[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 13

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yau ta kama alhamis ranar da zaayi henna a nan gidan su inaaya tunda ta tashi da safe bayan yagana tayi mata gyaran jiki tasaka wani chiffon riga sleeveless mai kunshi tazo tayi mata flott beauty lalle ne ja ake tsantsara mata kaman ka cinye skin din nata yanda lallen yayi kyau da yan matan Amaryan suma suna zaune wata me lalle nayi masu sai yumnerh tace “yauwa me lalle ina so kiyi heart a hannun amaryan ki rubuta F&A a jiki hararanta inaaya tayi tace “yumnerhhh mana” dariya su inteesar sukayi yumnerh tace “hehehh bakida say inaaya dole kiyi abunda nakeso tunda you failed to complete dare din mu” rolling idanu inaaya tayi tace “I’ll get back to you kema” babu yanda ta iya tana ji taba gani mai lallen ta zana heart tayi rubutun a ciki lallen ya jima har sai wurin 1:30 sannan ta wanke ya fito yayi kyau a dogayen yatsun ta sai lokacin ta sake wanka ta shirya cikin fulani saki blue colour the_cicada tayi mata yayi kyau sosai dazeita tazo tayi mata makeup very light and simple amma idan ka ganta sai ka kasa daina kallonta saboda kyau din datayi tunda ta fito duk inda ta bi MashaaAllah kakeji kawai suma kawayen amaryan da duk cousins sun saka fulani saaki blue amma zani kawai da head sukayi dashi sai rigan na atamfa suma duk sunyi kyau zuwa 3 gida ya cika taf da mutane ana ta kai kawo wasu ana masu kunshi wasu na ciye ciye ga masu traditional kida sunatayi kawaye da yan uwa nata rawa amaryan kuwa zaune take a sit din da aka tanada saboda ita photographer nata snapping dinta.

Aliyu tunda ya tashi yau sai recieving messages yakeyi daga abokan sa da sukayi school tare a Switzerland yan nigeria suna ta congratulating dinsa Akan auren nasa dan basu sani ba ya na gani yasan aikin fareed ne shi zaya sanar masu ya shirya ta nufa gidansu fareed ya na shiga ta tarar da mahaifiyar su a parlour ya gaishe ta ta amsa masa da fara’a sannan ya nufa part din fareed yana zuwa ga tarar dashi yana waya kawai ya buga tsaki “mutum kullum bayada aiki sai waya waya waya” murmushi fareed yayi yace “babe I’ll call you back” ya kashe ya kalla aliyu yace “ya dai kana lafiya” yace “eh mana ina lafiya har saida ka je ka sanar ma jamaa nayi aure” dariya fareed yayi yace “ohh ai dama na sani to miye a ciki gaya masu nayi na kuma gayyacesu dinner ba ka bar mani komai ba a hannu to miye laifina” rolling idanu aliyu yayi yace “ai dai kasan halin yanda auren yake ko miye na gaya masu” fareed yace “ohh god aliyu will never change nazata zaka sauko da kai and accept your marriage and your wife kasa komai yayi working but no hmm aliyu wlh kar ka cutar masu da diya fa” aliyu yace “ai ba cutan ta nace zanyi ba we can live under one roof but not as husband and wife cuz I can’t see her as my wife she’s like a younger younger sister to me” fareed yace “hmm to shikenan nayi abunda zan iya it’s upto you and ka rubuta ka ajiye you’ll surely come looking for my help lokacin da zaka fara son ta ka rasa yanda zakayi” aliyu yace “allah ya sawake ba bakinka ba” dariya fareed yayi yace “ohhk oo” sai kuma suka fara fira kaman basu ke musu yanzu ba.bayan Aliyu ya koma gida yayi sallah magrib yana zaune a daki ammah ya shigo tace “aliyu sannunka kaji wlh na kula tunda mukazo ranan da mukaje gidan daddy baka sake zuwa ba wlh aliyu kaji tsoron Allah ko ba komai matarka ce amana ce a gareka iyayenta ba dan basa santa ba suka baka yau har event sukayi ko hoto na tarihi a yakamata kaje kuyi ko amma bakayi” rasa abunda zayace yayi yaba ammah hakuri tace “to yanzu nakesan ka tashi kaje gidan daddy kuma ga kaya nan zani baka kai kaima diyata na budan kai ne musamman na yi mata kuma kai nakeso kakai mata ka bata hannunka da nata” bayanda aliyu ya iya haka ya tashi ya shirya cikin kananun kaya ya dauka mukullan mota yasa kayan a mota ya tafi dasu yana zuwa gidan daddy kai tsaye part din sa’id ya nufa ya tarar da sa’id suka gaisa yace “how far muke ganinka da daren nan ko matar akazo ganii” Murmushi kawai aliyu yayi yace “baza ka gane ba ammah ta bani sako na bata kuma tace dole ni zan bata ya na iya” dariya sa’id yayi yace “may Allah bless our parents ba yanda za muyi dasu.. yanzu bari nasa a kira ta ko zaka shiga ciki” aliyu yace “no call her” tashi sa’id yayi ya fita daga part din yana fita yaga twins yace “yauwa my favorites kuzo kuji” suna zuwa yace ” go and call ya inaaya for me kuce ina kiranta ina part dina” da sauri suka amsa suka nufa cikin gida maimakon sa’id ya koma part dinshi sai ya dan fita waje.

