[Advertisements⬇️]

GIDAN AURE CHAPTER 6 KARSHE BY ZAHRATEEY - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 GIDAN AURE CHAPTER 6 KARSHE BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ina shiga watan haihuwa ta hankali na ya mugun tashi domin banso cikin yazo duniya ba ta wani 6angare kuma ina son kuntatawa Ahmad da kuma nusar da mazaje irinsu aika aikar da matan su ke aikatawa saboda rashin kulawarsu, ba duka aka hadu aka zama daya ba amma kuma duk wani namiji ya dace ya san yanayin matarsa da iya gejin hakurin da zata iya yi idan babu shi a tare da ita, kamar yadda ake so ko wata mace ta san waye mijinta da kuma yanayinsa a ko wani lokaci, idan zama da cutarwa ya zama dole ayi maganinta ta hanyar rabuwa domin shine kawai abin da ya dace saboda karshe sai dai a fada halaka, misali gani nan ina da miji wai fa amma saboda rashin kulawar mijin yau gashi zan haifa mishi dan me gadinsa a cikin gidan shi, akwai matan ko mazan da abokan rayuwarsu ke kulawa da komai nasu tare da sauke hakki dai dai gwargwado babu cutarwa amma son zuciya ke kaisu aikata abubuwa marasa dacewa, akwai wanda shurunsu ke cutar dasu alhali

maganar idan da ace sunyi tabbas zai zame musu mafita, shi fannin namiji abu ne me sauki dan kuwa zai iya kara aure ya kuma samu biyan bukata ke kuma kasancewarki mace ba haka ne mafitarki ba mafita daya ce ku magantu da juna idan da halin ya sama muku mafita fine idan babu kuma ku rabu cikin aminci kiyi wani auren, akwai mata da yawa masu fama da irin matsalar rayuwata wasun jahilci ke kai su fadawa halaka wasu kuma son zuciya da rudin shaidan irin nawa saboda inada sani dai dai gwargwado kan abin da ya shafi addinina, dadin dadawa ma ni Hafiza ce.

+

Tabbas rayuwa tayi min ba dadi domin babu me fatan haihuwar shege ko shegiya sai dai kuma ya za’ayi da kaddara dole a hakura a barwa ubangiji, da ake na samu dama da tuni na 6aras da cikin dan nasha magunguna kala daban daban amma shuru kakeji abu yaki yuyuwa, asibiti ne kawai nake tsoron zuwa da sunan zubarda cikin dan babu makawa kasancewa ta maaikaciyar asibiti zan iya haduwa da idon sani, duk wani dabara nayi amma yaran sunce sai sun fito, cikin ikon Allah na samu yara har uku duk maza, murna akeyi ta ko wani 6angare daga iyayena, iyayen mijina da danginshi da dangina har zuwa abokan arziki, so da tausayin yaran shine ya cika min zuciya Allah sarki gashi har yara uku amma duk bana sunna ba, gasu kyawawa dasu masha Allah duk babu in da suka dauko na uban su sai nawa, sosai naci kuka na gode Allah dan abu biyu ne ke dawainiya dani farin ciki da bakin ciki me cike da dana sani ni duk dangi ma tausayi suke bani saboda yanda suka daura wa yaran so bama kamar maman mijina da kamar zata hadiye su dan soyayya, ni dai an barni da yaken dole dan shine kawai abin da zan iya yi saboda bakin cikin daya tsayamin a wuya, duk kawayena sunzo naga canji tare dasu, Jawahir duk tayi sanyi kamar ba matar Jamilu yar kwalisa ba, Zaliha duniya sabuwa sun shirya dame gida ita ma cikinta ya yi girma ta kara kyau gwanin ban shaawa, Nafi ma tazo da yan tagwayenta mata yan wata uku, haka Faiza da yarta daya yar wata biyu duk dai da gani basu da matsala a halin yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan anyi taron suna an watse ya rage dagani sai wata tsohuwa da aka bar min domin kula dani, sai kuma uban gayyan daya kasa komawa saboda soyayyar yaran da suka shiga cikin zuciyarsa, a wani lokaci yana bani tausayi a wani 6angare kuma yana bani haushi saboda shine silar duk abin da ya faru dani, da ace ya tsaya ya fahimce ni mun fahinci juna da ban kai ga yin wannan aika aikar ba da ko da rabuwa ne munyi idan zaman ba zata yuyu ba, amma babu abin da ya dame shi sai aikinsa da kuma idan nashi bukatar ya tashi sai ya biya ba tare da ya yi laakari dani halin da nake ciki ba shi kawai kanshi ya sani, kuma wallahi akwai maza da yawa irinsu da matansu sai dai suyi hakuri da lamarinsu tare da kai zuciya nesa, marasa hakurin ke kashe aure domin gudun fadawa halaka amma masu hakurin se dai suyi ta zaman jurewa suna cutuwa a cikin gidajen aurensu, wata duk ta lalace kullun tana cikin damuwa ga shegen mantuwa saboda hankalinta baya jikinta damuwa tayi mata yawa amma duk sai dai ta hadiye ta barwa cikinta ko kuma ta fada bin maza daga masu aikinta zuwa mazan waje.

