[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 16

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zaune inaaya take hankali kwance tana kallonta taji karan kofa ana knocking ta tashi a hankali ta nufa ta bude kofan wa inda ta gani ne tsaya ya sa ta ihu tana tsalle tana rungume su a tare Aminnan nata ne inteesar da sultaana da mimi sai ya khady tayi kusan 10days bata gansu ba dama duk kadaici ya isheta shiyasa tayi farin ciki sosai da ganin su mimi tace “ke malama sakemu kar mu koma sauran kuwa dariya sukayi mata yanda tayi da fuska kaman zatayi kuka khady tace “habaa inee kaman wata jaririya please let’s go in a tare suka shiga ciki suna murmushi a parlour suka zauna sai a lokacin suka gaisa inaaya na cewa “wallah you guys have the perfect timing dama I’m bored” kaman jira mimi take tace “dama married couple na zama bored” hitting dinta sultaana tayi tace

“corrupt lady” duk sukayi dariya, inaaya ta tashi ta nufa kitchen ta hado masu su ruwa da drinks da kayan motsa baki dai ta kawo ta ajiye masu tray din nan da nan suka hau ci dan dama ba bakon su bane gidan suna ci suna kallo suna labari. Sai da aka kira zuhr prayer sai ga aliyu ya sauko daga sama fuskan nan tasa neutral suka gaishesa ya amsa masu a sake ba laifi sannan ya nufa wurin kofan zaya fita yace “fateema come and close the door” sum sum ta tashi tabi bayansu su inteesar kuwa boye dariyar dasuke san yi sukayi, a tare suka isa wurin kofa ya bude zaya fita tace “Allah ya kiyaye” yace mata amin ba yabo ba fallasa har ya fita sai ya juyo kafin ta rufe kofa yace “uhmm please fareed is coming over for lunch can you cook something please” da dan Murmushi ta gyade kai tace “sure” sannan ta rufe ta nufa ciki su sultaana ke mata dariya wai tayi hankali yanzu ta iya ma miji rakiya ita kuwa sharesu kawai tayi sai tace “uhmm you guys please muyi sallah muzo kitchen ku tayani muyi lunch” mimi tace “ai mun dauka sayo miki akeyi har yanzu” dariya ya khady tayi tace “ku dai kun sa inaaya gaba ku tayata mana” inaaya na jin haka tace “kai ya khady har da ke fa” khady tace “lallai ma kinada aiki ni zani tayaku girki ba gidana ba” bata fuska inaaya tayi tace “ni ya khady ai bana yin lunch da yanzu sai dinner zanyi da yamma amma duk saboda ke ne yasa zaniyi kuma kice baki taya mu” yar dariya khady tayi tace “lallai ni ce glutton da zakice saboda ni zakiyi” inteesar tayi dariya tace “ahh to ai tasan mu bama ci” sultaana tace “help me see oo” inaaya tace “no ba wani glutton duk dalilin ki ne zaniyi girki ba husband to be dinki bane zayazo lunch kuma dan yasan kina nan shiyasa yace zayazo dan so daya ya taba zuwa gidan nan yanzu dalilinki yasa zayazo kinga dole ki taya” ai tun kafin inaaya ta gama maganan su mimi suka fara dariya mimi harda tafa hannu tace “ohh inee ke kuwa his heart his soul zayazo gani” khady kuwa har ta fara wani blushing kaman tana ganinsa sam ta kasa cewa komi ta barsu sunata fama teasing dinta a haka har sukaje sukayi sallah suka nufa kitchen inaaya tace “toh ya khady yanzu ki gaya mana favorite din na shi sai a dafa” khady tace “kun rainani dayawa yaran nan shaa biryani ko casserole da chicken salad da fruit parfait but na grapes preferably” inteesar tace “wow kiji love tasan komai kanshi” sultaana tace “love is cute” mimi tace “hmm bakusan its sweet bama tukunna” sunata dariya banda inaaya a gefe da ta shiga tunani kowa has a normal happy life banda ita Khady already knows alot about her husband to be da abunda yakeso but ita she can’t say ga abinci daya fi so apart from he likes zobo kaman tasa kuka haka taji tana tunanin wace irin rayuwa ce haka inteesar ta tabota tace “lafiya malama” tace “uhm..ahh..aa ba komai let’s get started ayi casserole din da biryani da salad and parfait and i have some cupcakes it’ll be for dessert mimi tace “cool lets get started ya khady tayi biryani din ni kuma da sultaana zamuyi casserole and inteesar should make the salad inaaya kuma parfait” haka sukayi deciding kowa da fara aikinsa inaaya tace ma inteesar “inteesar i already have marinated chicken kawai kiyi grilling dinshi” duk suka fara aikin nasu cikin two and half hours suka kammala sun fara jerawa a dining inaaya kaman ta tuna wani abu tace “ohh I have something to do” da ido kawai suka bi ta ta dauki karamin pot a wanke ta bude wani drawer a kitchen ta fiddo ganyen zobo ne ta zuba a ciki saida ta wanke shi sannan ta dora a wuta mimi tace “ohh abunda mijin naki keso kika manta kiyi shine harda sauri ohh ni aminatu aure me canza mutane” duk suka sa dariya inaaya ta daure tace “mimi mimi wlh ke ba hmm!” Nan ma dariya sukayi sultaana tace “ya kika kasa cewa komai inee” sukayi ta tsokanan ta cikin 20minutes ta gama hadan zobon tasa a jug tasa fridge sannan suka nufa sama zuwa dakin inaaya ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya cikin dogon riga na voile mint green da ash yayi kyau sosai khady tace “hmm dolen ya aliyu yayi drooling” sukayi dan dariya sannan ta kuma ce “kaii nima i need a bath I’m smelling kitchen” mimi tace “dama ya khady dolen ki tunda husby to be zayazo” share ta khady tayi ta shiga tayi wanka ta fito cikin closet din inaaya ta nemo wata sabuwan abaya maroon tasha stones ta saka sosai tayi kyau tana ta faman kallon mirror tana blushing.

