[Advertisements⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

yunwa ga fuskarki ma duk a kumbure sai ka ce kin ci kuka?” Nafisa tayi rau-rau tare da fadin “Hmm! Bari Anty Maimuna, wallahi ina cikin wani hali a gidannan. Sai da nayi ta yiwa Mama mita a kan wannan auren ta ce ba haka ba, gashi yanzun tun ba a je ko’ina ba bakin ciki zai kashe ni.”
Anty Maimuna ta zaro ido, “Fada min abin da ke faruwa don Allah, ke da mijin ko ke da kishiyoyi?” Nafisa ta soma kuka, “In su ne akwai wadda zan daga ma kafa ne? shi ne da kansa. kullum in dai yana dakina to fa sai sanda yaga dama zai dawo, in yi kwalliya in ta jiransa a banza.
Karfe shida fa yake dawowa, amma ni jiya sai sha dayan dare. Nayi magana ya shiga fada min maganganu, har da yin yaji yana kwana a falo.
Kuma gashi babu sirri, da safe yaje ya barbada ma matansa komai.” Ran Anty Maimuna ya baci, ta ce “To mene ne na zuwa ya fada musu don yaja miki raini?”

Nafisa ta ce, “Hmm! Ni yanzun ban san ma me zan yi ba wallahi.” Anty Maimuna ta ce, “Muje kicin din.” Suna girkin tare tana ci gaba da karanto korafinta.
Anty Maimuna ta ce, “Gashi can nazo miki da wasu sirrika na mata, wata ke kawo wa barikinmu daga Maradi (Nijar). Kayanta masu kyau ne sosai, don akwai wata kusa da mu, mijinta kwallon dan neman mata ne na gaske, gata da yara biyu, amma baya ba su abin kirki, ba fa karamin Soja ba ne.
Ai ko da na hada ta da matar nan, kin san Allah yanzu baya wannan yawon, kuma duk hakkinsu da ke wuyanshi yanzun yana saukewa, har da mota ya sai mata yanzu.”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Nafisa cikin fara’a ta ce, “Ai ko zan ansa.”
Anty ta ce “Amma fa suna da tsada, Allah Yasa
dai kina da kudi.” Nafisa ta tabe baki, “Ina zan ga
kudi? Kin san Allah sisi bai bani ba, ban san suba”
Ta ce, “Zan biya miki wannan, gaba na san za ki zo da kudinki.” Nafisa ta ce, “Nawa ne kudin?” Tayi dariya tare da fadin “Kyaji in lokaci ya yi.’ Nafisa taji duk kuncin da ke ranta ya kau, sannan taji tana jin yunwa, dama dai burinta ta zama ‘yar gaba-gaba a gurinsa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Daidai wannan lokacin Salma ta fito gurin Maigadi zata bashi sako. Tana jin kunyar aiken dattijon wanda tasan zai haifi mijinta ma bare ita. Ta risina.
“Baba dama sako ne zan baka.” Ya ce,
“Alhajin ya fada min. Ta mika mishi dubu daya, “Kubewa danya ni ke so da kuma nama.” Ya ce, “Kubewa ta nawa?” Salma ta dan yi shiru, bata san ta nawa zata isheta ba, don haka sai ta ce bari in tambayo Anty.”
Ta samu Aliya tana kallo, ta ce “Anty kubewar nawa zata ishe mu ni da Yaya?’ Aliya ta ce, “Ta dari daya ma kacal ta isa, yau kuma tuwo za ki yi?”
Ta ce, “Ya ce yana son cin tuwo ne in yi
mishi.” Aliya ta ce, “Lallai kuwa, sai ki dage kiyi
shi me kyau yanda zai ci.’ Salma cike da wauta ta
ce, “Hala ya fada miki bai taba cin abincina ba?”
Aliya ta ce, “Ya fada min wai ba ki iya girki ba.” Ta fada cike da son tura ma Salma haushi. Salma ta saki dariyar wauta. “Ai yau zan bashi mamaki, zan yi tuwon da zai yi santi.
Aliya ta taba baki, a ranta ta ce, “Wannan sokuwa ce, to sai ya ci tuwon in gani.” Ta ce, “In
Www.bankinhausanovels.com.ng
ko haka kike so sai ki sa kifi, kubewa danya tafi dadi da kifi.”
Salma ta ce, “Haba?” Aliya ta ce, “Allah kuwa.” Salma ta ce, “Dama na gaji da cin nama. Kullum sai na sa kilo daya a dan abincina, kuma baya ci.” Aliya ta ce, “Ai gashi nan kin soma kyau.”
Salma ta ce, “To bari in je in sa ya siyo min da kifin.” Aliya ta saki dariya bayan tafiyar Salma ta ce, “Shashasha. In ni ce ke bani da da, bakina ni kadai kullum a bani dubu daya ta kilon nama ai tarawa zan.
Bai zama dole in ci ma nama kullum ba. Amma ba zan fada mata ba tayi ta dirkar namanta. Ta ba Maigadi kudi, ya siyo mata kifi da kuɓewa.