A haka rayuwa yaci gaba da tafiya sai dai yanzu yana zuwa a kai a kai saboda yaran amma dai still bukatarsa shine nashi damuwar bai damu da tawa ba. shekaru shida sun shige yara sun girma sunyi wayo a lokacin kuma Allah ya azurtani da cikin mijina Ahmad, duk da cewa jiya e yau babu abin da ya sauya zani daga 6angarensa son kansa sai abin da ya yi gaba bai damu da bawa hakkin ba, sai dai nawa 6angaren nayi kokarin chanja hali domin ban sake amincewa da tarayya da baban yan uku ba domin abin ya ta6amin zuciya ganin yara har uku shegu a gabana kuma babban zunubin ma da aurena na aikata wannan danyen aikin, kullun sai nayi kuka na nemi gafaran ubangiji tare da tunanin makomata da kuma yanda zan fuskanci Ahmad da gaskiyar zancen yan ukun dana haifa, sam sam ban bari wani ya gane halin da nake ciki ba shima me gadin na sallameshi tare da kar6an lambarsa saboda halin rayuwa kuma na mishi alkawarin zan bashi yaranshi idan na samu damar fayyace wa Ahmad komai, bai wani damu ba saboda auren da ya yi wanda aka hadashi da yar uwarsa kuma cikin ikon Allah har sun haifa yara biyu a yanzu wanda suka dauke mishi hankali har ya kan manta da yaranshi na gurina sai dai idan ya tunasu ya kan kirani yaji lafiyarsu nima kuma na kan bashi su a waya da sunan uncle dinsu ne.

Cikin ikon Allah cikina ya shiga watan haihuwa duk a tsorace nake ina tunanin kar in mutu a gurin haihuwar gashi ban sanar da Ahmad waye yan uku a gurinshi ba, yan uwa dai sun san ina da ciki amma basu san yaushe haihuwata zata kasance ba sai shi Ahmad wanda mukayi dashi sai dai a buga ace musu na haihu, duk kuma ni nayi planning abu na saboda a wannan ga6ar nake son sanar dashi gaskiya ko da ace zan mutu bayan hakan amma gwara ya sani tun kafin lokaci ya kuremin, a ranar da na fara nakuda ya iso Kaduna muka garzaya asibiti inda aka fara bani taimakon gaggawa, awa biyu awa uku har zuwa dare shuru babu wani zance hakan yasa sukace tunda na kasa kawai gwara ayi min aiki, sam sam naki yarda da wannan shawaran tasu karshe dai shi suka kira yazo ya min magana saboda lokaci na kara tafiya, bayan ya shigo ya fara bani hakuri kamar ba Ahmad din dana sani ba karshe dai na amince da sharadin ina son muyi magana dashi, yace to sannan yaje yasa hannu yacevsu bashi yan mintina kad’an zamuyi magana suka amince babu jayayya, bayan ya zauna na fara da yar nasiha da jan hankali akan irin rayuwar da mukayi dashi da irin abin da ya jawomin har ta kai ga naci amanarsa karewarta ma haihuwar yaran wani a cikin gidansa, ban 6oye mishi komai ba na sanar dashi tare da neman yafiyarsa na kuma shaida mishi cewa cikin jikina nashi ne idan yana tantama sai ayi gwaji idan na haihu, duk laifinshi da nawa laifin na karonto mishi wanda ya sanyaya jikinshi yaji ya tsani kanshi bai iya cemin komai ba ya fice ni kuma na soma kuka wanda tashin hankalin da nake ciki saboda halin da Ahmad ya shiga yasa na fara labour gadan gadan inda Allah ya taimakeni na haihu da kaina na samu yan biyu mace da namiji sak Ahmad, yau kam kukan farin ciki nayi wanda rabon da nayi irinshi tun bayan graduation din mu na Tahfiz, sosai nayi kuka na gode Allah daya bani ikon ganin yarana na sunna daker na tsagaita na koma ajiyar zuciya, lokaci kankani mutane suka fara hallara dan yin barka, ganin babu wani matsala a tare dani kawai aka sallame mu muka koma gida, bamu dade da isa ba Mama na da maman mijina suka iso a lokaci daya tare da yan uwana, cikin aminci akayi suna kowa ya koma cikin farin ciki da annashuwa yara sukaci sunan mamanshi da babana, wancan karan dama yaran baa musu me suna ba kawai an rada musu bisa irin sunayen da yakeson sanyawa yaransa da Muhammad Alamin da Aliyu Haidar da Abubukar Sadiq, tun bayan rabuwar mu a asibiti ban sake saka shi a ido ba ina dai jin muryarsa idan yazo gaida mutane a lokacin ina wanka kuma na lura sai a wannan lokacin yake zuwa ya duba yaransa, bayan an watse ya rage ni yaran da wata tsohuwa daga dangin mamana sai mijina wanda har lokacin bamu hadu ba.

