[Advertisements⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

kunnansa daidai bakinta “Me ki ka ce?”
Ta ce, “Tsawona ba zai kai ba.” Ya ce, “Zan taimaka miki.” Ta matso ta dan yanki kasan, ta kalle shi a zatonta zai durkuso ne tasa mishi, sai kurum taji caf! Yayi sama da ita, ya rike kugunta.
Ta kalmashe kafafunta tamkar masu rawar
turanci, sannan ta saka mishi a baki. Gurin ya dauki
sowa. Maimakon ya dire ta sai kurum ya shiga juyi
da ita. Guri kuwa ya dauki ihu da sowa.
Sannan ya sauke ta, kowa ya koma mazauninshi, aka shiga ci da sha. Ba a tashi ba sai sha biyu da mintuna.
Tun da aka dawo daga Dinner Salma ke zaune a barandarta, ga makulli a hannunta amma bata iya bude kofar ba, don tun kafin su Yaya Hadiza su tafi suka kulle suka bata makullin tasa a jaka.

Domin babu wanda yaje a cikinsu. Ranar dama yinin yunwa suka yi tunda ba a kawo musu abincin. ‘yan jere ba, wa ma yasan sun zo wani jere? Shi yasa suka ce ba za su je wata Dinner ba.
Tana shawarar yanda zata yi, taga mota ta shigo. Taga abokan Ango ne suka rako shi, taje kusa da Munnir ta ce, “Yaya.” Ya waiwayo.
“Lafiya ba tun dazu aka maido ku ba?” Ta ce, “Ban iya bude kofar ba ne.” Shatima ya fito a motarsu da ta shigo daga baya.
Munnir ya ce, “Ango kazo ga Amarya ta kasa bude kofa.” Ya iso “A’a, Salma dama tuni kina nan? Ina su Hadiza?” Ta ce, “Sun tafi tunda muka zo wai suna jin yunwa ba za suje ba gurin Dinner.”
Ya ce, “Subhanallah! Da yunwa suka tafi?”. Salma ta ce, “Eh.” Yaje ya bude mata sannan ya ce “Za ki iya kwana ke kadai?” Ta ce, “A’a, ina jin tsoro. Ya daga wayarshi ya kira Badi’atu, ta daga cikin
yanayin bacci ta ce, “Yaya” Ya ce, “Dan fito gani a
nan cikin harabar gida, za ki taya Salma kwana?” Ta ce, “To.” Da ta fito ya ce, “Yanzun daga dawowa har kin soma bacci?” Ta ce, “Na gaji Yaya.” Ya ce, “To ku shiga.” Badi’atu ta ce suje su kwanta don bacci take

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


ji.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tare da Alkalamin
Sai taga Salma ta kwanta da kayan jikinta. Ta ce, “Yaya zaki yi bacci da kaya masu kyau? Zama ki iya bacci da wannan kayan?”
Ta tashi zaune a kan Gadon tare da fadin “Nima duk na gaji ne.” suka bude akwatin kayan ciki hade da na bacci. Ta ciro mata wasu kayan baccin ta ce tasa.
Salma ta dago wasu irin masu shara-shara din nan. Dan wando ne da ‘yar riga. Ta ce, “Yanzun wannan ma sai a sa?” Badi’atu ta ce, “Me zai hana, ran da mijinki ke dakin ki za ki sa.”
Salma ta ce, “Tabdijam! Wallahi ba zan iya ba.” Badi’atu ta ce, “Ke da za ku yi gasa!” Salma ta ce, “Ni ba ruwana.” Ta dago wata bireziya ta ce, “Dubi fa wannan ina zan kaita, duk kayan ciki sun yi min yawa.’
Badi’atu ta ce, “Ai ba a zata Karama ba ce shi
yasa, kuma Yaya bai tambayo size din ki ba ne ko?”
Salma tana dariya ta kalli kirjinta.
“To ni me zan sa ma bireziya a nan, ban fa dade da farawa ba, da kirjina shafe yake. Kawai Anty Badi’atu ki kwasa.”
