[Advertisements⬇️]

AMRAH NAKESO CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMRAH NAKESO CHAPTER 2

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sai dare sannan mahaifinta ya dawo, a gajiye lis yake, wanda kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da baya tattare da walwala.

Duk da cikin halin da nake, na tausayin ciwon Amrah, bai hana ni tashi na tarbe sa ba.

“Sannu da dawowa Mallam. Zauna ka huta kafin na kawo maka abinci.” Na fad’a ina mai k’ara dubar yanayinsa.

“To Murja.” Ya fad’a jiki a sab’ule.

Kitchen na nufa na zubo masa dafadukar shinkafa da na ajje masa, na d’ibo ruwa daga tulu na kawo masa.

Sai da ya ci ya yi nat, na tabbatar ya samu natsuwa sannan na ce,

“Allah dai Ya sa an yi nasara.”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce,

“Babu nasara Murja. Abin dai sai hamdala kawai.” Ya kalle ni ya gyad’a kai, sannan ya ci gaba da fad’in,

“Duk yinin nan guda da muka sha, wai Alhajin ya fasa zuwa. Har fa lokacin da na ga magrib ta yi na ce ni dai zan tafi, wasu suka ce in dai k’ara ha’kuri, an tabbatar cewa yana gari wai zai zo. ‘Yar d’ari biyun da nake da ita, da ita na ci abinci da rana, naira ta hamsin d’aka da waje yanzu haka. Ban san ya zan yi ba Murja. Talauci babbar cuta ce, wacce samun maganinta yake da matuk’ar wahala.” Ya dafe kansa.

Cike da tausayi na ce,

“Sai hak’uri Mallam. Ta ko wace hanya Allah Yana jarrabtar bayinSa. Hakan kuma ba wai yana nunar da baYa sonmu ko kuma Ya manta da mu ba ne, a’a, na tabbatar cewa mun fi wasu, tun da mu da wuya mu rasa abin da zamu ci. Wasu kuwa babu, abin da zasu saka ma cikinsu ma wata wahala ne. Fatana dai kawai Allah Ya bamu ikon cinye wannan jarabawar.”

“Ameen. Wai duk jiran nan da muka yi, sai bayan isha’in nan wani d’an korensa ya zo yana fad’in mu tafi, wai Alhaji ba zai samu zuwa ba, sai kuma wani lokacin. Dama kyauta ce ya yi niyya ba rok’arsa aka yi ba, kuma wani uzuri ya sha gabansa.”

“Shi ke nan ai Mallam. Ka cire damuwa daga ranka. Allah Yana tare da mu…” tun ban rufe baki ba Amrah ta fasa kuka tare da tashi zaune, saboda dama tun d’azu ta yi bacci.

Da sauri na kama ta na d’ora a bisa cinya, ina rirrigarta a hankali had’e da tofa mata addu’o’i, dan a tunanina ko firgita ta yi ne. Abin mamaki sai d’ago min hannunta ta yi, cikin maganarta da bata gwanance ba ta ce,

“Umma hannu ciwo..” ta kuma fashewa da wani kukan.

Gyad’a kai na yi cike da tausayi, na kama hannun nata a hankali ina mammatsawa ina tofa mata addu’a har na samu ta yi shiru.

Bayan kamar mintuna biyar ta ce,

“Umma ya daina ciwon.” Ta sakar min murmushi.

“To ki gode wa Allah kin ji ‘ya ta? Allah Ya baki lafiya da duk kan ‘yan uwa musulmai.” Na fad’a ni ma ina mata murmushin.

Bakinta dama ya dad’e da sabawa da furta amin, hakan ya sa ta ce,

“Ameen Umma.” Ta sauka daga jikina da sauri ta nufi mahaifinta, saboda sai a lokacin ma ta kula da shi.

Saurin kawar da damuwarsa ya yi ya d’auke ta,

“Amrah ‘yata sannu kin ji? Insha Allahu zaki samu lafiya ke ma kamar kowa.”

STORY CONTINUES BELOW

Bata ce komai ba sai lafewa da ta yi a jikinsa, take bacci ya d’auke ta.

Tabbatarwar da muka yi ta yi bacci ya sa a hankali ya nufi uwar d’aka da ita, ya kwantar sannan ya nufi yin sallah.