STORY CONTINUES BELOW

Event din ya wuce in a blur akayi aka gama kowa ya watse har dare yayi lokacin duk sun gaji kowa ya cire kayansa yayi wanka ya canza to pj’s suna zazzaune parlour harda su khady su farhana da su aleena da ya fareeha da anty fareeda duka dai ana ta labaran duniya twins ne suka shigo da gudunsu ammar yace “yaa inaaya ya inaaya ya sa’id na kiranki yace yana a part dinshi” bata kawo komai a ranta ba tace “kaii ya sa’id and his wahala ko me zanyi masa” ta tashi daga ita sai pj’s dinta navy blue wandon ma bai kai har kasa ba ya wuce knee dinta sai hula a kanta kawai ta nufa part din ya sa’id tana zuwa ta turo kofan a hankali ta shiga ta maida kofa ta rufe ta taka ta karasa parlourn da sallaman ta taga mutun zaune ya bada baya taji an amsa mata sallama kawai taji muryan aliyu duk ta daburce ma tarasa yanda zatayi takai minti uku tsaye kawai tayi baya da saurinta zata fita aliyu daya juyo yaganta tsayuwan me take yaga tana baya shima tashi yayi da sauri ya bita dan so yake ya bata sakon ya wuce har ta kai bakin kofa da sauri ya riqo hannunta ya fizgo ta har ta kusa fadawa kanshi cikin haushi yace “miye haka ni din nayi kama da ba mutane ba zaki wani gudu dan kin ganni and yes I sent for you” shiru tayi ta kasa cewa koma zuciyanta nata bugawa gashi har a lokacin bai saki hannunta ba ya jata har zuwa parlourn sum sum take biye dashi ba yanda zayayi kayan ya dauka ya bata ya dora kan hannunta daya riqe yace “gashinan it’s from Ammah tace na budan kai ne” yana gamawa ya fice bai jira komai ba bin bayan sa tayi da kallo har ya fita sannan ta kalla kayan sai kuma tayi cikin gida a hankali tana zuwa bata wani tsaya parlour ba tayi sama ta nuna ma mamii kayan mamii tace to ta kira ammah tayi mata godiya, daga dakin mamii direct dakinta ta wuce ta ajiye kayan sannan ta kira Ammah tayi mata godiya ta kashe ta koma kan gado ta kwanta kaman wacce take bacci ta lumshe ido ida kadai tasan yanda takeji.

Washegari karfe 8 suka tashi duk sukayi wanka inaaya saida aka gama mata gyaran jiki sannan tayi wanka itama duk yan matan sun shirya tsab zasuje gidan su inteesar zata dauko sauran kayanta mimi tace “inee baki zuwa” Aleena dake zaune dakin tayi mata kallon kinada hankali tace “lallai mimi ko cewa tayi zata baku ce mata Aa kawai riii sai ta tashi ta bi ku gidan sirikai ana hidimar biki” dariya mimi tayi tace “to ai naga dai ba wani abu bane duk daya ne” aleena tace “lallai kinada aiki kudai kuyi tafiyanku muna nan tare da fav lil sis” mimi tace to sannan suka fita suka tafi inaaya dai bata ce komai ba har suka gama maganan su. Bayan sun tafi daga aleena sai aleesha sai ummi da inaaya a dakin aleena tace “dama ina so mu sama time alone gashi nasa mu sun tafi lil sis kinyi abunda na gaya miki” danshiru tayi tace “no ya leena I can’t” aleena tace “habaa inee me na gaya maki it’s not easy but try idan ba haka ba ke zakiyi ta hurting kanki do you think zama under one roof and not talking is nice wlh depression sai ya fara kamaki baki da wanda zakiyi magana a gida nan kin saba ga aneesah da twins da ma mamii dole ki koya yi masa magana abunda kike tunani ba zaya yiwu ba duk yanda kike tunanin abun ya wuce nan idan akace miji da mata ba wasa ne ba” inaaya tace “ni bansaniba I don’t know me akeso nayi” aleena tace “now get to know him what he likes and doesn’t like ki cire wani kunya and ask inteesar cux tafi mu sanin shi” aleesha ma tace “yess inee she’s right abun ba na wasa ne ba” ummi ma tace hakane ba wasa ne ba nan sukayi ta bata shawarwari dai har lokaci yaja karfe uku gidan ya cika da mutane kakannin inaaya na both side din mamii da daddy sunzo bikin suma, inteesar sun dawo har mai makeup din da zata masu su duka kawaye rjt makeuppro tazo saboda 5 ne kamun kuma suna da dan yawa, karfe 4 inaaya ta fito wanka bayan an mata gyaran jiki na yamma dazeita mai mata makeup tazo ba bata lokaci ta tsara mata makeup dinta ta sha kyau tubarakallah dinkin iro and buba ne na mint green fabric dinta sai head shima mint green sai silver jewelries da accessories aka gama mata makeup tasa kayan 5:00pm daidai ta kammala shirin nata tsab! Tayi kyau mai makeup din sai yaba mata take tana cewa “your groom is so lucky seriously you’re an epitome of beauty real definition of lady with class may Allah bless you Marriage my dear” smiling kawai tayi baa jima ba ta tafi sai ga friends din nata sun shigo da ankon nasu na atamfa julius holland embellished light blue da golden sunyi kyau suma har sun gaji sunata yaba kyan inaaya aneesah da saleemah ne suka shigo sunyi anko na lace suma aneesah tace “ya inee idan kin gama shirya photographer na a kasa” friends din nata suka riko amaryan tasu har zuwa parlour na kasa inda duk mutane sun watse an tafi wurin event din gidan baffah bedge photography ne photographer din nan da nan ya fara aikinshi ya dunga snapping dinsu wani ita kadai sai da friends dinta da sisters dinta harda su aleena su khady da su anty fareeha da anty fareeda da suma ankon lace irin na su aneesah suka saka sun sha pictures har ya sa’id yazo sukayi tayi da daddy da mamii da twins dukkansu har zasu tafi can sun gama pictures din khady tace “yakamata a fara tafiya amma banda amarya ita tukunna cux angon zayazo suyi pictures” inaaya ta kalleta tana zaro ido amma batace komai ba haka suka fara tafiya baa jima ba fareed ya kira khady yace gasu nan sun zo tace su shigo parlour daga khady sai inaaya ya rage kowa ya tafi a tare aliyu da fareed suka shigo sun sha kyau fareed ya saka ash shadda aliyu kuwa yadi mai kyau fari yasaka da hula baki da takalma baki ya fito a angonshi sak yayi kyau suna shigowa khady ta tashi tana Murmushi ta karasa wurinsu ta gaishe da ya aliyu fareed ma ta gaidasa kashe mata ido yayi yace “baybeeee kin ganki kar kija na kasa rufe baki” dariya tayi ta rufe fuska da hannu aliyu kuma tabe baki yayi suka karasa parlour inaaya na zaune kanta a kasa zuciyanta nata bugawan da ya saba zama sukayi sai fareed yace “ahh ahh amarya MashaaAllah wannan kyau haka yakamata mun biya kafin ganinki ma” dagowa inaaya tayi a hankali tayi Murmushi tace “ya fareed ina wuni” ya amsa mata da lafiya qlw aliyu dake zaune baice komai ba kaman bazata yi magana ba sai kuma tace “inaa wuni” ba yabo ba fallasa ya amsa mata da lafiya sai khady tace “to we’re late already a gama pictures din mutafi kafin ayita kiranmu” fareed yace hakane nan suka jera akayi clicking dayawa su hudun wasu kuma banda khady aka yi dayawa sai fareed yace “babe muje mota mu jira ko” kaman plan Khadyyy tace eh suka bar couples din parlour suka fice, photographer yaci gaba da aikinsa yana daukan su biyun har ya gaji a position daya suke yasa sukayi facing juna yayi snapping yace su canza style let him hold her hands su kalla juna duk dan ayi a gama aliyu ya kamo hannunta wani shock yabi jikinta yana riqo hannun nata a hankali kasa dagowa tayi haka akayi snapping photographer din yace “perfect one last style you should lean on his chest and place your hand on his bosom and you put your hand around her waist” inaaya kaman bata ji ba tayi shiru ta tsaya photographer yayita kara fada masu yanda zasuyi da aliyu ya gaji kawai ya sa hannu ya jawo ta ta fado kanshi tayi saurin rufe ido da sauri sauri chest dinta ke bugu aliyu ya jawo dayan hannunta yayi placing on his bosom ya sa hannunshi ya zagaye waist dinta ko motsin kirki inaaya ta kasayi ta kasa bude ido photographer kuwa haka yaso ya yi snapping dayawa aliyu yace “uhm i think it’s ok sir this your pose are too much and uncomfortable” Murmushi yayi yace “sorry sir I just want to give the best outcome” Murmushi yayi masa kawai sai ya fara tattara kayansa domin binsu zuwa can wurin event din a gama pictures din a hankali inaaya ta zare jikinta daga na Aliyu ta matsa gefe ta tsaya duk a tare suka fito da photographer ya shiga motanshi sukuma suka nufa motan fareed inda fareed da Khady nazaune a gaban motan yasan duk shirin su ne sai ya kyalesu kawai har ya zayaga zaya shiga gaba ya fasa zai koma daya side din ya shiga baya inaaya na tsaye zata bude kofan baya dake direct saitin khady Aliyu kawai ya samu kansa da ja ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya bude ya shiga ba wanda yace komai fareed ya tada motan suka nufa gidan baffah kawayen amarya da sisters sukafito sukayi entrance din amarya wurin yayi kyau yasha decoration sai bayan da akayi kamun amarya aka biya friends kudi dangin ango sukayi spraying mata turare sunata yaba amaryan dangin ammah of course da basu san ta ba suka yi ta yaba kyawunta bayan haka ango ya shigo da abokinsa fareed ya karaso ya zauna gefen amaryan mutane nata daukan su hoto ana ta serving abinci kowa wasu nata rawa dj nata saka masu wakoki sai can aka bukaci amarya da ango suzo suyi rawa suka fito suka tsaya har wakan ya kare ko juyawa ba wanda yayi basuyi wani rawa ba daga baya suka koma suka zauna haka har aka watse ya rage dangi kawai har Aliyu barin wurin yayi suka wuce part din ya abby yin sallah nan kawayen amaryan suka ja ta suka sakata rawa dole saboda suna cewa its her wedding so daya akeyi she should enjoy tun bata biye masu har ta sake suka sha rawa karfe 9:30 event ya kare suka koma gida.

