[Advertisements⬇️]

INAAYA CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

INAAYA CHAPTER 10

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washe gari sai karfe 10 suka tashi saboda gajiya suka tashi sukayi wanka sannan suka sauko kasa sukayi breakfast pancakes ne ba laifi inaaya ta dan sake ta ci sosai suka gama mamii tace suyi sauri karfe 12:00 ne waliman aleesha a gidan iyayen mijinta dake nan abuja dawaki extention layout, daki suka nufa suka daura dankwali inteesar tasaka wani voile purple da pink dinkin straight gown sai mimi ma irin voile din ne amma nata peach da blue dinkin doguwan riga cinderella style ne sai inaaya kuma nata wani black da blue dinkin doguwan riga A-line tasa wani blue veil mai kyau yasha stones sai sultaana wani atamfa tasaka dinkin straight gown kasa suka nufa suka tafi waliman tare da mamii a can suka tarar da ammah har ta je duk suka je suka gaida ammah inaaya duk sai taji tana jin nauyin ammah, dakin da aka ajiye ya aleesha suka nufa tayi kyau cikin wani lace dinta red mai kyau anyi mata makeup an daura mata dankwalin ta yayi kyau sai veil ta dora har kan kai suna zuwa sukayi hugging dinta tayi smiling tace “darlings nayi missing naku wlh shine jiya baku zo ba kuka tafi dinner ko” murmushi sukayi mata sai ta kalli inaaya cikin tsokana tace “Anty amarya an bar kukan” inaaya dai batace komai ba dan smile kawai tayi mata dan yanzu abun ya bar bata mamaki ta amince da haka

kaddarar tata take. Anyi walima an gama sai da yamma wurin 5:00pm zasu tafi aleesha tayi kuka tana cewa su zauna sai dare, haka suka samu suka tafi sultaana tace su sauke ta gida suka kaita har gida suka shiga gaida ummah suka gaisheta nan ta tsaresu tayi ma inaaya nasiha don jiya sultaana ta gaya mata abunda ya faru tayi mata Allah yasa Alkhairi sukayi bankwana da sultaana suka tafi gidan su inaaya suka koma sai mimi tace “nima yau fa zani koma gida tunda dai Alhamdulillah hidima is over” inaaya tace mata “ki kara kwana mana mimz” tace mata “no inee kinsan gobe ake komawa school and inada lectures by 4 so inaso naje gida nayi settling” kai inaaya ta gyada alamun gamsuwa sai tace ma mimi “please let the marriage stay between us I don’t want mutane suyita damuna da questions yan department din nan namu kinsan su” kai mimi ta kada mata sai inaaya tace “not even Ihsan please” ta amsa mata da to shiru ya biyo baya inaaya na tunanin ya rayuwar tata zata kasance a yanzu da auren wani a kanta. Bayan sallah magrib ne ya habib yazo zaya maida mimi gida yana ta insisting akan ta bari yazo yayi missing din ta he wants to see her su inaaya tace ma “to amarya natafi Allah ya tabbatar da Alkhairi, ya habeeb is here” kallonta inaaya tayi tace “mtsww wace amarya please ke dai wuce mu rakaki lover girl komai ya habeeb” murmushi kawai mimi tayi sai inteesar tace “wlh kuwa ni da su abbah sun gane ke suka aurar saboda naga kin matsu” mimi tayi dariya tace “rufamun asiri” hijab suka saka zasu rakata suka tarar da mamii da ya sa’id da twins a parlour tayi ma mamii sallama mamii tace “to mimi Allah ya huta gajiya ki gaishe da umminki sai mun shigo” ta amsa da to sai ya sa’id yace “to Aminatu sai aje a huta wannan rawa da aka sha” dariya mimi tayi tace “kai ya sa’id inteesar dai zakayi ma maganan rawa ta fi ni” tana fadan inteesar ya kalleta suka hada ido suka sakin ma juna Murmushi sai suka fita raka mimi har bakin mota suka je sannan ta shiga suka gaida ya habeeb ya amsa yace “inaaya ashe abunda ya faru kenan to Allah ya tabbatar da Alkhairi ciki ciki tace amin tana hararan mimi tasan ita ta gaya mishi sukayi sallama suka tafi su kuma suka shigo cikin gida parlour suka zauna nan ana ta fira mostly ya sa’id ne da inteesar sukeyi sai mamii kadan kadan inaaya dai tayi shiru tana ta tunani kala kala.