Bayan ya gama a lokacin nima na shigo d’akin har ma na kwanta a kusa da Amrah, ya hau gadon zai kwanta na yi saurin mik’ewa na ce,

“Ka gaji ko? Da alama kwanciya kake son ka yi. Gashi kuma ina son da mu yi wata magana.”

Bayan ya hau gadon ya ce,

“Babu komai Murja. Ina saurarenki.”

Saurin share k’wallata na yi sannan na ce,

“Dama gani na yi ya kamata mu kai yarinyar nan asibiti, sam bamu kyauta ba zaman da muke yi haka da ita, ba tare da sanin halin da take ciki ba. Mallam ban tab’a jin yaro mai irin lalurin Amrah ba, rayuwata tana matuk’ar dugunzuma a duk lokacin da ciwon yarinyar nan ya taso, tana matuk’ar bani tausayi. Tun bata san miye ciwo ba har ta kai ga ta sani yanzu. Yarinya ‘yar shekara biyu da watanni amma har ta san ciwukanta.”

Cike da tausayi Mallam ya ce,

“Haka ne Murja. Ni ma kaina na jima ina wannan tunanin, ina jin tausayinta sosai musamman yanda har cikin dare ba wani baccin kirki take samu ba. Ya kamata mu je asibiti, idan ma wani ciwon ne sai mu sani, mu bi dokokinsa ko ta samu sassauci.”

Cikin kuka na ce,

“Haka ne Mallam.”

Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce,

“Gashi kuma bani da kud’i Murja. Ban ajje ba ban ba wani ajiya ba. Na abin hawa ma kanshi babu bare kuma na sauran hidindimun asibiti. Wayyo ni Abdallah!” Sai ga hawaye suna zarya a bisa kumcinsa.

Duk da ni ma ina jin hawayen amma a haka na daure, shi ya koma macen ni kuma na koma namiji, na ci gaba da rarrasarsa har na samu ya yi shiru.

“Akwai ‘yan samiruna da tasoshi tun na aure, suna wancan d’akin na ajiya tun-tuni. Insha Allahu da sassafe zan je gidan Rakiya Dillaliya, wata k’ila zata siya. Ko nawa ne ma dai ta bamu mu samu a kai ta asibitin. Ai ya fi mu je maula ana wulak’anta mu.”

“To shi ke nan Murja. Allah Ya kai mu goben Ya sa a yi nasara.” Ya furta a hankali.

“Ameen Mallam. Ka kwantar da hankalinka, Allah’n da Ya d’aura mata wannan cutar shi zai warkar da ita, insha Allahu zata warke, ta murmure kamar sauran yara.”

Murmushi ya yi sannan ya ce,

“Ina fatan haka Murja. Na gode k’warai Allah Ya miki al-barka.”

Da murmushi ni ma na ce,

“Ameen Mallam.”

Daga haka bacci ya d’auke mu.

***

Washe gari kuwa tun da sassafe na fiddo ‘yan tarkacen da zan siyar, sun yi k’ura sosai saboda sun kai kusan shekaru biyar a ajiye cikin d’akin ban fitar ba. Bashin omo na ci na wanke su tas, har shek’i suke yi sannan na kife suka bushe.

Buhu na nema mai tsafta na saka a ciki, sannan na nufi gidan Rakiya Dillaliya.

Da yake Allah ya duba zuciyarmu, kyakkyawar niyya ce a ciki, babu ko b’ata lokaci Rakiya ta siyi kwanonin, cas ta cake min naira dubu takwas da d’ari biyar.

Na matuk’ar jin-d’adi, da murna na nufo gida, zuciyata sayau, tamkar an ce min Amrah ta warke ne.

Sai da na fara biyawa na biya ku’din omo, sannan na siyo mana bredi da sauran kayan shayi, sai da dai na kaso dubu d’aya sannan na iso gida.

Ko da Mallam ya ga fuskata ya san akwai nasara, ga uwa uba leda a hannuna cike da karikitai.

“Mallam ta siya har dubu takwas da d’ari biyar.” Na fad’a masa ina dariya.

Shi ma dariyar ya yi ya ce,

“Ahh lallai abu ya yi kyau. Ta kyauta sosai wallahi.”

