[Advertisements⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 14 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI 

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.”
Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi.
“Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.”

Ta juyo ta dube shi. Ya ce, “Kina sona?” Ta
zaro ido cikin tsananin mamaki. Ta murtsuke idanunta wai ta ga ko mafarki take yi. Ta sake kallonshi a gabanta. Ta cce “Nasan kana tsokanata ne, ni ban fi
yar wanke-wanken gidanka ba.” Ya ce, “Ni fa
na tambaye ki ne kawai, kina sona?”
Ta durkusa kasa, “Don Allah kada ka cutar dani, wallahi na dauke ka na musamman a rayuwata, na soma tsoron ka.” Hawaye suka zubo mata.
Ya tsugunna shima, “Ba ki sona dai a takaice kenan ba za ki aure ni ba?” Ta dago ido, suka kalli juna hawaye suna sauka a kan kumatunta. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ni ina sonki, kuma zan aure ki, kuma za ki

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


yi karatunki har ma ki cika burinki na zama ‘yar
Jarida. Ki ci gaba da daukana na musamman a
rayuwarki, koda ba ki sona.” Ya mike tsaye. “Sai dai ke ce ta hudu da zan aure ku rana daya.” Ta mike tsaye, “Don Allah ka fada min wani zancen daban ba da wadannan zantukan na. zolaya ba.”
Yayi murmushi, “Na tafi zan sake zuwa.” Nan ya bar ta tsaye tana al’ajabi. Ta jingina da bango, ba zan fada ma kowa wannan zancen ba, don na san ba gaskiya yake fada min ba.
Ta share idanunta ta nufi cikin gidan ta ci gaba da harkokinta, tana jin su suna tattauna zancen dauko kanin Babansu. Ta ce a ranta ‘Ni dai zan ga ikon Allah!’
Daga nan gidan Anty Momiyo ya nufa, ta kai shi dakin da a kwatunan suke. Yayi murna da ganin su don sun birge shi. Ya ce, “Yanzun nawa ne cikona da Allah kai su yau, zuwa jibi a kai ma kowa kayanta.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Anty Momiyo ta ce, “Ai ba don ciwonka ba yau muka tsara za a kai kayan amma jibin ma ya yi. Ya ce, “Nawa ne ciko na?”
Ta ce, “Hajiyar ku ta biya kudin ukunnan, tace ba za ta bada na karshen nan ba, shatima ya ce Au! Ta sai min ne? gaskiya ta min komai. To. ki cire kudin na Salma din, sai ki bata canji. Ta ce, Ta ce tuni na cire har ma nayi maka karambani.”
Ta janyo wata Ghana most go wasu lesuka ne masu shegen kyau, ta ce “Ka gan su guda goma sha biyu ne kowacce guda uku.
Ya ce, “Ai da kin bani kudina don na ba Hajiya kudin komai.” Ta ce, “Duk dai ba zai ki ba.” Ya ce, “Bari ma in je in samu Hajiyar muji ya za ayi?” Ta ce, “To muje da akwatunan mana. Ka dibi wasu nima in diba a mota ta muje ya ce “To.”
Yasha mamaki da Hajiya ta fito da kayan da aka siya. Sai dai ta ce ita na mutum uku ne, sai, yasan yanda zai yi da dayar.
Ya ce, To bari in bada kudi itama sai a kawo mata.” Hajiya ta ce, “Sam! Je kasuwa ka siya. Yayi shiru yana kallon kayan.
Anty Momiyo ta ce, “Kana zuwa kasuwa za ka hada komai.” Ya ce, “Anty ku ne ku ka san kayanku. To ke don Allah in ba ki ki sai mata tace yawanci kayan nan ba ‘yan nan ba ne ba, lallai a samu irinsu ba. Amma ka kawo sai a duba.”
Hajiya tana jin su kala bata ce ba. ya ce, “Zan yi miki Transfer cire mata kukan ta kija mata cikin akwatin ta kada kuma  ta ce ban da ita marainiyar Allah. Take ya tura mata kudi don ta sai ma Salma kayan lefeb
Lefen Amna a ka soma kawai kafin ranar sai da ya sanar da ita zuwan su Hajiya kuma sai da Www.bankinhausanovels.com.ng
ta sa kayan Amna sun fi na kowa a cewarta babban goro sai magogin karfe. Suma sun samu sauka ta musamman sannan sun dauko tukuici mai tsoka.
Washegari aka kai na Nafisa. Nan ma sun yi bajintar tukwici. Na Aliya ma an kai, suma sun ba da daidai karfinsu. Aka dawo ana ta tsegunguma.
