[Advertisements⬇️]

ZAFIN RABO CHAPTER 10 BY SAKIEYY - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZAFIN RABO CHAPTER 10 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bata tashi daga barci ba sai 10, tana farkawa tayi hanyar bathroom d’inta ta tsara wankan ta sannan ta fito, tayi shiriya cikan wata doguwar riga navy blue and pink ta material ta saka mayafi sannan tayi duk wani abunda ya zaman mata aladarta ta fito daga d’akin, amma sai da ta tabbata bata ji d’uriyar kamal ba, kitchen ta fara zuwa dan samar wa cikinta abunda zata ci, d’aura ma kanta tea tayi sannan ta d’auki bread tayi sandwich, sai da abincin ta yayi taci sananan ta k’ara dawowa kitchen d’in ta shiga dube dube, store d’in mak’il yake da kayan abinci da drinks ba abunda babu, tana bud’e fridge shima a cik’e taga su fruits, da vegetables da snacks da wasu drinks d’in, tana bud’e freezer itama tagan ta cikin da nama, su kaza su kayan ciki da dai suaran su, duk basu fara k’ank’ara ba alamun ba’a dad’e da zuba su ba, fitowa tayi da kayan cikin da kaji guda biyu ta ajiye a gefa, sannan ta shiga gyara su, sai da ta gyara su tsab sannan ta d’ora kayan cikin ta bar kajin a madanbaci, sannan ta fita daga kitchen d’in.

+

A hankali sakeena ta taka ta shiga d’akin kamal, tana shiga d’akin k’amshin turaren mad dad’in kamshi ya dake ta a hanci, share wa tayi ta fara duba d’akin, ganan yarda d’akin yake kawai ta girgiza kanta, haka ta shiga gyara mishi d’aki, ta canza mishi bedsheet, ta wanke mishi band’aki, ta shiga closet d’inshi ta gyara abunda zata gyara, kayan shi na dati ta saka a laundry basket, kan kice me d’akin yayi k’al dashi sannan sakeena ta fito, parlor ta k’ara gyarawa shima ta gama tayi d’ayan side d’in da bud’e d’aki d’aya ta gyara shi sosai shima ta wanke toilet, ta shimfid’a bedsheet shima daman ba komi akan gadon, sai da ta tabbata d’akin yayi k’al sannan shima ta fito da gyara parlor d’in saboda bata sani ba ko k’annan nashi zasuyi amfani dashi, sai da sakeena taga gidan ta yayi k’al kamar zaka zuba ruwa a k’asa kasha sannan ta koma kitchen, nan da fara yanke yanke yanken abunda zata iyayi da d’ora abubuwa da suk’e dad’ewa kan su dahu, ka ganta ta ta fita daga hayyacin ta aiki kawai take durk’a dan tunda ta tashi bata zauna ba, sai jin horn tayi, gabanta ne ya fad’i ta zata ka’annan nashi ne suka zo, d’aga idanunta tayi kan agogo taga hud’u da rabi, har lokaci ya jaa haka bama ta sani ba, fitowa tayi ta koma parlor dan ta l’eka, tana l’ekawa ta ji hankalinta ya kwanta, kamal ne ya fito daga mota, yana sanya cikin suit black, hannunshi ruk’e da wata briefcase, wata harara ta daka mishi ta window d’in tare da jan wani mugun tsaki, ta komawa hanyar kitchen,

“Ai kin banza, ya saka duk na wani rud’e na zata k’annan shi ne zasu shigo su ganni a haka”

Duk ta fad’i a ranta tana mita, haka ta koma kitchen ta cigaba da girkin ta, anyi kusan awa d’aya tun dawowar kamal, bata k’ara jin d’uriyar shi ba, sai jin knocking tayi, kan ta amsa an bud’e k’ofar, maida idanunta tayi wurin taga kamal a tsaye, ji tayi munfashinta yayi sama bata san daga ina ba kawai ganin shin da tayi da had’a idon da sukayi, yana sanye cikin manyan kaya yadin gray kana ganinshi kasan mai tsada ne hula na kanshi, ga turaren shi da duk ya mamaye gidan, haka ta bishi da kallo, bata san me ya saka ba,