Halawartsinke na fiddo daga cikin ledar na mik’a wa Amrah, da sauri kuwa ta karb’a tana dariyar jin dad’i.

Kitchen na je na dafa mana ruwan zafi, na zuzzuba mana sannan na zuba kayan ha’di.

K’arfe goma da rabi muka gama, na ma Amrah wanka muka shirya sannan muka fito, Mallam ya rufe gidan muka nufi bakin titi.

Bamu jima ba muka samu keke napep, asibiti muka ce ya kai mu, ya tambaya,

“Mallam wace asibitin zan kai ku?”

Shiru muka yi mu duka dan bamu san inda zamu je ba, hakan ya sa ya sake maimaita mana.

“Wace asibiti ce ka sani wacce ake kula da k’ananan yara sosai?” Mallam ya tambayi matashin.

Shiru ya yi jim kad’an sannan ya ce,

“Ku je asibitin Turai, dama ta yara da masu ciki ce kawai ai.” Ya fad’a yana kallon Mallam.

“In haka ne, ai ga Turai d’in can ma babu nisa sosai ko? A nawa zaka kai mu?”

“Ku kawo d’ari da hamsin.” Ya fad’a.

Shiga ciki muka yi ya kai mu har cikin asibitin, dama kuwa babu nisa daga gidanmu, duk cikin unguwa d’aya ne sai dai kuma dole mutum ya hau abin hawa, idan ba haka ba kuma akwai gajiya.

Bayan mun shiga reception, muka tambaya abin da ya kamata mu yi, wata mata ta ce sai mun sai mata kati kafin komai.

Mallam ya je da kanshi ya sai mata katin aka cike, sannan aka d’ora a layin ganin paediatrician (likitan yara.)

Har bayan azahar layi bai zo kanmu ba, kusan k”arfe biyu aka kira sunanta.

Likita ce mace, sanye da lab court da medical glasses.

Kujerar dake fuskantarta ta bani izinin zama, bayan na zauna na gaishe ta da sakin fuska ta amsa.

“Me yake damunta ne?” Ta tambaye ni tare da mik’o hannu ta karb’i Amrah.

“Dr. Tak’amai-mai ban san me yake damunta ba, saboda wannan ne karo na farko da na kawo ta asibiti. Kawai dai na san ta jima tana fama da k’ai-k’ayin tafin k’afa da hannu, daga baya kuma sai abun ya canza, ta koma ciwon k’asusuwa, da zarar ta fara zazzab’i sai ko wace gab’a tata ta ringa mata ciwo, yanzu ko babu zazzab’in ma ciwo suke mata.”

Zare glasses d’inta ta yi ta ajiye daga gefe sannan ta hau dudduba Amrah, ta cire mata kaya.

Tana cikin dubawar ba tare da ta d’ago kanta ba ta ce,

“Me nene genotype d’in ki? (Sinadarin jini)”Cikin mamaki na kalle ta, ina k’ok’arin tuna a inda ma na san kalmar, saboda na yi boko bakin gwargwado, sai dai ban yi zurfi sosai a ciki ba, daga JS 3 na tsaya ban samu damar ci gaba ba. Mahaifinta kuma ya gama secondary ne bai wuce ta gaba ba.

“Me nene genotype d’in ki?” Ta sake tambaya ta bayan ta d’ago kanta ta kalle ni.

“Dr. Ban gane nufinki ba.” Na fad’a idona a cikin nata.

“Sinadarin jini nake nufi. Wane iri gare ki?” Ta mayar da glasses d’inta.

“Uhm…ni ma ban sani ba Dr. Kamar dai zan iya tunawa, sanda zamu zana jarabawar aji uku an auna mana jini, blood O gare ni.” Na fad’a ina tunani. “Tabbas ma kuwa O ne, O negative in ban manta ba.”

Gyad’a kai likitar ta yi ta ce,

“Ba shi nake nufi ba Maman Amrah, wannan ai type ne na jini (blood group), genotype nake nufi. An tab’a yi miki awo?”

Sai a lokacin na gane manufarta. Na ce,

“Gaskiya ba’a tab’a yi min ba Dr.”

“Subhanallahi!” Ta furta had’e da dafe kanta. “Ina mahaifinta yake?”

“Yana waje ne, bari in kira sa.” Na mi’ke tsaye.

