[Advertisements⬇️]

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA'ADATU WAZIRI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

iya ganin damuwarta ko fahimtar abin da ke damun ta, takan iya hadiye ta shanye shi a cikin ta.
Sai dai irin kyakykywan sanin da Deeni ya yi mata ya sa ya fahimci damuwarta a game da danta wanda ya sanya wa ransa sai ya nemo wa Bahijja danta wata rana ya dawo hannunsu da zama, saboda irin kyautatawa da biyayya tare da soyayyar da Bahijja take nuna masa, hakan ya sa kullum yake so ya ga ya faranta mata, kula da tattali da Bahijja take masa ko shi baya kula da kansa haka.

Kwanci tashi babu wuya gurin Allah, har Farida ta gama zaman takabarta, zaman shiru da kadaici ya dame ta, kullum za ka gan ta cikin damuwa da rashin walwala, duk da kuwa cewa babu abin da ta nema ta rasa a rayuwa, Alhamdu lillah, komai Deeni da iyayensa suna mata gata, ko a gidan iyayenta sai haka.
Mama tana iya kokarinta wajen ganin ta kawar mata da damuwarta tare da raba ta da yawan tunani, walwalarta daya idan tana tare da yaranta, yanayin da take ciki yana matukar daga wa mama hankali.
Hakan ta sa wata rana Deeni da Bahijja da suka zo Kaduna ta koka masu damuwarta game da halin da Fareeda take ciki, Misbah ta kalli mama da Deeni ta ce, “mama ga wata shawara ko za ta yi maku.” Mama tace, “Me zai hana, wace shawara ce Bahijja?” ta fada tana kallon ta. Misbah ta kalli Deeni, murmushi ya yi mata ya girgiza mata kai alamar ya ba ta izini. Mama ta kalle su ta yi dariya, ranta ya yi mata dadi, wannan kauna da girmama juna da fahimta da ke tsakanin Deeni da Bahijja yana burge ta, ina ma a ce haka kowane ma’aurata suke fahimtar juna.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Yana da matukar muhimmaci a kowane irin. dangantaka fahimtar halin da dan’uwanka yake ciki, mai dadi ko mara dadi. Yi wa dan’uwankai kyakkyawar zato, samun yarda a tsakani, yi wa juna adalci, ba wa juna hakki, sannan kasancewa da juna a lokacin da daya ke bukatar daya, duk
Www.bankinhausanovels.com.ng
yadda suka samu sabani, da zarar dayansu ya shiga cikin matsala ko wani damuwa ta hanyar kalamai masu dadi tare da nuna wa juna, duk rintsi, duk wuya, duk dadi, ana tare da juna, ba za su taba barin juna cikin kunci ba. Haka kuma ba sa taba yin abu ba tare da neman shawarar juna ba, wannan alkawari da suka daukar wa juna shi ne ba sa taba yarda su yi rashin magana da juna ko fushi da juna, da ya wuce na minti biyar.
Bahijja ta katso wa mama tunani da cewa, “Da ma ina tunanin mai zai hana ko Farida ta yi aure ko ta yi wani abu mai ma’ana a rayuwarta, da irin wannan zaman shiru da take, banda kadaici da tunani babu abin da zai kara mata. Ko ta fara karatu ta yi aure, ko dai in ta samu miji ta yi aure ,ko kuma karatu in ta gama za ta iya taimakon baba da Deeni da wasu ayyukan, Farida da yarinyarta da baiwarta, irin nata lokaci ya yi da zai mata anfani ta anfanar da wasu.”
Mama ta kalle ta tana murmushin jin dadi, “da ma ni a tunani na auren ya kamata ta sake, ina jira in ga wanda za ta fitar cikin maneman nata, da na yi mata magana sai ta ce a ba ta lokaci ba yanzu ba tukuna, ni kuma ba na son takura, amma ina ga zan sa babanku ya yi mata magana, ya ba ta zabi, duk wanda take so a ciki, auren ko karatun.
Deeni ya kalli Misbah cikin tsananin son ta da kaunarta, kullum Misbah kara burge shi take yi da halayyarta da kyakkyawan tunani irin nata, ya sha
Www.bankinhausanovels.com.ng
ganin tana kokarin gyara rayuwar mutane da kyautata rayuwarsu,
Mama ta mike ta yi kicin saboda kira da mai aiki ta mata, hakan ya ba wa Deeni damar kamo hannun Misbah yana wasa da ‘yan yatsunta, sannan ya manna hannunsa da nata yana mata kallon so da kauna tare da murmushi mai kashe zuciya. Ita ma murmushi take mishi tare da daga masa gira ta ce, “Yaya dai jarumina?”
