KASAR WAJE CHAPTER 13 BY MARYAM DATTI

Advertisements

_____

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Advertisements

_____

A hankali ya fara bud’e fayell d’in yana dubawa mugun fad’uwa k’irjinsa yayi ganin sunayen masu project d’in “Armando Martinez da Khadija Yusuf Suleiman”..  Shiru yayi na mintuna yana tunani saidai ya kasa fahimtar abu d’aya “Hayfarsa sunanta khadija Khalid, wannan kuma khadija Yusuf Suleiman”.. d’an d’aukar wayarsa yayi ya lalubo wani number ya jefa kira.. Daga d’ayan b’angaren aka ansa+

..Yarona na kaina ya kake..? Kamal ya ansa lafiya Aunty, pls Aunty wani abu na keson tanbayarki..

d’an dariya tayi tace Allah yasa na k’aruwa ne kud’i nake nema inason canza mota.. Dariya yayi yace Aunty wai dama maganar canza motar nan tana nan har yanzu..? Langwab’e murya tayi tace to ba kace sai nx year zaka canzamin ba ni kuwa yanzu nake so sabida Ammah tace na kawo jst 1.800 ta bani BMW d’inta wai tayi order sabo kasan yanzu tanada Range Rover ne.. Ajiyar zuciya yayi yayi tsaki idan Aunty Luba na bashi labarin arzikin mijin hayfa ji yake kamar ya had’iye zuciya ya mutu ko da yake shima ay yana dab da komawa aiki a CBN kuma yayi alkawarin yana komawa ko ta wani hanya sai ya dawo da hayfa gareshi.. Muryar Luba ya dawo dashi tunaninsa.. Ina jinka mana kuma kayi shiru.. Ajiyar zuciya yayi yace yanzu nawa kika had’a na sanja motar..? Cikin zumud’i tace na saida tawa 700k sai 200k da baban yara ya bani sai loan da na ansa a office 300k.. Yace OK za muyi agreement yanzu zan cika miki sauran 600k d’in bisa sharud’a in kin amince.. Da sauri tace ko meye sharad’in na amince..

Murmushi yayi yace “OK” da farko menene sunan mijin hayfa..? Ko b’ata lokaci ba tayi ba tace “Yusuf Suleiman”.. Sosai hankalinsa ya tashi.. Ya sake daurewa yace ko hayfa ta zo Nageria kwanan nan..? Da sauri tace eh ay jiya ma ta koma nima ko had’uwa ba muyi ba yayarta tace wai aiki tazo na btaimakawa mabukata ann kauyukan kasuna to tayi tafiya kuma kasan halin hayfa dama ya lafiyar kura bare tayi hauka domin girman kanta k’aruwa yayi sabida tsabar wulak’ancinta babu inda taje gaida kowa har ta bar garin nan wai duk yadda mu ke ni da yayarta amma ko gidana bata zo ba.. Ajiyar zuciya yayi yace.. Shikenan Aunty bari na barki za kiga alert yanzu sannan sharad’i na k’arshe kada ki bari Mommy tasan munyi wannan maganar fa pls.. Cikin zumud’i tace ko da wasa da ke ita da Kamal ba wani tazarar bane tsakaninsu dayawa shiasa suke yi kamar sa’oi nan suka yi sallama tana ta shi masa albarka.. Ko minti hud’u basu yi da sallama ma ba  taji alert ta daka tsalle tana neman layin Ammah domin motar ta kai 3m kawai kusan kyauta ammah ta bata shiasa ba tason tayi wasa da damarta bugu biyu ammah ta d’aga wayar

Kina gida..? Ammah tace eh saidai ina shirin fita.. Luba tace bari nayi miki alert yanzu.. Ammah tace OK ay motarki na ajiye kinsan tuni na daina using zan barwa laraba key in kika zo sai ki ansa.. Godiya luba ta fara sosai kafin su kayi sallama ammah na murmushi sabida ita wannan shine dream d’inta tuni ta rik’a kyawta irin ta manya.. Lol Ammah duniya

