[Advertisements⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI 

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

dawo. Ka ban tausayi sai naga duk ka fada.”
Ya ce”Ai naso in zo in da ki ke lokacin, Salma ce bata ci abinci ba, na fita na siyo mata.” Gaban Aliya ya fadi. Ta dake ta ce, “Ai da ka kira ni nan ga Www.bankinhausanovels.com.ng
abinci sai yanzu ma na kwashe kayan.” Ya ce, “Tana dakina ita daya ce, ta bani tausayi,
har kusan karfe biyu ina gurinta. Aliya ta sake danne kishinta tace, “Allah Sarki!
Da ka rako ta nan sai mu kwana. Ya ce, “Babu

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

komai, yanzun ma tana ta bacci.” Ta ce “Daya ‘yar uwar tawa fa ta Kano?” Ya ce, “Yanzun zan kira ta, in mun gama waya.”
Ta ce, “To ka shigar da gaisuwata. Ya Nafisa?” Ya ce, “Tana lafiya, da na shiga gurin Hajiyarmu na ganta.” Ta ce, “To Masha Allah.”
Bayan sun yi sallama ne ya kira Amna. Ta ce, “Honey sai yanzun ka tuna da ni ko?” Ya ce, “Kiyi hakuri honey, ban samu sukuni ba. Kina lafiya ke da duk mutanenki ko?”
Ta ce, “Duk muna lafiya. Yaushe zan gan ka ke nan?” Ya ce, “Ai sai su Hajiya sun gama wannan bikin al’adar tasu, kin san wai ba dama in ganku sai an yi budar kai.” itaka Ta ce, “Yau ne za’ayi ko?” Ya ce, “Eh, ba ki Www.bankinhausanovels.com.ng
bukatar komai ko?” Ta ce, “Hajiya tasa an yi mana
komai.” Ya ce, “Shi kenan sai mun hadu?”
Ta ce, “Eh, amma kana tunawa da ni kuwa?” Ya
ce, “Haba honey, ko yaushe kina nan a raina.” Bayan sun yi sallama ya mike ya fita a ďakin, ya nufi gurin abokansa.
Su Hadiza Yayar Salma kuwa jiki babu kwari suka isa gida, sai dai Hadizar ta hana a fadawa Innar don kada ta sake shiga damuwa.
Sun ci gaba da shirin kai kaya a washegari kenan. Su ba su san ma za’a yi wani biki a gidan surukanta ba, sai da aka dauke ta. Sun za ci Kaduna za a kamar yanda ya ce musu lokacin da ya basu makullin gidan nata.
Sun kammala siyan duk abin da suke ganin muhimmi ne a kai mata. gado da kujerunta mai zaman mutum uku, da guda
dai-dai, sun sai katifa da kayan kicin wanda ya sawwaka.
Sun siyo gara, Buhun shinkafa babba, da Taliya katon daya, sai dan karamin garin tuwo na Semovita. Sun hada da Mangyada da su maggi, sannan ta dan samu gudunmawa daga makota, ‘yan kofuna da dai dan abin da ba a rasa ba.
Gidan su Aliya kam tun ana sauran ‘yan kwanaki suka kai mata kaya, don haka gara za su kai mata a washegarin. Sun yi mata kowanne bugu guda biyu, nufinsu daya su kai gidan Amarya daya su kai ma surukanta tare da kwanukan da ake ba dawa bisa al’ada. Www.bankinhausanovels.com.ng
Badi’atu da sauran ‘yan uwa da suke tare da Nafisa tuni sun soma wanka suna sheka kwalliya tun bayan da suka karya.
Shahida ta miko ma Badi’atu waya wadda ta fito wanka tana fadin, “Gashi har an gama yin Decorations din ko’ina da za’a saka mutane.”
Ta amshi wayar tare da cewa, “Na manta ma ina mallakin wata wani kam.” Tana ganin Yaya Shatima ta zaro ido, tun da taga kiran ta tuna ajiyar da ya bata.
Ta daga tare da fadin “Na’am Yaya!” Ya ce, “Kin kai mata kuwa?” Ta ce, “Yanzun zan kara dubawa don bata tashi ba.” Ya ce, “To kije da wayarki, zan yi magana da ita.” Ta ce, “To.”
Ta fita taje kicin, duk babu wani abin kari. Ta shiga gurin Alhajinsu inda aka sauki su Amna. Su kam ga kayan karin nan sun ci naci sun bar na bari. Ta dauki Plate ta zuba dankalin Turawa soyayye
da kwai da naman kaji. Ta dauki wani kofi ta zuba ruwan shayi, ta dauki madara da sauran kayan tea ta dora kan wani tire. Sumayya kanwar Amna ta ce, “Ba ki karya ba Badi’atu?” Ta ce, “Wata bakuwa aka yi.”.
Ta aje can gurin kafar bene, sai da ta zo ta duba Hajiya suna can falonta da kawayenta suna tsara yanda za su gabatar da lamarin. Ta dawo da sauri ta dauka tayi sama.