“Nazo na gaya miki yanzu zanje na d’auko su, suna garin nan ma tun safe, so nan da magrib insha Allah zamu dawo”

Yana maganar yana duba agogan shi, sakeena da har lokacin kallon shi take ta kasa d’auke idanunta maganar shi ce ta dawo ta ita, tayi sauran maida idanunta wurin juya brown spaghettin da take, bata amsa shi ba, har ya k’araci tsyauwar shi ya fita, yana fita tayi wata ajiyar zuciya, ta fara tambayar kanta me ya saka tayi ta binshi da kallo, ta fi minti biyar tana ma kanta tambayar da ta kasa bama kanta amsa can kuma ta juya ta cigaba da aikinta, minti talatin duk ta kamala girkin da zatayi, ta shiga zubawa a flask tana kaiwa dining table, sai da ta tsara komi tsab ta koma kitchen ta fara dirk’ar wanke wanke, ita ta manta rabon da tayi irin wannan aikin, minti talatin shima ya d’auke ta ta gama tare da gyra kitchen d’in tsab, sannan ta d’auko ta kunna turaran wuta ko ina a gidan har d’akin kamal, da side d’in da k’anan shi zasu sauka, tana duba agogo taga shida da rabi, sauri tayi ta ajiye kaskon turaren wutan akan center tabla a parlor sannan tayi d’akinta da sauri dan tasan a kowane lokaci zasu iya shigowa, sai da ta kulle d’akinta da muk’ulli sannan ta fad’a bathroom ta tsala wankan ta, fito, a niste ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa, d’inkin yayi kyau, ta sakama fuskar ta hoda ta kwalli da d’an lipgloss, ta d’auko mayafi dan ya shiga da kayan ta d’ora akan ta bayan ta d’aura d’ankwali, ta feshe jikinta da turare sannan ta fito, tayi mamaki da bata ga koma a parlor ba dan yanzu har bakwai ta wuci alamun basu iso ba, k’ara kunna wani turaran wutan tayi ta shiga sakawa a ko wane lungu na gidan, tana cikin haka taji k’arar horn, sauri tayi ta leka ta window ta ga mai gadi na shirin bud’e gate, a hankali ta ja baya ta koma kitchen ta kulle, gabanta wani irin fad’uwa yake, sai ta d’an sami nustuwa sannan ta fito, ta ajiye kaskon hannunta a gefe, sannan tayi hanyar k’ofar parlor da ake ta dannan doorbell, murmushin yak’e ta saka a fuskar ta sannan ta bud’e k’ofar bayan tayi ajiyar zuciya.

STORY CONTINUES BELOW

Kyawawun k’annanshi, farare sol ta gane a tsaye dukan su na cikin bak’ar abaya, murmushi ta sakar musu tare da musu sannu da zuwa da basu wuri su wuce, suna wucewa da dubi kamal wanda yake a tsaye, manyan idanunshi kaf akanta, ko k’ifta su bayayi wata harara ta daka mishi ta juya zata bisu ciki, sai ji tayi ya jawo ta jikinshi, k’anshin turaren shi ya k’ara dakar mata hanci, a hankali taji wannan deep voice din tashi a kunan ta,

“Kin manta, yi zamuyi kamar ba wata matsala a tsakanin mu”

Wata ajiyar zuciyar tayi, a haka ta kyale shi, tana jikin shi har suka koma parlor, suna shiga ta gansu a tsaye a tsakiyar parlor d’in, murmushi ta musu, suma d’in murmushi na d’auke akan fuskar su, ga mamakin ta sai gani tayi k’aramar tayo kanta da sauri ta rungume,

“Finally, yau naga yayata da idanuna”

Yarda kausar tayi maganar sai da ta bana koma dariya a parlor d’in harta sakeena, sun dad’e a rungume sai can taji an kwace ta daga jikin kausar, tana d’aga idanunta suka had’a ido da kamal,

