[Advertisements⬇️]

RAYUWAR IRFAN CHAPTER 2 BY (UMMU KHAIRIYYA) - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RAYUWAR IRFAN CHAPTER 2 BY (UMMU KHAIRIYYA)

Www.bankinhausanovels.com.ng 

  ……….✍️K’amewa Irfan ya yi Agurin Yana kallan Babansa idan Nan nasa ya kad’a ya Yi jajir zuciyarsa na K’una, wasu hawaye ne masu tsanin zafi Suka zubo Masa……

“Abba in bakasan Ummata ka saketa Mana ta huta da wannan Rayuwar” A fusace Alh. Habun ya wqnkeshi da Mari “Anya kuwa Irfan Kai jinina ne gaskiya Ina tan tama Kullum Kuna k’un ta tawa Rayuwata kaida Mahaifiyarka Dubeni da Haka nake duk kunbi Kun tsofar Dani duk Abin da nake samu Akanku yake k’arewa 

Ya kukeso nayi da Rayuwata!!!!!!!!.

Wani huci Irfan yakamayi Ummansa ce Tai maza ta kamashi tajashi tsakar gida Kofi  Tai maza tad’auko ta tofa wasu Ayoyi daga cikin Alk’ur’ani me girma ta kafa Masa Abaki Nan da Nan ya Shanye Ajiyar zuciya ya dinga saukewa.

Baban ne ya fito ya kallesu kallan wulak’anci kana yace “Nakusa yadda k’wallan Mangwaro na huta da k’uda wannan bala’i har Ina ga ‘yan Mata can Masu jini Ajika ke kuwa kin tsofe kin tsofaddani keda d’anki kunsani Agaba Sai tatsata kukeyi Nagaji!!!! Nagaji!!!!! Wallahi Sure zan Yi kwana kwanan Nan!!!.

Ya yi maganar cikin k’araji jikin Irfan ne yafara tsuma Ummansa kuwa ganin wannan Masifa kuka ta fashe dashi Tareda Kama Irfan ta Kuma jansa d’aki Dan tasan Irfan hawaye na zuba A fuskarsu tamkar fanfo Saida ya Yi cin Mutunci me isarshi ya Gama ball da kwani Kan tsakar gidan sannan ya fita.

“Umma Wai meye Amfanin Auranki da Babane Kira budashi nizan iya rik’eki Kuma daga yau bazaki K’ara zubda hawayanki Akansa ba”.

  

Girgiza Kai ta shigayi A ah-A ah Irfan baza’ayi hakaba Allah Yana tare damu Kuma Ina da yak’inin cewa bazamu tab’e ba, katashi kaje kayi wanka kazo kaci Abinci” jiki A sanyaye yatashi ya je ya yi wanka yasa kayansa Robar man shafawa ya D’auko zai shafa yaga Babu wurgi ya yi da Robar yace “Dole ne ma na nemi kud’i Saboda halin da muke ciki fita ya yi daga d’akin ya Nufi d’akin Umman tasa da sallama ya shiga  d’akin.

“Umma zanfita” “Irfan katsaya kaci Abinci banaso kafita da yunwa”  “kibarshi Umma inada kud’i A wurina Zan siyi wani Abu inci kiyi hak’uri” cikin tausayawa halin da suke ciki tace “Irfan  banasan karinga sa Abun da Yake faruwa A gidan Nan cikin Ranka Saboda kaga kai  yaro ne yan zu kake ta sowa ko Dan Kar karatunka ya koma Baya katashi kaje Allah ya Yi maka Albarka ya kareka Sharrin Mak’iya”.

“Ameen ummana Nagode” fitowa ya yi k’ofar gida Dan yau ya d’auki d’amarar can za sana’a ya Dena tallan pure water, Tafiya ya somayi cikin hankali da nutsuwa ya iso dai-dai kwanar da zai bar layinsu Sai ya hango Abokansa na layinsu sunyi Dan dazo kowa ya d’au wanka Anata Danna waya.

Murmushi kawai ya yi yak’arasa gunsu tare da bawa kowa hannu Suka gaisa ya yi musu sallama ya wuce tafiya kawai yakeyi be san inda yake jefa k’afarsa ba Saboda tunani ya Yi Masa yawa.

Kuuuumm yaji ya yi karo da Mutum ouch ya fad’a tare da dafe goshinsa ji ya yi An wanke shi da Mari An Kuma wankeshi dashi hawaye ne ya ringa tsiya ya A fuskarsa wani Nabin wani Kafin ya yi wani Han zari wan da ya mareshi ya Shiga Mota har yaja ya tafi.

