[Advertisements⬇️]

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 18 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 18 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

………….Har suka iso gida Taufiq be bar zolayar Shuriem ba, Shi kuwa gogan yazo wuya saura k’iris ya fashe Koda suka Shigo gida da Momy suka Fara cin karo Afalo tambayar su tashiga Me yasamu d’anta taganshi Yana cika yana batsewa.

Saida Taufiq yay Dariya Me isarshi San nan ya bawa Momy labarin Abinda ya faru Momy ma dariyace ta kufce Mata Tace” to Kai son meye natada hankali ga Heedaya ga Badd’o Kaga wata ta tafi kamaye gurbinta da wata Meye na b’acin Rai kamar baka Saba Zama da Mata 2 ba.

Gogan kuwa saura k’iris ya fashe d’akin Momy kawai yawuce yabarsu A tsaye, Ina zaune gefen gadonta Ina Shan fruit naji Anturo k’ofa yayanmu nagani ya wani Murtuke da Alamu ransa Ab’ace yake, San nu da zuwa nai Masa Amma ko kallona beyiba direct toilet Naga ya wuce Bayan ya fito Naga ya haye Kan gadon Momy yaja bargo Ni kuwa Ak’ule nace” Yaya fa kwanciya nakeso nayi Inna Gama d’ago kansa Yayi yace” Nan d’akin kine ki koma d’akin Mana ki kwanta wani ya hanaki, bana San yawan surutu yanzu kubarni naji da Abinda ke damuna.

Nima Ak’ufule nace’  wallahi Yaya seka tashi wannan Ayfin karfine wlh da Rana tsaka k’aton ka dakai kazo ka hayemin gado, Murmushi Yayi daga cikin bargon San nan yace” ki fadi duk Abinda ke Ranki Amma wallahi karki Bari na irga 5 Baki bar d’akin Nan ba, 1 2 3 4, Ai da sauri kamar Me tata nabar d’akin Saboda Nasan inya tashi zan gayawa Aya zak’intane.

Bayan su Anty Saudat sun huta Suka tafi gurin ABBA tareda Momy, Akwance suka sameshi jikinnan ba inda yake Motsi, Momy ce tazauna kusa da shi tareda Yi Masa sannu San nan Anty Saudat ta Zauna itama ta gaishe shi tareda da tambayarsa yanda yakejin jikinnasa, San nan ta Fara magana kamar haka Abban Yara yau munje katsina D’azu Malam da inna sunce suna gaishe ka.

Kuma Akan ciwanka mukaje ya bada rubutu yace” yazama ruwan shanka yace” sihiri Akai maka kuma dayar dar Allah zaka samu lafiya kadawo yadda kake da, Amma mu iya lanka muna naiman wata Alfarma Agurinka munaso in Rahanatu tazo d’akinnan ka nuna Mata Bakaji baka magana Sai dai gani kawai idan kayi haka zaka fahimci komai da kanka.

Godiya Abba yay musu sannan yace” ze jarraba Allah kuma yasa mudace Allah kuma yabashi lafiya, haka suka barshi cikin tunani to me suke nufi da hakan Amma yasan Acikinsu bawadda zata cutar da shi zeyi Abinda sukace Dan sanin Abinda ya shige masa duhu.

Yau yakasance girkin ummy ne tun safe Bata ko lek’o Shiba Sai Momy ce keta d’awai niya dashi Sai dare wajen k’arfe goma ta Shiga d’akin Tai sallama taji be Amsaba maganar Duniya Taga be ko kalleta ba wata irin shewa tayi Tace” Kai Sai Ni muguwa Rahanatu burina ya kusa cika zan shek’a ka lahira na shek’a d’anka na kwashe dukiyarka nayi gaba na tarwatsa iyalanka su koma b’ara Atiti, kuma kasan wani Abu Nina turo Meerah ta Auri d’anka Shuriem Dan inta samu ciki muka sheshi kaga tunda Yana d’a gado yazama namu Amma kuma Maki rar matarka ta wargaza min shirina ta hanyar Aurasa Mata yar’ta Meerah tasamu ciki muna Murna Aka had’a Baki da Shegiyar yar’ Nan tazubar da cikin daganan Likitoci suka ce Maihaifarta tasamu matsala.

Kasan wadda ta bada Shawarar Aiwa Heedaya dashe nice domin ta hakanne zamu samu d’a daga Shuriem. 

Yanzu Heedaya ta kusa haihuwa kajira kagani Agaban idanka zan kashe Shuriem kuma zan kasheka kuma mukarb’e d’a mukarb’e dukiya bakada yadda zakayi domin ka na kasa.

Juyawa tayi tabar d’akin domin Yanzu baida wani Amfani Agurinta hawayene ya silalowa Abba Momy ce taga ficewar ummy Dan tana lab’e tasan dama bazata iya kwana da Abba ba.

