[Advertisements⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 3 BY ZAINAB LAWAN BIRGET - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 3 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Bayan kamar mintina biyar ya dawo hannunsa rike da wasu takardu daga hanyar labority ya fito koda ya zo daidai inda suke sai ya sake yi musu sallama, ganin Nafisa ta gama wayar da take yi sai ya matso kusa da fadin “Sannunku da hutawa”.
Safina na ta karatunta ko dago kanta bata yi ta kalle shi ba, ita kuwa Nafisa tayi caraf ta

amsa “Yauwa sannnun ka kaima” Tayi haka ne sabida yanda taga komai na jikinsa yana fadin naira,ga kuma motarsa data zama babbar shaida akan haka, yana sanye ne da wata tsadajijiyar shadda edcelsion gren da hular data amsa sunanta yana da kwarjini da kamala ga jindadin daya ɓoye ainihin shekarun shi, amma a kiyasce zai iya kawai shekarun talatin da takwas zuwa arba’in.
Daga irin kallon nazarin daya lura Nafisa tana yi masa sai yace “Suna na Alhaji Nura Maitama, na zo karbar sakamakon test da aka yiwa mahaifiña a jiya, ku dubiya kuka zo?”.
Har wannan lokacin kan Safina na kasa tana karatun hints dinta amma kunnuwanta duk suna sauraron abinda yake cewa.
Cikin jin dadi kulawarshi garesu sai Nafisa -ta amsa masa tambayar da ya yi musu “No mamanmuce bata da lafiya anyi admitting dinta anan female word”.