Tana zuwa ta samu Salmar zaune ta dauki sauran naman jiya tana ci. Badi’atu ta kalle ta cikin tsananin tausayi, ganin yanda idanunta suka yi jajir, sannan
sun kumbura. Ta ce, “Ajiye wannan ki ci wannan.” Salma ta amsa tare da yin godiya. Badi’atu tayi masa flashing sai gashi ya kira. Ta ce, “Na kawo mata, gata ma.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Salma ta amsa. Ya ce, “Salma!” Ta ce, “Na’am!” Ya ce, “Kin tashi?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To ki ci abinci kiyi wanka.” Ta ce, “To, amma ba a zo min da kaya ba, tunda dama yau ne za su je min da kayan can Kaduna.”
Ya ce, “Zan je in anso miki, zan ba Badi’atu ta kawo miki.” Ta ce, “To.” Ya ce, “Duk abin da ki ke bukata ki fada mata.” Ta ce, “To.” Ta ba wa Badi’atu wayar. Ya ce ma Badi’atu don
Allah ta taimaka mata zai je ya kawo mata kayanta
da zata sa. Badi’atu ta ce, “Insha Allahu zata yi.”
Lokacin ya tafi gidan su Salma cikin sa’a dama suna son Auwal ya zo a kira shi batun motar da zata kai musu kaya Kaduna.
Yaya Hadiza ce ta fito da Umar yaje ya sanar da ita zuwan nasa. Suka gaisa, ya ce a bashi kayan da Salma zata saka. Yaya Hadiza ta ce, “To.” Sannan ta ce, “Dama
muna maganar motar kaya za’a tafi ayi mata jerene.Shatima ya ce, “To bari ya je zai aiko kaninshi Mustapha, ko ya kira Auwal ya amshi kudi sai a nemo mota don bai fito da katin shi na (A.T.M) ba.
Badi’atu bata fito daga dakin ba sai da taga Salma ta ci ta koshi ta shiga wanka. Ta dawo ta debi kayan kwalliyarta lokacin ta tambayi ina Hajiyarta? Aka ce mata tana wanka.
Ta ce, “Bari taje an aiketa in ta fito tana nemanta.” Can dakin ta koma inda ta samu ta fito. Ita ta zauna ta tsara ma Salma kwalliya, don haka kawai taji tana son Salman wai tana yi mata kama da wata Fatima kawarta Aminiyarta ce suna JS1 ta rasu. Salma ta ce, “Allah Sarki! Allah Ya jikanta.”
Ya kira layin Badi’atu, ta sauko ta amshi kayan. Leshi ne mara nauyi mai kalar makuba da ruwan madara, ta saka shi, tayi kyau sosai.
Badi’atu ta dauke ta hotuna kala-kala, ta ce “Zan nuna ma Yaya ne don yasan na cika alkawarin da na daukar masa.
Salma tayi ta godiya. Badi’atu ta ce, “To, anjima in za a yi budar kai amma za ki canza kaya?” Salma ta dubeta cikin muryar tausayi ta ce, “Ai ba da ni za’ayi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Badi’a ta ce, “In ji wa? Kuma saboda me?” Salma ta ce “Hajiya ta ce ban da ni.” Badi’atu tayin shiru, don dama taji Hajiyar tana ta fadace-fadace.Mamakin halin da Hajiyar ta canza take yi, don
iyaka saninta da Hajiyarsu ba muguwa ba ce. Ta samu Shatima a can waje Gate yana waya da
Mustapha, wai in ya ciro kudin ya kai gidan su
Salma. Da ya gama ta dube shi da murmushi. “Yaya wai duk cikin su kafi son Salma din nan ne?” Ya ce. “Me yasa ki ka ce haka?” Ta ce, “Naga kafi damuwa da al’amarinta fiye da na sauran.”
Yayi murmushi, “Duk ba za ku gane ba ne. Kin gama abin da na sa ki?” Ta ce, “Eh, bari ma ka gani.” Ta ciro wayarta ta fito da hotunan Salma ta mika mishi.
Yana ta kallon su cikin mamaki. Ya ce, “Amma kin yi editing ko?” Ta ce, “Sam! Ban yi ba.” Ya ce, “Ashe “yar small din tawa kyakkyawa ce.” Ya mika mata wayarshi, “Ki tura min su duka yanzu.” Ta ce, “To.”
Tun sha biyu gidan ya soma dinkewa da manyan mata, don yau ne bikin Hajiyar karo na farko da zata aurar da danta, kuma zai auri mata uku, don ta ce su ta sani bata san ta hudun ba.
An tsara gurin zaman amaran guda uku sai gurin da ango zai zauna da abokansa guda biyu. Sai rumfuna wanda jama’a za su zauna.Tuni wadanda aka baiwa kwangilar abinci sun kawo tare da wadanda aka dauko haya don su raba abinci, su ne za su ba kowa har abin sha. Sun tsara budar kan za’a fara shi karfe daya, don haka aka ce kowacce Amarya ana son ta shirya kafin lokacin. stil Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiyar da kanta tasa aka kawo mai kwalliya. Amna a ka fara yi mawa, sannan Nafisa. Lokacin da ta zo gurin Aliya ta samu suna shawarar siyo mata audugar mata don taje alwala taga al’ada.