STORY CONTINUES BELOW

Ashe ya koma gurin aiki babu labari sai a bakin mamanshi nake jin wai ya koma, dama nayi tunanin haka saboda mun kwana biyu banji motsinshi ba a haka har mukayi arbain tsohuwar ta koma ya rage nida yarana dan yanzu bani da me gadi gidan shuru sai mu kadai. Bayan wata biyu da rasuwan maman mijin Faiza ina zaune a falo ina yiwa yaran assignment ya shigo da faraa kamar anyi mishi albishir da aljanna ni abin ma har ya bani tsoro na rasa dalilin wannan murmushi, oyoyo ya yi wa yaran dukansu sannan ya dauki yaransa ya musu wasa tare da zubamin ido, ni duk sai naji kunyarsa ta kamani duk jikina ya yi sanyi a hankali na zame na wuce daki, ina zauna ina dirzan kuka ya shigo da sallama tare da yaran ya kwantar dasu da alamun sunyi bacci, zama ya yi kusa dani yace “bana son mu tuna abin da ya wuce kuma har ga Allah na yafe miki duniya da lahira saboda nine silar komai wanda hakan kesa nake jin kunyarki, banyiwa yaran test ba domin ko makaho ya shafa ya san yarana ne, kuma sauran yaran suma na kar6e su hannu bibbiyu tare da amincewar mahaifinsu dan na same shi bayan barina gida mun tattauna dashi, kuma yace ya bani su duniya da lahira kuma ni na yafe mishi saboda sakaci na ne ya janyo miki haka, ina so hakan ya zama sirrin mu wanda babu wanda zaiji wannan batu har abada ki yafe min dan Allah” ni kuka shi kuka an rasa wa zai rarrashi wani a cikin mu ni duk abin kamar a mafarki nakeji, na dauka zan zama abin walakantawa a halin yanzu na dauka cewa zai tona min asiri ashe ni har yanzu ban gama sanin mijina ba, ashe yana da irin wannan kyakyawar zuciyar, kuka nakeyi tsakani da Allah kuma na kudirta a raina dole zan fadawa hajiyarsa gaskiya domin gaba, ban dai sanar mishi ba a haka muka sha kuka muka gode Allah, karshe dai shi ya koma rarrashina har yaran suka farka a barci sannan na tsagaita, kamar babu abin da ya faru haka muka koma rayuwar mu, sai dai har yanzu naki sakin jiki dashi sosai saboda tsoro da kunya da fargaba, a haka ya yi wata guda yana gida bai koma gun aiki ba, bayan sati biyar da zuwansa muka dunguma Kano inda naci alwashin fayyace wa hajiyarsa gaskiyar zance ai kuwa munyi sa’a har Alhaji shima yana gari, bayan kwana biyu da zuwan mu na same su a falo dashi da iyayenshi duk yanda yaso hanani magana sharewa nayi na fada musu komai daya faru duk a tsorace da kuma alajabi suke sauraron zancena, irin haka labarinsa suke ji  sai gashi yau ya faru a kan dansu.

