[Advertisements⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 8 BY ZAINAB LAWAN BIRGET - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 8 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

 ta yi zaton zata ga wani babban mutum a matsayin ma’aikacin manaja amma ga mamakinta sai taga wani dan siririn saurayi mai ruwan Larabawa, idan har ba balarabe bane to kwara ne, domin kuwa farin shi ya so ya yi yawa, kyakkyawan gaskene mai doguwar fuska da dogon karan hanci, bakinsa dan karami, labbansa kuma ja zur kamar an zizara musu janbaki sai sheki suke yi, sumarsa akwance take har keyarsa, kwantacciyar girarshi mai yalwar gashi ta kusa
gadewa da juna. Ya bude baki tare da nuna mata kujera “Have a seat”.
Sai taga hakoranshi farare tas kamar bai taɓa tauna wani abu da su ba, hakan ya dada fito da kyansa sosai, tayi maza ta dauke idonta daga kanshi domin gudun karta kasa daukewa idan tadade tana kallonshi, irin bayin nan ne da ubangiji yake halitta wadanda kyansu yafi karfin misali.

Ta zauna ta gaishe shi tare da yi masa bayanin matsalarta duk a harshen turanci, tuni bayanan nata suka gamsar da shi ya gano matsalar tatta dan haka yace da ita “Mene ne sunanki da lambar Account dinki?”.
A razane tadago suka dubi juna dan kwata-kwata bata yi zaton yana jin Hausa ba, domin ko a fuska bai yi kama da Hausawa ba “Sa…Safina Yusuf” Ta fada muryarta tana rawa.
“Ah ashe sunan naki babbane? Domin kuwa sunan mahaifiyata ne”. Duk da Hausar tashi ba fita take yi sosai ba amma tana da dadin sauraro, bata samu abin cewa baya ci gaba .”Amma ni sunan Mahaifiyata Saffanatu, shin akwai wani bambanci da naki sunan?”. Safina bata sani ba ko akwai wani bambanci ko babu domin bata ma taba jin irin