Da suka koma gida mamii tasa aka kai masu abinci daki dan duk rannan basuci abinci sosai ba kaman tasan sunajin yunwa duk sukaci banda inaaya da taci kadan duk tayi shiruuu kawai tana tunanin gobe zata bar gidansu data tuna sai hawaye su cika mata idanu ta gama cin abincin ne ta tashi kawai ta nufa dakin aneesah ta tarar da su biyu a dakin daga ita sai saleema tace ma aneesah “anee I came to talk to you” aneesah tace “uhmm su ya inee me nayi kuwa” smiling tayi tace “come and sit” zuwa aneesah tayi ta zauna inaaya tace “you’re a naughty girl you know but you’re still my only and best sister I can’t tell how much I love you lil one but that won’t change the fact that i am more beautiful” murmushi aneesah tayi hawaye sun fara taruwa a idonta dan dama tunda aka fara bikin take avoiding inaaya dan saboda she’ll get emotional kasa rikewa tayi ta fashe da kuka ta rungume inaaya tana cewa “ya inee you’re always the best can’t still believe you’re going to leave me everything will change without you the house will be boring i will miss you so much i love you” itama inaaya kasa rikewa tayi hawayen nata suka fara saukowa saleemah dake gefe duk taji wani iri tace “ya inee mana don’t be a cry baby kunga nima zaku saka ni kuka” goge hawayen inaaya tayi tace “come on neeshasha stop crying you can always come and see me and I’m just a call away and if you want to we can even move in together” dariya taba aneesah sosai tayi dariya ta manta da kukan tace “habaa ya inee so kike a koroni Aa na dai dunga zuwa everyday everyday har sai kin gaji” Murmushi tayi tace “thats my sister” sai ta tashi ta bar dakin tayi masu sai da safe ta nufa part din ya sa’id a parlour da tarar dashi zaune da waya a hannu yana ganinta yace “su sis an tuno ni” tace “haba ya sa’idoo yazan manta ka” dariya yayi yace “super story kenan” cikin nishadi sukayita magana kafin ta kwantar da kanta kafadan shi hawaye ya fara zuba yana jin digan hawayen ya dagota yace “inee habaa mana what is this why are you crying” fashewa da kuka tayi ta rungume shi tace “ya sa’id i am going to miss you” dago ta yayi ya lallasheta yace “I’ll be coming everyday kawai ki dunga dafa mun delish” Murmushi tayi saida sa’id ya tabbatar ta warware sannan as an elder brother ya mata nasiha sannan ta bar part din nashi har tayi deciding taje wurin twins sai ta fasa dan tasan idan suka fara kuka daren nan sai a hankali cikin gida ta wuce ta nufa dakinta tana shiga duk suka juyo suna kallonta yumnerh tace “uhmm inee ina kikaje kika dade haka is it our husband that came” kallon kinada lafiya Inaaya tayi mata tace “ke kika sani yumnerh” dariya kowa yayi wuri inaaya ta samu ta zauna ana ta fira ita dai shiru take duk tunaninta na kan yanda zata bar gidan nasu har dare ya karayi sukayi bacci.

