RAWANIN TSIYA CHAPTER 10 BY FADEELAH

 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

6 days later..

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE ASOKORO

A yau kwanan ta shidda a gidan Sadiq.. tun ranar da aka kawota bata gan shi ba..

Hanifa dai a ranar da aka kawota gidan bayan kowa ya tafi kawai hayewa gadonta tayi abinta tayi bacci..

Washegari ranar Lahadi ne ta samu damar zagaya gidan.. Sossai gidan Sadiq ya bata mamaki.. Bata taba ganin tsarin gida irin shi ba a rayuwarta. Gida kamar Zane.. like 70% na abubuwan da ta gani ma bata gane ko meye su ba.. Babu qarya an narka dukiya a cikin gidan! Aikuwa dai gidan Sadiq ya mayar da ita first class baqauya.. Duk da ta tsani mai gidan sossai gidan ya birge ta.. ji take dama ta kore shi ta cigaba da zama a gidan har abada amma kuma inaaa… hakan bazai yiwu ba.8

A yanzu jira kawai take su hadu ta karta mishi rashin mutunci ya sallame ta.

A cikin kwanakin nan shidda kuwa a kullum sai Naana ta aiko mata da abinci breakfast, lunch da dinner.. Har lambar wayarta ta aiko aka bata da saqon cewar idan tana da matsala she shouldn’t hesitate to call her!

Ita dai Hanifa tayi saving lambar amma kuma bata taba kiranta ba..

Ni kuwa nace aiki da rashin hankali wurin Hanifa.. ana aiko miki da abinci ai ko babu komai kya kira kiyi godiya!!6

A kullum dai idan Zubaida (One of Naana’s Maids) ta kawo mata abinci zata tarar da previous dishes (used ones) a bisa dinning.. haka zata kwashe su ta wanke a kicin sannan ta hada ta tafi da su.. Ko sau daya Hanifa bata taba wanke dishes din da ake kawo mata abinci a ciki ba..

Ta ya zata wanke tunda bata iya ba.. tabdijam!!1

Hanifa dai dayake ba wani fitowa take yi ba she spent almost 90% na kwana shiddan nan a sashen ta.. Yawanci dai idan ta fito bai wuce ta ci abincin Naana ba ta koma abinta.2

Bata ga Sadiq ba a tsawon kwanakin kuma she didn’t care at all.. dukda ta qagara ta gan shi suyi rikici a part of her really wants to live longer in the beautiful mansion.

A yau Saturday bayan ta gama breakfast as usual ne ta wuce dakinta tayi wanka….

Ko da na kalli dakin Hanifa sai ganin shi nayi a hargitse.. dukkanin kayan da ta sanya a cikin kwanakin nan shidda suna nan a yashe a dakin.. Hatta qaton gadon dakin jibge yake da kaya, gefen da take bacci ne kawai babu komai..1

Tsaye take a gaban Vanity mirror dinta sanye cikin wani black bum-short da wata doguwar rigar material mai black and white pattern with side slits wanda ya kai hips dinta har yana revealing bum-short din da ta sa.. Rigar material din dai see through ce don haka har black color bra din da ta sanya is visible… Babu abinda take yi sai baza qamshi..4

Ita dai Hanifa dama can mayyar sa qananan kaya ce, su ma din marassa nauyi.

Dogon gashin kanta wanda yake ta qamshi take tajewa.. Mai karatu sossai Hanifa tayi kyau.. don kyau dai akwai shi, Halin ne kawai sai ahankali..4

Ta gama daure gashinta a tsakiyar kai kenan na ga tayi freezing a dalilin qamshin turaren da ta ji- turaren SADIQ.1

Da sauri ta juyo ta gan shi tsaye a bakin qofa with his hands folded around his chest.

Rabon da Hanifa ta sa Sadiq a ido tun ranar da Paapa ya gindaya mata sharadin nan a Kano.. Zuciyarta ce take ta bugawa a dalilin mugun kyau da kwarjinin da yayi mata kamar kullum..

Sanye yake cikin grey three-quarter sweatpant da black polo T-shirt, Gashin kan shi da na fuskar shi sun sha gyara sai qyalli suke yi..

STORY CONTINUES BELOW

when will she get use to this??? she thought!!

“what the hell is this??”1

Wani irin kallo tayi mishi tace “what??”

Ran shi a bace ya nuna kayan da ta baza ko ina yace “meyasa kika baza kaya ko ina kamar dakin mahaukaciya? haka kika tarar da dakin lokacin da kika zo??”

Hanifa wadda ranta ya baci jin ya kira ta da mahaukaciya ta harare shi tace “toh ya kake so inyi da su.. wannan ai aikin house help ne kuma ban gan su ba”

Cike da mamaki Sadiq ya girgiza kai har yana murmushi..

“Ooh I see, da alama baki san yadda abubuwa suke tafiya ba a gidan nan..”2

Gani nayi ya zuba hannuwan shi a aljihun sweatpant dinshi yayinda ya qarasa shigowa yana qara bin dakin da kallo… Kai tsaye Closet dinta ya leqa ya ga akwatunan kayan ta baje a qasa.. kowanne ta bude shi ga kaya ko ina..

Ji nayi yace “interesting”

Yana fitowa ya fara approaching dinta da fuskar shi a murtuke.

Hanifa dai jikinta ne ya fara rawa a yanzu… Ganin yana closing gap din da yake tsakanin su ne na ga ta fara ja da baya.. hakan kuwa bai hana shi cigaba da approaching dinta ba..

Hanifa wadda take ta komawa baya bata san lokacin da ta kai bango ba don haka ne kawai ta rufe idanuwanta yayinda Zuciyarta ta cigaba da bugawa.. she could swear Sadiq wanda yayi closing gap din da yake tsakanin su a wannan lokacin yana jin qarar bugun zuciyar nata.

Dafa bango yayi tare da kai fuskar shi daf da nata yace “Hello Mrs Bunza, idan bacci kike yi ki farka don kuwa nan ba gidan Paapa bane.. this is Abubakar Sadiq Bunza’s”

Janyewa yayi daga gareta yayinda tayi saurin bude idanuwanta tana kallon shi tana sauke numfashin da ta dade tana riqe da shi..