Wannan kallo na musamman da ake min tare da wannan murmurshi suna kashe min jiki ko na mene ne? Na san matata ne da alfahari, na gode Allah da ya azurta ni da mata ‘yar baiwa, mace ta gari mai kyakkyawar zuciya da kyakkyawar manufa kan AL’UMMA gaba daya.
Ta fadada murmushinta tare da shafar gefen fuskarsa, ta ce, “Ina tare da jarumin jarumai wanda manufarsa da tunaninsa kullum yaya zai kyautata rayuwar AL’UMMA wadda yake ciki, duk wani hangena da kwarin gwiwata daga gareka nake samu, ba ka ji ana cewa, ‘idan hangen mutum da tunaninsu ya zama iri daya, sun fi zama lafiya da juna da jin dadin juna ba?””
Duk da na kasance mace mai rauni, wani lokaci ana samun rauni a tunanina a matsayina na mace, kana saurin ankarar da ni da irin naka tunanin, cikin wasa da dariya, ba da fada ko tsangwama ba.”. Ta rungume shi sosai a jikinta tare da fadin,
“na gode Allah da ya hada ni da miji irin Deeni, ba
Www.bankinhausanovels.com.ng
fada ba zagi ba tsangwama, ba kyare sai mutunci da kyautatawa tare da fahimta da kuma soyayya mai tsafta.” Shi ma kara mannata ya yi a jikinsa, yana yabon ta tare da maimaita mata kyawawan halayenta da ke kara masa so da kaunarta.
A wannan hali, mama ta shigo ta same su, sai Misbah ta yi sauri ta janye daga jikin Deeni, kanta sunkuye, duk kunya ta kama ta, tana sha’awar ganin su haka, tana yabo da jinjina wa danta tare da yin alfahari da shi a zuciyarata, ganin yadda ya iya rike mace, macen ma irin Bahijja, ba karamin namiji ba ne zai iya rike mata irinsu, ba ya sa su a hanya, su zama (under control) macen  da take jin ta isa mace, ga kuma wayewa ya ratsata amma yanda Deeni yake murza sitiyarin rayuwarta tana biyewa tare da biyayyan aure, ya burge ta koda yake ita ma Bahijja tana da hali mai kyau ga kuma tarbiyya, amma duk da haka mace tana da rauni, matukar ba ta samu namiji mai taka mata birki ba sai ta kauce hanya.
Mama ta kalli Deeni, “ina ga yana da kyau kai ka yi wa Farida maganan, kasan cewar kun san juna sosai, akwai fahimta da kuma iya ba wa juna shawara a tsakaninku, kuma Farida na jin maganar ka na san mu ma za ta saurare mu, amma zai zama kamar mun takura ta, kai kuwa kana iya sa wa ta amince cikin dadin rai.” Ya amsa da, “toh mama, insha Allah zan mata magana.” Misbah na jin su, ba ta ce komai ba, kanta sunkuye, sai dai fa ta ji zuciyarta tana tsananin bugawa, don haka nan da
Www.bankinhausanovels.com.ng
nan ta hau yin adu’a a cikin ranta, don samun saukin abin da take ji a cikin kirjinta, tana gudun abin da zai hada Deeni da Farida, musanman a ce su kebe su biyu. “Ya Allah! ka yayen min wannan kishi da nake ji a zuciyata, ka saukake min wannan kunci danake sa wa kaina, duk da kuwa na mallaki Deeni,
amma kusan kullum cikin tsoron rasa shi na ke.”
Bayan fitar mama, Deeni ya juya ya kalli Bahijja tare da kamo hannunta, ya hada da nashi, ya girgiza mata kai, yace “kar ki damu, kwantar da hankalinki, kar ki min rashin faminta, don ba na son ganin ki cikin damuwa ko wani tashin hankali, tsakanina da Ferida ya wuce HAR  ABADA ba ni da wani sauran so ko kauna ko sha’awa ko kadan, kallo daya nake na manta da batun dan uwana da ya rasu da kuma zumuncin dake tsakaninmu da gidansu, bayan shi ba wani abu.”
Tayi masa murmushi ta ce, “Ba komai Deeni na fahimta.” Wani son ta ya ji ya kara shigar sa, duk da mita irin ta Bahijja a kan kishi tana saurin fahimtar sa ta yadda da duk abin da ya fada ba sai sun ta yi rigima a kan abu daya ba, duk zafi da tsananinsa.
