[Advertisements⬇️]

GIDAN AURE CHAPTER 2 ZAHRATEEY - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIDAN AURE COMPLETE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sunana Mardiyya ni yar garin Kaduna ce mazaunan Lagos. A lokacin muna Lagos kafin mu dawo Kaduna da zama muna zaune ne a Getto Area, anguwa ne wanda ya tara yan iska da dama baga mazan ba baga matan ba. A lokacin kaf cikin anguwar babu gidan masu kudi sai gidan mu saboda muna da Generator sannan gidan mu nada feshin fenti wanda yake karawa gini kyau alhali kaf cikin unguwar babu irinsa. Ana mana lakabi da yan gayu ko kuma idan an gammu sai a rinka nuna mu ana cewa “iyakar gayu Annan” wato mun kure gayu iya gayu. Ni nice auta a gidan mu kuma karama a tsakanin yayyina, ina jss3 akayi bikin yayata wacce nake bi a lokacin shekaruna goma sha hudu, sai ya rage ni kadai ce a gidan.

Inada kawaye na hudu duk yan Kaduna kuma cikin ikon Allah sai duk mukayi aure a Kaduna, sai dai iyayena ne kawai suka koma Kaduna da zama nasu iyayen suna zaune a Lagos basu da alamun tashi su koma mahaifarsu.

Babban kawata wacce nafi kusanci da ita fiye da kowa itace Faiza, sai Nafi sai Jawahir sannan Zaliha. Faiza da Zaliha gidansu yana kallon gidan mu, sai Nafi gidansu na gefen gidan mu ta dama sai Jawahir ita kuma gidansu na gefen gidan mu ta hagu.

Dukan mu kawaye ne sosai makaranta ne kawai ya rabamu inda su suke makarantar gobnati ni kuma nake na private, islamiya kam tare muke zuwa mahaifina ke daukan dawainiyar mu, a haka har muka sauke alqurani me girma muka fara hadda. A lokacin Zaliha ta biyewa saurayi har ya mata ciki, kafinnan ma Mahaifiyarta tayi cikin shege da auren ta wanda hakan shine silar mutuwar auren ta, sai yayarta itama tayi cikin shege na uku inda sauran biyun suke 6arewa amma na ukun sai suka haifeshi tare da uwarta. Wato maman Zaliha kenan, a lokacin duk sai iyayen mu suka mana katanga da Zaliha muamalar mu da ita ba wani sosai bane ya mafi yawa a islamiya.

Bayan an gama da cikin shegen mamanta da yar uwarta sai kuma gata itama ta kunso nata, a lokacin duk mun gama sakandiri muna jiran sakamakon zuwa jamia. Bayan ta haihu sai iyayen saurayin suka musu aure saboda karamci irin nasu, kasancewar yana aiki a Kaduna sai suka tattara suka tafi, shekaru biyu tsakani akayi bikin Jawahir da Nafi suma duk aka kai su Kaduna, inda Jawahir ta auri dan abokin babanta ita kuma Nafi ta auri dan yayan babanta wanda matarsa ta rasu ta bar yara mata biyu. Kasancewar sun fara karatu a nan sai  babana ya nema musu transfer suka koma can da karatu, sai ya rage nida Faiza, mukam sai da muka gama jamia sannan mukayi aure inda Faiza ta auri wani dan makocinsu a Kaduna ni kuma na Auri wani Soja wanda muka hadu dashi a bikin yaye dalibai na makarantarmu.

STORY CONTINUES BELOW

A 6angaren Zaliha tunda sukayi aure zama yaki dadi a tsakanin su domin shi dama jikinta yake so ba ita ba, son shi dama ya lalatata sai ya yar da kwallon mangoro ya huta da kuda, sai dai reshe ya juye da mujiya domin sai ga shi ashe matarsa ce ya lalata, tunda ya aureta walakancin yau daban na gobe daban duk dai so yake tace bata son auren dan ya samu ya rabu da ita amma ita kuma taki bada kofar da hakan zai kasance tananan tana zaman hakuri da shi, a haka har ya kara aure ya auro wata yar garin Jos wacce ta badeshi da magani ciki da waje. Makwanci ne abinci ne komai dai da magani ake had’a mishi yanata aikin gabza be sani ba, cikin ikon Allah tunda tazo gidan take zazzaga y’ay’a Zaliha kuma ta koma yar aiki kuma yar kallo, bata da wani matsayi a gurin ne gida, ko wani shara a kanta yake juyewa musanman idan yar Gwal ta had’a mata wani bala’in, tana nan dai tana zaman hakuri tare da kula da yaronta wanda bashi da matsayi a gidan.