“for your information babu house help don haka ke ce zaki cigaba da maintaining gidan nan.. So get to work” ya fada yayinda ya juya zai bar dakin.

Cike da tsananin mamaki tace “are you kidding me???”

Sadiq wanda ya kai bakin qofa ne ya tsaya sannan ya juyo yace “No Mrs Bunza.. it will be your daily task for the rest of your stay here…”

Kafin ya rufe baki tace “I swear to God baka isa ba.. kana nufin ‘yar aiki zaka mayar da ni??”

Yana murmushi yace “ai tunda kika amsa title din Mrs Bunza kika zama house help din gidan Mr Bunza.. afterall why should I need you if not for that??”

Ya nuna dakinta ya cigaba da fadin “get to work starting from this room, your closet and then move to other parts of the house right now.. kar ki kuskura ki bari in fita in dawo in tarar da bakiyi abinda na sa kiyi ba”

Hanifa wadda mamaki ya cika ta ce tace “idan na qi fa??”2

“Zakiyi” ya fada kai tsaye sannan ya fita ba tare da ya jira jin abinda zata ce ba.

Hanifa dai haka ta tsaya kamar statue tana kallon qofa…

“Lallai ma.. na rantse da Allah baka isa ba, babu wanda ya isa ya sa ni yin abinda banyi niyya ba talk less of aikin gida.. Yanzu zaka ga bala’i a cikin gidan nan in ya so idan ka gaji sai ka sallame ni”

Hanifa dai tun lokacin da Sadiq ya fita komawa tayi kan gado tana ta masifa..

“Lallai ma ya raina mun wayau, saboda Paapa ya bashi Go ahead na ya hukunta ni yadda yake so shine zai mayar da ni jaakaa a cikin gidan shi?? ina matsayin ‘yar Alhaji Aliyu Bugaje zai wulaqanta ni?? toh wai idan ma har zan yi aikin, yana nufin ni kadai zan yi aikin gyaran wannan qaton gidan??? toh ai ko slave sai haka balle ni da ‘yanci na”3

STORY CONTINUES BELOW

Wayarta ta janyo tace “Wallahi bazan yi ba.. bari in kira Paapa in fadi mishi abinda yake yi mun”

Ni kuwa nace Allah ya baki sa’a Hanifa!

Aikuwa ko da ta kira Paapa ringing biyu kawai yayi answering..

“Babyn Paapa yau ta tuna da Paapa.. how are you??”

Turo baki na ga tayi kamar yana ganinta tace “toh Paapa ko jiya na kira ka baka yi picking ba.. daga baya kuma ya qi shiga”

“Sorry Baby, Network din mu was bad jiya.. it was a general issue a nan Kano. Toh yanzu tell me, ya kike ya gida?? ya Sadiq? ya dawo daga American??”

Shiru Hanifa tayi tana mamaki.. wai dama can da bata ganin Sadiq ashe America ya je?? har Paapa ya sani amma ita da ya ajiye ta a gidan shi bata sani ba??

“Paapa I am not fine kuma wallahi Sadiq mugu ne.. Ni kawai gida nake so in dawo, please Paapa ka raba auren nan…” daga nan ta fashe mishi da kuka.

Tabbas kukan da Hanifa take yi yana taba zuciyar Paapa but dole ne yayi mata jan ido akan zaman ta wurin Sadiq.. she needs to learn life a tare da shi..

“Calm down Baby, me yayi miki??”

“Paapa ka ga wai babu mai aiki a gidan ko daya wai shine yace ni zan dinga yin aikin gidan…” ta fada tana kuka.

“toh Baby duka aikin gidan nawa ne??? ai zaki iya yi..”

Kafin ya qarasa maganar shi tace “Paapa??? ka ga girman gidan kuwa??? ko mutane goma fa bazasu iya yin aikin ba.. ni wallahi bazan iya ba Paapa, kawai ka kira shi ka gaya mishi ya kawo masu aiki suyi aikin su”

“I am sorry Baby, just manage and do what he says please.. kuma ko da wasa kar ki kuskura ki qi yin abinda yace kiyi”

“Paapa why do I feel like you dont love me anymore?? kenan ko kashe ni Sadiq zai yi babu ruwan ka?”

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Sadiq bazai kashe ki ba Baby. Kar ki manta abinda na fadi miki… Aljannar ki tana qarqashin qafar shi shiyasa nake so kiyi mishi biyayya.. just do your best and please dont call me again to complain over these kind of things”

Hanifa wadda take kuka dai ta fahimci lallai Paapa bazai yi mata komai ba.. ita ta rasa dalilin da yasa Paapa baya taba ganin laifin Sadiq, at this point ma sai ta fara gani kamar akwai wani abu a qasa, gani take yi kamar Sadiq yana forcing Paapa yayi abu simply because of taimakon da yayi ma kamfanin shi… Hakan ya qara sa ta tsane shi!

“Baby can you hear me?”

Share hawayen fuskarta tayi tace “Yes Paapa”2

“Please just do as he says… Allah yayi miki albarka sannan ya baku zuri’a dayyiba”

Zuciyarta ce ta buga jin addu’ar Paapa.. ‘Zuri’a dayyaba??’ kenan shi Paapa har jira yake ta haifi yara a gidan Sadiq.. ta ya ita da Sadiq zasu zama intimate da har zasu haifi yara??? Impossible and never shall it happen..!!

“Ban ji kin amsa ba Baby”

“Ni bana so Paapa, wallahi bana son shi.. Kawai saboda kai ne nake zaune tare da shi amma”

“toh shikenan Baby.. Allah yasa mu dace. I love you so much”

“I love you too Paapa”

Bayan ta kashe wayar ne ta koma ta kwanta a kan gadon ta cigaba da rusa kuka..