Duk abin da suke fadi Farida na labe daga nesa tana jin su, duk kishi ya turnike ta, ga soyayyar Deeni da ya hana ta sakata kullum, ta tuno irin soyayyar da suka yi da Deeni da irin so da kauna da ya nuna mata, tana mamaki wai yau wannan soyayya ta gushe, wanda ita ko sau daya ba ta taba
Www.bankinhausanovels.com.ng
jin kaunarså ta ragu a zuciyarta, hasali ma dai saukin da ta samu a zama da Shamsu yanayi yake mata da Deeni, hakan ya sa yake sa mata kaunarshi, da juriyar iya zama da shi.
Jin yana shirin matsowa daf da inda take ya sa ta yi saurin shiga daki ta tura kofar, sallama ya yi, yana tsaye daga kofar daki kana ya sa hannuwana daga kofar, ta taso, zuciyarta na tsinkewa ta amsa tare da bude kofar, kanta a sunkuye tana sanye da hijabi.
“Deeni ne, ta fada ta dan murmushi kasa-kasa, shi ma murmurshin ya mata ya ce, “eh ni ne hajiya Farida, ina wuni.” “Lafiya lau,” ta amsa a takaice tare da fadin, “Ashe kune gidan ina ta jin hayaniyar shiga da fita tana maganar tana satar kallonsa, yayin da ya dauke kai bai ma san tana yi ba, sam baya son bata damar da za ta yi wani tunani a kansa, ya kalle ta a fakaice ya ce, “magana za mu yi, ko za ki sameni ni a falo?” Ya juya, bata musa masa tabi shi,
Misbah zaune a falo tana ta danne-dannen (Ipad) din dake hannunta, duk da tana jin zafi da radadi a zuciyarta, amma sam ko kadan ba ta nuna ba, ta ci gaba da yin harkokin gabanta, ganin Deeni da Farida a falon ya sa ta mike za ta fita, Deeni ya rike ta “ina zuwa kuma?”
Misbah ta murmusa, “zan leka mama a kicin ne.” יי Ba ta saurari mai zai ce ba, ta fice ya riga ya san halinta, dan haka ya kalleta kana ya bi ta da kallo, sam bai son ganin ta daga hankalinta insha Allah
Www.bankinhausanovels.com.ng
ba zan ci amanarki ba Misbana, abin da kike gudu
da tunani ba zai faru ba..
Farida ta kira sunansa tare da mai da kallonta gareshi ta ce, “Wace magana ce za mu yi?” ta lura har yanzu hankalinsa yana kan Bahijja, hakan ya sa ta ji ranta yana baci, kishin Bahijja duk ya turnike ta, har yanzu ba ta gajiya da mamakin yadda Deeni yake tsananin son Bahijja, ita kuwa tamkar ba su soyayya ba soyayyar ma ba ta wasa ba.
Ta kalli Deeni da har yanzu bai ce mata kala ba ta ce, “da ma shaukina canzawa haka?” Juyowa ya yi ya kafa mata idanuwansa masu rikita ta, duk da ya gane me take nufi, amma sai ya kalle ta bai ba ta amsa ba ya ce, “Da ma maganar zaman da kike haka ne Farida, ba ma jin dadinsa, kin takura kanki da rayuwarki guri guda, wannan ba daidai ba ne, kina da damar yin rayuwar farin ciki da jin dadi kamar kowa.”
“Me zai sa ki kuntata wa kanki da yarantarki da ranki da lafiyarki. mutuwar Shamsu ba zai sa ki tsaya da rayuwa ba, don haka a matsayina na dan uwanki kuma abokinki da ya san ki tun kina karama, nake ba ki shawara da ki fito daga kejin da kika shiga, ina tunawa da a da mun yi burin za ki yi karatu mai zurfi, za ki zama wata abu a rayuwa da za ta amfani al’umma, za ki fadada kimarki, me zai hana ko dai ki yi aure ke ma ki samu abokin rayuwa kamar kowace mace, ki ji dadin rayuwarki, ki samu gidanki da iyalanki, ko kuma kafin hakan ya samu ki koma makaranta, amma ba ki zauna
Www.bankinhausanovels.com.ng
wuri daya kullum kina zaune a gida a daki ba, wannan ba daidai ba ne, iyayenmu ma ba dadin hakan suke ji ba. Ina fatan za ki duba shawaran nan ki san me kike ciki da rayuwarki.”
Kallonsa Farida take tana fahimtar me yake fadi, har ya gama maganarsa sannan ta muskuta ta ce, “Na ji maganar da ka fadi, dangane da maganar aure, mutum daya na so a rayuwata, shi kuma na taba jin cewa zan iya kuma na shirya aurensa da kaina, bayan wannan ni Farida ba wani da namijin da zan iya kalla in ce ina so, har ma in ce wa iyayena na shirya auren sa.
