[Advertisements⬇️]

ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 18 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

karatuna ki tafar min da su gida, idan na dawo don ba gida za ni yanzu ba zan zo na karba, ba kuma na son ki yi min gardama duk abin da zan ce miki a cikin makaranta zai zamo UMARNI ne a gurinki.
OK, malam babu matsala zan bi UMARNInka a makaranta a gida ma zan bi umarnin ka na matsayin yaya duk zan yi matukar ba za ka shiga rayuwata ba, amma idan abin ya yi min yawa zan iya sanar da Abba Aminu, domin shi ne kadai zai iya ba ka UMARNI bani ba, ba ni key din.” Ta sa hannu ta karbi key din da yake ta hangi motar yana kusa da ita.
Mamaki ne ya kama shi ya saki baki yana kallonta yadda take yin abu cikin kwarin gwiwa, murmushi ya yi ya ce, ‘Yarinya za ki yi laushi ne in dai ni ne

Ta je ta dauko ta dawo ta mika masa key din ta ce, ‘Happy. “Ta wani tsare shi da idanunta masu sa shi rikicewa. Girgiza kai ya yi ya ce, “Ko kadan UMARNI ne fa mai zai sa na yi murna dole ya zamo miki kiyi ne. O.K, ka huta lafiya.”
OK, thank dear Raihanah.” Ya wani fada cikin shauki.
Juyawa ta yi ta kalle shi yana sakar mata wani irin murmushi, juyawa ta yi ta tafi abin ta. Zahra na can gefe tana kallonsu da haka ta
karaso gurinta niki-niki da jaka kayan suna son fin karfinta. Zahra ta shiga dariya ta ce, “Kai mutanen nan kuna burge ni kin ga wani irin chemistry da ya hadu lokacin da ku ke kallon juna idan ku ka yi aure ban san wane irin so za ku yi wa junanku ba
Haana.Cikin daga murya ta ce, “Zahra za ki karbe ni ko sai na zubar da kayan nan mutumin nan

sabon wulakanci ya zo min da shi, amma zan san abin da zan yi masa ba dai ta nan ya biyo min ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ta rage mata takardun ta ce, “To me ye amfanin ki idan bai fara nuna miki aikinki tun yanzu kafin ki je gidan.”
“Hmmm! Zahra kin sha kwaya ne ki ke min wannan maganar wa ye zai aure shi kin manta mai na fada miki?”Don kar ta ja zancen sai ta ce, ‘Au! Haka ne fa.” Ta yi saurin rufe bakinta.
Harararta ta yi ta ce, ‘Kya ji da shi muguwa.” Dariya ta yi da haka ta je motarta suka rabo kowa ya yi gida.
Tana zuwa gida tun kafin ta wuce nasu ta tsaya ta bawa maigadin gidan ta ce don Allah ya mikawa gidan ko ya ajiye gurin Yaya Muhammad na zuwa ya ba shi ya ce in ji ta ta dan sinna masa dari biyar ya shiga godiya.
Ran ta fari tas ta ja motarta ko ba komai ta san ransa zai baci, ita kuma haka take so dama ya yi hakan ne don ya samu damar yadda zai ke kula ta tunda an toshe masa hanyoyi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Daf da za ta wuce ta hangi Fadeelah na kokarin shiga gidan Uncle Habib, hon ta danna mata da kamar ba za ta juyo ba sai kuma ta dake ta juyo.
Da motar ta karasa gurinta ba ta fito ba ta tsaya ta ce, ‘Oh! Fadeelah zumunci na da ke ya gutsure ko? Haba Fadeelah na san dai kin samu labarin komai gurin Haaya, lambar ki kin yi blocking so biyu ni da Rauda muka zo neman ki ana cewa kina barci. Fadeelah me ye rayuwar in dai a kan Yaya Muhammad ne ki saka ranki a inuwa Abba ya yi mana tsakani da shi ba ruwansa da ni.”
Dubanta ta yi ta ce, “To na ji tunda kin fada min abin da yake ranki ni zan wuce ki huta lafiya.’ Tana gama fada mata ta wuce abin ta.