Ji nayi tana fadin “wannan wace irin rayuwa ce?? meyasa Paapa zai yi mun haka??? wallahi bazan yi aiki a gidan nan ba.. babu wanda ya isa ya sa inyi abinda ban ga dama ba.. ya dawo in ga abinda zai yi”

toh fa…1

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

LATE ALHAJI ABUBAKAR MUHAMMAD BUNZA RESIDENCE – ASOKORO

STORY CONTINUES BELOW

Kwance yake a kan cinyarta da idanuwan shi a rufe yayinda take yi mishi head Massage ahankali..

Sadiq dai ko da ya bar gidan kai tsaye family house dinsu ya zo..

Tun washegarin ranar da aka daura auren shi ne yayi tafiya zuwa qasar America shi da Faisal inda suka halarci wani World Petroleum Congress da aka yi a Houston. Asali dai an yi inviting top global energy industries ne wanda a Nigeria aka gayyaci Bunza Oil & Gas da wani Sonaha Oil & Gas.

Jiya da daddare ne ya dawo wanda ko alama bai nemi Hanifa ba.. At a point ma ya manta cewar tana gidan.. Da safen nan ne da ya fito zai sha juice shine ya ga kayan abincin da ta ci a dinning wanda ya gagare ta kai su kicin balle ta wanke su…

“toh wai meyasa baka tsaya can ba matar ka tayi maka massage din?”

“Lokacin da na fito daga gida bata tashi daga bacci ba”

“ah ah, sai dai idan ta koma ne tunda dai ko da Zubaida ta kai mata breakfast tace she saw her”

Kalaman Naana ne suka sa ya gane cewar breakfast din da ya gani a dinning ita ta aika mata.. it didn’t even occur to him cewar Naana ce take ta aika mata abinci.

Bude idanuwan shi yayi yace “wai dama tun da aka kai ta ke ce kike aika mata da abinci???”

“Yes, why?”

“Haba Naana, tana matsayin yarinya newly-wed wadda ita yakamata ta dafa abinci ta aiko miki shine ke kike dafawa kina aika mata??”

“toh meye don na aika ma sirika ta abinci?? baka san ana aika ma amarya abinci ba kafin ta fara shiga kicin???”

“dukda haka Naana, yau kwanan ta Goma fa a gidan sannan ace bata fara shiga kicin ba???”

“Kwana goma fa kace Abba, kwanakin da auren naka yayi ne baka sani ba?? Anya ka damu da auren nan kuwa?? ni dai na ga kai ka kawo matar kace zaka aura ba wai auren dole aka yi maka ba.. kwana daya kawai da yin aure kuma ka tattara ka tafi America ka barta a nan… are you sure everything is fine??”

Da sauri ya tashi zaune yace “Yes Naana, everything is fine.. kin San how very important the Congress is for the Company, kin sani cewar if it wasn’t important I wouldn’t have traded my honeymoon for it.. besides, itama she understood that… Ni fa kawai na ga kamar wahala ne ace kina aika mata abinci everyday”

“Babu wata wahala..”

“toh Yanzu dai tunda ta wuce sati daya a gidan please ki daina aikawa haka nan, daga yau zata fara shiga kicin”

Murmushi tayi tace “kace dai tunda ka dawo kana so ka fara cin girkin amarya”

Murmushi kawai yayi amma bai ce komai ba.. Shi kam ainihin abinda ya sa shi hana ta aika ma Hanifa abinci shine don yana so Girki ya zama added work for her.. he just wants to make her so very much uncomfortable a gidan shi har zuwa lokacin da zata sauke girman kanta ta fahimci rayuwa sannan ya sallame ta..

“toh yanzu dai na ji, bazan qara aika mata da abinci ba.. toh amma kuma ya maganar masu aikin gidan?? shin ka dai sallami Chefs dinnan naka maza ko??? don dai gaskiya bai dace gidan Matar aure a dinga ganin gardawan maza ba”

Fashewa yayi da dariya yace “na sallame su tun kafin bikin Naana”

“Toh kayi hiring Mata kenan??”

Kai tsaye yace “eh”

A ran shi kuwa yace ‘matar gidan ai ita ce house help Naana, I am sorry for lying to you’

“toh madallah..”

“Wai Mini-Me bazata dawo bane?? daga zuwa salon sai ta je tayi zaman ta??” Sadiq ya tambaya yana kallon wayar shi.

“Ai kam ta dade, da ta san zaka zo na tabbata bazata fita ba.. Kodayake tunda har Faisal ne ya kai ta yanzu haka na san tuntuni an gama tana can ta ja shi yawon shopping din da baya qarewa.. bawan Allah ya dawo daga tafiya ko hutawa bai yi ba”

Sadiq wanda ya girgiza kai yana murmushi ne yace “Haka fa a America kodayaushe suna maqale a waya… Gaba daya ma hankalin shi baya kan abinda muka je…” bai qarasa magana bane wayar shi ta fara ringing…

Hanan

Yana murmushi yayi answering yace “Hey dear, har kin tashi daga baccin?”

“Haba dai Chocopie, har fa nayi sallan Zuhr” ta fada cikin shagwaba.

“Oooh really, mu nan da saura… so tell me how you?? yaushe zaki zo mun yawo??”

Naana wadda take murmushi ta miqe zata tafi kicin tace “yaushe dai zata zo kashe maka aure”

Hanan wadda ta jiyo muryarta ce ta fashe da dariya tace “haba Naana, Allah ya hada abu ni kuma in zo in raba??”

A lokacin kuwa Ammi ta fita daga falon..

Sadiq wanda yake dariya yace “I dont mind idan kika zo kika kashe auren Hanan.. if only you will accept my proposal”3

“not again Chocopie”

“toh shikenan.. Yanzu dai yaushe zaki zo??”

“ba nayi niyyan qara sati daya ba after your wedding and you decided to travel to America?”

“I’m sorry dear.. you know how important the Congress is for our company.. but I am all yours yanzu so please ki zo”

“I’ll think about it Chocopie”

Murmushi yayi yace “thanks dear”

“hows your wife??”

“You mean my new student???”3

Fashewa tayi da dariya tace “har an fara classes kenan..”

“Yes…”

“toh ka dai bi ta ahankali dukda na san kai ba mugu bane..”