“Mutumin da na so, ya so ni, muka so shirya rayuwa, soyayya muka yi ba ta wasa ba, ba kuma wai (normal) soyayya muka yi ba, tamu soyayyar ta bambanta sosai, tun daga abota ta koma shakuwa ta rikide ta koma soyayya mai tsanani, soyayyar gaskiya kuma wacce aka gina domin Allah.
“Ba na jin irin waanan söyayyar tana kArewa ko da kuwa Allah bai kaddara mun yi aure ba, ko da kuwa na auri wani na haifi ‘ya’ya dari da shi, ko da kuwa shi ya auri wata, tamu soyayyar ba mai kArewa ba ce.
“Dan haka Deeni abu daya zuwa biyu zau fada maka, idan ka ga na yi aure to, shi na aura, karatu kuwa, da ma wannan burinsa ne na yi karatu na zama wata abu. In har ya aure ni na san zai cika wannan burin nasa a kaina, in kuwa bai aure ni ba, to ba ra’ayin wannan a tsarin rayuwata, da kuma tsarin gidanmu, ina fatan ka samu amsar abin da ka
Www.bankinhausanovels.com.ng
fada min, komai na hannunka, in kana son rayuwata ta canza, farin cikina ya dawo to, kana da zabi, in kuwa baka iyawa toh, ina mai tabbatar maka rayuwata sai dai ta kare a haka.”.
Kalamanta sun sa ya ji zuciyarsa ta fara zafi, ya mike ba tare da ya kalle ta ba balle ya tamka mata, ya nufin hanyar fita daga falon, ita ma ta mike tare da kiran sunansa, “Deeni, ina sonka, ni ce Farida, ka tuna baya Deeni, ka tuna soyayya da kaunarmu, ni na tabbata har yanzu da soyayyata a zuciyarka, ba za ta taba, barin zuciyarka ba.”
Bai saurare ta ba, ye fice daga falon, kai tsaye ya nufi hanyar fita ba tare do ya yi wa kowa sallama ba, ransa a bace ya dunga jin zuciyarsa tana masa wani iri zogi da radadi, ya rasa dalilin da ya sa ya ji wani iri mummunan bacin rai yana taso masa.
Gida ya wuce kai tsaye, yana kaiwa da kamowa, ya rasa me ke masa dadi, daga karshe ya nemi wuri ya zauna tare da daura kafa bisa table, idonsa rufe, tunani kala-kala a cikin zuciya da kwakwalwarsa, yana kokarin neman mafita.
A wannan halin Bahijja ta same shi, tana ganin yanayinsa ta san da ma ba lafiya ba, tun daga yadda ya fita ba tare da ya yi mana sallama ba, haka nan ya taho ya kyale ta, tabbas ta zargi abin da take tunani zai faru shi ya faru, zuciyarta tana mata zogi da radadi, tana hango wani mummunan tashin hankali da zai faru a gareta, tuni ta soma jin ita kadai ce maraicin da take jin ta rabu da shi, ta ji yana son dawo mata.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta dinga jin gatan da take da shi ya zo karshe, ta dinga jin zafin yadda Deeni ya mance da ita a gidansu, lokaci ya yi da za ki yi wa kanki gata Bahijja, lokaci ya yi da za ki biya rayuwar da kika zaba wa kanki da tsada, a wannan lokacin baki da wata gata a duniya sai Allah, sai kanki.” “In Allah ya yarda ba zan bari in wulakanta ba, zan nuna wa kaina gata, zan tsaya wa kaina, ba zan taba karaya ba, haka nan Deeni ba zan taba shiga tsakaninsa da abin da yake so ba,
ba zan taba zama sanadin samun matsalar zumuncin da iyayen Deeni da na Farida suka gina ba, tun kafin ma Deeni ya san da ni.”
Nan take ta yanke wa kanta hukuncin abin da za ta yi. A hankali ta matsa ta kunna wutar falo, haske ya mamaye falon sannan matsa gareshi tare da shafar kansa ta ce, “lafiya kuwa, Deenina da ba ya son duhu yake zaune cikin duhu? Ni dai na san ba karamin abu ne zai sa Deeni ya manta Misbansa a gidansu ba.” יי
“Wa ya taba min miji, hala (poultry) dinka ne ya samu matsala, shi ne ka dai na san zai iya daga ma hankali.” Nan ya dago kai ya kalle ta, ta sakar masa murmushi, wani irin sabon son ta ya ji yana shigar sa yana tsuma shi, shi kam bai san yawan son da yake yi wa Misbah ba. Ganin fuskarta mai kwarjini da cikar kamala ya sa ya ji ya samu wani irin sukuni da natsuwa, ya ji wani irin sukuni a zuciyarsa.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]