[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 14

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Aliyu na shiga dakin nasa closet ya nufa ya rage kayan jikinsa ya yi wrapping towel a waist dinsa ya shiga bathroom yayo wanka sannan ya fito ya saka kaya ya kwanta a kan gado ya fara tunanin abunda yayi ya dace kokuwa kaman he’s being harsh on the poor girl yana ta tunani kala kala. Inaaya wayanta ta dubo sannan ta kwanta a kan gado ta daga wayan ta kunna data ta kwana biyu ma bata kunna ba messages sukayi ta shigo mata masu yawa ta ma kasa dubasu saboda yawa kawai tasa alarm ta ajiye wayan ta kwanta amma sam ta kasa bacci tunanin kalaman Aliyu take wasu zafafan hawaye na saukowa a idonta a rai take tunanin yanzu her dream to to marry a lovely and romantic husband to have the best marriage is shattered she’s stucked with someone who doesn’t like her a bit in the name of marriage tunanin wannan yasa hawayen nata suka karu idanunta duk sun kumbura sunyi ja a zuciyanta tace “ya leena was wrong thinking it’ll work by me trying nothing is going to work” ta sha kukanta can taga dai ba abunda kuka zaya mata ta lallashi kanta ta tashi ta dauro alwala ta kabbara sallah da takai sujjada ta jima tana kai wa Allah kukanta na ya kawo mata sauki a rayuwanta sai wurin 12 ta gama ta koma ta kwanta sai daya ta wuce ta samu bacci ya dauketa da tunani kala kala a ranta. Shima aliyu yana kwance yana ta tunane tunane daga baya ya fada toilet yayo alwala yazo da dinga salloli yana miqa bukatunsa da kukansa ga Allah ya gama ya zauna ya fara karatun qurani in his serene voice har sai 2 sannan ya kwanta bacci yayi gaba dashi.

+

Bayan sallah asuba inaaya wurin 6 ta koma bacci karfe tara ta farka tana tashi ta jawo wayanta ta duba lokacin sannan ta shiga closet ta cire kayan jikinta ta shiga bathroom ta jima tana wanka sannan ta fito a hankali take shafa mai kan fatar ta mai laushi ta gama ta bude akwatunan ta tana duba kayan da zata saka wani voile ne purple da red dinkin doguwan riga cinderella style ta daura dankwalinta babu wani kwalliya a fuskan ta fayau kwalli kawai ta shafa da lip balm ta fito daki ta zauna ta ja wayanta ta fara duba messages tana replying duk yawanci congratulatory message ne tagama ta fara duba status duk friends da yan uwa duk data duba hotunan su ne na biki tana ta kallon posts din mimi sai taci karo da video din couple dance dinsu na ranan dinner tasaka tayi caption “love lives here❤️💏” haushi ma inaaya taji ganin caption din sai tayi ma mimi message “habaa mana mimz you know this caption doesn’t fit in here ki cire shi” tayi sending amma bai je ba mimi bata online kawai ta kashe data din ta ajiye wayan tarasa me zatayi duk taji babu dadi kadaici ya mata yawa kawai sai tayi deciding da ta sauka parlourn kasa haka ta sauka ta ta zagaya ta shiga kitchen din ta fito ta shiga dakunan kasa sai kuma tayi wurin dining table nan taga kwalin pizza sai wani leda dauke da shawarma da grilled chicken ta dan tabe baki tuno jiya datayi sai ta kwashi kayan ta je ta bude fridge ta saka su tana fitowa daga kitchen ta ji karan ana knocking kofa wurin kofan ta nufa bayan ta dauka key din ta bude kawai sai taga mimi da inteesar har wani ihu tayi ta rungume su biyun a tare inteesar tace “ke malama get off me ko bacci bamu gama ba kinsa Ammah ta tado mu” mimi tace “hmm i feel like crying sef” sakinsu tayi sai lokacin ta kula pyjamas ne jikinsu da hijab ko wace sai ta fashe da dariya tace “kun ganku kuwa” mimi tayi hissing tace “abeg take ko shigowa bamayi” basket ne babba dauke da kuloli a ciki mimi ta miko ma inaaya ita kuwa inaaya kallon alaman miye ta maata inteesar tace “what else da yunwa zaku zauna breakfast ne which ammah bazata iya ba driver ya kawo ba sai ta hado da mu muna dan baccin mu na safe” inaaya tace “ai ta kyauta ku shigo to” ta fada tana basu hanya mimi ta ce “mu yi meee? Rufa mana asiri mana wannan faran safiyan muna zuwa gidan amare” dariya inteesar tayi tace “ahh ahh to kuma dama ammah ce wa tayi driver ya jira mu ya dawo da mu just kallanmu a pajamas muke fa” shagwabe fuska inaaya tayi tace “habaa mana ai nan din ma gida ne da toilet kuna iya wanka and ba sai ku saka kayana ba ai ba wani abu ne ba kallon juna sukayi su biyun sai inteesar tace “come on inee don’t be a baby wlh ammah tace muje mu dawo and zamuyi wanka and come back with lunch it’s a promise wurin 2 zamu dawo InshaaAllah yanzu ma we left our phones at home” har inaaya ta dan fara hawayenta saita goge su tace “promise” mimi tace “yess it’s a promise InshaaAllah” sai ta dan kakalo masu murmushi ta karba basket din sukayi mata sallama suka tafi ita kuma tayi cikin gida bayan