[Advertisements⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 87 BY AZIZA IDRIS GOMBE - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 87 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

dawo ba ta kiransa hakan.

“Na’am Twinkle me ya faru?”

“Ina tsoro…”

“Wani abu ki ka gani?”

Wuyanta ta shiga shafawa kamar tana goge

wani abu. Ya san tsigar jikinta ne yake

tashi. “Fada min me ki ke so na yi miki?”

“Uhm! Za ka iya canza daki?”

Fuskarsa ce ta tattare cikin mamakin kala-

manta. “Me ya faru da nan din, bai miki

bane?”

Rarraba idanu ta yi ta ce, “Uhm… Ya yi min

kawai ina so ka canza daki ne, ka bar ni

a nan.”

Kallonta yake yi kamar ta sha omo ko giyar

wake. “Yaya ki ke tsammanin na raba

daki da ke? Sannan a garin da ba namu ba

cikin otel? Me ya faru?”

Idanunta ta sauke, “Ba na son… Ehm. Ba dai

kai bane, amma ba na son ganinka.”

Shiru Zaid ya yi, ya kura mata idanu wani iri.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Umm Adiyya, yau kin yi karatun Azkar
dinki?”
“Na yi mana, kawai ka yi hakuri. Wallahi tun
shekaranjiya ba na son ganinka.”
Tashin hanakali! Mikewa ya yi daga kan
gadon, ya yi zirya a dakin ya je ya dawo
cikin tunanin abinda ya yi mata ba daidai ba.
Bai tuna komai ba sai ma, tun isowarsu
da ya nemi zuwa kusa da ita ta ce ba ta jin
dadi.
“Wani abu na yi miki?”
“A’a babu, kawai dai haka nan.”
“You’re not serious.”
“Wallahi da gaske na ke yi. Tsigar jiki na yana
tashi, ina jin abubuwa suna min yawo
a jikina da cikin kaina. Ba na son jin
Kamshinka, ka yi hakuri.”
Komawa ya yi ya zauna dabas! A kasan dakin
a gaban gadon da take. Tashin
hankali ba a sa maka rana! “Ba abinda na yi
miki, mun rabu lafiya da safe, ba kya
son ganina, ba kya son jin kamshina.”
Kai ta gyada masa.
Tashi ki shirya.” Da ta kalle shi idanu a ware
ne, ya sake cewa, “Ki tashi mana.” Jiki a sanyaye
ta sauke kafafunta daga kan gadon, ta tafi tangal-
tangal kamar za ta fadi,
da sauri ya riketa. Ai kuwa tana shakar tu-
rarensa ta wanke su gaba daya da amai.
Matsar da ita gefe ya yi, ya zaunar da ita yana
mata sannu. Sannan ya kwabe rigar
jikin sa, ya dauko karamin towel ya goge inda
ta bata.
Dawowa ya yi ya kamata zuwa bandaki, inda
ta samu ya tara ruwa. “Za ki iya
wankan da kanki?”
Kai ta gyada masa kawai, don ta san yana
zuwa kusa da ita, za a kuma ne. Bai
takura mata ba ya bari ta shiga ta yi wankan.
Ya fitar mata da kayan da za ta saka.
Sannan ya shiga shi ma ya yi wankan yana
gama sa kaya zai fesa turare ne. Umm
Adiyya ta ce, “Don Allah ka yi hakuri kar ka
fesa.”
Zare idanu ya yi yana kallonta. “Adiyyah, ak-
wai abinda ba kya fada min.”
Dago idanu ta yi a sanyaye ta ce, “Ina ga ka
mar ina da ciki.” Shiru ya yi kawai yana
kallonta, kamar bai san yaren da take yi ba,
kafin ya ce, “Ban gane ba.”
Haushinsa ta ji dama yaya take yi ta daure ta
kalle shi bare yana ta nuna mata
kamar bai da fahimta.
“Ciki nawa ake da shi, na ce maka ina da ciki.”
Ta fada a kufule.
“Easy, ina kusa ba sai kin daga murya ba, na
fahimceki. Abinda ban fahimta ba shi
ne meye alakarsa, da ni kuma?”
Ganin ta zaro idanu ne, ya sa ya yi saurin gyara
zancensa, “Nufina, me zai sa ni a
tsaneni? Ba ki shirya bane tukun?”
Ta ma gaza ba shi amsa don takaici. “Kar ki
damu, ranar na tambayiiDr. Astha ta ce
ba komai za ki iya sake daukar ciki ba tare da
samun wata matsala ba. Allah ya raba
lafiya, ya ba ki lafiya. Ki kwantar da han-
kalinki, kin ji?”
“Na gane duka wannan, ba kuma tsoro na ke ji
ba. Ya Salam! Na fada maka ka
canza daki kawai, shi ne abinda na ke so.”
Zaid kam hannaye kawai ya sa ya tallafe
kansa, ya ma rasa me zai fara yi. “To, na ji
zan canza, yanzu ki daure mu je asibiti ko?”
Shiryawa ta yi ta same shi a kasa inda yake ji-
rarta a falin karbar baki saboda
kwayance masa ta yi ita tana jin abubuwa suna
mata yawo idan ta gan shi.
*************
Ai kuwa abinda ta yi zargin dai shi aka tabbatar
masu da shi a asibiti, don haka ga
farin-ciki, ga kuma taraddadin sabon abinda ya
bullo masu. Ranar dole yana ji yana
gani ya bar mata gadon.
“Ba zan bar ki ke kadai a nan ba, idan rashin
lafiya ya sameki fa cikin daren?” Shiru kawai ta
yi ta bar shi, yadda ta ga safiya haka ta ga dare ta