Dariya yayi yace “ai baki sani ba… she is not even as tough as i thought, I am certain bazata dade ba zata yi hankali in sallame ta”

“how I wish abubuwa zasu canza ku fara soyayya before then.. I am so looking forward to seeing the stone-hearted Abubakar Sadiq Bunza fall in love with a Lady”

“what the hell Hanan..”

“what?? are you scared?? kana tsoro kar abinda na fada ya tabbata…”

Kafin ta qarasa maganar ta ne yace “Now that you’ve managed to spoil my mood just hang up.. lokacin Sallah ya kusa, bari in je in yi Sallah”

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE

ASOKORO

Wuraren qarfe takwas da kwata na dare ya shigo gidan.. Kai tsaye sashen shi ya wuce yayi shirin wanka..

Sadiq dai a yau family house dinsu yayi lunch.. Naana ta dinga yi mishi qorafi akan ya hana a kai ma matar shi abinci sannan shi ya zauna ya ci nata.. Shi kam haquri ya bata tare da fadin tunda kadan ya ci wurinta idan ya koma gida zai ci na Hanifa. Da wannan ne ta haqura ta qyale shi..

Suna Lunch din ne Asma’u ta dawo tare da Faisal.. Aikuwa sossai tayi murnar ganin yayan nata.. Hana shi tafiya tayi har sai bayan Asr sannan suka tafi shi da Faisal..

Ko da suka bar gidan su Sadiq kuwa Faisal ya ja shi Golf Court din Dad a dalilin za’ayi wasa a yau din.. dayake Sadiq yana enjoying Sport din sai kawai ya bi shi suka je.. Daf da Magrib ne aka gama suka wuce masallaci.. basu bar masallacin ba sai da suka yi sallan Isha’I. Daga masallacin ne finally suka yi ma juna Sallama.

Sadiq dai bayan ya fito daga wanka ya shirya cikin dogon wando da T-shirt ne na ga ya fita.

Kai tsaye dinning ya fara zuwa inda ya san zai gane idan Hanifa tayi abinda ya sa tayi ko bata yi ba..

Aikuwa yana shiga dinning din ya ga kayan breakfast din da tayi tun da safe..

Gani nayi ya girgiza kai yace “like seriously???”

Juyawa yayi ya fita yayinda na ga ya wuce sashen ta.

Hanifa ce zaune a kan Ottoman din gadon dakinta yayinda na ga ledojin Chocolates masu yawan gaske a gaban ta..

Asali dai da rana tayi ta jira ta ga Ammi ta aiko mata abinci amma ta ji shiru, ta shiga kicin din tayi ta zagaye amma ta kasa dafa komai.. bata kuma dafa ba a dalilin bata iya ba! Fridge ta bude ta dauki fruits wanda da qyar tayi slicing dinsu ta ci.. Daga nan ne ta kwashi Chocolates dayawa da ta gani a cikin fridge din ta wuce da su sashenta..

A yanzu haka da dare yayi ta ji shiru babu Dinner shine ta sa Chocolates din a gabanta tana ta ci.. Kamar da safe dai dakin yana nan a hargitse, babu abinda ta gyara.

Muryar shi ta jiyo daga bakin qofa yana fadin “ina wasa da ke???”

Chocolate din da yake hannunta ta saki yayinda tayi saurin miqewa tsaye tana kallon shi..2

Sanye take cikin wata Navy blue gajerar sleeveless rigar bacci wadda ta tsaya iya cinyarta.. Rigar dai dukda ba see through bace amma tayi revealing cleavage dinta. Ta hade gashin kanta a tsakiyar kai as usual yayinda take sanye cikin wani slippers mai laushin gaske.. Sossai tayi kyau!

Nan da nan tayi Composing kanta ta harare shi tare da fadin “me nayi???”1

“ban sa ki aiki ba kafin in bar gidan nan da safe??”

“Ni fa na fadi maka bazan yi ba… Ko a gidan mu bana yin komai don haka baka isa ka sa inyi abinda ban yi niyya ba”1

Gani nayi yayi murmushi sannan ya qarasa shigowa dakin yace “really??”

Hanifa wadda jikinta yake rawa shiru tayi ba tare da tace komai ba…

Bata ankara ba ta ji ya kamo hannunta wanda ta ji kamar yayi mata shocking.. his hands felt very soft kamar na jarirai.. it’s actually the first time da Sadiq ya taba ta..!!

Kafin tayi processing abinda ke faruwa ta ji yace “it’s time for you to see what will happen to you idan kika tsallake doka na a gidan nan”

Da qarfin tsiya ya ja ta suka fita daga dakin..

STORY CONTINUES BELOW

Duk qoqarin qwacewa da take yi tana masifa bai sa ya sake ta ba domin kuwa riqo yayi mata da qarfin gaske..

Bayan sunyi tafiya mai tsawo ita dai Hanifa sai gani tayi sun shigo wani Indoor swimming pool arena mai masifar kyau.. it’s more like kamar underground ma wurin yake! tuni ta daina masifa yayinda ta koma kalle-kalle.. ta cika da mamaki sossai na yadda bata gano wurin ba a zaman ta gidan tsawon kwanaki.. kenan there is more to the house than abinda ta gani??

Sadiq dai yana qarasowa kusa da glass wall din arena sin ne na ga ya danna wani button a jikin glass wall din (more like soft touch)

Glass wall din ya rabe biyu ya bude yayinda ya tura ta waje sannan ya danna button din sai kuma Glass din ya rufe..

Hanifa wadda ta ci birki da qyar ta saita tsayuwarta yayinda na ga ta dafe qirjin ta da hannuwan ta biyu.. Numfashinta ne ya fara qoqarin qwacewa yayinda take qoqarin dawo da shi..

Wani mugun ihu ta saki a dalilin ganin wasu Manyan Karnuka da tayi a cikin Cage…

Mai karatu ni kaina da na kalle su sai da na firgita a dalilin yanayi da girman su.. Irin karnukan ne masu gashi dayawa, da ganin su karnukan turawa ne don kuwa ko kadan basu yi kama da breed din Africa ba..2

Ihun da tayi kuwa ya sanya suka fara haushi yayinda suke qoqarin neman hanyar fita daga Cage din..