STORY CONTINUES BELOW

Daga masallaci Aliyu direct gidansu yayi yaje gaida iyayen nasa bai jima ba sosai wurin 3:30 ya baro gidan saboda zuwan fareed har Ammah saida tace ya tsaya yaci lunch yace Aa har tana tsokanansa akan cewa yafi son abincin matarsa amma bai ce komi ba ya fito daga gidan daidai isowarsa gate yayi hon kenan gateman ya fara bude masa ta mirror din mota ya hango motan fareed ya shigo layin nasu kaman a tare haka yana shigowa shima fareed ya shigo da motan tasa yayi parking kusan a tare suka fito dan manly hug sukayi exchanging fareed da fara’a a fuskan sa yace “yane daga ina haka” aliyu yace masa yaje gaishe da Ammah a tare suka isa bakin kofan Aliyu ya danna doorbell din kusan 3minutes sannan aka bude masu kofan inaaya ce tsaye tayi kyau so simple ba wani makeup a tare da ita banda kohl da lipgloss amma saboda pink lips dinta sai yayi kaman ta sa lipstick ta daura dankwalinta ta sa Gyale har saman kyau son kowa kin wanda ya rasa, da kyakyawar fuskar ta Aliyu ya fara karo tana bude kofan he couldn’t help but stare and muttered MashaaAllah a cikin ransa fareed ne yayi gyaran muryan sai lokacin Aliyu yayi saurin shiga ciki tana cewa welcome, fareed yace “ahh amaryan mu sannu dai” dan Murmushi tayi kawai ta rufe kofan ta dawo a hankali take tafiya har sun isa parlour cikin natsuwa ta zauna sannan ta gaishe da fareed suka gaisa har ta dan tsokane shi tace “ya fareed mu dai ai mun san zuwan waye akayi wannan” Murmushi yayi harda blushing lol kitchen ta nufa ta kawo mishi refreshments sannan ta barsu ta nufa sama zuwa dakin nata tana shiga tace “ya khady bakon ki ya zo” hitting dinta khady tayi tace “wlh kun rainani yaran nan” sannan ta tashi tafita su mimi suka bi bayanta kusan a tare suka sauka kasa su mimi suka gaishe dashi har mimi na cewa “haba bro in law na daina ganin ka” yayi Murmushi yace “sis in law kina bacci kullum ina zan ganki” tayi yar dariya kawai suka koma sama banda khadyy da ta dan zauna a kunyace ta gaishesa fareed instead of ya ansa se cewa yayi “Babe babe kunya this is not you gaskiya when did we become this shy” Aliyu dake zaune gefensa yayi hitting dinsa yace “you’re a jerk wlh ko kunya bakaji wani babe a gabana” fareed ko a jikinsa dariya kawai yayi aliyu tashi yayi ya bar masu parlourn dan yasan fareed baya kunyanshi saidai ma shi yaji kunya. Basu jima ba sai ga aliyu ya dawo yace suje suyi sallah suka fita masallaci tare basuyi 20minutes ba suka dawo dayake masallacin tafiyan 3minutes ne da kafa bayan sun dawo Aliyu yace bismillah suyi lunch suka nufa dining a tare daidai lokacin da su inaaya suka sauko sun gama sallah duk dining din sukayi suka zauna banda inaaya da ta nufa wurin fridge ta dauko parfait din da akayi akasa a disposable cups tasa a tray tayi wurin dining din dashi ta ajiye sannan ta koma ta dauko zobon datayi kujera daya ne not occupied na gefen Aliyu haka taja ta zauna tana ajiye zobon kusa da shi ganin haka yasa ya dago ya kalleta suka kallo juna dan Murmushi ya sakan mata sannan ya juya, kowa serving kanshi yayi abunda yakeso suka fara ci in silence can midway to the lunch fareed yace “the person that made this biryani have blessed hands Wlh” da inaaya,intee,mimi and sultaana basu san sanda suka saki wata dariya ba and it got Khady blushing so hard mimi tace “bro kawai kace ka gane girkin your wifey to be” fareed yace “wow no wonder ashe ita tayi shiyasa nake jin wani exceptional feeling it was made with pure love” they couldn’t help but start awwwing banda inaaya da kawai dan Murmushi tayi, the rest of the day passed so fast but it was fun inaaya taji dadin having dinsu they had fun sosai sai 9 suka tafi inaaya duk ta gama night routine dinta ta tafi daki around 10:30 tayi bacci saboda gajiya ta bar Aliyu a parlour ta shige dakinta ta rufe kofan ta fada kan gado ta kunna data dinta ta shiga Twitter dinta ta fara scrolling tana ganin different tweets har past 11 sannan bacci sosai ya fara daukan ta ta kashe data ta ajiye wayan gefen ta tofa addua cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita.