“Ya isa haka kausar kada ki, b’alla mun ita”

Yarda yayi maganar da wani irin salon shi, ga idanunshi basu bar kanta ba, hannunshi sak’ale akan k’ugunta, suara k’iris ta mishi wata harara, kawai sai gani tayi ya matso, bata ankra ba sai jin lips d’inshi tayi akan kumatun ta ya sumbata, tsigar jikinta wani tashi tayi saura k’iris ta kwace bada ban kamal ya mata wani mugun rik’o ba, a haka da kyar ta dake tayi murmushi yak’e sannan ta maida idanunta kan k’annan shi, da suke musu wani irin kallo alamun suna burge su, sakeena wata harara tayi a cikin ranta, sannan ta fara cewa

“Muje na kaiku d’akin da zaku sauka ko,”

Tana maganar ta kwace daga jikin kamal da k’arfi sannan tayi wurin babar ta karb’i akwatin ta, ta fara takawa d’ayan side d’in, tana ji babbar ta fara ce mata dan Allah da barshi zata jaa abun ta, ita kuwa sakeena tace mata bakomi a haka har suka isa guest bedroom d’in, suna shiga wani dad’in kamshi ya cika d’akin ga sanyin ac, sakeena ta samu ta ajiye mata akwatin a gefan gado sanan ta juya ta maida hankalinta kansu, fuskarta d’auke da murmushi,

“In kun gama abunda zakuyi, ku zo parlor abinci na nan na jiran ku”

D’aga mata kai sukayi, murmushi ta k’ra musu ta fita daga d’akin tare da jawo musu k’ofa, tana fitowa parlor taga kamal a zaune akan kujera, ya cira hular kanshi tv a kunne, wani mugun kallo tayi mishi sannan ta koma kitchen, fruit salad da zob’on da ta saka a fridge ta d’auka ta dawo dasu kan dinning sannan ta koma ta k’ara kunnan farfesun kayan cikin, sai da yayi ta zuba a wani katon plastic bowl sannan ta fito shima ta ajiye akan dinning a daidai lokacin k’annan shi suka fito,

“Sannu, mun saka ki aiki ko”

Kamila ta fad’i a yayain da ta k’araso dining area d’in ita da kausar murmushi na d’auke akan fuskar su, zata amsa kenan sai jin bayan ta tayi ya daki wani fad’ed’an k’irji gaba d’ayan ta ta shige, kamshin turaren shi ne ya sanar da ita ba kowa bane in ba kamal ba, numfashin shi taji da muryarshi taje a wurin wuyan ta,

“Eh mana, kun saka nun baby na aiki, gaba d’aya kun gajiyar mun da ita”

A wani hankali yayi maganar tare da k’ara rungumota da manna ta ajikin shi, kunya ce ta kama sakeena, wai dan Allah me matsalar shi ne, ko lafiyar auran su k’alau bai kamata ya dunk’a mata haka ba a gaban k’ananshi balle yanzu da dukan su ba abunda suka tsana irin junan su, a hankali ta cire hannanyrn shi daga kan cikinta ta juyo ta kai idanunta kanshi, shima d’in ita yake kallo, manyan idanunshi sunyi wani narai narai dasu, sai ki rantse da Allah akwai soyayya mai k’arfi tsakanin su,

“Lallai kamal, you are a very good actor”

Ta fad’i a ranta yayin da azahiri ta maida kallonta kan kausar da kamila, wanda fuskar su har lokacin akwai murmushi a cikin ta, hannunta na cikin na kamal saboda yak’i sakin ta tayi musu nuni da su zauna, tana gani sun zauna akan kujerar dining table d’in, ta maida kallon harara ta kanshi, wanda har lokacin bai d’auke idanunshi daga kanta ba, a hankali ta fara mosta bakin ta yarda k’anan nashi baza su ji ba ta fad’i,

“Ka sake mun hannu”