Haka ya ciga ba da tafiya Yana kuka can yaji Ana hon A bayansa cikin Sauri ya Matsa gani ya yi me Motar ya gan gara gefen hanya parking.

Wani farin Matshin mutum ne ya fito daga Motar Wan da Shekarunsa bazasu Haura 45 ba,  Shikuwa Irfan cigaba ya yi da tafiyarsa ji ya yi kawai an dafa kafad’ar sa ta Baya waigowa ya yi don yaga wan da ya dafashi Mutumin da yaga ya fito daga motarnan ya yi Arba dashi.

Cikin tausayawa Mutimin ya kalli Irfan yace “Kai kuwa yaro me yake damunka da K’arancin Shekarunka kakeso kasawa kanka cikin wani Hali kana tafe kana kuka meye yake da munka yaro Amma zo muje daga mota ka nutsu kaimin bayani “.

Gaba ya yi Irfan yagoge hawayensa yabishi Amma zuciyarsa na d’ar_d’ar Dan Yan zu Mutanan Duniya ba’abin yadda bane lokacin daya Isa bakin motor tararwa ya yi Mutumin har ya shige “Shigo Mana kasaki jikinka” cewar Mutumin Shahada Irfan ya yi yanata Addu’a cikin Ransa bayan ya zau na Mutumin ya kalleshi yace “Da farko Sunana Alh. Sai’d Meshin kafa Nasan duk Wanda ya kwana yatashi Agarinnan yaro da Babba ba wan da be sanniba Dan Haka Yan zu kagayamin damuwarka insha Allahu indai batafi k’arfina ba Zan maka Maganinta cikin izinin Allah”.

Gaban Irfan ne ya yanke ya fad’i Yana dukan uku-uku lallai wannan baban Zeeza ne shi Saida ya fad’a ma yaga kamanninsu “kayi shiru yaro Ina jinka” cikin in Ina yafara magana Kamar Haka “Sunana Irfan Kuma A unguwa Jambulo muke da Zama Yan zu na fito Neman Aikine Saboda na tallafi mamata Saboda Bata da k’arfi” lokaci d’aya Alh. Sai’d yaji Irfan ya kwanta Masa “to Malam Irfan kowane irin Aiki kasamu zakayi”  “Eh zanyi”.

Yawwa Irfan ga Katina gobe  kamar k’arfe 40pm kayimin waya saina gaya maka inda zamu had’u”  Hannu biyu yasa yakarb’a sannan ya kuma mik’a Masa kud’i da baisan nawa bane “kabarshi Alh. Nagode goben Zan kiraka saika gayamin inda Zan Sameka Sai Anjima” bud’e Motar Irfan ya yi yafita yad’auki hanyar gida zuciyarsa cike da farin ciki.

*****************************

Koda Mubarak yadawo gida besamu mamanshi ba hakan Kuma be dameshiba dan yariga ya Saba. Kayansa yacire ya yi wanka yaci Abinci Sannan ya D’auko waya ya kunna data Shine whatsApp Shine Ticktalk shine Instagram shine Facebook, Koda Me Aiki ta fahimci yadawo zuwa tayi ta k’wank’wasa Masa k’ofa “waye” “Nice Irfan Naga lokacin Islamiyya ya yi ne  baka fito katafi ba gasu Aifa harsun tafi” “ya isheki Malama Ni yau bazani ba karki takurawa Rayuwata”.

Juyawa Hauwa Me Aiki tayi tatafi Dan tasan bazai jeba tunda ya fad’a. Misalin k’arfe 6pm Daddynsu Mubarak yadawo daga office da Sallama ya shiga Babban falon gidan Arfa da Aifa najinsa Suka taho da gudu suka Rungumeshi sunai Masa oyo_yo cikin farin cikin ganin yarannasa ya Kama hannayensu Suka koma Kan kujera suka Zau na tqmbayarsu ya yi ko momynsu ta dawo Aiface ta bashi Amsa “Daddy Bata dawoba har yan zu kullum Sai munyi barci take dawowa Kuma kafin mutashi ta fita Shafa Kan yaran ya yi sannan yace “kuyi hak’uri Momynku na zuwa wurin Aikine Kuma Aikinta Akwai wahala Sosai da Sosai Arface ta B’ata Rai “Daddy nifa banasan Momy Saboda itama batasanmu”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Arfa banasan irin wad’an Nan maganga nun kutashi kud’auko littafinku Bari nai wanka nafito nai muku Homework d’in tashi ya yi ya Nufi d’akin Mubarak Akwance yasa meshi yanata Shirgar bacci Kai kawai ya girgiza sannan ya Nufi d’akinsa.

