[Advertisements⬇️]

RAYUWAR IRFAN CHAPTER 3 BY (UMMU KHAIRIYYA) - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RAYUWAR IRFAN CHAPTER 3 BY (UMMU KHAIRIYYA)

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Aikin Shine Kawai Sa idone inaso kasamin Ido Akamfani na da nake Sarrafa shinkafa ta yadda Zan kaika A Matsayin Me gadi Amma duk wani Shige da fice na kamfanin inaso ya kasance Atafin Hannuna Sannan Akwai Babban Yaro na Salim shine wannan danace ya bamu guri d’an Uwan Matata ne Shike rik’e da komai na kamfanin inaso duk wani Motsin da zaiyi ya kasance Akan idonka Yan zu Ina wayarka? Sosa Kai Irfan ya yi yace “Ranka ya dad’e Ai banida waya” “yawwa Koda kanada waya yazama lallai na can za maka ita Saboda Aikin da zakayi Ina buk’atar video Acikinsa Kuma inaso ya fito yadda Zan Ganshi tar tar” waya ya D’auko Samsung Galaxy note 10 Sabuwa dal Akwali ya mik’a Masa karb’a ya yi yana jujjuya wayar Alh. Sa’id ne ya d’ora da cewa “A wurin kowa bani da wata Alak’a tsakanina dakai Kuma wannan ya Zama Sirri tsakaninmu zakaje kamfani A Matsayin Me gadi duk da cewa Ina da Me gadi Zaka Zama matai makinsa wajan gabatar da Aikin kalura da Masu Shige da fice Sannan Ina jadda da maka ka lura da Salim da kyau Saboda Yana da Mugun wayo Sosai da Sosai Dan Haka ka kunna wayar duk wasu bayanai zamu k’arasa Anjima da daddare kasauka lafiya”.

Rissinawa Irfan ya yi ya dinga kwararo godiya kana ya mik’e ya yi fita Abakin k’ofa yaci karo da Salim Sallama  ya yi Masa kana ya wuce ya yi hanyar fita har yakai bakin get Ya ji Ankirashi daga bayansa juyawa ya yi cike da Mamakin Wanda ya kirashi Salim ya gani yanayi Masa murmushi Koda ya k’araso kusa dashi da fashi ya yi kana yace “Irfan ko? Nasan zakayi Mamakin inda Nasan Sunanka Yan zu dai mubar wannan maganar Muje na rage maka hanya Dan Nan unguwar bazaka samu Abun Hawa da wuriba” da har zaice A’A Kuma Sai ya yi wani tunani yace “badamuwa muje ko?” Gaba ya yi Irfan na binsa Abaya har Suka iso gaban wata dalleliyar Mota duk da cewa Irfan be San kud’in Mota ba Amma Yana ganinta yasan cewar Motar me tsada ce.

“Bisimillah Shiga ko? Salim ya fad’a Yana  bud’e Masa k’ofar Motar Shiga Irfan ya yi Sannan ya maida k’ofar Motar ya Rufe kana ya zagaya ya Zau na A Mazaunin Driver yaja Motar Suka tafi.

Har k’ofar gida ya Kai Irfan kana ya yi Masa godiya har zai fita Salim ya dakatar dashi da fad’in Ni kuwa Irfan ya kukayi da Alhaji kasan nine babbab yaransa ba kuma Abin da Yake boyemin ko Yan zu ma Inna koma Sai ya gayamin yadda kukayi dashi Dan gaskiya Kai na musam manne Saboda Alhaji be tab’a zuwa ze gana da wani ba yace na fita Dan Haka bani nasha”.

Murmushi Irfan ya yi Sannan yace “Bakomai kawai dai Aiki nazo nema Kuma cikin ikon Allah nasamu”, “yawwa D’an gari na ganka Saurayi yaro K’arami Kuma kozan iya Sanin Aikin Daya baka”.