“Ku hanzarta please, daga ku ma na tashi aiki wani zai karb’e ni.” Ta fad’a tana mai ci gaba da dudduba Amrah.

Babu jimawa muka shigo ni da Mallam. Da sallama na ce,

“Dr. Ga Mahaifin nata nan.”

D’ayar kujera ta sa na jawo sannan muka zauna, mik’o min Amrah ta yi na karb’a ta ce,

“Mallam menene genotype d’in ka?”

“Tab! Na dai san ko menene genotype saboda na karance sa a Biology shekaru da dama da suka gabata. Sai dai kuma babu abin da zan iya tunawa game da shi Dr. Ban wani tab’a yin gwajinsa ba. Lafiya dai ko?”

Jinjina kai ta yi ta ce,

“Gaskiya dole ku yo wannan gwajin, sai kun yi shi sannan zan sake duba ta. Ita ma yarinyar a yi mata, gobe sai ku dawo.” Ta rubuta mana awon a wata takarda ta bani. “Ku gwada wannan takardar. Dan Allah ku tabbatar kun yi shi daga nan zuwa gobe.”

Mik’ewa muka yi sannan muka mata godiya muka fita.

Bamu bar asibitin ba sai da muka binciki inda ake awon genotype, duka d’ari biyar aka caje mu mu duka ukun, aka ce sai zuwa gobe mu karb’i sakamako.

A sa’bule muka nufi bakin asibitin, muna isa kuwa muka samu keke napep ta kawo wasu, babu b’ata lokaci ya d’auke mu sai gida.

Bayan mun isa, a k’ofar gida muka tarar da Annur zaune ya yi tagumi, ya k’urawa k’ofar gidan ido.

Sauka muka yi daga napep d’in muka sallame shi, sannan muka iso k’ofar gidan.

Da sauri Annur ya mik’e, take bak’in cikin da ke bisa fuskarsa ya kau, ya karb’i Amrah daga hannuna.

Murmushi na sakar masa na ce,

“Annur lafiya dai ko?”

Mallam ya yi saurin fad’in,

“Yo sai ma kin tambaya? Bai ga ‘yar lelen tasa ba ne yau.” Ya ci gaba da zura makulli a cikin kwad’o yana k’ok’arin bud’e k’ofar.

“Haka fa. Ai Annur ba nisa sosai muka yi ba. Mun je asibiti ne.” Na fad’a ina masa murmushi had’e da shiga cikin gidan yana biye da mu.

STORY CONTINUES BELOW

“Ai Umma da har hankalina ya tashi, na zata ko wani wurin mai nisa kuka tafi babu ko bankwana.”

“Ko kad’an Annur. Iyakacinmu asibitin Turai.” Mallam ya fad’a.

Bayan ya sauke Amrah tsaye ya ce,

“Waye ne ba lafiya? Ko jikin Amran ne ya motsa?”

D’aga masa kai na yi sannan na ce,

“Amma kar ka damu, ta ji sau’ki sosai. An saka mu awon genotype ne, sai gobe zamu karb’i sakamakon mu kai ma likita.”

Dafe kansa ya yi, cikin lokaci kad’an yanayinsa ya sauya, idonshi ya yi jajur kamar wanda zai yi kuka, yana son yin magana amma lab’b’anshi sai k’yarma suke kamar ba zai iya ba.

Ganin haka ya sa na ‘kirk’iro murmushi na ce,

“Annur miye ne haka wai? Babu wata matsala mai girma fa. Idan ma akwai, wayo da dabararmu ai ba zasu tab’a magance mana komai ba, addu’a kawai zamu rik’a, domin ita ce makamin mumini. Insha Allahu zata samu lafiya.”

Da k’yar ya iya furta,

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Umma ina matuk’ar tausayin Amrah, bana so wani abu ya same ta. Jikina yana bani in har wata babbar matsala ce tattare da ita, to tabbas ni ma zan iya kamuwa da wata cutar. Ummah wallahi tausayinta nake ji…” sai a wannan lokacin hawayen da yake b’oyo suka samu nasarar fitowa.

Ita kuwa Amrah kallonsa kawai take, ta dai san tabbas ba lafiya ba, ganin babban abokinta yana kuka…”

Maryama ce ta yi saurin dakatar da Ummah da fad’in,

“Kar dai na katse ki Ummah, baki fad’a min shi Annur d’in ko waye shi ba.”

