HEEDAYA CHAPTER 55 BY By Khaleesat Haiydar

Advertisements

_____

HEEDAYA CHAPTER 55 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Advertisements

_____

Shiru Ammi tayi tana kallonta, Heedayah ta kasa kallon Mahaifiyartata sai fidgeting din yatsunta take, mika mata 

wayar Ammi tayi, ta karasa ta amsa ta juya ta bar parlon ta kulle mata kofa ta koma dakinta, gefen gado ta xauna 

tayi dialing number Khaleel, yana fara ring ya daga, a hankali tace “Ina yini?” Cikin Husky voice dinsa yace “Lafiya 

lau, ya gida?” Tace “Alhmdllh, ya kowa da kowa” Yace “Fine…..” D’an murmushi tayi tace “Do you like it in there?” 

Ya d’an yi shiru sannan yace “Nop, not when u are not here Heedayah” Tace “Uhn you need to get use to ur relatives, 

and nasan Sumayya xata dinga keeping dinka company ai” Yace “Wace haka?” Tace “Cousin dinka mana” yyi shiru, 

tace “Ko ba haka ba?” Yace “Haka ne” turo baki tayi kamar xata yi kuka tace “Haka xaka ce min?” Yace “Toh yi 

hakuri, ba haka bane…” Knocking kofarta aka yi, tayi kasa da murya tace “Hold on pls xan bude kofa ana knocking” 

a hankali yace “Ohk dear” ta mike ta bude kofar taga Maid dinsu ce Amina, gaisheta Amina tayi tace “Hajiya kin yi 

bako a parlor yana jiran ki” Da mamaki Heedayah tace “Bako?” Amina ta gyada mata kai tace “Ehh” Juyawa tayi ta 

koma dakin, Amina ta bar bakin kofar, Khaleel yace “Wani bakon kika yi?” Heedayah tace “Nima ban sani ba wllh, 

let me go and check idan na dawo daki xan kiraka” A hankali yace “Alright…” Tace “Bye…” Daga haka ta katse 

wayar, ta dau mayafinta ta yafa snn ta fita, parlon baki ta nufa ta bude a hankali ta shiga da sallama tana leka ciki, 

Shuraim ta gani xaune idonsa a kan screen din wayarsa, ya dago kai suka hada ido, ta turo baki tace “Toh kai ne 

bako?” Bai ce komai ba har ta karaso cikin parlon ta xauna kujeran dake kusa da nasa tace “She told me nayi bako” 

Shuraim yace “Ohk to kilan bakon ki ka yi a waje, ki je ki samesa” Ta buda ido tace “I tot kai take ce ma bako?” 

Yace “Nima ban sani ba, na dai san nace ta kira ki ki amshi laptop dinki” Heedayah ta langwabar da kai tace “Ohk… 

A xubo maka abinci?” Yace “I’m not hungry” Tace “Good evening” Yace “How are you” tace “I am fine” ta wara ido 

tace “Two minutes plss” Daga haka ta mike da sauri tanufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, can dakinta ta 

koma ta dauko wayar Ammi ta fito, tana kusa parlon da Shuraim yake ta tsaya tayi dialing Number Farida, yana fara 

ring Farida ta daga, Heedayah tace “You know what sweetheart?” Farida tace “No, what?” Heedayah tace “Ya 

Shuraim ya xo ya tambayeki bari in kai masa wayar ku gaisa ynxu” bata saurari Farida ba ta shige parlon da sauri ta 

isa kusa da Shuraim dake kallonta, ta mika masa wayar hannunta murya can kasa tace “Xa a gaisa da kai” Bata jira 

yace komai ba ta kai masa wayar kunne ganin sai kallon wayar yake, ya kama wayar da mamaki, ta xauna arm din 

kujeran murya can kasa tace masa “Toh kayi magana mana” A hankali yace “Assalamu Alaikum” Murmushi kawai 

Heedayah ke yi tana kallonsa, Farida da taji gabanta ya fadi daga daya bangaren ta amsa a hankali ita ma tace “Ina 

yini Ya Shuraim” Shuraim ya kalli Heedayah da mamaki, ta wara masa ido, dauke idonsa yyi yace “Lafiya lau ya 

kike?” Farida tace “Alhmdllh, ya kano? Ya aiki?” Yace “Fine, ya su Mami?” Tace “They are all fine” Yace “Maa sha 

Allah, ana ta lectures?” Tace “Aa exams xa mu fara next week” Yace “Toh Allah ya bada sa’a, ayi karatu sosai” 

