[Advertisements⬇️]

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 14 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Www.bankinhausanovels.com.ng 

           D’aukan papern Yaya Shuriem Yayi ya kekke Tata, Ni kuma ina ganin haka nace ” wlh Shuriem ko kak’i, ko ka so saika sakeni dama Ni Alfarmar Abba kaci, na Aureka.

Ni dama Hamza ne zab’ina ba kaiba, Dan haka kawai karubuta min takar…. Aibe barni na k’ara saba ya kaimin wani naushi Afuska Saida bakina ya fashe, shi kuma yaja Baya Yana huci kamar wani matashin Zaki, kuka nasaka inayi Ina k’wallawa.

Saiga Anti Meerah ta shigo da gudu tana tambayar Abinda ya faru, kanta ya koma ya fara zazzaga Mata masifa kamar haka” Ai duk kece muna fukar da kika gayawa Taufiq Abunda muka shirya gashi Nan kinja Aurena ze mutu Abanza”.

Bak’in cikine ya mamaye Meerah tasoma magana cikin b’acin Rai “Toni Dan Auranka ya mutu Sai me ba gwara ma ya mutuba, kowa ya huta da wan Nan gan ta lalliyar yarinyar”, Ai Shuriem ya Kai wuya duka ya rufe Meerah dashi kamar An Aiko shi.

Ni kuwa kayana na cigaba da had’awa dan naga  Ahalin danaga Yaya ba k’alau yake ba.

Shuriem kuwa Saida Taufiq ya dawo Baibar jibgar Meerah ba da k’yar  Taufiq yasamu nasarar k’wace Meerah Han nun Shuriem, bayan ta yay Mata jina jina ya turashi A d’aki yasawa d’akin key Meerah kuwa tana gani ta kub’uta, Jan jiki tayi da sauri ta shiga d’aki ta D’auko wayarta ta Kira Mamanta tana kuka, hankalin Hajiya Laila yatashi sosai.

Tambayarta tashiga Yi me yake faruwa cikin kuka ta Fara magana” Mama Shuriem kasheni zaiyi Dan Allah kigayawa Daddy ya turomin kud’i na dawo gida.

Ke!!!!! Banasan Sha shanci Wana irin kisa Ana zaune k’alau kiyimin bayani dalla dalla yanda zan fahimta”.

 Cikin shash shek’a da gala baita Merah ta Fara magana”  Mamah  Anyi Aikin nan to shine bayan Anyi Aiki ko cewa tayi Bata yarda ba, ban saniba.

Shine Naji yanata dukanta tana ihu tana cewa ya saketa shine na Kai Mata d’auki shine yaymin dukan mutuwa”.

Wani dogon tsaki Haj. Laila taja San nan tace” maganinki to Ina ruwanki mudai tunda Anyi Aiki buk’atarmu tabiya.

Kedai kiyi k’kari kizauna da shi lafiya har Ahaife Miki d’anki, ki dena Shiga sabgarsu.

Amma wani hanzari ba guduba boka yace” Aikin da Yay mana yanada shard’i, yace karmu sake ya kunsaceta idan kuma haka ta faru to Aikin da Mukayi na  Mallaka zai war ware.

Shiyasa tun kina Nan Nijeria nace kiyi duk yanda zakiyi ki hanata kwana Ad’akinsa”.

Ai Mama shi Bata gabansa ma be ma Damu da itaba, Sai Abinda nakeso shiyakeyi, 

Murmushin Jin dad’i Maman Meerah tasaki San nan tace” harkinsa Hankalina ya kwanta to yanzu ki bud’e kunnen ki kijini da kyau kiji Mezan Gaya Miki.

Ba ruwanki Dasu kome ma zasuyi suje can su k’arata, kiyi hak’uri data haihu Zamu karb’e D’an kinji.

Nagode Mama Sai munyi waya katse Kiran tayi, San nan Meerah ta tashi ta Yi toilet don ta gasa jikinta.

Ni kuwa bayan nagama had’a kayana,

 Mukayi waje nida Yaya Taufiq, bamu tsaya ko Ina ba Sai filing jirgi, fita Mukayi daga taxi muka Shiga ciki, wayar Yaya Taufiq ce ta d’auki tsuwwa d’auka Yayi ya Duba Sai Yaga Shuriem ne karawa Yayi Akunne.