Jinjina kai ta yi ta ce,

“Haka ne Maryama.

Annur Ikra Hussain shi ne asalin sunanshi.

Mahaifin Annur babban mai kud’i ne, saboda a duk fad’in unguwarmu babu gida mai girman nasu, babanshi ya fi kowa kud’i, saboda tsohon pharmacist ne wanda ya jima da yin retire, yana da share a wasu daga cikin magungunan da ake yi, ciki kuwa har da kamfanin dana.

Annur shi ne d’a na biyar a gidansu, duka yayyenshi mata ne, sai shi d’in ne kawai namiji, sai kuma k’anwarsa mai bi masa, auta ke nan.

Yaro ne d’an kimanin shekaru sha uku a lokacin. Annur na da tarbiyya sosai, yana da son mutane, haka kuma akwai shi da girmama na gaba da shi.

Mun had’u da shi ne tun wata rana a k’ofar gidansu, ni kuma mun je cike wani form na tallafawa mata, wanda mahaifiyarsa take kula da shi, kasantuwarta ma’aikaciyar gwamnati ce ta b’angaren state government.

A lokacin Amrah na da wata biyar a duniya, shi kuma bai fi shekara goma sha d’aya ba. Tana ta tsala min kuka alamun ta gaji, shi kuma ya fito a inda muke jere a layi ya ji kukanta.

Da sauri ya iso inda nake, ya kalle ni ya ce,

“Me kika mata take kuka?” Har da nuna alamun shi ya ji haushi sosai.

Murmushi na masa na ce,

“Babu abin da na mata, rigima ce kawai. Ina ji ta gaji ne.”

“To ki mata yanda take so ko kuma na kai k’ararki wurin Babana, in fad’a masa kina ba ‘yar yarinya wahala.”

Sosai ya bani mamaki, na d’aga kai na kalleshi, har a lokacin bai daina kallon Amrah ba. Na ce,

“To ko zaka karb’e ta ka taya ni rarrashinta ne?”

“Ehh kawo ta.”

Na kuwa mik’a masa ita.

Duk irin kukan da yarinyar nan ke tsalawa, Annur na kar’barta ya ringa rirrigata ta yi shiru, k’arshe ma sanda ya dawo min da ita sai wangale baki take, kamar ba ita ce ta gama kuka ba.

“Gata nan ta yi shiru. Ya sunanta wai?” Ya tambaye ni bayan ya mik’o min ita.

“Sunanta Amrah.” Na bashi amsa.

“Ta burge ni. Ina ne gidanku? Zan ringa zuwa ina d’aukarta kullum idan tana kuka.”

“Gidan namu akwai ‘yar tafiya yaro, ta can k’asa ne.” Na gwada masa layin namu.

“Sunana fa Annur ba yaro ba. Zan jiraki idan kin tashi tafiya sai mu tafi tare. Ina son Amrah, kaman ki bani ita ta dawo gidanmu.” Ya kama latsa mata kumatu sai wangale baki take.

Wannan shi ne silar had’uwarmu da Annur, tun daga wannan lokacin ya d’auki Amrah ya saka ta a ranshi, duk sanda bata lafiya haka zai wuni a gidan nan, idan tana kuka kuwa shi ma kukan zai yi, har sai sanda ta daina.

Amrah ta matuk’ar sabawa da Annur, kamar yanda shi ma ya saba da ita sosai.

Baya shigowa gidan nan ba tare da ya kawo mata wani abu ba, ta dalilin Annur har mahaifiyarsa ta zo nan gidan, ta kawo ma Amrah abun duniya iri iri, wai saboda yanda d’anta d’aya tal namiji ya nuna k’aunarsa ga yarinyar.

Tarihin Annur Ikra Hussain ke nan. Bari mu koma mu ci gaba daga inda muka tsaya.”

Gyara zama Maryama ta sake yi tana mai sauraron Umma…Umma ta ci gaba,

“Ganin halin da Annur yake ciki, ya sa na ce,

“Annur akwai Islamiyya fa yau, ka tashi ka tafi kar ka makara. Kuma ka share hawayen nan bana so ka tafi gida da shi.”