ta rufe kofan taje ta cire kulolin daga basket ta ajiye a dining table ta bude babban taga fries ne a ciki sai dayan gizdo(gizzard and plantain) ne a ciki sai dayan kulan chicken sauce ne duk ta gama gani ta rufe ta dauka basket din ta kai kitchen ta fara bude drawers din kitchen din ta dauko plates biyu da serving spoon da forks ta kai a dining table ta ajiye sannan ta bude fridge ta dauko wani farm fresh yoghurt da ta gani da cup tana ajiye cup din ta ji ana knocking kofa ta fara tunanin waye yazo ta je ta bude mimi ta gani da flask a hannu ta mika mata tace “sorry har mun tafi ashe mun manta da flask din Ammah tace it’s for ya aliyu every morning coffee yake fara sha before breakfast” inaaya ta karba ta gyade mata kai sai mimi tace “bye muna sauri” ta ce mata bye sannan ta rufe ta koma ciki shima flask din a dining table ta ajiye shi ta zauna gizdo din ta diba ba dayawa sosai ba a plate ta bude yoghurt din ta tsiyaya a cup ta fara ci a hankali. Karfe 11 daidai aliyu ya farka daga bacci ya karanto addua sannan ya tashi ya shiga toilet yayi wanka da brush sannan ya fito wani jallabiya ne fari ya saka bai ida kai mishi kasa sosai ba ya fesa turaren nasa sai yaji cikinsa na kuka ya fara jin yunwa ya bude kofa a hankali ya fito a zatonsa inaaya bata tashi ba dan kar ya tada ta tana bacci ya sauko kasa ya nufa wurin dining tsayawa yayi ganin mutun zaune yana mamakin ta tashi haka ya kara sa wurin dining ya ja wani kujera zaya zauna ita kuwa inaaya tana cikin cin abincin nata bata ji zuwan kowa ba sai turarensa da ya dake hancinta da sauri ta dago ta gansa ya ja kujera ya zauna da sauri tayi kasa da kai tana cewa “ina kwana” ba yabo ba fallasa ya amsa mata da “lafiya lau” tunawa tayi bata dauko cup din shan coffee din ba sai ta tashi a hankali ta fara tafiya taji muryansa yana cewa “get back and finish your food” murya kasa kasa tace “cup zani dauko” bai ce mata komai ba sum sum ta kara kitchen ta dauko mug ta dawo ta ajiye gefensa yana bude kulolin yace “where did you get all this” tace “Ammah ce ta aiko” kada kai kawai yayi ya ja flask yaga cup din da ta ajiye mashi ya dan kalleta briefly kanta a kasa tana cin abincin a hankali ya juya ya bude flask din yaga coffee cikin ranshi yaji dadi yana ta godewa Ammah ya tsiyaya a mug din ya dauka ya fara sha ya gama ya diba dankali da chicken sauce kadan ya fara ci inaaya kuwa duk taji abincin ya fita ranta da kyar ta cinye ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke ta zo sum sum ta wuce ta hau sama ta shiga dakinta ta zauna ta jawo wayanta ta shiga Instagram ta fara kallon stories din mutane har tazo kan yan uwanta da friends duk pictures din bikin ne sukayi posting different pictures da videos ta gama kallo sai tazo kan wani status kawai taga video dinsu na couple dance anyi posting a arewafamilywedding sai ta shiga page din sai taga pictures dinsu na biki duk anyi posting tun daga day one har ran budan kai kan na dinner din ta shiga pictures ne da video na couple dance na cutting cake video din da me make up ta mata duk anyi posting over 2,000 comments ta gani sai ta shiga ta fara dubawa ta dinga ganin different comments wasu na masu Allah yasa Alkhairi wasu na wow wow and yan awwns association tana ta scrolling sai taga wani comment “my heart💔 Wlh I’ve been looking for this guy tun ba yau ba i so much love him” wadda tayi comments din ta samu replies dayawa wata tace “wayyo baiwar Allah sorry amma bai kamata ki dinga fadan haka ba mijin wata ne who knows ko tana ganin comment din is not nice” exchanging comments sukayi tayi yarinyan tace “idc shi din ai namiji ne mijin mace hudu kuma I won’t stop looking for him zan gano shi and get married to him InshaaAllah” comments dai iri iri mutane na allah wadan wadda tace sai ta nemo shi haka dai wasu comments din yanmata ne keta faman wow the husband is hot inaaya dake karanta comments din tarasa miyasa amma zuciyanta zafi yake mata tana jin haushi “mtswww” tayi tsaki ta kashe datan ta wurga wayan a kan gadon ta kwanta tana ta tunani kala kala.