya tafi wurin aiki, to
muna nan a waya ba ma gajiya, amma da zarar
na sa shi a idanu kuma sai na ji
kamar zan yi hauka.”
Takiyya ta sa dariya, ta ce, *”Wannan bebi ya yi
min daidai, haba ku din ne sai da
haka ai. Shi kenan sai ku koma long distance
marriage.
Ke
Ke muguwa ce Wallahi, ina fada miki
damuwata, ki na min dariya ko?”
Okay, na yi shiru, amma ki gwada sawa a
ranki ba kya jin komai, ki ga ko zai yi aiki
wasu lokutan a kanmu abubuwan suke, ki ji ba
kya son abu ka za ko abu ka za ki ke
SO…”
Ina! Wannan ya wuce a kaina Takis, tsorona
Allah kar na sake kure shi, don na san
abin ba sauki. Amma babu yanda na iya.”
“Hmm! Bari idan na yi tunani zan kawo
shawara, amma for now dai… ehm ehm dole
kawai ki san abin yi.”
Ajiyar zuciya kawai ta yi ta kashe wayar.
Ranar ne ta kokarta ta shiga kicin don ta shirya
masa lafiyayyen abinci, tana
kammalawa ta shiga ta gyara kanta ta yi fes da
ita, ita kanta ranar ta ji dadin jikinta.
Za ta gwada sawa a ranta, kamar yadda
Takiyya ta fada mata.
Ba Karamin mamaki Zaid ya yi ba, da ya zo ya
ganta cikin kwalliya ta musamman,
domin dai rabon da ya ga wannan daukar
kwalliya tun suna Germany, watanni uku
da suka shige.
Ta kara kyau sai sheki take yi. Fatar ta ta sake
murjewa, kau da kansa ya yi ya
maida hankalinsa kan abincin da ke gabansa.
Yau kuma ina aka kai mu?” Ya fada yana
nufin abincin da yake ci.
Dariya ta yi ta ce, “Senegal.” Shiru ne ya dan
ratsa tsakaninsu, sannan ta ce, *”Yaya
aiki?”
Lafiya kalau. Gaskiya ina son wannan. Ki
ajiye min sauran.” Ya sake mayar da hirar
kan abinci, tun kan ya fadi abubuwan da suke
boye cikin zuciyarsa.
Anyi an gama, Yallabai.” Dago idanunsa ya
yi ya kalleta.
“Me yake faruwa da ke yau?”
Murmushi ta yi ta ce, “Yau na ga ta kaina, ba
dama na zauna mu yi hira?”
“Tun yaushe muka zama abokan hira? Ko kin
warke ne?” Ya fada hade da daga
mata girarsa duka biyu cikin alamar tambaya.
Hmm! Ina so ne na warke, wannan kokarina
ne na ganin hakan ya faru.” Cikin
fara’a take masa maganar. Kallonta ya yi, har
cikin ransa ya ji dadi. Yau sai ya ga
hatta hakoranta kamar sun kara wani fari da
sheki. Hadiyar wani abu ya yi ya kau
da kansa.
Kar ki damu ba, sai kin sa kanki a wani hali
ba, na san ki na iya kokarinki. Allah ya
saka da alkhairi, Ya kuma yi miki albarka.”
Ameen Ya Rabbi, kai ma Allah ya biyaka
hakurin da ka ke yi da ni.”
Lumshe mata idanu ya yi kafin ya tari aradu
daka, ya ce, “taho nan..” Mikewa ya yi
ya isa wurin kujerarta, ta tashi tsaye ya saka ta
a jikin sa na wasu ‘yan dakikai.
fita,
Sannan ya sake ta. Good night, zan fita,
watakila kafin na dawo kin yi barci.”
Bude idanu ta yi tana masa kallon mamaki.
Za ka fita? Yanzu fa ka dawo…”
Tsumewa ta yi, kumatunta suka loba.
Wani
abu ne ya taba masa zuciyarsa, ya sa
hannu ya shafi fuskarta. “Ba na son ki yi
rashin lafiya Adiyyah, duk yadda na ke son ka-
sancewa da ke, dole na hakura.”
Yau na warke.” Ta fada cikin karfin hali don
a hakikanin gaskiya lokacin kanta ma
ya fara juyawa. Kawai tausayinsa take ji.
Goshinta ya sumbata, ya wuce daga wurin, sai
jin karar taba kofa ta yi, ya bude,
idanunta a runtse lokacin da ta ji karar rufewar
kofar. Take ta ji wasu hawaye sun
sulalo mata daga idanu, sai kuma yunkurin
amai ya taso mata, ta yi bandakin falo da
gudu.
Koda ya dawo a dakinsa ya sameta ta yi barci.
Tausayinsu ya kama shi duka biyu,
kwanciya ya yi ya sa hannu ya shafa kanta,
gashin kanta baki wuluk ya kwanta lub-
lub a kanta. A hankali ta bude idanunta ta gan
shi.