“Umma yau ba zan je Islamiyya ba, ko kin manta ke kika ce min daga asibiti kuke? Zan zauna har sai na tabbatar Amrah bata da wata damuwa daga nan zuwa dare, sannan zan tafi.” Ya sake gyara zamansa.

Mallam ya ce,

“Ba za a yi haka ba Annur, gidanku ba zasu ji dad’i ka zauna a nan baka je makaranta ba. Mu ma kuma ba zamu so ta dalilinmu kana fashin makaranta ba. Ka tashi ka tafi ka ji? Gobe sai ka dawo ka duba ta, ka ga a lokacin ma an bata magani ta ji sauk’i ke nan.” Ya sakar masa murmushi.

Shi ma murmushin ya yi ya ce,

“Kuma fa haka ne Abba. Bara in tafi to. Amrah..” ya kama mata hannu. “…zan tafi makaranta, zan fad’a wa Malaminmu a saka ki a addu’a, Allah Ya baki lafiya ko?”

Murmushi kawai Amrah ta masa, ta ce,

“Ameen.”

Ta san dai idan an ambaci addu’a to amin ake cewa, ita ma shi yasa ta ce haka.

Sakar mata hannu ya yi, ya ce,

“To sai Allah ya kai mu.”

“Allah Ya kai mu, Annur. Ka gaishe da Momy’nka.” Na ce da shi.

“Zata ji.” Kawai ya fad’a tare da barin gidan.

Na juyo ga Mallam na ce,

“Wato k’aunar da yaron can yake ma Amrah, abin har mamaki yake bani. Yaron da bai yi ko shekara sha hud’u ba, amma ya ta’allak’a rayuwarsa ga Amrah, ya sadaukar da baki d’aya lokacinsa ga Amrah.”

Mallam ya jinjina kai ya ce,

“Ai k’aunar da Annur yake ma Amrah, a jininsa take. Ki tuna ranar da Amrah ke ta kukan nan bata da lafiya, sai gashi fa da gudu ya zo, wai jikinsa ne ya bashi cewa Amrah na kuka bata da lafiya, kuma sai gashi hakan ne. Haka zai zauna ya rizgi kukansa idan bata da lafiya, sai idan ta yi shiru ko shi ma zamu samu ya yi shiru. Haka ita ma yarinyar, duk iya rigimar da take sai idan bai d’auke ta ba, tun ma kafin ta kai haka. Da zarar ya d’auke ta sai ta yi shiru.

Ni tsorona d’aya ma, yanda iyayensa suke da kud’i, kar wata rana su wula’kanta mu saboda d’ansu, musamman yanda shi kad’ai gare su namiji, suna so su inganta rayuwarsa, amma wasu lokutan sai ya k’ek’ashe ya k’i tafiya makaranta saboda Amrah. Ina matu’kar tsoron ranar da abin zai cika su, zasu iya yin komai fa saboda Annur.”

Ajiyar zuciya na sauke, na ce,

“Haka ne Mallam. Amma kuma fa son yaron nan da suke shi zai sa su masa duk abin da yake so. Ka tuna ranar da ya kawo Mamansa ta zo har nan ta duba Amrah? Alamun suna bayan buk’atarsa fa ke nan.”

“Allah dai Ya mana jagora.” Kawai Mallam ya fad’a. “Da kin nufi d’ora abinci ai ko dan yarinyar nan, kafin ta nema.”

“Yanzu kuwa. Ai da yake mun yo cefane, d’orawa kawai zan yi.” Na tashi na nufi d’ora girkin rana, a lokacin har la’asar ta kusa.

Washe gari,

Tun da sassafe muka gama shiri, takwas ma bata yi ba muka karya sai haramar komawa asibiti.

STORY CONTINUES BELOW

Tun ba mu fita ba sai ga Annur ya zo, sanye yake da Uniform na Gobarau Academy, school bag goye a bayansa.

Da fara’a ya ce,

“Umma na zo duba Amrah ne, ta ji sauk’i sosai ko?”

“Alhamdulillahi! Duk yau ko cikin dare ma bata yi ciwon komai ba. Ka ga shirin tafiya ma muke, asibitin zamu koma karb’an sakamako.” Na bashi amsa ina tab’a kanshi.

