[Advertisements⬇️]

KASAR WAJE CHAPTER 12 BY MARYAM DATTI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Hayfa ta kalla Surayya tace “ya shirin exam”? Surayya tayi murmushi tace lafiya aunty saidai babu sauqi ko kad’an.. Hayfa tace ay dama amma ki dage IA komai zaiyi kyaw idan kika maida hankali kina karatu sosai

Surayya tace IA.. Suka ci gaba da hirarrakinsu suna gurin Armando ya shigo duk da yaran basusanshi ba Khairat ta kwashi gudu taje jikinsa ya d’agata yayinda y’an uwanta da sauran k’annin surayya duk suka fara gaisheshi

Zama yayi itama hayfa ta gaisheshi suka d’an fara tattaunawa a kan wasu ayyukansu da kuma tafiyarsu gobe zuwa k’auyuka..

A Toronto su Yusuf ansha aiki sosai gashi anata sa ran gobe za a tashi da azumi inda suna waya da Yasir Madam hayek itama gobe take parking don haka Yusuf dama ya gama contract d’insa na ansa har ya biya kud’in 3mths sabida yanaso in ya dawo yayiwa su Qassem aike ko yaya dukda yanzu suna yawan ce masa basu cikin buqatar komai wanda shi bai yadda ba yana ganin basuson fad’a masa ne kawai..

Yasir yana gida ya ci abinci ne yanason zuwa gun Tiffun kafin lokacin club su wuce aiki sbd gobe bazaije club ba zai tsaya taya madam hayek parking sannan ya gyarawa su Yusuf yadda in suka dawo komai na tsaf zasu tare..

Bayan anyi dinner wajajen 8:30 pm a gidan Ammah kafin suwaiba ta wuce gida saidai yara su duk nan zasu kwana wai tare da hayfa wanda hakan yasa dole hayfa ta koma d’akinta na gidan tare da su duka sabida k’aton toyal bed ne a d’akin

Duk sun ma yi bacci 11:40pm ta mik’e a hankali da niyar sauka k’asa ta nema Yusuf a hankali take tafiya gudun tashin wani a gidan saidai daf d’akin Ammah taji tana waya da ya d’an d’auki hankalinta a hankali ta tsaya

Amma taci gaba Adda wlh babu wani alamar ciki tare da Hayfa tun jiya da tazo nake kula amma banga komai ba kinsan da akwai komai k’ank’antarsa zakiga ma yana sata laulayi musamman irin cikin wannan zamanin

Batasan mai aka fad’a a d’ayan b’angaren ba taji amma na cewa “eh na yiwa malam duka wannan bayanin yace zai duba kinsan yace tabbas yanzu akwai soyayya tsakaninsu ba kuma aikin da yayi bane na sanya musu yawan sha’war juna kinsan dama yace aikin da zarar tayi jini ko wani iri ne aikin zai lalace saidai aikin ya k’ara taimaka musu wajen son kusantar juna   haihuwarce ni narasa yadda zamu b’ullo Adda

Ajiyar zuciya hayfa tayi..  Ta jiyo muryar Ammah ay bama zai yuwu ba da duk wahalar da mu kasha wajen had’a auren ace na bari danginsa su rabasu idan sukaga bata haihuwa, yadda muka yi aiki ya aureta ba tare da ya shirya ma hakan ba haka yanzu komai zanyi domin shiga tsakaninta da duk wani wanda zai raba su

Mugun fad’uwa k’irjin hayfa yayi “wasu irin hawaye masu zafi suka fara sintiri a kumatunta a hankali ta juya ta koma d’aki kan kujerar d’akin ta zauna ta kama kanta tanata hawaye sosai

To a inama suka samoshi har suka masa asiri don ya aure ta..? Innalillahi take maimaitawa tabbas suna tsammanin mai kud’i ne shiasa suka aikata haka

Wani irin mugun taisayinsa da sonsa taji suna ratsa zuciya da jininta wani d’an jaririn kuka ta saki a hankali tana dana sanin duk abbubuwan da ta rik’a yi masa a farkon aurensu kuma IA da zarar ta ajiye aiki zata je ta kwance mahaifarta ta fara haihuwa kamar yadda yake so da fata baza ta k’ara bari ayi masa wani abu mai sunan asiri ba

Mik’ewa ta sake yi a hankali ta d’auki wayarta cikin sand’a ta fito har lokacin Ammah na waya don haka ta wuce ta sakko k’asa can waje ma ta fita wajen baranda ta zauna kafin ta fara nemansa

STORY CONTINUES BELOW

Suna wani k’auye can cikin Cubec suna aiki Yusuf shi yana ma motar kayan yana jerawa tare da mik’awa masu rabo yaji wayarsa na ringing

d’an ajiye kwalin madarar hannunsa yayi ya ciro wayar ya kalli screen ganin hayfa ce ya Kira wani waishi Mahfuz yace ya d’an karb’a aikin zaiyi waya

d’aga wayar yayi saidai baiyi magana ba sabida fushi da yayi da ita… Cikin sanyi murya tace.. “Pls kayi hak’uri wani aiki nayi ne”..