“Gadi Zan Ringayi A kamfaininsa na Sarrafa Shinkafa” Ajiyar zuciya Salim ya Sauke kana yace “To mutumina  Bari nabarka karna cika ka da Surutu Sai mun had’u goben ko Ina fatan duk wani Abu da baka gane ba zaka iya zuwa ofishina Kai tsaye ka tambayeni”.

Sallama Irfan ya yi Masa ya fita daga Motar Yana ta tunanin Abin da yake tsakanin Alhaji da Salim lallai Akwai Babban Aiki Agareni domin kuwa Dole nayi ta ka tsan_tsan da Salim Yana da Shegen wayo da ya kuma iya dukan cikin Mutum gaskiya Dole nayi taka tsan_tsan.

Koda ya shiga gida cikin Murna da farin ciki ya yi wa Umma bayanin Aikin daya Samu Amma gadi kawai yace Mata be Gaya Mata Ragowar Aikin ba domin wannan yabarshi Amatsayin Sirri tsakaninsu da Alhaji Sa’id.

*****************************

Washe gari k’arfe 800am A Makaranta Tayiwa Irfan da mubarak yau ko Assembly ba’ayi dasu ba Saboda litinin Mezuwa zasu Fara WAEC kowane D’alibi hankalinsa ya koma kan karatu.

Aji Suka wuce kaitsaye duk inda Suka wuce d’alibaine sun cika Suna karatun jarrabawa Koda isarsu cikin Ajin wuri Suka nema Suka zau na Irfan ne ya kalli Mubarak yace “Ta Ina zamu Farana? “Kaidai kayi Irfan ninasan ko nayi karatu ko banyiba zanci jarrabawa Saboda irin kud’in da iyayanmu suke kashewa wajan karatunmu”.

“Nasha Gaya maka Mubarak kacire wannan tunanin Aranka Saboda wani lokacin dama Sau d’aya take ZUWAR maka A Rayuwa Katina fa Kaine Babba Agurin Mahaifinka Yan zu ingirma ya kamashi waye zai tallafeshi? Waye Kuma zai rik’e gidanku? Kadaiyi tunani Mubarak kaji” Shirune Yara tsa gurin “Mubarak  Irfan ya Kira Sunansa Jin Shirin ya yi yawa d’ago Kai ya yi daga kallon littafin da Yake ya kalli Mubarak Sai yaga Ashe hankalinsa Baya gurinsa ya kafe guri guda kawai da Ido.

Shima waigawa ya yi yaga me Mubarak d’in yake kallo Zee ya gano da k’awayen ta irin ta Sun Sata Atsakiya Suna Tai Mata fadanci be Ankaraba kawai Sai ganin Mubarak ya yi ya Nufi gurin “ya Subuhanallah” Irfan ya fad’a tareda dafe kansa “Mubarak! Mubarak!” Ya fad’a da d’an k’arfi Yan da ze jiyohi Amma gogan naku ko Ajikinsa.

Yana Isa gurinsu ya dubi zee yafara magana kamar Haka “Abar k’aunata inasan magana dake “uhm Ina jinka” ta fad’a tana wani ya mutse fuska Kamar taga kashi “Haba zee Agaban yarannan zamuyi maganar Mik’ewa tayi Tace musu tana zuwa.

Fitowa tayi daga inda take zau ne Kai tsaye ta wuce dai_dai kujerar da Irfan yake zau ne ta tsaya takalli Mubarak tace “inajinka muyi maganar Anan Amma kayi Sauri dan inada Abinyi” Mubarak ne ya kalli inda Irfan take yaga ko kallo Basu ishe shiba shi Sabgar gabansa ma kawai yakeyi nutsuwarsa ya dai_daita yafara magana Kamar Haka “Zainab inaso kibani dama Kinga yau daddyna da naki duka basa Nan Sunje Abuja inaso mud’an  fita yawo ko ya kikace wani kallan wulak’anci Tai Masa kana Tace “Kai wane irin wawan yaro ne mubarak Kai Yan zu in Akace Zan fita dakai Saika yadda to in mafarki kakeyi ma ka farka Saboda da yau Anatashi daga Makaranta Yaya Salim d’ina zaizo ya d’aukeni mufita kaji” .