“To tun da ta ji sauk’i bari in tafi. Dama na matsa wa Baba Amadu ne lallai sai ya biyo da ni na duba Amrah. Bara in tafi, idan mun tashi zan biyo ko kun dawo lokacin.”

“To Annur, Allah Ya bada sa’a. Ka yi karatu sosai ka ji?”

Ya jinjina kai had’e da fita daga gidan, a dai-dai fitowar Mallam daga d’aki ya rufe.

“Kamar muryar Annur na ji ko?” Ya tambaye ni bayan ya datse d’akin.

“Shi ne fa da kan shi. Wai ya zo duba mutuniyarsa ne.” Na bashi amsa had’e da saka ma Amrah takalmanta.

“Allah sarki!” Ya fad’a ya yi gaba na kama hannun Amrah, muka mara masa baya.

Bayan ya rufe gidan, muka nufi titi, babu jimawa muka samu napep aka nufi Turai da mu.

Ko da muka isa Turai child and maternity hospital, mun tarar da mutane sosai, kasantuwar akwai special doctor da yake zuwa a irin ranar ko wace talata, wanda musamman k’ananan yara yake dubawa.

Kai tsaye laboratory (d’akin gwaje gwaje) muka nufa, mutum uku ne kawai a gabanmu, su ma kuma ba wai result suka je karb’a ba, sun je a yi masu wani awon ne na daban.

Zama na yi bisa kujera na rungume Amrah, mallam kuma ya shiga ciki inda zai karb’o sakamakon.

Bai jima ba sai gashi ya fito, ya ce in tashi mu tafi.

Kusan minti arba’in muka d’auka kafin a bamu izinin shiga wurin likita, likitar jiya mai suna Dr. Xarah ce muka tarar, sai kuma wata d’aya likita zaune daga wata kujera, lab court ce a jikinta ta yi rolling d’in bular mayafi.

Da sallama muka shiga, bayan mun gaisa ta ce,

“Sannunku Maman Amrah. Ku zauna mana.” Ta gwada mana kujeru guda biyun da ke fuskantarta.

Zama kuwa muka yi, waccan d’aya likitar ta ce,

“Dr. Xarah ni zan wuce, sai na gan ki.”

Dr. Xarah ta ce,

“To shi ke nan Dr. Rabiatu. Insha Allahu zaki ji ni very soon. A gaishe min da yarana da Babansu.”

Bankwana suka yi sannan ta juyo gare mu,

“Ina results d’in?” Ta fad’a bayan ta mayar da glasses a idonta.

Mallam ya mik’o mun sannan na isar da shi gare ta,

“Ga shi Dr.” Na mik’a mata.

Ta jima tana dudduba takardun, shiru ya biyo baya na tsawon minti sha biyar ko ma fin haka, kafin ta zare glasses d’inta ta ce,

“Ya Salaam!”Ta dafe kanta.

Bamu ce mata komai ba, sai dai ambaton sunan Allah da ta yi ba kad’an d’in razana ni ya yi ba, take na ji hankalina ya tashi, zuciyata na dukan uku-uku.

Ajiyar zuciya nannauya ta sauke kafin ta ce,

“Ban san me ya sa ba, abu mai matuk’ar muhimmanci amma mutane sam! Basu yarda da shi ba.

Shekara da shekaru manyan likitoci sun sha fad’akarwa, cewa mu kasance masu awon genotype kafin mu yi aure.1

Ba wai ku iyayen ake ji ba, su yaran da zaku haifa d’in ne abun ji.

Yaro k’arami, bai ji ba bai gani ba, bai san halin da duniya take ciki ba, amma tun yana k’arami a wargaza masa rayuwa, ta k’i yin inganci.

Me yasa ba’a kula ne? Me yasa soyayya take rufe wa mutane ido su gagara aikata abin da ya dace? Shin mutane basa tausayi ne? Basa duba future d’in su? Su dai soyayya kawai, kar a b’ata ran masoyi.1

Yanzu fa wasu a tunaninsu da zarar na ce da wanda zan aura ya kamata mu yi awon genotype, zai iya daina so na ko? Zai iya ganin kaman ban yarda da shi ba ne? Zai ji a duniyarsa na raina masa hankali ko?

