[Advertisements⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Bayan ya sa ta ta rufe kofa, ya nufi dakin Aliya yayi wanka yasha sabbin kaya, ya dauki makullin mota ya fita.
Kajin Amarci ya siyo da madara mai sanyi, da
sauran kayan zaki, don ya lura Amna tana son
shan zaki ko ya ce an saba musu da shan zaki.
Kai tsaye gurin da motocin ta suke ya wuce, ya saka tashi. Sannan ya fito da ledojin ya nufi falon Amna. Yana shiga ya kulle kofar, don yasan ba zai fito ba sai gobe.
Dakin da ta sanar da shi cewa nan ne nashi, nan ya nufa. Karan ruwan da ya ji daga cikin bandakin shi ne yasa shi tunanin tana ciki. Sai ma ya ga kayanta da ta cire a kan gado.

A ranshi ya ce, “Wannan yarinyar wanka a gurinta ko kifi sai haka.”
Ya cire hularsa ya ajiye a kan durowar da ke gefen gado. Tana fitowa daure da babban Tawul, ta rufa da karami tana goge jiki. Ya sakar mata murmushi, tare da cewa, “Koma kiyi alwala muyi
wa Allah godiya.” Dan jim din da tayi sai ya ji tsoron kar dai itama bata sallah! Ya ce, “Kin ji ni kuwa?” Ta ce, “Ina tunanin kamar nayia alwala, amma bari in
sake.” Shi ne yaja musu sallah suka yi raka’a biyu, ya dafa kanta yayi addu’o’i kamar yanda ya zo a sunna. Taje gaban madubi zata shafa manta wanda take shafawa in zata kwanta, ya zo bayanta, “Kawo in shafa miki.”
Ta kalle shi ta cikin madubin, ya kashe mata ido daya. Tayi murmushi, “A fuska kadai zan shafa.” Ya ce, “Eh kawo.” Tamkar yana shafa kwai a kan kanta haka ya yi wa fuskar. Ya kalli ledar da ya shigo da ita ya ce, “Ina zuwa.”
Yaje ya dauko plate da wuka da cokali mai yatsu. Ya samu tana saka rigar bacci. Ya ciro kajin da sauran abubuwan ciye-ciye. Ta kalle shi, “Me za ayi kuma? Ba dai cin abinci ba?” Ya ce, “A’a
Www.bankinhausanovels.com.ng
cin kazar amarci zamu yi.” Ta waro ido, dole ne cin kazar?” ya daga mata gira.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Ta shafa ciki, “Gashi na koshi ne da yawa honey.” Ya cire rigarsa farar singileti kar ce a jikinsa, ya ce “Bari in ba ki kadan.” Ta hau tsakiyar gado ta zauna. Ya dauki tiren ya hau shima, yasa wuka ya yanko naman ya tsira da cokali ya ce, “Bude baki.”
Sau hudu ta karba ta ce ta koshi. Ya bata madara, shima kurɓarta daya. Ya sauka yayi shirin bacci. Yana hawa gadon ya ce “To tashi in fada miki abinda zai biyo bayan kazar nan da ki ka ci.”
Ta ce, “Ka kwanta ka fada min.” Ya kwanta, sannan ya dagota zuwa saman cikinshi. Ya kai hannu ya latse fitilar dakin.
Ya fito daga bandaki, ya zo ya sake jan yatsunta. Tashi mana honey kiyi wanka muyi sallah. Da kyar ta sauko ya jirata tayi wanka da alwala.
Shi ne ya ja su sallah, sannan suka koma kwanciya, ya janyota jikinshi. “Jiya kin hana ni bacci.” Ta ce, “Ka hana mu dai Honey.” Cikin shagwaba tayi maganar, suka rufa sai bacci.
Kamar jiya ya shiga dakin kowacce ya duba lafiyarta tare da tambayar bukatarta. Su ukun
Www.bankinhausanovels.com.ng
kowacce tana bukatar Gas don dafa abinci. Salma kuma tana bukatar kalanzir tun da wuri ya ba kowaccen su abin da take bukata.
Salma da Aliya ya siyo musu kayan abinci, kayan miya ne ya ce bai san ina zai samo ba. Ya tambayi Maigadi, ya ce a ba shi ya siyo. Aliya ce ta rubuta mishi kuma ya ba shi kudin mota zuwa kasuwar Kawo.
Da aka kawo ta raba hudu, ta ba da na kowa. Kafın yamma duk ya sallame su. Ranar dakin Nafisa zai kwana, kuma washegari zai koma aiki.
Itama dai yasai Kaji da sauransu kamar dai na Amna. Ya ji dadin darenshi da Nafisa, domin ta kasance mai shagwaba tare da kokarin faranta mishi, kuma da sassafe ta hada mishi abin kari. domin ya fada mata dan hutun da aka ba shi ya kare office zai koma.
Tana rataye da jakar a kafada ta rike wayoyinsa, ta ce “Sweety muje in raka ka mota.” Ya ce, “To.” Suna fitowa barandarta ya ce, “Bari in duba yanda sauran ‘yan uwanki suka kwana.”