Salma kuwa cewa yayi a bari zai kai mata, don ya ji lokacin da Hajiyarshi ta kira Baba Alhaji Musa tana tambayar shi game da Salma, bayan sun dawo kai sadaki da kudin gaisuwa. Wai nawa suka bada?
Ya ce, “Dubu hamsin suka ce kudin gaisuwa ashirin.” Ta ce,”Wai an binciki asalin yarinyar?” Ya ce, “Shi ya ce ya bincika.” Ta ce, “Yasan ‘yar matsiyata ce shi yasa baya so aje gidan, ai za a kai lefe, za’a zo min da labari.” Shi kuma yana falon bata san ya shigo ba, don haka sai ya juya.
Ranar da za’a kai na gidan su Salma ya ce su bar shi shi ne zai kai. Hajiya ta ce, ai ko dole a kai. Ya ce, “Hajiya kiyi hakuri zan kai mata da kaina.”
Alhaji yace, “Wannan fa al’ada ce, don haka ki har shi kawai.” ya kai da kanshi. Bayan ya kai ya baro gidan, Inna ta ce “Kai Hadiza! Ku lura da lamarin nan da kyau. Ba shi da dangi ne zai kawo lefe da kansa! ni fa ina tsoron in’kai ‘yata mahallaka da kaina?”
Hadiza ta ce, “Ni dai ban tsorata ba, ai ba boyayyu ba ne. mu dai yanzun mu san ya ya zamu yi da wannan kudin, a sai mata gado da ‘yan kujeru.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Salma dai bata magana, domin har yau gani take ba’a ne duk da kayan da aka kawo masu tsada na lefe, da kudin dinki Naira dubu dari. Sun yanke a cire ishirin tayi dinki, tamanin a
hada da saba’in a sai mata kayan daki da na aiki,
tun dai daga wannan ranar har yau Salma bata
kuma sa shi a idonta ba.
Domin ko da ya kawo kayan lefe bata nan taje cefane, gashi har yau saura kwana goma biki cif-cif!
Tun sassafe ranar Amna ta kira Shatima tana ce masa yau ‘yan gidansu za suje jere can Kaduna. Ya ce, “Ai tuni na ba da makullai ko?” Ta ce, “To honey ai ba wanda yasan gidan ka manta?” Ya ce “Au! Haka ne, to su biyo ta gidanmu sai su dauki kananina Mustapha.” Ya sauko kasa ya shiga gurin Hajiya ya sanar da ita. Ta ce, “To ai ba dan rakiya za’a basu ba, ka dau har da abinci.”
Nan tayi waya in da ake yo musu abincin sha’ani, tasa ayi abinci na alfarma da kaji. Lokacin da suka iso daukar Mustapha har abin sha da na cin an shirya, suka kwasa suka wuce.
Shatima ya ce musu za su ga plat guda hudu duk wanda suke so su zaбa. Na ciki suka zaba wai saboda tsoro. Mustapha dai yasha mamaki, domin sabon aiki yaga an tsiro ma gidan an canja fenti, sannan ga wallpaper irin na zamani an zuba a bangon tun ma kafin kayan su iso guri tsaf.
An zuba kaya fadin su ma kauyanci ne, kayan kicin kuwa irin masu amfani da lantarki abin sai wanda ya gani. Dakuna guda uku kowanne an saka mishi gado na alfarma.
Daidai da kayan bayi abin ba da labari. Hajiya ta ce, “Ni nasan za’ayi haka. Ai harkar manya ba karya.”
Duk a ranar daí Ango yayi niyyar kai ma duk Amaran nashi da ke nan Zaria kudin walima shi da abokanshi. Abu daya ke damunshi yanda bai samu ya fayyace ma sauran Amaren cewa sun cika su hudu ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisa ita ce yake da yakini a kan cewa ta sani domin ta kira shi bai daga ba, sai tayi masa message cewa ya daga wayarta suyi magana, tana son tabbatar da abin da taji Babansu yana fada ma Mama.
Ya ki dagawa sam! Ya sani sarai tana zaman jiranshi.
Gidan su Aliya suka soma zuwa shi da Munnir da wani abokinsu Usman. Cikin sa’a kawarta Aisha tazo ganin lefe, sai suka fito tare. An gaggaisa sannan ya bata dubu talatin ya ce, kudin walima, sannan suka bata katina na daurin aure, sai na dinner din da zasu yi bayan an kai Amarya.