OK yace kawai “ya kike”? Ta ansa lafiya yace me kike yi..? d’an shiru tayi kafin tace “waya da mijina” dariya ce ta kub’uce masa kad’an yace ” baby tsokana ko”? Dariya tayi itama tace “to ba  haka bane”? Ajiyar zuciya yayi yace “miss u so much baby ki shiryamin kanki da kyaw kinji”? Shiru tayi kad’an kafin tace IA.. Yaushe zaka dawo..? Yace inasa ran nan da 6dys IA indai komai ya tafi daidai domin aikin dayawa sosai

Allah ya kaimu tace, yace “amin” suka ci gaba da hirarsu ta tsakaninsu kafin suka yi sallama sabida kiran Yusuf da ake tayi a dole yace ” love u baby”.. Kasa bashi ansa tayi tunaninta duk ya koma kan wayar ammah da taji ya kamata tasan komai “yaya suka fara? Ina suka samoshi ya ya fara sonta? Wani mugun hawaye ta matse tabbas akwai rud’ad’en al’amari cikin mafarinta da Yusuf.. Jin muryarsa yana “baby talk lttr” yasa a hankali tace “bye”!

Bayan ta kashe wayar kuka ta fara sosai na bak’in cikin wai sihiri aka masa kafin ya aureta to k’ila ma ba da kansa yake sonta ba shima aikin sihiri ne in haka ne kuwa ta shiga uku tace yayinda ta k’ara sakin wani sabon kukan

Tayi kuka ta gaji ta kwanta 3sitters d’in falon tare da lumshe idanunta amma ba bacci take ba tana tariyo komai ne na yadda yake nuna mata zallar so tun daga zuwanta zuwa yau yadda suka rik’a yawan son yin sex kenan duk bawai don soyayya bane ta daga Allag da yake mata “Innalillahi take maimaitawa cikin zuciyarta yanzu tanbayar mominsu za tayi ta bata labarin komai ko yaya za tayi ta tabbatar da Yusuf son tane ba sabida asiri ba “ya zanyi in sani ta fad’a tana sakin wani marayan kuka..

Ganin asuba ta gabato a hankali ta mik’e ta haura saman kowa na baccinsa dama haka godansu yake ranar da babu school shigewa d’akin tayi ta wuce bayi ta had’a ruwan d’umi ta shiga ta zauna tayi shiru idanunta a lumshe tana hasko Yusuf da yanayinsa

Ajiyar zuciya tayi Tana ayyana yadda Yusuf yake da kyaw da kwarjini ga Aji kamar ba talaka ba sosai kamun kansa da nutsuwarsa ke d’aukar hankalinta da zuciyarta a gefe yadda yake nuna mata zallar So da tattali kamar wani sarki ajiyar zuciya ta k’ara yi idan har duk wannan kulawar ba daga Allah ba ne tabbas nayi asara tace tana matse hawaye yaya zanyi ta tanbayi kanta..? Kusan 25mnts kafin ta gama ta fito bayin tasa abaya ja ta gama shirinta tsaf tasa son glass ta fito duk suna bacci ta sauka gaisawa suka yi da laraba da mairanjo bata karya ba  tana shirin k’arasawa b’angaren Armando ya fito suka gaisa yace shi zai karya ta barshi ta wuce zuwa gaida iyayenta.

Tun kan ta k’arasa ta hango goggo alje da bak’i tsakar waje kamar ko yaushe sun baje a tabarma suna karyawa suna tad’i.. Gaishesu tayi duk suna mata ban gajiya.. Goggo ce ta kalleta da kyaw tace “auta baki lafiya ne”..? hayfa ta dake dukda jinta take kamar duniya ta fad’o kanta tace “ban samu bacci bane sosai ina wani aiki”..! Goggo tace ki rik’a hutawa kinji?  Tace “toh” ta mik’e don shiga gaida abban su..

Yana zaune shima yana duba littafin durusul muhimmah..! Sallama tayi ya ansa yana kallonta da karantar yanayinta yace ta zauna..

Zama tayi k’asan carfet kanta na k’asa ta fara gaisheshi yayinda yana ansawa yana karantar yanayinta a hankali ya kira sunanta “Hadiza”..! Ta ansa.. Yace ya kamata ki saki ranki domin nayi magana da abokin aikinki yayimin bayanin komai abinda na keso idan kika koma ki maida hankali wajen kyawtatawa mijinki har Allah yasa wannan aimin na ki yazo k’arshe yace nan da watanni hud’u zaki gama wannan, kuma ki kiyaye duk wata alama da mijinki zai gane halin da kike ciki har Allah ya kawo k’arshen abin domin idan kika bari ya sani bansan ya zamu b’ullowa abin ba mu shawo kansa domin y’an uwanki za suyi komai domin raba aurenku idan har suka gano ba  daga gareshi kike samun kud’I ba wanda shima idan ya gano manufarsu da aikin ba lallai bane ya cigaba da aurenki.. Wani mugun hawaye mai zafi hayfa ta saki sai a y’an kwanakin nan ta k’ara gano matsayin Yusuf a zuciyarta da rayuwarta

Babanta naci gaba da yi mata nasiha tana kuka sosai wanda shima a k’arshe sosai tafara bashi tausayi kula da yayi tana son Yusuf sosai.. Kusan 37mnts kafin da k’yar ya ce ta share hawaye ta maida glass kada su goggo su zargi wani abu suje tafiyarsu sai jibi zasu dawo washegari su koma Canada

A hankali ta mik’e yanata mata addu’a da fatan nasara da albarka ta fito tayiwa su goggo sallama ta k’arasa tuni Armando mota Ammah bata tashiba kuma dama k’aida in tana bacci ba’a tashinta saita tashi da kanta

Tana shiga Armando ya d’an kalleta ya gano yadda idanunta duk sun kumbure baice komai ba driver ya tayar suka bar gidan.. A hanya ma ko k’ala ta kasa yi da Armando sai sharar hawaye lokaci zuwa lokaci Armando ma ya k’yaleta yanata aiki a system d’insa har suka shiga birnin gwari..