+

Washegari anty bee ta shigo ta tada su tana cewa “ku tashi yau kunsan yinin biki ko yanzu zaa cika gidan kee inaaya tashi kinsan yau kike gyaran jiki na karshe ko kiyi maza agama kiyi wanka ki shirya” duk haka ta tada su suka tashi yagana tazo ta fara mata gyaran nata da ta ma saba dashi zuwa yanzu ta gama mata sannan tayi wanka karfe 12 tayi karfe daya dazeita tazo tayi mata makeup wani lace tasaka purple na fitting gown an daura mata turban sai bridal veil din ta tayi kyau very simple sukayi ta clicking pictures ne dan event din cikin gidane na mamii so no need suyi sauri yau sauran friends dinta kowa kayanshi yasaka banda cousins da sukayi anko na super wax embellished wata blue da flower red a jiki sunyi kyau sosai sai karfe 3 suka sauka kasa zuwa waje inda akeyin event din mutane nata daukan amarya hoto wasu na dauka tare da amaryan.

Saboda hayaniya aliyu ya bar gidansu yana a gidansu fareed sai 11 ya tashi bacci yayi wanka ya shirya yana zaune wayan shi yayi kara ya duba yaga abbah ne ya dauka ya gaishe sa da girma mawa abbah ya amsa sai yace “aliyu kana ina” yace “abbah ina a gidansu fareed” abbah yace to yanzu kazo ka samemu gidan baffah” ya amsa da to sai bayan yayi sallah la’asar sanna yace ma fareed ya rakasa gidan baffah, a tare suka je gidan suna zuwa duk ba mutane dayawa duk bakin da aka sauke kowa ya tafi gidan bikin yana zuwa a parlour din baffah ya samesu su duka iyayen nasa baba,baffah,abbah da daddy da kakannin su baaba da daada duk cikun girmamawa ya gaishe su suka amsa masa shiru ya biyo baya daada tace “to mijin nawa anyi amarya inadai kishi amma Allah ya zaunar daku lafiya” kowa yayi Murmushi sai baaba ma yace “yanzu sai kaji da amaryarka a kyale mun mata” nan ma duk sukayi dariya aliyu kuwa Murmushi kawai yayi baffah ya gyara murya yace ” uhmm to Aliyu dama fadane da gargadi zamuyi maka mun dauka diya mun baka ba wai dan ba a santa ba ko bata da gata ko ta rasa masoya dan haka aliyu ka sani fateema amanah ce muka baka dan haka idan baka rike amanan nan ba kasan Allah bazaya barka ba ka saba amana muna son yar mu sosai muka baka ba dan ka cutar da ita ba dole ne ka kula da ita sannan ita yarinya ce har yanzu sai ka kara da hakuri da ita da wasu halayan yarinta ka kula mana da ita ku zauna lafiya ka rike ta da mutunci ka kyautata mata koma tsoran Allah zakaji wurin yin hakan” shiru aliyu yayi kansa kasa abbah ma yace “aliyu ya zama dole ka kula da amanar da muka ba dan wallahi ka saba mata ni da kaina zan saba maka kar kaga wai dan hakanan aka baka ita ka wulakanta mana diya dan bazan amince da wannan ba kasan hakkinta a kanka kuma kasan yanda zaka sauke hakki Allah ya taimaka” ciki ciki aliyu ya amsa Amin daddy yace “toh! Daa na Allah ya baka ikon yin daidai kawai zan ce” shima yace amiin baba yace “to duk dai kaji aliyu yanda suka fada hakane ka kula mana da yar mu sannan kuyi hakuri da juna Allah ubangiji ya baku zaman lafiya da zuria dayyaba ya hada kawunan ku” kowa na parlour din yace amiin sannan suka sallama aliyu ya tafi, acikin mota yayi shiru fareed yace “lafiya ” yayi shiru sai kuma yace “wlh fareed ina tsoron kar Allah ya kamani abun na bani tsoro i am helpless I don’t know how to see her as my wife ko nayi kokari bana iyawa amma fadan da su baffah sukayi mani suna cewa sun bani amanah naji tsoron Allah na sauke hakkinta dake kaina shike tada mun hankali bansani ba abun baya yiwu ne i can only see her as a younger sister I don’t why I can’t” fareed yace “kayi hakurii komai zaya daidaita InshaaAllah kaci gaba da addua.