D’akin ta Shiga ta ga Abba na zubar da hawaye da sauri ta k’arasa gunsa tana tambayarsa lafiya.

Duk Abinda yaji ummy na fad’a Sai da ya kwashe tas ya gayawa Momy San nan ya d’ora da cewa dama kinsan da wannan maganar bawanda yagaya min Shiru tayi hawaye Nabin kuncinta Tace” kayi hak’uri Abban Yara insha Allahu zaka samu lafiya kabari kawarke tukunna Allah bazai Basu Nasara ba.

Abba nata samun sauk’i Dan Momy tana kula wajan bashi maganinsa, ummy Kam ko lek’oshi Bata yi, yau yatshi jikinnasa da sauki domin Yana iya zama, kuma Malam ALU yace” duk Randa Abba ya Fara Zama Kar su Bari ya k’ara kwana Agidan sukaishi katsina.

Haka Momy ta shirya Abba Bayan tagama Shuriem da Taufiq suka d’auke shi suka fita  dashi Dan kaishi mota, ummy ta hangonsu ta fito da sauri tana cewa Ina zaku kaishi haka Taufiq ne yay Saurin cewa” Egypt muke so mufita dashi Akwai wani Asibiti Acan Me suna Alwadi Hospital suna da k’wararrun Likitoci Acan Shine muke so muje can ko Allah zesa A  dace tanajin haka tace” to Allah ya sawwak’e ko k’arasowa bataiba ta koma Dan ita A tuna ninta jikina sane ya k’ara rincab’ewa, Shuriem kuwa jiya keyi kamar ya Shak’eta Dan Momy ma ta Hana shi Tanka Mata tace” kome zata Yi batayi Bata yadda yay Mata ko kallon banza ba har Sai Asirinsu ya Gama to nuwa sun Karb’i saka mako, Amota suka sahi suka d’au hanyar katsina.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Iya Sai ba’a Gaya Mata komaiba tasan Sai Abba ba lafiya Amma Bata San sanadin ciwansa ba sun San inta Dani birkice musu zatayi bazata Bari subi Abin Ahankaliba.

Suna tafiya befi da Awa 1 ba nafara Jin ciwo  gadan gadan dama tun jiya banajin dad’i Momyce ta d’aukeni Mukayi Asibiti Dan bataso Ummy tasan halin da muke ciki cikin Abinda befi Rabin Awa ba na santalo yarana guda 2 duka maza farare tas Masu Kama Dani kamar An tsaga Kara……

…………Su Shuriem sun Isa katsina lafiya, Bayan sun Isa gidan Malam ALU Ak’ofar gida suka sameshi Kan dadduma Yana Jan carbi  Yana ganin Motarsu ya mik’e yace” Allah sarkin baiwa Ashe isma’ila kana da raban Shan ruwa Aduniya Bayan sunyi parking Malam ALU mik’e tare sa takalminsa yak’arasa  gurinsu.

Fitowa sukayi San nan ya lek’a yaga Abba Azaune Abayan mota su Shuriem ya kalla yace” su kamoshi San nan yayi hanyar Shiga cikin gida Koda iya ta gansu da sauri taje ta bud’e musu d’akin da suka Zauna ran nan.

Shiga sukayi da Abba suka zaunar da shi Abinci da ruwansha Aka kawo musu Nan suka ci suka k’oshi, Abba ma yaci Abincin da d’an dama Bayan sun Gama iya turo Badd’o tazo ta kwashe kwanu Kan, Ai Taufiq na ganinta ya zunguri Mutumin Shi kuwa kamar An Aiko Masa da sak’on mutuwa haka yayi, Taufiq kuwa mezeyi inba Dariya ba Malam ne yay Mai dak’uwa Dan yagane Me yake nufi, sannan yace” kabar Yi Masa dariya kaima zan samo wata fillon na aura maka.

Ai Nan da nan ya had’iye dariyarsa Shuriem kuwa yayi zaraf yace” Ai kuwa Malam hakan yayi kaga se Ahad’a Ayi Rana d’aya, Taufiq dai Shima yau ya shak’a Abba dai murmushi kawai yake.

Haka suka cigaba da Hira cikin bar kwanci, da k’aunar juna.

Washe gari Abun Mamaki Abba ya taka da k’afarsa Amma dai tafiyar yanayi Yana dafa Shuriem ko Taufiq, Murna gurinsu ba’a cewa komai Koda Momy takira Anty Saudat tagaya Mata haihuwa cewa tayi karta gayawa Shuriem Dan Shuriem cewa zeyi ze biyota Dan dama ita rakiya tayi musu kuma tunda tayi kwana 1 to komawa zatayi.

ABBA tasamu A keb’ance tagaya Masa yayi matuk’ar Murna sosai, San nan Akagayawa Malam Ai suna ciki hirar saiga Taufiq da Shuriem sun Shigo d’akin Aikuwa A kunyace ya kalli Abba yace” Ni zanbi Anty daga Baya na dawo kwana d’aya kawai zanyi.