Tunda su kayi sallama da Luba ya fad’a tunani shin waye Yusuf Suleiman..? da ya rabashi da farin cikinsa Idan kud’i yake tak’ama dashi to zasu zuba daga yanzu shima ya sha alwashin ko zai rasa k’arshen kobonsa zai dawo da hayfa gareshi tunani ma yayi tunda Daddynsa ya gama masa komai na komawa CBN to zai koma nx mouth dama shi yak’I cewa sai nan da six mouth da haka ya gama duba fayell yana mamakin gurin da suka saya har 130M lallai sai yayi da gaske ya tabbata dai hayfa na sonsa kud’ine ya rud’i y’an uwanta suka mata dole kuma a wannan karon babu mai taka masa burki har sai ya dawo da hayfa gareshi..

Sai wajajen 4:30am ta d’an bud’e idanunta a hankali Clara na kujerar d’akin tana bacci a hankali taci gaba da bud’e idanunta har ta bud’e gaba d’aya saidai kanta ya mata nauyi sosai ta fara d’an kalle-kalle inda ta hango Clara na bacci tayi ajiyar zuciya.. Ko kad’an bai k’ara runtsawa ba tun bayan da Clara ta tasheshi joyo motsin su mahfuz yayi suna sahur inda yaji ana k’wank’wasa masa k’ofa a hankali ya mik’e ya bud’e mahfuz yace “kazo muyi sahur.. d’an jimm yayi tabbas yana jin yunwa saidai baya jin zai iya had’iyar wani abu amma ya daure ya cewa mahfuz bari yayi brush yana fitowa..

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sahur su kayi jam’i kamat yadda su keyi a falon masaukinsu inda hankalin Yusuf duk yana kan wayarsa yana so yaji Clara ta kirashi.. Bayan sun gama musabaha aka ce yau sai 10am za a fita sabida aikin a kusa ne gobe kuma suka Kama hanyar Toronto.. Yusuf d’akinsa ya koma dukda mahfuz yaso suyi fira.. Kasa jurewa yayi ya jefa layin Clara..

Hayfa ce ta hango wayar na haske a gefenta alamar shigowar kira sabida Clara da zata kwanta ta saka silent sabida kada a kira karar ya tashi hayfa.. A hankali hayfa ta mik’a hannunta mara drip kan bedsyd d’in gadon ta d’auki wayar ko kafin ta d’aga ya tsinke ba tama ga mai kiran ba.. Sake shigowa kiran yayi a hankali ta d’aga saidai ba tayi magana ba numfashinta na fita a hankali mai d’umi.. Wani irin runtse idanunsa yayi jin numfashinta da cikin wani yanayi yake yaji ya sani.. Cikin wata irin murya mai susuta jini da zuciyar wanda duk a kayi anfani da muryar wajen yi masa magana ya furta ” ya jiki”..? itama wani irin runtse idanunta tayi gaba d’aya jini da ruwa da b’argon jikinta sai da suka ansa yanayinsa tare da aika mata wani dunk’ulallen yanayi cikin zuciyarta taji kamar ya zuk’e mata dukkan jinin jikinta.. Kasa magana tayi sabida yadda take jin wani yanayi na fisgarta izuwa gareshi tabbas inda yana kusa da ita yaga yanayin da ta shiga zai d’auka ta zauce.. Jin shirunta yayi yawa cikin yanayin da ya k’ara birkitata ya furta “pls baby 4give me halin da kike ciki a yanzu kawai ya isheni azaba ba sai kin k’ara da yimin hukuncin rowar muryarki ba “.. Wani irin hawaye ne mai kauri da d’umi ya fad’o mata tana ajiyar zuciya ta furta “da sauqi” ajiyar zuciya shima yayi yace ” ina Clara”..?  3second kafin ta bashi ansa “tana bacci”..! Yace ke ma ki k’ara yin bacci sosai ki jirani gobe IA ina tare da ke zan kula da ke da kaina kinji..? Hawaye ta k’ara saki tana jin yadda Wani irin zazzafan soyayyarsa ke k’ara bin jikinta da k’wak’walwarta a hankali ta furta “Allah ya dawo da ku lafiya”..! Amin yace kafin yace ki kwanta yanzu kafin Dr ya shigo anjuma zan kiraki.. Toh tace su kayi sallama.. Bayan kashe wayar k’ara fad’awa tunani tayi tana masifar nadamar yanayin da ta jefa rayuwarta sabida abin duniya saidai a hankali idanunta suka fara rufewa sabida sosai a ka saka mata maganin Hutu a drip. 