6angaren Jawahir kuma ko a lokacin muna gida daga mahaifina a kudi sai nata mahaifin domin shima akwai rufin asiri ba laifi, sai Allah ya hada ta da miji me kudi kuma me wadatar zuciya, amma ita kuma sai ta fito da banzan halinta wanda mukayi tunani ta dade da dainawa wato k’azanta. Sosai mijinta yake hakuri da ita amma sam bata gani, ban sani ba kila sai randa ya auro wata zata shiga hankalinta ta gane me duniya yake ciki. Yaran da Allah ya bata na duk hadesu tayi ta kaiwa uwarsa kiwo domin ita jikinta bana wahala babe wai, sai dai tayi wanka ta dauki gayu taje biki taje suna ta dawo ta hau kallo ta daura kafa daya kan daya tana canja tasha.

A 6angaren Nafi baiwar Allah gata uwar hakuri sai Allah ya jarabceta da mugun miji, sosai take shan wahala a gidan shi har ta kai ta kawo dalilin dukan da yake mata sau biyar tanayin 6arin cikin jikinta, ga kuma makirun y’ay’an miji da Allah ya hadata dasu, yanzu sai su gayawa uban karya da gaskiya ya hauta da duka ko fada ko kuma ya yi mata gorin haihuwa sai kace ba shine silar rashin haihuwar nata ba. Ga shaye shaye kamar dan ruwa kullun sai ya dawo mata gida a buge sannan ya shirga mata amai a ko ina yaga dama ya barta da aiki, dan ma dai ba kazama bace kullun gidanta na tashin kamshi.

6angaren Faiza kuma matsalar uwar miji shine yake addabarta, kwata kwata matarnan taki ta sake mata mara tayi fitsari duk tabi ta hana ruwa gudu babu damar ta samu ke6ewa da mijinta yanzu uwar zata fara kwala mishi kira saboda batason zaman su tare, bai isa ya sayo mata abu ya bata a fili ba sai dai a 6oye, idan kuma mahaifiyarsa ta kama shi to ranar kashinsu ya bushe domin ta dinga bala’i kenan, ga kuma rashin haihuwa daya kara janyo mata wani fitinan kullun sai ta sha zagi da gori a gurin matarnan sai kace ita zata bawa kanta haihuwar. Kullun tana cikin kuka da bakin ciki saboda damuwa da ya yi mata yawa dan ma tana samun natsuwa daga mijinta.

Nawa 6angaren kuma ina samun soyayyar uwar miji da danginsa amma na rasa nashi soyayyar, ni dai tsakanina dashi na san akwai soyayya amma fa kafin muyi aure dan kamar zai maidani ciki saboda soyayya, sai dai bayan anyi auren sai komai ya lalace, wata biyu bayan auren mu na gano ainihin waye shi, na farko ma yana min amfani da maganin hana daukan ciki, na biyu kuma da ya biya bukatar kansa shikenan an wuce gurin zai tashi ya barni bai damu dani din wani hali zan shiga ko kuma wani hali nake ciki ba, kansa kawai ya sani shi shi kadai, bayan wannan matsalar sai kuma idan ya tafi aiki sai baba ya gani abin dai kamar zuwa makka a kafa dan kafin ya dawo sai Allah ya kado kyeyarsa idan kuma yazo daya samu biyan bukata zai ware sai wani jikon, wani lokaci sai inyi watanni biyar shekara guda koma fiye da haka kafin in ganshi, sannan be damu daya kira yaji lafiyata ba, nice ma da nake kiranshi amma daga baya na ajiye zancen shi a gefe nima na manta da inada wani abu wai shi aure balle kuma miji. Wani zuwanshi ne ya samu me gadin mu ya samu matsala a kafa shine ya turashi gida yaje ya yi jinya daganan ya kawomin wani santalelen saurayi tun daga lokacin komai na rayuwa ya canja.