Ta dan taba baki, tare da fadin “To.” Dakin Aliya ya nufa, wadda dama tana tsaye a windownta na falo tana hango lokacin da suka fito, kan ya Karaso ta koma cikin uwardaki da sauri.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Taki amsa sallamar har sai da ya nufo dakin da ya san zai same ta a ciki yana kiran “My love!” Ta amsa daga ciki. Ya shiga, ta gaida shi tare da dan yatsina fuska. Ya ce, ” ba dai ba ki jin dadi
Ba
Ta ce, “Na kwana da ciwon ciki ne.” Ya ce, “Shi ne ba ki kira ni ba?” Ta zo ta dafa kafadarsa. “In na taso ka da wannan daren ina za ka neman magani, gashi mu baki ne a unguwar, sannan kuma na tuna kai da Amarya ne zan katse muku
soyayya.” Yayi murmushi, “Komai soyayya ai ciwo ya fi komai.” Ta ce, “Na samu sauki har za ka fita office!” Ya ce, “Eh.” Ta ce, “Allah Ya ba da sa’a, Ya tsare mana kai, Ya saka samo mana halak.” Ya ce, “Ameen.” Ta rako shi har zuwa Barandarta.
Nafisa ta kalli lokaci a wayar hannunta ya dauki tsawon minti tara a dakin Aliya. Ya nufi gurin Salma ya kwankwasa kofar don ya murda ba a bude take ba.
Ya buga sosai sannan ta bude, daga gani bacci ta tashi. Ya shiga ta durkusa ta gaida shi. Ya amsa tare da tambayar kafiyar ta. Ta ce, tana lafiya. Ya mike yana tambayar ta karya kuwa? Ta ce, tun da tayi sallah bacci ya dauketa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “To akwai abinda take bukata?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “To zai tafi office. Ya koma yau. Ta ce, “To Allah dawo.dakai lfy ya bada sa’a.” Har ya fita ya tuna ya
“Yau a nan zan kwana fa!” Shiru yayi yana kallonta yanda tayi tambayar cikin tsoro. Ya ce, “Naga kin tsorata ne.” Ta kirkiro yake, “A’a ban ji tsoro ba, sai ka dawo to.”
Yayi ‘yar dariya,sannan ya fita. Nafisa ta kalli wayar, ya ci minti shidda ya zo zai je dakin Amna. Ya ce, muje tare da na fito zan shiga mota, tunda kin ga motar tana kusa da dakinta. Nafisa ta ce, je ka fito.
Amna ma bata tashi ba, yana tsaye ta bude bayan yayi ta bugu. Kayan bacci ne a jikinta, zai shiga ta rungume shi, suna rungume da juna ya ce, “Zan tafi office.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Ya sumbaci kumatunta sannan ya ce, “Zamu yi waya ko?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “Kin ci abinci?” Ta ce, “Yanzun na tashi, ban san me zan ci ba, in da ka siyo shawarma din nan da nisa?”
Ya ce, “Sai an fita unguwar nan, can cikin gari ne. Shi za ki ci?” Ta ce, “eh.” Ya ce, “To bari in tafi da Maigadi sai ya kawo miki. Allah Yasa dai suna da shi da safe nan.” Ta ce, “Amin.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Leda hudu ya bashi, ya ce ya mika kowane daki. Salma ta yini cikin damuwa da tunani tun da Shatima ya sanar da ita. Duk tsoronta tafi son ta kwana ita daya da ta ya zo dakin.
Da rana ta dafa shinkafa dafa-duka, shirman da Salma tayi ta manta bakinta ne ita daya, ta shirga abincin fal tukunya. Yini tayi ci, bayan ta shake masa kula.
Da dare ma shi zata ci. Karfe shida ya shigo, dakin Nafisa yayi wanka, itama sai da yaje siyo kajin amarci. Yana can ne ma ya ga kiran Amna. Cikin sauri ya daga. Ta ce, “Honey.” Ya ce, “Na’am honey ya aka yi?”
Ta ce, “Ina jin yunwa ne, da rana ma banci komai ba.” Ya ce “Ba akwai danye ba kuma nasa muku Gas.” Ta ce, “Honey indomie kawai na iya dafawa, kuma ta gushe ni, kai kuma ba ka kawo min me aiki ba.”
Ya kasa magana, can ya ce “To bari in zo gidan amma yanzun me ki ke son ki ci?” Ta ce, “Chips.” Ya ce, “Shi kenan.” Leda hudu yayo, ya kuma mika kowane daki.
Lokacin da ya shiga gurin Salma tana zaune cikin kujera sanye take da riga doguwa baka da dan kwalinta. Har kafafunta ta zauna a saman
Www.bankinhausanovels.com.ng
kujera, zuciyarta cike da tsoro, fatanta kada ya ce zai bukace ta, domin duk wautar ta dai tana da labarin abin da ake yi in an yi aure.