Aliya tayi ta masa godiyar kudi har sai da ya ce, ta bari don Allah. Bayan barin su gurin ne abokan suke yabon halin Aliyan, suka ce daga gani tana da hankali kuma zai ji dadin zama da ita.
Gidan su Nafisa suka tafi. Gabanshi yana ta faduwa. A harabar gidan suka tsaya. Ya kira ta a waya, har sau hudu amma bata daga ba.
Yaje ya kwankwasa kofar falon. Momi ce ta bude. Ya ce, “Kira min Nafisa.” Ta ce, “To.” Sannan ta gaishe shi ta juya.
Sun kusa minti hamsin har ran Shatiman ya soma baci, bata fito ba tana can Mama tana fama da ita a kan ta fito ta ki, sai da taga ran Maman ya baci sannan ta tashi ta dauki dan mayafin doguwar rigar da ke jikinta, ta saka takalmi mara tudu ta fita.
Har ya ce su shiga mota su tafi sai ga ta ta fito kamar tana tafiya a kan kwai. Duk da cewa dare ne, kallo daya za ka gane ba walwala a tare da ita.
Ta gaida su gaba daya a tare, Shatima bai amsa ba illa kallonta da yake yi tare da tunanin me ma zai ce mata? Munnir da Usman suka koma cikin mota. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya cc, “Kudin walima da kati na zo ba ki.” Tayi shiru tana kallonshi. Yaje motar ya ce, “Ku bani katunanta.” Ya mika mata ta ce, “Ka bar shi, ni ba zan yi wata gayyata ba.”Ya ciro kudin ya cc, “To ga kudin walimar ko itama ba za ki yi ba?” Ta ce, “Eh ba zan yi ba.” cikin bacin rai ya ce, “Ok.” Ya wuce ya shiga mota ya ce, “Ku muje.” Nan suka bar ta tsaye sai kuma ta soma kuka.
Tsakin da ya yawaita yi ne yasa Munnir tambayarshi abin da ya faru. Ya ce, yarinyar nan wai ni zata yi wa fushi? Ta ki amsar komai ita ta sani.”
Munnir ya ce, “Nafisa tana kishinka da yawa ne.” Ya ce, “Ai wannan shirme ne ba kishi ba, tun kafin a zo zama zata soma haka?”Usman ya ce; “Ba dai ka ce zaka hadiyi
Gatari ba?” Suka sa dariya. Shi dai Shatima bai
ce musu kala ba. sai da suka hau titi sannan
Usman da ke tuki ya ce, “Ina muka dosa?”
Shatima ya ce, “Muje ku aje ni a gida.”
Munnir ya ce “Salma fa ba za a kai mata ba?”
Ya ce, “Zan kai mata gobe.”
Washegari da sassafe da zai tafi aiki, shi ne ya tsaya a unguwar su Salma. Umar kaninta ya fito za shi siyan kosai yaga Shatima, shi ne ya nufe shi yana yi masa sannu da zuwa.
Ya rusuna ya gaida shi, Shatima ya tambaye
shi, “Salma fa?” Ya ce “Tana ciki.” Ya ce, “Kira min ita, ka ce tayi sauri zan tafi office ne a Kaduna.”
Cikin sauri ya juya ya kira Salma da karfi. Ta fito daga kicin tana cewa, “Kai! Mene ne?” Ya ce, “Alhaji ne a waje, ya ce kiyi sauri yana jiranki.”
Ta kalli jikinta, zanin tsoho ne gashi tana kauri. Tun da Allah Ya hada su yau ce rana ta farko da ta soma kallon jikinta don zata kiranshi.
Inna ta ce, “Ki canza zani mana ga na Hadiza nan a kan kofa da ta manta jiya, ki daura mana.”
Ta janyo shi ta daura ta zira hijabi ta fita. Numfashinta ya tsaya cak! Da ta ganshi tsaye jikin mota sanye da suit masu ruwan toka, idanunshi sanye da bakin gilashi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce “Iso mana, sauri nake yi.” Ta durkusa ta gaida shi, ya ce “Mike muyi magana.” tashi. Ya ciro katuna daga mota ya mika mata. “Ta
“Na daurin aure ne kawai babu na dinner. Sannan ya bata dubu talatin “Wannan koda za ki yi walima da kawayenki.”
Ta ce “Sun yi yawa Yaya.” Ya ce, “Haka na ba sauran.” Ta kalle shi zata sake magana ya ce, “Ki je gida ina sauri ne naga bakinki da magana, lokacin yinta yana zuwa amma ban da yau.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]