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan Aliyu ya gama breakfast ya dawo parlour ya kunna tv yasa al jazeera yana kallo wanda duk ya ma gaji hakanan yake kallon ba wai dan yana maida hankali ba yana zaune nan har lokacin sallah yayi ya fita ya je wani masallaci dake kusa dasu sosai da dawo parlour still ya zauna amma tv a kashe yana rike da wayan sa gallery ya shiga ya bude wani hoto shine a jikin hoton da wata yarinya fara tas! Da manyan idanunta da dogayen eyelashes da karamin bakinta da dogon hanci wando ne a jikinta da jacket doguwa brown har knee dinta ta yafa veil a kanta tanada tsayi sosai amma duk da haka aliyu ya fita tsawo daka ga pictures din zaka gane shine duk da bai kai girma yanzu ba zooming hoton yayi zuwa fuskan yarinyan yana shafa fuskan ta kafin kace me hawaye ya taru a idanunsa tears din yayi dropping a wayan yasa hannu ya goge a hankali ya fara magana “jaan it’s been long I’ve been busy but with everything i do i missed you so much, jaan life is so hard without you i missed all the moments we shared I miss everything about you jaan i hardly smile i am not just my normal self and Ammah it’s hurting her i can see it in her eyes she’s hurt she miss her old aliyu but I’m helpless I can’t bring back her old son I just can’t jaan, and jaan guess what Abbah got me married few months back but the wedding took place few days back” wani Murmushi yayi me ciwo ya cigaba “you remembered how we always plan our wedding night we’ll eat till there’s no space in our tummy lol, we will eat noodles with cheese your favorite but we couldn’t fulfill it you just left me without notice jaan, and jaan I don’t know what to do they got me married but it won’t change anything i pity the girl they got me married to cux she’s just a young girl jaan she’s just 16 she’s my cousin and her name is also fatima, i even told her not to expect anything from me or the marriage do you think I’m doing the right thing jaan” ya gama fadan haka ya sa ma hoton ido yana ta kallo idanunshi sunyi jaa kawai yaji karan ana knocking kofa fita yayi gallery din ya kashe wayan yaga 2:15 yayi mamakin yanda lokaci ya tafi sosai, tashi yayi ya nufa kofan yana murza idanunshi yana budewa inteesar ya gani da mimi da sultaana inteesar na rike da basket suna ganinshi gaishe sa sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa ya basu hanya suka shigo parlour suka zauna inteesar tayi wurin dining ta ajiye basket din inteesar tace “uhmm ya aliyu ina inaayan” shiru yayi mata kawai ya nuna mata hanyan sama ya wuce sama da har zaya wuce dakinshi sai ya samu kansa da zuwa dakin nata a hankali ya bude kofan taji karan bude kofa tana kwance tun bayan tayi sallah zuhr kwance ya isketa sai ta dan bashi tausayi tana ganin shi ne ta tashi tayi kasa da kanta kallonta yayi sai yace “su inteesar sun zo” yana gama fadan haka ya fice ya nufa dakinshi da jin dadinta ta dauka dankwalinta tasa a kai tayi sauri ta sauka kasa tana cewa “uhmmm ai naga yanzu 2 yayi” dariya sukayi inteesar tace “uhmm su anty amarya wani hutu ma akeyi a daki” mimi tace “uhmm to so kike ki zo kiga tana aiki banda abunki intee” sultaana tace “kai haba. Kar ku matsa mata mana kafin mijinta ya jiku” duk sukayi dariya banda inaaya da ta daure tace “ku ba ma ku da aikinyi” ta kara sa tayi hugging dinsu tace “I’m so happy you guys are here dama duk boredom ya isheni” sukayi dariya mimi tace “better get used to it babe dan ba kullum za mu na zuwa ba” inteesar tace “yesso inee and by the way ga lunch can na ajiye maku a dining” gyada mata kai inaaya tayi ta nufa dining din wani basket ne irin na safe amma babban shi da manyan kuloli a ciki ta fiddo su ta jera a dining ta bude rice ne sai curry soup da peppered chicken sai chicken salad ta jera a dining sannan ta fito ta nufa kitchen ta dauko tray ta jero drinks da ruwa da dambun nama da su chin chin ta dauko shi ta nufo parlour tazo ta ajiye masu kan centre table sultaana tace “wow duk mu kadai kaman wasu bakii ok oo lets start digging can’t wait to eat the dambu” mimi tace “yo sultaana ai dolenta ta hado mana gara dangin miji ba wasa ba” hararanta inaaya tayi inteesar kuwa tayi dariya tace “sure thing mimz dangin miji dole tayi mana kafin muje mu fara cewa bata da kirki” duk hararansu inaaya tayi tace “please idan abunda kukazo yi kenan zan sallameku fa” sultaana dariya kawai tayi masu sai tace “inee we brought food fa” inaaya tace “ehh nagani” sai tace “to shikenan kin gani” inaaya tace “to me zanyi na ajiye a dining ko zaku ci ne ni I’m not hungry” sultaana tace “dummy i mean baki ba wa mijin naki” kallon lafiya tayi ma sultaana tace “idan yanaso zaya zo ya ci” kada kai sultaana tayi tace “lallai inaaya akwai aiki ba haka akeyi ba wlh at least dai tunda yana daki kije ki ce mishi ga abinci me zaya ci atleast dai kin fita hakkinsa ko” mimi tace “yess inee you just need to adjust somethings in order to build a relationship with your husband” inaaya wani sigh tayi tace “to please naji naji kar ku cinye ni” ta shi tayi ta nufa hanyan sama ba dan taso ba dan kar suyi ta damunta ta hau sama ta nufa dakinsa ta kai 5minutes a kofa kaman bazata shiga ba sai tayi knocking a hankali cikin sasanyar muryan sa yace “come in” ta tura a hankali da sallama a bakinta yace “wa alaiki salam” ta