+

Aliyu ne zaune a parlour din part dinshi shi da fareed dake ta faman waya da khady, gajiya aliyu yayi ya fixge wayan ya kashe yace “kun wani ishi mutane da waya idan kun matsu kuce a daura maku aure mana kuntafi can kuyita maganan” dariya fareed yayi yace “please don’t disturb my life mana me kake so nayi maka? na zauna na maka fadan akan ka rungumi matarka da su abbah suka daura maka aure da ku zauna lafiya she’ll make the best wife for you but all in vain ya kakeso nayi maka ni ba sai naje ma rungumi tawa fiancée din ba” hararanshi aliyu yayi yace “to din anki a runguma wai i don’t know what everyone is thinking me kuke so naje gidan su nace mata that i love her and that I can’t do without her or what” dariya fareed yayi yace “hakan ma da zakayi daidai ne” haushi fareed yaba aliyu yace “you’re sick wallahi” sai fareed yace “but seriously aliyu you should be nice and not harsh on the girl wlh she’s scared of you ni na kula ka dinga sakin fuska koma me zaya faru nothing can be changed she’s your wife treat her how you intended to treat the one you’ll love to marry remember what you always say you’ll try hard to treat your wife how the prophet SAW treated his wives” shaking head aliyu yayi yace “may Allah forgive me but I can’t I can’t even look at her as a wife just a little younger sister” fareed yayi tsaki yace “kai kaima ka sani keep forming big older brother sanda zaka zo ka kamu da son diyar mutane ka rude babu ruwana na gaya maka ma” hadiye rai aliyu yayi yace “Allah ya sawake” fareed yace “shikenan lets see” ya karbe wayanshi ya sake dialing numbern Khadija yana bata hakuri akan kashewan da akayi shi kuma aliyu ya zauna a nan yana tunanin maganan fareed a zuciyan shi yace it can never be possible ma.

2

STORY CONTINUES BELOW

Washegari karfe 11 suka tashi bacci sun sauko yin breakfast mamii tace suje kitchen suyi abun su tace “kuna yara mata sai baccin tsiya bare ke inaaya yanzu haka zaki tare a kai ki gidan naki ki je kina bacci sai waye zaya ciyar da mijin bansan shirme fa” ita kuwa inaaya da anyi mentioning ita ke da aure sai jikinta yayi sanyi ta dinga tunanin wannan wace irin rayuwa ce ma haka sukayi making golden yam da kidney sauce suka ci sannan mamii tace su shiga kitchen su yi abincin rana suka shiga suka girka chicken biryani rice da wani peppered beef sauce inaaya ta hada zobo tasa cucumber sai kamshi yakeyi suka jera komai a kan dinning table sannan suka nufa sama suka sake wanka sukayi sallah inaaya ta saka wani riga a-line na wani fabric by ladies lounge black and white tayi kyau sosai ta yafa black veil sosai tayi kyau fuskanta daga kohl sai lip gloss a dakin suka zauna suka fara kallo a mackbook din inaaya suna kallon bahubali 2 har laasar yayi sannan sukayi sallah sai mamii ta kirasu suyi lunch. Aliyu tunda ya tashi yau yana daki saida abbah ya aika a kirashi yaje ya tarar da abbah da ammah a parlour din abbah yace mishi “aliyu kaje gidan daddy tun Saturday” yace aa sai abbah yace “to jira kakeyi na gaya maka kaje ko ya na?” Yace “abbah kayi hakuri dama yau zanije” abbah ya amsa mishi da to sai ya tashi ya koma daki hakanan ba