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

sunan ba sai yau tace “Duk sunan iri daya ne”.
Nan da nan ya yi clearing din komai kuma bai bari ta zari ko sisi daga asusun nata baya bata kudade masu yawa a dirowarsa, shi ne ya taka mata har bakin bankin a zaton shi da mota ta zo, domin haduwar safina tafi karfin tana bin yawon motar haya, suna cikin harabar bankin yace da ita “Momi baki bani lambar wayarki ba, ko bakya son na rika kiranki muna gaisawa ina kwasar albarka? Kinsa manya sai da gaisuwa”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ciokin jin dadi tace “Mai zai hana tunda na samu da mai biyayya”. Suka yi dariya sannan suka yi musayar
lambar waya, ganin ta nufi get zata fita sai yace
“Oh Momi baki zo da mota bane?” Let me drop
you yaushe zan bari Momi na ta shiga rana ni ina
inuwa?”
Wata makekiyar jif ya dauko ya bude mata ta shiga tunda take bata taba shiga mota irin wannan ba, sai dai taga suna wucewa a manyan titian wani irin dadine ya lullubeta domin ta lura da take-taken sa wani abin mamaki daya dami kwanyarta shi ne “Shin wannan saurayin wanne irin nasibi gareshi haka da ya yi karatu cikin kankanun shekarun shi har ya taka wannan babban matsayin?”. Zuciyata ta yiwa wannan tambayar ba dan yau suka fara haduwa data yi masa wannan tambayar.
Take-taken shi ya nuna akwai alamar sonta a tare da shi, idan kuwa sonta yake yi da gaske idan har ta same shi to lailai ta zo duniya a sa’a domin ko a irin mafarkanta bata taba mafarkin zata samu kamar shi ba, tana ganin idan har yace yana sonta to ita fa ta samu mijin aure, duk burinta na auren kyakkyawan bata taba zaton zata auri balarabe ba, ya tattara duk wasu karko da take son mijinta da su har ma da,
Www.bankinhausanovels.com.ng
harma da wadanda bata taba hararowa ba, soyayya da Balarabe lallai haduwarta ta kai matuka.
Imadudden Garba dane ga Alhaji Gambo Mahmod tsohon ambasada Nageriya a kasar Syria, mahaifin nashi ya rike mukamai da dama a Nigeriya kafin ya zama ambasada, dan haka sunan shi ba ɓoyayye bane, yana da iyalai da dama matanshi hudu, uku bakakene harda uwargidansa ta ladan noma, bayan ya je Syria ne ya auri Balarabiya, ita ce ta Haifa masa Imadudeen da kannen shi biyu mata Rakiba da Hmrah duk a Syria suka girma danko bayan da Mahaifinsu ya dawo Nigariya mahaifiyarsu bata tawo da su ba sabida a lokacin suna yara ita kuma ba zata iya reno ba, a can duka suka yi karatun su suna jin yarukan Larabci, turanci, faransanci dama Hausa dan suna zuwa hutu Nageriya akai-akai yanzu duk sun dawo Nageriya gidan Babansu kusa da Mahaifiyarsu sai ‘yar autarsu kawai Himrah da har yanzu take Syrian saboda bata kammala karatunta na jami’a ba. Imadudden na da kwakwalwar lisafi sosai domin akan shi ya yi digiri na farko dama na biyu a can Syria, yana dawowa gida Nigariya mahaifinsa ya samar masa aiki a Banki tunda dama shi yake sha’awa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tunda Safina take haduwa da samari bata taba jin katarin haduwa da irin Imadudden ba saboda irin mahaukatan kyautukan bajintar da yake yi mata, tun bayan haduwarsu tsawonwatanni uku, domin kyautarsa ta biyu ma a gareta itace ta wata dankareriyar mota kirar zamani, itace taki amsa kyautar gudun abinda za a ce a gidansu, tana ganin kyautar ta yi mata girma, dan haka tace masa lokaci bai yi ba daya kamata ya yi mata kyautar mota, dan haka ya bari akwai lokaci da ko jirgin sama ya siyamata ma babu laifi.
Shi kuma mamakine ya kama shi, yana ganin akan me har za ayi mata kyautar mota taki karba wai dan gudun abinda gidansu za su ce, yana gani yanzu ai ita ba karamar yarinya bace, she is matured enough and suppose to have a freedom, ya kamata ace tana da ‘yancin yin abinda take so, ita kuwa kokarinta tayi ta nusar da shi cewar ita fa musulmace kuma Bahaushiya, bisa koyarwar Addini da Al’ada har yanzu a karkashin ikon iyayenta take.
Haka ya rika yi mata kyautuka na fitar hankali tamkar bai san ciwon kudi ba, hakan ne mana tunda bashi da matsalar su, ya gaje su
Www.bankinhausanovels.com.ng
gaba da baya da ma can danginsu masu kudi ne, sannan kuma shi mutum ne mai kyauta tamkar ruwan sama, muddin kuna tare da shi to komai zai iya yi maka, sannan kuma uwa-uba akwai wauta irin ta samari da sakarci irin na dan fari dake dawainiya da rayuwarshi. Duk da son kudi irin na Safina da zarmiyarta amma saida ya kure mata buri, wasu abubuwan da yake kawo mata ma bata taba ganinsu ba, a yanzu kuma ita sam ba wannan ne yafi damunta ba, burinta bai wuce na auren Imadudden ba, tana ganin idan tayi nasarar auren shi ta gama takar sa’a a rayuwarta, cikin lokaci kalilan suka yi sabo da shakuwa mai karfi a tsakaninsu, sai dai ma iya cewa Safina ce ta zarme akan shi domin shi ba ya zuwa gidansu, duk haduwar da za su yi sai dai ya kirata a waya su yi meeting point su hadu acan, ko kuma wani wajen shakatawa, idan tayi mai korafi kan zuwan shi gidan su sai yace ba zai iya gane wadannan lungunan nasu ba, kuma yana tsoron kada ya shiga motarsa ta makale, da yaketa zarme da yawa akan sa da yawa sam bata ji haushin ba sai tayi mai uzurin cewar bakone shi bai san gari sosai ba kuma dama can bama’abocin yawo bane.
Bugu da. kari kuma Imadudden sam bai iya soyayya ba, bai iya kalamai soyayyah masu
Www.bankinhausanovels.com.ng