Hajiya haushin danta ne ya kamata saboda duk laifinshi ta gani, Alhaji kam haushina ne ya kama shi nan take yasa Ahmad ya sakeni saki biyu sannan yace in tattara in bar mishi gida tare da shegun yarana, dana nayi zaton hakan zai faru but nayi tsammanin that reaction will come from Hajiya not Alhaji, duk yadda Hajiya da Ahmad suka so magiya kinji ya yi haka na tasa yarana a gaba muka hau mota zuwa Abuja inda iyayena suke a yanzu, mahaifina dama ya rasu mahaifiyata da kakata na taras suma na fayyace musu komai ranar nasha duka sai da na kwana a asibiti, sati na biyu ina jinya a gida kafin kawuna yayan Mama na yazo ya nata tatas ya nuna mata ai ba laifina ni kadai bane da ace tana jana a jiki da ta san abin da yake faruwa har ma ta bani shawara kuma da hakan bata faru ba sannan kuma ya nusar da ita kaddaran haihuwar yaran ne yazo a haka, ranar dai duka yan uwana na gida munsha nasiha a gurin Kawu masu jin haushina sun daina kuma mun nemi yafiyar juna shima uban yaran anje har garinsu iyayensa sun san komai game da jikokinsu na waje sun kuma kar6esu hannu bibbiyu tare da yarda da kaddara sannan sukace a barsu a gurin su, sosai suka burgeni kuma nauyin dake zuciyata ta ragu, bayan wasu watanni Hajiya da kanta tazo ta ba da hakuri wanda iyayena da yan uwana suke ganin ai sune ya dace su ba da ba ita ba, a haka dai aka sulhunta sai da nayi kusan shekara a gida Alhaji ya amince aka sake daura auren mu, shi kuma Ahmad ya ajiye aikinsa ya bude babban shago yana saida kayan mata dana maza, zaman lafiya mukeyi sosai sai a yanzu na san nayi auren soyayya domin a halin yanzu sai godiya ba zance ga abin da Ahmad ya rage ni dashi ba, da din ma ajizanci ne na aan adam ba wai dan ban zai iya samamin natsuwa a matsayina na matarsa ba, bayan dawowata na sanar da aminai na komai ban boye musu ba, sosai suka jajantamin tare sa nasiha ne ratsa jiki, a yanzu haihuwata biyu a gidan Ahmad bayan Twins na haifi me sunan Alhaji da kuma me sunan mamana dana nan haihuwa ya tsayamin, yarana yan uku sun dawo hannuna kamar yanda Ahmad ya yi alkawarin kar6osu sosai nayi kukan farin ciki domin banyi tsammanin zaa barni dasu ba.

_________________________

6angaren Faiza soyayya me tsafta ke gudana da zaman lafiya tsakaninta da mijinta da abokiyar zamanta, duk yanda Mama taso ta hana zaman lafiya taso shiga tsakaninsu Allah bai nufa ba, sosai Dada take gasa nata Aya a hannu kuma babu damar magana duk abin da akeyi Salmanu bai da labari domin duk lalacewar mahaifiyarsa uwa uwace ba zai so ya ga ana walakanta ta ba, duk da cewa ba cin mutunci Dada take mata ba amma duk abin da ta shuka shi ta girba domin yaranta biyu kannen Salmanu duk sun dawo gida saboda hana su zaman lafiya da iyaye da dangin miji sukayi, duk sun lalace gashi duk babu wanda Allah ya bawa haihuwa a cikinsu, duk dai cin mutunci da gori da takeyiwa yar mutane sai ya sauka a kan yaranta, watansu uku a gida kafin lamarin ya daidaita suka koma cikin aminci, kuma silar Faizar da suka tsana domin har gidajensu taje cikin sanyi ita da Dada suka nusar da iyaye mazajensu abin da sukayi da be dace ba tare da bada example da kanta ita Faizar a cewarta Allah ne ya dubeta kuma ya saka mata ta hanyar hana su zaman lafiya a nasu gidajen, dan haka idan ba fata suke hakan ya faru da nasu yaran ba sai suyi hakuri su gyara, sosai ta sa musu sense a cikin kwakwalwarsu tare da nasiha me sanyaya jiki da jini wanda dalilin haka suka sanya yaransu suka dawo da matan nasu tare da neman yafiyar juna, yanzu sosai suke zaman lafiya tare da kauna me tsafta domin sun koyi darasi me karfi na idan kayi zaa maka kuma duk abin da ka shuka shi zaka girba, yanzu Faiza bata da matsalar komai hakurinta shine abin da take mora a yanzu dan dangin miji sun dawo mata dai dai da taimakon Dada, shiyasa take kaunar Dada tsakani da Allah suke zama Na amana, Mama tayi sanyi ta cire idonta kan lamarinsu tare da binsu da addua, haihuwar Faiza uku Dada kuma biyar saboda ta samu tagwaye har sau biyu. A halin yanzu Mama ta rasu haka Dada itama ta rasu ta bar amanar yaranta a hannun Faiza wacce tayi kuka mara iyaka har da zazza6in sati biyu dan sabo da sukayi da juna, shima Salmanu mutuwar ta girgiza shi saboda Dada mace ce ta gari wacce ta zama silar kwanciyar hankalinsa da kuma zaman lafiyar ahalinsa.Wahala sosai Latifa ta bawa Hafiz da matarsa ko kadan ta hana su zaman lafiya da kwanciyar hankali, bata dai shiga hakkin yaran matan Hafiz ba amma da Hafiz da matarsa sun garu iya garuwa, har ta kai sai da suka koma rokonta suna hadata da Allah kafin ta barsu, duk da haka gargadi me tsanani tayi musu akan yar uwarta, ko da wasa basu sake ko da kallon banza bane a Zaliha kuma abin da take so shi a keyi a gida, inji Latifa wai zata fanshe kwanakin da sukayi suna zalintarta, Latifa da tazo yan kwanaki sai ta buge da zama har sai da Zaliha ta haihu, a lokacin da Hafiz ya san da cikin ya yi matukar farin ciki sa6anin matarsa da a dole take nuna farin ciki a fuska, cikin ikon Allah Zaliha ta haifi namiji aka saka mishi sunan babanta Harun, sai a lokacin Latifa ta shirya tafiya bayan gargadi me tsanani a cewarta suka kuskura suka ta6a yar uwarta wallahi zata dawo tayi musu rashin mutunci, tsoro da fargaba daya darsu a zuciyarsu game da ita shine yasa duk sukayi sanyi kowa ya shiga taitayinsa.+