Yace” Hello bro ykk cikin Masifa ya Fara Magana Taufiq Ina Heedaya”  murmushin mugunta Yayi yace” gata Akusa Dani Nanda mintuna goma ma mun hau jirgi, harzu k’a Shuriem Ya kumayi, San nan yace” karka yadda kabar k’asan Nan tare da Mata ta.

In har kuma ka Aykata haka zan manta da cewa Kai D’an uwana ne zan d’auki hukunci mai tsauri Akanka domin kana Shiga gonata kana tsallake iya karka”   Dariyar mugunta Taufiq ya kamayi  San nan  lokaci d’aya ya Sha Mur cikin tsawa yacewa Shuriem Ina Mai jiraaaaa!!!!!!!!!……..

Yana katse wayar Na dubeshi nace” Dan Allah Yaya Taufiq karka maidani  gurinsa, saboda nasan shiya kiraka yanzu.

Murmushi yayimin tare da cewa”ki kwantar da hankalinki bazan maida keba Nasan yanzu haka ze biyo bayanmu kuma insha Allahu bazai same muba.

Mun d’an jima kad’an Aka kiramu domin Shiga jirgi, muyi sauri Yaya Taufiq Yace haka muka Shiga jirgi Ina Addu’ar Allah yasauke mu gida lafiya.

Bayan munshiga mun Zauna ne cikin jirgi  zuciyatafal farin ciki zan koma gida wani b’an gar’an kuwa cike take da duhu saboda Abinda ya faru dani.

Yaya taufiq ya katse min tunanin da nakeyi yace”  Heedaya Abinda nakeso dake shine Shuriem Mijin kine kuma bayan Aure ma Akwai yan’ uwan taka Atsakani banaso kiyi hirar Nan da kowa A halin yanzu duk sun San Abinda ya faru.

Kina da Hankali nasani inaso Kar Aji wan Nan zan can daga wurinki indai ba k’urewa tayiba kuma bance ki d’agawa Shuriem k’afaba  ta hakanne ze San kina da k’ima da mutum ci Agurinsa San nan kibi Abin A hankali bance ki k’etara maganarsu ABBA ba.

 

Toh Yayah insha Allahu bazan baka kunya ba kuma zanyi hak’uri najira Naga Abinda magaba tanmu za suyi.

Daga haka kowa shiru Yayi Yana tunani cikin ransa.

Bayan mun iso Nigeria ABBA ne yazo d’aukan mu Ina ganinsa na Fara kuka, Rarrashina ya kamayi yace min nayi shiru, muje gida, Shima Abba mama ki Yayi yadda yaga fuskata ta suntuma wato shi gashi tsohon D’an danbe in tsohon tsiminsa yatashi bawanda ya Isa ya tsaida shi.

Girgiza kansa Yayi yace” zezo yagamu Dani, bayan mun Isa gida iya muka ci karo da ita A bakin get Momy nata fama da ita ta dawo ciki ta jira.

Ita kuwa ta kafe  bazata koma ciki ba Sai da  Heedaya, muna tsayaww ko Gama parking ABBA beyiba Sai ga iya da saurinta har tana tun tub’e Nima da sauri na bud’e motar na fito muka rungume juna.

Kuka take Nima Ina kuka wai gawa iya tayi ta kalli Momy Tace” kisa Akwasomin kayana Amaidamin b’an garanki can zan koma d’akin dake kusa da naki.

ABBA ne yace” to kuyi hak’uri kukan ya Isa haka mu Shiga ciki su huta, dukkanmu shigewa ciki Mukayi Momy Kam zuciyarta ba dad’i duk da Anty Saudat Tai Mata bayanin komai Amma tace” karta Bari kowa yaji Akwai lokacin daza su fad’i Ainihin Abinda ya faru Amma bayanzu ba.

Bayan mun Shiga ciki d’akinmu na wuce nida iya nai wanka Naci Abinci na kwanta Sai barci.

ABBA ne zaune shida Momy Yana jin jina Rashin hankalin Shuriem Momy ce ta nisa Tace” Alh. Kamata Yayi kairawo yaran Nan kace ya baro garin Nan zamansa A can d’in bashida wani Amfani.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Waya ABBA ya d’auka ya Kira Shuriem Ai Yana d’agawa ABBA ya Shiga surfa Masa masifa” Sannnu Shuriem na gode da Abinda kayi kuma  sa k’onka ya sameni kace zaka d’auki mataki Akan Taufiq.