Murmushi Farida tayi tace “In sha Allah….” Xai cire wayar a kunnensa Heedayah ta mayar da sauri ta wani tsuke 

fuska murya can kasa tace “Kace yaushe xata xo kano joor” Kallonta kawai Shuraim ke yi, can dai yace “Yaushe xa 

ki xo Kano?” Farida tace “After my exams In sha Allah” Yace “Toh Allah ya kai mu muna jiran ki” Farida na 

murmushi tace “In sha Allah, ya kano weather?” Shuraim ya wani hade rai ya sake kallon Heedayah, wara masa ido 

tayi tana washe masa hakora, can dai yace “Alhmdllh” Farida tace “You like it there?” Yace “Sure it’s cool, ki gaida 

su Mami” Heedayah ta turo baki ta matsa kusa da kunnensa kuma, murya can kasa tace “Kace kana son ta fito da 

first class” Hannu yasa ya ja bakin nata, tayi wani kara ta rufe bakin da hannunta da sauri, Shuraim dake sauraron 

Farida dake masa sai da safe yace “In sha Allah, thank you” Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta bar wajen da 

sauri ganin Fixgota yake son yi, ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kallonta kawai yake, tayi me isarta ta koma 

kujeran da take xaune ta xauna tana wani murmushi tace “Kasan me ya Shureen?” Ya hade rai yace “What’s the 

meaning of what u just did?” Turo baki tayi taki cewa komai, ganin kallon da yake mata tace “Toh muna magana da 

ita ne shine take tambayata Ina ya Shureen shine na baku ku gaisa, is there anything wrong with that?” jingina yyi da 

kujera bai ce mata komai ba, ta ta6e baki tayi shiru, bayan few minutes yace “Abba yace xa a siya maki waya, 

wani iri kike so” Kallon wayarsa dake ajiye tayi ta mike ta karasa ta dauka tana duba wayar sannan tace “Irin 

wannan” Kallonta kawai yake, can yace “Toh sai ki rike wnn din kawai” Ta xaro ido tace “Ba sabo Abba yace a siya 

min ba” Yace “Wnn ma sabo ne ai” Ajiye masa tayi ta koma inda take tace “Bana son irinsa kuma” Murmushi kawai 

yyi bai ce komai ba, can ya kalleta yace “Ban taho maki da laptop din ba sai gobe” tace “Ohk, in kawo maka 

chargern?” Yace “Ehh” Mikewa tayi ta wuce dakinta ta dauko masa chargern ta dawo ta basa ya amsa yace “Thanks” 

Mikewa yyi yace “Sai da safe, kar ki ce ma kaka na xo” Tace “Baxa ka sha shayi ba?” Yace “Na koshi” Tace “Ohk, 

ina son xan maka magana, can I escort you say in gaya maka a waje” Ya kalleta yace “As u wish” bin bayansa tayi 

suka fita parlon…. Tafiya suke a tare tana gefensa, baka ta6a cewa dare ne don ko ina tarr da hasken fararen fitilu ga 

shukokin dake kewaye na ta bada Iska me dadi, bayan wani lkcn Shuraim ya kalleta yace “Har gida xa ki rakani 

kenan?” ‘yar dariya tayi tace “Aa, ai parking space din da nisa, but idan na rakaka sai ka sake rakoni rabin hanya 

sannan ka koma” Bai ce komai ba, jin taki magana ya kalleta suka hada ido, tace “Ya Shuraim ka gaya min irin qualities din da kake so a wajen mace?” Tsayawa Shuraim yyi yana kallonta yace “Why did you ask that?” Tace “No 

just tell me” Dauke idonsa yyi daga kallonta, ta kalli wani thatch me kyau dake dauke da kujeru tace “Mu je can mu 

xauna sai ka gaya min” Bata jira cewarsa ba ta nufi Thatch roofing din ta hau stairs dake wajen snn ta xauna kan 

daya daga kujerun, bin bayanta yyi xuwa wajen, ya xauna saman kujera, ta tallabi chin dinta tana kallonsa tace “Ina 

jin ka?” Ya shafa beard dinsa bayan few second yace “Ohkk… ina son mace me tsafta, me kuma rikon addini” Jin yyi 

shiru ta xaro ido tace “Shi kenan?” Yyi murmushi yace “Aa Ina son ‘yar doguwa fara, me manyan idanuwa da dogon 

hanci with cute lips” Heedayah ta wara ido tace “Dimples fa?” Yyi shiru yana kallonta, can yace “Yi dariya mu ga” 