Haka hayfa da Yusuf ke waya koda yaushe yayinda ta ita da Armando sosai suka samu nasarar aikinsu a duk k’auyukan sannan aikin gidan foundation d’insu yafara nisa gobe zasu bar Nigeria inda ammah taso ayiwa hayfa lalle hayfa ta qi gudun kada Yusuf ya zargi komai tayi dai kitso mai kyaw k’anana sai uban kayan mata da Ammah ta jibgo mata lodi guda tun daga Maiduguri ta aikawa wata y’ar uwar babnsu kud’i 250k ta had’Iowa hayfa ga tsimi duk tayi mata hayfa kam ta tsumu tayi tsam ba  magana..

A gefe hayfa sunyita waya da Aliy saidai bata samu ganinsa ba ta tura masa 500k tace yayiwa su Inna da su qassem hidima yayi mata godiya a madadin su Inna tunda bataso kowa yasan abinda take

Gobe zasu bi jirgin dare ansha hira an gaji Ammah taje kasuwa sabida nx wk daddyn yara zai dawo sannan ga tafiyarya china itama, goggo sunje badarawa suna

Hayfa da Abba a harabar gidan Abba ya kalleta yace akwai maganar da dama na ke so muyi mai muhimmanci amma koda wasa kada ki bari y’an uwanki su sani.. Toh tace tana d’an sunkwi da kai k’asa

Yace ban tab’a baki labarin asalinki ba sabida ganin yadda y’an uwanki suke k’ok’ari a kanki tun tasowarki amma a y’an baya-bayan nan sosai na ke mafarki da kakanki wanda tabbas nayi masa alkawari bayan aurena da mahaifiyarki cewa idan har muka samu zuri’a zan sanar da su komai na daga asalinsu wanda ya rok’eni sosai akan kada na bari zuri’arsa ta k’are ba tare da mun nemo koda tsatson y’an uwansa ba ..

Kakanki Sunansa Haruna amma yace ainihin sunansa “Inzo Haruna”  yace su shida ne wajen iyayensu maza biyar mace d’aya buzaye ne na Niger inda suna zaune wani k’auye na marad’i y’an ta’adda ne suka dami k’auyen sosai suna musu satar rak’uma da k’ananan dabbobi daga k’arshe suka fara kashe mazaje suna aure musu mata sannan suna yiwa yaransu mata fyade suna d’aukar yaransu maza suna koyar da su ta’addanci wannan dalilin yasa mahaifinsu kakanki ya yanke shawarar gudu tare da iyalinsa inda ya yanke hukuncin shigowa Nigeria.

Koda suka shigo Nigeria sai motarsu ta samu matsala a wani k’auye mai suna “dogon daji” can a sokoto saidai bayan motarsu ta tsaya tasha ana gyaranta duk yunwa da gajiya ya damu kakanki da iyayensa da y’an uwansa saidai su ganin guzirinsu da kud’insu ya k’are duk suka daure a yayinda kakanki ya tsananta rigimar yanason cin abinci wanda hakan yasa y’an uwansa suka far masa sunata fad’a na sangartarsa da ya saba ya manta halin da suke ciki na halin tafiya.. ana haka duk y’an uwansa aka gama gyaran mota suka shiga inda kakanki ya hango wasu masu saida abinci ya bisu.. Kamar da wasa y’an uwansa suka fara nemansa mota zata tashi domin dama babansu burinsa su yi masauki Malumfashi sabida akwai mutumin da ya sani a can