shiga ta rufe kofan ta tsaya a hankali tace “Ammah ta aiko da lunch will you like to eat now” shiru yayi na wasu seconds sai yace “miye ta kawo” ta lissafa mishi yace ta kawo mishi salad din kawai da yoghurt ta amsa da to ta fita ta nufa kasa tana zuwa kallonta suka hau yi suna smiling kawai ta dan yi musu murmushi ta tafi kitchen ta dauko plate ta wanke ta fork da glass cup ta fito tayi wurin dining suna kallonta suna magana kasa kasa suna dariya ta yi kaman bata ji su ba ta je ta diban masa salad din a plate ta bude fridge ta dauko farm fresh yoghurt din dake ciki ta yi hanyan sama tana jin shewan su mimi tace “uhmm let me come and get married oo” shaking head kawai inaaya tayi ta san halin kawayen nata tana zuwa ta sake knocking kofan dakin shi ta tura a hankali da sallama a bakinta ya amsa mata ta shigo a side drawer din dake gefensa ta ajiye ya juyo ya kalleta sannan yace “thank you” sannan ta juya ta fita ta koma kasa suna nan zaune sunata shewan su inaaya tace “you guys are not serious at all wlh” mimi tayi dariya tace “how will we ever be serious tunda we are not married” dariya duk sukayi suka ci gaba da fira har la’asar yayi basu san time ya wuce ba suna kallo a tv har aliyu ya sauko da tray a hannunsa a hankali yake saukowan bai ida sauka ba sultaana ce ta fara ganinshi ta dan tabo inaaya da kafada dake zaune a hankali tace “go and collect the tray girl” hade rai inaaya tayi kaman bata ji ta ba ta cigaba da taba inaaya tana mata alamun taje ta karba har ya ida saukowa ya nufa kitchen ya ajiye ya fito har yayi hanya fita su kuwa sunyi shiru kaman munafukai yace “um fateema come and lock the door” yanda yayi maganan da wani tone da yasa inaaya taji maganan har cikin kanta and goosebumps in her stomach ta tashi a hankali ta nufa kofan ta rufe bayan ya fita ta saki wani lumfashi da bata san tana rikewa ba sultaana tayi dariya tace “mimi wlh akwai gyara dole mu dinga zuwa muna ba inaaya lesson sosai sosai ki ga fa yanda ta zauna kaman wata mi ya sauki da tray ya kai kitchen zaya fita ko irin ta dan tashi dinnan ta bi shi tace Allah ya kiyaye babe amma sai da ma yace tazo ta rufe kofa” mimi dake ta dariya tace “aii sultaana munada aiki babba fa dole dole ne mu dinga zuwa muna koya mata yanda abun yake” inteesar kuwa dariya kawai take ta yi inaaya ta hade rai tace “see you guys are too corrupt ni zaku ba lesson” inteesar tayi dariya tace “ahh to gaya masu inee saidai ke ki basu course ba dai su baki ba” dariya duk suka saka inaaya tace “enough please let’s go and pray you guys talk alot” da dariyan su suka tashi sukayi sama zuwa dakinta inda sukayi sallahnsu suka cigaba da firansu a nan sukaji ana knocking kofa sukace “inaaya go and get your door gidanki ne fa” haka ta tashi ta je ta bude kofan aliyu ne ya dawo hanya ta bashi ya wuce sama yayi direct ta rufe kofan har tayi hanyan sama taji karan knocking tana tunanin waye har ta nufa tana budewa taga su khady,farhana,haneefa,aleena,aleesha,ummi,feena,anty fareeha da anty fareeda nan take ta saki wani Murmushi dan taji dadi ba kadan ba anty fareeha tace “our wiiiife kin bar mu mu shigo ko dariya zaki ta mana” inaaya tace “noooo anty fareeha I’m just soooo happy please ku shigo” ta basu hanya suka shigo.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Parlour suka shiga straight suka zauna ta rufe kofan ta karasa parlourn ta kasa rufe baki ta gaishe su duka tana tambayan anty fareeda ina twins tace mata suna tare da su ayman da ammar a gidansu nan inaaya ta tuno da gida da mamii da daddy tayi missing dinsu da tunanin kiransu anjima a ranta taji aleena tace “amaryanmu kin kasa rufe baki tun daxu” haneefa tace “ba dolenta ba dangin miji sunzo dole taita mana dariya da shimfidar fuska yafi na tabarma” duk dariya sukayi inaaya kuwa kaman zatayi kuka anty fareeha tace “kai ku kyale mana amarya kuma ni dai ba dangin miji bace na amarya nake” duk sukayi dariya sai gasu sultaana da mimi da inteesar sun sauko jin inaaya ta dade bata dawo ba suma nan sukaga yan uwan nasu mimi ta washe baki tace “kaii ashe baki mukayi” duk kowa ya juyo yana kallonsu aleesha tace “sannu masu gida” akayi dariya feena tace “wai ba dai nan kuka kwana ba ko” duk dariya suka saka inteesar tace “habaa ya feena rashin hankalin baikai nan ba daxu mukazo” suna magan suna dariya inaaya ta tashi taje kitchen suma ta kwaso masu drinks da abubuwan motsa baki harda cookies da chocolates a cikin babban tray ta kawo ta ajiye masu ummi tace “kaii zama dangin miji akwai dadi ji garan da aka tanadar mana” inaaya tace “kai ya ummi kema ko to shikenan ni wannan dangin na na kawo ma wa Ba dangin miji ba in kinsan ke ba dangina bace kar ki