Misalin k’arfe goma na dare gidan ya yi tsit Yara duk Sunyi barci Maman Mubarak ce ta shigo gidan Bata nemi kowa ba tawuce d’akinta tana zuwa ta yadda jaka ta haye gado Sallah ma ba’a Maganarta Daddyn Mubarak Yana Zau ne Kan dadduma Yana lazimi yaji Shigowarta Addu’a ya shafa ya Nufi d’akin nata.

“Sallama ya yi Shiru Bata Amsaba tana kwance Kan tafke Ken gadonta tana ta faman Danna waya bakin gadon ya k’arasa ya zau na “juwairiyya inason zanyi magana dake” “Haba baban Mubarak magana nake da Abokan kasuwancina kasan gobe zamuje Dubai Saro Kaya to Muna tsara yadda ta fiyar zata kasance kaikuma Yan zu kazo Wai zamuyi magana gaskiya bani da lokaci ka Adana zan canka inyana da Muhimmanci kabari na dawo na nutsu Sai muyi”.

Zuciyarsa ce takama suya shikam beyi dacan Mata ba Bata kula dashi Bata kula da yaran da Allah ya Basu. zuciyarsa yakai nesa sannan yace “to tunda gobe zakiyi tafiya yau dai ya kamata kibani hakk’ina  yau kimanin wata guda kenan kina hanani Yan zu Abin da kikeyi ya kyautu kenan ta shi tayi tsam daga gadon tayi hanyar fita har takai bakin k’ofa ta juyo Tace Masa “Kai Sai Masifar tsiya bazaka tab’a barin mutum ya hutaba Dan Haka kayi Kai kad’ai gwara nabar  maka d’akin in ba Haka ba Sai ka hanani barci da surutanka Marasa Amfani” ficewa tayi tareda Jan k’ofar d’akin Gaaam!!!!!!.

Daddyn Mubarak na zau ne Agurin tamkar An dasahi wata nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke kana yatashi ya Nufi d’akin yaransa Dan ya dubasu d’akin Mubarak ya Fara shiga Yana kwance ya yi dai_dai Akan gado ko ta kalmi besamu damar cirewa ba. bubbuga shi ya Shiga yi firgigit ya tashi Yana Mitstsike Ido kallan takaici Daddyn  ya yi Masa “Mubarak Nasha Gaya maka Kadena kwanciya Rigingine ga takalmi baka cireba wannan d’abi’ar ya hudawa ce kayi Sallar Isha’i ma kuwa? Sosa Kai Mubarak d’in ya shigayi Yana sussun kuyar da kai, girgiza Kai kawai Daddyn ya yi Yace “maza tashi kaje kayi Alwala kayi Sallah Ina Nan Ina jiranka” cikin Azama ya wuce ya yo Alwala baibar d’akin ba Saida ya tabbatar ya Yi Sallah da Addu’ar kwanciya bacci sannan ya kashe Masa fitila ya fita.

D’akinsu Aifa ya lek’a yaran suna baccinsu  cikin kwanciyar Hankali Addu’a ya yi ya tofa musu sannan ya koma nasa d’akin waya ya d’auka ya Kira Amininsa Alh. Sai’d Meshikafa bayan sun gaisa ya cewa Aminin NASA “Wai Sa’id Haka zamuyi ta Zama matanmu sudunga juyamu basa samun lokacinmu Dana yaranmu nikam gaskiya nagaji Aure zanyi wlh wannan Masifa har Ina”.

“Ai Kamar kashiga zuciyata Nima Shawarar Dana yanke kenan yaufa Dana dawo gida bansamu zainab Agidaba Dana tambayi yan’ uwanta Sai sukace Wai da Aka tashi School ne ta wuce gidan k’awarta Raina ya b’aci Matuk’a, Koda ta dawo Sai Dana Yi Mata Shegen duka Dan gaskiya ko uwar bangayawa ba Dan Nasan bawani Abu Zatayi Akaiba Mafita d’aya ce Muyi Aure gaskiya Danni nagaji wlh”.

“Shikenan badamuwa inmun had’u gobe se muk’arasa maganar” Sallama sukayi ya kashe wayar zuciyarsa na suya.

*****************************

Irfan kuwa gida yawuce Da gudu ya shige gidan Yana k’walawa Ummansa Kira da Sauri ta fito daga d’aki tana tambayarsa lafiya “Ummana nasamu Aiki insha Allahu Kuma da Alamu wahalarmu tazo k’arshe” Hannu ta d’aga Sama tana me godiya da Ubangiji, “Yan zu Abin da nakeso dakai Irfan karufe bakinka karka sake Babanka yaji kasamu wannan Aikin Yan zu yaushe zaka Fara zuwa Umma Sai zuwa gobe insha Allah zamuji bayanin yadda Aikin yake” Nan ya yi Mata bayanin yadda sukayi da Mai gidan nasa.