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Bayan suna haka suka cigaba da zama cikin dar dar tare da yin biyayya a Zaliha da gudun 6acin ranta saboda kullun sai Latifa ta kira tace a basu wayan idan sun gaisa ta tambaya ko sun koma gidan jiya, sannan ta sake jaddada musu cewa zasu iya ganinta a ko wani lokaci zuwan bazata dan haka su kiyaye, zaman lafiya da kwanciyar hankalin dole ya zagaye gidan daga yara zuwa iyayensu, a haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya inda Zaliha ta sake haihuwar diya mace aka saka mata sunan maman Hafiz Kaltume ana kiranta Ikram, bayan wasu shekaru Hafiz ya zo ya gano gaskiyar wacece matarsa inda ta samu labarin cewa da asiri akayi aurenshi da ita lokacin yaje bautan kasa garinsu kuma sannan duk yaranta ba nashi bane na ainihin saurayinta ne wanda auren Hafiz shine silar yin kudinsa, acewar bokanta idan ta samu bahaushe ta aura kuma tana muamala da Sani tabbas Sani zai yi kudi na shahara wanda zaa san shi a karinsu har ma a wasu garuruwa, sannan babu shi babu yin aure idan ba da ita ba, hakan yasa data hadu da garanta Hafiz ta makale mishi har sai da sukayi aure bayan ta asirce shi shiyasa bashi da kata6us, a garin tone tonen Latifa ne ta tono mata asirin data binne a wani lungu gurin shuke shukensu ta can bayan gidan, bata sanar da kowa ba tayi abin da ya dace wanda take gani yarbawan garinsu nayi idan sun samu laya ko wani abu daya danganci asiri, a haka ne abin ya fara barin jikin Hafiz har ya daina bin umarnin Bara’a kuma ita bata kawo komai a ranta game da asirin da tayi ba sai da Hafiz ya yi ido hudu da abin da ta aikata mishi sannan ta tona wa kanta asiri da kanta tare da sanar mishi cewa yaranta na nashi bane, ranar Hafiz ya yi kukan bakin ciki jin cewa yaran wani Gardi ya rike ya kuma walakanta nashi, sai ga Hafiz da shegen dansa a rungume yana kuka yana dana sanin kin kula yaron koba komai jininshi ke yawo a jikin yaron sa6anin wadancan shegun da da auransa a kan uwarsu amma ta badewa idonta toka rudin duniya ya kwasheta ta rinka haifa mishi su a cikin gidanshi, ranar kam dan Hafiz yaga gata da soyayya wanda hakan yana Zaliha kukan dadi dan farin ciki sai da tayi ta kyauta me tsoka a marasa galihu duk da cewa itama rufin asiri ne kawai da ita amma dai tafi wasu kuma Allah ya bata wanda zata iya fitarwa.

STORY CONTINUES BELOW

A ranar Hafiz ya saki Bara’a ya korata da ita da yaranta kuma basu kara jin labarinta ba, sosai ya sha wahala kafin suka shirya da Zaliha dan zuciya tayi itama ta fara dandana mishi abin da ya aikata mata, sai da ta garashi ya rame ya fita hayyacinsa sannan ta yafe mishi suka dawo dai dai, soyayya me tsafta da kwanciyar hankali ya ziyarci cikin gidansu, ga yaran shi duk ya hade kansu dana Sunna guda uku da Zaliha ta haifa da kuma wanda ya kasance kaddararsu, yanzu kam basu da wata matsala sai matsalar da baa rasawa tsakanin maaurata.