Ka dawo?”
Raunin da ke cikin muryarta ne ya karasa
tsinke duk wata dauriyarsa, don haka ya
jawota jikin sa ya riketa.
Hawaye ne ya fito daga gefen idanun Umm
Adiyya, yatsarsa babba ya sa ya goge
mata.
Dariya ya yi gajeruwa mai sauti, “Ba ki da abin
jin tsoro, gidan Abba na je.”
Ajiyar zuciya ce ta kubce mata.
Daga kanta ta yi kadan, har numfashinsu na
gaurayuwa. “Adiyya, kiyi bacci.””
“Na kyauta idan na barka idanu biyu kai?”
Ba damuwa zan lallaba.”
Make kafadarta ta yi ta ce, “Na Ki, da gaske ba
komai.”
Idanunta ya kalla, ya sumbace su daya bayan
daya, zukatansu kamar za su tsaga
masu kirji don bugu. Kan hancinta ya koma
kafin ya gangaro wuyanta, nan da nan ta
gama narke masa.
“Da gaske Umm Adiyya kin kusa ki daina zuwa
ko ina. Mashaa Allah wannan cikin
naki ai zai rinjayeki ki fadi.”
Kunya ce ta kama Umm Adiyya, tana dariya ta
rufe idanunta, “Anti.”
Gaskiya ne ai, ki zauna wuri guda kawai ki
hakura da tafiye-tafiyen nan haka, ban
san ma yadda aka yi Malam ya dauko ki a
haka ba dai.”
“Aunty ai Maryam ba za ta bar mu mu sha iska
ba, idan ba mu zo ba. Ko wayar da ta
rinka masa ma ai sai haka.”
“Lallai kuwa wata rana za ki haihu a titi ashe,”
Ummua ce ta aiko da abincinta dakin Antin,
haka aka sa ta a gaba, sai da ta ci ta
koshi, ita kam idan an bar ta kunun ayarsu mai
kaurin dadin nan shi za ta yi ta sha
har gobe, ga shi dama ta samu lafiyayyar awara
mai zafinsa, yaji kwai da kayan
miya ga barbaden lawashi an masa, tunaninsa
kadai ya tsinka mata yawu, bare idan
ta zauna ci. Gudun maganar Aunty ne ya sa ta
dan tsakuri kadan ta ci abincin.
“Meye hakan wai? So ki ke yi ki haihu ki gal-
abaita ko kuma ki haifa mana karamin
baby?”
Anti, ba na jin yunwa sosai.”
A nan dai kam ba za mu bar ki da yunwa ba,
idan kun koma gidanku sai ku yi ta
fama.” Dole ta hakura ta kara ci, tana kallon
kwanon awararta, yana harararta. Sai
da Antin ta shiga cikin gida, sannan ta sauke
ajiyar zuciya.
Boye kwanonta ta yi, sannan ta mike ta wuce
gidan Hajja Ku, tana shiga daga
tsakar gida Hajjan ta fara sa ta a gaba, ba ta
kula ta ba, burinta ta zauna ta take
awarar ta.
Daki ta wuce ta bude ta ci iya cinta, ta ji han-
kalinta ya kwanta kamar ta fito daga
fursuna. Har lumshe idanu ta yi don dadi, tana
cikin ci ne ta ji muryar Zaid a tsakar
gidan yana shigowa, ya dan dade suna gai-
sawa da Hajja Ku din da sauran matan
da suke gidan kafin ya karaso dakin. Ta rufe
kwanonta, ta goge hannunta da tissue.
“Twinkle, ba sai kin boye ba, na san me ki ke
ci, hancina na aiki.”
Tsumewa ta yi, *Na sani ai ka na shigowa za
ka fara sawa rayuwata idanu.”
Da gaske ki ka zage ki ka yi ta dura wannan
abin ki na kiba zan nemi mata ‘yar
dagwas na aura, ba zan zauna da Katuwar mata
ba.”
Noorie, ka auro mana, dadin abin dai in dai
wannan ke sa kattancin ita ma a kwan a
tashi za ta zama katuwar. Wannan din ma dai
bebinka ne ya sa ni zama katuwar ba
a haka ka ganni ba ai da.”
Zama ya yi a kasan kafet din dakin ya daga
kafafunta ya dora kan cinyarsa, ya
shiga matsawa.
Ba zaiyi aiki ba dai.”
Ba kya jin magana, an ce ki daina zama haka,
ki na dan daga kafafunki sama idan
kin zauna, amma ba za ki yi ba.”
Ana dai motsawa a huta, idan mutum ya
biyewa ‘yan asibitin nan numfashi ma sai
sun fadawa mutum yadda zai yi.”
Idan sun ce a miki ma ai, sai ai miki da gir-
man kujerarki gimbiya Adiyya, mai
sarautar Zaid.”
Juya idanunta ta yi, sannan kuma ta yi dariya,
Da gaske ka bari, ka na sani

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]