dan yaso ba ya shirya cikin kananun kaya black jeans da wani shirt white mai rubutun black a jiki ya dauka makullin mota ya fita a hankali yake driving har yake isa gidan daddy cikinn 10minutes. Bayan sun gama lunch suna daki suna kallo kawai sai ga fauziyya tazo tace “yaya inaaya mamii na kiranku tana kitchen” amsa mata sukayi da to suka nufa kitchen din har suka wuce ta parlour basu kula da mutun ba saboda hankalin su baya nan suka shiga suka tarar da mamii kitchen tace “inaaya ga aliyu can parlour ki hada ruwa da drinks da abinci ki kai mashi” ji tayi kaman ta zuba ihu haka ta dauko tray tasa ruwa da drinks sai mamii tace “ki hada da zobon da kikayi dazu” ta gyade kai ta dauko shi ta daura sai ta samu wani babban tray ta sa kulolin abincin da plate da su serving spoon tace ma inteesar ta tayata mamii tace “aa ki yi da kan ki kar ki sake ki saka ta har hawaye ya taru idanunta sannan ta fara daukan karamin tray din a hankali take takawa har ta isa parlour tana shiga kamshin turaren sa ya bugi hancin ta tayi kasa da kanta zuciyanta na bugawa har ta isa gabanshi ta jawo side table a daura mishi a kai tana cewa “ina wuni” kaman mai koyon magana ba yabo ba fallasa ya amsa mata da “lafiya lau”yana kallonta briefly ya maida kanshi a wayan shi haka ta koma ta dauko dayan tray din tazo shima ta ajiye shi sannan ta koma kitchen tace ma inteesar suzo su je daki har sunyi hanyan fita kitchen mamii tace “ina zakuje ne” sai inaaya tace “mamii na gama kaiwa daman daki zamuje” kallonta mamii ta tsaya yi tace “ke kinada hankali ma kuwa anya? kinje kin jera mishi tray mi kikeso yayi ke ba ke yakamata kije ki zuba mishi ba sannan ki zauna a can parlour sai ki barshi ke ki kama gabanki kina wani behaving kaman bakisan mi akeyi ba, inaaya kinsan cewa aliyu in that parlour is your husband it can’t be changed so it’s better kiyi abunda ya kamata ba wai wannan attitude din ba” hawayen da take rikewa har sun sauko gogesu ta shiga yi taba mamii hakuri ta nufa parlour din inda yake zaune har lokacin wani kujera ta samu ta zauna gefen wadda yake shiru kusan 10minutes da kyar tayi mustering courage a hankali ta zame ta sauka kasa ta dauki plate zata zuba mishi ta bude kulan ta shiga zubawa serving spoon biyu tasaka taji yace “it’s ok” cikin wata murya mai sanyi da ta ratsa jikinta ta bar zubawa ta zuba masa sauce din shima kadan yace ta isa dago kai tayi a hankali ta mika mishi ya karba cup ta dauka kawai ta shiga zuba masa zobo instead of drink kallon hannunta ya tsaya yi tana sa zobon a hankali hannunta ya tsura ma ido da yasha lalle da wani bracelet mai kyau da sauri ya kauda kai yana mamakin yanda akayi tasan zobo yakeso at the moment ba drink ba, wuri ta samu ta zauna tayi kasa da kanta abincin ya fara ci a hankali yazata baza ya cinye ba amma ya samu kanshi da cinyewa tas! Ya mishi dadi ya dauka zobo yana kaiwa baki yafara sha ya lumshe ido a zuciyanshi yana cewa there’s something special about this zobo ya shanye ya kara zubawa ya sha sannan ya dago ya kalleta yanda ta takure a zaune daka ganta tayi wani iri sai tabashi tausayi yayi shiru for some seconds ya gyara murya yace “I’m sorry for what happened I know it’s not your choice but what can i do what can you do nothing we just have to pray to Allah and everything will be ok” a sanyaye take sauraron shi har cikin zuciyanta take jin muryan nashi ta gyade mashi kai a hankali sai yace mata “I’ll be going now ya tashi itama tashi tayi a tsaye taga yana matso inda take zuciyan ta yanata bugawa jinshi very close to her hannu yasa a pocket ya ciro wallet dinshi ya fiddo wani naira master card tana nan still kaman an dasa ta a wurin ga kamshin turaren shi da takeji sosai gashi tsaye gabanta zuciyanta bai bar bugawa ba ji tayi ya kamo hannunta a hankali runtse ido tayi saboda yanda takeji zuciyan ta kaman ba nata ba yanda yake bugawa card din ya dora mata a hannu ya kalleta yaga yanda ta rufe ido ga chest dinta yana beating da karfi sai ya saki hannun nata yace “you should take this you can use it for your needs the pin is ****” ya juya ya wuce yana wucewa ta bude ido tana bin bayanshi da kallo har ya fita sannan ta kalla hannun nata kusan 5minutes tsaye sannan ta kwashe kayan ta nufa kitchen ta kaisu sannan ta tafi daki ta tarar da inteesar ta cigaba da kallo tana shiga ta nufa wurin dressing mirror ta ajiye card din ta shiga toilet ai kuwa tana shiga inteesar ta tashi ta nufa mirror din don ganin me ta ajiye ai kuwa card din tagani ta jawo shi taga na ya aliyu ne sai ta ajiye tayi murmushi sannan ta koma taci gaba da kallon ta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Inaaya ce kwance a daki ita kadai tayi shiru tana ta tunani abunta karan wayanta ne ya dawo da ita daga tunanin nata sultaana taga tana kiranta ba tsayawa ta dauka tace “hello babe” daga dayan bangaren sultaana tace “amaryaaaa how far” bata rai inaaya tayi tace “miye haka sultaana” dan dariya sultaana tayi tace “sorry sorry, so dama i wanted to tell you to get ready there’s going to be a funfair at millennium park today and I think it’ll be fun mu je” murmushi inaaya tayi don dama ta gaji da zaman gida sai tace “ohhk sounds good but kin gaya wa mimi and intee” sai sultaana tace “no na gaya ma mimi thought inteesar na gidanku” sai inaaya tace “no yau tunda safe taje gida kayanta sun kare zata dauko shaa ku biyo ku daukeni sai ki gaya mata” amsa mata sultaana tayi da “to get ready will be there in an hour with mimz and intee” sannan suka kashe wayan ta tashi ta nufa toilet ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wani straight skirt blue da riga sleeveless black sai tasa ka abaya black plain ne sai wurin hannun kawai ke da wasu stones masu shining tasaka black turban da veil din jallabiyan sai ta fiddo jikanta black na dolce and gabana sai takalma hermes black color, zaune take a daki bayan ta gama shirin nata tana jiran zuwan su don ta dauka kusan one hour tana shirin. Sai after 2hours har inaaya ta gaji tayi sallahn laasar sannan sai ga su sunzo duk kaman hadin baki sun saka abaya kowannen su mimi tace “ohh ni amina kinga yanda kike shining inaaya kin kara wani haske” dukan wasa ta kai wa mimi tace “bansan wulakanci fa” haka saida suka gama yan surutansu sannan suka fito daga dakin da niyyan tafiya.