_________________________

A 6angaren Jawahir tun da aka kawo amarya ta koma sukuku duk ta fige ta rasa nasuwarta, ko da wasa bata shiga sabgar amarya da ango, babban damuwar Jamilu kenan shuru shurun data zama tsoranshi kar wani cuta ya kama ta, kullun yana kokari gurin kyautata mata amma ko ci kanka bata ce mishi idan ya gaji sai ya tafi ya barta idan kuma ranar kwananta ne sai ya zuba mata ido ya yi ta kallon yanda ta koma kamar me takaba, yanzu ba kwalliya ba yawo sannan gidan ta jiya e yau yanda dai kuka sani tun farko haka take babu gyara koma bata sauya zani ba, abu daya ne ya faru yaranta data dauko daga gidan maman Jamilu ta koma jansu a jiki amma sun ki sakewa da ita dan yanzu sunfi ganewa Anty Amarya me son su da kaunarsu, me kaisu yawo da saya musu duk abin da bai fi karfinta ba, duk wani abin da suka rasa gurin uwarsu sun samu a gurin Anty Amarya, a lokacin da Jawahir ta fuskanci haka shine ta dawo dasu gurinta da zummar raba su da matan babansu amma abin yaki yuyuwa dan sunyi nisa a kaunar me kaunarsu, ko da suka dawo hannun ta sunki sakin jiki da ita abu kad’an Anty Amarya har sai da ta bugesu wanda ya kara janyo mata tsana da ja baya daga soyayyar da suka mata a matsayin mahaifiyarsa, kuka suka saka wanda ya tashi hankalin Jamilu kuma suka botsare akan ba zasu zauna da ita ba su gurin Anty Amarya zasu koma, babu yanda ya iya haka ya daukesu ya mayar dasu 6angaren Antyn nasu.

Duk yanda yaso ya sawa Jawahir sense abin yaki yuyuwa, karshe kawayen nata su Zaliha ya kira ya shaida musu matsalar da yake fuskanta da matarsa duk da cewa ya san sun santa da halin data kasa dainawa amma kuma yana so ta dawo hankalinta domin su daidaita da yaranta tun kafin abin ya wuce gona da iri, kuma yana so ta gyara ko dan karta jawa kanta raini a gurin amaryarsa duk da cewa ba zai bada damar a raina mishi mata ba amma kuma halinta shi zai iya saya mata rainin, ko da su Zaliha suka samu shiga wajenta ba wai nasiharsu da shawararsu ya shigeta bane kawai dai ta busu da to ne saboda a zauna lafiya kuma karsu cikata da surutu. A haka ta cigaba da zaman gida tana kunci ita kadai har ta gaji ta koma halinta na da na yawon biki da suna ga kazanta daya karu saboda cikin dake jikinta sai dai kun san dama ita kazantarta na gida ne bana jiki ba dan haka gidan ta ne kamar bola ga doyi amma duk ita bata ji hankali kwance take gudanar da lamarinta a jujinta inji Jamilu da fada, Anty Amarya ta rigata haihuwa inda ta samu diya mace aka saka sunan mamanta sai kuma Jawahir data haifi namiji aka saka sunan late mahaifin mijinta daganan bata sake haihuwa ba Anty Amarya ce kawai me haihuwar inda tayi yara biyar duk mata, gaba daya hankalin mijinta da yaranta na kan Anty Amarya domin itace ragamar rayuwarsu ita suka sani matsayin uwa ba Jawahir ba, domin ita kamar a Anty Amarya ta haifawa yaran dan bata da lokacinsu har mantawa takeyi dasu su kuma dama sun bar shiga sabgarta.

Wani zuwanta biki ne ta hadu da tsautsayi inda sukayi hatsari mutane biyar suka rasu cikin dangin miji dana mata kuma a cikin su ita kadai ce ta rayu da karaya a hannu da kafa, sosai tayi jinya wanda ya tsorata ta gaba daya ta fige ta zama kamar ba Jawahir yar gayu ba, Anty Amarya me kyakyawar zuciya ita take kula da ita ga kuma yara har takwas duk a karkashinta, sosai Jamilu ke tausayawa  Anty Amarya da kuma matukar so da kaunarta saboda ta cike mishi gurbi da yawa daya rasa a rayuwarsa, mata yar uwa aminiya kuma uwa ga yaransa da uwasu ta wofintar, ta kasance haske a cikin rayuwarsu tun Jamilu na kunyar Jawahir har ya sake ya nunawa duniya Anty Amarya itace rayuwarsa kuma farin cikinsa, tun Jawahir bata ganewa har ta gane cewa ta rasa mijinta saboda sakacinta domin yanzu bai wani damuwa da lamarinta tsakaninshi da ita gaisuwa shima sai idan sun hadu dan zuwa 6angarenta yana zuwa amma dakinshi kawai yake zama baya kula alamuranta duk abin da taso yi tayi damuwarta ne, bata gama tsorata ba sai da ya tashi tafiya kasar waje inda zaiyi aikin shekaru hudu sai gashi ya dauki matarsa da yaransa ita ya barta a Nigeria.