Ko kadan ba ta ji dadin abin da Fadeelah ta yi mata ba, kawai sai ta ja motarta cikin sanyin tanatunanin duk Malam M.J ne ya janyo mata haka ya faru tsakaninta da ‘yar uwarta.. Karfe biyar da kusan rabi na ranar zaune take gaban Abba Aminu don amsa kiran da ya yi mata.“Dama na kira ki ne domin neman alfarma da kuma jin ta bakin ki kafin na yanke hukunci kai
tsaye da fatan za ki ba ni hadin kai dari bisa dari.” “Insha Allahu Abba zan ba ka mutukar abin bai fi karfina ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ammi wani dan Aminina nake son na hada auransa da ke na yaba da hankalinsa da nutsuwarsa na fara yi miki maganarsa ne kafin na ba shi damar zuwa gurinki ina son jin amincewarki, saboda so muke da zarar kun gama karatunku mu hada ku gaba daya mu aurar lokaci guda.”
Wani irin tsananin bugun zuciya ne ya zo mata duk da ya ga razanar a kan fuskarta, amma sai ya share ya yi kamar bai gani ba.
Shiru ta yi ba ta ce komai ba gaba daya tunaninta ya tsaya babu mutumin da ya fara zuwa ranta sai M.J cikin su ukun shi ne ya fara zuwa ranta.
“Ammi kin yi shiru ko kina da wani UZURI ne game da maganar ko kina da wani da ki ke son gabatar mana da shi. Na yi wannan tunanin ne domin son ganin farin cikin ki kamar yadda kike son ‘yan wanki su samu abin da suke so to amma dai bari na ji me za ki ce.”
“Abba babu abin da zan ce kamar yadda ka fada burina ne haka ‘yan uwana su samu abin da suke so, matukar shi wanda za ka hada ni da shi din idan ka yarda da shi nima na yarda da shi na san ka yi haka ne don a samu zaman lafiya a family.
‘Yauwa Ammina kin kuwa fahimce ni. To Allah ya yi miki albarka ranar Juma’a gobe kenan zai zo ku hadu sunansa Muhammad Bashir dan abokina ne na kusa, zan kuma kira yayyanki na musu bayani da kai na don su san cewa ni na baki mijin da kaina kada su dora miki laifi.
Za ki iya tashi ki tafi idan har ba ki da abin
cewa, Allah ya yi miki albarka.” Mikewa ta yi ta tafi bayan ta ce masa ba ta da abin cewa.
Da kyar ta iya isa gida, domin ji ta yi duniyar tana juya mata babu fuskar wanda take iya hange a zuciyarta sai ta M.J kuka ta shiga daki tana yi, domin ba ta taɓa zaton kiran da Abba Aminu zai yi mata ba kan mijin aure ne ba.
Me yasa ba zai bar ta ta kawo wanda take so ba kai auren ma gaba daya ta tsane shi, da za a bar ta tana gama wannan karatun ta wuce Law School hankalinta kwance watakila ta samu wanda za ta aura. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yau ce ranar da ta ji wani irin son M.J ya zo mata sabo fil har ta ji haushin FAdeelah tabbas da ba ita cikin rayuwarta tabbas da ta auri Malam M.J dinta, tunda Ya Abba ya hakura yana farin ciki da Haaya cikin rayuwarsa. Shi ke nan ita dai ba za ta taba samun abin da take so ba.Babu yadda za ta yi da rayuwarta tunda haka Allah ya shirya mata, saboda ba za ta taba musu da Abba Aminu ba, domin dalilinsa ta samu saukin damuwarta, sai dai shi ma yanzu ya kawo mata wata sabuwar damuwar da ya hada ta da dan abokinsa.
Tamkar ruwa ya cinye su su biyun idan ka cire Ya Abba da shi yake ganin bai kamata a hada har shi a ce ga mijin da Abba Aminu ya tsayarwa da kanwarsa Haana ba, tunda ya hakura tun tuni kamata ya yi a cire shi cikin maganar damuwarsa daya ya san da wuya idan za ta yi farin ciki da wanda aka hada ta da shi, mutum daya ya sani a duniyar nan da zai saka Haana farin ciki shi ne Muhammad, da za a bi ta son ransa da an hada masa duk su biyun ya aura tunda Addini bai hana. ba, ya kuma tabbata zai rike su da adalci, shi kenan kowa cikinsu ya samu abin da yake so. Furucin AAbba Aminu shi ne ya dawo da Ya Abba daga
duniyar tunanin da ya tafi. “Kai kuma Sameer ka jira ni saura kai kwanan nan kai ma zan nemo maka wadda za ka aura duk rana daya za mu aurar da ku.”