Sai da ta gyara jikinta bayan Aisha ta fita ta siyo mata sannan aka zauna zaman yi mata tata kwalliyar. Duk kayan da suka saka a lokacin Hajiyar ce ta bada aka dinka musu tun kafin zuwan ranar.
Duk da ba a auna su ba, doguwar rigar ta zauna
ma kowa har tana jan kasa, kowace da kalarta. Koda
yake sai da sauran suka zaɓa sannan aka kawo ma
Aliya.
Masu kidan ‘yan kasar Mali ne aka dauko, guri dai ya tsaru sosai. Mc abin magana ya soma fadin “A fito da Amare don ayi musu budar kai.”
Salma tana jiyowa tamkar ta fito kallo. Lokacin ne Badi’atu tazo dauko ma Ango wasu kayan shi da zai sa shi ma. Ta ce da Salma “Ki fito kiyi kallonki, don Hajiya tana fama da mutane ba za ta gan ki ba.”Ta ce, “In wani ya fada mata fa?” Ta ce, “Ai babu wanda ya sanki bare ya fada mata din, ni kaina ai sai da Yaya ya aiko ni sannan na ganki.” Haka tabi Badi’atu cikin fargaba. Da suka fito
harabar gurin shagalin bikin ta ce, ta shiga kujerun
tsakiyar gurin ta zauna. Ta shige ta saje da Jama’a.
Amna ce ta soma fitowa rigarta kalar bulu mai haske, an sha dogon takalmi, fuskarta rufe da wani mayafi da ke manne a jikin rigar.
‘Yan’uwanta ke yi mata jagora suna fesa mata abin kamshi har izuwa kujerarsu. Can sai ga Aliya itama, tata rigar koriya amma komansu iri daya.
Da suka zauna kuwa zai yi wuya ka gane wannan wace ce, wannan wacece a cikinsu. Nafisa ce karshen fitowa ita kuma tata kalar siminti, sun yi kyau amma ita da ta zauna kasan ita ce karamarsu.
Me abin magana ya ce, “Kai! Wannan Ango dangata ne, nan da shekara me zuwa ka cike ta hudu, duk shekara ka dinga kwasar jarirai guda hudu.” Aka sa dariya. Ya ce, “Yanzun ango muke jira, kafin ya iso ina ‘yan rawar nan su nishadantar da mu?”
Nan fa ‘yan Mali suka shiga rawarsu mai ban sha’awa. Salma daga inda take zaune tana jin wasu mata suna musu. Wata ta ce, “An ce fa matan guda budu ne.” dayar ta ce, “Surutun mutane ne, su ukune. Ya dai so yin ta hudun Hajiyarsa ta hana.” Salma a ranta ta ce, “Gani ni ce ta hudun. Www.bankinhausanovels.com.ng
Can Ango ya iso da gayyar abokai. Shatima ya yi matukar kyau cikin shaddar shi Gizna mai ruwan zuma. Hula da takalmi masu ruwan kasa kalar zaren Hula da aikin.
Salma har mikewa tayi tana kallonshi, ya birge ta sosai. Sai da ‘yan bayanta suka ce “Zauna mana, kin tare mana.” Sannan ta zauna tana sauraron yanda matan gurin ke koda haduwar Angon.
Shi kan shi mai abin maganar fadi ya ke, “Ga kasaitaccen Angon mu nan ya iso, kyakkyawan Ango ya iso sauran abokan suka je inda aka tanadar musu. Shi da guda biyu suka zauna a inda aka tanadar musu. Nan fa aka soma shirin budar kai, wata kawar
Hajiya aka kira ta bude taron da addu’a, sannan aka
bukaci Ango ya zo ya bude kan wadda ya zaba a
uwargida. Abokanshi suka rako shi, ya zo gabansu ya tsaya. Nan ya dabirce domin ya kasa gane Aliya. Ya gane Nafisa don bata kai su girma ba, ya dan yi shiru, ya
kuma tsura musu ido yana son gano Aliya. Da bai gane ba sai ya ce, “Aliya!” cikin sauri ta amsa, Ya ko sa hannu ya daga ‘mayafin fuskarta. Nan aka dauki tafi da guda. Aka ce danginta su zo su nuna cewa ita ‘yar dangi ce.
Nan fa dangi suka yi tsuru-tsuru tunda ba su san da wannan irin lamarin ba. Abin da ke hannun su suka zo suka zuba mata, ba ma sabbin kudi ba ne, mutane sai kunkunai suke yi.
Aka ce yazo ya bude ta biyu, ya zo ya bude Amna. Ita ma aka yi guda aka ce dangin ta su zo su fidda ta. Ruwan kudi suka shiga zazzage mata sabbi fil! Haka Nafisa.
Salma da ke kallon ikon Allah ta ce, “Allah na gode maka da kasa Hajiya ta ce kar in fito, da wa zai zo ya fidda ni?”
Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda.
Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]