STORY CONTINUES BELOW

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Gida ya cika pam! Da mutane ana ta hidiman biki ana nan da nan inaaya tunda tayi sallah la’asar yagana tazo tana mata gyaran na karshe sun jima anayi yi har wani magani ta kara mata akan wanda takesha kullum tace mata asamo mata kunun aya ciki zata saka maganin tashi haka kuwa tayi suka gama gyaran jikin ta hada mata wani ruwan turaruka tace ta shiga cikinsu for wani lokaci duk aka gama tayi wanka ta fito taga anty bee a dakin da mama da ummi laffaya ne sai atamfa dinkin skirt da riga color din ash da laffaya ash anty bee tace ta saka jiki ba kwari inaaya ta saka kayan da jewelries na gold sarka da yan kunne da zobe sai bangles manya guda biyu anty bee ta daura mata laffayan ta zaunar da ita nan sukayi ta mata nasiha su duka ukun suka gama 6 suka fito daga dakin suka kaita dakin mamii nan waterworks ya fara ta fashe da kuka ta rike mamii tana cewa “mamii dan Allah banason natafi” hakanan itama mamii ta daure ganin diyan nata na kuka ta dagota ta dunga mata fada anty bee tace “tun dazu fa motan tafiya da ita an kawo shi mamii tayi mata alama da hannu su tafi da ita anty bee ta jawo ta ta rufe mata fuska da laffayan da kyar ta saki mamii kuka take kaman ranta zaya fita suka sauko kasa da ita sai guda mutane sukeyi aneesah tazo ta rungume ta tasa kuka itama saiga twins suma kuka suke sun makale ta ba na wasa ba da kyar duk aka raba su daga jikinta aka saka ta mota suka tafi gidan baffah. Suna isa aka kaita wurinsu baffah itama nan suka fara mata fada baffah yace “fateema nasan ki bakida matsala amma ina kara miki fada da kibi mijinki kiyi masa biyayya kuyi hakurii da juna InshaaAllah zakuga da kyau” daddy yace “my tee inaso kisa hakuri a ranki kinji kuma kibi mijinki Allah yayi maki albarka” baba yace ” Allah yayi maki albarka kinji zaman aure sai hakuri da understanding” abbah yace “mamana daya miki wani abun da bakyaso ni zaki gaya ma wa in saba masa Allah yayi miki albarka ya baku zama lafiya” ai kamar ana tunzurata ta kara kuka ta rungume daddy harda shessheka daddy ya lallasheta mama ta fito da ita domin tafiya da ita gidanta suna saukowa kasa mimi ce hawaye a idonta itama sukayi hugging juna suna kuka anty bee tace “kai kunfa ishe mu kamar wacce baku kara ganin juna kullum ai kuna iya ziyartar ta ai ko” ummi ta janye mimi aka fita da inaaya suka sa ta a mota suka dauka hanyan gidan amarya dake life calm a garin abuja ita kuwa inaaya nata aikin kuka da suka isa ba kowa suka sa tayi addua ta shiga da kafar dama MashaaAllah kakeji gidan Amarya ya hadu ba wasa gidane upstairs da palour 3 bedroom 4 da guest room sai kitchen furnitures dinta sunyi kyau ba na wasa daga ka gani kasan ba kananan kudi aka kashe ba dakin dayake nata aka kai ta aka zaunar bakin gado baa dade ba mutane suka fara zuwa yan ganin daki kowa nata tofa albarkacin bakinsa cewa gidan yayi kyau an kashe kudi wurin ginasa da kayan dakin mutane sukayi shigowa suna tafiya fada Anty bee ta karamata sannan ta tafi itama zuwa yanzu ta rage kukan aleena tazo tace lokaci na tafiya yakamata ai shirin dinner yanzu tace inaaya ta tashi tayi wanka da sallah me makeup ta zo haka duk kowa yatafi domin shirya wa inaaya tayi wanka da sallah sannan ta zauna aka fara makeup din ta as usual simple akayi mata amma words basa iya describing kyawun da tayi sai MashaaAllah ta daura mata turban sannan ta taimaketa tayi slipping into gown dinta maroon dinkin ya karbeta inaaya abun sai godema Allah kaman ita tayi kanta sisters da friends sunata dawo wa kowa ya sha shirinsa kowa da kallan beauty dinsa saida photographer yazo ya daukesu pictures sannan motocin abokan ango suka fara zuwa don daukan yan matan, motan da aka saka amarya a nan ango yake ciki fareed na tuka wa tunda ta shigo motan ta gaishe su kai a kasa as usual ta gefen ido taga aliyu sanye yake da brown yadi yayi masa kyau wani daddadan kamshin da take sai shiga hancin aliyu yake har wani mutuwa jikinsa yayi karfe 8:30 suka isa dinner hall din blue velvet marquee wurin yayi kyau decoration yasha white duka sai da sukayi kusan 10minutes sannan suka fito aka jera zaayi entrance har mamaki kowa da ya san aliyu yayi wai dama yana da abokai dayawa haka” friends din ango side daya na amarya dayan side din haka suka fara shiga sai amarya da angon sai bayansu sisters ne a entrance din ma mutane da photographers sai capturing sukeyi saboda how perfect the couple looks duk da inaaya heels ne a kafanta aliyu ya fita tsayi ba kadan ba wakan happy day na tashi by patoranking har suka isa inda aka tana dar masu su zauna sai side dinsu inda friends zasu zauna event ya fara da bude taro da addua tunda aka zauna friends din su aliyu ke magana suna cewa fareed wai ina aliyu ya nemo wannan hadadan matan ai MashaaAllah aliyu yayi mata saidai kawai fareed ya masu murmushi, entertainment mc ya gama sai yazo ya kira bestfriend din amarya tayi speech inteesar aka kira ta gabatar da speech da har saida hawaye ta kare sannan ta koma aka kira fareed ma a bestfriend din ango shima yayi nashi speech din sai bayan nan lokacin abinci ne waka slow one dj yasa akayi serving kowa da abinci kala kala wanda kakeso traditional dishes da continental dishes snacks da komai da komai, tunda suka shigo suka zauna babu wanda yace da dan uwansa wani abu sai mutane dake ta zuwa suna daukan hoto tare dasu bayan abinci sai photo session shima aka gama sai aka kira amarya da kawayenta suyi rawa sosai suka sha rawa su ihsan,mimi,inteesar,sultaana,khaleesat and co bayan sun koma aka kira ango da friends dinsa ba laifi friends din sun dan taka, duk bayan wannan sai aka kira amarya da ango suyi couple dance haka suka fita suka tsaya tsakiya dance floor din inda aka rubuta FA20 love story tunda aliyu ya gani yake hararan fareed dan yasan aikinsa ne wakan weekend aka saka masu babu wanda yayi rawa cikinsu har wakan ya kusa ya kare mc yace yau idan basuyi couple dance dinnan ba gaskiya haka event dinnan zaya kare suna a nan wurin dan sai sunyi haushi aliyu yaji ba kadan ba dan yasan duk aikin fareed ne ya juya suka hada ido ya zuba masa harara shi kuwa fareed ya kashe masa ido suna tsaye yanda suke aka saka masu wait for me by johnny drille shima har ya kusa karewa shiru mc ya kara cewa haka zaa ci gaba aliyu da ya gaji ranshi ya bace yasan bayada choice kawai duka hannunsa biyu yasa ya kamo nata ya dan matso da ita suka da fara moving kadan ihuu ya cika hall din kowa da wayan sa yana daukan video wakan ya yi changing to perfect by ed sheeran ita kuwa inaaya yana rike hannun nata kaman an zare mata natsuwa sai duka da chest dinta yake ta kasa ko dago kai, shima aliyu tunda ya kamo hannunta yaji wani abu ya bi spine dinshi ya kura ma hannun nata ido da yasha jan kalle ga dogayen yatsunta dama aliyu yana matuqar san red henna a hannun mace kura ma hannun ido yayi kaman mai duba wani abu can daga dan gefe yaga zanen heart with F&A written a ciki sai ya samu kansa da kai babban yatsansa a kan rubutan yana shafa a ranshi yana cewa F&A fatima and aliyu but miyasa ma tayi? wani hali inaaya ta shiga jin yanda hannun aliyu ke kan nata yana shafa wa suna cikin haka mc yace su canza wani dance style for the last time if not haka zaa ci gaba da kallonsu har event ya kare Aliyu duk ga gama kulewa da jin haushin fareed kan abunda yasa mc din yayi babu yanda ya iya haka ya saki hannunta daya dayan kuma ya dora on his bosom yasa hannunsa on her waist jiki ba kwari dayan hannunta ta do ra kan dayan shoulder dinshi suka dan dunga swaying a hankali sai hasken wayoyi ke haska su kowa nata video yana pictures waka ya canza to say you won’t let go by james arthur har wakar ya kare suna swaying sai da ta gama ya saketa mc din yasa akayi masu clapping for the wonderful dance sannan suka koma sit din su inaaya duk jiki ba kwari ta koma wurin zama.