Shima runtse idanunsa yayi sai yanzu da yaji muryarta yaji ya fara jin bacci a hankali ya mik’e kyakykyawan gadonsa na d’akin tare da k’ara lumshe idanunsa yana jin wani zaffafen soyayyar matar ta sa da ya ke hanashi sukuni a duk sadda ya fara tunaninta saidai nishad’in da ya samu a d’an wayar da su kayi yanzu ya sanyashi jin bacci na fisgarsa mai dad’i..

Yau suka gama aikinsu inda suke ta shirye-shiryen kamo hanya da asubahin gobe.. Ammah ta yita gwada layin hayfa ba ansa kasancewar sun bar wayar a goda da zasu tafi asibiti ita kuma yanzu ba ta cika son kiran layin Yusuf kada ya fara zargin yadda suke kwasar masa kud’i hakan yasa kawai ta yiwa hayfa text na ban gajiya da fatan sun isa lafiya..

A asibiti sosai hayfa ta farfad’o Armando yazo ya ganta inda shima yace ta kiyaye ta samu hutu na wk domin next wk zasu fara aikin campaign na Gala kuma dole ta yi aiki tuk’uru sannan ta maida jiki kad’an sabida ya d’auki alwashi sai ta samu bangon Gala domin idan yarinya ta samu bangon Gala to duk kamfanonin duniya sun rik’a bata aiki kenan sannan albashinta zai fara tsada domin sai manajanta ya karanta aiki ya yiwa aikin kud’i a maimakon kafin ta samu gala mai aiki ne yake fad’ar abinda zai biyata ita hayfa ma sam aikin ya fita ranta saidai dole ta cika musu contract d’insu kuma ita kanta idan ta samu kud’in k’arawa mominsu tasan har abada indai ana juyawa yadda ya kamata babu su babu talauci da wannan tunanin taji ta d’an samu nutsiwa..

Armando ya kalleta yace queen daga nx WK har ruwan shan ki ya sake komawa hannun Vivian sabida wlh aikin gala ba wasa ba ne sai kin maida hankali ba  kuma na so kina aikin komai da Liliana kin gane ko..? Gorgiza kai tayi..! Yace jiya na zuba miki sauran kud’in aikinmu na prince da na hotel da aka bamu kinga mun sauka gidanku don haka har nawa na hotel na saka miki a accnt d’inki yanzu kinada $185 sam bata damu da kud’in ba tace ka raba biyu ka turawa momina rabin yau za tayi tafiya nx wk.. OK” yace yana d’ukar wayarsa cikin abinda baifi 3mnts ba ya turawa Ammah $90 inda suka ci gaba da hira sama-sama har yazo wucewa ya bawa Clara $5000 ta masa godiya ya wuce.. Clara ta kalli hayfa tace khadija ba zaki ci komai ba.? Hayfa tace za taci chips..