gaza barci.
Washegari tunda safe ya fita. Bai dawo ba sai
da rana, yana zuwa ya ce “Ki shirya
Za mu tafi.”
Kallonsaa ta yi, take tausayinsu ya kamata,
domin tunda ya fahimci har cikin ranta
abinda ta
fada yake, kwata-kwata baya ma
zuwa inda take.
Zaune suke shiru kowa a kujerarsa da abinda
ko wannensu yake sakawa a ransa.
Kamar daga sama ya ji hannunta cikin nasa, da
sauri ya yi kokarin ya sakar mata
hannunta. Ganin suna cikin mutane kar yanzu
ma hankalinta ya tashi.
Girgiza masa kai ta yi, ta jingunu a jikin
kafadarsa, shi kuwa ya kwantar da kansa a
kanta. A hankali ya sumbaci kanta hade da
rike hannun nata da kyau.
Na lokaci kadan ba karamin razana ya yi ba,
daya zaci ya rasa ta a karo na biyu da
ta kalle shi ta ce bata son ganinsa.
“Idan ki na jin wani iri. Ki fada min da wuri.”
Ya rada mata a hankali. Murmushi ta yi ta gyara
kwanciyarta, lokacin da ta shaki sabon turaren da
ya canza a safiyar.
“Ba ni sweet na sa a baki na.”
Buttermint ya ciro a aljihunsa ya mika mata
har da orbit chewing gum, da kuma
mentos duka. Ware idanu ta yi tana ganin yana
ta fito da su.
“Noorie duka wannan? Na kai ina?”
“Ki yi ta sha har mu isa, saboda ya kamata ki
san ba zan taba barin gefenki ba.Zan
kasance tare da ke a kodayaushe.”
“Ga shi kuma bebinka ya ce, ba haka ba kuma
ba.”
Tabbas sai dai bebi yayi hakuri. Baba bai
yarda da wannan wayon ba. Ya fada
lokacin da ya kai hannunsa zai taba cikinta, da
sauri ta buge hannunsa, ta yi masa
idanu.
“Ka sa mutane sun fara kallonmu.” Ta rada
masa a hankali.
“Ina ruwana da su. Su yi abinda yake gabansu,
su bar ni na ji da guntulallen
honeymoon dina.” Ya fada a tsume har da
juya idanu.
“Aww! Ka yi kama da babies.”
“Zan saba miki, ni ne baby din?”
Dariya ta yi hade da toshe bakinta, “Subhanal-
lah, don Allah ba yanzu ba.” Zaid ya
fada a razane.
Kai ta gyada masa, da sauri ya ftar da enve-
lope din da suka yi tanadi. Ya ba ta
hanya ta mike saboda hakan ya sa ya yi mag-
ana a ba su kujerar kusa da bandaki.
Ba a dade ba, ta fito ta same shi yana jirarta
kofar bandakin. Yake ta yi ta dan tsuke
idanunta ta furta masa. “Yi hakuri.”
Murmushi ya yi mata ya cire hannayensa daga
aljihu. “Ba komai, ki na jin daidai
yanzu?” Kai ta gyada masa, sannan suka koma
wurin zamansu.,
“Tabbas wannan zai zamo mafi doguwar tafiya
garesu! Ya fada bayan sun zauna
sun daura damararsu.
*************
BABI NA HAMSIN DA BIYU
Tun dawowarsu daga kasar Jamus, ba su dade
ba suka kama hanyar Bauchi, don
ta ga malaminta, gidan Adda Zubaida ta yi
masauki. Sai dai ta kira shi ya yi sau uku,
yana kin ba ta lokaci. Wannan ya sa Zaid ya ce
ta tashi su je makarantar.
Kai tsaye office din Dr. Yusuf suka shige. Ka
na ganin fuskarsa, ka san ya ji
mamakin ganinta. Sai daga baya idanunsa suka
fada kan Zaid.
“Assalamu-Alaikum, Akramakallah.” Zaid ya
fada cikin fadada fara’ arsa hade da
mika masa hannu suka yi musabaha.
Wa-Alaikumussalam. Sannu da zuwa. Bismil-
lah zauna.”
Ya dai sha jinin jikinsa kam, tunda ya ga Umm
Adiyya da wannan mutumin mai cika
wuri da kasancewarsa.
“Yaya fama da jama’a da kokari?”
Ah alhamdulillahi, ana kai, abu ne na kullum
ai.”
“Allah dai ya taimaka ya biyaku, ai aikin bab-
bane babu sauki kam.”
Sai da Zaid ya dan bari suka saki jiki da juna,
sannan ya ce, “Ahm! Malam ga matata
nan na zo da kaina mu bada hakuri, ba ta ji
dadi bane hakan ya sa ba ta kammala
aikinta akan lokaci ba, da fatan za ayi mana
uzuri a dan kara mana lokaci?”
Umm Adiyya, ai ni na zaci mun yaye ta ne,
ban sani ba. Gaba daya ta yaye mu a
nan kam.”
Zaid ya yi dariya. Ummu ko kamar ta kwakule
idanun Dr. Yusuf take ji, yana wani
mata kallon kasa-kasa ko ya zaci shiri suka
hada da Zaid din ne oho masa?
“Ah ai yadda ta faro ta hannunku. Ta nan din
dai za ta gama Inshaa Allah. Ban sani
ba ko za a sa mata ranar da za ta yi Defense
dinta, tunda ta ce kun riga kun
kammala wasu gyararraki duk da suka daceea
kan aikin.”
Eh to wannan ba matsala, zan tuntubi sauran
na ga yaushe ne za ayi next seminar
din, sai na fada maku.”
“Yauwa mun gode sosai. Allah Ya kara
girma.”
Zaid ya juya ya sakarwa Umm Adiyya da mur-

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]