Saidai babu shi babu alamunsa haka suka sauka mota suka bazama nemansa hankali a tashe mahaifiyarsa na ta kuka da yayarsa a k’arshe haka dare yayi musu.. A yayinda shi kuma bayan ya k’oshi ya dawo saidai wayan babu danginsa babu motarsu haka yayi ta kuka wani mutum ya ganshi a tasha ya tanbayeshi dama ina zasu je da dangin nasa yace masa malumfashi mutumin ya saka shi a motar malumfashi ya wuce da nufin ya Gano danginsa.. Koda ya isa malumfashi haka yayi ta garari a tasha har kusan magrib Allah ya had’ashi da wani bawan Allah da ya d’aukeshi zuwa gidansa shima mutumin ainihinsa d’an Niger ne a Niamey saidai haka suka yita neman dangin kakanki shiru kamar da wasa lokaci yayi ta tafiya babu wani labari inda shi kuma ya nace cewa tabbas babansa malumfashi yace zasu zo gurin wani mutum da haka shekaru suka tafi sosai kakanki ya fara makaranta ya gama tare da yaran mutumin su biyu musa da tanimu haka suka tashi tare inda suke zuwa kasuwa aiki shagon wani attajiri da haka Allah ya k’ara bawa alhaji haihiwa inda aka haifi Takwararki “Hadiza” bayan hadiza na da shekaru 15 babanta ya yanke hukuncin had’ata aure da kakanki sabida kwantar masa da hankali akan damuwar rashin gano danginsa har wannan lokacin da haka suke zaune suna rayuwarsu a nan kusa da gidan iyayenta inda suma yayyunta ko wannensu yayi aure saida suka shafe 8yrs kafin Allah ya basu haihuwa aka haifi mahaifiyarki tun bayan haihuwarta kuma shiru inda hakan ke damun kakanki sosai sabida bashida burin da ya wuce ya tara iyalai a ganinsa hakan ne kawai zai sanya masa jin sauqin ciwon da yake dashi a zuciyarsa na rashin danginsa… d’an shiru yayi yana kallon hayfa da tunda ya fara labarin kuka take a hankali yaci gaba babu wani buri da naga kakanki dashi har ya koma ga Allah yana dashi irin gano danginsa da kuma tara zuri’a mai yaw a sosai yanason yara.. Ana haka baban kakarki ya kwanta rashin lafiya Na ajali inda ya rok’i kakanki da koda zai koma Niger neman danginsa kada ya rabu da kakarki kakanki yace ya masa alkawari.. Bayan kwanaki Allah yayi masa rasuwa wata 17 bayan rasuwarsa kakanki ya tara y’an uwan matarsa yace shi zai bazama neman danginsa ko ina cikin fad’in Nigeria suma da sunki amma daga k’arshe suka k’yaleshi da ganin ma bai nemi a bawa kakarki gadonta ba  da haka suka bar malumfashi zuwa funtua shekararsu 2 a funtuwa nan ma babu labari ya shiga Kano nan ma shiru yayi baushi nan ma haka ya shiga kebbi ke ya zaga dayawan garuruw babu labari, Sai a Yobe ne wani ya bashi shawarar shigowa Kaduna cewa a Kaduna buzaye na nan sosai suna aikin gadi mai yiwuwa suna can cike da farin ciki da fatan nasara ya shigo Kaduna inda ya fara aiki wani gida a “Ja Abdulqadir u/Rimi” daga nan yayi aiki katuru rd shekarsa daga nan ya dawo gidan wani tsohon soja a badarawa inda har Allah ya taimakeshi sojan ya bashi gidan kusa damu na badarawa wanda na wasu ne gado sojan ya sayawa kakanki sabida yadda yake jin dad’in aiki dashi a loakcin ne muka fara sabawa dashi dukda ya d’an girme min sosai saidai mutum ne mai barkwanci da girmama kowa da haka har matarsa ta kwanta rashin lafiya goggonku ce ma tayi jinyarta har Allah ya mata rasuwa bayan rasuwarta ma goggo ke kula da mamarki kasancewar da kad’an Suwaiba ta girmeta da haka ne kakanki ya nemi da in aureta ganin shima a lokacin yau fari gobe bak’i.. D’an d’agowa yayi hayfa na kuka sosai.. Yaci gaba tun bayan aurenki na fara neman maki danginki amma zuwa yanzu babu abinda na samu saidai nayi alkawarin zanje sokoto IA bayan anyi hutun makaranta na yara amma banaso y’an uwanki susan komai har sai bayan burinmu ya cika, ya barmin sunayen duk y’an uwansa da iyayensu na rubuta zan kuma baki ki tafi dashi ki adana da kywa, Sannan ki adana da kyaw ni kamar yadda na fad’a miki da anyi hutu zamu shiga sokoto sannan duk halin da ake ciki zan rik’a sanar da ke, ki kwantar da hamkalinki ki rik’e mijinki tsakani da Allah shi arziki daga Allah ne yana bawa wanda yaga dama a lokacin da yaga dama sannan kiyi duk k’ok’arin da za kiyi wajen kiyaye sirrin aikin ki daga gurin mijinki har y’an uwanki zanci gaba da yi miki addu’a Allah ya bud’a masa wata k’ila kafin ku dawo Nigeria Allah ya sa sun canza tunaninsu akan dole sai kina auren mai kud’i kuke da mutunci…. Har yanzu hayfa kuka ta keyi da kyar ya lallasheta ta mik’e ta koma zuwa sashinsu inda shima ya sake fad’awa tunani na rayuwar yarinyar tasa..

STORY CONTINUES BELOW

Zama tayi kan kujerar d’akin ta kulle k’ofar ta fara wani sabon kuka na yadda lokaci d’aya abubuwa suka fara rikice mata ta ko’ina sosai tayi kuka har bacci ya d’auketa….

Armando da driver sunsha yawo sunje “Gamji, Kauna garden, Dallema, dadai a lot gurare sannan yayi sayayyar tsaraba harda su Raudha da Liliana da Fabiola duk ya musu tsaraba kafin suka nufo gida inda ya bawa driver kyatar 100k yanata godiya.. Ammah ma gara ta k’ara yiwa hayfa kamar hauka kayan abincin gargajiya sosai sai danbun nama, Kifi, kaza, yaji kulikuli daddawa zogale yakuwa dadai kaya makil akwai uku zallan kayan abinci sai… Sai wajajen 7:23pm hayfa ta farka daga baccin wahala da bakin ciki ga ciwon kai da kyar ta shiga tayi wanka ta shirya ta sakko ammah bata dawo ba yara na gidan suwaiba zama tayi dinning ta d’anci abu a dole sabida yadda yunwa ta addabeta tun brk da tayi… Tana zaune Armando ya shigo cike da nishad’i da farin ciki yace “queen garinku akwai dad’i” lol Kaduna akwai dad’i.. d’an murmushi tayi saidai ta kasa magana shima yanayinya da ya gani tun shekaran jiya baya cika tsawaita yi mata magana.. Zama yayi dinning ya fara zuba abunci yace “queen y’ar soyayya mijinki kike missing haka kika koma kamar mai jinya”..? da sauri tace ah ah kwana biyu bana jin dad’in jikina ne..! OK yace gajiya ce kimasan duk watannin nan bamu huta ba ni kaina after Gala zan wuce Melbourne gurin mamana na huta 2wks… Murmushi kawai tayi.. Yace kuna waya da shi ko..? Girgiza kai tayi kawai, .. Yace shi yaushe zai dawo..? Tace nan da 3dys..!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Yace OK kan nan kin huta sai ki shirya honnymoon.. D’an murmushi tayi kawai a haka dai suna d’an tab’a hira suna cin abinci har suka gama ya wuce b’angarensa ta koma sama tana zaune shiru tunani babu wanda bata yi taji an bud’e k’ofar ta d’ago sai taga Ammah shiga tayi tana cewa “y’an matana ya gajiyar ce”..? Eh hayfa tace tana mata sannu da zuwa.. Zama tayi kusa da hayfan ta d’ago fuskarta tana kallo cikin yanayin kulawa tace “y’an matana mai ya faru”..? Kamar kinyi kuka idanunki duk sun tsume ko kewar mu kika fara tun yanzu.? Girgiza kai tayi alamar eh.. Ammah tace kiyi hakuri auren kenan kinga mijinki ba k’aramin k’ok’ari yayi ba ya barki kika zo da sauri haka.. Inaso ki kwantar da halalinki ki k’ara rik’e mijinki kinji..? Kiyita hak’uri da biyyaya kina kyawtata masa hakan ne zai sa ya k’ara sonki kuma kina masa girki da kanki na saya miki littafin “Akushi da Rufi” akwai dukkan girkin arewa na gargajiya ki rik’a yi masa kada kina yadda mai aikinki tana masa hidimar komai sabida in kinayi masa da kanki darajar ki k’aruwa za ta rik’ayi a gunsa kullum kinji..? Kallonta kawai hayfa take tana hawaye domin tasan duk mai yasa take bata wannan irin nasihar.. Haka ammah tayi tayiwa hayfa nasiha da koyar da ita yadda Zata k’ara cusa kanta a zuciyar Yusuf…