Ammah ganin kud’in wani irin murmushi ta saki domin tuni ta daina mamakin kud’in da hayfa ke aiko mata sosai take shirin k’wata kamfaninsu domin har Online office ta bud’e ta d’auka wani ma’aikaci wannan shine b’angarensa ga shi ta sa a kawo mata manyan mata dangin babansu daga maidugiri za ta bud’e b’angaren dafawa ma’aikatan kamfanin abincin inda su matan aikinsu dafawa sai daga b’angaren goggo tasa an kawo yara k’anana y’an 13yrs aikinsu rainon yaran mata ma’akatan kamfanin domin kuwa sosai kamfanin yake da girma abin dai kamar mafarki saidai ammah na da kyawta hakan yasa kowa ke sonta da kusantarta hatta da iyayenta suna yaba mata wajen kula da su domin in wata ce zagewa za tayi tayi tana ci ita kadai da yaranta..

Sai kusan 5:pm agogon Toronto Su Yusuf suka shigo Toronto inda kuma k’aida wai masallaci zasu fara wucewa kafin kowa ya nufi gida… A masallaci minista ya rabawa su Yusuf envelope da kwalin kaza kowa mai d’auke da kaji ashirin ko wani kwali sai kwalin madara mai d’auke da robar madara 40 sai kwalin shinkafa shima mai d’auke da sachets 40 ciki suka yi masa godiya inda Hamzad ya cewa Yusuf an bashi hutun 3dys kafin ya dawo aiki sosai Yusuf yayi godiya inda akace kowa drebobin masallaci su maidashi gidansa..

A hanya Yusuf ya kira yasir yace su had’u gida ya dawo.. Koda aka sauke Yusuf yasir na k’ofar gidan suka fara kwashe kayan tare suka shiga dashi gidan bayan sun gama suka runguma suna gaisawa kafin yasir ya kalli Yusuf yace “dude ka rame ciwo kayi a can”..? d’an ajiyar zuciya yayi yace wlh kullum waje muke wuni” yasir yace lallai mitumin nan na aiki neman lahira Allah ya saka masa Yusuf yace “amin” Yusuf yace bari na kwara ruwa mu je asibiti.. Yasir yace OK yana shiga kanta yaga ko mai zai tanadar musu na bud’a baki..

Yusuf yayi wanka ya sanja cikin pencil jeans dark blue da farin polo ya d’aura agogo ya fito d’aga fillow yayi ya ajiye envelope d’insa ya fito.. Yasir ya gama dube-dubensa bai gane mai zai had’a mai sauqi ba ya kalli Yusuf yace “dude mai kake so na bud’e baki”..? Yusuf ya saki dariya yace kaidai abinci tun yanzu ka bari a hanya munyi shawara yanzu mu je.. Yasir yace d’an wulakanci jarababbe azumi dai a keyi amma kai duk birinka kaje kayi mmmmm kada na furta nayi zunubi ina azumi.. Naushi Yusuf ya kai masa a kafad’a ya kauce yana dariya suka fito.. Clara ma tana café d’an bacci ne itama ya kwasheta bayan sun gama waya da Ammah.. Koda suka iso k’ofar word d’in hayfa Yusuf ya kalli yasir yace “ka tsaya idan naga komai daidai sai na maka alama ka shigo”..! Tsaki yasir yayi yace “lokacinka ne kayi” zamu had’u gaba wlh.. Dariya Yusuf yayi ya bud’e k’ofar a hankali.. Saidai yana saka k’afarsa cikin d’akin ta bud’e idaninta a hankali.. Wani irin numfashi ya ja ganin yadda ta zube fiskarta tayi fayau sai dogon hancinta da manyan idanuwanta.. A hankali ya k’arasa gabanta yana kallonta inda itama a hankali ta k’arasa bud’e nata idanun suka shige cikin na sa.. Wani irin ajiyar zuciya tayi itama tare da d’an lumshe idanunta da tuni suka fara tara ruwa na tsananin farin Colin ganinsa.. Matsawa ya k’arayi dab kafin a hankali ya zaune gefenta ya d’agota ya rungume tare da sakin wani kasalalen ajiyar zuciya da taji har cikin jijiyoyinta itamaBayan ya bata Irish da paper soup d’in kazar taci ba laifi suka zauna falon inda yayi ta k’ok’ari har ta saki suka fara hirarsu inda yake fad’a mata jibi zasu tare gidansu haka su keta hira har lokacin baccinsu Yasir da Yusuf su kayi waya kafin suka wuce suka kwanta…+

