[Advertisements⬇️]

ZAFIN RABO CHAPTER 9 BY SAKIEYY - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZAFIN RABO CHAPTER 9 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan sun idar da jam’in sallar azahar, kamal ya gama add’oin shi a niste, ya mik’e ya fito daga masallacin a hankali yake tafiyar shi, cikin nutsuwa da kasaita, yaso ya tsaya har ayi sallar la’asar yadda ya saba a kullum amma yaga yau bazai iya tsayawa ba, shima kanshi baisan mai ya saka ba kawai dai yana so ya koma gida, haka ya tsallaka titi ya nufi hanyar makeken gidan shi da yake tsallaken masallacin, yana knocking gate d’in bai dad’e a tsaye ba mai gadi ya taho da sauri ya bud’e mishi, yana mik’a gaisuwa, kamal d’aga mishi hannu yayi, tare da yin cikin gidan, bai tsaya danna doorbell ba ko knocking kawai ya saka muk’ullin shi ya bud’e k’ofar, bai yarda da ita ba soboda haka ko da wasa bai bar k’ofar a bud’e ba,

Baiyi mamaki ba da yaga parlor din wayam dan yasan bazata tab’a fitowa ta zauna a ckin shi, amma abunda ya bashi mamki da yaga ba kowa a dak’in ta, ko a bathroom d’inta da ya lek’a, haka ya k’ara fitowa ya lek’a duk d’akunan gidan bata nan, bai tada hankalin shi ba saboda yasan tana cikin gidan bata je ko ina ba, k’ofa a kulle ina ma zata, yayi hanyar kitchen saboda shi kad’ai ni bai duba ba, ai kan yayi rabin hanyar yaga an bud’e k’ofar a hankali ta fito cak ya tsaya, idanunta a k’asa, haka ta kulle k’ofar, manyan idanun kamal akanta,

dariya taso ta bashi yarda yaga ta kinkimo robobin ruwa, hannayen sa ya nanad’e akan k’irjin shi, ya had’e fuska ya bi sakeena da kallo wacce har lokacin idanunta na k’asa, bama tasan yana wurin ba, bai matsa ba har ta buge k’irjinshi, yana jinta a jikinshi yaji wani abu ya taho mishi tun daga tafin k’afarshi har tsakiyar kanshi, baisan lokacin da yayi baya ba a tsorace, itama sakeena tayi baya tare da sakin abun hannuta da zaro manyan idanunta waje, tsoro ya fara bayyana a fuskar ta, jikinta nasan fara rawa,

Zuciyar shi ce ta fara bugawa bai san dalili ba, lumshe idanunshi yayi da sauri dan ya rasa meke damun shi, sai da nustuwa tazo mishi sannan ya bud’e su, sunyi jajaye dasu, yana maida idanunshi wurin da yabar sakeena ya neme ta ya rasa, yana waiwayawa yaga har ta kusa d’akinta, tana tafiya a hankali dan bata so yaji takun ta, wato wayo zatayi mishi kenan,

“Ina kike shirin zuwa ma”

A hankali yayi maganar, yana gani ta tsaya cak da tafiyar ta, yana shirin yaga ta juyo ta maida hankalinta wurin shi, ai haba sai ganin yayi ta saka gudu, a guje ta shiga d’akin tare da banko k’ofar, yana jin k’arar muk’ulli alamun ta kulle d’akin, duk yarda baya san yayi dariya bai san lokacin da ya sake ta ba dan ta bala’in bashi dariya, haka kamal yabi k’ofar ta da kallo yana murmushi, can ya juya ya koma hanyar kitchen, yana shiga baiga alamun komi ba, shiga tambayr kanshi yayi komai tazo yi a kitchen, a haka har ya lek’a store, shima ya shiga ya fara dube dube, yaga kwalin indomie a bud’e da kwalin sardines, murmushi ya saki,

“Wato yunwa ce ta koro ta”

Ya fad’i a zuciya, girgiza kanshi yayi tare da bud’e kwalin talia da makaroni, da kuskus, duk ya d’auko guda biyu ya ajiye a gefe, sannan kuma yayi waje ta kofar baya ta kitchen d’in tare da kwalla wa mallam isyaku kira wato mai gadi, malam isyaku da sauri ya k’araso, kamal umarta shi yayi ya kwashe duk kayan abinci ya saka mishi a mota, malam isyaku mai zaiyi ba in ba binshi da kallon tambaya, kamal kuwa ya had’e girar sama da k’asa sai kace wanda bai tab’a dariya ba,