Bata san lkcn da ta kwashe da dariya ba, yyi murmushi yana kallonta, ta gaji don kanta tayi shiru, bayan few 

seconds yace “Bana son dimples” Ta marairaice tace “Why” yace “Kawai haka nan” Tace “Toh baka son me gashi 

har gadon baya?” Ya d’an yi shiru, can yace “Toh ai ban san ya gashi yake har gadon baya ba, do you mind showing 

me?” ta d’an yi shiru kafin tace “Toh ai ni nawa bai kai gadon baya ba” Yace “Ehh xan iya measuring with my eyes 

ai” ta fara bin inda suke da kallo ganin sojoji ne can nesa da su bakin daya daga many gates din building din ta sauke 

mayafin kanta snn ta cire hulan gashinta ta cire ribon din da ta daure dogon gashinta da shi, tuni kamshin gashin nata 

ya cika wajen, kallonta kawai Shuraim yake, ta juyo tana nuna masa bak’in gashinta da ya sauko kasan shoulders 

dinta bai karasa gadon bayanta ba, jin bai ce komai ba ta juyo, sauke idonsa yyi tace “Have u finish measuring?” 

Yace “Yeah” ta daure gashinta ta mayarda hulan snn ta daura mayafinta a kai tana kallonsa, flowers ya tsura ma ido, 

tace “So?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Ban son gashin da ya kai gadon baya” Da mamaki tace “Me yasa?” Ya juyo 

yana kallonta a takaice yace “Haka nan” Ta langwabar da kai tace “Toh kana son me wushirya?” Yace “Meye 

hakan?” Tace “Gapped teeth” Yace “How? In ga naki wushiryan?” Tace “Aa bani da shi ni” Daga haka ta bude masa 

fine set of teeth dinta, Kallonsu ya dinga yi tace “Uhm??” Ya girgixa kai yace “No, bana son wushirya” Tace “Ohk 

hips fa?” Yace “Meye shi?” Tayi dariya tace “Hips ne baka sani ba?” Yace “Ehh” Tace “Ohk forget that” yace “Aa 

nuna min” tace “Aa forget that” Shiru yyi yana kallonta, tace “And don’t you want a girl that can cook all sort of 

varieties” Yana mata wani kallo yace “As if you can cook varieties” tace “Ni daban warce xaka so daban, nasan I 

don’t have much cooking skills, but you will need a girl that can cook many type of food” Shuraim ya tabe baki yace 

“Ko ruwan xafin da xata hada min shayi kadai ta iya tafasawa ta isheni a hakan, I have never been a foodie” Dariya 

Heedayah tayi sosai, sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi, a hankali tace “Ya Shureen you know what?” A 

hankali ya matsa kusa da ita yana kallon lips dinta yace “Repeat the name again” Xaro ido tayi ta matsa daga kusa da 

shi tayi dariya tace “Yaya” Jin bai ce komai ba tace “Why haven’t you ever thought of dating Farida? She is pretty, 

nice, good hearted, even her flaws are lovely, all the qualities i mentioned above tana da su, and beside all this… she 

loves you wholeheartedly, she’s been admiring you from day one, tun jiya take min xancen ka shi sa na hada ka da 

ita yau a waya, I am telling you Yaya Shureen you won’t regret it, she’s a wife material wllh…” kallonta kawai 

Shuraim yake ko kiftawa baya yi, tana kallonsa a hankali tace “Kayi shiru Ya shureen” Dauke idonsa yyi kafin yace 

“Me yasa kike mata sha’awana?” Tace “Sbda every lady will love to have you, ka ga na farko you are handsome, 

sannan kana da hali me kyau duk da baka sakewa da mutane kuma baka da yawan magana, but I know you are not 

bad, you are just being who u are, most important of all u are religious, kana respecting Mum dinka sosai…. Ur flaws 

are odd and unique….” Shuraim yace “Toh me yasa ke baki yi ma kanki sha’awar inyi dating din ki ba sai ita” Dariya 

tayi sosai ta girgixa kai tace “Kai yayana ne bbu wnn tsakaninmu, kaga kai da Ya junaid da ya Sudais I can never 

imagine dating you 3, sannan ma ni ina da wanda nake so da aure” Yace “Wa kenan?” Tace “Khaleel” Ya gyada mata 

kai bai ce komai ba, bayan few seconds tace “I have never asked for a favor from you, ni bamu wani saba ba ma 

balle in tambaya, so plss do me this favor, wllh Farida na sonka sosai, na dade da sanin haka, Ina son in hada ku 

pls…” Shuraim yace “Toh kamar yanda kema kike da wanda kike so, nima haka nake da warce nake so” Heedayah 

tayi shiru lkci daya jikinta yyi sanyi, a hankali tace “Wacece ita ya Shureen?” yace “When the time comes idan baki 

riga ni aure ba xan kai ki wajenta” Daga haka ya mike yace “Sai da safe” Ta mike ita ma kamar xata yi kuka tace 