Hanifa tana ihu tana kuka na ga ta juyo a guje ta dawo tana ta buga glass wall din..

Glass wall din dai irin wanda idan kana ciki kana ganin komai a waje amma kuma idan kana waje baka ganin komai.. haka kuma idan kana ciki baka jin komai daga waje sai anyi activating sound proof!

Sadiq was standing right in front of her amma sam Hanifa bata sani ba… a tunanin ta ya tafi ya barta a wurin.

“don Allah ka bude ni.. karnukan zasu cinye ni.. please I beg you.. Please I dont want to die, Paapa please save me….”

Gaba daya Hanifa tayi jage-jage da hawaye harda majina..1

Sadiq wanda yake tsaye gani nayi yana murmushi, shi dai ya ga tana kuka tana magana amma kuma bai san me take fadi ba tunda ba’a ji sai anyi activating sound proof..

Gani nayi ya danna wani button a kan glass wall din… Nan da nan ya zama ma Hanifa Visible wanda tayi mamaki sossai ganin shi tsaye yana yi mata murmushin mugunta..

“don Allah ka bude ni, karnukan nan zasu cinye ni.. please”

Activating sound proof yayi sannan yace “sorry?? what were you saying?”

Hanifa dai dukda ran ta yana quna a dalilin kalar wulaqancin da yake yi mata for the first time dole ne ta roqe shi ya bude mata..

“Nace don Allah kayi haquri ka bude ni..”

“Zakiyi abinda nace kiyi kenan or what??” ya fada cikin rashin fahimta

Gani nayi Hanifa ta juya ta kalli karnukan wadanda suke ta qoqarin balle qofar cage din su yayinda ta juyo da sauri tace “eh zanyi”

“ban ji ba”

“Nace zan yi.. wallahi zan yi” ta fada tana kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.

“Very well Mrs Bunza”

Gani nayi ya danna wani button yayinda glass wall din ya rabe biyu ya bude kamar qofa..

Aikuwa wall din bata gama budewa ba Hanifa ta ratsa ta shigo.. kai tsaye ta rungume shi gam tana kuka yayinda take sauke numfashi kamar wadda tayi gudun kilometer dari..

Sadiq dai for the first time zuciyar shi ta buga a dalilin Hanifa.. I mean a dalilin wannan bone crushing hug din da tayi mishi.4

A rayuwar shi gaba daya bai taba rungume wata mace ba banda qanwar shi Asma’u.. A tunanin shi a hug is a hug toh amma kuma suprisingly for him Hug din Asma’u ba daya bane da wannan.. its definitely because he hates this girl shiyasa!! atleast that’s what he thinks.. but is it so???4

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi ya banbare ta daga jikinshi da qarfin gaske sannan ya tura ta baya yace “Ko da wasa kar ki qara taba ni balle ki rungume ni..”

Fuskar shi a murtuke ya nuna kayan da ke jikinta yace “and yes, kar ki qara sa mun irin wannan kayan a cikin gida.. nan ba gidan ‘yan iska bane”

Sossai wannan kalaman nashi suka bata ma Hanifa rai wanda batada damar yin magana a yanzu considering the situation amma tayi alqawarin har half naked sai tayi mishi yawo a cikin gida… idan bazai iya jure ganin ta a haka ba ya sallame ta…

Hannun shi ya sa a cikin aljihun wandon shi yace “kin ga Cage din karnukan can?? it will be your new room idan kika kuskura kika yi disobeying orders dina daga yau.. so the choice is yours..”

Hanifa dai hawaye ne suke bin fuskarta yayinda take ji kamar ta Harbe Sadiq.. Gaba daya plan dinta ya rushe a yanzu, she has no choice but to do everything that he asks, kenan how will she leave the house???

“Now that you’ve understood perfectly cewar baki da wani zabin da ya wuce ki bi umurni na, I think zaman gidan nan zai yi miki sauqi”

“what do i have to do??” ta fada yayinda take qoqarin daina kukan da take yi.

“i have already told you.. aikin cikin gidan nan zakiyi kullum, bana so in ga datti a ko ina cikin gidan nan, when I say everywhere I mean harda sashe na.. I want to see everything completely and spotlessly clean. As for today you will have to clean your room, the dinning room and the kitchen… get to work”

Har ya juya zai bar Swimming pool arena din ne na ga ya tsaya ya juyo yace “one more thing.. Naana bazata qara aiko miki da abinci ba don haka daga gobe ke ce zaki dinga dafa abinci. Ina zuwa ofis 7:45am don haka my breakfast should be ready before then.. well, kar ki damu da Lunch dina but I expect to see my Dinner on the table.. So all the best”8

Bayan ya gama magana ne ya wuce ya barta a tsaye…

Hanifa dai wani gululun baqin ciki ne ya taso mata yayinda na ga ta zame ta fadi a qasa.. Wani sabon kuka ta fara rerawa yayinda ta rasa abin yi… Duniya bata taba yi mata zafi ba kamar yau. Duk gatan ta a yau babu, Paapan da yake supporting dinta ya juya mata baya.. infact ya hada ta da mugun mutum wanda babu imani a tattare da shi.. Gashi ya bata sharadi lallai kar ta kuskura ta kashe aurenta da kanta.. Yanzu ta ya zata bar gidan Sadiq??

Gani nayi ta tashi tsaye tace “should I call his Naana and tell her???” can kuma ta turo baki tace “You fool Hanifa.. lokacin da take aiko miki abinci baki kira kika yi mata godiya ba sai yanzu zaki kai mata qaran danta.. what makes you think she will even side with you??”4

Juyawa tayi ta hango cage din karnukan wanda ya tabbatar mata da lallai Sadiq yana ganinta clearly lokacin da take ta kuka tana roqon shi a waje.. A yanzu karnukan sun koma sun natsu abin su kamar ba su suka gama haushi ba.. Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta wuce ta fita…

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Hanifa dai daga kan dinning din ta fara.. ina kallonta tana zubar da hawaye ta tattara kayan ta kai kicin..