Bayan sun koma sit din nasu mc ya kira sisters suma suxo suyi rawa nasu sun sha rawa ba kadan ba inaaya dai zaune take tana kallonsu sai rejoicing kowa yake yi hawaye ya taran mata a idanu tasa hannu ta goge Aliyu yana kallonta a ranshi yayi tunanin ko miye matsalan ta, bayan rawan da suka sha mc ya umarcesu kowa ya koma yanzu time for the couple to cut the wedding cake iya kulewa aliyu ya kule kan abunda fareed yayi kin tashi sukayi aliyu ya jawo wayanshi ya yi ma fareed message “wai miye haka wlh I regret leaving everything to you miyasa ka mun haka” murmushi fareed yayi sai yayi typing “chill man i was just fulfilling your dream wedding dinner oya now don’t be strong headed mana” mc ya kara kiransu babu yanda suka iya saboda duk mutane na nan suka tashi suka nufa wurin cake din wedding cake ne five steps kaman ka cinye idan ka ganshi knife aka kawo na cutting aka ba inaaya a hankali ta karba ta sa a cake din sai Aliyu ya dora hannunsa kan nata akayi cutting after the counting of five kowa na wurin ya taba ana ihu, ba nan ya tsaya ba mc yayi announcing sai sunyi feeding each other saura kadan aliyu yayi tsaki dan abun ya ishesa knife din ya dauka ya yanka small cut ya dauka yana kaiwa bakin inaaya a hankali ta bude bakin ta karba mutane nata videos yan awwns association ma sunata aikinsu na awwn! Awwn! Itama inaaya jikin duk ya gama mutuwa ba kwari tayi cutting piece kadan ta dauka hannunta na shaking kanta a kasa ta kai bakinsa ya karba yaci a hankali sannan suka koma suka zauna aka rufe taro da Addua mc yace it’s time to dance dance dance and dance ai nan dance floor ya cike sai rawa suke iya karfin su kowa da kowa sai karfe 12 duk aka watse wurin event din da motocin da suka zo duk suka bi aka koma gidan amarya daga ita sai kawayen ta a gidan aka bar su inaaya da duk ta gaji suna shiga ta cire takalman kafanta sannan ta cire jewelries din da kayan jikinta hot bath ta yo ta fito duk sai tagansu a tsaye kallonsu tayi tace “lafiya” ihsan tace “gida zamu tafi mana” marairaice fuska inaaya tayi tana kallonsu lateefa tace “yess inee gida zamuje sai kuma gobe InshaaAllah Allah ya baku zaman lafiya” mimi tace “let’s get going guys ana jiranmu fa” kawai hawaye ya faru zubowa idanunta sai kuka ta karaso ta yi hugging sultaana tana cewa “how could you guys do this to me please don’t leave me alone” duk sai jikinsu yayi sanyi da duk sun shirya tsokanan ta amma ganin tana kuka duk jikinsu yayi sanyi duk karasowa sukayi suka yi hugging dinta suna bata hakuri mimi tayi Murmushi tace “sorry inee dama so muke mu ja ki fa” duk dariya sukayi suka ajiye bags dinsu da duk suka dauka suka zauna haushi inaaya taji ta turo baki sai can kuma tace “intee please where are my clothes ina so nasa kayan bacci ne” inteesar tace ta duba closet but baayi unpacking ba ta shiga closet din ta dudduba akwatunan nata wani joggerset ne pink ta ciro ta saka da black hula sannan ta dawo dakin suna zaune kowa da waya a hannu mimi na cewa “wow this video is just perfect” yumnerh tace “ai Allah yayi ma mc dinann albarka” duk suka fashe da dariya sabeeha tace “hmm ai baza ku gane yanda ya burgeni ba” nasamu abun posting daga nan har wani month ya kare” nan ma duk sukayi dariya inaaya rolling idanu kawai tayi  tasamu wuri ta zauna aka turo kofan dakin farhana da haneef da khady ne har lokacin basu cire kayansu na dinner ba khady tace “ku anya kan ku daya ya zaku bar kofa parlour kasa bude baku saka key ba duk kuna nan inteesar tace “oops sorry wlh gajiya mantawa mukayi” khady tace “to sannunku yanzu bakujin yunwa ne kuna nan zaune dan nasan bakuci abinci wurin dinner ba” kaman suna jira duk suka fara wlh kaman kin sani ya khady yunwa ba kadan ba tace “to ku gode mani da na saka aka siyo maku abun da zakuci… uhmm bara mu tafi yanzu nagaji bakuji kafa na ba” dariya sukayi mata sai tace “uhmm inaaya mijin ki na kasa fa you guys ku sauko muje” jin abunda khady tace yasa inaaya jin wani iri duk suka tashi inaaya wani dogon hijab na sallah tasaka sum sum suka sauka kasa aliyu da fareed ne zaune a parlour kawayenta duk suka gaishe su fareed yace “to kawayen amarya ga abinci nan mun kawo maku saboda kar a samu matsala can cikin dare” duk sukayi dariya sannan yace “amma fa da mukazo kofan bude danAllah ku rufe shi da key yanzu idan mun fita akwai me gadi idan dai da wani abu” duk amsa masa sukayi da to sai yayi masu sallama suk nufa kofa suka tafi su kuwa yan matan suka rufe kofan da key sannan suka dawo parlour rufaidah tace “to yanzu let’s take a tour a gidan mugani ni wlh ina son gidan nan dama nii” duk dariya sukayi sadiya tace “ashe ba ni kadai nakeson gidan ba inee zan maki zaman daki danAllah” dariya kowa yayi inteesar tace “sady so kike a koraki wlh wayace maki ana zama gidan new couple” mimi tace “lallai sady da ace nice inee ni kika tambaya kiri kiri zance miki aa gaskiya sady I need some privacy and alone time with my love” dariya sukayi sultaana tace “toh lover girl munji” inaaya da ko mi batace masu ba tace “I’m sleepy ni dai” ihsan tace “to lets take a tour sharp sharp” haka suka fara da kasa parlour biyu ne sai guest room da toilet da wani room kuma daban sai suka hau sama parlour daya ne an sa mashi L cushions turquoise blue ga curtains kalan kujeran yayi kyau lateefa tace “kai I’m in love with this parlour wlh” sunata yayi kyau sai dakuna uku a sama daya na inaaya na gadon turkey ne grey a ciki sai daya dakin kuma royal bed ne fari sai dayan dakin da yake na Aliyu navy blue gado ne a ciki dakin yayi kyau ba kadan da wani glass window babban idan ka bude shi kama ganin view din waje inaaya kawai taji dakin ya burgeta sosai duk suka gama sai wurin 1 sannan sukayi bacci.