Cikin tausayi yace “Ayya, I’m sorry ko zan
iya zuwa in ganta?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mai zai hana?” Inji Nafisa ta yi masa jagora ya je ya gaida maman sannan suka dawo wajen, ya dubi Safina wacce da alama tana jin dadin karatun da take yi sannan ya maida
dubansa ga Nafisa yace “Ina fatan ‘yar uwar nan
taki bata da miji”. Nafisa ta tabe baki tace “Actually babu”.
“To akwai wani mai matsayin?” Ya sake tambaya.
Nafisa ta dan murmusa kafin tace “Babu ko daya, tana karatu ne”.
Ya yi dariyar jin dadi yace “Kenan zan iya samun lamabar wayarta?”. “Abu mai sauki kenan”. Inji Nafisa.
Nan da nan ta bashi lambar ya yi mata godiya tare da zaro rafar ‘yan dubu-dubu ya ajiye a gabansu tare da fadin “Ga wannan a sayawa mama lemo”. Nafisa kuwa tayi masa godiya, saboda dadin da taji har rakiya tayi masa zuwa motarsa sai daya shiga motar sannan ya tambayeta sunayensu da kuma kwatancen gidansu duka ta sanar da shi.
Nafisa na dawowa ta fizge mujallar hannun Safina “Yaushe kika zama bebiyar karfi da yaji ban sani ba? Kina jina da mutum amman kika yi shiru?”.
“To me zan ce muku? Na ga tunda ya zo nan yake faman bina da kallo”.
Nafisa tace “Ai ke dai ki godewa Allah tauraruwarki tana haskawa duk inda kika shiga sai kin sato zuciyar samari, yaudinma kada ki so kiga yanda wannan shima ya rikice akan ki, har na bashi lambar wayarki da kuma address din ki…”
Safina ta katseta “Haba Nafisa ya za ki yi min haka? Yanzu da kika jajibo min muturnin nan ya kuma zan yi da Kamal? Kinfa san auren shi zan yi?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisa taja wani dogon numfashi tare da kallon Safinar a kaskance ta yatsine fuska “To dan zaki aure shi sai me? Sai aka ce kuma ba za ki more rayuwarki ba? Ko shi Kamal din idan ya fita waje kin san abinda yake yi? Shi kenan sai ki hanawa kanki sakewa kamar aurenki yake yi?” Ta sassauta muryarta tace “Haba Safina ke fa mace ce allurer cikin ruwa ce mai rabo ka dauka, ki tsaya ki yagi rabonki Allah ne ya kawo miki shi har gida ai kowa da matsayinsa ke da ganin mutumin nan ai kin san yasha kwana a rayuwarsa”. Safina ta fara sassautowa “To amma ai ina samun duk abinda nake so a wajen Kamal komai nake so yana yi min”.
“Ai gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, shifa Kamal din dan maikudi ne, yanzu ga maikudin da kansa ya zo, shi kenan sai mu zauna muki yagar rabon mu?”.Safina tayi tsaki “Ke dai duk maganar ki bata wuce kudi kuma duk wanda kike samu ba sa isarki”.
Nafisa ta kalleta a kaskance “Ai dole nayi maganar kudi domin sune abokan rayuwa, kuma ma ko kogi baiki dadi ba tunda har yanzu mai kudi ma kara neman kudin yake yi, dan haka kada kiyiwa kanki ki kwantar da hankalin ki ki yagi rabonki kowanne ya kawo ki amshe, kila ma duk cikinsu babu mijinki”.
Cike da mamaki Safina tace “Kin manta Kamal ya kawo kudin aurena, saka ranar biki kawai ya rage a tsakanin mu”. Nafisa ta tabe baki.
“Ai kawo kudi ba aure bane, ya kamata ki nutsu dan gudun kada ki dawo kina nadama, yanzu ba lokacin aure bane, haka kawai kina kan ganiyarki tauraruwarki tana haskawa za ki daku she kanki da wani aure, kika san bayan Kamal da Alhaji Nura ko da wa Allah zai hadaki a gaba? Ya kamata ki yi karatun ta nutsu”.
Nan da nan kan Safina ya kwance tace “To ai ni ina tsoron haduwar Kamal da Alhaji Nura domin ba karamin kishi gare shi ba”.
Tayi tsaki da fadin “Aurenki yake yi da zai hanaki sakewa? Kuma ke bari za ki kowa ne yasan da zamar: daya, duk ina wayon naki da dabarar taki”. Ta soma jan wani tsaki sannan ta ci gaba da cewar “Idan ni ceke ga mai kudi da kanshi me zan yi da wani dan mai kudi?”.
Da ace Safina mai tunanice ya isa ace ta hankalta da Nafisa da kuma hudubobinta domin duk wanda yace zai baka riga ka kalli ta jikinsa duk tarin samarin Safina babu wani kwakwara guda daya duk abokan shiriritane, amman saboda son zuciya da son abin duniya sai Safina ta kasa fahimtar hakan, haka ta dubi Nafisa tace “Ai shima Kamal mahaifinsa mai kudi ne kuma gashi shi ne babban namiji…”.
Nafisa ta katse ta “Tafi can kina nufin Kamal bai taba baki tarihinsa ba ai ba dan Alhaji Lamido bane”. Mamaki ya bayyana karara akan fuskar Safina tace “Ba dansa bane, to dan wane?”.
Nafisa ta yi dariyar keta tace “Ashe ke Www.bankinhausanovels.com.ng
zaman ‘yar burum-burm kuke yi da Kamal din naki?”.
Safina tace “Ni ba wannan na ambaye kiba”.
“Na samu labarin gidan ne tsaf a wajen Aunty mu, kinsan kawar mamansu ce, babu abinda bata sani ba game da su asali mutanen ajingi ne, mahaifin Kamal yayan Alhaji Lamido ne tin yana karami mahaifinsa ya rasu, daga nan ne ya dawo hannun Alhaji da yake Alhaji yana da mata ta kwarai sai ta hada shi a cikin ‘ya ‘yanta ta runguma, idan ba fada maka aka yi ba bazaka fahimci basu ne suka haife shi ba, Mahaifiyar Kamal tana can tana auren wani a can ajingin kuma har tana da wasu ‘ya ‘yan, dan haka gwara tun wuri kiyiwa kanki kiyamullali domin Kamal bashi da gadon komai a gidan sai dan abinda aka sam masa”.
Ta danyi shiru ko Safina zata ce wani abu amma sai ‘tayi shiru, hakan ne ya bata tabbacin ta samu nasarar shawo kan kawarta dan haka sai ta dora daga wajen data tsaya, lokaci mai tsawo ta dauka tana nemarwa Alhaji Nura Maitama dama a wajen kawarta.
Rashin zurfin tunani shi ne babbar matsalar Safina, nan da nan hudubobin Nafisa suka shiga kanta har ta nemi kaunar da take yiwa Kamal ta rasa domin daman can badan Allah aka ginata ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WACE CE NAFISA?