Haduwar mu yawanci a gurin aiki ne kasancewar dukan mu mun karanci Nursing ne, sai mahaifina ya sama mana aiki a guri daya. Wani lokaci kuma mukan ziyarci juna, sai dai duk cikinsu nafi son zuwa gidan Faiza ba laifi dana bawa uwar mijinta kudi shikenan har in tafi babu wani matsala, Nafi kuwa bana son zuwa dan wataran zan iya wa yaran mijinta shegen duka dan ni ba zan dauki iskanci ba, Jawahir zuwa gidanta ko kayan amai, ko ina wari karni indai ba mutun irinta ba duk wanda zaije gidanta zaiyi wuya ya fito baiyi hararwa ba, Zaliha kuma duk randa naje gidanta sai na janyo mata bala’i dan cin mutuncin kishiyarta nakeyi matukar tace zata ta6a ta a gabana. Ni ina zama a Kinkinau, Faiza unguwar Dosa, Jawahir a Rigasa, Nafi anguwar Sanusi sai Zaliha kuma Kawo.

Ko wacce na san matsalarta amma ni kadai ce basu san halin da nake ciki ba saboda zurfin ciki irin nawa, kuma bana fatan wataran su riskeni a wannan yanayin. Bama kamar Faiza da Nafi na san fushi zasuyi dani me tsanani. Gwara na Zaliha ta san bata da bakin magana Hajiya Jawahir kuma babu abin da ya dameta duk abin da kake so kayi ba damuwarta bane in dai kai kaji ya maka dai-dai.

Ban ta6a yiwa kaina tunanin fadawa irin wannan rayuwar ba, gaba dayan mu mahaddatan alkurani ne, mun dan dai dai munsan akasin hakan, munyi karatu me zurfi tun muna gida kuma duk wani laifi da muke aikatawa munsan hukuncinsa, nawa yafi na kowa muni saboda zina nakeyi da aurena, hukuncina kisa ta hanyar jifa shine abin da ya kamcen Gidan Salmanu*

+

Sauri takeyi ta gama had’a abincin sirikarta kafin ta fita, dan mijinta sai yamma yake yawan dawowa gida, ita kuma sai bayan azahar take dawowa, kullun kafin ta fita sai tayi wa sirikarta abincin rana. Duk kokarin da takeyi matar bata gani haka zatayi ta mita tana kwashe mata albarka, ita ba dan matsayin mijinta a zuciyarta ba da babu abin da zai saka tayi ta wahalar da kanta babu godiya sai zagi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tana gamawa ta zuba mata a kulan abinci ta kai mata dakinta, kafin ta koma kitchen din ta gyara sannan ta shirya ta fita. Tana ji Amma tana cewa “kullun sai gantali baki nan baki can wama ya sani ko yawon banza kike fita amma saboda shi Salmanu shanyayye ne baya ganin laifinki shiyasa ya kasa gano bakin zaren” bata ce uffan ba tayi ficewarta, idan da sabo ai ta saba meye abin damuwa a ciki tunda shi wanda ya ajiye ta a gidan ya yarda da ita ai shikenan an wuce gurin.

Napep ta dauka zuwa General Hospital a bakin gate ta hadu da Nafisa ita ma tana kokarin mika wa me Napep kudinsa, bayan ta bashi suka gaisa sannan suka shiga Napep din cikin asibiti, a GOPD suka sauka sannan suka yada zango a Nurses station, sai da suka shiga suka canja kaya sannan suka fito suka kama ayyukansu, Jawahir ma a gurin suka sameta yau ta riga su isowa Zaliha ce dai sai da sukayi kusan mintina talatin sannan ta karaso.

_________________________

*Gidan Ahmad*

Yau hutawa nakeyi ban fita gurin aiki ba, kuma babu me iya tukarata da maganar banza domin na riga nayi wa shugaba wankan kudi dan haka duk abin da nayi babu me magana, musaman ma yan uwan mu ma’aikata wanda na riga na basu kudi suma, masuyi kamar sunfi kowa sanin addini sune suke kin kar6a kuma suke mita a tsakaninsu dan babu damar yi a fili yanzu shugaba zata saita musu zama koma tayi silar barin su aiki tunda sune da wuta a bakin murhu suna da matsuguni suna da mutane a sama masu basu karfin gwiwa suyi abin da suka ga dama.