dadi ba, shi dai barshi kawai yana da tsegumi da son lailai sai ya koyi Hausa sosai, a kullum bata da aiki sai koyar da shi Karin Magana da ma wasu zantukan azancin masu wuyar ganewa, duk hakan baya damunta a ganinta wannan ba matsala bace da zarar sun yi aure zata canja shi zuwa yanda take so musamman ma ganin yanda yake yi mata fiye ma da abubuwan da take so, ba ta da wani korafi akan shi, akan haka take lallabashi ta tattara duk burinta akan shi, shi ne saurayi na farko da yake samun kulawa fiye da kima daga wajenta, kafin ya kirata sau daya ita ta kira shi sau uku baya ga sakwannin da ba ta gajiya da aika masa. Haka ma takan shirya girke girke iri-iri na gargajita ta bishi da shi zuwa office.
Sam Safina bata daukar abinda take so da wasa, gaba daya ta bi ta yada labarinshi a gidansu da kuma tsakanin kawayenta duk wanda ya santa ya san labarinshi, hotunan shi duk sun gama watsuwa a gidansu ana ta zancen Safina zata auri Balarabe, cikin su babu wanda ya taba ganin shi a fili sai a hoto ko a waya dan takan hada shi da Inna ko Umma su gaisa yanzu kam burinta ya cika sabida zata auri mijin da za a yi ta labarinsa a gari.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Har zuwa yanzu babu abinda ya sauya alakarta da Alhaji Nura Maitama, shima bai san komai game da abinda take yi ba, Imadudden dai ba zuwa gidansu Safina yake ba balle har su hadu, kuma ko babu komai Alhaji Nura yafi karfin tayi masa kora da hali irin wacce tayi wa Kamal da Sulaiman saboda girman shi da kwarjininsa, Safina mace ce da bata manta alheri komai kankantarsa amman kuma bata iya maida alheri, har yanzu tana tuna hídimomin Sulaiman a gareta domin ta san komai ta zama a rayuwarta shi ne sila, amma hakan bai hanata watsa mai kasa a ido ba, haka Kamal ma ya yi mata dawainiya da ita duk da yana son aurenta amma daga karshe hakansa bai cimma ruwa ba,shima Alhaji Nura alherinsa yana da yawa a wajenta ya taimaka mata ta fanoni da dama amman hakan ba zai saka ta aure shi ba, matsalarshi guda daya yana da mata da ‘ya ‘ya, ita ba zata iya auren mai mata ba, tuni ta gama tsara yanda zata rabu dashi amma shi rabuwar lumana za su yi lokaci kawai take jira, ba zata iya yakice shi karfi da yaji ba, shi yasa take binshi a sannu tana ci gaba da morarsa, bata taba nuna masa akwai wani bayansa ba nuna masa take yi shi kadai ne gwaninta.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan Nafisa ta baro inda take tata
bautar(wato sakandiren ‘yan mata aka turata bayan Alhaji Nura ya yi kokarin dawo da su Kano) kai tsaye ta zarce gidansu Safina, Safinar ce ta kirata a waya tace idan ta taso ta biyo akwai labari, tana zuwa jikin Safina har rawa yaketa janyeta daki ta nuna maya wani agogon gwal cartier da wata akwati guda mai dauke da dogayen riguna da parkinstans, Imadudden ne ya kawo mata wai duk tsarabar kanwarshi Himrah ce ta dawo daga Syria shi ne ya kawo mata tsaraba.
Nafisa ta daddaga kayan ta yaba a takaice sannan cikin kyashi tace “Waike da gaske auren mutumin nan za ki yi?”.
“Aurenshi zan yi mana mene ne da shi?”
Nafisa tace “Kema dai kinsa Larabawan
nan sai a hankali al’adunsu sun sha bamban da
namu za kiyi ta ganin bakin al’adu a tare da su,
gaskiya akwai matsala”.
“Wacce irin matsala kuma? Nifa ko yaya yake zan iya zama da shi tunda ina son shi”. “Amma ya za ki yi da Alhaji Nura?” Nafisa
ta yiwa Safina tambayar.
Safina tace “Ai kin fi kowa sanin a tsarin mu babu auren mai mata, ba zan iya zama da kishiya ba”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kin san dai mutumin nan mai kudi ne,
karki je kiyi masa asara, ki kore shi kinsa yana da mamora”. Inji Nafisa Safina ta hararreta “To ce miki aka yi shi Imad din bashi da kudi? Ki share wannan
maganar Nafisa in har ba campaingn kike yiwa Alhaji Nura ba”.
“Babu wani campaign kawai mutumin ne mun moreshi da yawa”. Cikin rashin damuwa Safina tace “To mene ne a ciki? Ai namiji baa bin tausayi bane”. Don ta kawo karshen hirar sai tace Nafisa ta zabi abinda take so a cikin kayan, agogo kuwa ta boye shi sabida irin wadanan kyaututukan bata bari Inna ta gani, daga nan kuma suka tsayar da shawarar irin kayan da za su saka ranar Lahadi, a ranar su Imad za su yi party dan taya ‘yar uwarsu Himrah murna gama karatunta.
Gidansu Imad yana nan a sultan road tunda Safina take bata taba zuwa titin ba sai dai ta wuce, dan haka bata san haka gidajen layin suke ba, ganin gidansu Imad ya yi bala’in gigitata dan bata san yadda zata fasalta gidan ba, ko gidan kawarta Khadija Tahir da take ganin yafi duk gidajen data taba shiga kyau to gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, dan kuwa
Www.bankinhausanovels.com.ng
wannan ya taka shi ya dame shi a kyau, gidan tamkar dasashi aka yi yana da sassa daban daban da yake gidan dan siyasa ne kuma Babba harda wani matsakaicin hall dan taro a cikin gidan.
Koda Safina tayi ido hudu da ‘yan uwan Imad sai ta gane ashes shi ba komai bane a fagen kyau, sun nannade gashin kansu tamkar ganmo, haka nan taga Mahaifiyar tasu, dattijuwar balarabiya wadda babu abinda ya sauya na daga kyawun halittarta banda tsufa ya cimmata.
Shagali ya kayatar sosai musamman idan aka yi la’akari da kudaden da aka kashe, kayan ciye-ciye da makulashe sun wadata, ga irin shigar da mahalarta taron suka yi musamman ma su iyalin da suka shirya biki wani abin daya kara burgeta shi ne irin kyautukan da iyayen da sauran ‘yan uwan Himrah suka bata domin tayata murna.
Abu dayane bai yiwa Safina dadi ba wato irin gabatarwar da Imad ya yi mata a matsayin kawa kawai dan ita a zatonta duka ‘yan gidan su Imad sun san ta, kamar yadda duk wanda yasanta yasan da maganarsa, tana tsamanin suna ganinta za su gane ta sai taga sabanin haka, ranta ya sosu amma sai ta danne bata

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]