Ko da ta tsaya yin wanke-wanken da qyar ta tsara yadda zata yi shi.. bata kula da lafiyayyen dishwasher ba a kusa da ita.. well, zai iya yiwuwa ma ta gani bata san ko meye shi ba tunda dai ba aikin take yi ba..3

Hanifa tana ta kuka tana wanke-wanken.. Da ganin yadda take yi kuwa zaka tabbatar yau din ita ce rana ta farko da ta fara yin shi.. Sai da tayi kusan awa daya tana yi (kayan da yakamata a ce cikin minti biyar ma ta gama wanke su). Aikuwa sai da ta fasa plate daya kafin ta gama, Allah ya taimake ta bata ji ciwo ba.3

A gajiye ta fito daga kicin din ta wuce sashen ta..

Ko da ta shiga dakinta tsayawa tayi bakin qofa looking so confused, da alama dai bata san daga inda zata fara ba..

“I hate you Sadiq, Na tsane ka.. Allah ya isa tsakani na da kai” na ji ta fada yayinda ta fara tattara duka kayan da ta baza ta dinga kai su closet dinta..

Bayan ta gama kwashe su tsab ta gyara gadonta sannan ta koma closet din where the main work is..

Mai karatu ni dai ina zaune a gefe Hanifa ta fara jera kayanta a wadrobe… dukda she is doing it well, she is doing it very lazily and sluggishly..

Tun ina daga zaune har na koma na kwanta, kai har na fara gyangyadi… in taqaice muku dai ban san lokacin da nayi bacci ba, Ko da na farka wuraren qarfe biyu da rabi na ga Hanifa tana ta jeren kayan ta, abinda ya bani mamaki a wannan lokacin kuwa shine yadda gaba daya ta daina kuka amma kuma she looked very much tired and sleepy…

Sossai ta bani tausayi amma kuma babu halin in taimaka mata kar Sadiq ya hango ni ya ci qaniya ta don haka ne na juya na cigaba da bacci na…8

ABUBAKAR SADIQ BUNZA RESIDENCE

ASOKORO+

Tsaye yake a kan treadmill machine na danqararren Gym din gidan yayinda yake working out..

Its exactly 9:35am…

Sadiq dai tun da asuba bayan da ya dawo daga masallaci ya koma dakin shi ya cigaba da Azkar har qarfe 7:30am na safe…

Normally idan week days ne, the next thing he does is shirin zuwa ofis toh amma today being Sunday sai ya wuce Gym don ya motsa jiki..

Yanzu haka yana daf da gamawa ne wayar shi ta fara ringing..

Gani nayi ya tsayar da machine din sannan ya sauka ya nufi wurin da wayar take…

Mai karatu I had to lower my gaze a dalilin well built body din Sadiq da na hango. His six pack abs, so on point which I am sure yana ji da shi..

Gaba daya jikinshi zufa ne.. Gashin kanshi ma ya kwanta a dalilin zufa.. da alama dai yayi working out sossai..

“Assalamu alaikum Naana ina kwana” ya fada da yayi answering call din.

“Lafiya lau Abba… Ya gida ya amaryarka???”

“She is fine”

“Madallah.. Dama na kira ne in ji lafiyar ku, please ka gaida mun ita”

“Zata ji insha Allah”

“amma dai yakamata ka kai ta gidajen uncles dinka su gaisa.. ko ya ka gani?”

“Yes Naana, I think anjima da yamma zamu je and daga nan ma zamu zo mu gaishe ki”

“toh madallah, Allah yayi albarka”

“Ameen My Naana.. Mini fa???”

“tana sashen ta.. I am sure she is still sleeping”

“okay toh I will call her later”

Bayan sunyi sallama ne na ga ya janyo singlet dinshi ya sa sannan ya kwashe wayoyin shi ya fito ya wuce sashen shi.

*********************

Bayan Sadiq yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya ne ya fito ya nufi sashenta.

Yana shiga dakinta ya ga ko ina tsab-tsab amma kuma bai gan ta ba.. A tunanin shi tana bathroom don haka ne ya leqa closet dinta don ya tabbatar da ta gyara shi tsab..

Aikuwa yana shiga na ga ya tsaya cak yayinda fuskar shi tayi displaying mamaki..

Hanifa ce kwance a qasan closet din tana bacci. Gashinta da ta daure a tsakiyar kai duk yayi buzu-buzu yayinda gajerar nighty dinta duk ta tattare ta bayyana fararen cinyoyinta..3

A gefenta kuwa qaton trolley guda daya mai dauke da inner wears dinta kawai ya gani wanda yake a bude.. Da alama dai ta gama jera dukkanin sauran kayanta, Na inner wears din ne suka gagare ta wanda da alama bacci ne ya sace ta…

Tambayar da nayi itace shin tayi sallar asuba kuwa???

Sadiq wanda yake tsaye gani nayi ya juya zai bar closet din a dalilin yanayin yadda ya ga Hanifa.. he just doesn’t like seeing her dressed like that..

Har ya fita sai kuma ya dawo.. Da qafar shi na ga ya taba ta alamar yana tashinta daga baccin..

Aikuwa a firgice ta farka ta tashi zaune tana salati.. Daga kai tayi tana kallonshi yayinda take qoqarin gyara gashin kanta.. Fuskarta duk ta kumbura, da ganin ta ma zaka gane lallai baccin bai ishe ta ba..

STORY CONTINUES BELOW

Fuskar shi a murtuke yace “baki iya gaisuwa bane??”

Ran Hanifa a bace tace “ina kwana”

Ba tare da ya amsa ba yace “what is this doing here???” ya nuna trolley na inner wears din da ke gefenta.

Miqewa tayi tsaye tayi ‘yar miqa wadda ta sanya ta banqare qirjinta..

Sadiq wanda yake kallonta ne na ga yayi saurin kawar da fuskar shi tare da fadin “I have warned you to stop wearing these kinda clothes in this house..”2

“ban gane ba.. wai hijabi kake so in dinga sakawa a cikin gida ko me???”

