[Advertisements⬇️]

GIDAN AURE CHAPTER 4 ZAHRATEEY - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIDAN AURE CHAPTER 4 ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Gidan Ahmad*

+

Rayuwa yana tafiya kullun kwanan mu karewa yakeyi, yadda mutuwa ya tsalleka ya dauki wani haka wataran zai tsallake wani ya d’auke ka, yadda ya tsalleka naka ya dauki wanin wasu haka zai tsallake wanin wasu ya dauki naka. A yau mun tashi da rashin kannnen Ahmad su biyu a hatsarin mota da Umar da Aisha a hanyar zuwa clearance dinta a ABU Zaria, sai da yace ba zai rakata ba amma ta sashi a gaba, kasancewar suna shiri sosai shiyasa ya hakuri da rashin zuwan da baya so ya bita, ashe ajali ke kiransu gaba daya kafin su isa cikin Zaria sukayi hatsari.

Ina zaune a kan gado na gama hararwa kenan duk jikina a mace yake dan ina tunanin kar ciki ne dani, idan kuwa ciki ne na kade dagani har ganyena domin zai yi wuya ace ba cikin me gadina bane dan bana ma tunanin cewa na Ahmad ne saboda ya saba yimin amfani da maganin hana daukan ciki. Karar bude gate din gidan shine ya sa na tashi na leka ta window, ina dubawa naga motar Ahmah da sauran ma’aikatarsa, a take naji gabana ya fadi duk jikina ya fara rawa, har ya shigo dakina ina cikin tashin hankali ban lura ba, zuwa ya yi gaba na ya rungume ni ya saki wani kuka me ta6a zuciyar me sauraro, sosai naji hankali na ya tashi domin Ahmad namijin duniya ne baka gane karayarsa “me me me ya faru?…” Na fada ina janyo maganar daga bakina jikina sai rawa yakeyi.

Sai da ya yi kuka ya gaji sannan yace min in tashi mu wuce kano dan mu samu jana’izar Umar da Aisha, “Umar da Aisha?” Na fada ina mamakin su waye hakan, ni duk a rude nake ga ciki ga kukan da Ahmad ya yi ga kuma zancen wai zana’iza, ni sam tsaban rudewa na manta ma suna da Aisha da Umar a gidansu “wai wace Aisha da Umar kake nufi ne Ahmad?” Share hawayen shi ya yi sannan ya fada min cewa kannensa dai Aisha da Umar sunyi hatsari a hanyar Zaria, zaman dirsham nayi a kasa na hau kuka me hade da abubuwa da yawa, daker ya iya lallashina ya had’a mana akwati daya muka wuce airport.

Ko da muka isa gidan mun samu a cike da jama’a dama Hajiya ba dai mutane ba haka zalika Daddy duk masu son jama’a ne, da dangi da abokan arziki duk sun hallara, zama nayi kusa da Hajiya na fashe da kuka haka suka shiga rarrashina ita da Ahmad din daker nayi shuru sai kuma wani amai ya sake tasomin da gudu na shiga kewaye nayi ta hararwa sai da na zubar da duk wani abin da yake cikina.

STORY CONTINUES BELOW

_________________________

*Gidan Faruk*

A wannan daren amarcin dai anyi bala’i da amarya da ango domin bata zo da martabarta na diya mace ba, kuma sanin kansa ne bata ta6a aure ba hakan ya sa suka hau suka diro kowa na caccakar dan uwansa da munanan kalaman ita yar iska mara kamun kai shi kuma mashayi uban masu busa hayaki, Allah yaso yaran ba’a gidan suka kwana ba sun bi yan uwansu suka koma gidan kakanninsu da anyi abin kunya a gabansu.

Tana daki tana jinsu tayi gum kamar babu abin da taji yana faruwa, ta so taje tayi musu magana dan muryansu ya yi sama dayawa ta san tabbas wasu daga cikin makota suna iya jiyo su dan ma dai akwai karan inji a wasu gidaje, da abin ya isheta tayi tunanin fitowa taje tayi musu magana amma sai tayi wa kanta fada tayi zamanta kafin taje a 6arar da ita a kashe mata y’a ko d’a. Har zuwa washe gari basu bar hayaniya ba masu gulma yan unguwa kam sai da suka leko, daker suka rabu shima silar zuwan yan uwan amarya ne ya sa kawai ya fita a gidan cike da 6acin rai da bakin cikin auren sauran wasu gardawa.