Badi’atu ta ce, “Wai! Kar Yaya ya ji kina ce min Anty ba zan dauka ba, ki bár su nan gaba sai ki saka, masu tsada ne fa.” Salma dai ta dage sai da Badi’atu
Www.bankinhausanovels.com.ng
ta diba guda biyu pant biyu, don suma din sun yi
mata yawa. Ta ce, “Amma ki fada ma Yaya sai ya sai miki daidai ke.” Salma ta zaro ido “Sai kuma in ce ya sai
min pant!” Badi’atu ta ce, “To ba mijinki ba ne?”
Salma ta ce, “Ni ba zan iya ba.” Haka kayan shafa Salma ta ba Badi’atu damar ta zaba, Sun jima kafin suka hau gado suka yi bacci.
Nafisa tana ta juyi a kan gado, kadan-kadan tana jan tsaki, ranta kuwa wani kunci ne ke damunta. Ta tashi ta sauka a kan gadon tana kallon su Shahida, da sauran su suna bacci.
Ta kalli gurin da Badi’atu take kwance. Yayanta ya kirata. Ina ya tura ta oho. Ta kalli madubi, taga yanda tayi kyau, ga lalle tasha, ban da gyara da aka yi mata irin na Amare, amma yau duk sun tashi a banza.
Darenta na farko, daren da kowace ‘ya mace ke burin gani. Amma Angon yana can gurin wata. Hawaye suka zubo mata. Ranar dai bata runtsa ba sai da sanyin dare ya ratso, sannan ta kwanta bacci yayi gaba da ita.
Ba za ka gane yanayin da Amna take ciki ba. amma dai da ka kalle ta za ka fahimci tana yin
Www.bankinhausanovels.com.ng
nazarin wani abu. Har yanzu bata samu amsar da zata ba ‘yan’uwanta ba a kan Salma.
Domin ita kanta tana bukatar sanin wacece Salma. Kenan ita ma matarshi ce? Ta sani mata biyu suka yi magana duk da ita ne ta uku, kuma tayi iyakacin tunaninta don ta tuno ko ukun suka yi lissafi, amma bata tuna ba. In ko haka ne ya fara karya kenan?
Lokacin da abokan Angon suka shiga dakin Aliya, ita daya ce zaune a falon ta rufe fuskartą. Sun dan yi wasa irin nasu na abokai, sannan suka yi addu’o’i da kuma shawarwari, suka yi bankwana suka tafi.
Bayan sun ajiye mata abubuwa na al’ada. Ya ce, “Gobe fa za ku zo ku sake raka ni wani dakin.” Suka ce “Kayi kadan, mun yi maka wajibin sauran ya rage naka.
Bayan tafiyar su ne yazo ya samu Aliya, “Tashi muje ciki.” Ya kalli kajin da abokanshi suka kawo ya ce, “Wannan kuma ya zan yi da su?”
Ta ce, “Guda nawa ne?” Ya ce, “A’a ka bari kowacce randa zaka shiga gunta kaje a matsayin Ango da kajin ka da abubuwan da ake zuwa da shi na al’ada.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Amma duk wadda ka ba yanzun ka fita daga dakinta zata ji babu dadi.” Ya ce, “Haka ne, amma kwana nawa ya kamata in ke yi a tsakaninku?” tayi dan murmushi, “Wannan ka bari sai da safe in ka tara mu, ko ba za ka yi mana nasiha ba?”
Ya ce, “Zan muku mana, kin san fa har yanzun ban yi ma Amna zancen Salma ba, na rasa yanda zan yi.” Ta ce, “Kada ka damu, insha Allahu za ta fahimce ka.” Suka ci naman kazar sama-sama, sannan ya ce “Muje muyi sallah don godiya ga Allah tare da addu’ar neman albarkar da ke cikin aurenmu.”
Aliya ta ce, “Kash! Ina fashin sallah.” Ta fadi tare da kallon fuskarsa. Ya kuwa canza fuska, sai taji hakan bai mata dadi ba, domin itama a burinta ta zama ita ce ta farko da zai kusanta a cikinsu. Ta sake kallon shi. “Don haka kayi hakuri.” Ya
dan yi murmushin yake, “Haba ba komai, ai ba
laifin ki ba ne.” Ta ce, “Ko za ka je gurin wata daga ciki?”