Ba tare da ya amsa ta ba yace “I asked you why this is still here…”

Tun kafin ya qarasa magana ne tace “Bacci ne ya kwashe ni.. I was awake doing this work har asuba da aka kira sallah and bayan na idar na dawo in cigaba shine bacci ya sace ni”

the first time da Hanifa ta natsu tana yi mishi bayani.. Lallai karnukan jiya sun bata tsoro, he thought!

Murmushi na ga yayi sannan yace “get it done and go prepare my breakfast”

Ya juya zai fita ne Hanifa tace “wait”

“what?” ya fada tare da juyowa

Da hannu tayi mishi alamar ya tsaya yayinda ta juya ta nufi wata drawer ta ciro wata qatuwar envelope ta dawo wurinshi tace “take”

Ba tare da ya karba ba yace “meye wannan??”

“Kudin sadakin da ka bani ne da kuma blank cheque dinka.. I dont need your money”

Wani irin kallo yayi mata sannan yace “I don’t give and take back, it’s not in my character so kiyi duk abinda kika ga dama da su but you certainly should not give it back” daga nan ya juya ya fita abinshi.

Ranta a bace ta duqa ta dauki bra daga cikin trolley ta jefa a hanyar da ya bi ya fita tace “Mai shegen girman kan tsiya.. Yana so ya nuna mun cewar kudi sunyi mishi yawa basu dame shi ba. Mugu kawai, kar ka ga kamar you are on top of this game.. I swear you are not. I will somehow make my plan work”

Toh Hajiya Hanifa..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe goma sha daya da kwata tana tsaye a kicin sanye cikin wata sleeveless jumpsuit.. As usual ta hade gashinta a tsakiyar kai. Sossai tayi kyau!

Riqe take da wayarta yayinda ta shiga Google tana neman kalan breakfast din da zata hada..

Gaba daya abubuwan da ta gani babu mai dan dama-dama wanda zata iya yi…

Ganin lokaci yana tafiya ne tayi deciding ta soya qwai tunda ta ga kamar shine babu wahala..

Aikuwa ko da ta dauko qwan fasawa kawai ta dinga yi ba tare da ta kula idan shell ya shiga ba.. dayake fasawan rashin hankali ta yi kuwa sossai shell din ya shiga cikin ruwan qwan.

Qwai guda Goma ta fasa sannan ta bare maggi guda Goma da gishiri cokali goma.. To her, that’s the right proportion.6

Frying pan din kuwa shaqe shi tayi da mai sannan ta kunna Gas Cooker da qyar..2

Dukda sanyin AC da ke kicin din Hanifa sai zufa take yi.. babu shakka yau tana yin wani abinda bata taba yi ba.

Mai karatu in taqaice maka zance dai qwai yayi latsam a cikin frying pan.. Haka ya dade a nitse cikin mai.. ita kanta da take kallo ta san ba daidai bane.. Ba tare da ta bata ma kanta lokaci ba na ga ta kwashe shi tana fadin “idan bai yi mishi ba sai ya kawo wadda zata yi mishi da kyau”3

toh fa…

***********************

Zaune yake a kan kujerar dinning.. Cup na Orange juice ne a gaban shi yana sha yayinda yake jiran breakfast dinshi.3

STORY CONTINUES BELOW

Hanifa ce ta fito riqe da plate na qwan da ta soya..

Sadiq dai har ta qaraso ta ajiye plate din a gaban shi bai kalle ta ba..

Ta juya zata tafi ne yace “Come here” yayinda yake kallon plate din da ta ajiye.

Juyowa tayi tana kallon shi a wulaqance

“What’s this?? ya fada cike da mamaki

“Qwai ne???”

Murmushi na ga yayi sannan yace “zauna”

Babu musu ta ja kujerar da take kusa da shi ta zauna..

Tura mata plate din yayi yace “Bisimillah”

Kai tsaye tace “naka ne ai”

“Na san nawa ne kuma nace ki ci.. ko bazaki ci bane??”

Hanifa wadda ta kalli fuskar shi ta kula babu mutunci ce na ga ta harare shi sannan ta janyo plate din tana kallo..

Juice dinshi yayi sipping yana kallonta yace “go ahead Mrs Bunza”

Hanifa dai ta sani sarai wannan qwan da ta soya bazai yi dadi ba gashi ko alama babu kyan gani.. Tabbas Sadiq yana so ne kawai ya wulaqanta ta ba wani abu ba..

Gani nayi ta janyo fork tayi cutting a very small portion na qwan ta kai bakinta.. Aikuwa tana sakawa bakinta ta dawo da shi har tana kakarin amai..

Sadiq bai ankara ba ya ga ta janyo Cup na Juice dinshi ta fara sha…

“So how was it??” ya tambaye ta yana murmushin mugunta.

Hanifa dai ji tayi kamar gishiri zai yanke mata harshe.. sai yamutse baki take yi.

“imagine qatuwa da ke amma common qwai baki iya soyawa ba and you have the guts to insult your maids back there at home.. Instead of kiyi musu godiya na abubuwan da suke yi miki amma sai ki zauna kiyi ta wulaqanta su.. This alone shows that they are better than you! what can you even do in your life?? nothing I guess”

Ya miqe tare da kwashe wayoyin shi yace “ki cinye qwan nan don bazan yarda kiyi mun asara ba and yes, make sure you clean the house and failure to do so will attract a severe punishment”

Hanifa wadda hawaye suka fara bin fuskarta sossai ta ji haushin kalaman shi.. tayi niyyan ta gaya mishi magana amma da ta tuno abinda ya faru jiya sai ta kasa.. Gani nayi ta duqar da kanta a kan table din fa fashe da kuka.

Sadiq wanda yake daf da fita daga dinning din kuwa jin ta fashe da kuka ne ya dawo ya matso kusa da ita ya duqo tare da kai bakinshi saitin kunnen ta yace “crying won’t solve your problem Mrs Bunza, tashi tsaye zakiyi ki yi abinda yakamata..”