taba gaskiya” dariya sukayi sosai anty fareeda tace “kaii kin yi daidai inaaya ai yanzu sai mu gani” sunata shewa abunsu inteesar tace “lallai inee mu da ba dangin ki Ba dangin miji ne sai aka hanamu cookies din da chocolates” mimi tace “hmmm intee bari kedai” hararansu inaaya tayi tace “ai da kunje kun dauka gidan ba bakon ku ne ba” duk gwanin burgewa sunata dariyan su da jin dadi suna ciye ciyen kayan data kawo masu suna dan firan su sai aleena tace “waii ina ya aliyun yake ma ne” inaaya shiru tayi batace komai ba aleena ta kara cewa “inee dake nake fa ina ya aliyun” tace “ohh sorry ya leena bansan da ni kike ba fa” dariya tayi tace “lallai ma inaaya to wa zan yi wa tambayan nan banda ke kinfi kusa dashi kan kowa kuma nazo gidanku banganshi ba in ba ke ba wa zan tambaya” dariya sukayi fareeha tace “inaaya ikon Allah” sai tayi Murmushi tace “ohh yana a daki bara na kira muku shi” ta tashi sum sum ta nufa sama a dakinsa tayi knocking da sallama ta bude ta shiga tace “umm ya aliyu dama su anty fareeha suka zo suna tambayanka” ya gyada mata kai yace “ok ga ni nan zuwa” ta fice abunta ta koma kasa tace masu “gashi nan zaya zo” aleena tace to shikenan suka ci gaba da firansu sai bayan kaman 5minutes sai ga aliyu ya sauko yazo parlour din anty fareeha ta fara tsokanan shi “ango ango” Murmushi kawai yayi mata suka gaisa duk sauran suka gaishe da shi ya amsa masu da yar fara’a aleena tace “hmm ya aliyu ai dole mu yaba amarya bakaga tarban da tayi wa dangin miji ba ai komai da keda akwai na ci sai da ta kawo mana ai gaskiya amarya ta kama kafa wurin dangin miji muna yinta” dariya ma taba aliyu ya yai dariya yace “aleena ke ba” duk sukayi dariya inaaya na tsaye wurin kujera tana kallon yanda aliyu yayi dariya har wani kyau ya kara with smile on his face she couldn’t help but to admire him a ranta tana tunanin dama yana dariya haka sai ta samu kanta da yin Murmushi aleesha ma tace “ya aliyu da gaske fa leena take ai an mana tarba sosai” smiling yayi yace “to shikenan ai ta kyauta” nan ya dan zauna ana fira wanda mostly duk aleena ke ta ba da dariya aliyu ya sake yayi dariya sosai inaaya saidai daga inda yake ta saci kallonsa taga smile din nasa har akayi magrib aliyu ya tafi masallaci su kuma duk sukayi sallah a nan bayan ya dawo masallaci sukayi masa sallama su zasu wuce har wurin mota suka rakasu da har su inteesar sun ce zasu bi su saidai suka ga inaaya na shirin masu kuka sannan suka yadda sai anjima idan driver yazo sa bi shi, bayan sun tafi suka dawo cikin gidan aliyu ya nufa sama zuwa parlourn sama ya zauna a can ya kunna tv yana cikin kallo kaman ya tuna wani abu ya jawo wayansa ya kira wani numbern ringing uku aka dauka yace “hello” a dayan bangaren muryan fareed ne yace “hello latest ango ai ina ce duk saboda amarya ta tare ne an manta da ni” tsaki aliyu yayi yace “kai fa kanada matsala shiyasa ban ma kiraka ba” dariya fareed yayi ya kara tsokanan shi suka ci gaba da firan su, suna zaune parlour suna kallo inaaya tace “su ci abinci mana” duk suka ce a koshe suke sai tace “to um bara na hada kulolin Ammah ku tafin mata dashi to” kitchen ta je ta dauko kuloli tayi transferring abincin ta tafi da kulolin kitchen ta wanke tasa a basket ta ajiye wurin dining table sannan ta koma ta zauna, suna zaune tace “mimz where is your lover” inteesar tayi dariya tace “inee ba dama” sultaana tace “kowa da lokacin jan fadan nashi ai” mimi kuwa tace “uhmm ask sultaana mana ba gidansu daya ba” inaaya tayi dariya tace “tohhhh daga ji an samu matsala da habeebi da ba haka ba yanzu ta fara zuba kaman spoiled tap sai na gaji” inteesar tayi dariya tace “ashe kema kin gane jiya mimi batayi bacci ba sai bayan asuba ya dan dauketa ina bacci ina jinta sama sama tana sobbing” mimi ta daure tace “Allah ya isa intee ba sirri wlh” sultaana tace “wow what am I missing oh god! Mimz me ya faru tsakaninku shiyasa jiya ko dinner ya habeeb baici ba dana koma gida ummah tace naje na kai masa abincin ina zuwa ya koroni yana cewa “get out of my room” ya taso ya buga kofan da karfi daga gani dama nasan akwai wani abu sai nayi shiru na tafiyata” inaaya tace “wow this is serious mimi me ya faru” mimi da idanu sun fara rau rau kaman zatayi kuka” inaaya ta taso tazo tadan hugging dinta tace “oww sorry mimz” tayi shiru sai kuma ta fara magana murya na rawa “it’s not my fault and I apologized but he’s really mad at me ranan dinner he said he’ll come and take me he wants to see me i said ok so ranan i got busy and and sai muka tafi kawai na manta yace zayazo and ya ta kirana banga calls din ba sai daga baya rannan da dare I called him and apologized but still kaman he wasn’t happy yace ok ran sunday