Wani malolon bak’in cikine ya kashe Mubarak ya yi Mutuwar tsaye Awurin “zee Wai meyasa kike wulak’anta nine kituna fa cewa Momynki da tawa Kamar ‘yan uwa suke hakama Daddynki da nawa Meyasa bazaki bani dama ba? Kinga da mun Gama Makaranta Aure kawai za’ayi Mana” cikin Sauri ta dakatar dashi da fad’in “Kai wane irin Mara hankaline Mubarak da zakace za’ai Mana Aure to kabud’e kunnenka da kyau kaji A Yan zu dai ba Wanda ze maka Aure Ni kuwa Macace ko Yan zu A kakaini gidan Miji Zama zanyi kaikuwa kayi k’anka’nta Kuma ko zanyi Aure Yaya Salim Zan Aura dan hakama Kadena wahalar da kanka” Tana kaiwa Nan ta juya ta barshi A tsaye k’awayenta   kuwa me zasuyi Ban da  Dariya cikin b’acin Rai Mubarak ya kalli gurin da Irfan yake har Yan zu karatunsa yake cikin kwanciyar hankali “Irfan!!!” Ya fad’i sunan da k’arfi d’ago Kai kawai Irfan ya yi Yana kallonsa “Haba Irfan ya kana zau ne Ana cimun mutunci Amma ko Ajikinka Murmushin takaici Irfan ya yi   sannan yace Masa “Nina Aikeka? ko kayi Shawara Dani kafin kaje?” wani malolon bak’in cikine ya turnik’e Mubarak ya juya ya fice daga Ajin gaba d’aya.

Shikuwa Irfan tunda yaji Zainab Tace Salim Zezo ya d’auketa yaketa Samata Ido batare da tasani ba bayan Sun tashi daga School Bayan wani Aji Irfan ya nema ya lab’e mubarak nata nemansa Shida Drivernsa har Saida kowa ya tafi Sai ‘yan tsirari wad’anda ba’azo An d’auke suba ciki kuwa harda zainab.

Irfan ne ya fito daga mab’oyarsa  Sakamakon hango Zainab da ya yi tanayin hanyar fita bayanta yabi harta fice daga harabar Makarantar Yana fitowa kuwa ya yi Arba da Salim A tsaye jikin wata Mota bak’a Shikuma Yana Sanye cikin K’anan kaya Kai tsaye inda yake ta nufa da Sauri Irfan ya nemi wani d’an Sak’o ya lab’e ya Shiga Yi musu hotuna Atake yakunna data yaturawa Baban Zainab Saboda yaga lambarsa har guda biyu A cikin wayar.

Kashe wayar ya yi maida ita cikin jakar Yafito daga mab’oyarsa lokacin harsu zainab Sunja sun tafi Yana fitowa ya yi Arba da Mubarak gabansane ya yanke ya fad’i.

            ✍️Har ya k’araso Mubarak be d’auke Ido Akansa ba tambayarsa ya shigayi “Irfan Ina kasamu waya Haka kuma me kakeyi da ita gaskiya Irfan ya firgita da Jin maganganun Mubarak kenan yaga Sanda ya D’auko wayar “kagani fa wayar Megidana ce jiya na manta na taho Masa da ita Shine Yan zu yakira Ni kuma danaga wayar me tsada ce Shine ya sa na lab’e na Amsa Kiran Dan Kar A k’wace kasan yan zu yadda k’wacen wayar Nan ya zaga gari”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Jin jina Kai Mubarak ya yi Alamun ya gamsu sannan yace “Kana da gaskiya Kam Amma munjima Muna jiranka” waskewa ya kumayi yace “to ba ganiba Sai muwuce kawai Mota Suka Shiga Suka d’auki hanyar gida.