“You are rejecting my frnd ya Shureen??” Ya juya yana kallonta yace “Kema ki hakura da saurayin da kike so in 

hada ki da wani da ya dade yana son ki, in har kin yarda da hakan wllh wllh xan amshi soyayyar kawarki, I will date 

her” da wani irin mamaki take kallonsa, ya sauka stairs din yyi wucewarsa ta bi sa da ido har ta daina ganinsa. A 

hankali ta sauka ta koma cikin gida, Tana komawa dakinta cire kayan jikinta tayi ta shiga bandaki tayi wanka ta 

dauro alwala snn ta fito, bayan tayi sllh tayi shirin kwanciya ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta dau wayar 

Ammi, missed calls din Farida ta gani uku sai na Khaleel guda daya, kallon agogo tayi taga tara har ya wuce, shiru 

tayi tana tunanin abinda Shuraim ya gaya mata, can ta shiga contact din Ammi tayi dialing Shuraim taga bbu 

numbersa a wayar, mikewa tayi ta sa Hijab dinta ta fita dakin, bangarensu kaka ta nufa ta bude kofar parlon da 

sallama ta shiga, suna xaune sun cika parlon da hayaniya, ta xauna ta gaishesu gaba daya, kaka na mata wani kallo 

tace “Sai yanxu garin ki ya waye Deedaya? Tun safe sai yanxu xa ki shigo gaishe mu?” Heedayah tace “Toh na shigo 

kuna bacci” Tana fadin haka ta dau wayar kaka bata sake sauraron surutan da suke mata ba, ta shiga call log ta duba 

number din Shuraim cikin kankanin lkci ta kwashe a kanta ta ajiye wayar ta mike tace “Sai da safen ku” Daga haka 

ta fice daga parlon ta kulle masu kofa, tana komawa dakinta ta dau wayar Ammi, miss call din Farida ta sake gani, ta saka number Shuraim a wayar snn tayi dialing, har ya gama ring bai daga ba, sake kira tayi no answer, ta tsura ma 

wayar ido, can ta kira Farida kawai, Farida na dagawa tace “Wayar na wajen Ammi ko?” Heedayah tace “Aa na bar 

shi a daki ne?” Farida tace “ke kina ina?” Heedayah tace “Ina parlor, ya Mami fa” Farida tace “Tayi bacci, Ya 

Shuraim din ya tafi?” Heedayah ta d’an yi murmushi don dama ta san kiran da take ta yi mata kenan, Farida tace 

“Hello” Heedayah tace “Tun daxu ya wuce dama kawai xuwa yyi in kira ki a waya ku gaisa, bayan kun gaisa kuma 

ya wuce” Farida tace “Me yasa ya gaisa da ni to?” Heedayah tace “Uhn nima dai ban sani ba” Farida tayi shiru, 

Heedayah tace “Yace in basa number ki nace sai ya biya kuma ya ki biya” Farida tace “Nawa xai biya?” Dariya 

Heedayah tayi tace “Kudi me yawa na yankar masa shine ya ki” Farida tace “How much” Heedayah ta wara ido tace 

“Just 100k” Farida tace “Uhm, to turo account number” Dariya Heedayah tayi tace “Xa ki biya masa?” Farida tace 

“Ehh” Heedayah tace “Hm to xan turo gobe, yanxu xan maida ma Ammi wayarta” Farida tace “Toh don Allah send it 

tomorrow, I will call in sha Allah” Heedayah tace “Allah ya kai mu, byee” Daga haka ta katse wayar, lkci daya 

jikinta yyi sanyi, is she suppose to pull Farida’s leg this much, tausayinta ya cika Heedayah, a hankali ta ajiye wayar 

don dama bata son su ci gaba da magana tana bata hope ne yasa tace xata kai ma Ammi waya, bayan wasu mintuna 

ta dau wayar ta shiga Kiran Khaleel, har ya gama ringing bai daga ba, ta sake kira bai daga ba, ajiye wayar tayi a 

gefenta ta kwanta ta lumshe ido, tunani iri iri ta dinga yi kafin bacci ya dauketa, can cikin bacci taji vibration din 