To Allah ya baka sa’a San nan bayan Aika Aikar da kayi  harda duka ka had’a Mata wato Kai gaka shago in tsumi ya tashi ba Wanda ya Isa yada katar dakai.

To ka bud’e kunnenka kanlji da kyau in har nine nahaifeka kuma na Isa dakai to gobe duk Abinda kake kabari kazo garin Nan kuma inaso inzaka zo kataho min da takar dar sakina Heedaya.

Shuriem najin haka gabansa Yay wata irin fad’uwa tare da goge wata zufa data keto Masa lokaci guda, rissinawa Yayi kamar Agaban yake yace”  Ayi hak’uri ABBA marasa lafiyan da muka zo Dasu Basu Gama warkewa ba, Ai ABBA be Bari ya k’arasa ba yace” su marasa lafiyar k’annen ubanka ne Ina ya’n uwansu suke.

To kasani indai baka dawo gobeba kacanza wani uban badai Niba k’it ABBA ya kashe wayarsa, Momy ce ta kalleshi cikin sanyin murya Tace” Anya kuwa Alhaji wan Nan Hukuncin beyi tsauri ba…

Hannu ya d’aga Mata kawai taja Bakinta ta tsuke Dan tasan ransa bak’aramin b’aci Yayi ba.

Shi kuwa Shuriem hankalinsa ne ya tashi, mik”ewa Yayi daga zau nen da yake Kaya yashiga had’awa Meerah ce tashigo tasa meshi Tace Mai Dear lafiya banza Yay Mata da yaga zata isheshi cewa yay Mata ta had’a kayanta gobe zasu wuce.

Haka takama had’a kayanta badan ranta yasoba Dan yanzu Shuriem ya zame Mata wani dodo Koda ta tambayeshi Ina su Taufiq cewa Yayi be saniba.

Yanzu lallab’ashi take burinta kawai Heedaya ta haihu takarb’e D’an ta.

Washe gari natashin Raina fes ciwan ma Yad’anyi sauk’i da Anty Saudat ta gayawa Momy ta kula Dani, ruwan zafi Kam Ina shigarshi sosai harda wasu jik’e jik’e ta kemin.

Misalin k’arfe 5:00pm na na yamma Muna zaune Afalo na d’ora kaina Kan cinyar Sadiya tanaimin streching.

Ji Mukayi kawai An shigo falo dukkanmu Mikewa Mukayi Ni kuwa nakama raraumar D’an kwalina in sab’ashi Aka……

           Yaya muka gani kamar saukar Aradu Koh takalminsa be cire ba dashi yashigo Mana falon fuskar Nan tashi tamau ba Alamun Annuri, kallan Sadiya Yayi yace” ke! Bar Nan Ai Sadiya jiki na kyarma kamar ta saki fitsari tayi hanyar waje.

Nima binta nayi da niyyar fita, Ai kawai Sai ganin mutum nayi Aga bana, kamar zamuyi karo da sauri naja da baya, tahowa ya kuma Yi Ni kuma na juya nashige d’akin iya da saurinsa ya biyoni, iya ma tana ganinsa ta mik’e.

Lafiya malam kashigo Mana d’aki ba Neman izini, had’e Rai ya kuma Yi sa Nan yace Mata” kin D’auko min Mata ba dole kiganni A d’akin ki ba.

Kuma Nasan harda hannunki A da wowata nida Heedaya kuma harda Kama muku d’aki kuzauna ku biyu to wallahi kiji, Sai nasa Kinga Abinda Sai kin fita da gudu Ana ka moki, kuma maganar Shigowa d’aki ba Neman izini yanzu kika Fara gani wlh har tsakar dare saina shigo yar’ tsohuwa dake Sai fitinar tsiya, duk masifar iya gala la tayi da Baki tana kallon Shuriem.

Ni kuwa tuni na shige cikin bargo d’akin ya k’arasa shigowa Murya ya d’aga yace” ke Heedaya bazaki mik’e ba ko haka kika Momyn mu tanaiwa ABBA  in yay ta fiya to zoki wuce muje ki bani Abinci da ruwan wanka.

Daga bayansa yaji Ana cewa to Mara kunya kaikuma da salon daka shigo Mana kenan to zoka fice kagama k’arewa iya yanzu kuma kadawo kaina nida Abba to mungode zo ka fice kabamu gurin tun Kan Raina yak’ Ara b’aci, Momyce, tun shigowarsa taji yadda yake razana Mata ya’ya, data fito kuma Sai Bata ganshiba can kuma tajiyo shi Yana k’arewa iya tanadi.