idan zamu koma gida mun gama da gidan I should call him yazo ya maida mu nace ok sai shima jiyan su ya Khady sunzo sukace mu tafi and I couldn’t stay back ni kadai my phone was in my bag he called me banyi answering ba sai after mun koma gidansu intee na gani I called him back yayi picking yayi shiru nace hello yace meya faru i said I’m truly sorry I’ll make it up to him but he was so angry he started yelling that is it because he loves me so much that I’m giving him ill treatment is it because he’s dying to see me nake mishi haka nace no ba haka ne ba abubuwa ne da yawa shiyasa and he got angrier that abubuwa but atleast idan na yi picking nace mishi yayi hakuri he will understand but i treated him bad is it that I don’t like him anymore or don’t want the relationship if I don’t then i can tell him narasa me zana ce nayi shiru kawai ya kashe wayan I called him yaki picking the second time yayi rejecting the third time switched off I was hurt wallahi i love him so much and I don’t want to lose him I apologized but he is still angry” patting dinta inaaya tayi a baya tace “sorry mimz he loves you too ok that’s why he got angry but he’ll surely call you he just need to cool down” sultaana tace “ohh no sorry mimz I’m sorry that you’re hurt because of my brother he’s got this bad temper idan yaji haushi ne but he’ll surely come around” inteesar tace “yess and…….” bata ida magana ba wayan mimi dake inda inaaya take zaune a hanun kujera yayi ringing inaaya ta dauka zata mika mata a jikin screen taga wanda ke kira “habeebi❤️🔐” dariya inaaya tayi tabata tace “wow speaking of the devil and he shall arrive” duk sukayi dariya mimi tayi blushing ta dauka call din a hankali tasa a kunnenta tace “wa alaika salaam” ya habeeb yace “baybeeeee” mimi tace “habeebi” Murmushi yayi yace “I’m a jerk i hurt you last night please forgive this your stupid guy I just lost it I’m so sorry babyy please forgive me I love you so much please let’s not fight ever again” mimi har cikin ranta taji wani dadi tace “No I’m sorry I treated you bad please forgive me I’m truly sorry and I’ll always and forever love you don’t ever think I’ll stop and yess we’ll never fight again InshaaAllah cux I couldn’t even sleep last night” kallon juna sukayi suna dariya inteesar tace “wlh mimz ba kunya a gaban kanwar shi zaki zauna kina jero mishi kalamai” sultaana tayi dariya tace “mimin mu kenan” kallonsu tayi ta tabe baki ta ci gaba da wayan ta suna ba juna hakuri da kuma irin missing din juna da sukayi, karfe 8:50 driver yazo wanda ammah ta aiko ya dauke su inaaya kaman tayi kuka haka sukayi sallama tana rokon gobe ma su zo suka ce to kawai suka tafi ta rufe kofan ta nufa sama dakinta tana shiga ta duba wayanta ta dauko ta kira mamiii sun jima suna waya har ta bata daddy da su twins ta gama ta kira ya sa’id da aneesah suma sun dan jima suna waya sun debe mata kewa saida ta gama tana kwance taji cikinta na kukan yunwa sai a lokacin ta tuna bataci komai ba tun breakfast ta tafi kasa ya dauka abincin ta yi warming a microwave ta dauko plates biyu tazo ta ajiye ta zauna ta zuba daidai wanda zata ci a hankali ta fara ci tana cikin ci taji karan saukowa daga stairs tasan aliyu ne saida heart dinta yayi wani double flips ya karaso wurin dining din ya zauna shima ya bude food flask din yayi serving kanshi kadan abincin and they ate in silence inaaya ta riga gama amma bata tashi ba tana zaune kanta a kasa har saida ya gama ya tashi sannan ta tattara plates din ta je kitchen ta wanke ta dauko wani food flask medium ta juye abincin duka sannan ta fita taje ta ba me gadinsu ta dawo cikin gida ta nufa daki ta shiga toilet tayi taking hot shower ta fito sweatpants me da sweatshirt pink ta saka ta kama gashinta ta daure wuri daya in a ponytail har karfe 10:00 yayi ta kwanta tayi addua bacci amma ta kasa tana ta tunane kala kala har 12 sannan bacci yayi gaba da ita.

+

STORY CONTINUES BELOW

One week later

Inaaya ce ke saukowa a hankali daga kan stairs sanye da doguwan riga na lace A-shaped gown ta daura dankwali a kanta yau ya kama one week da tarewanta cikin satin nan tayi baki sosai cousins in nata da sauran yanuwa dangin Ammah duk sun zo da su aneesah da saleema so biyu suka zo mata su inteesar kuwa so uku duk dai sun rage mata kadaici a fanni aliyu kuwa babu improvement a relationship din nasu gaisuwa ce kawai take hada su idan sun hadu ko a kan dining table saboda kullum har satin sai ammah ta aiko masu abinci har da mamii da ummi ma dan a al’ada sai amarya tayi one week sannan ta fara girki, a hankali ta sauko ta nufa kitchen ta tsaya tana kallo tana tunanin abunda zata dafa yau ne ranan da zata fara girki