wayar ta bude ido a hankali ta jawo wayar tana kallon screen din..Kallon agogon jikin wayar dake nuna karfe sha daya da rabi tayi ta daga kiran ta kai kunne ba tare da tace komai ba, 

sallama ta ji yyi ta amsa snn tace “Ya hanya?” Yace “Alhmdllh” Shiru tayi daga haka, yace “I missed your calls” Ta 

turo baki tace “Eh ni ban gane maganganun da ka min daxu ba” Yace “Au haba?” Tace “Ehh mana” Yace “Then isn’t 

it better to forget it?” Tace “Noo, sai ka gaya min me yasa xaka wani ce kai kana da budurwa bayan baka da ita, ance 

maka Faridar bata da class ne? Ai dai bata ta6a nuna maka tana sonka ba, kuma ynxu kana nufin na xubar da class 

dinta na gaya maka kenan da xaka wani ce A’a?” Yace “Tare muke yawo da ke da kika san banda budurwa?” Tace 

“Ko ba tare muke yawo ba ni dai nasan baka kula mata, to me ma kke ce masu idan ka kulasu” murmushi yyi yace 

“Accept my frnd and I will accept ur frnd also, isn’t the equation balanced?” Ta marairaice tace “Amma dai kasan ni 

ina da wanda nake so and I made a lot promise to him…” Shuraim yace “Really?” Tace “Eh” Yace “What sort of 

promise?” Tace “That’s between I and him” Yace “Fine, nima I made lot of promises to my girl…” Shiru tayi bata ce 

komai ba, lkci daya taji wani haushinsa, calmly yace “Can I go off ur line now?” Bluntly tace “Noo, ba mu gama 

magana ba” Yace “Ohk Ina jinki gobe da safe xan fita aiki” Kamar xata yi kuka tace “Don Allah ya Shuraim kar ka 

mana haka, tell me is there anything wrong with Farida da kake tunanin you won’t love her?” Yace “Look, kema kiyi 

tunani, there is nothing wrong with my frnd dat will stop you from loving him, idan har da gaske kina son Farida 

you can sacrifice ur so called love for her, in har kika yi hakan wllh I am giving you my words gobe ma sai in kai 

maganarta gun Abbana” Kasa cewa komai Heedayah tayi mamaki ya cikata, jin ta kasa cewa komai yace “You just 

think about it, sai da safe” tace “Wait, waye mutumin da kake cewa” yace “Idan kince in kawo maki shi sae in kawo 

maki shi” Ta wani hade rai tace “Ka kawosa in masa me? Why don’t you want to understand ina da wanda nake 

so??” Yace “Fine, Kar ki sake kawo min maganar Farida nima” Daga haka ya katse wayarsa, ta6e baki tayi ta jefar 

da wayar tana tunanin maganganunsa, can ta kara ta6e baki a ranta tace “Lallai ma” d’an tsaki tayi ta kwanta, bayan 

kusan minti biyar ta sake jawo wayar, number Khaleel ta kuma kira bai daga ba har ya katse ta ajiye wayar ta 

lumshe ido tana karanto addu’ar bacci a xuciyar ta. Washegari da safe Heedayah ta gama duk abinda xata yi har 

karfe tara Khaleel bai kirata ba, daukar wayar tayi ta dialing numbersa amma har ya katse bai daga ba, lkci daya 

jikinta yyi sanyi, tana ta xaune dakin aka kira Ammi a wayar, mikewa tayi a hankali ta fita xuwa bangaren Ammi, da 

yake tun asuba ta fito ta gaisheta da Abbanta da step mum dinta, mika mata wayar kawai tayi tace “Ammi ana kiran 

ki” Amsar wayar Ammi tayi tana duba me kiranta, can ta ajiye tace “Ohk xan kirata, kinyi breakfast din?” Heedayah 

ta gyada mata kai, Ammi tace “Kin je gaida su kaka?” Tace “Yanxu xan tafi” Ammi ta ci gaba da abinda take,Heedayah tace “Ammi su Ashnaah fa?” Ammi tace “Yanda baki damu da su ba su ma ba damuwa suka yi da ke ba 

ai” Shiru Heedayah tayi tana kallonta, can ta juya a hankali xata fita, Ammi na kallon wayarta da ya hau vibrate tace 

“Wa ke kira?” Heedayah ta juyo ta dawo da sauri tana kallon wayar, Ammi tace “Waye?” A hankali tace “Ammi 