A Mota Irfan dogon tunani ya fad’a gaskiya Saiya sa Ido Sosai Dan Akwai Abun da ke faruwa Kan Ahalin guda biyu Dana Alhaji wada Haladu (wato baban Mubarak) da Kuma na Alhaji Sa’id me Shinkafa gaskiya Dole Sai nabi A sannu Dan gaskiya idan Mubarak ya gane Aikin da Baban Zainab yasani to Dole Nasan saiya Gaya Mata Saboda Nasan Yana tsananin santa.

“Irfan!! Irfan!! Firgigit ya dawo daga Duniya tunanin Daya lulak’a “Munfa iso Wai me yake da munka ne” Murmushi Irfan ya yi kana ya Murd’a k’ofar Motar yabud’e ya fita kana ya juyo ya kalli Mubarak yace “karka damu lamarin Rayuwar da Muka tsinci kanmu A zamanin namu Shiya ke da Muna” Murmushi mubarak ya yi kana yace “kaga Malam Sai gobe ka gaida Umma Dan Yan zu zaka Fara wa’azinnan naka daka Saba”.

Girgiza Kai Irfan ya yi ya juya ya Shige gida Yana Shiga Ya tarar da Abin Mamaki ma’aikata yagani Suna Rushe gidan har Sun Rushe d’akinsa da yake kwana ga Kayansu A tsakiyar tsakar gida d’akin Umma ya nufa duk’e yasa meta tana tattara Ragowar kayansu.

Jin shigowarsa yasa ta mik’e tare da fadin “yawwa Irfan kadawo? Shigo ciki ka zau na Akwai magana me Muhimmanci Dana keso zamuyi jiki A Salub’e ya shigo ya ya zau na itama Zama tayi cikin kwantar da hankali ta Soma magana “Irfan bayan tafiyarka Makaranta Babanka yasa meni yace min zai k’ara Aure sati biyu Masu zuwa.

Sannan yace ze Rushe gidannan ya sake  sabon gini Kuma yace indai muna so mu Zau na cikin wannan gidan Sai dai Muringa ci da kanmu Amma sisinsa bazai sake kashe Mana ba Amma Yan zu Ina mafita Irfan?.

“Ya sakeki kawai Umma dama nagaji daganinki cikin wahala” Murmushin takaici tayi sannan Tace “Kai yaro ne Irfan kamanta cewa Allah Yana sane damu Kuma zai kawo Mana mafita Yan zu gurin Zama zamu nema na d’an lokaci kafin A Gama ginin gidannan badan yaso ba Haka ya hak’ura Dan Shi duk Abin da ummansa Tace tanaso to gaskiya duk k’in da Yake Masa to Haka zai Soshi.

Mik’ewa ya yi yace “Ina zuwa Umma Bari naje Naga Mubarak Yan zu Zan dawo” “yawwa  yaron Arzuk’i yadda kake faranta min Allah ya Faran ta maka Irfan saika dawo”.

Fita ya yi ya Nufi gidansu Mubarak Shima

Mubarak d’in ya yi mamakin ganinsa da Irfan be fiya zuwa gidan suba Sai ta Kama Sai dai shi yaje yasa meshi gashi Yan zu suka rabu Kuma ya fahimci Akwai damuwa A tararre da Abokin nasa.

“Irfan lafiya dai? “Kasani dai Mubarak basai nace maka komai ba Akan lamarin gidan mune Alfarma nazo nema gurinka Inaso zamu Zauna Ni da Ummata nawani d’an lokaci Saboda Babana zeyi gyaran gida”.