Da safe sai 11:am suka tashi tun bayan da suka yi sahur harda yasir suka yi asuba kafin ya koma suma koma sai yanzu inda suka yi wanka tare ya shirya ya cewa hayfa kada tayi aikin komai tunda ta d’auki azumi sabida kada ta jigata dayawa yasir yazo suka fita zuwa shopping a supermarket tare.. Koda suka isa Albert na ta aiki suka gaisa jibi Yusuf zai koma aiki Yusuf da Yasir da Sebastian suka haura sama inda Yusuf ya zab’awa hayfa tv 40enchs inda za a rik’a cirewa albashinsa suka fito inda a k’asa suka d’anyi shopping kad’an suka wuto gida inda suka tsaya suka ajiyen tv suka k’ara gyara komai kafin suka dawo gidan hayfa ta gyara nan itama ta kunna musu turaren wuta sai k’anshi yasir ya kishingid’a a carfet Yusuf ya shiga d’akin ta taso ganinsa ya janyota ya ringume kafin ya kalleta yace “kinyi karatu”? Girgiza kai tayi yace gud..

Yau su hayfa suke tarewa gidansu inda Yasir ke jin kamar an aiko masa da mutuwa a dole yake murmushi tun 11am shi da Yusuf suka gama kai kayan Yusuf da hayfa gidan inda yanzu babu wani abu na su da ya saura sallama su kayi wa hayfa inda itama Clara tazo za su fita tare.. Itama shopping su kayi inda ta d’an saya k’ananan objects na mata matasa na bkwalliyar gida kamar su frames da dai k’ananan objects na gida sai K’aramin TV 34eanchs ta sayawa Yasir tayi musu shopping na su Irish da vegetables da su cornflakes jamb mayonaise da dai a lot tinks na su da Yusuf kafin suka nufo gida su Yusuf ba su dawo ba suka cikawa Yasir fridge d’insa kafin suka jera masa kayan abinci a inda suke ajiyewa kafin hayfa ta d’ibar masa kaji da madara da shinkafa wanda yusuf ya kawo kafin a toilet suka jera masa kayan wanka da detergents na wanki da dai na duk buqatun toilet Inda hayfa ta saka masa $5000 a envelope ta k’aramin note suka kulle gidan suka wuce nata.. Wani irin lumshe idanunta tayi yau su ne da gidansu ita da Yusuf sosai ta kejin farin ciki Mara misaltuwa Clara ta tab’ata “khadija”..? Murmushi tayi kawai suka k’arasa ciki inda suka fara gyara irin na su na y’an mata inda suka bud’e akwatin hayfa na kayan turare da kayan mata Clara ta ce mata ta saya shoglass nan suka shiga internet wani suka zab’a siriri mai tv stan d’insa suka saya na turkey ne ma suna ta aiki sun gama shirya komai a fridge suka cika kiching taf da kayan abinci haka bayi hayfa ta fitar da duk kayan cosmetics d’inta wanda su Armando suka bata a kamfani masu tsada komai akwai kayan wanka wanke gashi mace da namiji da kayan gyaran fata na wanka suka gama suna gyaran bedrm aka kawo shoglass inda masu kamfanin suka had’a komai hayfa ta sallamesu suka wuce ita da Clara suka jera gidan yayi kyaw inda Clara tace ta sayo dinning ko mai kujera uku ne nan suka k’ara kiran kamfanin suka yi order aka kawo musu sabida gidan madam hayek yafi na Yasir kad’an don haka suka saka dinning d’in dukda falon ya cike amma yayi kyaw domin akwai komai na buk’atar mutum a talauce amma masha Allah. sosai suka gama aiki gidan yayi kyaw sosai kayansu tare a k’aramin wadrop d’in kowa layi biyu sauran kayansu duk suna akwatuna inda wasu akwatin duk ta d’orasu sama wani kan wani inda nan ma Clara tace mata ta saya abin rataye jaka da adana takalma sanin cewa hayfa mai kud’i ce yanzu nan ma sika k’ara kiran kamfanin aka kawo suka bud’e akwatunan aurenta suka zab’o wasu jakunkuna kala h’udu da zata rik’a anfani da su da takalma duk suka shirya suka fito ganin har 5:pm tayi hayfa tayi sallah suka fara girkin bud’a baki inda Clara ke taya ta akwatinanta uku da ta dawo su daga Nigeria wanda Clara ta taho mata da su suka bud’e shak’e da abinci babu abinda babu garin kunun tsamiya da na acca da na gyad’a nan suka fidda duka suka jera kiching har babu gurin saka abu a dole ta bar wasu suka ajiye inda ta fara shirin yin jolof rice da peper soup na fresh meat da kunun tsamiya sai panke na alkama da Irish da ke sunyi cewa za suci gaba da bud’a baki tare su uku haka ta shirya abinci ta musu zob’o wanda ba  sugar sai dai an had’ashi da nik’ak’en abarba da vanilla..1