+

STORY CONTINUES BELOW

              Tunda safe  knocking ya tada su suka tashi inteesar ta fara tashi ta sauka kasa ta bude kofan su khady ta gani da su aneesah sunsha anko duk iri daya na swiss voile da kulolin abinci suka shigo dashi suka ajiye a wurin dinning table suka karasa ciki khady na cewa “lallai yaran nan jiya yaushe ku kayi bacci da har 11 baku tashi ba inteesar tace “wlh fa 1 muka kwanta kawai dai gajiya shiyasa” farhaana tace “ai yau sai a koma gida a huta da kyau da kyau” sama suka karasa a dakin inaaya suka tarar da ita zaune gefen gado haneefa tace “Anty amarya ina kwana” inaaya tace “habaa ya hanee ko kowa yayi ke ai nace banda ke” dariya farhana tayi tace “kenan mu in munce ba laifi ohh inee inee I can’t believe it wlh komai kaman ba gaske ba” khady tace “bari kedai duk wanda yace mun inaaya will get married before me zan masa kallon bakada hankali” sukayi dan dariya sai khady tace “yanzu dai duk ku tashi ga breakfast can from Ammah tasa mukawo maku kuma wurin 2 zaa zo a tafi dake gidan abbah tunda budan kan 4 ne ku tashi kuyi breakfast kiyi wanka lokacin me makeup tazo duk dai ku gama shiri before 2” a sanyaye inaaya ta amsa mata da to suka sauka kasa sukayi breakfast din dan kadan inaaya taci da kyar sannan ta koma sama tayi wanka ta fito ta tarar da ya aleena da me makeup hugging juna sukayi da aleena sannan tace “yauwa just in time ki zauna a fara maki makeup kar lokacin ya kure let me get your clothes suna ina” inaaya tace “a small trolley cikin closet” ta zauna me makeup ta fara tsara mata aleena taje ta dauko mata kayan wani lace ne navy blue dinkin straight gown me zani attached to it ya sha stones a jiki sai laffaya light blue mai kyau da wasu large flowers black a jiki da stones a kan flowers din ba jimawa sosai aka gama makeup din aleena ta taya ta tayi slipping cikin kayan ta aka daura mata head shima royal blue tasa jewelries dinta na gold aleena ta taya ta ta nada mata laffayan tubarakallah tayi kyau mai makeup din ta dauke ta pictures sannan sukayi bankwana inaaya ta mata godiya sosai  sannan ta tafi kofan dakin aka turo anty fareeha ce ta shigo ciki sanye da anko dinsu na voile tace “ah ah iyyeh amaryan mu kin ganki kuwa kai MashaaAllah Aliyu ai sai da rude ya ganki wannan kyau haka” dariya aleena tayi tace “nima fa nagani magana kawai ke banyi ba” kakalo Murmushi inaaya kawai tayi fareeha tace “leena please I want some alone time with her” aleena tace to ta tashi ta fita ta rufe masu kofan, kusa da inaaya fareeha tazauna ta fara magana “inaaya kinsan ke ba yarinya bace anymore ko” gyada mata kai inaaya tayi sai aleena taci gaba “kinsan dai yanzu kin canza rayuwa ba irin wadda kikayi a gida itace a nan ba akwai difference shi aure da kike gani ba wasa ne ba ki dauka kawai ibada ce it will be easy for you dan nasan the condition in which you guys were married amma babu abunda zaya canza nasan koma miye aliyu zai kula dake ke kuma the least you can do is kiyi masa biyayya ko abu yace kiyi idan har bai saba ma musulunci ba kiyi masa sai kiji dadin zaman, zaki na ganin kaman he is not nice ko wani abu but no aliyu is the most nicest and softhearted person you’ll ever find you’ll never find a nice husband like him never inaaya kawai the reason he is this way is because of what happened to him which i am in no place to tell you anytime your husband feels like telling you he sure will, take care of yourself and your husband please” inaaya a hankali ta amsa da to tayi mata godiya a ranta tana mamakin me ya samu aliyu a baya a haka anty bee ta shigo dakin tace “yauwa madallah da kika shirya har 3 yayi fito muje suka rufe mata fuska da laffayan suka tafi da ita aka saka ta mota suka nifa gidan abbah.