Da ya dawo sai ya kawo mata kifi busasshe da kubewa, ya kuma bata canjin dari uku. Ya ce, ta ce kayi na mota Baba. Ya ce, “Eh har ma na sai goro na ashirin in nayi canji zan ba ki.” Ta sake daukar Naira dari ta ce, “gashi Baba ka kara, wancan ma ka bar shi.”
Ya ce “To na gode.” Ya amsa. Har zata wuce ya ce, “Hajiya za ki ga na siyo miki kifi busasshe, Maigidan naku ba ya son danye. Domin waccan satin , Hajiya din nan ta karshe.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Bani in sai mata.” Sai Alhaji ya ce, “Kada tayi abinci da danyen kifi don ba ya so.
Salma ta ce, “To’na gode Baba.” Ta wuce ciki ta koma aikinta. Ta nutsu sosai ta zauna a gaban girkinta, ta gama ta kwashe a bakar leda guda biyu ta sa a kula.
Sai ta saka sauran ta kai wa Maigadi, don kullum ita ce kadai ke kai mishi abinci, sannan ta dumama abincin ta na jiya ta taci.
Da yamma tayi wankan ta tasa leshinta na akwati, don sabbin kayan ta ke ta mirtsika tunda ba a sako mata kayanta na gida ba, dama sun tsufa.
Sai da yayi Ishsha ya shigo gidan don yaje yayi aski. Yana shigowa ya wuce wanka. Da jallabiya ya zo ya zauna zaman cin tuwo, tana budewa ta juye a plate. Ya ce, “Iye! Lallai yau zan ci tuwo.”
Ta ce, “Naga kullum nama shi ne nasa maka kifi.” Cikin sauri ya ce, “Kifi?” Ta ce, “Bushasshe ne fa.” Ya ce, “Amma miyar bata yi karni ba dai ko?” Ta ce, “Har citta nasa don kada tayi karni.” Ta bude jikinta a sanyaye.
“Ci kaji kuma.” Ya shaki kamshin, bai ji karni ba, don haka ya ce “To ba ni cokali.” Shi kanshi ya ji mamakin tuwon da ya ci. Tare suka ci da Salma har da suka rage ya ce tayi masa dumame da safe
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Dama kana cin dumame?” Ya ce, “Ni da dumame nasan dadin tuwo ma, gidan Kaka in na kwana lokacin ina dan makaranta Kaka take yi min, sai ta ce dumamen gata, tasa min man shanu har da yaji.”
Salma tayi ta dariya “Nima ina son manshanu. Ya ce, “To zai siyo muku.” Ta ce, “Ka ce zamu yi maganar zuwanmu Zariya.” Ya ce, “Bari in kira Auwal ya kai ma Inna ku gaisa, shi kenan?”
Ta ce, “Allah Sarki, ka ce min zan je.” Ya ce”Ban ce haka ba fa, na ce ne in na dawo zamu yi maganar. Ta ce, “To yaushe za ni?” Cikin shagwaba take yin maganar. Ya ce “Sai kin yi kiba tukuna.” Ta ce, “Don Allah Yaya ina son ganin Yaya Hadiza ma.” Ya ce, “To ki bari sai kin kara kyau.
Ta ce, “Ya za ka gane na kara kyau?” Ya ce, “Ai ina kallonki kullum.” Ta ce, “Me na kara?” Yace “Haske kadai ki ka kara, sai fatar ki da ta soma murjewa, Ta tashi ta dauko dari biyun ta ce, “Gashi canjin ka na tuwon.” Ya ce “Har da canji?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To ki aje min.” Ta ce, “To.” Ta tashi taje ta aje.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Baccin Amna ya soma damun Shatima, domin yau da ya ke dakinta ma baccin take kwasa babu alamun zasu yi wata hira, shi kuma yana da bukatarta.
Yayi ta tashinta da kyar ta tashi zaune tana zuga hamma. Ya ce, “Amna!” Ta dube shi idanu lumshe, ta ce “Umm, don Allah Honey bacci nake ji.” Ya ce, “Amna, ki tashi don Allah.”
Ta kara cewa “Please, ka bar ni mana.” Ya ce, “Allah sai kin tashi.” Ya girgizata. Ta tashi, “Honey kaina ciwo yake yi, in ban yi bacci ba.” Ya ce, “To kin ci abinci?” Ta ce, “Bana jin yunwa, sai bacci.”
Ya ce, “Kai ki tashi muje asibiti.” Ta ce, “Ni
lafiyata lau, bacci ne kawai matsalata.” Ya bar ta
yazo ya gama duk abin da zai yi kafin ya kwanta.
Sannan yaje ya jata jikinshi ya kwantar suka ci
gaba da bacci.
Da kyar yasa ta tayi sallar Asubahi, don haka ya soma tunanin lallai babu lafiya. Ya kira Aliya a waya da safen yana tambayarta me yake saka mace yawan bacci? Aliya ta ce, “Dalilai da dama, ciki har da shigar ciki.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce “Wacece?” Ya ce, “Amna ce, yanzun ya za ayi a gane?” Ta ce, “Gwajin fitsari, tayi a wani abu ka kawo in gwada.”