Ya taso yazo ya rungume ta. “A’a ba gurin wadda zan je, na sani ko dukkanku ma kuna da larurar a yau.” Ta ce, “Ba zai zama haka ba insha Allah. Ya ce, “Na hakura zuwa gobe.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka suka rungume juna suka kwanta. Saboda gajiya, har makara ya yi. Shida ya farka, yayi sallah sannan yayi wanka ya maida kayanshi don bai zo da kaya ba.
Yaga har Aliya ta hada ruwan zafi ta jera kayan karin kumallo, dama har da kayan tea suka shigo mai yawa, jiya da za’a rako shi daki. Ya kalla sannan ya ce, “Bari in leka sauran mutanan gidannan, bai kyautu in zauna yin karin kumallo ba tare da nasan halin da suke ciki ba. Ta ce, “Haka ne.”
Har ya nufi gefen Salma, sai yayi tunanin zata ci masa lokaci da shirmanta, don haka sai ya juya zuwa sashin Amna. Sai da ya kwankwasa sannan wata tazo ta bude.
Ya ce, “Ba ku tashi ba ne ni na tashe ku?” Ta ce, “Mun yi sallah, mun koma ne.” Ta juya zuwa dakin da ta fito. Ya leka dakin da ya ke zaton Amna tana ciki.
Sumayya ya gani tana danna waya. Ya ce, “Har kin tashi sarkin chart?” Tayi murmushi, sannan ta gaida shi. Ya ce, “Ina honey take?” Ta kalli kan gadon “Gata can.” Sannan ta tashi ta fita.
Yabi dakin da kallo, an zuba dukiya mai yawa. Ya kalli kan gadon tana kwance a tsakiyar gadon
Www.bankinhausanovels.com.ng
ta rufe jikinta da bargo, gashin kanta ya sauka a dokin wuyanta, tayi kyau da baccin.
Ya matsa kusa da ita, ya saka yatsun shi na tsakiya, ya kwashe gashin ya maida kan filo. Sannan ya sunkuya ya sumbaci kumatunta. Tayi mika sannan ta sake gyara kwanciya, bargon ya dawo kan cikinta, sannan ta koma rigingine.
Rigar baccinta bata da nauyi, don haka yana kallon kirjinta ta leshin da aka yi kwalliya da shi a kirjin. Tsigar jikinsa ta tashi.
Ya juyo ya fita falo. Sumayya tana kan kujera ya ce, “Ashe tana bacci.” Ta ce, “Eh da ka tashe ta ai.” Ya ce, “A’a bar ta ta huta. Me ku ke bukata saboda karin kumallo?”
Ta ce, “Bari in kira Antynmu.” Ta shiga wani daki ta kira kanwar Mamansu. Ya gaida ta cikin girmamawa, sannan ya ce “Anty dama ina son in ji me ku ke bukata?” ta ce tana zuwa.
Suna da kayan tea da komai, biredi ne kawai. Sai gas da babu bare su soya wani abu. Ya ce, “Gas dole sai rana tayi, amma bari yaje ya kawo musu biredi.” Sumayya ta ce “Anty akwai abubuwa masu amfani da wutar lantarki a kicin din Yaya Amna.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ni dai zan gasa biredi kuma zan soya kwai.” Ta kalli Shatima. “Yaya ka siyo mana me yanka yanka.” Ya ce, “To Sumayya.”
Daga nan dakin Nafisa ya shiga. Kaf! Din su suna dakin da Nafisar take, ya shiga suka yi ta gaishe shi. Ya duba bai ga Nafisar a cikinsu ba. ya ce, “Ina Amaryata?” Suka ce, “Tana wanka.” Ya ce, “Me ku ke bukata?”.