“To Irfan Allah yasa Adace nidai nasihata gareka karik’e   gaskiya karka sake kaci Amanarsa”.  “To Umma insha Allahu zanyi Abin da kikace”.

Washegari Bayan sun dawo daga School gun Mubarak Irfan yaje ya Ari wayarsa ya Kira Alh. Sai’d ya Kira yakai Sai 5 ba’a d’aga ba har ya k’ura ya bawa Mubarak wayarsa can kuma Sai gashi yabiyo Kiran karb’ar wayar ya yi d’aga Sallama ya farayi sannan yagaisheshi kana yace “Ranka ya dad’e Irfan ne” Murmushi ya yi d’aga can b’angaran yace “Irfan yaran kirki kazo  gidana Dake Nasarawa G.R.A kasameni ka hau Adai_daita Sahu in ya kawo ka unguwar Saika kirani A waya Sai Driver ya k’araso dakai” To Ranka ya dad’e nagode Sai nazo” kashe wayar ya yi ya mik’awa Mubarak tare da yi Masa godiya ya tafi Mubarak dai tunanin Ina Mubarak zashi ya Shigayi da yaga dai bashi da Amsa wanka ya yi ya tafi gun Abokansa na bakin layi.

Gurin Ummansa ya koma ya yi Mata Sallama Tai Masa Addu’a ya tafi tun Acikin A dai_daita sahun yaketa Addu’a Allah yasa A dace tambayarsa D’an Sahun ya yi koyasan gidan Alh. Sai’d “Eh nasani can zakaje? “Eh can zanje

“Bakada Matsala har k’ofar gidan Zan kaika Yan zu Haka munkusa isa k’ofar gidan” Shiru ne ya Ratsa na d’an wani lokaci Sannan bayan Sun d’an jima Suna Tafiya Sai gasu A k’ofar wani Makeken gida Dan in baka saniba Sai kace Ma’aikatace ba gida ba “Munzo” fita Irfan ya yi Yace “Nawane kudinka” “bada  200” kud’in ya Ciro A Aljihunsa ya mik’a Masa ya k’arasa k’ofar gidan Dutse  ya d’auka ya shiga k’wank’wasa gidan ya jima Yana k’wank’wasa wa Sannan yaji An bud’e k’ofar tangamemen gate d’in wani Dattijo yaga ya lek’o da kansa yace “Dan Samari wake nema” katin ya D’auko ya mik’a Masa karb’a ya yi ya Duba Sannan yace “jirani” Sannan ya juya ya Rufe k’ofar gidan yakai kusan minti goma kafin ya dawo “yaro kashigo daga ciki inji Megidan” k’ofar ya bud’e Masa Suka Shiga ciki Shidai Irfan ban da kalle kalle ba Abin da yakeyi wani Makeken gini Suka iso Nan Mutumin yacewa Irfan “iya Nan ne wurin tsayawata ga k’ofa can k’arasa ka K’wan k’wasa Akwai wan da ze k’arasa dakai”  “to Baba nagode” Matsawa ya Yi kusada k’ofar ya k’wank’wasa Saiga wani Saurayi ya bud’e k’ofa ya fito Wanda Shekarunsa zasu Kai Arba’in da biyar.

Kallan Irfan ya yi Sama da k’asa sannan yace “kashigo inji Megida” Binsa ya yi Abaya Suka shiga katafaren falon, daga can nesa ya hango Alh. Sai’d Yana duba jarida Yana ganin Irfan kuwa ya Ajiyeta Yana Yi Masa Masa Murmushi k’arasawa ya yi inda yake ya tsugunna tare da gaisheshi cikin Fara’a ya Amsa Masa Sannan ya kalli Wanda ya shigo da Irfan yace “Salim bamu guri zamuyi magana wan da Aka Kira da Salim d’in ne ya duk’a yace “Angama Ranka yadad’e” fita ya yi ya Basu guri Alh. Sai’d ne ya fuskanci Irfan Sannan yace “Irfan kasan Aikin Dana ke kaimin gigiza Masa Kai Irfan ya yi  inaso ka Saurareni da kyau kaji banasan kuskure Ko kad’an inkayi gaskiya Kuma karik’e Amana ba Abin da bazan maka ba tukunna ma Yan zu Ajinka nawa A School? “A SS3 Nake yawwa to in har kayi Abin da Nasaka insha Allahu zan d’auki Nauyin Kara tunka har kagama Sannan duk watan Duniya Zan dinga baka Albashin Naira dubu Hamsin Aikin da zakayimin kuwa Shine…..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]