Malam yace” yaran zamani ba kunya Mu Ada Ina zamuyi irin wan nan, Amma badamuwa Sai in biku muje ma dawo tare, haka kuwa Akayi, duk kansu suka tafi Taufiq kawai suka Bari gurin Abba.

Nikuwa tunda na haihu ban samu kaina ba Sai Bayan magariba saboda nayi zubar jini sosai, Sai da Aka k’ara mini jini Leda 2 Nan Momy ta Kira Mamanta da yan’ uwanta nanfa Asibiti yacika Yara Kam tubar kallah Sai hotuna Ake musu haka kawai naji zuciyata na Rayamin dama Yaya Yana Nan gaskiya nayi Missing d’insa yanzu Inna kirashi kamar na zubda Ajina ne.

Haka ma washegari da wuri Muka dawo gida Bayan mun dawo Nan fa gida ya cika da yan’ barka Ni kuwa Ina d’aki iya taimin wankan Runhu na kwanta Sai bacci nake tayi.

Momy dakanta taje har part d’in Ummy tagaya Mata haihuwar Nan fa  ta Shiga Murna itama Momy na fita ta dokawa Maman Meerah waya Tace” Ay tayi sauri ta zo Abun nema ya samu matar falke ta haifi jaki, Nanda Nan kuwa suka garzayo suna isowa Motar Su Shuriem Na isowa, Shuriem ne ya bud’e k’ofa ze fita Dan ya gane Motar gidansu Meerah, Malam ne yay Saurin rik’e shi yace” kayi hak’uri karinga sarrafa fushinka duk sanda kasami kanka cikin wani yanayi Mara dad’i.

Hak’ura yayi yatuk’a Motar suka Shiga ciki Bayan sunyi parking Suma su Meerah suka faka, Bayan sun fito Anty Saudat ta tare su kamar Abin kirki suka Shiga ciki Momy ma tayi mamakin ganinsu dayake gidan cike yake da mutane yan’ barka Sai Bata nuna ba, Shi kuwa Shuriem ko Arzik’in gaisuwa Maman Meerah Bata samu daga gareshiba.

Bayan An zazzauna Anty Saudat da kanta ta fito musu da jari Rai samb’ala samb’ala kyawawa dasu gasu lafiya yay yu Ai Maman Meerah Bata Bari An mik’o Mata ba ta Mik’e ta Kama rawa tareda godiya ga Allah shi dai Malam da yaga sabgar Matace Nan yace” Shuriem ya nuna Masa d’akin Abba Anan yakeso yazauna Akwai Abubuwan da zaiyi Ad’akin da sauri yaje ya nuna masa yadawo, Ai kuwa Yana dawowa Meerah ta kalleshi tace”Shuriem nazo karb’ar ya’ya’ na Danni yadda nakejinsu Ayanzu bazan iya bawa Heedayah ko d’aya Acikiba, Ni zanje Nasan yadda zanyi na shayar dasu, kallon Baki da Hankali yay Mata yace” Anty Saudat  Karb’i yarannan tunkan in sassa b’a musu kamanni ita da uwarta Nan fa wuri ya ka ceme Ana haka saiga Ummy da Hajiya Amina.

Ashe Haj. Lailace Tai musu text nanfa suka shigar wa su Meerah nanfa wuri yaka came kafin kace Meye wannan Mata sunyi Musu dukan tsiya nanfa Malam yajiyo hayaniya yafito  koda yagansu jina jina kuma Ana cigaba da jibgarsu tsawa ya daka musu yace” Matan su daina dukansu.

Shuriem yacewa ya Kira yan’ sanda San nan yace” Akira Taufiq suzo shida Abba Koda Aka Akira Taufiq cewa yay gasunan insha Allah yanzu kuwa zasu taho, San nan yakira yan’ sanda jimawa kad’an Sai gasu.

Nanfa sukace Arufe k’ofa kowacce ta kirwo mijinta dukkansu kuma Sai hankali yatashi da suka ga bayadda zasuyi haka kowacce ta Kira nata Mijin yan’uwan Momy dai Anan Aka sallamesu tareda jawa mazajensu kunne.

Yarage daga Haj. Laila Sai Meerah da Ummy da Haj. Amina Bayan wasu Awanni saiga Abba ya shigo tareda babansu Merrah domin tun Ahanya yakirashi yace” su had’u Agidansa dama kuma Matarsa ta kirashi tace’ tanacen, Bayan sun Shigo ummy naganinsa Yana tafiya tamkar be tab’a ciwo ba nanfa  tafirgice ta Shiga tashin hankali, can saiga yaro yayi sallama waiga Mijin Haj. Amina yazo Abbane yacewa D’an sanda d’aya yaje ya shigo dashi jimawa kad’an segasu sun Shigo Nan fa Haj Amina ta Shiga zazzare Ida nuwa…….⁸⁰

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]