Tana gani ya girgiza kanshi, sakeena itama girgiza kanta tayi, zata saka hannunta ta kwace ya ruga ta, k’ara matsowa kusa da ita yayi, sannan ya kai bakinshi kan kunanta, ya rad’a mata a hankali,

“Zan sake ki, amma sai kin yarda zaki bani abinci a baki”10

Da mugun sauri ta fusge daga jikin shi, wani irin abu taji ya taho tunda kaf’arta har tsakiyr kanta da yayi maganar, harara dai ta k’ara daka mishi, shi kuma fuskar shi d’auke da murmushin mugunta, sauri tayi ta maida hankalinta kan su kausar ko sunga mai ya faru, taga hankalin su baya wurin suna hira, hamdala tayi tare dayin wurin su zatai serving d’insu, sai ganin kamila tayi ta mik’e,

“Ai ki sami wuri ki zauna, zanyi serving d’in kada ki k’ara wahalar da kanki”

Wani dad’i taji ya mamaye ta, gaskiya y’an gidan su basu da matsala ita kuwa bata san inda kamal yaje ya samu wannan mugun halin nashi ba dan ko kamil kirkin shi yayi yawa,

“Bakomi Allah, ku ne da gajiya tunda ku kuka yi tafiya dan haka koma ki zauna na k’arashe lada na”

Muryarta d’auke da murmushi, k’ara ganin kausar tayi ta mik’e tayi kanta, hannunta ta rungumo,

“In batun lada ne muma ki barmu mu samu sobada haka ki zauna k’afafuwan ki suma su huta, ki bari mu taya ki”