Bai lura da ita ba ya ce, “Salma!” Ta amsa, daga in da take ya waiwayo. “Dama kina nan?” Ta sakko tazo ta tsugunna a gabansa. “Gani Yaya.” Ya ce, “Amshi wannan ki kai ciki.” Ta amsa tare da cewa kicin zan kai?”
Ya ce, “Daki dai ki kai tare da plate da cokali da kofuna.” Ta ce, “To.” Da ta aje bata fito ba, sai ta zauna a bakin gado cikin sake-sake. Ya ce, “Salma!” Ta amsa daga ciki. Ya ce, “Zo.” Ta tsugunna a gabanshi. Ya ce, “Kije gurin Nafisa ki ce ta baki jakata ta office.”
Har ta kai bakin kofa sai ta waiwayo, “Yaya dakin da muka ci abi Anty Nafisa din?” Ya ce, “A’a na farkon.” A bakin kofar ta tsaya ta kwankwasa. Nafisa ta fito ta dan bude ta leko.
Ganin Salma sai ta hada rai tayi, mata kallon sama da kasa. Sannan ta ce, “Lafiya?” “Yaya ne ya ce ki ba da jakarshi ta office.”
Ta sake tabe baki, sannan ta juya. Salma da karambani ta shige ciki don kawai tana son ganin dakin. Cikin sha’awa take bin falon da kallo, har ma bata san Nafisa tana miko mata ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai da ta ce, “Dalla ni karbi.” Da sauri ta kalli Nafisa. Cikin ‘yar fara’a ta ce, “Kema Anty dakinki yayi kyau wallahi.” Nafisa ta taba baki tare da fadin “Ni rike da Allah.” Yaya Shatima ya rasa wadda zai aura  mata sai wannan abin?”
Salma cikin sanyin jiki ta amshi jakar ta fita. A zuciyarta kuma tana cewa ita wannan bata san abin arziki ba.” ta shiga falonta bata ganshi ba in da ta bar shi ba.
Ta dora jakar a kan doguwar kujera. Sannan ta leka dakin ta don ta ga ko yana ciki. Daga bayan ta taji sallamar shi ya shigo. Ta waiwayo, dama ka fita ne?”
Ya ce, “Eh.” Ya shiga cikin dakin ya aje kayan hannunshi a kan gado. Ta kalli kayan da na bacci ne da kuma gogaggu kala uku.
Ya ce, “Ina za ki sa min kayan nan?” Ta ce, “Ga akwatuna na nan an kwashe kayan an saka a sif sai waccan bababr ce kadai da kayan da suka min yawa a ciki.
Ya ce, “Wane kaya ne suka yi miki yawa?” Ta ce, “Ga su can cikin akwati, wannan rigar ma ta jikina ai ta min yawa.” Ya kalli akwatin, cikin zolaya ya ce, “Dauko.” Ta ce, “Ba zan iya ba, rannan ma Anty Badi’atu ce ta sakko da ita.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “In daga ki ki dauko?” Taja baya, ba zan iya ba. Ya sauke akwatin a kan gado ya zauna a bakin gadon. Ya bude, kayan cikin ne ya gani. Yayi murmushi tare da daga wata bireziya, yanzun wannan tayi miki yawa?”
Tasa tafin hannunta ta rufe fuska. Ya ce, “To wannan fa?” Ta bude taga pant a hannunshi. Da sauri ta juya baya. Ya ce, cire in gwada miki in tabbatar. Ta waiwayo ta zare ido cikin mamaki.”
Ta ce, “Haba dai!” Ya daure fuska, ina wasa da
ke ke ne! Laifi ne Inna ce ki cire ki gwada in
gani? Idanunta suka yi rau-rau a lamun kuka. Ta ce, “Don Allah kayi hakuri Yaya.” Tamkar yayi dariya amma sai ya dake. Ya ce, “Ban isa ba ke nan ko?” Ta fara buga kafa tana fadin Yaya don Allah kayi hakuri ka ji.” Yanda
take yin abin ya birge shi, dan shi mutum ne mai son shagwaɓa.
Ya tura akwatin gefe, ya hau gadon gaba daya ya mike kafa. “Zan kirga uku in baki cire ba zan zo in cire miki. Kuma duk abin da ya biyo baya ba ruwana.”
Ta ce, “Yaya babu kyau kallon tsiraicin wani, Allah haka Malaminmu ya ce Shatima ya sake
Www.bankinhausanovels.com.ng
daure fuska tamkar gaske ya ce, “Shi Malamin naku har da miji da mata ya ce?” Tayi shiru.
Ya ce, “daya!” Da sauri ta cire dankwalinta ta jefar a kasa, tana kuka kasa-kasa. Ya ce, “Biyu!” Ta ce, “Wayyo! Don Allah Yaya kayi hakuri.” Ya ce, “Ina cewa uku zan taso.”
Ta ce, “To bani wannan din.” Ya wurga mata pant da bireziyar. Ta dauki bireziyar ta zage zif din da ke makata zuwa kafadarta, ta soma saka bireziyar.
Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zaki yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawar ido goma in ce uku.”
Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakamakon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi mata yawa sosai.
Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta ɓari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]