*Two weeks later

Yau ta kama Wednesday ana gobe su Abbah da iyalanshi zasu koma Switzerland ciki harda Aliyu tun bayan zuhr prayer Aliyu suka fita da inaaya saboda bankwana da Ammah tasa yaje duk gidan yan uwansa yayi dan dama har kaduna sukaje gidan Baba a weekend din daya wuce, yanzu haka sunje gidan baffah da gidan Anty fareeha da ya aleesha yanzu suna a hanyan zuwa gidan Abbah wato gidan su aliyu, sun dan jima a gidan har sai bayan magrib sannan suka je gidansu inaaya wurin 8 sukabar gidan suka koma gidansu zuwa yanzu relationship din nasu is very ok cux inaaya yanzu ta daina tsoron sa sun saba daidai har fira suke sha shi dai aliyu kawai yana daurewa yana daukarta tamkar kanwarsa. Da suka dawo gida kowa daki ya nufa yana hada kayansa saboda inaaya tace ya barta ta koma gida tafison haka inda har iyayen nasu suka amince saboda tunda baya nan zaman kaidaicin me zatayi, ranar basuyi wata fira ba dan kowa was busy.Da safe karfe 9 aliyu ya tashi saboda 2:00 ne jirginsu direct fadawa yayi toilet yayi wanka ya shirya ya sauko kasa inaaya ce yaga ta fito kitchen dauke da mug hannunta tasaki murmushinta me kyau ta gaishe sa tace “Ya Aliyu dama yanzu zani kai maka coffee ashe har ka shirya shima ya dan murmusa yace “wow Thanks lil sis ai har na shirya” mika masa coffee din tayi suka nufa dining tare sukayi breakfast cikin sakewa har suka gama sai wurin 11 suka sa kayansu a mota suka nufa gidan su Aliyu duk su Ammah sun shirya suma da su mamii duk suna gidan don duk koma wa sai sun kai su airport gaishe da iyayen nasu sukayi cikin girmamawa suka amsa nan suka zauna sukayi having dan family time sai 12 suka nufa airport cikin motoci daban wannan karon inteesar da inaaya suka shiga mota daya dan kamar suyi kuka zasu rabu da juna na tsawon lokaci 12:40 suka isa airport din zama sukayi har saida aka kirasu nan waterworks din aminnan ya fara da mimi da inaaya da inteesar kamar wasu yara sukayi hugging juna suna hawaye Aliyu kallonsu yayi yana mamakin yarintar tasu Ammah ma rungume inaaya tayi tace “diyata ki kula mana da kanki kinji Allah yayi maki albarka” har kunya inaaya taji ta amsa da Amin Abbah ma ya ce “mamana ki kula da kanki kuma da kinyi hutu zaki zo kinjini ko” tace “eh abbah na” ya dan murmusa Ahmad kuwa sai faman tsokanan ta yakeyi tana basarwa kiran da aka karayi ne na passengers din flight dinsu yasa su sauri zasu tafi Ammah kaman jira take ta maka ma Aliyu harara sarai yasan me hakan ke nufi kaman yayi kuka ya ja kafa a hankali har kusa da inaaya ita kuwa dum! Dum! Gabanta ke cewa tarasa miyasa Aliyu ke da effect dinnan a kanta gab suke da juna har suna iya jiyo lumfashin juna Aliyu yace “you should take care lil sis and study well and also be good” nan take jikinta yayi wani sanyi ta rasa dalili sai kawai taji hawaye na sauko mata tana daga masa kai alamun Eh shi kuwa Aliyu ya daga hannu yace mata bye ya juya yayi gaba ita kuwa sai share hawaye takeyi wanda ita kanta ta rasa na miye 2:10 daidai jirginsu ya tashi duk sauran suka juya zasu koma gida inaaya with a heavy heart duk bayan wani lokaci sai taji hawaye sai ta goge tarasa gane kanta haka ta dinga yi har suka isa gida dakinta tayi direct tsab yake kaman yanda ta barshi da ta bar gidan kofan ta sa ma key ta fada kan gadon nata kawai ta fashe da wani matsanacin kuka tafi 30minutes tana kuka wanda ita kanta aka tambayeta na miye bata sani ba saida tayi me isarta sannan ta wanko fuskan ta ta dawo tayi sallah ta jawo wayanta ta duba whatsapp messages ta gani a group din su ka