Wanka nayi na shiga kitchen na dafa taliyar yara gida biyu sannan na soya kwai uku na zuba a plate na fito falo, TV na kunna na chanja tasha zuwa Bollywood kafin na dora kafa daya kan daya na fara cin abincina cikin kwanciyar hankali. Inajin sanda ya bude kofa har ya shigo falon sannan ya dauki mintina yana kallo na kafin ya bude kitchen ya shiga, har na gama cin  abinci na be fito ba, a bakin kofar kitchen din mukayi karo yana fito wa ina kokarin shiga, abincin hannunsa ya 6are duk ya zube a gurin, “sorry” shine abin da na fada sannan nayi gaba, sai da na wanke plate dina da tukunya ta sannan na fito still a gurin na same shi duk ranshi a 6ace, ta gefen shi nabi zan wuce sai ya jawo ni na dawo baya “baki da hankali ne ke wace irin kidahuma ce kinyi abinci bani na shiga na dafa nawa kin 6arar min dashi sannan kinyi tafiyarki wa kike so ya kwashe miki? Yanzu yanzu ki kwashe kuma ki shiga ki dafamin wani abin kafin in 6allaki a gidan nan”.

STORY CONTINUES BELOW

Kallon tara saura kwata nayi mishi sannan naja tsaki ” aikin banza harara a duhu, a matsayinka na waye zaka bani umarni? Sai wani bubbude ido kakeyi kamar zakayi dambe, idan ka saba yi wa masu aikinka ni ba me aikinka bace da zaka sani a gaba, kuma wallahi ni da kai shege ka fasa zamu ga wanda zai fara zubda makaman yakinsa ya dawo hanya, a yadda ka za6a mana rayuwa a haka zamu cigaba idan ka sauya nima in sauya amma ni bana kallonka a matsayin miji na” na fada  tare da wuce wa abuna, wato ga jakarsa, ya dinga juyani yadda yake so abin sauke dora kamar ruwan kunu, mu zuba mu gani wallahi idan bai dawo namijin gaske ba yana ruwa dan ni bani da asara.

_________________________

*Gidan Jamilu*

Kamar kullun dai yau ma ya samu gidan a wargaje kamar motar da ya yi hatsari, ajiye kayan hannun sa ya yi sannan ya nade hannun riga ya hau aiki baji ba gani, ba shi ya gama ba sai da aka kira sallar magriba, wanka ya yi sannan ya fito da take away din da ya yi na shinkafa da miya ya hau ci kamar mayunwacin zaki, sai da ya gama tas sannan ya yi sallan magriba ya samu guri ya zauna dan hutawa.

Fitowa tayi daga daki taci kwalliya sai tashin kamshi takeyi, sosai gidan ya yi mata kyau “sannu da aiki Jamilu ashe har ka dawo? Da yanzu zan kiraka ince maka zan fita dinner din bikin kanwar mijin Ummu Suhail makociyar ku, ashe ma ka dawo” ta fada tana saka dan kunne tare da gyara zaman gyalenta, ko uffan bai ce mata ba kawai ya cigaba da kallon tashar wa’azin daya sa, ganin haka yasa itama tayi ficewarta.

Bata dawo gida ba sai kusan karfe sha biyun dare wai sai da aka kai amarya da ita da aka fara watsewa shine itama ta dawo gida, wasu da sukayi tunanin ita ba matar aure bace har da neman izinin soyayya da ita, abin ya yi mata dadi sosai ganin dai har yanzu ba’ayi mata kallon wacce ta haifi yara har biyu, daya daga cikin wanda ya nuna yana sonta shine ya kawo ta gida sai da suka iso sannan ta nuna mishi gidanta a matsayin ita fa matar aure ne, sosai mutumin ya sha mamaki dake na Allah ne sai ya mata fatan shiriya.

A falo ta same shi ya na ta safa da marwa sai kallon agogo yakeyi ya na leka window minti minti, har ta shigo bai lura ba saboda damuwar da yake ciki na rashin dawowarta, sai da tayi mishi magana sannan ya yi ajiyar zuciya tare da yi mata fada akan kaiwa har irin wannan lokacin a waje da sunan zuwa dinner a matsayinta na matar aure, ko yan mata ne bai dace su kai ya warhaka a waje ba balle ita, jinsa kawai takeyi ya na shiga ya na fita ta dayan kunnen bayan ya gama tayi wucewarta ko wanka bata samu tayi ba saboda gajiya tabi lafiyar gado.

________________________

*Gidan Faruk*

Cikin sanyin jiki ta shiga gidanta duk hankalinta a tashe saboda tsoro barin ma data ga babur dinsa a waje kenan yau ya dawo da wuri ita kuma ta wuce k’aidar dawowa gida, da sallama ta shiga falon nasu inda ta same shi a zaune yana kurban giya hankali kwance, yaransa kuma suna gefe suna ta hiransu tare da kwalin sigari suma suna zuqa ganin duk hankalinsu baya kanta yasa cikin sand’a ta fara tafiya zata shige daki “Old Man ga munafukar matarka ta dawo daga yawon gantali zata shige daki babu neman izini” Ainau ta fada tana harare harare tare da zukar sigarinta. “Kai Old Man ya dace ka saki matar nan haka fa domin ni na fara tantaman cikin dake jikinta naka ne kona waninka” Rasho ta fada itama tana busa mata sigari a fuska.