Bayan wata biyu da auren nasu komai ya fara canjawa a gidan, Faruk ya rage zaman gidan saboda masifar Wasila yaran kuma sun koma makaranta suna bodin a Queen Amina inda suke aji hudu a sakandiri, sosai hakan ya yi wa Nafi dadi ko ba komai ba zasu samu daman sauraron munanan kalaman iyayensu ba, kuma tabbas da suna nan tashin hankalin sai yafi haka domin dole zasu goyi bayan daya ko ubansu ko kanwar uwarsu. Itama kuma ta samu saukin lamuranta masu yawan hadata da mijinta basa gida, ko da wasa bata ta6a shiga harkar amarya ba kowa sabgarsa yakeyi sai dai taji suna masifarsu amma nata ya yi sauki tunda munafukan gidan basa nan.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Yau ma ta dawo daga gurin aiki a gajiye Allah ya so ba ranar girkinta bane, tana shiga ta riske su a bakin rijiya suna dambe, tsoro yasa taja gefe ta tsaya tama rasa ya zatayi, ko wanne gaban shi da bokiti alamun ruwa suke son diba amma kowa ya hana dan uwansa, cikin sauri ta isa kofar 6angarenta ta bude ta shige tana haki kamar da ita ake damben, tana shiga ta rufe kofar har da key, sai ta koma window ta cigaba da lekensu a haka har aka buga Faruk da kasa saboda ya shawu ya bugu babu wani karfi sosai a jikin shi, sannan ta dauki gugan ta diba ruwanta ta shige bandaki, shi kuma ta barshi a yashe harta fito bai iya tashi ba dan neman bala’i ta sake dibo ruwa sannan ta zuba mishi a jiki ta shige nata 6angaren, sanyin ruwan daya ratsa jikin shi shine yasa ya tashi ba shiri ya hau sababi harda wuka a tsakar gida, ita dai Nafi tana window tana kallon ikon Allah.

_________________________

*Gidan Salmanu*

Washe gari da safe haka suka tashi sukuku babu wani karfi a tare dasu ga mutuwar jiki saboda zancen auren da Mama ta faro, suna cin abinci ta leko dakin “saboda nayi maka zancen aure shine ka kasa fitowa ka gaishe ni ko? Uwarka ta karya ta 6ata rai zuciyarta ya yi mata zafi shiyasa duk hankalinka ya tashi ka rasa sukuni, wallahi ka fita a idona ka kuma kiyayeni, matukar kana so mu rabu lafiya toh wallahi ka tabbatar kaje kaga Dada yau dinnan kafin ka shigo gidannan, kuma magana wannan mara dadi kayi mata ban yafe ba kaji dai na fada maka? Ja’iri mara son albarkan iyaye”.

Kan shi a kasa ya shiga bata hakuri amma taki kulashi bayan ta zage Faiza ta wuce abin ta tana ta banbamin bala’i, ture abincin ya yi daga gabanshi tsaban takaici kasa kallon Faiza ya yi kawai ya dauki wayarsa da hullansa ya fice, sai da ya isa gurin aiki ya natsu sannan ya tura mata sakon ban hakuri, ko da ta gani bata kula shi ba saboda duk ranta ya gama 6aci abu dame ciki ji takeyi kamar taje tayiwa Mama rashin kunya ko zataji sanyi a ranta.

Kamar yadda Mama ta umurce shi yaje ganin Dada hakan ne ya kasance, sai dai tunda ya ga yarinyar sai yaji ta kwanta mishi a rai saboda natsuwarta da kamun kanta, hiran nasu ba wani abin kirki bane ya mata sallama ya tafi cike da farin ciki shi da yazo a fusace, ko da ya koma gida ya sanar da Mama ya amince da auren amma Faiza kam be ce mata komai ba saboda hali irin na mata kawai ya share zancen tare da kokarin kwantar mata da hankali. Tsakanin mata da miji sai Allah a daren suka shirya kansu tare da adduar Allah yasa auren shine mafi alkairi.