STORY CONTINUES BELOW

Sosai tayi kuka ta gode Allah har sai da maman Jamilu ta shiga lamarin ta hanyar mata nasiha da ban baki da shawarwari na yanda zata dawo da martabanta a idanun mijinta, farko dai ta fara yakice kazanta ne sannan kuma ta kara shiga makarantar girke girke dan gyara cikin mijinta, daga nan ta shiga islamiya ta fita sabgar Jamilu da matarsa, a can 6angarensa shi da kan shi ya san bai kyauta ba amma hankali yake son koya mata shiyasa ya barta, sai da suka shekara biyu sannan ya dawo ya dauketa bayan ta cika shi da mamakin sauyawar da tayi ta 6angarori da dama, tsakanin mata da miji sai Allah tun tana shareshi harta saki jiki suka koma kamar farkon lokacin aurensu har abin yaso ta6a zuciyar Anty Amarya (mata baa raba su da kishi duk kyaun zuciyarsu) a haka yaranta suka fara sakewa da ita harma da yaran Anty Amarya duk ta jasu jiki wanda haka ya yi wa Jamilu da Anty Amarya dadi, kwata kwata bata nuna banbanci saboda kyatatawar da Anty Amarya tayi mata ba zata manta ba a lokacin da ita tayi watsi da yaran itace ta so mata yaran kamar ita ta haifesu, zaman lafiya zaman amana shine abin da Jamilu ya samu a cikin gidan shi kuma shima ya yi kokari gurin adalci da kyautatawa a tsakaninsu, a haka har suka 4years suka dawo sai lokacin Jawahir ta sake haihuwar namiji Anty Amarya itama ta samu namiji duk sukaci sunan iyayensu maza.

_________________________

Dambe shine ya zame musu rigar sawa, kullu yaumin sai sunyi basu damu ko yaran suna nan ko basa nan ba, har Nafi ta haifi yan tagwayenta babu abin da ya sauya zani a gidan, har an lakawa gidan Gidan Dambe saboda shaharar mutanen gidan a iya dambe ba kunya ba tsoron Allah har gaban sirikai, ita dai Nafi da Allah ya yi ta me hakuri sai ta kauda kai ta rinka abin da ya shafeta da wanda aka sakata ta bar wanda baa sakata ba, yaran Faruk da suka raina ta yanzu basu da lokacinta sai lokacin rabiyar fada idan suna gida karshe ma sukayi hannun riga da Antynsu saboda sun shiga 6angaren babansu sun daina shiga nata komai akayi suna bayan uban saboda ganin Anty Wasila tafi shi karfi a duk sanda aka dambanta shi ne yafi shan wahala. Da taga haka kuma sai ta hada da uban da yaran duk babu wanda ta bari kullun fada duka da cin mutunci kuma ranakun girkinta sai dai a kwana da yunwa dan girki iya cikinta takeyi, itama Nafi a wadannan ranakun bata dawowa gida da wuri sai yamma kuma tana zuwa take garkame dakinta bata sake fitowa sai taji fitan Faruk masallaci, dan ta rantse ba zatayi girki ranar aikin kishiyarta ba matukar kishiyar nada lafiya, haka kuwa Faruk da yaranshi ke wahala karshe sai dai su hadiyi bireda da shayi.

Abubuwa suna tafiya yanda aka saba ko kusa Nafi yanzu itama bata daukan cin kasa dan hakurinta ya kare, idan suka shiga shaaninta cin mutuncin su takeyi idan kuwa basu ta6ata ba ko iskan daya kwaso su bata kallo dan bata ga dalili ba itama ai matar gida ce aurora akayi ba sadakarta aka bashi ba, ganin itama wuyanta ya yi kauri kuma yana tsoron fara dambe da ita su mai dashi kayan jigba sai ya fita shaaninta sai dai idan masifar yakeji ita kuma ta gasa mishi mara dadi, Wasila kam matukar bata daki banza ba hankalinta baya kwanciya dan bata ga ribar aure ba, a haka tana zaune Nafisa ta kara haihuwar namiji aka saka mishi sunan uban Faruk sai kuma ta sake mace aka saka sunan marigayiya matarsa dan yan matan farko sunan mamanta da mamanshi ne, gashi har yanzu ita Wasila shuru kakeji ita kuma har ga Allah haihuwar take so dan ta kara samun matsuguni saboda tazo kenan babu yaji balle tafiyar abada, Nafi bata ragawa kowa ita dai ba zakuyi fada ko cacan baki ba kawai magana zata fada maka masu zafi da zaka kasa mai da martani saboda maganganun basu gama breakingdown a cikin kan ka ba balle ka bada amsa dai dai da zancen.