ta kai 10minutes a tsaye sai tayi tunanin hada club sandwich dinta nan da nan ta fara fiddo kayan hadin cikin one hour 30minutes ta hada abun ta a wani karamin tray ta saka tasa cling film ta rufe ta kai dining sannan ta dawo ta hada dalgona coffee dinta da ta dade tana craving ta nufa dining din ta zauna taci abunta a hankali har ta gama Aliyu yau bai fito ba haka yasa ta bar mashi nashi nan kan dining ta koma daki tana shiga wayan nata yayi ringing ta duba wayake kira taga mamii ce da jin dadinta ta dauka ta gaisheta suka gaisa sai tace “inaaya ina fatan kinsan yau kikayi one week” tace “eh mamii na sanii” mamii tace “to ai kinsan dai yanda al’ada ta tanada ko yau zaki girka abinci ki kai ma sirikan naki” a hankali inaaya tace “toh mamii” mamii tace “inaaya nasan halinki fa banda rashin wayau ki girka atleast two different kinds of foods kina ji na ko ba wai ki dafa pasta ki kai masu ba dan tafi komai sauki” duk da mood din nata saida maganan mamii ta bata dariya a hankali ta murmusa tace “mamii InshaaAllah zanyi yanda ya kamata” mamii ta ce mata “to yanzu zan turo driver ya kawo aneesah da fauziyya su taya ki” dadin hakaa inaaya taji tace “yawwa mamii nagode Allah ya kara girma” amiin mamii tace sannan ta kashe wayan inaaya ta zauna tana tunanin abunda zata dafa egg basmati rice da goulash(meat and vegetable stew) taji dadi dan idea din ya kwanta mata sai kuma ta tuna abbah na son tuwon shinkafa da egusi soup hakan tayi deciding ta dafa sai tayi grilled fish da chicken pepper soup dadi sosai taji saboda idea din nata ya kwanta mata ta tashi ta sauka kasa zuwa kitchen ta fara kafin su aneesah su zo.Aliyu tunda ya tashi yayi wanka amma sam bayajin saukowa he just wants to be alone yana kwance kan gado ya kura ma sama idanu yana kallo kaman wanda ke san gano wani abu wayanshi ne yayi kara ya duba yaga Ammah ce ya dauka cikin natsuwa a hankali ya gaisheta ta amsa jun muryan dan nata kasa tace “lafiya Aliyu me ya sameka” yace “Ammahh babu komai I just want to be alone” tausayin shi sosai ya cika Ammah tace “habaa Aliyu you need to get yourself together kullum sai ka yi isolating kanka kace wani you want to be alone banason hakan ko kadan” yace “to Ammah kiyi hakuri inshaAllahu bazan sake ba” Ammah tace “to ya dai fi dama kira nayi na sanar maka dan nasan halinka idan ban gaya maka ba bakayi yau anyi sati daya da biki dan haka yau zaka kawo man diyar tawu sannan ka kaita gidansu ku gaishesu da gidan Baffahn ku duk sai kun zayaga gidan dangi kun gaishesu dan haka sai ka shirya” Aliyu kaman ya dora hannu a kai yayi ihu amma ba yanda zayayi yace ma ammah to sukayi sallama ta kashe wayan ya dafe kansa yana tunanin yanda zaya fara ya tashi ya fita dakin sanye da sweatpants black da white shirt ya sauka kasaa ya nufa wurin dining table din ya ga sandwich sam baya iya ci haka yayi hanyan kitchen din ya ji kara yana shiga ya ga inaaya wurin fridge a tsaye tana faman ciro wani abu wannan karon ta canza kaya sweatpant ne da sweatshirt grey da dan touches of white a jiki ta daure dogon gashin nata daya sauko kan bayanta sosai babu dankwali a kanta ta daura aprone tsayaa yayi yana kallonta ta side kusan 5minutes ita kuwa ji tayi kaman ana kallonta ta juyo kawai ta ganshi tsaye ya hade hannu a kirji ya jingina da bango a daburce batayi expecting dinsa ba tace “umm umm in..ina kwana” sai lokacin ya dauke idonshi a kanta ya amsa mata ya karasa cikin kitchen din ta nufa wurin coffee maker tsaye tayi kaman an dasa ta na wasu minutes sannan ta juya da sauri ta cigaba da abunda take shima ya maida hankalinsa kan abunda ya kawo sa ya hada coffee dinsa ya gama yayi hanyan fita rike da mug yace mata “uhmm you should get ready we are going out” bai bari ta amsa ba ya fice abunsa, tilapia fish ne da yayi kankara sosai ta ciro a fridge din Ta ajiye su gefe daya sannan tazo ta yi grinding onions da scotch bonnets data gama fish din sun saki ta dauko kayan hadinta dasu spices nan ta fara marinating kifin tana cikin yi taji karan knocking kofa wanke hannunta tayi ta fito kitchen din ta iske aliyu har ya bude kofan aneesah ce da fauziyya suka shigo gaisheshi sukayi aneesah kuwa da dan gudunta ta karasa tayi hugging inaaya tana cewa tayi missing dinta sunyi minti biyar a nan tsaye kafin suka nufa kitchen tare aneesah ta kalla fish din tace “ya inee me zaki dafa” a jindadi inaaya ta lissafo mata dariya aneesah tayi tace “wow that’s alot fa mu fara yanzu me zamu yi dan ayi beating time” inaaya tayi Murmushi tace su fara da vegetables ita kuma ta ida marinating fish din haka suka fara su uku, Aliyu bayan ya gama shan coffee din nasa ya hau sama zuwa parlourn sama ya kwanta a kujeran.