Sultaana~heyy loves ina kuke I’m already missing intee

Mimi~she’s gone💔

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Sai kuma next Zuwa

Sultaana~wayyo intee i miss that beautiful soul🥺 btw where’s inee

Mimi~inee😂😂 hmm nata case din babba ne wai kinganta tana kuka zawj zaya tafi ta ma kasa controlling ina kallonta hawaye nata zubo mata

Sultaana~wow Allah sarki love kenan mimz i can even feel the pain she’s feeling ke kuwa her heart her soul zaya tafi bata san when next zasu hadu ba ai sai da kuka

Mimi~ I swear ba sai da kuka she’ll badly miss him she doesn’t know when next she’ll see him when next he’ll hug her so tight when next she’ll fell secured in his arms OMG😩❤️

Sultaana~laaaaa ohh ni hafsatu to wlh mimi kin girmeni ni kuwa

Duk da mood din inaaya saida tayi dan chuckling kadan ta kada kai tana mamakin halin aminnan nata nan ta nan tayi typing message

Inaaya~ kaii innalillahi wlh mimi aure kikeso corruption kadai a ranka kuma ni yaushe kikaga ina hawaye kawai damukayi hugging intee ne zanyi missing dinta shiyasa.

Ba bata lokaci nan da nan mimi tayi mata reply

Mimi~ehh mana zakiyi missing intee da yayan intee ko😂

Kasa replying dinta inaaya tayi ta kyale kawai, the rest of the day passed in a blur duk mostly inaaya na a daki duk sai taji gidan nasu ya mata wani iri saboda sabo da ta fara yi da gidan nata, tun 11 bacci nan da nan ya dauketa.