Kausar ta fad’i yayin da ta zaunar da sakeena a kan kujera, sannan ta juya ta koma wurin yayarta, sakeena kuma binsu tayi da kallo da murmushi, dan taji sun bal’in kwanta mata a rai, jin zaman da tayi akan kujerar kusa da ita ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin ta, manyan idanun kamal akanta, hankalinshi gaba d’aya shima fuskar shi d’auke da murmushin muguntar nan nashi, sai da gaban sakeena ya fad’i, dan tasan wata muguntar yake shirin aikatawa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Yana zama a kusa da ita yaga da d’an ja kujerar ta koma baya, yarda su kausar baza su gane ba, kamal murmushi yayi yayin da ya saka hannun shi ya jawo da kujerar ta kusa dashi, sauran k’iris ya k’ara kai hancin shi kan wuyan ta dan ya shak’i dadd’an kamshin ta da ya mamaye mishi kwakwalwa yayi saurin dakatar da kanshi, wata irin harara ta daka mishi, shi kanshi baisan mai ya saka ta kyale shi yake yin yarda yaga dama da ita ba, haka ya k’ura mata ido, yana shafa bayan ta a hankali har da wuyan ta da k’afad’unta, ita kuwa idanunta ta maida kan su kausar, tayi kamar baya wurin har kamila tazo kanshi tayi serving d’inshi, sai lokacin ya maida hankalinshi gaban shi, fried rice ce tasha hanta da vegetables, mac and cheese, potato salad, snacks, kebab, chicken nuggets da dai sauran su, abinci ba damun shi yayi ba amma gaskiya abincin gaban shi ya bashi sha’awa, mai da idanunshi yayi kan sakeena, dan halin da ta nuna yau ba k’aramin mamaki ta bashi ba, yarda ta tashi ta zage tayi wannan hidimar kamar bata tsane shi ba, bai san ya dad’e yana binta da kallo ba har sai da yaji kausar na cewa,
+
“Ya kamal, abincin ka zaiyi sanyi”
Sannan da sauri ya maida hankalin shi kan abincin tare da d’aukan spoon, a hankali ya fara tsakura kamar baya so, yana kaiwa bakin shi baisan lokacin ta ya zaro idanunshi waje ba, kan ya ankara ya k’ara d’ibowa ya saka a bakin shi, kan kice me ya fara saka loma, sai dai ya cinye komi na gaban shi tsab sannan ya d’ago yana goge baki da napkin ya had’a ido da kamila da kausar da suke mishi murmushi,
“Tunda nake yau ce rana ta farko da na tab’a ganin ka cinye abincin plate d’inka”
Kamila ta fad’i tana maganar kausar na d’aga kai alamun itama ta yarda,
“Nima haka,”
kausar tayi maganar tare da maida hankalinta kan sakeena, wacce har lokacin idanunta nakan abincin gabanta tana tsakora dan ba ci take ba, amma daga ganin hankalinta nakan su, duk tana jin me suke cewa,
“Ya sakeena kina da labari sai yayi 2 days ba abinci a cikin shi sai dai yayi ta shan fruits ko smoothie, mami da abba ba asibitin da basu kai shi ba daga k’arshe choronic ulcer ce ta kama shi da in ta tashi sai yayi kamar zai mutu”
kausar akwai shegen surutu, duk kallon da kamila ke mata na da tayi shiru amma ina, zai zuba take kamar famfo, a hankali ya maida kallonshi kan matar shi wacce yanzu itama ta ajiye spoon din hannunta tana kallan kausar, fuskar ta sai sa sai sa,
“Tunda yazo hannuna yanzu zan tabbata ulcer d’inshi baza ta k’ara tashi ba, zan kula dashi fiye da yarda kuke tsamani”
Dariya ce taso ta kuboce mishi dan yasan duk maganar ta k’arya ce dan duk duniya ba wanda zai so ya mutu sama da ita, maganar kamila ce ta dawo dashi daga tunanin da yake,
“Kai wallahi ba abinda zamu cewa da Allah sai godiya da ya bamu suruka irin ki, ya kamal is very lucky”
Yana ganin sakeena ta saki murmushin yak’e tare da mik’ewa da fara kwasar kayan da suka ci abinci dan yin kitchen, yasan abunda take shirin yi wanke wanke, a hankali ya jawo hannunta, sai gata akan cinyar shi, ya had’a bayanta da k’irjin shi, ya fara mata rad’a a hankali, amma rad’an ko su kamila zasu ji shi,