_________________________

*Gidan Jamilu*

Har yau babu sauyi a cikin gidan shi, jiya wa yau komai yana nan yadda aka sani, hakurin shi dai ya fara karewa domin yanzu baya zama a gidan wani gida ya kama yake zaman shi kuma sannan yake ta fafutukan yin aure da wata kanwar abokinshi.

Damuwarsa ya samu macen da zata kula da shi da yaranshi, mace me tsafta da sanin darajan aurenta ba me hali irin na Jawahir ba domin irin su zama dasu sai mutum ya rinka kai zuciyarsa nesa kuma sai me hakuri sosai idan kuma hakurin ya kare za’ayi ba dadi ne. Bukatarsa yaransa su dawo kusa dashi ko zasu rinka ganin mahaifiyarsu dan ya san suna mugun son kasancewa da ita, sai dai ita lokacinta na yawon gidan biki ne da gidan suna, dan haka ne ma yasa ya fara gini ta wani 6angare a cikin gidan shi inda zai ajiye amaryarsa.

Ita kuma hankali kwance take gudanar da lamarin ta, rashin shi a gidan bai wani d’ad’ata da kasa ba ita hakan ma dadi ya mata saboda tana yin duk abin da take so a sanda take so ba tare da takura ba. Haka zalika ginin da aka fara a cikin gidan bai wani sha mata kai ba domin a tunaninta kawai zai kara musu daki ne din suji dadin watayawa. Yawo kam sai abin da ya yi gaba ga samari da masu aure duk sunyi mata caaa kowa son had’a guri yakeyi da ita saboda yadda take daukan wanka kamar ba matar aure ba.

_________________________

*Gidan Hafiz*

Yau ana tashin hankali a gidan Hafiz, matarsa ta haihu bakwaini dan ba rai shine ta kakabawa Zaliha wai itace silar hakan dan ta ga har zuwa yanzu ita babu cikin balle haihuwar, Firdausi kanwar Zaliha da tazo biki Kd shine ta biya gun yar uwarta ta taras da ta’asar da za’ayiwa uwarsu da Hafiz da matarsa da kanwar matarsa da kawar matarsa sun yi nashe nashe a jikin Zaliha sai narkarta sukeyi kamar kayan wanki. Cike da 6acin rai ta samu itace zabgegiya ta shiga narkar su sai da tayi musu dukan tsiya sannan ta sarara ta taimakawa yar uwarta suka shige daki.

“Dama ashe bakin ki da kinibibinki duk na banza ne bansani ba? Kina da hankali zaki tsaya gardi ya na narkar ki kamar baki da gata? Ba wai ma gardin gayen kawai ba har da wasu mata da basu wuce loman tuwo a gurin ki ba? Wallahi kin bani mamaki sosai kin mugun bakanta raina Zaliha, a kan me a wani dalili baki da baki ko baki da hannu ko wani makami da ba zai illata su ba kema ki kar6i yancinki, to wallahi da sake ko ki canja hali ki koma Zalihar dana sani wacce bata bari ta kwana ko kuma inje in sanar da Uwa ta zo ayi duk wanda za’ayi” ta fada tana huci (Uwa sunan da suke kiran mahaifiyarsu kenan) duk yadda jikinta yake ciwo bata kula ba tayi saurin mikewa “ki rufamin asiri Latifa kar ki sanar da Uwa wannan zancen kinji da Allah?” Harararta kawai tayi ta cigaba da banbamin balai.

A 6angarensu Hafiz kuwa duk dukan yazo musu a bazata, kasancewarta basamudiyar mace shiyasa taji dadin kir6ansu kamar kayan miya, matar Hafiz aka fi cuta saboina.danyen jego, duk suna nan a jefe kamar ledan pure water an rasa me taimakawa wani, shi kanshi Hafiz ta kanshi yake abu da marasa nama a jiki sai uban kashi shiyasa dukan ya kai musu ko ina.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]