Yaran Faruk an wayi gari daya ta mutu saboda shaye shaye daya kuma tayi cikin shege wanda ya fusata Faruk har hawan jini ya kama shi hade da shanyewar 6ari daya na gangan jikinsa, sosai Falmata tayi kuka tayi bakinciki yayinda Anty Wasila abin ya mata mugun dadi, ko kad’an Nafi bata nuna musu komai ba haka tayi ta jinya karshe kaf kudinta ya kare a kansa dan ma tana wasu yan sanaar hannu yanzu, cikin ikon Allah sai da ya shekara kafin ya dawo dai dai duk kunyarta ya isheshi shi da Falmata data haihu yar tazo ba rai, saboda kulawar data basu ko cikin dangin an kasa samun me tsaya musu balle Wasila da dadin abin yasa har waka take sawa take taka rawa takeyi a tsakar gida, ai yana warkewa ya bata takardarta har saki uku sakin da babu dawowa sannan ya fara neman hanyar sulhu da Nafisa baiwar Allah, tun tana kaucewa harta hakura ta godewa Allah daya kar6i adduar ta, Falmata tayi aure itama ta auri dan yayan Mama Nafisa wacce Falmata ta rada mata Mama yanzu komai Mama sama Mama kasa kamar zata mata sujjada dan duk wanda suka san cewa tayi cikin shege an rasa me aurenta Nafisa ce tayi silar soyayya da aure tsakaninta da dan yayanta wanda suke zaman aminci duk da cewa uwarsa ta sata a gaba haka kannen miji basu raga mata ga zagi ga habaici duk kuma tana shanyewa kamar ba Falmata yar dan dambe Faruk ba kuma me taya ubanta dambe, sai da ta shekara uku a gidan ko wani cikin data samu sai kannenshi sunyi silar 6arewarsa wanda hakan yasa ta tuno da cikin Mama Nafisa da yayi ta 6arewa sanadinsu, har gida taje ta sake bata hakuri tare da neman yafiyarta kuma tace ta yafe mata duniya da lahira, dake Allah ba azzalumin sarki bane sai da tasha wahala sosai kafin ta samu farin ciki yanzu haka ta samu yarinya daya me sunan Nafisa. 

*ALHAMDULILLAH*

Abubuwa da yawa masu mahinmanci ne a cikin wannan littafi me albarka wanda duk ya dunkule a guri guda ko wani gida akwai son zuciya da rudin shaidan, duk abin da mutanen ciki suka shuka shi suka girba imma me kyau ko akasinsa, gidan Ahmad gida ne me cike da kalu bale wanda rayuwarsu a juye take kwata kwata babu tsari gashi kuma duk suna da sani a kan addini amma basuyi amfani dashi ba har sai da shaidan ya gama lalata komai sannan aka dawo ana dana sani wanda bai da wani amfani sam sam ba zasu ta6a goge wannan bakin fentin daya shafi rayuwar su ba domin idan wasu basu tanka ba wasu zasu tofa, gidan Hafiz kaikayi koma kan mashekiya duk dan saboda abin duniya mata ke fadawa halaka su take gaskiyar suyi son ransu ba tare da tunanin zasu iya mutuwa ma a wannan process din ba, Zaliha tayi wauta amma kuma da Allah ya tashi kama Hafiz seya kasance ashe matarsa ya cuta, dama ance idan zaka gina ramin mungunta ka gina yanda idan ya rufta da kai abin ze zo da sauki. Gidan Salmanu da uwar miji tasa Faiza a gaba sai kuma dake Allah ba azzalumin sarki bane sai abin ya koma kan yaranta wanda da zata shuka sharrin ina ga ta manta da wanzuwarsu, karshe ma gashi Allah ya dauki rayuwarta ta barsu a duniyar suna jin dadin rayuwarsu, gidan Nafisa duk sharrinsu a kansu ya kare tunda sunga sakayyar ubangiji tun a duniyar kowa ya dandani masu zafi, gidan Jawahir sakacinta ya kaita ga kusan rasa yaranta da mijinta baki daya, da Allah ya sota ma sai ya hadata da abokiyar zama ta gari wacce ta san abin da takeyi, mata da maza a yanzu akwai su da matsaloli iri iri na rashin godiyar ubangiji da son hada ubangiji da waninsa ma’ana SHIRKA sai dai ace Allah ya kyauta ya kuma rufa asiri…

ALLAH ya yafe mana kura kuren dake ciki ya kuma bamu ikon daukan darussan dake cikinsa…

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]