“Baby nace kin gaji da yawa, ki barsu suyi wanke wanken ke ki zauna ki hutu kinji”
Yana ji tana so ta kwace daga jikin shi amma yayi mata mugun kamu, banza yayi da ita tare ta kwantar da kanshi akan k’irjin ta,
“Gaskiya kam, nida kausar dai bamu gaji ba tunda flight muka hau, bari muyi wanke wanken”
Kamal najin abinda kamila tace ya mik’ar da sakeena daga jikinshi tare da ruke hannunta ta da fara janta, ko da wasa bai kai idanunshi kanta ba dan yasan ba abunda zai gani a fuskar ta sai wannan disgusting look d’in da take mishi wanda yake had’e da tsana, kada ta damu dan shima haka ne daga wurin shi, dole ce kawai ke saka shi yin abunda yake,
Suna shiga bedroom d’inshi ta fusge hannunta da mugun k’arfi, bayan ya kullo k’ofar, tare da saka duk k’arfinta akan k’irjin shi da ture shi daga kusa da ita, kallan shi take, kallan da baya dauk’e da komi sai tsan tsan k’iyayya,
“Kai wana irin d’an rainin wayo ne? Dan na yarda zanyi kamar ba komi a tsakanin mu bance ka dunk’a tab’a ni kana shiga personal space d’ina ba,”
Kwata kwata baiyi mamaki ba, yasan daman ya gama k’ular da ita, hannunshi ya nad’e akan fad’edan kirjin shi fuskar shi d’auke da murmushi, a hankali a niste ya fara ce mata,
“Ki dube ki da kyau, kiga kinyi irin kallar matan dan zanso tab’awa in har ba dole ba?”
Sannan a hankali ya matso dab da ita, fuskar shi har lokacin tana d’auke da murmushi, a hankali ya k’ara furta,
“Ko duk matan duniya gaba ki d’ayan su sun k’are ke kad’ai kikayi saura bazan tab’a sha’awar ki ba, kada ki manta kin bud’e k’afafun ki ma wani gardi kwanaki da suka wuce ya gama amfani da ke, banga mai zanyi da ragowar wani k’at..”
Kan ya k’arasa zancen shi ta d’auke shi da wani wawan mari da a take yastunta biyar sai da suka fito a farar fuskar shi, a hankali kamal ya juyo da fuskar shi da tayi gefe dan sanadiyar marin ya sauke akan ta, idanunshi sun k’ad’a sunyi jaa, mace bata tab’a tunanin marin shi ba sai yau, wata irin tafasa zuciyar shi ta fara amma duk abinda yake ji yasan bai kai kwatan abinda sakeena kije ba a lokacin, idanunta suma sunyi jaa bayan hawayen dake ambaliya a fuskar ta, abun tausayin ya mamaye fuskarta, daga gani maganar da ya gaya mata ba k’aramin ciwo da zafi tayi mata ba, tsanar da take mishi ta k’ara bayyana a cikin kwayar idanunta, a hankali muryarta na rawa ta fara ce mishi,
“In addu’a da Allah ya d’auki raina cikin gaggawa in har zaman da zanyi dakai a rayuwata na dindindin ne”
Yarda tayi maganar itama sai da ta saka dukkan tsanar da take mishi a muryar ta, ga cikin sanyin jiki tayi maganar sai tayi mugun baka tausaya, tana kuma gama zancen ta ta fita daga d’akin shi da gudu fuskarta ta bac’i da hawaye, kamal naji ta buga k’ofar ya lumshe idanunshi tare da d’ora hannunshi akan kyakyawar fuskar shi, wani irin takaici yake ji, abunda ya bashi mamaki shine rashin jin k’unar ran da yayi da ta mare shi, ya tabbata da wata ce sai ya b’alla hannunta, a hankali ya sami wuri ya zauna akan gadon shi, ya k’ara lumshe idnunshi da jan laulausan gashin kanshi, ba abinda ke yawo a kwakwalwar shi irin maganarta ta k’arshe da abinda ke d’auke a idanunta bayan ya gaya mata maganar,
“Anya yana kyautawa abinda yake mata?”
Ya fad’i a ranshi, sai dai yana fara tunanin yayi saurin kawar dashi yayin da wata zuciyar ta tuna mishi da irin rayuwar da kamil yayi saboda ita,
“Ita ta kashe kamil ka manta?, farin cikin ka shine ka ganta a cikin k’unci da bak’in ciki, ka lalata mata rayuwar ta”