Nafisa ta taso ne a gidan da sukari da rashin tarbiyya suka yi katutu, gidan da ake zama irin na ‘yan marina kowa da inda yasa gaba.Ubansu rikakken dan boko ne, dan boko zallah yake gudanar da rayuwarsa, babu ruwan shi da batun tarbiyyar ‘ya ‘yansa yana ganin tunda yanzu a karni na ashrin da daya muke karnin takurawa yara ya wuce, lokaci ne da za a baiwa kowa damar ya gudanar da rayuwarsa yanda yake so, babu ruwanshi da irin rayuwar da yaro yake tunda shi dai ya ajiye komai na bukata a gidansa shi kenan ya gama a ganinsa, shi dai babban burinsa ‘ya ‘yansa su maida hankalin suyi boko.
Mahaifiyarta kuwa irin matan nan ne masu yiwa aure rikon sakainar kasha ita bata da kyautata zaman auren nata ba sannan kuma bata barshi ya yi wani auren ba, yana da akidar auren mace fiye da daya, sannan kuma itama babu bata barshi haka ba sai yadda ta yi da shi, kasuwancin kayan mata take yi, kama daga sutura kayan kwalliya da kuma sarkokin daham, Www.bankinhausanovels.com.ng kasashen daban-daban take zuwa domin siyo kayayyaki sannan kuma koda tana gida ba mazauniya bace, kullum a tafiye-tafiye take daga bukukuwa sai tarukan kungiyoyin nasu na ‘yan kasuwa mata, bata san a wane hali ya ‘yanta suke ciki ba, tsakaninta dasu sai da waya.
Wani abin mamaki ga wadannan iyayen shi ne yanda hankalinsu yake a kwance ganin sun bar ‘ya ‘yan nasu a hannun ‘yan aiki, zato suke yan aikin za su yi musu tarbiyyar da suka kasa, cikin yaran duk wanda kagani da tarbiyya to duniya ceta masa amma ba iyayene suka suka yi masa ba, wannan ce damar da Nafisa da ire-irenta suka samu a gidan suke abinda suka ga dama babu mai kwabarsu.
Akwai hatsari mai girma gaske a duk lokacin da wani uba ko uwa ke kallon dansu ko yarsu a matsayin wacce tasan abinda ya dace har suka barta tana gudanar da rayuwarta ba tare da sanya idanunsu ba.

**

Tun daga wannan huduba ta Nafisa Safina ta saki jiki da Alhaji Nura Maitama ta dauki shawarar ta biye masa ta yagi rabonta amma ba auren shi zata yi ba duk da tarin dukiyiar daya mallaka saboda yana da iyali, matarsa daya da ‘ya ‘ya uku, ita kuma a tsarinta babu auren mai mata, saurayi take so wanda za su shimfida rayuwar aurensu tun daga tushe, ba ruyuwar da wata ta riga ta kafa wa ba, tsananin kihin da take da shi ne ya hana kudinshi ya rufe mata idanu, Alhaji Nura babban kusa ne a gwamnati, haka kuma dan kasuwa ne da yake fita kasashen duniya, zuwa yanzu daga shi har Kamal babu wanda take jin zata iya aure, saboda a yanzu bata fidda ran auren Gwamna ko minister ko wani basarake ba shi yasa take bin Alhaji Nura sannu domin tafi cin moriyarsa.
Ta fahimci shi din da gaske yake domin tun haduwar su ta biyu ya fara bijiro mata da maganar aure tunda shi ba yaro bane, bai ga dalilin da zai tsaya yin wata soyayya ba, Safina ‘yar duniya ce nan da nan ta kalallame shi cikin kissa da hikima ta nuna masa ai laifin ba nata bane, matsalar baban su ne sai sun kamala karatun jami’a sai ya yi musu aure, harma da ce masa ya bari zata yi kokarin shawo kan mahaifinsu, da haka da sauran Www.bankinhausanovels.com.ng dadadan kalamai ta yaudare shi har ya danka mata dukkan yarda da amanarsa, burinish bai wuce na mallakar Safina ba, idan har ya sameta ya san ya gama sa’ar aure, dan haka ta same shi yanda take so.
Wani lokacin idan taga yanda yake yi mata barin kudi sai taji kamar ta aure shi amman idan ta tuna yana da mata sai ta fasa, domin bata dauki lamarin kishin wasa ba, sannan kuma tana hangen zata iya samun wanda ya fishi a gaba.
Yau ma da yamma tana zaune tana
gyaran faratanta Alhaji Nura ya kirata da ganin
kiran nashi tayi murmushi ta daga kiran tare da kara wayar a kunne tana Magana cikin yauki, yanga harma da tsokana “Alhajin Allah barkanka da yamma, ko dai ba shi bane?”.
Daga daya bangaren yace “A zatonki wane ne? ko dai an yi min kishiya ne?” Dariya ta yi ta rike baki tamkar yana ganinta tace “Wane ni da wannan danyen aikin? Ai duk ka mamaye zuciyar babu ta inda wani zai samu shiga”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayi dariyar nishadi “Dadin dake akwai dadin baki”. “Baka yarda ba kenan?” Ta tambaya.
“Ni na isa nace ban yarda ba?kin san
nima tawa zuciyar tana gareki sai yanda kika yi
da ita, dan haka nake son ki nadani sarautar
zuciyarki na zama sarki mai jan ragamarta ba waziri ba”.
Tayi wata dariyar mamaki da kissa “Au a cikin zuciyar harda wani sarki da waziri”. Alhaji Nura ya amshe da sauri “Eh mana a cikin zuciyar ko wace mace akwai sarki da waziri, cikin samarinta wanda tafi so shi ne sarki me biye masa kuma waziri”.
Dariya ta yi tace “Ba kowacce macen ba, domin ni sarkin kawai nake da shi bani da waziri kuma kai ne sarkin”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]