“Zaka fara kwasar kayan ne ko kuma zaka ci gaba da kallo na”

Yana gama maganar mallam isyaku da sauri ya fara kwasar kaya, dan yasan halin mai gidan nasa, baya san raini da wasa, kamal na ganin ya fara d’ibar kayan, shima ya juya ya kwashi way’annan abinci da ya d’ebo ya fito daga kitchen d’in, bedroom d’inshi ya fara zuwa dan d’aukar spare key, bayan ya dauko ya fito yayi hanyar bedroom dinta, ya saka key d’in ya bud’e kofar, yana bud’e kofar ya ganta zaune akan gado, ta kankame jikinta, tana jin shigowar shi d’akin zumbur ta mik’e, kamal na ganin yarda tsoro ya baiyana akan fuskarta bayan zaro manyan idanunta waje, d’auke idanunshi yayi daga kanta sannan ya cilla mata abincin kan gado, fuskar shi a d’aure tamau ba wasa a ciki,

“Ga abincin da zai ishe ki na wata d’aya, bana san kina shiga kitchen d’ina kina mun sata kamar wata b’era”

Wani irin kallo ta bishi dashi, wanda yake d’auke da tsoro da harara,

“Sata??, dan ina jin yunwa na shiga na dafa ma kaina abincin da aka siya da kud’in ubana shine nayi sata?,

Mamaki ta k’ara bawa kamal, yarda duk abunda zai mata bakinta baya tab’a mutuwa, a hankali ya fara matsowa kusa da ita, ita kuma tana ja baya har bayan ta ya bugi bango, a haka kamal ya k’ara matsowa kusa da ita baifi inchi d’aya bane tsakanin su, sunyi kusa sosai sobada har numfashin su ya zama d’aya, yana gani yarda ta kwada kanta tare da lumshe idanunta, tsoro ya k’ara kamata, kamal wani murmushi ya saki a ranshi, tsoro fal cikinta amma bai hana ta maida mishi da magana ba,

“Kika k’ara wata maganar zan kwashe abincin dana kawo miki ki zama baki da abunda zaki saka a bikin ki har na tsawan kwanaki”

Yana ganin jikinta ya fara rawa, ta k’ara shigewa jikin bango, har lokacin idanunta na kulle, matsawa yayi, saboda kamshin jikinta da turarenta sun fara tada mishi hankali, sai da ya tabbata bata da abinda zata k’ara cewa sannan ya juya zaibar d’akin, baiyi taku uku ba yaji wani abu ya daki bayan shi, da sauri ya juyo tare da maida idanunshi k’asa yaga ledar makaroni, sannan ya d’ago su ya maida kan sakeena wace take ruk’e ta ledar kuskus tana shirin k’ara jefo mishi, sai da ta kalle shi cikin idanunshi sannan ta jefo mishi ledar, yana gani ta jefo yayi saurin kwacewa sai ga ledar a k’asa, k’ara maida idanunshi yayi kanta, wanda sun k’ad’a sun koma jaa, farar fuskar shi itama ta koma jajawur saboda b’accin rai, sakar mata fuska yake da har zata dube shi ta cilla mishi wani abu,

“Ka kwashe abincin ka bana so, da nakai wani abu naka bakina na gwammace yunwa ta kashe ni”

Kamal kawai binta yake da kallo ya rasa mai zaiyi a wurin, tunda yake a rayuwar shi bai tab’a ganin mace ba irinta, saboda ko yarda take da yarda tayi maganar yanzu a tsorace take, amma bai hanata yi mishi abunda taga dama ba, ya zaiyi da ita ne, yaga bata da shirin canza halinta, da sauri ya tako har isa wurinta tare da ruk’e kafad’unta ta buga bayan ta da bango, ya kafa mata wannan jajayen manyan idanun nashi, muryarshi a d’an sama, sai huci yake, in ka ganshi a wurin dole ya baka tsoro,

“Baza ki daina maida mun da magana ba, ni mijinki ne, kiyi respecting d’ina”

3

Ga mamakin shi sai gani yayi ta saki murmushi, sannan ta k’ara kafa mishi manayan idanunta wanda suke cike da tsoro,