Karfin hali Mr Sameer ya yi ya ce, “Abba don Allah ina neman ka ba ni dama da kaina na nemi wadda zan aura ko da a cikin dangi ne zan yi wannan kokarin.”
‘An ki a ba ka damar babu wacce zan yarda ka nema cikin dangin da ba akwai wadda take son ka cikin daingin ba ka ki yarda ni na gama magana mada uban yarinyar amsarsa kawai nake jira na tura. ka gidan.
Zai sake magana ya daga masa hannu ya ce, ‘Kada na kara jin ka ce da ni wani abu ku tashi ku ba ni guri kuma duk wanda na ji ya yi wa Ammina ko yaron da zai zo gurinta magana sai na sabawa duk wanda ya yi haka ku tashi ku je. Allah ya yi muku albarka.”
Lokaci guda suka mike hankalin Abba Aminu duk yana kan Muhammad ya ga tarin damuwa sai dai bai hangi karaya a tare da shi ba, kamar yadda ya ganta a fuskar Sameer ba.
Sauri Muhammad ya yi ya fice ya bar su. Smeer ne ya ce, “Abba don Allah ba wani taimako da za ka yi min ka janyo min Www.bankinhausanovels.com.ng hankalin Rauda wallahi ni yanzu ita nake so ka san halin Abbah zafinsa ya yi yawa duk abin da ya ce babu mai hana shi tunda ya fadi hakan na san dole da watan zai hada ni ni kuma wallahi ba na so.””Maganar gaskiya Sameer ban san ya zan yi ba saboda na ga Rauda zuciyarta ta nutsu da Fu’ad kana ganin ba wata matsala za a sake samu ba?”
Tsaki ya yi ya ce, ‘Abban nan sam ba ya fahimtar irin hälin da za mu shiga ka duba dai Muhammad yadda ya dauki zafi.
Kamata dai ya yi tun farko mu tsaya mu daidaita matsalar muka ki ga shi nan da iyaye suka san maganar sun zartar da hukunci a kan mu.” Cewar Ya Abba.”Gaskiya Abba ba zan iya hakura ba da girma na a yi min auren dole wallahi ba kin Rauda nake ba ban san tana sona ba sai da Fareeda ta fada min lokacin idona ya rufe da son Haana.
Hatta kundin sirrinta sai da ta kawo min na gani, amma na ki hakura ni yanzu idan ba ita na aura ba ba zan taba samun farin ciki ba. Haana kuwa tuni na janye don na san ko hauka nake Abba ba zai taba yarda na aure ta ba, ka bar ni kawai ni na san abin da zan yi.’
Wucewa shi ma ya yi ya bar shi a gurin murmushi Ya Abba ya yi ya ce ‘Gaskiya ne yau na ga son Rauda na gaskiya a idanunka Sameer zan so hakan ta kasance sai dai ina ba ni da iko iyayenmu ne ke da zarafin hakan.”
Kai tsaye Muhammad ya samu a gida ya fara masa magana ya tsaya yana saurarensa..
“Muhammad ina da shawara mai zai sa ba za ka yarda ka auri Fadeelah da Haana ba a matsayin matanka da ka yarda a hada ta da wani can ba cikin zuri’a din mu ba idan ka zowa da Abba Aminu da wannan batun zai yarda ya kai gurinsauran iyayenmu.” maganar
“Abba ka bar wannan maganar idan ka sauko Fadeelah ciki raina yana ɓaci na rantse maka ba zan auri Fadeelah ba domin na sha fada mata ta nemi wani ta ki, kuma ka ga dalilinta na ke shirin rasa Raihana, ba zan iya hada son Raihana da kowa ba ko na aure su su biyun ba zan iya adalci ba, idan har ban samu Raihanah ba to har abada Fadeelah ba za ta same ni ba. Kai bari na fada maka wallahi sai na yi wa su Abba karamin hauka sannan za su gane inda na dosa. Wannan da ake maganar zai zo gurin Raihanah ranar da na raunata shi ya kwanta jinya sa san yadda za su yi da iyayensa kuma wallahi idan ba a ba ni
Raihana ba sai na tayar musu da hankali kaf cikin
zuri’a din nan wannan shirun da ka ga ina yi ka ji tsoronsa.