Mamii na zaune a parlour ita da aneesah tana ta bata labarin zuwan nasu gombe kai amarya sai ga su inaaya sun sauko kasa su duka hudun mamii a ranta take cewa ko ina zasuje parlour din suka zauna dayake duk sun gaisa da mamii da suka zo sai inaaya tace “mamii please zamuje wurin fun fair a millennium park” sai mamii tace “so?” Dan shiru inaaya tayi sai tace “tambayanki wai nayi mamii ki ban permission” wani murmushin takaici mamii tayi tace zauna nan tana mata nuni da kujeran dake opposite dinta sai tace “inaaya ke dai ba karamar yarinya bace kuma a zamanin nan da yara suka san komai ko aneesah nan da kike gani” sai mamii tayi pause tace “aneesah bamu wuri” sum sum aneesah ta tashi ta bar parlourn ta haura sama sai mamii tace gaba “ko aneesah bazata dinga yin wannan sakarci da rashin wayau da kike yi ba, amatsayin ki na musulma mai zuwa makarantar islamiyya duk ba littatafan da bakuyi mostly kinsani kuma malamai na fada kina ji” ita dai inaaya tayi kasa da kanta shiru don har ga Allah batasan me tayi ba mamii ta ci gaba “abun naki ma baxan saka shi a yarinta ba saboda ke dai ba wata yarinya bace a wasu kauyuka yara yan shekara 12 ake yi wa aure kuma su zauna ko yaran kauyen sun fi ku na birni ne ko miye ohon muku” sai ta juya ta kalla su mimi tace “yanzu ku kunga ya dace hakan” kallon mamii sukeyi in confusion sai kawai mamii taci gaba “yanzu ku dukkanku bara na maku wata tambaya, ke mimi da zaki baro gida hakanan kika fita kika tafi ko kin tambaya izini” mimi tace “mamii wallahi sai da na tambaya ummi da baffah duk suna tare na gaya musu kuma sun bar ni” mamii tace “very good ke fa sultaana” sultaana tace “mamii na tambayi ummah har tace ko driver zaya kaimu nace aa ni zanyi driving na daukesu mu wuce” nan ma mamii tace “very good ke fa inteesar” intee tace “mamii ammah fa tasani ki kirata ki ji kuma” mamii tace “aa kawai ba ce wa nayi zan kirata ba tambaya ne, ke fa inaaya” jiki a sanyaye tace “mamii shine nazo ina tambayan ki” cikin haushi mamii tace “kin rufemun baki nan ko sai na buge shi, ai ina ce nima dai ina da mahaifiyar nan tana borno idan zani fita ita kike ganin ina kira na tambaya permission” inaaya gabanta ya wani buga dum! Sai lokacin ta fahimci inda zancen mamii ya dosa mamii cikin fada tace “ba da ke nake ba hajiya kikaga ina kira na tambaya idan zani fita” hawaye ya cika idon inaaya ta gyade kai alamun aa da karfi mamii tace “da baki zaki bani amsa” har hawayen sun fara zubowa inaaya tace “Aa daddy kike tambaya” sai mamii tace “to kinsani kenan kuma ke ba mahaukaciya bace kinsan cewa kin fita daga hannunmu yanzu kawai dan dai baki tare a gidan mijinki ba doesn’t mean mu zamu baki damar fita dukkansu nan sunje sun tambaya izini daga wanda suke kasansu sai ke, yes bance bazaki tambaya nawa ba tunda a cikin gidan ki kike but sai ki fara tambayan na mijin naki sannan ki tambaya nawa ko kin taba jin ance mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba” mamii ta dinga ma inaaya fada ita kuwa inaaya hawaye ke ta zirarowa daga idanunta zuciyanta na mata wani nauyi wai yau itace mamii ke ma fada haka abunda bata cika yi ba sai idan ran ta ya bacii ba kadan ba which is rare, wai yau itace sai ta tambaya izinin wani a matsayin miji kafin ta fita data tuna haka sai hawayen su karu, daga karshe mamii tace “tashi ki bani guri ki wuce kije ki nema izinin mijinki idan ya barki idan kuma bai bar ki ba ko baki nema ba babu inda zakije” da kuka ta tashi ta nufa sama su mimi nan suka shiga ba mamii hakuri kafin suma suka nufa sama. Inaaya na kwance a bisa gado kuka take kaman ranta zaya fita tana shessheka duk sai jikinsu yayi sanyi suka zauna a kan gadon mimi ta dafata tace “sorry sis please don’t make us cry” sultaana tace “yess inee please stop it I’ll start crying now too” inteesar tace “inee please clean those tears sorry get up and wash your face and we will sort things out” hakanan inaaya ta daure ta tsaida kukan nata ta dago tana kallonsu da jajjayen idanu tace “sorry don’t be sad I’m ok you guys should carry on it’s getting late go and enjoy yourselves, i have to face my reality and fate the sooner I accept the fact that I’m not the same with you guys now the better it’ll be for me didn’t you hear what mamii said i can never step out without my husband’s permission so just go and enjoy yourselves” tagama tana kakalo murmushin da iyakanshi kan lebe ita kanta saida taji abun wani iri a bakinta wai husband, kallonta sukayi da ban tausayi inteesar tace “inee being married doesn’t mean you won’t enjoy or be happy mamii is just insisting on the permission thingy that’s all and I’m very sure ya aliyu will not refuse please just call and ask him here is his number” tana fada tana nemo numbern shi a wayanta ita kuwa inaaya wani Murmushi mai ciwo tayi tace “no intee forget it you guys should go kawai” sultaana tace “how can we go without you” mimi tace “exactly atleast try just call him” inaaya tace “please no! For my sake you guys should just go ahead” kawai inteesar tayi dialing numbern ya aliyu.