Koda su Yusuf suka dawo suka shiga gidan mamaki ne ya ishesu na yadda su hayfa suka yi gayaran gidan Yasir ga tulin cefane haka Yasir ya gani har kiching inda Yusuf ya ce shi zai je ya dubata wannan aikin da ta maka nasan sai nayi jinyarta na gajiya.. Yasir yace sai ayi jinya lafiya d’in yana dariya..

Bayan fitan Yusuf ya bud’e fridge bushewa yayi ganin ba gurin saka komai yadda fridge d’in yayi mak’il komai akwai tunda yazo Toronto ko gidan tiffun sarkin ci bai tab’a ganin fridge d’insa yayi rabin cika haka ba ga kantarsa ma cike da kayan abinci sai shiwa hayfa albarka yake da Yusuf ya fito ya shiga d’aki inda nan ma tas ya lek’e bayi nan ma zama yayi gefen gadonsa sai ya hango envelope da sauri ya d’auka ya bud’e ya fara karantawa..

Salaam..!

Sosai na ke godiya a kan kauna da amanarka a mijina, ga wannan babu yawa..! Nagode

Ganin har $5000 mamaki ne ya cika shi na yadda yarinyar ke kashe kud’i masu yawa akan Yusuf  kuma ba ta son mijinta ya sani..ajiyar zuciya yayi yana rok’on Allah shima yasa layla  ta soshi haka

Cike da murna ya mik’e gobe zai turawa Aunty da Mama $4000 shima ya ajiye sauran ya fara shirin biyan gidan nx mth tunda sun rugada sun biya wannan watan.. Saidai ko da ya fito falo nan ma yaga latter na gidan a gefen kujera ya bud’e an biya masa nx 3mths ya duba signing yaga ansa “Khadija Yusuf Suleiman”..! Shi firgita ma yayi kashe kud’in yarinyar yayi yawa saidai da ya tuna inda tayi karatu kuma yaji gidansu na kuse rd maybe iyayenta ke turo mata kud’i ganin Yusuf bai da k’arfi domin wannan k’aramin aikin masu kud’in Nigeria ne k’ila shiasa bata so Yusuf ya sani sabida da mugun fad’in ransa ya tabbata bazai yadda tana anso kud’i gun iyayenta ba.. Tsaki yayi yace nine wlh Bayan ya bata Irish da paper soup d’in kazar taci ba laifi suka zauna falon inda yayi ta k’ok’ari har ta saki suka fara hirarsu inda yake fad’a mata jibi zasu tare gidansu haka su keta hira har lokacin baccinsu Yasir da Yusuf su kayi waya kafin suka wuce suka kwanta…+