Few days later**

Karfe 6 inaaya ta tashi yau saboda lectures din da take dashi 8 shiri take da sauri amma cikin natsuwa yau Tuesday ta kama 5 days da tafiyan su Aliyu inaaya couldn’t help it tayi ma kanta admitting ma cewa kewan Aliyu take dan tun tafiyan su ta zata zaya kirata but shiru she has been expecting his call da wayanta yayi kara har sauri takeyi ta duba tun ranan da suka isa inteesar ta kirata sunyi waya taso ta tambayeta Aliyu amma ta kasa gashi duk abun ya dameta komi take sai ya fado mata a rai, ita ba maabociyar shan coffee ba Amma yanzu ta maidashi habit da ta tashi da safe sai ta hada ta sha kuma hakan ba kadan yake sa ta tuna da Aliyu ba, cikin sauri ta karasa shanye coffee din dake hannunta ta sauko kasa ta tarar da mamii zaune a table da twins suna breakfast cikin uniform din su na school gaishe da mamii tayi tana dan hugging din ta sai twins ma duk sukayi hugging din nata suna “good morning anty inee” da Murmushi ta amsa tana pinching cheeks din nasu sanan ta kalla mamii tace “mamii ina aneesah” mamii tace “aneesah sarkin bacci ta tashi tunda bata da school hutu takeyi sun gama BECE” Murmushi kawai inaaya tayi tace “ah dole kuwa,uhmm ni mamii bara na wuce kar nayi late lecturer din baya bari a shiga idan kayi late” mamii tace “to baki yin breakfast” tace “aa mamii na ci abincin a can” mamii tace mata “to Allah ya kiyaye” ta amsa da ameen tana fita daga gidan bakin motan Aliyu ta nufa da ya zama kaman nata tunda ita yabar ma wa saboda school, ta shiga ta tada tayi reverse ta fita daga  gidan nasu ta kama hanayan baze university 7:55 daidai ta isa har gaban department din nasu a hankali ta fito tana adjusting gyalen ta na abaya ta riko jakarta tasaka key din motan a jika da sauri sauri take tafiya tanason ta isa venue din before time taji sn kira sunan ta ko baa gaya mata ba tasan muryan waye ta juyo da fara’a tace “ihsannnn it’s you how comes na riga ki yau” ihsan tayi Murmushi ta danyi hugging din ta suka gaisa sannan suka nufa class tare a sit daya suka zauna 8:00 lecturer din ya shigo ya fara lectures din nasa sai 10:30 ya gama lectures din ya basu assignment ya fita, kaman suna jira ya fita kowa ya tashi ya fara tafiya inaaya tace ma ihsan “huh! I’m so hungry Ihsan please let’s go and eat something” Ihsan tace “nima fa kaman kin sani let’s go” sun tashi zasu tafi aka tari gabansu dagowa inaaya tayi taga waye wannan me isa daya taresu suna dagowa su ka ci karo da fuskan saifullahi yana masu Murmushi ihsan ce ta masa murmushi tace “saifiii how far shikenan da anyi hutu ba zumunci” Murmushi yayi yace “kaii habaa ihsan ai kune kuka boye” inaaya dake tsaye ya juyo ya kalla yace “hajiya fatima ba magana” dan kakalo murmushi tayi tace “ahh saifullah ya kake ya hutu” Murmushi yayi yace “Alhamdulillah mun gode Allah, shine ko gayya babu saidai muga hotunan biki to shikenan Allah yasa Alkhairi” inaaya mamaki ma tayi ina yaga pictures sai dai ta daure tayi masa Murmushi tace “Allah sarki kuyi hakuri nagode sosai” shima Murmushi yayi suka fara tafiya da shi da su inaaya dai shiru take shi kuwa sunata faman labari da ihsan har suka isa cafeteria sannan suka rabu yabi wata hanya suka shiga suka samu wuri suka zauna inaaya tayi order din chips da kidney sauce sai chapman ita kuwa ihsan tace bata iya cin chips yanzu fried rice tayi order da chicken da chapman inaaya saboda yunwa har ta fara cin abincin ita ihsan kuwa na rike da wayanta tanaa pressing can sai wayan yayi ringing ta dauka a hankali take maganan “hello love ohhk to gani nan zuwa” sai ta kashe ta kalli inaaya da itama idanunta na a kanta tace “inee ina zuwa please” da kallo kawai inaaya ta bi ta har ta fice. Tana fita ta hango shi tsaye bakin wani mota da Murmushi a fuskan ta ta karasa wurin shima ya sakin mata Murmushi yana cewa “my baby kin ganki kuwa” blushing ihsan tayi tana cewa “no tunda ka shigo school din da ka taba koyawa I’ll call you Dr Anwaar only” (ni kuwa nayi mutuwan tsaye inaso in kara tabbatar wa wai Dr anwaar na gani kuma yana kiran ihsan his baby) Murmushi yayi yace “no not acceptable I’ll only answer when you say love and as it is bakiji me kikace ba school din dana taba komawa which means yanzu ba nan nake ba so banida case dasu” tayi