Tashi ya yi cikin halin maye kamar zai kife sai hagu da dama yakeyi ya rasa guri guda da zai tsaya ya fuskance ta, batayi aune ba taji saukar mari a fuskarta kafin ta farga ya sake zuba mata wani wanda ya gigitata har sai da ta zauna dabas a k’asa, duk da cewa marin ya shigeta sosai amma zafinsa a zuciyar ta bai kai shegen ta mata d’a ko y’a da yaranshi sukayi ba, kuka ta fashe da shi zuciyar ta na zugi duk ta rasa meya dace tayi musu daga shi har yaransa, kuka takeyi tsakaninta da Allah dan maganar ya yi mata zafi sosai, ball ya yi da ita har sai da ta buge kanta a jikin bango tunkarato ya soma yi ya na karayin ball din da ita wannan karan har sai da ta buge cikinta tayi wani kara daya sa duk sukayi kanta suna tunanin ko ya mata mugun illan daya saba, ganin ba wani abu bane sai suka ja tsaki tare da kara hura mata hayaki a fuska sannan suka wuce dakinsu shi kuma ya zare belt ya mata dukan tsiya a haka tayi ta kare cikin ta harya gaji ya barta taci kuka ta koshi ga shi duk jikinta ba karfi.

Washe gari da safe ya tsareta akan sai ta gaya mishi gurin wasu gardawan taje ko kuma ina ta tsaya bata dawo gida ba har sai bayan awa biyar da tashinta daga gurin aiki? Cikin kuka ta sanar dashi cewa dama tun cikin wancan satin takejin zazza6i sai dai batayi kokarin shan magani ba dan idan ta sha zai kwantar da ita, shine jiya bayan tayi aiki ta gaji jiri ya kwashe ta sai da aka kara mata ruwa da alluran barci bata tashi ba sai kusan magriba kuma kafin ta samu abin hawa sai da ya d’au lokaci sannan akwai hold up a hanya shiyasa basu iso da wuri ba. Ba dan ya yarda ba ya kyaleta kawai acewarsa rana tara na 6arawo rana daya na meshi, idan wani abin take aikatawa da sannu zai gane wata rana.

_________________________

*Gidan Hafiz*

“Abin kunya dai baya karewa a duniya uwa ta haifi yar gaba da fatiya y’a ta haifi d’an gaba da fatiya sannan dayar y’ar itama ta haifi d’an gaba da fatiya, ikon Allah kenan ko da yake ai su abin kunya gaba suka ba shi ba baya ba” Zaliha tana jinta suna hira ita da kawarta kuma tabbas ta san da ita takeyi amma bazata kulata ba saboda kulata tamkar ta6a igiyar aurenta ne domin tana sane da cewa Hafiz zai iya sakinta saboda matarsa.

Kunun da tayi mata ta kwashe ta zuba a flask sannan ta dauki kofuna biyu ta had’a ta kai mata, fitowarta taji tana kwala mata kira cikin sauri ta koma dan jin kuma yau dame ta sake zuwa, “ke yar iskan inane wai? Ina ce kunun tsamiya nace kiyimin saboda inji dadin bakina shine zakiyimin kunun kanwa salon ya lalatamin cikin jikina, dama ina sane da cewa bakin ciki kikeyi da y’ay’ana wanda suke yan sunna, to ahir dinki wallahi wahainiyarki ta kiyayi ramata, aikin banza babu abin da uwar ki ta koya miki sai yawon ta zubar” saurin d’auke flask din tayi ta fice dan zuciyarta na gab da bugawa saboda kalaman da kishiyarta take jifanta dashi duk da cewa aikin gama ya riga daya gama babu damar mai da hannun agogo baya sai dai ayita neman yafiyar ubangiji amma tabon ba abune me gogewa ba, sosai taci kuka ta gode Allah sannan ta shiga kitchen din ta sake mata wani kunun tana gamawa ta bawa yaronta ya kai mata dan ba zata koma ta sake jin wasu abubuwan da zasu sa ta tanka ba karshe ya samu damar tsinka igiyar aurenta.

_________________________

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]