“Respect fa kace?, ai ni yarda na sani respect is earned not given kamal, da kana so nayi respecting d’inka ka a matsayin mijina da ka…”

Ai kan ta k’arasa zancen ta, ya d’auke ta cak, ya saka ta akan kafad’arshi, yana ji tana dukan shi dan ya sauk’e ta, amma kamal a zuciye yake, ya gaji da gasa mishi maganganun da take, ko dan tasan bazai tab’a saka hannun ya dake ta ba, a haka tana ta dukan shi da jan laulausan gashin kanshi, da ihon ya sauke ta shi kuwa yayi banza da ita har suka fita daga cikin gidan.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Duk yarda take so ta daina shiga harkarshi bata iyawa, duk lokacin data ganshi wata irin tafasa zuciyar ta take, kan tayi tunanin kulle bakinta ta maida mashi da murtani, ko yanzu da ya d’aga ta cak akan kafad’arshi bakin ta yak’i ya daina shiru, duk maganganun da take yayi banza da ita sai tafiyar shi yake abunshi, sakeena k’ara saka hannun tayi ta ja mishi gashi da kai mishi duka wai duk dan ya sauke ta, amma ina yak’i ajiye ta har sai da suka shiga wani d’aki da yake a wajen gidan sannan ya dire ta, d’akin kamar store ne, dan taga kwalayen tv, washing machine, microwave, dishwasher, da dai sauran su, tana gama k’arewa d’akin kallo ta juyo ta sauke idanunta akan shi, da suka had’a ido sai da gabanta ya fad’i, fuskar shi ba annuri ko na d’igo d’aya, gaba d’aya kamaninshi sun canza, tsoro ne ya kama, tayi saurin ja baya dan fargabar kada yayi mata wani abu, kamal jajayen idanunshi ya saka akanta ta baya ko k’ifta su, duk da sakeena a tsorace take, haka ta dake ta kawar ta tsoranta gefe ta kalle shi cikin idanunshi, ta fara cewa,+
“In ka cigaba da mun irin wannan wulaqanci kamal wallahi zan yi sanadi…”
“SANADIYAR ME??, ME ZAKI IYA YI MUN??”
Kan ta k’rasa zancen ta ya daka mata wata gigitaciyar tsawa da ta saka sakin toshe kunnuwanta da kanta, tare da saurin zubewa a k’asa, dan ya bala’in tsorata ta, a tunaninta kai mata duka zaiyi, barin ma yarda taga gaba d’aya kamun nunshi su canza, farar fusar shi ta koma jaa, ga sai huci yake, kamar wani zaki, haka tayi shiru a tsugunne tana jiran duka kawai sai jinshi tayi yace,
“ki zauna a d’akinan ba abinci, ba ruwa, har sai wannan kan naki ya gane mai damun magana ba inda zai kaiki sai dai ma k’ara miki wahala”
Yarda yayi maganar ya saka jikinta fara rawa, ga yana maganar ya juya ya fita ko kallanta bai k’ara yi ba, sakeena tsabar shock da tsoro ta kasa mosti, har lokacin jikinta rawa yake, tsawa ya daka mata kawai amma gaba d’aya ya rikita ta, wannan wana irin namiji ne, gaskiya tana cikin wahala, ta shiga uku, k’arar muk’ullin da taji ne ya dawo da ita daga duniyar da take, ta mahaukacin sauri ta mik’e tayi hanyar k’ofar tana bugawa dan ya bud’e, haka yayi kunnane shegu da ita ya koma cikin gidan, sakeena kuwa tai ta faman buga k’ofa har ta gaji, ta samu wuri ta zauna a k’asan d’akin tayi shiru, ta zuba ma bango d’akin ido, a haka har aka fara kiran sallar la’asar, tana ji mai gadi ya bud’e mishi gate ya fita masallaci, sakeena saka kanta tayi akan cinyoyinta tayi shiru, tsabar takai ci tama kasa kuka, dan tagane komai kukan da zatai kamal bazai tab’a tausaya mata ba, saboda zuciyar shi a kyankyashe take, kamar dutse take, bashi da imani ko da na sakwan d’aya, ya saka an dawo da ita gidan shi dan kawai ya cigaba da wulaqanta ta, da ya barta acan da jabir ya cece ta, ta fita daga hannunshi, wani irin bak’in ciki ne ya k’ara rufeta, ta fara niyar tashi tayi salla la’asar tunda tana da alwala, kawai sai jin period d’inta tayi, hankalinta ne ya k’ara tashi, da ta tuna a yanayin da take, ga ba toilet ko wani abu d’akin, k’ara kank’ame jikinta tayi kwalla ta cika idanunta, wai ita yau ake wa wannan irin cin mutunci, da gatan ta da komi ya kama ya kulle ta a d’aki kamar wata prisoner , lallai kamal bak’in mugun ne,