Khaleel ne” Ammi tace “Kiran me yake maki haka ne?” Heedayah ta kasa cewa komai, Ammi tace “Tambayar ki 

nake” Heedayah ta sunkuyar da kanta still bata ce komai ba, Ammi tace “Dauka ki fita” Daukan wayar Heedayah 

tayi ta juya ta fita daga dakin, nata dakin ta koma ta xauna gefen gado ta yi dialing numbersa don tuni kiran nasa ya 

katse, sai da ya kusa katsewa ya daga, ta wani hade rai tace “Why ain’t you picking my call tun jiya?” Yace “Na jira 

baki gama tadi da bakon naki ba shine na kwanta, daxu da kika kira kuma I was together with my uncle, is there any 

thing wrong with that?” Tace “Tadi kuma?” Yace “Ehh” Tace “Ya Shureen ne fa ya xo” Bai ce mata komai ba, tace 

“Toh da shi din xan yi tadin?” Calmly yace “Na sani??” Shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace “Xan 

fita yanxu, later…” Bata ce masa komai ba still taji ya katse wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din, 

ta fi minti goma xaune a haka kafin ta ajiye wayar, lkci daya ta ji jikinta yyi sanyi sosai, ta kasa ma fita daga dakin, 

knocking aka yi bakin kofar dakin ta kalli kofar kamar baxata tashi ba sai kuma ta mike ta isa kofar ta bude, Amina 

ce tsaye bakin kofar ta gaisheta snn tace “Hajiya tace ki kai mata wayarta yanxu” Heedayah ta juya ta koma daki ta 

dau wayar ta tafi ta kai ma Ammi, Ammi na amsar wayar Heedayah bata yarda sun hada ido ba ta juya ta fita daga 

dakin, dakinta ta koma ta fada kan gado ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, tayi me isarta ta hakura tayi shiru, 

tana ta kwance dakin aka bude kofar, Kaka ce ta shigo Amina da tayi mata jagora ta juya ta bar bakin kofar, kaka na 

washe baki tana bin dakin da kallo tace “Ba shakka, ke kuma nan ne bangaren ki kenan, wnn makeken daki haka 

kamar parlon gidan Amadu, ashe kina nan kusa kusa da uwarki mu kuma an ke6e mu can gefe tunda cin arxiki ne, to 

ae dai ya fi babu wai d’an agwai da bak’in d’a….” Heedayah ta mike xaune a hankali tace “Ina kwana kaka” Kaka 

tace “Aa ba ruwana, meye kuma ina kwana, da ban kwana ba xaki gan ni? baki san inda nake bane da xaki wani 

gaisheni da na shigo dakin ki? ke dai ba kinga na xo gidan ubanki ina ta xama ba dole ki tsiro wani shakiyanci daban, 

amma baxan biye ta taki ba tunda ba ke kika rokeni in xauna ba” Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka ta mika mata 

wayar hannunta tace “Tun daxu Farida ke son magana da ke, gashi nan kiyi mata flashing don nima ba katin gareni 

ba, dubu biyar ce jiya Babanki yace ya sa min, gwara inyi ta cancana kayana Ina jin muryar ‘ya yana da jikokina” 

Heedayah tace “Toh na ji” Kaka tace “Idan kun gama ki maido min da wayata yanxun nan” Daga haka ta fita, 

Heedayah ta duba balance din Kaka taga kusan dubu sha biyar ce a ciki, Kiran Farida ta shiga yi, yana fara ringing 

Farida ta daga, Heedayah tace “How are you doing Farida?” farida tace “Am fine dear, na kira wayar Ammi baya 

wajen ki koh?” Heedayah tace “Eh na mayar mata tun daxu, and kilan bata kusa ne” Farida tace “Ohk, kin fasa 

turowa ne in sa maki?” Heedayah tayi murmushi tace “Ki bari da daddare xan turo maki” Farida tace “Uhn but tell 

me, why did he even ask of me all of a sudden” Heedayah tace “Kawai yana son gu gaisa ne” Farida tayi shiru, lkci 

daya jikin Heedayah yyi sanyi tace “Bari idan na gama abinda nake xan kira ki ynxu” Farida tace “Ohkk” daga haka 

Heedayah ta katse wayar, ta fi minti talatin a ynda take, damuwarta biyu a lkcn, na farko abinda Khaleel yyi mata 

har da kashe mata waya, na biyu kuma hope da ta fara sa ma Heedayah alhalin Shuraim din isn’t even interested, 

gashi Farida har ta fara farin ciki, can dai ta mike jiki ba kwari ta fita dakin, bangaren Ammi ta koma, a hankali ta 

lallaba ta isa gun wayar Ammi ta dauka ta kwashe number Khaleel a wayar kaka ta fita da sauri ta koma dakinta. 