Kwance Aliyu yake kan kujeran dakin shi ya dan rufe idanu yana ta tunani kala kala na past da na wanda ke faruwa da yanda future zata kasance gashi jiya abbah ya kirashi yace he should start preparations zaayi hidiman bikin nashi nan da 3months amarya zata tare after that zasu tafi switzerland idan ta koma makaranta sai ta dawo nigeria kuma zaayi mata jera a nan nigeria a gidan aliyun dake nan wuye acacia estate so idan da abubuwan da zayayi wa gidan duk ya shirya kuma yayi lefe da komai da komai duk ya lissafo mishi sannan dora ya mishi nasiha akan kar ya wulakanta auren da suka yi mishi kar ya wulakanta masu diya dan yaga hakanan suka bashi aurenta, yana cikin tunanin nan wayanshi yayi ringing yayi tsaki ya duba yaga inteesar ke kira har ta kusa katsewa kaman bazaya dauka ba sai kuma ya dauka yace “hello” a dayan bangaren inteesar har ta fitar da ran zaya dauka sai taji ya dauka inaaya dai shiru take tana sauraro dayake a speaker inteesar tasaka, inteesar tace “hello ya aliyu ina wuni” yace “lafiya qlau, ya dai” inteesar tace “uhmm ya aliyu dama zamuje fun fair ne” sai yace “so? How is it related to me?” A hankali tace “can we go with inaaya” haushi ma maganan ta bashi hakanan yara su raina shi a kufule yace “how is that my problem is not like am holding her legs” inteesar tace “no! Dama mamii tace bazata je ba till she asks for your permission” yace mata “ohhh i see what did mamii said?” Inteesar tace “she should ask for your permission” sai yace “very good! And I’m sure you’re inteesar not her right” a hankali inteesar tace “yes” yace “great and mamii did not say inteesar should ask for permission for her she said she should ask permission her self” a hankali inteesar tace “yes but ya aliyu pleas..” bata karasa ba yace ” so let her do it not you” kashe wayan yayi bai jira me zata ce ba ita kuwa inaaya kuka ne yaci karfinta cikin kukan tana stammering tace “plea….se yo..u shoul…d go” kallon juna sukayi suka kalleta da tausayin kawar tasu sosai mimi tace “please inaaya just call him and ask yourself please please” ta tsaida kukan nata tace “no please I don’t want to go anymore please you guys should just go I just need some time alone now” haka sukayi ta insisting basusan time ya wuce ba har magrib yayi saida suka fasa zuwa dukkansu sai da sukayi sallahn magrib bayan sun sha lallashi sannan duk suka nufa gidajensu. Aliyu kuwa haushi maganar inteesar ta bashi wato ita ta raina shi da bazata kirashi ba saidai tasa inteesar ta kirashi wannan ai raini ma ne su abbah suka jawo mishi shiyasa ya ce ma inteesar ai ba ita akace ta tambaya ba ya kashe wayan yana jin haushi yayi wurgi da wayan kan gado.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]