Allah ya kyawta shi miji mai kud’i kullum ana tunanin yadda za a k’ara mallakarsa ne sab’anin talaka..!

Saida ammah ta shafe kusan 2hrs tana way area hayfa kai sosai akan sirrin rik’e miji da mallakar ziciyarsa ba boka bare malam bayan nan tace suje d’akinta inda ta bawa hayfa k’aramar kitt dake cike da kayan mata na sha da fruits da madara. Inda ko wanne da bayaninsa a jikin kwalbarsa… Sannan ta k’ara yiwa hayfa fad’a da nuna mata ta zaman aure “mu kashe mu binne ne ke da miji”..! Koda wasa kada ki yadda hirar komai na aurenki da k’awayenki nasan kina chatting da su ki kiyaye kinji..? Girgiza kai tayi tana hawaye.. Haka suka k’arasa hira laraba ta kawowa Ammah abinci a d’aki inda ammah ta tilasta hayfa ta d’an k’ara ci kafin suka yi shirin bacci yara duk gidan suwaiba zasu kwana wai ana walimar Marwan autan suwaibar ..

Hayfa na son kiransa amma dole ta hak’ura sabida yadda Ammah ta maida hankali kada ta gano wani abu a tare da ita.. Haka har bacci ya kwasheta wanda rabi da rabi ne kawai baccin.. Yayinda cikin baccin take jin yadda ammah ke waya da mijinta suna soyayya kamar zata had’iyeshi tasha tunani yadda ammah ke nunawa mijinta soyayya duk kuwa da kasancewarsa talaka ammah ita sun tsananta mata k’in auren talaka saidai a yanzu gaba d’aya al’amuran rayuwarta sun fara rud’ata ta kasa gane ina zata dosa tana jinsu sunkai 2hrs suna waya kafin su kayi sallama itama ammah ta kwanta…

Gidan liliana

Raudha ta kalli liliana tace ” wallahi ko yaya zanyi dole zuwa wannan lokacin na maida burina na mallaki guy d’in nan ki duba yaushe rabona da yin sex kuma duk sabida shi.. dariya liliana ta saki tace gaskiya ranar gamonku ba  zaki raga masa ba .. Raudha tace ay nima bazan so shima ya ragamin ba.. Liliana tace toh yanzu ke yaya kike shirin b’ullowa abin..? D’an ajiyar zuciya raudha tayi kafin tace abin ne kamar yanaso yamin yawa ga shegiyar nan kinga gala sai k’ara matsowa yake har yanzu bansan yadda nayi da ita ba kafin vote sabida walla hi bazan bari taci ba ina nan koda ban samu ba bazan bari ta samu ba … Liliana tace tuntuni nayi wani tunani akan khadija na matakin da zamu d’auka indai bamu so ta samu bangon Gala.. Da sauri raudha tace “me”? Liliana tace mu had’a baki Suarez da Viviane… Raudha tace kamar yaya? Liliana tace ya zama ko wani abincin Khadija tana dafawa da “Vodkha” kinsan yadda yake saurin bin jikin mutum yadda ita da kanta cikin k’ank’anin lokaci zata jarabtu ta fara nema tana sha kinga cikin sauk’i mun fara susutata kafin mu nema hanya ta k’arshe sai Suarez mu tabbatar yana sakaci wajen bata aikinta na exercise yadda in taje audition Bunill zai fara complain hakan yasa ya fara kokwanton anya za a sata a campaign d’in Gala kinga shikenan da wuya ta samu shiga campaign d’in bare har ta samu Gala