Me yasa zaki zab’i faranta ran wani namiji, ki cuci yaron da zaki haifa? Ko kin san cewa matuk’ar hakan ta kasance, mijinki zai iya dakatar da haihuwa da ke saboda gudun wahala? Ko kin san cewa zai iya zuwa ya nemi mai AA ya aura, wacce zata ci gaba da haifa masa lafiyayyun yara?1

A rayuwar nan ta yanzu, wacce kud’i da lafiya suka yi k’aranci, kamata ya yi tun farko a gina rayuwa a kan abu mai kyau, a gina rayuwar yaro da tubalin mai kyau.

Wallahi auren soyayya ba tare da bincika sinadarin jini ba, babu abin da yake haifarwa face wahala. Ba wai ga yaron kawai ba, har ku iyayen da zaku yita jerangwama da shi, kuna cikin damuwa.

Yanzu ke baki sani ba, kin auri namiji wanda sinadarin jininsa AS ne, shi ma kuma ya aure ki, naki jinin AS ne, wane irin yara kike tsammanin zaku haifa?

Idan masu sinadarin jini AS suka yi aure su duka biyun, akwai yiuwar fa su haifi yaro mai amosanin jini (sickler)

Ba wai na ce lallai sai mai sickler zasu haifa ba, sai dai zasu iya samun sirkin mai sickler d’in.

Zasu iya samun mafi rinjaye AS a cikin yaransu.

Ita kanta AS d’in nan fa, akwai mai wahala, kafin ma a kai ga SS.

Matuk’ar S d’in da ke cikin jininka ta rinjayi A d’in, to zaka iya zama mai laluri a ko da yaushe, tamkar yanda mai sickler zai yi, sai dai zaka iya samun sauk’i ba kaman na me SS d’in ba.

Yanzu ku bayin Allah, kun san abin da rashin awon genotype ya haifar maku?

Kun san cikin halin da kuka hefa ‘yarku?

Yanzu kai, kana da AS, Ita ma mamanta tana da AS, What do you expect? Kuna zaton zaku ci gaba da haifar yara lafiyayyu ne? Idan ma duka yaran naku lafiyayyu ne, kun san wanda zaku haifa a gaba?

Ban ji dad’i ba ko kad’an, ku ne silar ciwon ‘yarku, yarinyar da bata ji ba bata gani ba, jininta yana d’auke da amosani a cikinsa (sickle cell) a bisa sakaci da son zuciya irin naku.1

Duk ciwukan da kuka ga tana yi, wasu daga cikin illolin sickler ne, cutar yarinyarku ke nan….” ta dakata daga nan ita kanta cike take da tausayi, idonta kamar zai kawo ruwa.

“…kuma duk irin wahalar da take tun tana da shekara d’aya, baku ta’ba tunanin kawo ta asibiti ba sai yanzu.

Any ways, da sauk’i ma tun da kun zo yanzu d’in ai.

Zan rubuta mata magunguna, sannan kuma akwai shawarwari da dama wanda in dai kuka bi su, insha Allahu cutar zata jima bata ringa tasar mata ba;

Babban abin da yake tasar da ita shi ne malaria, saboda haka sai kun kula, ko da wasa kar ku ringa bari sauro na cizonta. Duk yanda zaku yi, ku tabbatar baku barta inda sauro zai cije ta ba. Akwai gidan sauro ana bayar da shi kyauta a ko wace asibiti, ku nema, da zarar magrib ta yi ku tabbatar kun saka ta a ciki, kar kuma ku bari sauron ya shiga a ciki.

Abu na biyu, kar ku ringa barinta a cikin sanyi, saboda wannan sanyin zai iya saka mata zazzab’i, kuma zazzab’in masu sickler shi ne wanda ba a so. Saboda su basu iya zazzab’i ba, da zarar sun fara shi zai iya k’onar masu da baki d’aya jininsu, idan ma ba a hanzarta an saka masu wani ba, zasu iya rasa rayuwarsu.

Abu na uku, banda duka. K’ashinsu ba wani k’wari ne da shi ba, da zarar kun duke ta, zaku iya tab’o inda bai dace ba, kuma k’arshe wahalar ta dawo a kanku. Hakan kuma ba wai yana nufin kar ku tarbiyyantar da ita ba, a’a, sai dai ku kula. Ku san ta hanyar da zaku bi idan ta yi laifi. Ko School ta shiga nan gaba, ko da wasa kar ku bari ana dukanta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]