A haka tana zaune ita kad’ai cikin duhu, dan ta nemi switch d’in fitila ta rasa, ga zafin gari ya rufe d’akin dan ba ko fanka, yanzu ta fara jin k’ishin ruwa dan da ta ci abinci d’azu bata sha ruwa ba, tana ji ya fita a mota bayan ya dawo daga masallaci, har yanzu bai dawo ba, d’azu ta tashi ta lek’a ta window tana kwalla ma mai gadin gidan kira dan yazo ya taimaketa amma ina, ko yaji ta ko baiji ba bama ta sani ba dan ko kallan d’akin baiyi ba, haka ta koma ta zauna tare da zubawa sarautar Allah ido, ta cigaba da zama ita kad’ai cikin duhu, har taji k’aran gate alamun kamal ya dawo, da sauri ta mik’e ta l’eka window, dan a zatan ta zai bud’e mata k’ofa sai gani tayi yayi cikin gidan, ko kallon inda dake baiyi ba, wata tsinuwar sakeena ta k’ara mishi sannan ta samu wuri ta zuana.
Kwanan zaune tayi yanzu rana ta fito sosai bata ji d’uriyar kamal ba tun da daddare da ya shiga gidan, Allah ya taimake ta period d’inta kad’an yake zuwa bata b’ata jikinta ba sosai, k’ishin ruwa ta fara addabar ta, har ta fara zama weak, tana kwance dai dai saitin k’ofa, tana jiran ikon Allah, sai dai ta kulle idanunta tayi bacci ta farka ba abunda take iya yi, har duhu ya fara, yanzu bama ta iya d’aga koda d’an yatsan ta saboda tsabar kishin ruwa, gaba d’aya ta zama dehydrated, yarda take jinta bata da wani k’arfi, daman lafiya bata gama isarta ba, har ta k’addarawa kanta mutuwar ta tazo, a haka ta cigaba da kwanciya har dare yayi sosai, ta tabbata ta kusa awa 30 a d’akin in ma bata fi ba, yanzu har numfasin ta ya fara sama, hawaye ma sun kasa zuba saboda ba ruwa a jikinta, ko bud’e idanunta ta kasa yi, sakeena ta barwa Allah komi ta cigaba da kwanciyar ta tana addu’a dukda da kyar take samu tayi,
STORY CONTINUES BELOW
Can sai ji tayi an bud’e k’ofa, wani ta gani a tsaye kamar kamal, uku uku take ganinshi, tana gani ya k’araso ya d’auke ta cak, irin d’aukan bridal style d’innan, sakeena bata da k’arfi bama ta iya yin gardama dashi ba, a haka tana jikinshi har suka isa bedroom d’inshi, ya ajiye ta akan gado, sannan yayi wurin dressing mirrior d’inshi ya d’auko ruwa, ya k’ara dawowa inda take, ya ajiye ruwan a bedside drawer sannan ya k’ara d’aga ta ya jingina ta da headboard d’in gadon shi, sakeena kuwa ba abinda take sai binshi da kallo, dan yanzu sai dai yayi yarda zai yi da ita dan bata da energy ko kad’an, jin robar ruwan tayi a bakin ta saurin kwada kanta tayi gefe, jin wannan muryarshi ta wace take masifar tsana,
“In baki san ki mutu gwanda ki bud’e bakin ki kisha ruwan nan”
Wani zagi ta aika mishi a k’asan ranta, ya bala’in raina mata hankali, me yake nufi da ita nema tukun, ya kulle ta a d’aki har na tsawan awa 30 yanzu kuma yanayi kamar ya damu, k’ara jin robar ruwan tayi a bakinta, ta k’ara matsar da kanta, da kulle idanunta, bala’in so take ta sha ruwan amma taurin kanta ya hanata, tana wannan tunanin kanta ankara sai jinta tayi akan cinyarshi,, da sauri ta bud’e manyan idanunta ta sauke akanshi, tare da zaro su waje, kamal kuwa murmushi ne d’auke akan fuskarshi tasan murmushin bana komi bane in banda na mugunta,
“Na lura na biye miki zaki b’ata mun lokaci”
Kan ta ankara ya toshe hancin ta yarda bakinta zai zamana yana bud’e bayan k’ankametan da yayi a jikin shi, yarda baza ta kwace daga jikin shi ba, sannan ya shiga tiltila ma cikinta ruwa, sai da ya tabbata tasha ruwan sosai sannan ya sake ta, yana sakin ta da saurin dorowa daga kan cinyar shi, tsoro a fuskarta b’aro b’aro, idanunta akan kamal wanda yake faman kab’e jikinshi saboda ruwan ya jik’ashi, wani haushin shine ya k’ara kamata yarda taga ko ajikinshi, tana gani ya mik’e, ya k’ara ajiye empty robar ruwan akan bedside drawer, ko kallon ta baiyi ba ya shiga bathroom d’inshi, sakeena kuwa ta tana can lungun gadan duk a takure, tsoro fal cikinta, ga period dinta dake faman zuba, tayi mamaki da bama tayi staining kayan jikin kamal ba, ya d’an jima a ciki sannan ya fito, yana fitowa yayi hanyar inda take, ai ina tsoro ya k’ara kamata ta k’ara shigewa bango, kamal kuwa ya haye kan gadon a tsaye ya fara taka katifar har ya isa wurin ta sannan ya k’ara daukan ta a hannunshi,
“Wai mai matsalar shi da d’auka na ne”
Sakeena ta fad’i zuciya, ita kuwa yau tama kasa mosti koyi mishi gardamar ya ajiye ta, har ya sauko daga kan gadon tana hannunshi suka shiga bathroom d’inshi, ai tana ganin sunyi hanyar bathroom hantar cikinta ya k’ad’a, sai a lokacin da fara mosti dan ya ajiye ta, shi kuwa bai kula ta ba har suka shiga ya ajiye ta a k’asa, amma hannayen shi na ruk’e da ita, waiwaiye ta fara, tana kai idanunta wurin bath tub d’in taga ruwa cike a ciki, wato ruwan wanka ya had’a mata, sauri tayi ta maida idanunta kanshi, dan kasa gane kan abun, shi kuwa hake yake gaba d’ayan shi bashi da fasali, yanzu me ya saka yake kula da ita bayan ya gama wulaqanta ta, jin hannushi tayi a jikinta yana shirin cire hijab d’inta, ai da sauri tayi baya, har ta fara juyi zata fad’i saboda wani jiri da ya kamata, amma kan ta fad’i kamal yayi saurin ruk’ota tare da dawo da ita jikinshi, tana jin jikinta ya tab’a kirjinshi ta k’ara yin baya, sai dai yanzu bata kwace daga hannunshi ba saboda ya ruk’eta sosai, kunya ce ta rufe ta, wai me ya same shi yau d’innan, anya kamal ne wannan, mai da manyan idanunta tayi kanshi taga shima nashi manyan idanun nakan ta, zuciyar tace ta fara mahaukacin bugawa a k’irjinta, fuskar shi d’auke da murmushi, kamar yana jin d’ad’in abunda yake faruwa da ita, ita tasan duk duk sabon salan muguntar sa ce,
“Baza kiyi wankan bane”
Yarda yayi maganar harda d’aga mata gira, wani haushin shi taji ya k’ara kamata,
“Ka sake ni, zan iya tsayawa da kaina”
Ga mamkin ta sai taga ya cire hannushi daga jikinta harda d’aga su sama ba wata gardama, ai kuwa yana cirewa ta k’ara baya zata fad’i, saboda har lokacin bata da wani k’arfi, sai da ya tabbata ta kusa kaiwa k’asa sannan da sauri ya k’ara kamata, bayan ya sakar mata wani murmushi da duka dimples d’inshi sai da suka fito,
“Ina sakin ki fad’uwa zakiyi, in kuma kina so in sake ki sai na kyale ki yarda in kaka tashi fad’uwa sai ki buga kanki da bangon can dan tiles d’in nada sartsi, gobe da safe muyi janaizar mutuwar ki”
Wata muguwar harara da daka mishi, kamal kuwa gaba d’aya fuskar shi na d’auke da murmushin zolaya, duk abinda take baya damun shi, da dukkan alamun abun dad’i ma yake mishi,
“Ina da bathroom d’ina zanyi wanka a can”
Dan dole tana buk’atar abubuwa a halin da take ciki, baza ta tab’a iya wanka a band’akin shi ba, fara takawa tayi a hankali tayi hanyar fita daga band’akin, har lokacin hannayen kamal na ruk’e da ita, tana ji ya k’ara jawota jikinshi gaba d’aya ta shige, sannan ya d’ora hannun d’aya akan k’afad’arta,
“Nasan in k’ara d’aukan ki duka zaki kai mun sobada haka ki ruk’eni sosai dan in har na sake ki zaki fad’i”
Share shi tayi dan yanzu ba abunda take buk’ata illa tayi wanka, kuma ta biye mishi sai da cusa mata bak’in ciki ne, a haka kamal ya ruk’eta yana mata jagora har ya kaita bathroom d’in d’akinta.
Yana jingine makeken gadon shi, hannun shi d’auke da wani book yana karantawa, so yake yayi sauri ya gama ya kwanta dan gobe zai fara zuwa office, wayar shi ce ta d’auki yin ruri da take kan bedside drawer d’inshi, kamal a hankali ya juya ya d’auko tare da sakin murmushi me mugun k’ara mishi kyau, bayan yaga sunan da ya fito akan screen d’in, a niste ya latsa wayar ya saka a kunnan shi”
“Ya kamal guess what?”
Abunda ya fara ji kenan, ba sallama ba gaisuwa, matsalar shi da kausar kenan, ba ta da tunani wani sa’in,
“Yaushe guess what ya koma gaisuwa da sallama kausar”
Yana ji tayi shiru, allamun tana so ta bashi hakuri, shima shiru yayi yana jiran ta,
“Sorry, wallahi excitement ne ya saka ban gaishe ka ba”
Kamal girgiza kanshi yayi, yana ji ta fara gaishe shi, shima d’in amsawa yayi, sai da suka gama gaisuwar su tsab sannan kausar ta k’ara cewa,
“Kasan baban su saudat da ya sajida ya rasu d’azu da safe, a kano za ai zaman makokin”
Kamal d’aga kanshi yayi kamar k’anwar tashi na kusa da shi, su saudat ba wasu bane illa family friends d’insu, a daa sun zauna a unguwar su a kusa dasu shine dalilin da ya saka, kausar da kamila yin k’awance dasu da har suka saka mami ma ta zama k’awar mamansu, abba ya zama abokin babansu, sunyi zaman abuja amma yanzu gaba d’aya sun tattara sun dawo kano,
“Eh, mami ta kira d’azu ta gaya mun, daman nace gobe bayan na dawo daga office zanje gaisuwa”
“Muma gobe zamu zo, flight d’inmu da safe ne, dan haka kai da ya sakeena kuyi shirin k’arbar bak’i”
Da mugun sauri, ya d’ago daga jinginan da yake, zuciyar shi tace wani dum, bai tab’a zatan zasu sauka a gidan shi ba saboda sanin halin mami baza ta barsu ba gwanda su kwana a hotel dan kawai kada su takurawa sakeena, kausar ce ta k’ara magana kamar tasan mai yake tunani,
“Mami tace mu zauna a hotel, ya kamila ma, amma nayi ta rokonta da ta bari muzo gidan ka, a karshe dai sai da na had’a ta da abba sannan ta bari”
Da murnar ta tayi maganar, kamal lumshe idanunshi yayi dan yana ruwa, ta ina zai fara, bashi da ko kwayar shinkafa a gidan duk ya kwashe yakai gidan marayu, ga sakeena, yana tunawa da sakeena na can a kulle yayi zumbur ya mik’e hankali a tashe, in har k’annanshi suka zo suka ga mai yake mata baza suji dad’i ba kuma dole zance ya koma wurin mami da abba, in kuma suka ji shikenan tashi ta k’are, sauri yayi yai ma kausar sallama tare da cewa sai sun k’araso, sannan ya fita daga cikin gidan da sauri.
———–