Da yake ranar Asabar ce ba shi da aiki, bai ko fito gaida saura ba, yana dakin ya sata gaba yana kallo “An ce tana da ciki.” Sha daya ta farka da yunwa, ya ce tayi wanka taji karfin jikinta. Ya ce”Me za ta ci?” Kafin ta fito yasa me aikin ta tanadar mata. tana ci zuba mata ido yayi. Ta ce, “In za ka ci muci mana.” Ya ce, “A’a ki ba babyna ya koshi.” Ta saki dariyar da ta sa ta ta kusan kwarewa.
Ta cc, “In ji wa?” Ya ce, “In ji masu ilimin abin. Yanzun ma fitsari za ki bani in kai a gwada. Ta ce, “Wa zai gwada?” Ya ce, “Aliya kin san Nurse ce. Ta ce, “Wace ce Aliya kuma?” Ya ce, “Ta dakin farko.”
Ta tabe baki “Oh, dama a nan gidan take? Ya ce, “Eh.” Ta ce, “Cikin matanka?” Ya ce, “Eh.” Ta girgiza kai “Ba wadda zan ba fitsarina, don ni ba tsararsu ba ce. Kuma bana dauke da wani ciki domin lokacin al’adata bai yi ba bare in tabbatar. Abin da na sani bacci lafiya ce, ina rama baccin da ban yi ba ne a baya lokacin ina Makaranta, da kuma lokacin biki.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayi murmushi, “Shi kenan muje asibiti.” Ta ce, “Wane irin asibiti, ba zan je ba.” Ya ce “Shi ke nan.
Aliya tayi ta damuwa tana son jin me ake ciki da batun cikin Amna, ga na Nafisa. Koda ta kira Shatima cewa taji shiru bai kawo fitsari ba. Ya ce, “Ashe babu komai ta bar shi kawai.”
Suna cikin hira ta gama cin abinci, sai taji zuciyarta na tashi. Ta ce, “Honey zuciya tana tashi, naci abinci da yawa.” Ya ce, “To kin taba jin haka?”
Ta ce, “A’a sai a ‘yan kwanakin nan. Abin kamar wasa Amna ta shiga bandakinta tana sheka amai. Nan fa Shatima ya ce sai sun je asibiti. Ita kuma ta dage ai taji daidai da ta yi amai din.
Yayi ta lallashinta amma ta ki. Ya kira Hajiayrshi ya kai mata kara. Nan take ta kira layin Amna, cikin sigar lallashi ta ce, “Amna ta yarda taje a dubata.” Ta ce, “To Hajiya.” Ta dube shi, “Ka ci albarkacin Hajiya.”
Sai da suka yi sallar Azahar sannan suka shirya zuwa asibiti, doguwar riga ta saka da dan mayafinta, shi kuma yasha kananan kaya. Sun yi kyau abin su sosai
Www.bankinhausanovels.com.ng
A kan idon Nafisa da Aliya suka wuce. Kowaccansu da abin da ta kisima a zuciyarta. Cikin gari suka shiga, in da ya kaita wani asibitin kudi gwajin nan take kala biyu suka yi mata.
Cikin sati uku da kwanaki ya bayyana. A gaban Likitan Shatima ya rungume Amna. A nan ya kira Hajiyarshi ya fesa mata. suna hanyar dawowa a mota Hajiyar ta kira shi.
Ta nuna matukar murnarta da samun cikin, kuma ta ba ta shawarwari matsayinta na uwa. Amnar tayi godiya, suka yi sallama. Har suka kai gida Shatima na yiwa Amna sannu da zaran sun hada ido.
Da ya tsaya da mota kuma bayan sun kawo gida, cikin shagwaɓa ta ce sai dai ya dauke ta. Ya ce, “In kullum ki ke son in dauke ki wannan abu ne mai sauki.” Kafin ta ce da wasa take yi har ta ji ta caraf a hannunshi ya yi sama da ita, yasa kafa ya rufe motar.
Bai dire ta ko’ina ba sai a kan gadonta. Ya kira Aliya a waya ya fesa mata. Tayi murna sosai a wayar amma a can kasan zuciyarta takaici ne da damuwa.
Ranar yana dakin har bayan Isha’i, sai da suka yi sallah yaga ta dan ci wani abu sannan ya
Www.bankinhausanovels.com.ng
lallabata tayi bacci, sannan ya fita bayan ya fada ma mai aikinta cewa ta kula da ita saboda dare.
Dakin Nafisa ya nufa dama can yake, in san
ranshi ne yaje ya duba Salma don bata da wayar da
zai ji laifiyarta, amma baya son mitar Nafisa. Lokacin da ya shiga gurinta ba ta falo, dakin shi ya shige don ya yi wanka, bai neme ta ba ne don yasan yanda suka rabu.
Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba.
Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya ce, “Sosai ma, za ki sammin?”
Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce, “Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]