Wani irin wawan duka raudha ta kaiwa liliana a baya tana dariya tace “kai shegiya ashe da gaske dama soyayyar nadal ke dak’ushe miki tunani kamar yadda Armando ya tab’a fad’a.. B’ata fuska liliana tayi tace wlh zan janye in kina tayarmin da tabona.. Da sauri raudha tace to ayafemin amma gaskiya kinyi kokari sosai yanzu to shi jarumina ya kike ganin zan b’ullo masa..? D’an ajiyar zuciya tayi kafin tace kinsan African suna son mace na musu biyayya so kici gaba da binsa a hakali zuwa a yi campaign na Gala in kika samu sai musan abin yi a kansa shima amma yanzu mu maida hankali akan khadija sabida wallahi yarinyar mugun farin jini ne da ita in bamuyi kokari munyi mun ruguzata ba muna ji muna gani zata fara aiki da su Giselle bunchell da Naome cambell da Kimora Lee Simons alhalin mun rigata shigowa munafikin nan ya maida hankali a kanta sai samo mata aiki yake ki duba yadda gidan sarautar Saudi basu bawa sababin fuska aiki komai k’ank’antar aikin amma Armando sai da ya saka aka bata aikin nan shiasa kikaga nima tsanar yarinyar ya k’arumin a zuciya ga shi kansa Suarez yayi ta damunmu wai ta fimu nutsuwa da maida hankali akan aiki.. Raudha tace a toh gara da kika gani da kanki.. Haka suka ci gaba da mugun shirinsu akan hayfa inda suka yanke hukuncin zuwa gun Viviana kafin Liliana tace za tayi seducting d’insa suyi sex da haka zasu rik’a blackmailing d’insa yana musu abinda suke so..

Tunda ta tashi suka gaisa da ammah ta wuce d’akinta ta fara shirya kayanta, sai wajen 11am yara duk suka dawo suka wuce dukkansu b’angaren su bgoggo harda suwaiba da ammah inda iyayen su kayita yi musu nasiha har asar akaci abinci akayi sallah Armando yazo ya iskesu yayiwa yaran rabon kud’i sosai kafin kowa ya k’ara shiri aka d’unguma abuja rako su hayfa motar suwaiba ta ammah ta gida….

Sun dad’e a airport kafin aka fara kiran matafiya inda a kasha kuka aka fara bankwana sosai hayfa ke kuka suka runguma sosai da babanta a karon farko a rayuwarta ta tsinci kanta da jin wani irin kewarsa d’an kusan ci da suka samu a y’an kwanakin nan da basu tab’a samu ba iya rayiwarta da shi.. A hankali ya rad’a mata “ki kiyaye duk abinda na fad’a miki Allah yayi miki albarka” a hankali ta ansa amin ta d’ago ta kama hanya bata ko k’ara juyowa ba saidai su sunata d’aga mata hannu har suka shiga a yayinda kowa ya wuce sai Abba da ya dad’e tsaye yana hangota tana mik’a takardunta ga security har ta gama ta wuce kafin yayi ajiyar zuciya ya juya shima..

Tana jirgin hankalinta na kan abubuwan da suka faru tun ranar da ta shigo Nigeria kwata-kwata kamar rayuwarta ta canza take ji kamar da can ba rayiwa take ba yanzu ne zata fara rayuwa hawaye ta matse mai d’umi tana tariyo tarihinta da babanta ya bata tabbas ita k’ask’antaciya jikar mai gadi y’ar mai gyaran agogo ya akayi ta manta haka tun farko ta d’auki girman kai da buri tasa a rayuwarta wanda gashi hakan yasa a k’arshe ba ma ta auri wanda ke hauka a kanta ba sai wanda aka d’auki alhakinsa wajen yi masa asiri domin ya aureta.. Wani irin kuka ta saki da har turawan da ke gefenta suka fara kallonta da tausayawa ganin dama tunda ta shiga jirgin take hawaye Sosai take kuka a can gefenta wani bak’in fata matashi kamar bahaushe ne ya furta “ki daure ki bar kukan haka ko mai yake damunki ki barwa Allah”..!

Armando ne ya hangosu ya taso yazo ya kalli matashin ya mik’a masa hannu suka gaisa yace ” Armando”..! Matashin yace “Haruna” Armando yace pls ka tayani tanason kashe kanta domin ina tabbatar maka tafi 5dys aikin da take yi kenan.. Baturen da ke kusa da Haruna ganin Armando ya mik’e ya bawa Armando gurinsa ya koma na Armando inda hira ta b’arke taakaninsu.. Shi haruna d’an Malumfashi ne yana PHD d’insa a nan Toronto sunata hira hayfa batasan ma mai suke yi ba  inda haruna da Armando suka yi musayar number, Haka suke ta hirarsu yayinda shi Haruna ya kan saci kallon hayfa cike da tunani kala-kala.. Na farko shi yana karanta international relations ne so yana karatun jaridu da magazines sosai na duniya kuma ya tabbata yasan fuskar hayfa a magazine sannan akwai yanayi da ya tsinci kansa a kallon farko da yayi mata wani kusanci wani alaqa haka kawai tun shigowarsu jirgin ita da Armando wanda yanzu a zucoyarsa yana godewa Allah da Armando ya kasance mai son mutane domin zaiyi anfani da wannan wajen kusantarta da saninta..

Yusuf da suna can wani k’auyen kusa da Ontario aiki suke sosai saidai kwata-kwata baya cikin mood na rashin sanin dalilin rashin kiran hayfa tun jiya yau ga yamma na yi still shiru shi baya son ko yaushe yana saka yasir cikin sabgarsu kuma bayada number Clara a dole ya hak’ura saidai sosai yake fushi da ita idan har lafiya qalau amma bata neme shi ba bayan tasan shi baya iya samunta..