Bayan ya kaita band’aki ya sami wuri akan bedside drawer d’inta ya zauna, dole ne yayi mata kirki har su kausar su zo su tafi dan kada ta tona mishi asiri, dauko wayar shi yayi ya fara dannawa da zaman jiranta, ta dad’e a band’akin sosai har saida ta fara bama kamal haushi, dan yama gaji da duba agogo, shifa shi ya saka baya shiga sabgar mata saboda akwai su da shegen iyayi, taya mutun zai zauna a band’aki har na kusan awa d’aya, tashi yayi da zaman da yake dan yanzu ya harzuk’a, sannan yayi hanyar bathroom d’inta, ya sa hannun zaiyi knocking k’ofar yace mata tayi sauri a dai dai lokacin ta bud’e k’ofar, ko wace gab’a ta jikin kamal tsayawa tayi cak saboda abunda yake gani a gabanshi, tana cikin wani d’an k’aramin towel, gashin kanta da yake a jik’e duk ya sauka a bayan ta, hannunta d’aya ruke da wani towel ga ruwan da yake d’iga a jikinta, bak’ar fatar jikinta tayi wani kyau da ita ko daga ido, zuciyar shi ta fara mahaukacin bugawa, bugawar da bai tab’a ji tayi ba, bayan wani sabon abu da yake ji ya mamaye jikin shi, wani abu ne ya taho tunda ga kafarshi har tsakiyar kanshi, ya kasa d’auke idanunshi daga kanta dukda yasan kallan nata ne ke saka shi jin abubuwan da yake ji, a lokacin sakeena ita kuma ta kulle k’ofar da k’arfi a daidai fuskar shi har da y’ar k’aramar k’arar ta, yana ji tayi maganar ta cikin bathroom d’in,
STORY CONTINUES BELOW
“Me kake yi har yanzu a bedroom d’ina”
Daba dan tayi magnar da k’arfi da kuma iho ba da yasan bazai ji ba dan gaba d’aya baya cikin hankalin shi, ya d’an jima a wurin ya k’urawa k’ofar bathroom d’in ido, can kuma da sauri kamar wanda aka tsikarawa allura, ya fita daga d’akin yayi bedroom d’inshi, bathroom ya wuce a guje yayi sink, ya kunna famfo ya fara zubawa fuskar shi ruwa, ya wanke fuskar shi a k’alla yakai sau talatin amma har yanzu bai daina jin abunda yake ji ba, jikin shi wani iri yake mishi da bazai iya misaltawa ba bayan har lokacin zuciyar shi bata bar bugawa ba, gaba d’ayan shi a rikice yake, a hankali ya d’ago da idanunshi ya sauke akan mirror, idanunshi sun k’ad’a sunyi jaa, a hankali ya furta,
“Meke damu na ne?”
Fara zage band’akin shi yayi, yaje ya dawo ya kasa zama, amma still har lokacin bai bar jin abunda yake ba, fita ya k’arayi ya koma bedroom d’inshi ya cigaba da zagaye, kamal yakai minti ashirin yanan abu d’aya amma har lokacin jinshi yake daban, da yaga dai har lokacin ya kasa dawowa yarda yake, ya samu wuri ya zauna akan godo tare da kwanciya da bayan shi, ya lumshe manyan idanunshi, sannan ya saka dantsen hannunshi ya kulle fuskar shi, amma mai, hotan ta tana tsaye a cikin towel ne yayi mishi gezau, kamal da mugun sauri ya mik’e, ya d’ora hannayenshi a kanshi tare da jan sumar gashin shi wai shi a dole sai ya daina jin abunda yake ji, ya jima yana abu d’aya ya kasa sukuni, sannan can ya gane ya fara addu’a, da kyar ya dawo cikin hayyacin shi, yana jinshi dai dai, yayi hamdala, a cewar shi daman shed’an ne, ba daga shi bane sannan yayi kitchen.
Zuba mata abincin da yayi order d’azu a plate daman kad’an yaci, ya mata warming a microwave, sannan ya saka spoon, yayi hanyar fridge ya dauko ruwa ya fito, hanyar bedroom d’inta yayi, tunda ya fara yin hanyar d’akinta zuciyar shi ta dawo bugawa a k’irjinshi, kamal share wa yayi, yana zuwa k’ofarta yayi knocking, sai da ta barshi a tsaye yafi na minti biyar, spare key d’in d’akinta yana cikin aljihun wandon shi amma ya kasa d’auka ya bud’e shi kanshi baisan me ya saka dalili ba, amma kuma haushin ta yake ji, daba dan yana so su d’an daidaita kan su kausar su zo ai da bazai ma zo wurin ta ba tana mishi wulaqanci, yana cikin tunani yaji k’arar muk’ulli a hankali k’ofar ta bud’e, sakeena na tsaye, a cikin wani k’aton hijab ba abunda take mishi in ba binshi da wani mugun kallo ba mai d’auke da harara ta kuma tsana, kamal kuwa murmushi ya sakar mata, yasan zai k’ara k’ullar da ita ne, sannan yabi ta gefan ta ya shiga cikin d’akin, ajiye mata abincin yayi akan bedside drawer sannan ya juyo, tana tsaye a wurin da ya barta, idanunta kaf akanshi, yaga tsoro a cikin su,
“Kace baza ka bani abinci ba, yanzu ka canza shawarar ka ne?”
A hankali ya fara takawa har ya matso kusa da ita, manyan idanunshi nakan ta, yana gani ta fara jan baya, sai da ya tabbata fuskar shi na d’auke da murmushi sannan yace,
“Eh, na saka miki poison yarda in har kinci zaki mutu na daina ganin fuskar ki”
Yana gani ta zaro manyan idanunta waje masu d’auke da tsaro, kamal kuwa da yaga yanyin da take na alamun ta yarda da maganar shi bai san lokacin da ya saka dariya ba, sai da yayi dariyar shi me isar shi sannan ya d’ago ya maida idanunshi kanta, kallon shi take da harara, kamar zata shak’e shi, girgiza kanshi yayi sannan ya koma gurin abinci ya d’auko ya juya ya maida idanunshi kanta, spoon ya saka ya d’ibo abincin yakai bakin shi, idanunshi nakan ta har lokacin ya fara taunawa har ya had’iye, sai da aka fi sakwan talatin sannan yace,
“Kinga naci amma kin ganni lafiya k’alau”
Kallon harara ta cigaba dayi mishi, zuciyar tafasa take in har tana hararar shi dan bala’in raini ne, amma kuma ya share ta, bazai ce mata k’alla ba, zai ci gaba da binta har k’anan shi su tafi, maida abinci yayi kan bedside drawer sannan ya juyo ya koma inda take a tsaye, fuskar shi na dauke da murmushin nan ya fara cewa,
“In gaya miki wani abu?, ke zaki mutu in har baki saka wani abu a cikin ki ba dan yanzu kin kusa 40 hours ba abinci”
Yana gani ta nanad’e hannunta akan k’irjinta bayan wannan kallon da take mishi,
“Lets get straight to the point, me ya saka kake mun kirki? Dan nasan ba halinka bane”
Maganar da tayi ta bala’in bashi mamki, lallai she is bold, idanunta basa d’auke da komi sai dai alamun tambaya, tunda she wants them to be straight forward bari shima ya gaya mata dalili,
“K’anne na zasu zo gobe, bana so su gane akwai wata matsala tsakanin mu”
Murmushi ne ya fara bayyana a fuskar ta a hankali, zuciyar kamal ce ta fara wani bugawa har yana jin sautin ta a kunnan shi ganin murmushin ta dan yau ne na farko, ya bala’in k’ara mata kyau, wannan abun da yaji d’azu ne ya k’ara dawowa ya mamaye duk wani sansa na jikinshi, haka ya bita da kallo yana gani ta saukar da kanta k’asa, ta d’an dad’e a haka sannan ta d’ago ta maida idanunta kanshi,
“Allah wa dai dame irin halinka”
Tsana na d’auke akan fuskar ta, yarda tayi maganar itama na d’auke ta tsana, duk abinda kamal yake je nema yayi ya rasa, zuciyarshi ta daina bugawa ta koma wata irin tafasa, jijiyoyin fuskar shi da wuyan shi suma suka fara fitowa bayan ya had’e fuskar shi tamau kamar wanda bai tab’a dariya ba, duk saboda abunda tace ya mugun b’ata mishi rai, baisan lokacin da ya d’amk’e hannunshi ba, wani irn azalzala k’irjinshi yake mishi, yana gani ta wuce ta gefan shi,
“Naji me kace, zaka iya fitar mun daga d’aki?”
Da sauri ya fita daga d’akin ko juyawa baiyi ba, ba wai dan abunda tace ba, dan kawai ya tabbata in har ya k’ara sakwan d’aya a cikin shi zai iya yi mata wani abun da zai saka shi dana sani, da k’arfi ya buga mata k’ofar yayi hanyar bedroom d’inshi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]