‘Muhammad ka dauki komai da sauki sai ka ga ka yi nasara a kai.”Look! Abba ka bar ni kawai ba a yi min sauki ba, nima kuwa ba zan yi shi ba tunda haka aka nema a gurina. Kawai ka je abin ka ka jira lokacin ka gani,.
Washe gari ba ta samu ta shiga school ba kasancewar tun kafin ta fita aka kira ta Malamin ba zai zo ba. Ta ji dadin haka saboda ko ba komai za ta huta da fitinar M.J da ya dame ta da waya tun jiya a kan kada ta sake ta saurari mutumin da Abba Aminu zai sa ya zo gurin ta.
Cacar baki suka shiga tana dole ta kula shi tunda shi ma yana da matar da zai aura ba zai hana ta kula mijin da za ta aura ba, tunda ba zamansa take ba.
Jin kalmar mijin da za ta aura ya daga masa hankali nan ya shiga yi mata masifa yadda ya so, a takaice dai jiyan bai bar ta ta huta ba dole ta sa ta kashe wayarta.Da safe da ta bude wayarta text ne iri-iri na yi mata kashedi share shi ta yi ta ki bi ta kansa.
Tana zaune ta ji sakon kiran Mr. Smeer da ta yi niyar kin zuwa, amma sai wata zuciyar ta ce bari ta je domin ba ta san abin da ya zo da shi ba. Ranta bace ta zo ta same shi a falo, ganin ranta a bace ya -ce, ‘Hajiya maida wukar ni ba da wani abu na zo gurin ki ba taimako na zo nema.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai lokacin ta saki ranta tun kafin ta zauna ya ce, ‘Miss Haana zuwa na yi ki taimaka min a kan Rauda ta saurare ni wallahi inan son ta, Abba ne yake shirin ba ni wata wadda ban san wane irin rayuwa take ba, please ki je ki shawo min kanta sam ta ki ta saurare ni hankalina ya tashi.”
“Gaskiya ka makara ya zan yi da Yaya Fu’ad bayan yanzu sun shirya kawai ka hakura ka karbi wadda Abban zai ba ka ni ma shi ya zabar min.Miss HAana ke ce ki ka ga za ki iya amma ni
ba zan yarda ba na hakura da ke, domin irin ikirarin da Abba ya yi min tunda na hakura na gano mai sona wallahi ita zan aura.”
“O.k Mr Sameer ka zo ne nima ka zuga ni na ki abin da Abban yake so na yi to gaskiya ba zan iya
ba” “Oh! No, ni fa ba haka nake nufi ba, ga maganar da na zo miki da ita a kai kawai nake so ki yi min wani abu.
“Ka je zan duba na gani, amma fa na san da wuya sai dai ka je ka samu Fu’ad din ku yi magana.Tsaki ya sake yi ya ce, ‘Ke tsiyata da ke kenan
idan ba za ki min ba kawai ki fito ki fada min.” “To zan gwada amma idan ban yi nasara ba kar
ka dora min laifi.” Bayan masallaci ne Abba Aminu ya kira ta ta je gidansa a can za ta karbi bakon nata. Suna zaune suna hira da su Fareeda, Abban ya aiko aka kira ta. A nutse ta same shi ya ce, ‘Ki je falon bakon naki ya zo.Cikin ladabi ta karasa da “To.
Sallama ta yi cikin falon murya kasa ba ta daga fuskarta ba. Ya amsa a nutse tare da cewa, “Bismillah ga waje. Haushinsa ta ji ya kamata sai ka ce shi ne dan gidan har da nuna mata wajen, ta zauna ta ce,Sannu.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yauwa Raihanatu ya gida ya muka same ku.”
Daga ido ta yi ta dube shi babu laifi ya dan
hadu, sai dai ko kadan ba ya cikin tsarin mijin da take so.
Gajeriyar hira suka yi bayan ya gabatar mata da kansa ya ce mata yana aiki a PHCN. Bai wani jima ba ya tafi ita a takaice ta gabatar da kanta gare shi.
Zaune suke ita da Muhammad Bashir a farfajiyar gidansu gurin da aka tanada don hutawa, tunda ta hango shi ta ji gabanta ya fadi, yadda ya nufo su kamar wani mawiyacin zaki da ya kwana ya wuni bai ci komai ba.
Ko sallama bai musu ba ya maida kallonsa ga Haana ya ce, “Ke na gaji da wannan rainin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]