Tsugunna wa Yayi har k’asa yace” Momy Ina wuni, hannu ta d’aga Masa san nan tace da ban wuni ba Ai bazaka ganni ba Shuriem Aikasan d’akina kasan inda nake da can Anan kake gai sheni to bazan Amsaba tashi kafita.

Tashi Yayi simi_simi jiki ba k’wari ya fice, iya Momy ta Shiga bawa hak’uri San na ta nufi d’akinta, tana Shiga kuwa Tayi Arba da Shuriem ya kin Shigid’a Akan gadonta yana Danna waya, yanajin ta bud’e k’ofa ya tashi da sauri yace” sannu Momyna kin taho wlh Momy nagaji yunwa nakeji, kallansa tayi Tace” bana ce kabar gidan Baki d’ayaba me kuma kake Anan, kwab’e fuska yayi, San nan yace” To Momy inkika koreni Ina zanje, ina nake dashi Daya wuce nan wallahi Momy Taufiq Sharri yay min duk Abinda yazo ya Fad’a ba gaskiya bane.

Sai kuma ya fashe da kuka juyawa kawai tayi tafita batareda ta sake magana ba,

Kitcheen ta wuce tasa key ta ciki ta rufe, kuka ta farayi itama har ga Allah tana tausayin rayuwar Shuriem bataso yarasa farin ciki ko kad’an.

Duk Abinda ya faru tasan duk sharrin sihirin da Akayi masane Amma ta d’auki Alk’awarin insha Allah daga yanzu bamai k’ara Nasara Akansa, ruwa ta D’auko cikin friedge ta tofa Ayatul shifa Aciki wato Ayoyine da suke k’arya sihiri, Sai ta karanta falak’i da nasi da Ayatul kursiyyu, ta  bud’e murfin Robar ta tofa Aciki, San nan ta bud’e k’ofar ta koma d’akinta.

Shuriem Yana Nan zaune yadda ta barshi Amma yanzu yabar kukan da Alama yashiga dogon tunani hannu tasa ta D’an tab’ashi Kai ya d’ago ya kalleta, karbi wan Nan ta mik’a Masa ruwan karb’a Yayi yace” nagode Momy.

Bisi Milla yayi ya kafa Kai Saida ya shanye ruwan duka San nan ya bawa Momy gorar , karb’a tayi tareda ficewa ta barshi A d’akin.

Bayan Abba yadawo ne ya Tara mu duka A falo bayan tak’ai taccen bayani da yay Kan Abunda ya faru tsakanina da Yaya, Shuriem Abba ya Kira sunan sa  Shikuwa Shuriem ga bansane ya tsananta fad’uwa, Abba ne yay gyaran Murya ya sake cewa, Ina jiranka Ayanzu nakeso kowa kuma ya shaida kabani takadd’ar sakin Heedaya in ba haka ba, zan ya feka na kuma cireka cikin ya’ya’ na Dan haka kabani ita yanzu ya fad’a Yana me mik’a Masa hannunsa.

Ummy ce tayi zaraf Tace tokai Banda nacima Ance kasa keta ka gwqmmace uban naka yayi fushi da kai.

Sunkuyar da Kai Shuriem yayi idansa ya kad’a Yay jajir cikin rawar Murya ya Fara Magana kamar haka” Ni Shuriem Na………  Momy ce ta fashe da wani Matsa nancin kuka ta tashi tayi shigewar d’aki Shiru Yayi ya kuma Sun kuyar da Kai Abba ne cikin d’aga Murya yace” bada Kai nake maganaba.

Momy na jiwo Abinda Akewa Shuriem Kan Abinda bada hakk’insaba domin zuciyarta bazata iya daurewa ba.

Zaraf tayi tafito daga d’akin Abakin k’ofa ta tsaya San nan ta kallesu duka Tace” Bani na haifi Shuriem ba kuma indai natsine Masa Sai tsinuwar ta bishi domin Allah Baya barin hakk’in Wanda ya kyau tata maka, in dai har kuka Bari ya saketa saina tsine Masa daga haka ta fashe da kuka ta koma d’akin shi kuwa Shuriem Sulalewa yay Awajen idansa ya Fara kafewa….⁶⁷ ⁶⁸

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]