Da safe sai 11:am suka tashi tun bayan da suka yi sahur harda yasir suka yi asuba kafin ya koma suma koma sai yanzu inda suka yi wanka tare ya shirya ya cewa hayfa kada tayi aikin komai tunda ta d’auki azumi sabida kada ta jigata dayawa yasir yazo suka fita zuwa shopping a supermarket tare.. Koda suka isa Albert na ta aiki suka gaisa jibi Yusuf zai koma aiki Yusuf da Yasir da Sebastian suka haura sama inda Yusuf ya zab’awa hayfa tv 40enchs inda za a rik’a cirewa albashinsa suka fito inda a k’asa suka d’anyi shopping kad’an suka wuto gida inda suka tsaya suka ajiyen tv suka k’ara gyara komai kafin suka dawo gidan hayfa ta gyara nan itama ta kunna musu turaren wuta sai k’anshi yasir ya kishingid’a a carfet Yusuf ya shiga d’akin ta taso ganinsa ya janyota ya ringume kafin ya kalleta yace “kinyi karatu”? Girgiza kai tayi yace gud..

Yau su hayfa suke tarewa gidansu inda Yasir ke jin kamar an aiko masa da mutuwa a dole yake murmushi tun 11am shi da Yusuf suka gama kai kayan Yusuf da hayfa gidan inda yanzu babu wani abu na su da ya saura sallama su kayi wa hayfa inda itama Clara tazo za su fita tare.. Itama shopping su kayi inda ta d’an saya k’ananan objects na mata matasa na bkwalliyar gida kamar su frames da dai k’ananan objects na gida sai K’aramin TV 34eanchs ta sayawa Yasir tayi musu shopping na su Irish da vegetables da su cornflakes jamb mayonaise da dai a lot tinks na su da Yusuf kafin suka nufo gida su Yusuf ba su dawo ba suka cikawa Yasir fridge d’insa kafin suka jera masa kayan abinci a inda suke ajiyewa kafin hayfa ta d’ibar masa kaji da madara da shinkafa wanda yusuf ya kawo kafin a toilet suka jera masa kayan wanka da detergents na wanki da dai na duk buqatun toilet Inda hayfa ta saka masa $5000 a envelope ta k’aramin note suka kulle gidan suka wuce nata.. Wani irin lumshe idanunta tayi yau su ne da gidansu ita da Yusuf sosai ta kejin farin ciki Mara misaltuwa Clara ta tab’ata “khadija”..? Murmushi tayi kawai suka k’arasa ciki inda suka fara gyara irin na su na y’an mata inda suka bud’e akwatin hayfa na kayan turare da kayan mata Clara ta ce mata ta saya shoglass nan suka shiga internet wani suka zab’a siriri mai tv stan d’insa suka saya na turkey ne ma suna ta aiki sun gama shirya komai a fridge suka cika kiching taf da kayan abinci haka bayi hayfa ta fitar da duk kayan cosmetics d’inta wanda su Armando suka bata a kamfani masu tsada komai akwai kayan wanka wanke gashi mace da namiji da kayan gyaran fata na wanka suka gama suna gyaran bedrm aka kawo shoglass inda masu kamfanin suka had’a komai hayfa ta sallamesu suka wuce ita da Clara suka jera gidan yayi kyaw inda Clara tace ta sayo dinning ko mai kujera uku ne nan suka k’ara kiran kamfanin suka yi order aka kawo musu sabida gidan madam hayek yafi na Yasir kad’an don haka suka saka dinning d’in dukda falon ya cike amma yayi kyaw domin akwai komai na buk’atar mutum a talauce amma masha Allah. sosai suka gama aiki gidan yayi kyaw sosai kayansu tare a k’aramin wadrop d’in kowa layi biyu sauran kayansu duk suna akwatuna inda wasu akwatin duk ta d’orasu sama wani kan wani inda nan ma Clara tace mata ta saya abin rataye jaka da adana takalma sanin cewa hayfa mai kud’i ce yanzu nan ma sika k’ara kiran kamfanin aka kawo suka bud’e akwatunan aurenta suka zab’o wasu jakunkuna kala h’udu da zata rik’a anfani da su da takalma duk suka shirya suka fito ganin har 5:pm tayi hayfa tayi sallah suka fara girkin bud’a baki inda Clara ke taya ta akwatinanta uku da ta dawo su daga Nigeria wanda Clara ta taho mata da su suka bud’e shak’e da abinci babu abinda babu garin kunun tsamiya da na acca da na gyad’a nan suka fidda duka suka jera kiching har babu gurin saka abu a dole ta bar wasu suka ajiye inda ta fara shirin yin jolof rice da peper soup na fresh meat da kunun tsamiya sai panke na alkama da Irish da ke sunyi cewa za suci gaba da bud’a baki tare su uku haka ta shirya abinci ta musu zob’o wanda ba  sugar sai dai an had’ashi da nik’ak’en abarba da vanilla..1