Kiransa ta shiga yi bayan ya daga tace “Shine ka kashe min waya?” Yace “To save you from struggling for words, ya 

gida ya kike?” Kin cewa komai tayi, yace “don’t you want to say anything?” Ta fashe masa da kuka, lkci daya ya 

rikice yace “Kuka kuma Heedayah? to ki yi hakuri don Allah, I am really sorry” Cikin rawar murya tace “Sbda na 

damu da kai ma shine xaka wani katse min waya, kuma nake ta kira ka ki dauka” Ya kwantar da murya yace “Wllh 

bana kusa, kiyi hakuri….” Jin tayi shiru yace “Kin hakura?” Tace “Nima ban sani ba” yace “Wahala xaki bani ko?” 

Ta turo masa baki, yyi kasa da murya yace “For the love you are having for me kiyi hakuri pls” A hankali tace 

“Nayi…” Yyi murmushi yace “Good gal, ya su mama?” Tace “Suna lafiya” murya can kasa yace “But kar ki sake ce 

min kinyi bako plss, that hurts…” Shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace “Gobe xan bar gombe, am 

tired” Da sauri tace “Da gaske?” Yace “In sha Allah” tace “Kai da wa?” Yace “Driver….” Tace “Toh plss just drop at 

kano pls” yace “Kano?” Tace “Yes plss” yace “Why?” Tace “Ka xo ka gaida Abbana da Ammina” Yace “That’s idan 

Mami ta amince, and ita ma tace gobe xata shigo kano tana da case” Da sauri tace “Xata amince ai, plss tell her you 

will drop there too” Murmushi yyi yace “Ohk Allah ya sa…. You know what karfe nawa xan kira ki ynxu xa mu d’an 

fita ne” Tace “Ina xa ka?” Yace “Gidan Gwaggwo na” tace “Toh xan kira ka anjima” yace “Alright dear” a hankali 

tace “Take care of ur self” yace “In sha Allah” daga haka ta katse wayar, tana ta kallon wayar kafin ta nemo number 

Shuraim, Har xata kirasa sai kuma ta fasa ta ajiye wayar. Yau ma da daddare Amina ta kwankwasa kofa ta sanar 

mata tayi bako, Heedayah dake kwance tana waya da Khaleel a hankali tace “Ya Khaleel wai Ammina tana kirana” 

yace “Ohk, should I wait for you or I should go to bed?” Tace “Aa ba dadewa xanyi ba ynxu xan dawo, idan na dawo 

xan kiraka” yace “Ohk then” katse wayar tayi ta ajiye ta dau hijab dinta ta sa ta fita, visitors palor ta tafi, xaune ta 

samesa tana kallonsa ta karasa cikin parlon ta xauna tace “Ina yini ya shureen” ya d’an daga kai ya kalleta yace 

“Looks like da gangan kike 6ata min suna” Tace “To ya xan ce maka?” calmly yace “Aliyu” murmushi tayi tace “Ni dai ya Shureen na sani” ya gyada mata kai bai ce mata komai ba, kallon ledan dake gefensa tayi tace “Wayana ka 

kawo min” yace “Ehh” ta mike ta dau ledan ta fiddo kwalin ciki, wara ido tayi tace “Waow…” Ta kallesa cike da 

farin ciki tace “I really like it ya Shureen, irin wanda nake so ne wllh” ta isa kusa da shi ta xauna arm din kujera tana 

murmushi sosai tace “Thank you….” Ta gefen ido ya kalleta amma bai ce komai ba, ta turo baki tana kallonsa tace 

“Nace thank you” yace “I prefer a cup of tea to that thank you” dariya tayi tace “Ohkk” daga haka ta mike ta dau 

hanyar kitchen ya bi ta da ido…. Shayi ta hada masa ta xubo masa pepper soup din offals a bowl snn ta fito, har ta 

shigo parlon kallonta yake ta isa gabansa ta durkusa ta ajiye bowl din offals din da cup din shayin ta wara masa ido 

tace “Is the thank you enough?” Yana kallon pepper soup din yace “Sure you are wlcm” ta dau spoon ta deba ta xai 

baki ya cafkota, xaro ido tayi, yace “Mayar ciki” da sauri ta fiddo a tafin hannunta tace “Toh xan karo maka 

sakeni…” yace “Wnn za ki ajiye” ganin ba saketa xai yi ba ta mayar da naman cikin bowl din, a hankali ya saketa 