Sai kusan 11:pm suka dawo masauki duk a gajiye domin hatta bud’a baki ma a waje su kayi duk suka baje a falo Mahfuz ne suka d’an fara sabawa da Yusuf ya kalleshi yace “kanada damuwa”..? Yusuf yayi ajiyar zuciya yace no kawai gajiya inason nayi bacci..! Mahfuz yace nima haka amma dole zan duba wani assignment d’ina sabida inason canza course nx yr IA… Yusuf yace wani course kake yanzu..? Yace Industrial engineering saidai wlh ina wahala.. Yusuf yayi ajiyar zuciya yayi shiru sosai yake son karatu saidai sam har yanzu baiga ta yaya zai fara ba.. Mahfuz ne ya tab’oshi yace kai wani course kake..? Yusuf yayi ajiyar zuciya yace ban koma karatu ba tukuna.. Cikin jimami mahfuz yace “why”? Yusuf yace hidimomi sunyi yawa saina k’ara kintsawa.. Mahfuz yace idan kabi ta hidimomin rayuwa wlh ba  zaka yi karatu ba sabida mutum kllm cikin hidimomi yake, ka ganni inada mata da yarinya d’aya ga mamana ga k’anina k’arami babanmu soja ne ya rasu amma munada gidanmu a nan kusa da masallaci ni nake kula da iyalai da dangina saidai tabbas muna samun sauqi domin gomnati na taimaka mana amma hidimar kai da komowa inda zanbi wannan da nauyi uba da miji da ya hau kaina da ba  zanyi karatu ba sam.. Zan baka shawara a masallaci suna bada schoolaship ko wani shekara wannan shekarar ma sallah saura 5dys zasu fitar ka gwada sa’arka.. Ajiyar zuciya Yusuf yayi ya kalli mahfuz to amma ni har yanzu ban riga na samu takardar zama d’an k’asa ba kana ganin zasu bani..? Mahfuz yace ay sunfi bawa bak’i dama ka yiwa Hamzad magana zai taimaka maka yadda zaka cike komai IA zaka dace.. Yusuf bai tab’a kasancewa cikin farin ciki ba tun barinsa Toronto kamar yau sannan duk fushin da yake da hayfa yaji ya gushe illa fatan Allah yasa ya gwada a SAA.

11:07am agogon Toronto su hayfa suka sauka duk tayi laushi ga azababen ciwon kai a haka suka fito Haruna da Armando tana biye da su a baya tuni motar kamfani tazo d’aukarsu inda Armando suka yi sallama da haruna da fatan sai sun had’u hayfa ko kallon inda harunan yake ba tayi ba bayan wucewarsa a taxi Armando ya tanbayi hayfa ina za a kaita tace gidan Clara direct a motar ma k’ala bata ce ba  har suka iso gidan Clara Armando ya kalleta yace “queen a huta gajiya” sai munyi waya to kawai tace ta shige shima driver ya wuce dashi..

STORY CONTINUES BELOW

Liliana tayi nasarar d’anawa Suarez tarko inda ta bashi appointment a gidanta cewa akwai bak’i da suke so ya rik’a basu aiki zata gabatar masa da su kada a gani a kamfani a fad’awa Armando ko bunill bai zargi komai ba yace “toh” inda tace yazo yayi launch da b’akin..

Inda ita kuma raudha ta d’anawa vivian tarko cewa tasan tana satar kayan abincin kamfani tana kaiwa gida bata cefane so in bata yi mata abinda take so ba zasu tona mata asiri kuma tasan halin bunill korarta zaiyi a dole Vivian ta amince saidai sosai take tausayin hayfa domin tana mata ihsani tym to tym haka kawai ko bata sata aiki ba

Inda Raudha ta fad’a mata doses d’in da zata rik’a zubawa hayfa har a coffee domin so suke ta gigice da wuri kafin sunayen campaign na Gala ya fito kuma duka-duka saura 5wks ya fito Vivian tace toh inda raudha tace in kinyi aiki da kyaw za kiga sakamakon da zan miki kuma dole ki kiyaye yadda za a zarge ki ko yaya ne tunda kowa yasan abinci mu tare kike yi duka kin gane ay..? Vivian jiki a mace tace “eh”..!

Tunda ta isa gidan tayi wanka ta kwanta shiru domin sai jiya ta gama jininta da bata gane tsarinsa ba kasancewar tayi period b4 sumanta da kwanciyarta a asibiti kafin tayi tafiya.. Shiru tana kwance tana tunani komai na dawo mata kamar film tun ranar da ta shigo Toronto.. Hawaye take tana tanbayar kanta shin yaya zata gano gaskiyar tsakaninta da shi “yana cikin hayyacinsa ne ko har yanzu suna rayiwa ne bisa asirin da aka masa”.. Sosai take hawaye a hankali ta mik’e ta d’auki hand bag d’inta ta ciro sim d’inta na Canada ta saka tayi shiru na lokaci kafin ta jefa layinsa…

Suna wata unguwa anyi layi sosai na maza daban na mata daban na tsofaffi daban sunata rabon wayarsa ta fara ringing ya share yaci gaba da aikinsa sai da ya tsinke ta kuma jefawa har ya tsinke still bai d’aga ba ta ajiye wayar ta yi tagumi ita sam yanzu bata san ya za tayi ta k’ara sakin jikinta da shi ba alhalin bata san haqiqanin matsayinta a rayuwarsa da zuciyarsa ba.. Tana nan zaune sabida Clara sai 5 zata dawo komawa tayi ta kwanta tanajin yunwa amma batajin zata iya had’iyar komai dole ta koma ta k’ara kwanciya ba zata kira gida ba yanzu domin su dare ne k’ila suna tarawih kuma batajin yin magana da kowa bayan “mijinta”..!

Sai daf magrib suka gama aikin rabon gobe suka k’arasa jibi su dawo murna yake sosai yayi missing d’inta saidai dole ya hukuntata na shareshi da itama take tunda yayi tafiya..