            Cikin parlour suka nufa da ita direct suna shiga gidan inda Ammah da yan uwan ta da sauran yan uwan Abbah suke aka tarba amarya a kasa ta zauna ammah ta ja ta ta dora kan kujera tace “habaa ya zaayi a ajiye man diyata kasa” duk manyan dake parlour suka murmusa Ammah ta bude mata fuska duk sukayita MashaaAllah duk aka gama ganin amarya ammah tace a kaita part din aliyu kafin lokacin da zaa fara budan kai din su aleesha da aleena da kawayenta suka kaita part din ko baa gaya mata ba tana shiga tasan part dinsa ne dan yanda duk yake cike da kamshin sa, a nan amarya ta zauna har sai bayan la’asar mimi ta dan gyara mata makeup sannan aka fito da ita compound din gidan inda akayi decorating event din yayi kyau sosai dangi sun ba wa amarya suna noor tasha kudi da liki sosai sai can da yamma ango yazo da aminin nasa yasa light blue shadda yayi kyau ya karaso ya zauna kusa da amaryan akayi ta masu pictures har magrib yayi duk jama’an da suka zo biki sun watse sai amarya da kawayenta da cousins karfe 7 aka kai inaaya Ammah tayi mata nasiha kaman uwa sannan aka koma da ita gidanta da kawayenta da su khady sai anty fareeha da anty fareeda sai anty bee suma dai basu jima ba sukayi ma inaaya sallama da fada na karshe tayi kuka sosai saida aleena tayita lallashinta har tayi shiru tace ta shiga tayi wanka tayi wanka tana fitowa taga wani dogon riga na voile aleesha ta fiddo mata tace ta saka tana bata rai haka ta saka wurin karfe 8:30 su aleena sukazo suna mata sallama nan fa inaaya tasha kuka kaman karamar yarinya ta dinga kuka suna bata hakuri aleena da ummi sukace zasu kara zuwa kafin su koma haka suka samu suka tafi ya rage daga ita sai abokan ta sai khady da haneefa da farhana suna nan zaune a dakin mimi da inteesar suka fito daga closet da wani abu hannunsu a ksn gado suka ajiye kowa na masu kallon lafiya suka kalla juna suka fashe da dariya yumnerh ta jawo ta duba wani lingerie ne black na net tsayinshi baifi thighs din inaaya zaya tsaya sai na samanshi da zaka iya using dogon hannu ne silk amma shima guntu ne dukkansu dariya suka saka mimi tace “serious something guys miye na dariya kawai fa kayan bacci muka dauko mata kar tasha wahalan nema” sultaana tace “amma mimi wulakancin ku dayawa yake” sukayi dariya dakin sukaji an bude ya khady ta shigo 9:30 tayi tace dasu “guys ga angwayen nan gaskiya siyan baki zaayi baa sauko da amarya sai sun biya” duk suka yadda nan dama inaaya na zaune a daki  suna zaune parlour sai ga su sun shigo aliyu da fareed da wasu abokansu su biyar tashi yan matan sukayi suka basu wurin zama suna gaishe su suka gaisa fareed yace “ahh to ya banga amaryan tamu ba kuma ita mukazo gani” dariya sukayi mimi tace “haba bro inlaw not so fast amaryan mu fa is not cheap pay first” wani friend dinsu mai suna kabeer yace “ahh yanzu duk mun biya sadaki nan ma muzo ku tare kuce sai mun biya” duk dariya sukayi banda aliyu dayake zaune shiru ya gaji so yake su tafi yace “nawa kukeso” sabeeha tayi dariya tace “kun gani ko gashi ango bai ma damu ba kawai ko nawa ne mu fada yana san ganin amaryansa” duk sukayi ta dariya ana shewa sai farhaana tace “five hundred thousand yayi da saukin da mukayi maku” wani abokin nasu abdulkareem yace “kaii kaii kaii yanzu ina mu mukayi maki kama da kalan kudi ina zamu samo five hundred thousand haba a diba mana” sukayi ta shewa ana ta ciniki sukayi reaching agreement suka basu two hundred thousand sannan inteesar da sultaana da mimi da ihsan suka nufa sama suka sauko da amarya  an rufe mata fuska da babban gyale suka zo har wurin kujera suka zaunar da ita gefen Aliyu dake kan wani two seater abokan sa nata “MashaaAllah to aliyu ka bude muga fuskan amaryan ko” ba dan rai yaso ba aliyu ya juya yayi facing dinta yayi lifting veil din kanta a kasa bata dago ba fareed yace “amarya yau ba magana” a hankali ta dago ta kallesu duk ta gaishe su da dan Murmushi duk suka dai masu fatan Alkhairi nan fareed yace “to yanmata dare nayi yakamata mu gudu yanzu ko nan zaku kwana” dariya sukayi suna ihun a’a a’a a’a yayi Murmushi duk sama suka nufa suka dauko kayan su inaaya da ta fara kwalla tana zaune nan ta kasa tashi suka sauko lateefah da khaleesat sukazo suka yi hugging dinta suna mata fatan Alkhairi tashi tsaye tayi inaaya ta rungumesu tana fashewa da kuka suka samu ta sake su haka duk sukayi hugging dinta suna mata fatan Alkhairi daga karshe mimi sultaana da inteesar sukayi engulfing inta into a warm hug nan kukan nata ya karu taki ta sake su sai faman kuka take har tasa su kaman suyi kukan sun kusan 10minutes a haka har saida haneefa tazo tace “mimi ku zo mu tafi ana jiran mu fa” da kyar khady tazo ta rabo su ukun daga inaaya ta dan lallasheta sannan suka tafi, kujera ta zauna har lokacin tana ta faman goge hawayen dake sauko mata Aliyu daya raka su ya rufe kofa ya dawo zai wuce daki yaganta zaune tana kuka ta bashi tausayi wata zuciya yace ya bata hakuri ya karasa parlourn a hankali inaaya na ganinshi ta goge hawayen idonta yasamu kujera ya zauna shiru ya biyo baya kusan 5minutes sannan yafara magana “uhmm so i I’m sorry for everything you’re going through i know it must be hurting and you’re too young for all that.. it’s because of me you had to go through all this had to get married at young age I’m sure you definitely have your dreams and I’m also sorry for what i am about to say” yayi dan shiru sai kuma ya ci gaba “the thing is I actually don’t expect anything from this marriage when i say nothing I mean nothing I don’t expect anything from this marriage and also from you and i am sorry to say please don’t also expect anything from me also yess quiet alright I’ll provide everything you’ll need but apart from that nothing more..to the world we’re married and leave under the same roof but to me you’re like inteesar and mimi that’s younger sisters yess I don’t bite you can feel free and talk to me as an older brother” tunda ya fara magana bata ce komai ba but she was shattered within hearing those words from him sai kuma yace “I’m sorry if you find what I said hurtful but it’s the bitter truth, i know you must be hungry there’s something to eat it’s on the dinning table” yana gama fada ya tashi yayi sama bayan shi inaaya tabi da kallo zuciyanta na zafii saida tayi kusan 20 minutes zaune sannan ta tashi a hankali ta kashe wutan parlourn da dining ta shiga kitchen ta bude fridge ta dauka bottle water ta nufa sama dakin dayake nata ta shiga ta tube kayan jikinta tasa pyjama’s ta shiga toilet ta wanke fuskan ta tayi brush ta fito har zata kwanta kaman wacce ta tuna wani abu ya tashi ta fara neman wayanta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]