Koda su Yusuf suka dawo suka shiga gidan mamaki ne ya ishesu na yadda su hayfa suka yi gayaran gidan Yasir ga tulin cefane haka Yasir ya gani har kiching inda Yusuf ya ce shi zai je ya dubata wannan aikin da ta maka nasan sai nayi jinyarta na gajiya.. Yasir yace sai ayi jinya lafiya d’in yana dariya..

Bayan fitan Yusuf ya bud’e fridge bushewa yayi ganin ba gurin saka komai yadda fridge d’in yayi mak’il komai akwai tunda yazo Toronto ko gidan tiffun sarkin ci bai tab’a ganin fridge d’insa yayi rabin cika haka ba ga kantarsa ma cike da kayan abinci sai shiwa hayfa albarka yake da Yusuf ya fito ya shiga d’aki inda nan ma tas ya lek’e bayi nan ma zama yayi gefen gadonsa sai ya hango envelope da sauri ya d’auka ya bud’e ya fara karantawa..

Salaam..!

Sosai na ke godiya a kan kauna da amanarka a mijina, ga wannan babu yawa..! Nagode

Ganin har $5000 mamaki ne ya cika shi na yadda yarinyar ke kashe kud’i masu yawa akan Yusuf  kuma ba ta son mijinta ya sani..ajiyar zuciya yayi yana rok’on Allah shima yasa layla  ta soshi haka

Cike da murna ya mik’e gobe zai turawa Aunty da Mama $4000 shima ya ajiye sauran ya fara shirin biyan gidan nx mth tunda sun rugada sun biya wannan watan.. Saidai ko da ya fito falo nan ma yaga latter na gidan a gefen kujera ya bud’e an biya masa nx 3mths ya duba signing yaga ansa “Khadija Yusuf Suleiman”..! Shi firgita ma yayi kashe kud’in yarinyar yayi yawa saidai da ya tuna inda tayi karatu kuma yaji gidansu na kuse rd maybe iyayenta ke turo mata kud’i ganin Yusuf bai da k’arfi domin wannan k’aramin aikin masu kud’in Nigeria ne k’ila shiasa bata so Yusuf ya sani sabida da mugun fad’in ransa ya tabbata bazai yadda tana anso kud’i gun iyayenta ba.. Tsaki yayi yace nine wlh

Advertisements

_____

About AIS

Check Also

KASAR WAJE CHAPTER 15 BY MARYAM DATTI

Advertisements _____ KASAR WAJE CHAPTER 15 BY MARYAM DATTI Www.bankinhausanovels.com.ng  Advertisements _____ Tana saka d’an …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *