[Advertisements⬇️]

ZAFIN RABO CHAPTER 7 BY SAKIEYY - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZAFIN RABO CHAPTER 7 BY SAKIEYY

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana zaune akan katifa da had’a cinyoyinta da k’irjinta, ita kanta bata san awani nawa ta shafa tana yin abu d’aya wato kuka kenan, yanzu kanta ba irirn sarawar da baya mata, jin da tayi an bud’e k’ofa ya saka ta saurin mik’ewa, ka ganta gaba d’ayan ta a tsorace take, duk ta birkice bayan fargabar da ta cika mata ciki, ummeeta da sisi ta gani a tsaye, sakeena jikinta ne ya hau rawa ganin irin kallon da suke mata, hantar cikinta ta k’ara kad’awa,+

“Mik’a mata kayan”

Sisi da fad’a a gadaran ce, haka ummeeta ta ajiye mata su a kan katifar, sakeena kuma ba abunda take in ba binsu da kallo ba, idanunta d’auke da alamun tambaya

“Ki kintsa cikin kayan nan dan nan da k’aramin lokaci zakiyi bak’o”

Zuciyarta wani mahaukacin bugawa tayi, tare da fara harbawa kamar zata tsage daga k’irjinta, yanzu idanunta sun k’ara cika taf da k’walla, tayi zuru zuru da ita ba abinda take sai bin tsinaniyar rigar baccin da take a ajiye akan katifar da ido, ko yau da yake daran farkon ta ita da kamal wanda igiyar shi uku take d’aure akanta kuma koda tana gidan shi, baza ta saka irin wannan kayan ba, balle har ta d’auka ta saka ma wani banza k’ato, wanda ba muharamin ta ba, maganar sisi ce ta dawo da ita duniyar tunanin ta,

“Baza ki d’auka ki fara shirin ba ko sai na saka yaran nan sun tub’e ki sun saka miki da kansu ne”

Ji tayi jikinta ya fara rawa, barin ma yarda taga fuskar sisi bata d’auke da alamun wasa, sakeena k’ara rikicewa tayi, ba abunda take fad’i a ranta in banda nashiga uku, ba irin tsinuwar da bata aikawa kamal ba, duk da a rud’en da take bata da shirin d’aukar rigar ta saka, a hankali ta bud’e bakinta ta fara ma sisi tambaya,

“Ki gaya mun kamal ne ya baki umarnin a cimun wannan irin mutuncin”

So take taji amsa, so take ta k’ara tabbatar ma kanta wani irin mugun namiji ta aura, Tana jiran taji amsa kawai taga sisi ta tintsere da dariya ta d’an dad’e tana abu d’aya kamar tab’arb’iya, sannan can kuma ta had’e fuskar ta tare da juyawa dayi ma ummeeta wani irin kallo, kan sakeena ta ankara kawai taga doguwar rigar atamfar dake jikinta a k’asa, tana tsaye daga ita sai bra da underwear, ga ummeeta ta take shirin b’alle ma b’allin bra d’in jikinta , tsirara suke san yi mata da gaske, wata irin k’ara ta saki tare ta saurin tsugunnawa, da rugume jikinta, kan kice ma hawaye sun fara ambaliya a fuskar ta,

“Yi miki tsirar kad’an ne daga cikin aiki na, dan haka in zaki tashi ki saka kayan nan da kanki tunda sauran mutunci to in kuma kinga baza ki iya ba in saka ta ta cigaba da abinda ta fara”

Tsigar jikinta wani irin tashi take, amma gaskiya way’annan mutannen laananu ne, su basu damu da suga tsaraicin taba wato, ba abunda zuciyarta take in ba bugawa ba tsoro fal cikin ta, amma har lokacin sakeena bata da niyar canza ra’ayin ta na baza ta saka kayan ba, ko kashe ta zasuyi da kanta dai baza ta tab’a kai kanta ga halaka ba, jin ummeetan da tayi akanta ne ya sata saurin k’ara damk’e jikinta wuri d’aya, tana ji hannuwa sunkai hud’u suka rik’eta, bama tasan lokacin da sauran y’an matan suka shigo ba, wani hawaye ne masu zafi suka k’ara zuba, ita yau za’a tub’e ma kaya me yakai wannan cin mutunci, shure shure ta fara tana ihon da su kyale ta, amma ina sarkin yawa yafi sarkin k’arfi, haka suka cire mata sauran kayan ta suka barta a cikin pant d’inta, sakeena ba abunda take in banda kuka me abun tausayi, jikinta wani rawa yake tsabar k’arfin kukan, haka suka saka mata wannan jar rigar bacci, wacce da ita da babu duk d’aya ne a wajan ta, kan ta k’ara ankara taji an d’aga ta cak, wani shure shuren ta fara, dan a ajiye ta, amma baza ta tab’a iyawa da k’atotan gardin da ya ruk’e ba, wata irin tashin hankali ta shiga da taga namijin da ba muharaminta ba ya ganta a cikin wannan yanayin bayan kayan dake jikinta da suke nuna tsaraicin ta b’aro b’aro, kamal ya saka yau an tsige mata duk sauran mutuncin ta na y’a mace,

“Sai da aka gaya miki ki saka kayan tunda sauran mutuncin ki amma taurin kai ya hanaki”

Tana ji ummeeta na fad’a, ita kuma bata bi ta kanta ba sai faman saka hannunta take tana shirin kulle jikinta a haka har suka shiga wani side daban a gidan aka shigar da ita wani bedroom sannan wannan gardin ya jefa ta akan gado, yana ajiye ta ta k’ank’ame jikinta wurin d’aya, tana ji ya fita ya kullo k’ofar, sakeena na ganin haka ta duro daga kan gadon tayi wurin k’ofar a guje, ta murd’a handle d’in amma an kulle ta waje, tuni ta fara buga k’ofar tana rok’an su da Allah da annabi su bud’e mata, haka akayi banza da ita har ta gaji ta k’ara zubewa a k’asa ta cigaba da kukanta, bata san lokacin da ta shafa a wurin ba, tana fara jin k’arar takun mutum gabanta ya fara fad’uwa, zuciyar ta ta fara wani irin bugawa, da mugun sauri ta mik’e ta yayimo duvet blanket d’in dake kan gadon ta kulle gaba d’aya jikinta harta kanta wanda baya d’auke da d’ankwalli, dube dube ban d’anki ta fara yi yarda zata iya shiga ta kulle kanta amma ba band’aki a cikin d’akin, ta taji k’arar key a jikin k’ofa ya k’ara saka ta saurin shigewa jikin bango, haka ta rungume jikinta wurin d’aya tare da k’ara damk’e duvet d’innan, ta sunkuyar da kanta k’asa tare toshe kunnanta da kulle idanunta, ko wane bil adama ne zai shigo d’akin bata san jin muryarshi balle ta ganshi, in ka ganta a lokacin ko mara imani ne sai mutuk’ar tausayinta ya dakan maka zuciya, tana ji aka shigo ko da wasa bata d’aga kanta ba, ba abunda take in banda add’ua ga jikinta da har lokacin bai bar rawa ba saboda tsoro, jin mutum d’in da tayi a kusa da ita ya k’ara saka ta shigewa jikin bango tare da cigaba da addu’ar da take,

“Duk tsoro ne ya saka ki yin haka?, kada ki damu nan dan lokacin kad’an zan tabbata kin nemeshi kin rasa”

Dukda ta kulle kunnanta tana d’an tsintar maganar shi, ji tayi hantar cikinta ta k’ara kad’awa, hawaye sun sake jik’a duvet d’innan, jikinta ya k’ara kyarma, sakeena ta k’ara rungumo jikinta wuri d’aya, kamal ya gama da rayuwar ta, kamal azalimi ne, haka kawai bata ji ba bata gani ba, wannan wace irin mugunta ce yana ji Allah zai barshi abunda yake shirin sawa a aikata akanta, jin wata irin tsanar shi tayi tana bin jinin jikinta, Allah wadaran da irin mai halinshi, Mommy da daddy suka san irin mugun da suka aura mata sai sunyi mutuk’ar dana sanin, danshi kamal a mugayen mazan ma ya cira tuta, dan ita tunda take a rayuwarta bata tab’a ji ko ganin inda miji yakai matar shi ta sunna wurin karuwai ba duk tsanar tan da rashin santan da yake, ko a litafi ko a film.

Jin hannun da tayi akanta ne ya saka ta saurin d’agowa da idanunta da suke d’auke ta tsan tsan tsoro da fargaba, wanda ta gani a tsugunne a wurin ne ya saka hankalin ta k’ara tashi, tare da k’ara zaro manyan idanunta saboda abun mamakin dake gabanata, me ya kawo shi wurinan me yake yi anan? Haka ta fara jera ma kanta tambayoyi, a hankali ta furta sunan shi.Yana kwance yana sharar baccin shi kamar wanda bashi da wata damuwa, ka ganshi ya k’ara wani fresh, ga sajen fuskar shi da ya k’ara zama, ya k’ara haske da wani masifaffan kyau tsabar baya fita kullum yana gida, ga bazai fara aiki ba sai next week, rurin da wayar shi ta fara yi ne ya farkar dashi daga dogan baccin da yake, bai iya bud’e idanunshi ba saboda sauran baccin dake cikin su haka ya fara laliban wayar shi har ya samu ya gani ta, duk bai kalli screen d’in ba yaga suna haka kawai ya danna kan green button d’in ya maida wayar kunnan shi, muryar da yaji ce ta saka shi saurin wartsakewa tare da mik’ewa, daga kwanciyar da yake,

“Ku bakwa neman mutane ne? Tun yaushe muke jiran muje kiran ku amma shiru har anyi kwana biyar”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Ji yayi gabanshi yayi wata irin mummunar fad’uwa, zuciyar shi ta fara bugawa da ya tabbat ma kanshi muryar mami yake ji,

“Mami wallahi ba haka bane, yidimomi ne sunyi yawa”

A rud’e yake amma a dake yayi maganar dan kada ta gane wani abu, jin da yayi tayi dariya, ya saka shi yin ajiyar zuciya, abunka da mara gaskiya,

“Ai harda zan saka makwabciyar ku hajia zaliha ta aika a duba mun ku ko lafiya dan naji shirun yayi yawa dana kirata tace ai tun washegarin ranar da muka kaita suma suka kama hanya suka koma rivers daman hutu ne ya kawo su”

Kamal wata irin dariya yak’e yayi tare da cewa Allah sarki, haka suka d’an gaisa da y’ar hira har da kausar, suka dunk’a tsokanar juna, can mami ta karb’i wayar,

“Wai ina surakar tawa?? Banji d’uriyar ta ba, mommin ta ma ta kira ni jiya tace itama bata neman ta,”

Wata irin zufa ce ta keto mishi, hanta cikin shi ta kad’a, yarda yake jin tsoron mutuwar shi haka yake jin tsoron fushin mami, yasan ranshi ba d’an k’aramin b’aci zai yi ba in har taji labarin abunda yake faruwa da sakeena, tuni wata k’arya tazo mishi,

“Screen d’in wayarta ne ya d’auke tun ranar da muka zo shi yasa bata kira ku ba, amma yau zanje in k’arbo mata daga wurin gyara, ga yanzu tana bathroom dana bata kun gaisa”

Yarda yake zufa duk sanyin ac d’in dak’in sai ya baka mamaki, addu’a kawai yake a k’asan ranshi Allah ya saka mami ta yarda da k’aryar shi, jin maganar ta da yayi ya saka shin yin hamdala,

“Tom shikenan, in har ka karb’o wayar kace ya kamata da kira gida su gaisa, nima zan kira anjima na gaisa da ita”

Suna sallama ya kashe wayar, tare da k’ara maida numfashi, can ya tashi yayu hanyar bathroom, sai da yayi wankan shi tsab ya fito, yayi shigar shi cikin wani bak’in yadi, yayi masifar kyau ga farin shi ya k’ara fitowa, dole ka k’ara kallon shi in ka ganshi saboda ya had’u iya had’uwa, bayan ya saka hula tare da d’ora rolex d’inshi a hannunshi, ga k’anshin designer turaren shi da cika d’akin yayi wajan bedside drawer d’inshi, jawota yayi ya d’auko wayar sakeena wace take a kashe a wurin sannan ya saka ta a aljihun wandon shi, dole bayan sallar juma’a ya ziyarce ta.

——–

Yana cikin motar shi da take pake a harabar gidan yana jiran fitowar hajia maimuna, bai dad’e da jiran ba ya hango ta tana taho ta mirror d’in motar shi, tukan ta k’araso ya fito daga cikin motar ya jingina da ita tare da had’e hanna yanshi akan fad’ed’an k’irjinshi, fuskar ji d’aure take tamau, ba alamun dariya, tana isowa ta fare washe mishi hak’ora, kamal ya k’ara had’e fuskar shi, koda ta fara gaisawa dashi sama sama yake amsa mata dan shi ba abunda ya kawo shi ba kenan, da sisi taga haka, shine da fara mishi bayani,

“Daman yanzu nake shirin na kira ka a waya, dan yarinyar kafa ba lafiya, tun bayan abunda ya faru ranar da ka kawota ta canza, ko kukan da da take ta daina, sai dai kullum tana kan abun salla, tana ta addoin, bata cin abinci bata shan ruwa, jiya da yamma hadi ta same ta a sume a band’aki, shine na kira wata nurse na samu ta saka mata drip, ga dai ta can har yanzu bata farfad’o ba”

STORY CONTINUES BELOW

Wanna d’an labarin da yaji ba k’aramin saka shi yayi ba a cikin farin ciki, amma sam baza ka gani a fuskar shi ba, yi yayi kamar baiji abunda tace ba, tare da mik’a mata wata nokia, irin mai touchlight d’innan,

“Sim d’inta na ciki, bance ki bar mata ba a wurin ta, wayar ta zama tana wurin ki duk wanda zai kirata ki bata tayi magana, kuma ki kasance kina wurin tana gama wayar ki amshe daga hannunta”

Yana gama maganar ya juya zai koma motar shi ya kama hanya, maganar sisi ce ta dakatar dashi,

“Baza ka shiga kaga yarda jikin nata yake ba”

Wani abun ne ya tsaya mishi, ya shiga yayi mata mene, wata zuciyar ta shawarce shi ya shiga ya gane ma kanshi halin da take ciki da idanunshi, juyowa yayi ya umarci sisi da ta kaishi wurinta, tunda ya shiga cikin gidan, y’an matan ke kallan shi, gaba d’ayan su sun saki baki sun bishi da kallo sai kace tsohon mayu, kamal wani mugun tsaki yaja a ranshi tare da k’ara had’e fuska, yana shiga d’akin ya ganta a kwance, idanunta a rufe bayan drip d’in dake manne a hannunta, kana ganinta kasan tana shan jiki, maida hanna yanshi yayi kan k’irjinshi ya k’ura mata kallo, gaba d’ayanta ta canza ta fita daga hayyacin ta, wani sabon farin ciki ne ya k’ara kamashi, ya dad’e yana kallonta can ya bud’e baki ya fara magana, sai dai yana farawa a dai dai lokacin ta bud’e idanunta ta sauke su akanshi, idanunsu cikin na juna, kamal ya k’ara kafeta da wannan manyan idanun nashi,

“Daga yau ko tak’i cin abinci ki saka a danne ta ayi mata d’ure kamar jaririya, ko ta amayo dashi ki tabbata kin maida mata shi bakinta, har sai ta cinye”

A hankali yake maganar kuma har lokacin idanun shi na cikin nata,

“Bana so ta mutu yanzu dan bata gama ganin rayuwa ba”

Yana gama fad’i ya juya yayi waje abunshi, zuciyar shi ta k’ara yin wani fari, tsan tsan anushuwa da farin cikin ya mamaye shi, bayan ya danna key motar shi ta bud’e, ya shiga ya kunna har ya fara jan motar, yaji mutum a gabanshi baisan daga ina ba, wani birki ya saka ya tsaya cak da motar, abunda ya gani a gabanshi ba k’aramin bashi mamaki yayi ba, sakeena ce a tsaye, gashin kantan ne mai yawa duk ya tashi, ba yanzu ya barta a kwance ba, fitowa yayi daga motar dan ranshi a mugun b’ace yake, sai da ya zo dab ta ita ya lura ko takalmi babu a kafarta, tana sanye da wani pink doguwar riga ta material, yana gani jini a kan hannunta da alamu tsige drip d’in tayi, ka ganta a wurin kamar zararriya, maganar da ta fara ce ta saka shi d’auke idannunshi da suke k’are mata kallo tare da mai dasu kan fuskar ta,

“Ka gaya mun mai ya saka ka saka aka tozarta ni, ka gaya mun mai na tab’a maka da ka saka aka cimun mutunci, aka zubar mun da k’imata ta y’a mace kamal”

Ba abunda yake in ba binta ta kallo ba danshi bala’in ganin k’arfin halinta yake da har ta taso a yanayin da take ta tunkare shi, yarda take a wurin yana tab’a ta yasan fad’uwa a k’asa zatayi dan daga ganinta ba wani saurin k’arfi a jikinta, saura k’iris ya fashe da dariya yarda yaga da dage bata san hawayen da suke shirin zubowa su zuba, shiru yayi kamar bazai amsa taba, can kuma ya fara

“simple, abunda kika mun nake ramawa”

Yarda yayi mata maganar ko ajikin shi, shima duk yarda baya so ya nuna farin cikin shi yanzu ya fara nunawa dan fuskar shi d’auke take da murmushi, yarda yaga ta k’ara daka mishi wata harara ya tabbata ya k’ara k’ullar da ita ne, amma maganar da tayi ne ya katse mishi duk wani nishad’i da yake ciki,

“Bansan ta inda ka zama azalimin namiji ba dan nasan daga gidan tarbiya ka fito, dan da tarbiya nasan kamil”

Ta farar d’aya idanunshi suka kad’a sukayi jaa, suka canza kama, farar fuskar shi itama tayi jaa bayan k’ara had’etan da yayi, a rayuwar shi ba abunda ya tsana irin sunan kamil ya fito daga bakinta, a hankali ya furta,

“Me kika ce?”

Yarda yayi maganar sai ya saka ka jik’e da gumi bayan kallon da yake binta dashi, yana gani tsoro ya fara bai yana a fuskar ta, amma da mamkin shi ta k’ara yin wata maganar,

“Da kamil nada rai yaga abunda kake kamal da sai ya ji ciwon had’a jinin da yayi dakai dan ya tsani maza masu irin halin ka”

Wata irin tafasa zuciyar shi ta fara, bayan zafin da take, hannunshi ya damk’e dan kada ya kai mata duka, baya dukan mata da a wurin sai yayi mata dukan mutuwa, lumshe manyan idanunshi yayi ko zuciayar shi zata daina azalzala shin da take, da kyar ya iya bud’e su, a hankali ya fara takwo har ya iso daf da ita,

“Kada ki ki k’ara ambatar sunan kamil a gabana dan zan zubar miki da hak’oran ki yarda baza ki k’ara mafarkin bud’e bakin ki ba ballanta na har ki iya magana”

Har wani huci yake yana maganar, ga jijiyoyin wuyanshi da suka fara fitowa dan tsabar baccin rai, yana ganin jikinta ya fara rawa, shi yasan fusakar shi bata dad’in kallo in har ranshi ya b’acci, yarda kamal ke kallanta kamar zai shak’eta, tsoro kuma ya gama rufe fuskar sakeena, har yana ganin yarda gumi ya fara zuba a fuskar, sai dai ya gama mata wannan mugun kallon nashi, kuma ya tabbata rashin kunyar tata ta tsaya bata da sauran abunda zata ce mishi, sannan ya juya ya koma motar shi, yana shiga ya kunna ta ya fusga a guje yabar gidan daman already gate a bud’e yake, da kuwa sakeena batayi saurin matsawa ba da sai yayi gaba da ita.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]