yana kallonta, da mamaki take kallonsa ita ma, ya sauke idonsa ya dau cup din shayin ya fara sha snn yace “So what 

have you decided?” Tace “About?” Yace “Our talk yesterday” Shiru tayi na d’an lokaci, sai kuma ta kallesa tace “I’ve 

decided discard my request, cause ba a forcing soyayya, I will console Farida in ce mata may be kai din ba alkhairi 

bane gareta Allah xai bata wanda ya fi ka” kallonta kawai yake ko kiftawa bbu, can yyi murmushi yace “That’s 

because you are soo self centered, kanki kawai kika sani, you can never sacrifice ur love for her, nasan kuma da ita 

ce she will gladly do that for you” Heedayah tace “I am not being self centered, kaga kai ba sonta kake ba, ni ma 

kuma I will never agree to ur so called frnd, to ae hakan ba shi da amfani, ita ya kamata tayi hakuri tunda ba wai 

sonta kake ba” Shuraim dake ta kallonta yace “Haka nace maki bana sonta?” Tace “To tunda kana sonta snn ita ma 

tana sonka, ni me yasa xaka min dole, you are not being fair to me kenan?” Wani murmushi yyi yana ci gaba da shan 

shayin hannunsa, Khaleel ne ya fado mata ta xaro ido gabanta ya fadi, ta san yana can yana jiran kiranta, a hankali 

tace “Ya Shureen can I go now ina yin wani abu ne a sama” ya d’an kalleta kafin yace “Noo, wait in gama sai ki 

wuce” bata ce komai ba, bayan ya sha shayin ya ajiye yana kallonta yace “Take them back to the kitchen” tace 

“Pepper soup din fa?” Yace “I am full” tace “Ai baka ci ba” yace “Na sani” mikewa tayi ta dauka ta wuce da su 

kitchen gaba daya….. Tsaye ta gansa parlon yana kallonta yace “Mu je waje xan maki magana” Ta kalli agogo kamar 

xata yi kuka bata ce ma Khaleel xata dade haka ba, kofa ya nufa ta bi bayansa har suka fita parlon….. Abban 

Heedayah na xaune parlonsa tare da Ammi sai mom Islam, Abba ya kalli Ammi da gaba daya mood dinta ya canxa 

lkci daya kuma tayi shiru, yace “Say something Aisha” Ammi ta girgixa kai a hankali tace “But ur Excellency what’s 

wrong with the Junaid da xa a biye mata don tace bata so? Idan ma bata sonsa ga Shuraim dama ni hankalina ya 

kwanta da shi” Abba yace “Ke dole kike son ayi mata? snn still wanda tace take so ai d’an gidan ne shi ma naga” 

Ammi ta kallesa da sauri tace “Wa kenan??” Abba yace “Wan Junaid din, Khaleel…” Da mamaki Ammi ke kallonsa, 

can tace “Haba ur Excellency, ni gaskiya ban amince da wnn xancen ba, me yasa xa a biye mata kamar ita ta haife 

mu??” Abba yace “Abinda yyi Junaid shi yyi yayansa, haka ko ba haka ba?” Ammi tace “Aa wllh, his past…” Sai 

kuma tayi shiru, Abba kallonta kawai yake, Mom Islam tace “His past is nothing to write home about…. And kina 

duba reputation na gidan nan ko?” A hankali Ammi tace “Exactly Maimuna” Murmushi Mum Islam tayi sannan tace 

“Amma kar ki manta Aunty, Mahaifiyar wnn mutumi bata san wacece Heedayah ba, bata san ‘yar wacece ita ba, bata 

san daga inda take ba amma ta yrda ta amince ta riketa bayan shi wanda ma ya tsinceta an ki rike masa ita cikin 

iyalinsa” Kasa cewa komai Ammi tayi, Mum Islam tace “It isn’t Khaleel’s fault he found himself in such life, kar ki 

manta yau da Heedayah ba hannu na gari ta fada ba Allah kadai yasan wani irin rayuwa xata yi, Allah kadai yasan 

abinda xata xama, albarkacin wnn bai kamata ki kyamaci d’an wannan baiwar Allah da ta inganta rayuwar ‘yar ki ba 

ba tare da hakan ya bata wahala ko shakku a ranta ba….” Murmushi kawai Abban Heedayah ke yi bai ce komai ba,

Ammi dai ta kasa cewa komai…..

Advertisements

_____

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Advertisements _____ HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Advertisements _____ …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *