[Advertisements⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Mon. Sep 26th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba.
Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya ce, “Sosai ma, za ki sammin?”
Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce, “Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya.

Bayan ya gama da abincin kuma ya jinjina mata. Nafisa ta sha mamaki a kwanciyarsu, yanda ya tara da ita sau biyu a daran. Sannan da safe da yake Lahadi ce yana makale da ita sai gurin tara sannan ya tashi ya yi wanka.
Tayi ta tabara wai ya gaji da ita ba za ta iya tashi ta shiga kicin ba. Ya ce “Zauna in shigar miki.” Shi ne ya hada musu abin kari, tayi wanka, tayi kwalliya suka karya. Ya ce, “To bari ya je ya duba lafiyar sauran Jama’ar gidan.
Nan ne ta ɓata rai, wai haka jiya ai ita bai zo ya duba ta ba, kuma ta fito taga ya dauki Amna. Nan take ya dauke ta da yake Nafisa irin matan nan ne marasa kiba, sai dai tana da dan tsawo. Amma sanfurin jikinta, sanfuri ne irin wanda zai yi wuya tayi kiba ko me zata ci.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Ya ce, “To dauka dai gashi na dauke ki ina zan kai ki? Ranta yayi dadi ta ce, “Ka kai ni dakina.” Ya dire ta kan gado, a kunne ya rada mata wata magana da ta sata fashewa da dariya, tare da saka kanta cikin filo. Yayi mata cakulkuli ya fita ya barta tana dariya.
Sha biyu ya gani lokacın da ya kalli agogon falon Amina. Lallai yau hira tayi dadi tsakanin shi da Nafisa. Ya samu Amna zaune tsakiyar gado
Www.bankinhausanovels.com.ng
tana waya da ‘yan gidansu. A yanayin maganarta ya gane cewa ‘yan gidansu sun sani, ta fada musu kenan.
Ya zauna suyi da wannan, wannan ya kira. Bayan ta gama ta dubi Shatima, “Su Mom suna gaida ka.” Ya ce, “Ina amsawa. Ya jikinki?” Ta ce, “Naji sauki.” Ya ce, “To kin yi karin kumallo?” Ta ce, “Eh, su fa suka tashe ni da kiran waya. Yanzu kam dole in tashi in yi wanka in karya don Direba yana hanya zai zo mu tafi.”
Cikin mamaki ya ce, “Ina?” Ta ce, “Gida mana! Dad zai sa a duba ni na musamman. Shatima ya ce, “Ba ki fada musu cewa an duba ki a nan ba?” Ta ce, “Na fada musu, ka san Dad baya son wasa da lafiya.” Ta fadi tare da sauka ta nufi bayi.
Shatima yayi shiru kanshi a daure, lallai wata
sabuwar matsala kuma zata kunno kai a gidan shi.
Shi ne mijinta shi ya kamata a nemi izininsa kafin a fada mata, shi ne ya kamata ya fada mata cewa Dad ya ce za ki je Kano a sake duba lafiyarki, amma sai gashi ita ce take bashi labari, babu wani neman izini. Jiki babu karfi, ya shige zuwa gurin Aliya. Yanayin da ta ganshi taso taji ko menene, amma ta
Www.bankinhausanovels.com.ng
san ba zai fada ba. Haka Salma duk shirmenta sai da ta lura cewa yau din yana cikin damuwa.
Domin taga be tsokane ta ba. Ya dai miko mata kudin nama. Ta ce, “Me zata dafa?” Ya ce, “Tayi abinda take so. Gaba daya sai ya ji gidan yayi masa kunci. Dakin Nafisa ya nufa ya dauki makullin mota ya fita.
Shi kanshi bai san ina ya dosa ba don yana bukatar shawara. Titin da zai kai ka filin bajakoli nan yasha kwana ya tsaya, saboda akwai karancin zirga-zirga a titin. Ya kifa kanshi a kan sitiyarin motar.
Kamar minti daya ya dago, ya dauki waya ya shiga kiran layin Munnir. Babu jimawa Munnir ya daga, tun daga gaisuwa Munnir ya fahimci akwai matsala. Ya ce, “Ya ya abokina, naji muryarka wata
kala?” Ya ce, “Akwai matsala.” Ya karanto mishi
komai. Munnir ya ce, “Tabdi! To ai tun da wuri
zaka yi maganin wannan matsalar ba sai ka bari
tayi girman da zaka kasa magance ta ba.”
Shatima ya ce. “Ta ya ya? Ni bana son ne a ce daga aure dududu ko wata biyu ba mu cike ba amma na soma kuno da matsala.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Munnir ya ce, “Kai da ka ke da basira ma, kayi kokari sosai fa, da harka tara mata guda hudu zuwa yanzun babu wata matsala ko wani korafi.
Mace daya ma in ka aje in ba a yi sa’a ba kafin kuyi wata daya makota sun soma jin ku.” Shatima ya ce, “Ai kaina ya kulle, basirar tawa duk ta toshe, ka riga ni aure dai, ka san kuma yanda kowane Maigida yake takama da ikon gidansa.”
Munnir ya ce, “Haka ne.” Shatima ya ce, “To sai a ce an tauye maka wannan ikon.” Munnir ya ce, “Abin da yafi kawai ka cije ka hana, ka ce ba ka bada izini ba, nasan dai za a dan samu fushi da sauransu kayi lallashi daga baya. In ko ba haka kayi ba, tabbaci hakika matsalar ta samu gindin zama.
Shatima ya ce, “Haka ne, bari in koma gidan kawai da na fito ne nayi fushi a kan in sun tafi suma wuce Kano don ni.” Munnir yayi dariya. “Ai ka tsaya a namijinka nawa.”
Shatima ya ce, “Har ina son in kira Hajiya itama in ji ta bakinta.” Munnir ya ce, “Kar ka sake kayi wannan kuskuren, domin zaka yi da na sani a gaba. Bari in fada maka wata magana abokina, duk rintsi kar ka sake ka sako iyayenka a cikin abin da ya shafi matsalar gidanka.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Na farko zaka jona raini tsakanin Mahaifiyarka
da matarka, domin ka san suma iyayenmu sai a hankali, basa so a ce kaza laifinmu ne, don haka sai kaga sun dora mu kan shawarar da mu zamu fitamma zamu cutar da iyalanmu.
kuma kayi rashin sa’a a goyi bayan matar kai kuma kiri-kiri ka dinga cutuwa. Don haka kar ka sake ka zama mai kai matsalar cikin gidanka ga Mabaifiyarka, shi ke haddasa irin rikicin nan na tsakanin sirika da sarakuwa, wanda har yanzun an kasa cimna nasarar kawo karshen wannan lamarin shekaru masu yawa.
Kawei abokina ka zama wanda kullum iyalansa suke ganin girman darajar iyayensa. Su kuma iyayenka kullum kana fada musu labari mai kyau, mai faranta rai daga iyalansa.
Kai ko wata ce cikinsu ta kai kararka gurin Mahaifiyarka, in kaje kar ka ce ita ce ta min kaza da kaza, ka ce ayi hakuri zaka gyara.”
Shatima ya ce, “Amma dai na gode da wannan shawara, in Allah Ya yarda zan kiyaye. Shi yasa a ka ce me shawara aikin sa baya baci, sai dai asirinsa ne a tone.” Suka sa dariya, sannan suka yi bankwana kowa ya kashe waya.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya aje mota ya nufi dakin Amna. Tana zaune a kan Dining tana cin kwai da Tea. Ya kalleta, “Sai yanzun ki ke karyawa?”
Gira ta daga masa alamun “Eh.” Ya ce “Me yasa? Ki daina wasa da abinci ba fa ke daya ba ce yanzu.” Ta ce, “Na gama hada abin da ni ke bukata ne, kar ya zo ya yi tajirana, ban dauki kayan sawa ko daya ba, don ina da kaya a gida a dakina. Ko lefena ma yana can…” Ya katse ta da cewa, “Ina wai za ki je ne kina ta fadin kar ya zo ya yi ta jiranki.”
Ta cc, “Sau nawa zan fada maka cewa Dad ya ce a zo a tafi da ni.” Ya ce, “Amma Dad din bai fada min ba. Ya za ayi ki tafi ba tare da neman izinina ba
Cikin mamaki ta kalle shi ya wani hade rai. Ta ce, “Dad dina fa na ce, ko ba ka ji da kyau ba ne?” Ya ce, “Naji ki sosai, amma tafiyarki kiran Dad din naki ikona ne ba ikonsa ba, don haka bisa ikona babu in da za ki je, ki kira shi direban a waya ki ce masa ya juya.”
Ta mike a fusace, “Shatima kana son ka ce min za ka hada kanka da Dad dina? Shi ne fa ya haife ni ya raine ni, ya sani Makarantu mafi tsada a in da muke, har waje ya kai ni a can ka ganni ka ce,
Www.bankinhausanovels.com.ng
kana sona. To don Allah ka dawo cikin hankalinka bana son mu samu matsala, don… ihun murna da Summy ta shigo da shi, shi neya katse Amna daga zafafan maganganun da ta
tanada don fesar ma mijin nata. Ta rungume
kanwar tata, tare da nuna murnar ganinta. Sumayya ta kai hannu ta shafi cikin Amna tare da fadin “Na riga Dad taba Baby.” Amna ta saki dariya tare da tambayar ko sun yi muhawara ne? Sumayya ta ce “Ai ba su san na biyo dircba ba, domin Dad yacd babu wanda zai fara shafa Baby.”saishi
Amna cikin dariya ta kalli Shatima, wanda ya harde hannu yana kallonsu. Ta ce, “Honey dubi son kudi irin na Summy. Bai ce komai ba, Sumayya ta dan risina “Ina yini Ya Shatima, ban ganka ba fa.” Ya ce, “Ai ba za ki ganni ba, idonki ya rufe.” Suka yi ciki suka bar shi nan tsaye.malala
Kafın yayi wani tunani har sun fito, me aikinta dauke da dan karamin akwatinta. Sumayya da me aikin suka yi gaba, bayan ta ce “Yaya har da kai zamu?” Ya ce “A ‘a ina da office Summy.” Ta ce, “Yau Sunday.” Ya ce, “Gobe ni ke nufi
nima.” Amna ta kalle shi, “Honey sai mun yi
Www.bankinhausanovels.com.ng
waya.” Ya ce, “Za ki tafi ba da izinina ba? Za ki tafi cikin fushin Allah da tsinuwar Mala’iku?”
Amna ta ce, “Ni ban gane zantukanka ba, in ka gama fushin zamu yi waya.” Ta fice abinta. Bai fito ba har sai da ya daina jin sautin motarsu. Ya fito ya kulle dakin ya nufi dakin Nafisa.
Kan kujera yaje ya zauna ya zabga tagumi. Nafisa ta zo ta zauna kusa da shi, ta dafa shi. “Lafiya kuwa?” Shatima ya ce, “Kanshi ke ciwo.” Ta ce, “Gashi babu magani a gidan ko za’a aiki direba ne ya siyo?” Ya girgiza kai tare da lumshe
ido. “Gajiya ce da kai-kawo, in ya dan huta zai daina.” Ta rage TV sannan ta ce, “In baka guri ko?”
Ya ce, “Ta zauna.” Ya janyo ta jikinshi suka yi shiru. Yana ta son ya danne bacin ranshi, yana karanta ma ranshi cewa ga wasu matan nan yana da su, me zai sa ya damu kansa da bakin ciki don ta tafi? Amma duk da haka ya kasa.
Ya mike zumbur! Nafisa ta bi shi da kallo. Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikinshi zuwa shadda. Yasa hula da takalmi, yana saka turare Nafisa ta shigo. Ya ce, “Zariya zan je.” Ta ce,
Www.bankinhausanovels.com.ng
Lafiya kuwa?” Ya ce, “Lafiya lau.” Ta ce “To sai ka dawo.”
Ya leka dakin Aliya, ya ca “Beri ya shiga Zariya ya dawo.” Ta ce. “Allah ya tsare hanya.” Ya isa gun Salma. Tana jin ya ambaci Zariya ta daka tsalle ta ce, “Yaya in zo muje?” Sai ya ji wani mugun bacin rai ya taso masa tamkar ita ce Amna.
Ya shigo rai bace “Ina za ki zo muje? Don na ce za ni Zariya za ki ce ki zo muje, ni sa’anki ne? kin san me zan je yi ne? in ki ka kara yi min irin wannan sai na miki dukan tsiya!”
Salma ta tsorata iya tsorata, jikinta sai kar
karwa yake, tana mamakin dama haka Shatima ya
iya fada? Tsaki yaja sannan ya fita. Tayi ta kuka,
Tsonsa ya darsu a zuciyarta.
Kai tsaye gidan su Munnir ya nufa, don ya kira shi cewa ga shi nan zai shigo Zariya ina zai same shi? Ya ce, Gida. A kofar gida suka tsaya don ya ce ba zai shiga ciki ba.
Ya ba Munnir labarin yanda aka yi da yaje gidan. Munnir ya ce, “To fa! Ai shi kenan tunda an riga an yi.” Shatima ya ce, “Kar ka ji yanda raina ke baci, ni kaina ai zam fi so a ce suna kusa da ni
Www.bankinhausanovels.com.ng
ina ririta cikina. Amma nayi alwashi a zuciyata ba zan je ba har ta dawo.”
Munnir ya ce, “In kayi haka ba laifi ba ne, amma kar kayi. Ka kira waya kuma kaje. Ta yiwu su basu da ilimin sanin mahimmancin aure, ko bambancin da ke tsakanin miji da kuma iyaye. A hankali za ka ke nusar da ita, har ta gane. Kai
kuma ka kwantar da hankalinka, ka sani ma ko
cikin sauran wata na da cikin?”
Shatima ya ce, “Nayi ta kokarin in cire abin a raina, amma na kasa.” Haka dai Munnir yayi ta ba shi shawara kafin suka rabu. Yaje ya gaida su Hajiya, take tambayarsa “Lafiya da yamma?” Ya ce, “Lafiya lau, yaje gurin Munnir ne akwai abin da suka yi.”
Ta ce, “Ina mai jiki fa, laulayi da sauki?” Ya ce, “Ta ma tafi gida dazun.” Hajiya ta ce, “Gida kuma?” Shatima ya ce, “Eh, ai za su dubata na musamman ne.
Hajiya tayi dariya, “Kadan da aikin masu hali, shima dan zai ga gata.” Shatima dai ya ce, “Umm!” Ya mike yayi mata sallama.
A hanya yayi Magriba. Koda yazo yayi fakin ya jima cikin mota yana takaici kafin ya fito. Har

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

One thought on “RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]