Amma me yasa yanzu baya jin da-, sauri yayi ya girgiza kanshi tare da k’ara kawar da tunani gefe, a hankali ya mik’e dan ya fara bama kanshi tsoro, parlor yayi dan ya koma wurin k’ananshi, yasan dai ba wanda yaji komi a cikin su dan shi da sakeena ba wanda ya d’ag murya in har ba ganin ta sukayi da ta fito daga d’akin shi da hawaye ba.Tana fita daga d’akin shi d’akin ta tayi a guje, tana shiga ta kulle k’ofar tare da zubewa a kusa da gadon ta, wani irin kuka me mugun abun tausayi ta saki, bayan ta toshe bakinta dan kada bak’in gidan suji, kuka take yi sosai kukan irin cin mutuncin da kamal yayi mata, ita ya kira ragowar wani k’ato, tunda take a rayuwar ta ba wanda ya tab’a bud’e baki yayi mata irin wannan wulaqanci sai shi, ba abinda yaka k’ara mata ciwo shine yarda yayi mata abinda yayi mata bayan gwaninta da hidimar da tayiwa k’ananishi, sa kanta tayi a cikin cinyoyinta ta cigaba dai rairai kukanta, ba abunda ke yawo akanta irin kalaman kamal, wanda suka tsaga cikin zuciyar ta suka shiga sukayi mata tabo mai mugun zafi, ya zatayi da rayuwar ta ne, ta lura ba abinda yake so irin ya k’untata mata, kuma yana yin aiki mai kyau dan yanzu ta manta rabon da tayi farin ciki, wasu hawayen ne suka sake zuba, haka ta k’udindina kanta tana ta kuka har bacci yayi awan gaba da ita dan tayi mugun gajiya.
+
Jin alamun ana tab’a ta ne ya farkar da ita, a hankali ta bud’e idanunta ta ci karo da fuskar kamal, wanda yake shirin d’aukan ta cak daga inda take a tsugunne a bakin gado, sakeena da wani mugun sauri ta mik’e har ita da kamal na buge goshi, dan suna dab da juna, ita bata ji zafin karon da sukayi ba amma tana gani shi ya kama goshin shi alamun wurin na mishi zafi, jan gefe tayi ta tsaya ta bishi da kallo har sai da ya gama murgususun shi ya mik’e daga inda yake, suna had’a ido taji wata irin tsanar shi ta k’ara bugar ta a zuciya, zaiyi magana tayi saurin katse shi,
“Me kazo yi a d’aki na bayan ka gama yanka ta da kamalan ka masu mugun dafi”
Tana gani ya lumshe idanunshi bayan ya ci gaba da mulmula goshin shi da yanza yayi jaa saboda farar fuskar shi, ji tayi yayi ajiyar zucya bayan ya bud’e idanunshi, sannan ya nanand’e hannunshi a fad’edan k’irjin shi yarda kullum yakeyi, ya fara ce mata,
“Bazai yu mu raba d’aki ba yau kinsan su kausar na gidan nan bana so…”
“Na yi musu tarb’a iya k’okarina, na kyautata musu tunda suka taka k’afar su a gidan nan, nayi musu abunda zan iya, bazan iya zuwa d’akin ka ba in kwana dan yanzu ba abunda na tsana irin ganin fuskar ka, ka fitar mun daga d’aki”
Sakeena ta katse mishi zance, yarda tayi maganar a hankali, amma cikin fad’a da tsawa, bayan hawayen da suka cika mata idanunta taf, ga k’ok’arin da take kada ta sake su, jira take taga ya juya yayi hanyar k’ofa amma taji shiru, ganin fuskar shin da take a lokacin k’ara tunzara tayi, ta tsane ganin shi, ta tsane shi, bata san lokacin da ta k’ara wata maganar ba cikin mahaukacin iho,
“KA FITAR MUN DAGA D’AKI NACE”
yanzu hawaye sun fara zuba a idanuta, ihon da tayi ya saka kamal zaro manyan idanunshi waje bayan ya juya da suari ya kalli k’ofar a tsoarace, tare da saurin yin kanta, sakeena baya ta k’ara jaa da taga yana k’ara matsowa, maganar da tayi ce ta tsayar dashi cak,
“Kana k’ara taku d’aya zan k’walla k’ara yarda k’anan ka na waje zasu ji na tabbata kasan me ake kira da sharrin y’a mace”
Zaro manyan idanunshi ya k’ara yi waje, fuksar she d’auke da abun mamaki, ita kuwa sakeena ba abunda ke zuba a fuskar ta sai hawaye masu mugun zafi, idanunta sunyi jaa ja wur ga tsana d’auke a cikin su, a hankali taga kamal ya fara jan baya, sai da ya k’ura mata ido na tsawan mintoci, ita kanta a lokacin bata san me yake tunani ba dan ya saka wannan poker face d’in tashi, sai da ya k’are mata kallo sannan ya juya zai fita, sai da ya kusa wurin k’ofa sannan ta k’ara dakatar dashi,