Murmushi tace “to lets go” a tare side ba side suka nufa cafeteria din. Inaaya na zaune tana cin abincin ta hankali kwance kaman ance ta daga kai taga ihsan tare da Dr anwaar na shigowa wurin ai ina mutuwan zaune tayi tama kasa rike fork din dake hannunta ta sake shi har suka karaso wurin kujera dr anwaar yaja ma ihsan ta zauna suka yi ma juna Murmushi sannan shima ya zauna murya na rawa inaaya tace “in..in…ina kwana sir” Murmushi yayi yace “fatima you can call me anwaar and lafiya lau ya school” tace “Alhamdulillah” ya juya ya kalla ihsan a hankali yace “babe I’m hungry” Murmushi tayi tace “chill mr glutton they’ll serve  you in no time” sukayi Murmushi inaaya kuwa zaune take kaman an dasa ta a wurin tama rasa me zatayi tunani ihsan and Dr anwar calling her baby she’s confused ma sai taji muryan Dr anwaar yace “so fatima ansha hidiman biki Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku zaman lafiya” kanta a kasa tace amin wurin shiru sai ihsan da anwaar da suke fira kasa kasa har suka gama cin abincin su suka gama dama sunada class 12 suna zaune nan har 11:30 sunata fita inaaya na kallonsu 11:30 ya tashi tafiya yayi ma inaaya sallama ya tafi ihsan ta rakashi ta dawo, kallon i need explanation inaaya tayi mata amma shiru bata ce komi ba sai can inaaya tace “ihsan kinsan ina bukatan karin bayanin abunda na gani ko” Murmushi Ihsan tayi tace “ohh Dr anwaar and i are dating we love each other” dan Murmushi inaaya tayi tace “Allah sarki shine ko ki gaya mani baki ma dauke ni kawa ba” Ihsan tace “habaa inee of course you’re my special kawa amma ni ai me sauki nayi ke da you got married and didn’t even think of telling me saida issue dinnan ya faru nima i was hurt wlh” inaaya tace “ohh to ramawa kikayi.. haba ni ai baki gane situation dina ba amma sorry kawata so yanzu gayamun ya akayi aka fara baby baby da love dinnan ban sani ba” blushing ihsan tayi tace “hmm wlh it all started after incident dinku bayan na kira mimi nayi confirming you’re married I felt bad for him but i did all I could to tell him in a polite way and consoled him from then I became like his buddy na dinga advising dinsa he became free with me ya gaya mun abunda ya sameshi na late wife dinsa ya bani tausayi sosai haka dai we became so close komai nashi yana gaya mun har yace he’s thinking of taking his old job anyi mishi proposing ya koma I supported him convinced him assured him that his wife and daughter are in better place ya yarda yayi resigning daga school dinnan ya koma aikinsa a NDIC har gidan mu yake zuwa har gaishe da mum ya taba yi we became so close sosai fa one faithful day he called me and was like let’s have lunch and i agreed mukaje after lunch yace he wanted to tell me something yace shi kar nayi tunanin he is a player or something yace yana son wanann yana son wannan by Allah tunda matanshi ta rasu he never looked at any girl yace yanaso mamanshi taso ta hadashi da dayawa yayi declining sai ke daya yi asking out and yanzu ya wuce he found out that kawai admiring dinki yake it’s not love and he have been praying but with what he’s feeling yasan Allah ne yasa you’ll be his means da zaya nemo true love dinsa please i should understand him with what he’s feeling if i refuse him his life will be a forever mess cux he loves me and is too attached to me that he can’t leave without me, girl! I couldn’t breath sosai abunki da dama the feeling is mutual dan tun ranan dana fara ganinshi i know it was love at first sight but ya nuna ke yake so shiyasa nayi consoling kai na I can’t force myself on him I cried tears of joy instantly I confessed too he even proposed to me on his knees inee” ta karasa maganan tana murmushi tana nuna ma inaaya ring din dake hannunta inaaya smiling kawai takeyi tace “wow wow wow wanann kaman wani cinderella story wow I’m really so happy for you that you find love ihsan stay happy always” hugging dinta ihsan tayi tace “thanks inee and he’s coming to greet dad during the weekend” addua Alkhairi inaaya tayi masu dan ba karamin dadi taji ma ihsan ba sunata magana basusan time ya wuce ba har 12 tayi da sauri suka tashi suka nufa class, karfe 1:30 lecturer din ya fita direct parking lot suka nufa kowa ya shiga mota ya nufa gidansu.