Shahida ta ce, “Dama yunwa muke ji.” Ya ce,
“Akwai kayan tea ne nan?” Momi kanwar Nafisa
ta ce, “Sosai ma, gasu can a store.” Ya ce, “Bari in
kawo muku biredi.” Hamida ta ce, “Yaya Nafisa
kuwa bata cin biredi.” Ya ce, “To fa! Yanzu me zan kawo mata, me take ci?” Momi ta ce, “Ai naga akwai Indomie sai ayi mata.” Ya ce, “To bari yaje ya kawo musu biredi.
In ta fito a ce, yana gaida ta kafin ya dawo. Ya shiga gurin Salma itama sai da ya Kwankwasa kofa. Tazo ta bude, ya kalle ta. Sanye take da kayan bacci, sun yi mata yawa. Sai gashinta da ya sauka a bayanta. Sannan ga abin risho a hannunta tana ta kici-kicin sawa da zabori, tasa daya tana fama da na biyu.
Ya ce, “Mene ne wannan? Ta ce, “Abin risho ta durkusa “Ina kwana Yaya?” Ya ce. ne.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Lafiya. Na ce miki ni ba Yayanki ba ne ko? Yanzun me za ki yi da wannan?”
Ta ce, “Zamu sa ruwan wanka ne, kuma zamu karya.” Ya ce, “Tashi daga tsugunno mana, ba ki da butar jona ruwa ne?”
Ta girgiza kai, “Bani da shi.” Ya ce, “To ai babu kalanzir din da za ki kunna rishon ko?” Ta ce, “Babu.” Ya ce, “Kina da flask din ruwan zafi?” Ta ce, “Bari in duba.” Ta fito dashi a cikin kwalinsa ya ce “Ciro.” Ta ciro, ya amsa ya ce, “Bari in je sai Aliya ta dafa miki. Ina Badi’atu?”
Ta ce, “Tana bacci.” Ya ce, “To ina zuwa.” Yaje gurin Aliya ya bata filas din ya ce, a sa ma Salma ruwan zafi a nan.”
Ta ce, “To.” Ya ce, “Bari in je in siyo musu biredi.” Ya dauki makullin mota. Ta ce, “To amma wanda ba shi da kayan tea ga wannan da su Munnir suka shigo da shi.” Ya ce, “Su duk suna da kayan tea Salma ce kawai.” Ta ce, “To in ka zo sai ka kai mata.
Da yawa ya siyo, kofar Amna ya tsaya ya ba Sumayya ta dibi wanda zai ishe su, itama Shahida ta dibar musu. Sannan ya koma gurin Aliya.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Gashi in za ta kara.” Ta ce, “Nasun nan ma ya yi yawa.” Ta bashi kayan tea har da ragowar kazar da suka ci jiya, ta ce ya ba Salma.
Ya dubeta cikin jin dadi ya ce, “Allah Yasa yanda ki ke bani hadin kai da na zauna lafiya, sauran ma su bani.” Ta ce, “Za su ba ka insha Allah.”
Ya kai ma Salma, sannan ya dawo suka karya suna ‘yar hirarsu irin ta masoya. Da suka gama ya ce bari yaje inda su Munnir suka kwana. Ta ce, “Har da Munnir aka kwana a nan?”
Ya ce, “A wannan dare ina zai koma Zariya?” Ta ce, “To kaje musu da abin kari.” Ya ce, “A’a masaukin da suka sauka akwai gurin cin abinci, nasan yanzun sun ma karya. Kila tare za mu wuce Zariya da su in kwaso kayana.”
Yana gaida Hajiya, Mustapha ya shigo. Ya gaishe shi, Shatima ya ce “Don Allah Mustapha ka hada min duk kayana. Sannan kuma in an gama zirga-zirga ka dauki motar nan tawa ta da.”
Dadi ya rufe Mustapha, ya shiga godiya. Hajiya ta ce, “Kafar yawo ta karu, ai dole kayi murna.” Mustapha yace Ai na huta, in na ari motarki, ko ta Alhajinma, sai a kira ni a ce dawo min da motata yanzun nan.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

One thought on “RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI”
  1. I have study a few of the blogposts on your blog now, and I truly like your style of blogging. I bookmarked it to my favorites internet site list and will be checking back soon. Pls visit my internet site too and let me know your opinion.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]