Clara tunda ta dawo taga yanayin hayfa sunyi hira amma ba sosai ba Clara ta mata sallama tace zata gidansu babanta na son ganinta ta wuce hayfa na ta mamakin rashin kiran yusuf kodai sihirin ya kwance ya daina sonta innalillahi ta fara nanatawa tana hawaye ta na shiga uku ta furta tana sakin kuka mai ban tausayi kenan yanzu haka za tayi ta rayuwa dashi cikin fargabar kada sihiri ya kwance ya saketa ko ya daina sonta.. Wani irin mugun ciwo kanta ke yi ga zazzab’i mai tsanani da taji ya far mata ta kwanta tana fidda numfashi mai zafi haka hawaye shima yana bin kumatunta

Bayan tarawih yana tsananin son jin muryarta ya share shima idan har zata iya jure kwana da wuni ba tare da taji muryarsa ba ya kamata nima na jure saidai ba kad’an ba zuciyarsa ke kewarta tare da k’ara rura masa wutar sonta da haka yayi shirin bacci ya kwanta cike da tunaninta su mahfuz na waje suna shan shayi suna fira..

Koda Clara ta dawo tayi mamakin jin gidan shiru ko hayfa ta fita saidai ta bushe ganin hayfa da ke k’udundune tana rawar sanyi ga fuskarta duk ta k’ara kumburewa fiye da d’azu da alama tana cikin damuwa da sauri ta k’arasa ta tab’a goshinta mugun zafin da taji ya firgitata ta ma rasa mai za tayi da sauri ta lalaubi wayarta tanada lambar Yusuf sabida itama lokacin da Yusuf ke aiki café suna shiri shi da ita hakan yasa ta kamu da b’oyayyiyar soyayyarsa.. Jefa lambarsa tayi Yusuf da bacci ya fara d’aukarsa yaji ringing baiso d’agawa ba amma ganin lambar Clara ya d’aga.. Ko gaisheshi ba tayi ba  ta fara magana” khadija ba tada lafiya temperature d’inta yayi sama sosai na rasa mai zanyi”.. Sosai yaji hankalinsa ya tashi yace ki kaita asibiti zan turo miki address zan yiwa Sebastian magana zai muku komai ta accnt na supermarket ki kaita yanzu pls.. toh tace tana kashe wayar, sake kiranta yay I yace ki sanar dani komai in kuka isa pls “toh” tace ta kashe wayar tana mik’ar da hayfa da sam ta jigata sosai da zazzab’i, Ko bayan ya kashe wayar idanunsa bushewa su kayi gajiyar ma gushewa yaji tayi burinsa kawai ya ganshi kusa da ita yana kula da ita.. Mik’ewa yayi da kyaw ya jingina bayansa da gadon ya kama kansa yana jin kamar ya runtse idanunsa ya bud’e ya ganshi tare da ita…. Wani irin mutuwar sonta ya keji yana fisgarsa ta yadda labarin ciwonta yanzu ya sanya shima yaji zazzab’i na shirin dirar masa…

koda suka isa asibitin aka basu d’aki inda Likita ya duba hayfa ya fad’awa Clara stress ne da rashin bacci aka d’ora mata drip nan da nan ta samu bacci inda Clara ta mata pic ta turawa Yusuf.. Yana zaune yaji shigowar saqon ya bud’e wani irin ajiyar zuciya yayi yana lumshe shanyayyun idanunsa a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta da ta wani zube gaba kamar tayi wata cikin rashin lafiya.. Sosai yake kallon hoton yana ji kamar ya je ya cire mata ciwon…. Kusan 10mnts yana kallonta tare da jin wani irin ciwo shima a zuciyarsa na rashin kasancewa kusa da ita a irin wannan lokacin da zata fi vuqatarsa..

Kiran Clara yayi ta ce masa tana bacci kuma Dr yace zata jima tana baccin suka yi sallama akan in ta tashi ta kirashi..

First Bank yakubu Gowon way Kaduna..!

Yana zaune makeken office d’insa duk tunani ya isheshi tun 18 da hayfa tayi aure bai k’ara kasancewa cikin farin ciki ba tun ranar da mijinta yayi masa wulakanci.. Ajiyar zuciya yayi tabbas ko wace hanya zaibi sai yabi ya dawo da farin cikin sa wato Hayfa”

Yana cikin tunanin aka qonqonsa k’ofar office d’insa aka shiga.. d’an kallonsa yayi yace..” Dude ya wai ka gama duba fayell d’in nan kuwa”..? D’an tsaki Kamal yayi yace No sai zuwa ajuma.. D’ayan yace haba Oga pls ka duba yanzu mana mutumin zai shigo anjuma kasan jiya nayiwa da mai Foundation d’in Email kasan d’an Canada ne amma wai project d’in shi da wata yarinya ne y’ar nan Kaduna…. wani irin d’agowa Kamal yayi jin an kira Canada yana kallon abokin aikin na sa yace.. Canada..? Eh Abdulmalik yace tun zuwan Baturen bayan da Alhaji Hassan baba estate ya had’ani da shi kasan hannunsa wai baturen ya saya gidan da suke ginin foundation wanda project d’in na masarautar Saudi ne saidai shi baturen da wata yarinya y’ar nan Kaduna ke jagorantar project d’in domin yarinyar ce ma ambassador na Foundation d’in hakan yasa bayan sun saya gidan hannun Hassan Baba estate ya bawa baturen  shawara su bamu congilar ginin kasancewar shi yanada accnt da mu hakan zai k’ara taimakawa “Hassan baba estate” benefits da mu.. Ajiyar zuciya Kamal yayi da sauri ya kalli abdulmalik yace ka bani 30mnts zan gama dubawa.. Mik’ewa Abdulmalik yayi ya masa sallama ya bar office d’in inda Kamal har rawa hannunsa yake yayin jawo fayell d’in sabida wani abu da yaji ya d’arsu masa a zuciya tunda a ka anbaci Canada

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]