+

               Tun bayan sun koma Switzerland Aliyu ya cigaba da rayuwanshi hankali kwance kaman baya da wani aure dan kuwa hidimansa kawai yakeyi yaje aiki ya dawo kuma kullum sai Ammah tace masa ina inaaya yana kiranta sai ya amsa mata da eh suna waya kuma ko sau daya bai taba kiranta ba kawai dan yayi avoiding fadan Ammah, ko ba komai he missed his little sister’s morning coffee duk da yana sha kullum but dole sai yayi making da kanshi and it’s like akwai wani special abu a nata da yayi missing, yau yana zaune a parlour tareda Ammah saboda bayada aiki sai night suna ta fira sai Ammah tace “Aliyu dan je ka kirawo mun inteesar a dakinta” ba musu ya tashi ya nufa dakin inteesar din dan ya kirata yana zuwa bai wani tsaya knocking ba ya turo kofan ya hangota kwance rub da ciki da laptop gabanta bai kalla me take ba da laptop din yace “inteesar kizo Ammah na kiranki” skype take da inaaya kawai sai taga ta tsaya cak kaman tayi hooking kana iya hango yanda kirginta ke heaving inteesar tace “inee whats wrong” aliyu na jin abunda ta fada har ya juya zaya tafi ya juyo da sauri ya kalla screen din fuskan inaaya ya gani kwance a screen din sai fa gabansa ya buga dum! Fuskan plain saidai dan ramewar da tayi ne kaman an sa mishi gum a wurin ya tsaya yana kallo ita kuwa inteesar tashi tayi ta gyara hulan kanta ta jawo laptop din zata fita tayi attending to kiran Ammah kawai sai taga mutum tsaye dan ta zata ya tafi tace “ya Aliyu ohh sorry gani nan zuwa fa” da sauri ya duke kai yana sosawa ya fice a dakin dan Murmushi inteesar tayi dan ta gane screen din ta yake kallo ta kalla inaaya tace “ke malama lafiya kaman kinyi hooking ko motsi bakiyi to idan ma mijin naki kike ma wa ya tafi tana magana tana tafiya har ta isa parlour tazauna kusa a Ammah dake zaune a three seater aliyu kuma kasa a gefenta inaaya tayi saurin cewa “intee i need to go now we’ll talk later” kafin ta kashe inteesar tace “noo ga Ammah” inaaya gani tayi fuskan inteesar ta dauke sai Ammah da tayi appearing a screen din Ta gaishe ta sukayi yar fira sannan takashe kafin inteesar tayi wani move dan taga take takenta tana kashewa ta rufe laptop din ta kwanta a kan gado tana dafe kan ta zuciyanta sai bugawa take deep muryan Aliyu nayi mata yawo a kunne da yace “inteesar kizo Ammah na kira” hannu tasa ta rufe kunnuwanta ko zata bar ji amma ina kaman an kara, shaking kanta ta fara yi hawaye na zirarowa a idanunta kuka tayi bana wasa ba har la’asar tayi sannan ta tashi tayi sallah ta dunga addua sannan taji sauki a ranta amma idanun nata sunyi ja mamii ce ta shigo dakin ta ganta zaune a kan prayer mata da sauri ta karasa tace “subhanallah inaaya meya samu idanunki” dan kakalo Murmushi tayi tace “mamii kinga dama kaina ne ke ciwo fa” mamii cikin kulawa tace “too! Sannu ko in kira Daddynki ko said mu je asibiti” tace “aa mamii danayi bacci shikenan” kallon tuhuma mamii tayi mata tace “inaaya bakisan cin abinci duk kin rame gashi kullum idanunki suyi ja kice mun ciwon kai ke! Anya ba ciki ne dake ba” duk da yanda take jin maganan mamii na ciki bai hana ta jin kunyan maganan mamii ba tace “mamii ni ciki kuma” mamii tace “ehh ciki a kinsan me nake nufi” tace “wlh mamii Aa kawai ciwon kai ne” mamii ba dan ta yarda ba haka ta kyaleta tasa aka kawo mata abinci da magani tasata dole taci sannan ta sha ta kwanta har magrib yayi tayi sallah ta sauka kasa sukayi having dan family time da daddy da ya sa’id dasu aneesah da mamii karfe 10 ta shiga daki ta kwanta tana ta tunani har bacci ya dauketa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]