“Amma cewa ya yi kubar gidan ko ya ya? “Yan zu ba lokacin wannan maganar bane mubarak mayita daga Baya” waya mubarak ya d’auka ya Kira Daddynsa yasanar dashi halinda su Irfan ke ciki beyi wata doguwar tambaya ba ya Amince Ajiye wayar ya yi yakalli Irfan Aboki Muje mu taho da Umma” A gurguje Mubarak ya cire Uniform Suka tafi gidansu Irfan Koda isarsu Sai suka tadda Abban Irfan d’in ya dawo.

A k’ofar gida Suka Ganshi Shida wata Mata daga ganinta kaga irin ‘yan duniyan Nan zuciyar Irfan na k’una yaja Hannun Mubarak Suka wuce batare da ya sake kallonsu ba A tsakar gida Suka tadda Umma Gaban Kayansu ta tsugunna tayi ta gumi, tana ganinsu ta mik’e ta nufoshi tana tambayarsa “ko Ansamu gurin zaman? Kama Hannunta ya yi yace “Umma Ansamu Kuma Agidansu Mubarak zamu Zau na Yan zu Mu kwashe kayan tukun” Mubarak da tausayinsu ya hanashi magana Sai Yan zu yasamu damar yin magana “Umma kubar kayannan Abbana ze Sake Miki wasu”.

“Kana ganin ba da muwa Mubarak “Eh Umma Mutafi kawai Kinga gidan ya cika da k’ura” fitowa Sukayi da Niyyar tafiya har zasu gifta taga ban Abban Irfan ya dakatarsu da cewa “Fatima Wace irin tarbiyya kika yiwa d’ankine da be San darajar Mutane ba, yazo wuce wa yaga (Babar sa talatu ya nuna Matar da suke tare) Amma ya yi Kamar be gan taba ya wuce” Shidai Irfan Abinne ya d’aure Masa Kai ya kalli wadda AKA Kira da Babarsa yaga irin Hajiyoyin Nan ne ta girmi Babansa ma Sosai da Sosai Umman sace ta katse Masa tunani “Irfan tsugunna ka gaisheta” ta fad’a tana Mai kawar dakai “to Umma ita wannan d’in wacece” Ai Irfan be Gama Rufe bakinsa ba uban ya Amshe “to tabba tacce  wan da A ko Ina Saika nuna baka da Mutumci to wannan da kake gani itace kukaci Dara jarta  Zan Sake Muku ginin gida.

Itace Amarya ta Dan Haka tsugunna ka gaisheta” Wani malolon bak’in ciki ne ya turnik’e zuciyar Umman Irfan cin Mutunci A k’ofar gida wannan wace irin Rayuwace yanaso yanunawa Duniya da Kuma Matar da zai Aura ita da d’anta Basu da wani Sauran k’ima   ko Mutunci A idon sa kukane ya sub’uce Mata.

Irfan kuwa Yana ganin Haka yaja hannun Mahaifiyarsa Sukayi hanyar gidan su Mubarak Shima Mubarak ya Mara musu baya cikin d’aga Murya Abban irfan yace “wallahi na Rantse indai bakisa d’anki Irfan ya Duk’awa  talatu ba to Se na sakeki” Umman Irfan jatayi ta tsaya Irfan Kuma yak’ara k’an k’ame Hannunta “Wallahi Umma bazaki Koma ba kuma bazan duk’a Mata ba Sai dai ya Sakeki d’in, Ni nafi San hakama” wanke shi da Mari tayi ta Kuma wankeshi da wani Marin da Fe Kuncin  shi ya yi idanuwansa na tsiya Yar hawaye.

Hannunsa ya zare daga nata yaje ya tsugunna A gabanta

Wata irin Dariya Alhaji Habun ya yi kana ya kalli Irfan yace “Har Yan zu uwarka nada Muradin cigaba da Zama Dani Saboda tasan Bata da wani Gata Saini Dan Haka karage zafin Rai da zuciya kaga Akan Wannan Matar tawa Talatu Zan iya korar ku kaida Mahaifiyar taka”.

Tashi kawai Irfan ya yi yakama Hannun Umma Suka wuce Mubarak Kam Sai hawaye wani Nabin wani Suna Isa gidan su Mubarak Suka tarar Arfa Aifa Sun dawo Nan fa Suka Shiga Murna Sunga Umman Irfan Koda Mubarak ya Bata wani d’aki Daba kowa kin Zama tayi Tace ita dasu Aifa zata Ringa kwana yaran ma Sunji dad’i gaskiya Don Ranar Sunga gata Har wanka ita tayi musu tasa musu Kaya ta shiryasu tsaf Sai k’amshi ke tashi Ajikinsu Koda Daddynsu ya Kira Mubarak Daddare yace yabasu Suyi magana ya Sha labari iri_,iri Aifa har da cewa ita tasake Sabuwar Momy daga yau Momyn Irfan ta koma Momynta Dariya ya Yi tayi musu Amma zuciyarsa fal farin ciki Sukayi Sallama ya kashe wayar.

Alhaji Sa’id ne ya kalli Alhaji wada yace “ya ya dai naganka cikin farin ciki “Hmmm Kai dai Bari ba Dole ka ganni cikin farin ciki da Wal Wala ba D’azu nai maka maganar Abokin yaro na da Mahaifinsa ya koresu daga gidansa Wai zai yi Sabon Aure saboda Shirme irinna wasu Mazan to Shine na Basu d’aki guda Su zau na kanaji Uwar yaron Tace itada Su Aifa Zata zata zau na Raban danaji yaran Nan cikin Wal Wala irin Haka har na manta Mubarak yace min har shi A gaba take sashi ya Su tafi Masallaci shida d’anta in lokacin Sallah ya yi kaga kuwa irin wad’an Nan Matan Inka barsu A gida lafiya k’alau kenan”.

“Gaskiya Dole kayi farin ciki Alh. Wada ni kuwa ga Shawara Meze Hana tunda  suna cikin Wani yanayi ita da yaronta katai maka su kad’au keta Matsayin me Aiki in mijinta zai Yar da tunda Bata da K’anan Yara kaga zasu ringa Samun Albashin da zasu biya buk’atunsu kuma kaga kaima hankalinka zaifi kwanciyar tun da dai kayar da da Tarbiyyar Matar”.

“Bank’i ta takaba Amma kasan Muna da me Aiki Kuma munjima tare da ita tun tana batafi Shekara 13 ba muke tare A jiyar zuciya ya yi sannan ya yi yaci gaba da cewa Amma Babu da muwa tunda gidan Yana da girma d’aukan Masu Aiki biyu bazai Zama da Matsala ba”.

Baban Mubarak ne ya karb’e zan can da fad’in “Hakan zakayi Abokina kaga lafiya k’alau kenan Ni Yan zu nine Aruwa ban San halin da nawa yaran ke ciki ba Bari naduba Naga yaron danasa shi Aiki ko da Akwai wani sak’o wayarsa ya D’auko ya shi ga whatsApp ya Fara Duba Sakonni karaf idonsa yakai Kan Sak’on irfan  zuciyarsa ce ta Azalzale shi da son ya shiga ya Duba yaga Abin da ke cikin Sak’on Shiga ya yi ya ga hotuna ne Amma Rashin network ya Hana subud’e wani d’an guntun tsaki yasaki Mtssssss….. 

Alhaji wada ne yace “kaikuma lafiya kake yimana tsaki Kamar wani tsaka”, “Bazaka gane bane Sak’o Aka turomin Amma Network ya hanashi bud’ewa wlh”.

“Kawo nan na duba maka Kai dama Haka kake wani lokacin garaje ne dakai” karb’ar wayar Baban Mubarak ya yi Wanda ya yi dai_dai da bud’ewar hotunan Zumbur ya mik’e tsaye Yana nuna hotunan Yana cewa ” Salim!!! Zainab!!! Salim!!! Zainab!!!.Innalillahi wa Inna ilaihirraji un.¹¹,¹²

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]