“Daga yau ka k’ara tab’a ni bada izini na ba sai na tona maka asiri, sai na gaya ma duniya kai wani irin mugun namiji ne, sai ko ina a k’asar nan sun san kai wana irin azalimi ne”
Duk tsanar da take mishi sai da ta saka a cikin maganar ta, a tunanin ta zai zuyi ya mata wata muguwar maganar sai gani tayi ya cigaba da tafiyar shi har ya fita daga d’akin bai juyo ya kalle ta ba, tana jin k’arar kulle k’ofa, tak’ara fashewa da wani kukan.
————
Sai da ta shirye tsaf cikin wata straight gown me mugun kyau wacce ta fito da dirin ta ta ko ina sannan ta fito daga d’ak’in, kana ganin fuskar ta kasan ba lafiya ba yarda manyan idanunta suka kumbura suntum tsabar kukan da tasha daran jiya, duk da ta cika kwalli a idanunta kallo d’aya zaka yi mata ka gane, kitchen ta nufa ta fara fito da ganda ta d’aura a pressure cooker sannan ta shiga aikin yin breakfast, tasan su kamila na dab ta tashi, ko k’dan kamal bai fad’o ranta ba dan yanzu baya gabanta kuma ta tabbata yana office, ta kusa kamala abincin sai gani tayi an turo k’ofa an shigo, kamila ce a tsaye tana mata murmushi, itama murmushin ta saki,
“An tashi lafiya?”
Sakeena ce ta fara mik’a gaisuwar ta, kamila murmushi ta cigaba da yayi yayin da ta matso har kusa da ita,
“Ya gajiya?, ya kamal yace mana jiya kin kwanta da wuri saboda gajiyar da kikayi”
Yarda taga ta amsa ta ya bata tabbacin basu jiyo hayaniyar su ba ita da kamal jiya,
“Ina shiga d’aki bansan lokacin da bacci yayi gaba dani ba” tayi maganar tare da k’ara jaddadda k’aryar kamal,
Kamila murmushi ta saki tare da yin kusa da ita, “sannu ai mu kanmu munsan mun gajiyar dake”
Murmushi tayi, bata ce mata komi ba ta juya ta ci gaba da kwashe suyayiyar duyar da ta d’ora, tana cikin aikinta bata ankara ba taji an jawo hannunta,
“Lafiya??? Kinga yarda idanunki suka kumbura”
Kamila ta fad’i cikin tsan tsan damuwa yarda taga gaba d’aya manyan idanun sakeena sun kumburo ya bata tsoro, sakeena dariya tayi,
“Gajiya ce ta saka na kumbura, ai ni daman haka nake”
Yarda tayi maganar zaki rantse da Allah gaskiya ta fad’i, ganin haka ya saka kamila ajiye zance ta cigaba da taya sakeena hira da wasu aiyukan har suka kamala abinda suke suka kai dinning, sun fara karyawa kenan sai ga kausar ta sauko, cikin rigar da wando kanta ba d’ankwali, gaishe su tayi sannan ta sami wuri itama ta zauna, sai da itama ta tambayi sakeena idanunta, ta k’ara mata same amsar da ta bama kamila, sai da suka gama cin abincin tsab suka taya ta wanke wanke, bayan sun kod’a iya girkin ta har kamila nace wa zata zo lesson suna ta dariya dai, haka har suka dawo parlor.
Tv a kunne suna hira jefe jefe, sakeena bata cika saka musu baki ba dan tunanin da ya cika mata kanta ya ishe ta, kausar ce ta tab’o ta wacce tana can wata duniyar,
“Ya sakeena ina ta magana, tunanin me kike haka?”
Saurin saka murmushin yak’e tayi kamar ba abunda ke damunta, “ba tunanin da nake, me kika gani?”
Girgiza kanta tayi, “nace anjima zaki je gidan gaisuwa?? Ya kamal zai kaimu sannan ya ajiye mu a airport”
Ji tayi gabanta ya fad’i da aka ambaci kamal, yanzu ko sunan shi bata san ji balle wani abu ya had’a su, zata amsa da a’a kenan kamila ta ruga ta,
“Kausar wannan wace irin tambaya ce, kinsan ai zata je ba sai kin tambaye ta ba”
Shiru tayi, dan yanzu an kulle mata baki ba daman cewa a’a, kausar murmushi tayi har da y’ar murnar ta, nan suka kama wata hira yanzu kam sakeena na sauraron duk abinda suke cewa.²⁶

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]