Tun karfe 10 suka fara aiki har 2:00 tayi duk sun gaji sun gama komai tuwo kadai ya rage zaa tuka shima ya kusa yayi abinci suka girka da yawa 3 different set din warmers manya manya inaaya ta ciro ta sa wanda zasu kaiwa su Ammah sai na gidansu dana gidan baffah sai ta sa na su a wasu warmers din ta kai dining aneesah tace “kaii na gaji munyi kokari fa ya inee wannan girki haka” dariya inaaya tayi tace “sai kace ke kikayi komai sai laziness” suna tsaye kitchen suna firansu har tuwon ya isa a tuka shi inaaya ta fara tukawa bata ida ba ta gaji sai fauziyya ta karba ta ida suka saka a warmers din sai fauziyya tace “ya inaaya ai duk an gama kije ki huta ni zan gyara gidan duka” inaaya tayi Murmushi tace “kinji ki fauziyya wai in huta kuma ai kun gaji mu dai gyara duka tare sai naje nayi wanka ma” aneesah tace “kaii ni dama ni akace na huta” dan dukan wasa inaaya tayi mata haka suka shiga gyaran gidan cikin kan kanin lokaci suka gama suka share ko ina akayi mopping da duk wani goge goge da wanke wanke sannan inaaya ta sa turaren wuta duka gidan ga ac a parlourn kasa yayi sanyi sosai nan da nan ko ina ya kama kamshi sosai ga kamshin girki da na turaren wuta aneesah tace “kaii ya inee turaren wutan ya isa hakanan bansan miyasa kika cika son turaren wuta ba ni wlh” inaaya tace “to so kike na zauna bana so ko? ko ina yayita wari” dariya aneesah tayi tace “babu wani wari fa” inaaya tace “ke kika sani bara naje nayi wanka” ta nufa sama zuwa dakinta aneesah kuwa ta zauna parlour ta kunna tv tana kallon disney channel inda tafi kwarewa. Tun lokacin zuhr da aliyu ya fita masallaci bai dawo ba ashe yana garden din gidan can ya zauna sai wurin past 2 ya taso dan komawa cikin gida ya shirya dan wurin 3:00 zasu fita a hankali yayi knocking kofan aneesah dake parlour ta ji karan ta taso ta bude kofan Aliyu na shigowa ciki wani kamshi ya dakan masa hanci na turaren wuta dana girki me dadi batare daya sani ba ya lumshe idanuu aneesah tace “ahh uncle aliyy sannu da dawowa” a hankali ya bude idanunsa yace “yauwa aneee” ya karaso cikin parlour ya zauna aneesah ma ta dawo ta zauna shiru na wasu minutes yace “yanzu disney kike kallo” ta danyi dariya tace “ai yafi komai wlh uncle aliyy” dan Murmushi yayi kawai sai can tace “ohh sorry uncle aliyy na barka zaune ya inaaya taje tayi wanka ne but amma lunch is ready” yayi Murmushi yace mata “ok nima zanje nayi wanka ne” ya tashi ya nufa hanyan sama.inaaya ce ta sauko daga stairs ta gama shiryawa lace tasaka wani irin turquoise da simple design dinkin fitting gown ne da abun peplum sai yayi kama da skirt da riga ansaka net daga gaban da hannun ya karbeta sosai kaman a jikinta aka dinka mata tasa wani simple silver jewelry da agogonta mai kyau ta dauran dankwalinta sosai tayi kyau babu makeup a fuskanta daga kohl sai lipgloss cikin parlour ta karaso aneesah dake rike da waya inaaya tace “heyy jealousy tashi ki gaya mun nayi kyau” tana tsokanan ta aneesah ta dago ta saki baki tace “wooooooo ya inee today i must admit wayyo ni kin ganki kuwa MashaaAllah i have the finest sister” inaaya tayi dariya tace “useless girl” aneesah tace “bada wasa ba fa kin ganki OMG ki zauna na dauke ki picture” inaaya tayi dariya har tace aa sai kuma ta yarda ta zauna aneesah ta fara daukanta da wayan inaayan sunata daukan pictures suna dariya Aliyu ya sauko basu ma sani ba sunata dariya Tsayawa yayi yana kallon yayi mamakin yanda inaaya take ta dariya tana jin dadi unlike yanda take a cikin gidan sai ya fara feeling guilty she’s not happy with him he’s only inflicting pain on her yaji ba dadi a ransa haka ya karasa parlourn a hankali inaaya ce ta fara ganinsa tayi shiru ta bar dariyan da take sai aliyu yaji ba dadi tana ganinshi ta bar dariyan ta ya karaso yayi Murmushi sanye da shadda fara kal dinkin kaftan yayi masa kyau sosai shiru ya biyo baya sai yace “uhmm anee nima baki dauka na” dariya aneesah tayi tace “kaii habaa uncle aliyy kaga kyan da kayi ai dole na nadauke ka” yayi Murmushi kawai yace “aa wasa nake miki fa” inaaya dai shiru take tana saurarensu aneesah tace “habaa no please ka zauna na dauke ka” Aa ya sake ce mata dole ta hakura sai inaaya tace “umm lunch iss ready” yace “ok” suka nufa dining su duka inaaya ta kira fauziyya ma tace suzo suci tare duk suna zaune a dining inaaya ce a tsaye gefen kujeran aliyu zatayi serving dinsa a hankali ko kusa da inaaya kake bazakaji abunda tace ba ta tambaya aliyu abunda zayaci yace a very little rice and goulash with the grilled fish ta bude kulan rice din ta fara zuba masa ya dago zaya ce mata ya isa sai ya ma manta hankalinsa ya na akan kallonta tayi kasa da kai dongon hancinta da dogayen eyelashes dinta kawai kake gani bai ma san ya kura mata idanu ba aneesah dake gefe idanunta kyam a kansu ba shiri ta jawo wayanta tana capturing moment din nan inaaya ce ta dago ta tambaya idan ya ishesa taga idanunsa a kanta idanunsu sukayi clashing kasa dauke kai tayi they just kept looking at each other in the eyes aneesah kuwa sai snapping takeyi kaman wanda ya tuna wani abu yayi kasa da kai yace “umm its its ok” itama kasa tayi da kan nata.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]