Hanifa wadda take jin shi a daf da ita kuwa sai sauke numfashi take yi yayinda zuciyarta take ta bugawa.. A duk lokacin da Sadiq yake very close to her akwai wani weird feeling da take ji wanda take kyautata zaton QIYAYYAR da take tsakanin su ce take janyo hakan.. toh amma kuma shin hakan ne??3

Janyewa yayi daga gareta yace “Ki shirya anjima da yamma around 5:00pm zamu fita kuma kar ki bata mun lokaci..”

Daga nan ya fita abinshi.

Yana fita Hanifa ta dago kanta tana kuka tace “Allah ya isa tsakani na da kai.. mugu kawai”

Gani nayi ta miqe ta kwashe plate din qwan da Cup na Juice dinshi tayi clearing table din sannan ta wuce kicin ta zubar da qwan a waste bin ta fara wanke dishes din.. amma fa tana yi tana kuka tana zage-zage!

Ko da ta gama komawa tayi ta fara bin gidan tana gyara abinda ba daidai ba.. Allah ya taimake ta ma komai na gidan is in order so there isn’t really much to do.4

STORY CONTINUES BELOW

Sashen Sadiq ne kawai ta qi shiga ta gyara.. Ko meyasa???2

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe biyar da kwata yana zaune a main sitting room na gidan yana magana da ita a video call..

Hanan!!

Sanye yake cikin wani tsadaddan baqin yadi wanda aka yi ma dinkin half jumper daidai jikin shi.. Sai baza qamshi yake yi. Tabbas idan dai a fannin kyau ne Sadiq zai zo na daya don kuwa samun namiji mai kyau da kwarjinin shi sai an tona..

“I swear Hanan har na gaji.. ina zaman zamana na dauko ma kaina aiki”

“Haba teacher, you are suppose to be enjoying the class ai.. kenan ta gagare ka within one day?”

Yana dariya yace “bazaki gane bane.. kin san mugunta ba hali na bane Hanan, right now I just..” bai qarasa magana bane ya jiyo qamshin turaren ta..

Yana daga kai kuwa na ga ya miqe da sauri ran shi a bace a dalilin ganin yanayin da Hanifa ta fito..

Sanye take cikin dinkin fitted gown na wani blue and Gold lace half way revealing the bra she is wearing..

Da sauri yace “meye haka zaki fito mun tsirara?? how many times do I have to tell you cewar nan ba gidan ‘yan iska bane??”1

Hanifa dai tsayawa tayi cak confusedly ta kalli jikinta sannan ta kalle shi tace “tsirara kuma?? baka ga kaya a jikina ba?? again, ni ba ‘yar iska bace.. kai ne baqauye”

“what???” ya fada ranshi a bace yayinda na ga yayi composing kanshi. Da alama ya kula so take ta bata mishi rai.

Kauda kai yayi yace “if you don’t dress properly I swear zakiyi regretting abinda zanyi miki??”

“toh ai shiyasa na zo ka taimaka mun..” ta fada tare da qarasowa wurin shi..

Ko da Sadiq ya juyo idanuwan shi suka sauka a kan qirjinta sai gani nayi ya runtse su ya bude yace “Hanifa ina wasa da ke??”

Murmushi tayi tace “No” tare da juya mishi baya ta zura hannuwan rigar tace “Ja mun Zip”

Sadiq wanda ya zama speechless gani nayi ya sa ma dogon gashinta idanuwa babu ko qyaftawa..2

“Please Mr Bunza..”

Composing kanshi yayi yace “Kin san dama zaki iya sa hannun rigar shine baki sa ba tun a dakin ki??? do you have to cone out naked???”3

“Mr Bunza ba fa naked na fito ba, I am putting on a bra.. baka gani bane??” ta fada cike da tsokana tana murmushi yayinda ta cigaba da fadin “please ja mun Zip mu tafi, sai dai kuma idan mun fasa fitan”

Gani nayi ya sa hannu ya fara ja mata Zip din yayinda idanuwan shi suka cigaba da kallon dogon gashinta…

At a point sai na ga kamar yayi freezing while staring at her long hair wanda in the process hannun shi ya taba bayanta..

Flinching tayi a dalilin wani shocking da hannun nashi yayi mata.. Runtse idanuwa tayi ta bude yayinda zuciyarta take bugawa.. thesame feeling again! why???

Gani nayi Sadiq ya kama dogon gashin nata ya daga sannan ya qarasa ja mata zip din.. abin mamaki kuwa ko da ya gama ja mata kasa sakin gashin yayi..

Hanifa wadda ta fito daga state of reverie din da ta shiga ce ta ji ya qi sakin gashinta.

“Mr Bunza ka gama???”

Da sauri ya saki gashin nata yayinda ya koma ya zauna.

Juyowa tayi ta kalle shi tana murmushi tace “thanks” sannan ta juya ta koma daki..

Bin ta yayi da ido har ta bar falon yayinda yayi resting bayan shi a kujera ya lumshe idanuwa..

The first time da wani abu na Hanifa yayi attracting dinshi.. her long hair!4

A rayuwar Sadiq dogon gashin mace yana bala’in birge shi.. infact it’s the only thing he finds attractive in a lady!!

Tun kafin suyi aure yana ganin gashinta a bude amma bai taba kallon shi ba closely kamar a yau.. Very long, So soft, beautiful and most importantly qamshin da gashin ke yi mai dadin gaske..!

Bai ankara ba ya ji Hanan ta fashe da wata muguwar dariya..1

Da sauri ya kalli wayar a gefen shi kan kujera.. gaba daya ya manta cewar he was talking to her on phone when Hanifa came in.

Yana daukar wayar ya ganta tana ta kwasar dariya harda hawaye…

Ranshi a bace yace “what’s funny??”

Hanan wadda take qoqarin saita muryarta ce tace “I swear Chocopie you are in trouble.. Hanifa ita ce daidai da kai, wani abun ma sai kun fara soyayya..”2

Bai jira ta gama magana ba ya kashe wayar ya jefar…!!2³

About AIS

Check Also

RAWANIN TSIYA CHAPTER 5 BY FADEELAH

RAWANIN TSIYA CHAPTER 5 BY FADEELAH Www.bankinhausanovels.com.ng  ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE NASSARAWA GRA+ A yau …

One comment

  1. Thanks,Muna jiran update

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *