[Advertisements⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 84 BY AZIZA IDRIS GOMBE - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 84 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Saudat ta fara girgiza kai kunya kamar ya kar

ta, ba tantama da safe ma shigowar

Yaya Saadik duba su yana zaune ta sha shayin

wata kila shi ya sa Maamin ta fadi

hakan yanzu.

“Sa min kunun.” Ta fada don ba yadda ta iya.

Sai da Maami ta ga ta kafa kai tukun,

sannan ta fice a dakin.

Asma ta ce, “Ki ka biyewa Maami, sai kin

zamo sanuwa kan ki bar gidan nan, kin ga

yadda Adda Zubaida ta dawo haihuwar Walid?

Da kyar ta koma size dinta. Shi ya sa

koda Abban Maama ya ce ko zan zo gida hai

huwa, na ce can ma ya yi min.”

Saudat na dariya ta ce, “Kin ga ta kanki Asma’

da ki zo gun Maami ki yi kiba,

gwamma miki can?” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wayar Umm Addyya ce ta yi kara tana

dubawa ta ga sako ne daga Zaid.

Twinkle, a tsagaita zancen haka nan ko? Ina

jiranki a falo.”

“Yanzu za mu tafi? Ta tura masa sakon a gag-

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

gauce
Ba ta ga amsarsa ba, don haka ta shagala abinta
su ka ci-gaba da hira, ba abinda
take so irin haduwa gaba daya dangi. Bayan
kusan minti talatin, sai ga sallamar Abba a sama,
daga kofar dakin da Saudat take suna jiyo shi
yana cewa, “Ina
Ummun ne?”
Da sauri ta zabura ta zari mayafinta ta yiwo
waje.
“Na’am Abba?”
“Zo ki wuce gida, tun dazu mijinki yake nan,
kar ki dawo kuma.”
Sumui-sumui ta koma ciki ta dauko jakarta ta
masu sallama. Abin sam bai mata ba
tana cikin ‘yan-uwanta suna jin dadinsu da hi-
rarsu ya zo tun karfe uku, ina laifin
biyar na yamma ko ma bayan Issha’i? Yanzu
me za taje ta fara yi a gidan?
Ita kadai sai mita take yi a ranta. A mota ta
same shi, don haka ta bude kofa ta
shiga. Tada motar ya yi ba tare da ya ce mata
komai ba, sun yi tafiyar kusan minti
biyar bai tanka ta ba.
“Noorie…”
“Uhm?” Ya fada yana kallon gabansa yana
tuki.
“Ba za ka yi min magana bane?”
Shiru bai ce mata komai ba. Ganin haka ne ita
ma ta juya ta kama gabanta ba ta ce
masa komai ba. Har da nade hannunta a kirji
ita ma a dole ta yi fushi.
Suna shiga gida, ta yi sama don ajiye jakarta da
mayafinta. Wanka ta yi ta daura
alwalar sallar la’asar, sannan ta sa wasu riga da
Skirt. Simple dan kunne ta saka ta
sanya turare masu sanyin kamshi da gazal a
cikin idanunta. Za ta shafa Lipgloss ne
ta ajiye ta dauko setin NYX dinta ta fitar da
jambakin-ciki ta shafa.
Tana shirin yin sallah ne, ta ji wani siririn kara
alamar taba kofa. Ta tashi don ta
duba, tana isa bakin kofar ba ta ida maida ko-
farta ba ta ji hannu ya ja ta, sai jinta ta
yi ta taho masa gaba daya, hannunta ta sa ta
dafa kirjinsa saboda ya dauketa ba za
ta. Baya ya matsa da ita ya hada ta da jikin
bangon wajen dakin.
Za ki sake kin yin abinda na ce?” Idanunsa
sun yi ja babu alamar wasa a tare da
shi.
Nata Idanun ta kwalo waje, cikin mamaki da
tsoro, wani abu ta hadiya, da ba ta san
meye ba. Idanun Zaid na kan makogwaronta,
yana bin ko wani motsin ta da kallo.
Ya dago ya dubi cikin idanunta.
Shiru suke amma bugawar da zuciyarta take yi
tana tsoron kar ta fashe a kirjinta.
Kafin ta shiga hayyacinta har ma ta gane fushin
duk na meye ne. Ta yi saurin
marairaice idanu.
“Noorie..
Ba ta fadi zancenta ba bare ta bada hakuri. YYa
shiga wassafata ta hanyar da ba ta
isa ta kauce ba. Www.bankinhausanovels.com.ng 
karar Lasfika ta soma ji. Wasu masallatai sun
fara kirar sallah, ta kauce masa
kadan, “Kamar ana kiran…” Ta fada numfash-
inta sama-sama. Tana mayar da
numfashi, gaba daya ba ta jin kafafunta, ba
don bangon bayanta ba da rikon da Zaid
ya yi mata da ba ta tsammanin za ta iya
tsayawa.
“Twinkle, yau ko karar me ki ka ji, Sai dai ki
yi ta ji, amma ki san da cewa. Ba zan
bar ki ba, saboda haka ki natsu, ki ba ni han-
kalinki, and let me love you.”
Kai ta gyada masa, a hankali, don ba tantama
idan ba ta yi yadda yake so ba, yau
ba za a wanye lafiya ba a gidan, ba zancen ta
musa masa. Shi kuwa ya ci-gaba
daga inda ya dasa aya, sai dai wannan karon a
tsanake yake bi da ita. Har ita ma ta
biye masa. Ba ta san dai yadda aka yi ba, ba ta
san ma a ina take ba, ita dai ta san
daga baya sun bar bakin kofar dakinta.
**** ********
“Twinkle,”
“Uhm?”
“Ki tashi ki yi sallah, lokaci ya tafi.”
“Uhum.” Kada kansa ya yi ya fita daga dakin.
Bayan minti goma da ya dawo, ba ta
tashi ba, dagata ya yi ta zauna, ya shafa mata
ruwa a fuskarta hade da hura mata
idanunta.
“Kamar wacce ba ta yi barci ba?” Ya fada
muryarsa cike da zolaya.
Tsuke fuskarta ta yi, ta dan harare shi. “Ka tafi
ka bar ni, barci na ke ji.”
“Da gaske rana zai fito yanzu, kin yi latti so-
sai.” Wannan ne ya zaburar da ita, da
sauri ta mike ta nufi bandaki, ta yi shirin yin
sallah.
Bayan ta idar, tare suka zauna suka yi karatun
Alkur’ani, sannan ya mika mata
hannunsa. “Meye?”
“Zo nan.” Ya fada, hade da riko hannunta. Ta
matsa kusa da shi. A kan kafafunsa
ya yi mata matashi, “Koma barcinki zan
tasheki anjima.”
“Ina kwana?” Ta fada
“Ina
idanunta suna
lumshewa.
“Lafiya kalau, yaya gajiya?” Ya fada
yana
murmushi.
Murmushin ita ma ta yi, ta boye fuskarta cikin
hannayenta.
“Ko ta bi lafiya? Saura wata?”
Girgiza kai ta yi. Dariya ya yi har tana jin dirin
muryarsa daga kirjinsa. “Matsoraciya
kawai. Yi barcinki.” Ba ta kai ga gyada kanta
ba, barcin ya yi awon gaba da ita.
Kallon gashin idanunta ya yi da suka shimfidu
a saman kumatunta. Goshinta ya
sumbata a hankali “Allah ya yi miki albarka
Adiyyatah.”
Muskutawa ta yi cikin barcinta, haka ya zauna
bai motsa ba, tsawon awa daya yana
karatunsa yana amsa sakwanni da Mails da
SMS. Ya ki amsa waya don kar
maganarsa ma ta tashe ta. Wuraren karfe tak-
was ne ya maida ta kan gado ya
kwantar.
Ya yaye bargon kan gadon shi ma ya kwanta a
gefenta. Ba su suka tashi ba, sai sha
biyu da rabi, nan ma Umm Adiyya ce ta gaji
da kwanciya jikinta duk yana ciwo.
Da sauri ta wuce dakinta ta yi wanka ta shirya
cikin atamfarta ruwan daurawa da
baki an yi masa dinki da Side Peplum , wanda
ya kara fiddo da surarta da kyau.
Ta yi masifar kyau kamar a sace, dauri ta yi ta
sako jelar kitsonta yana reto ta
tsakiyar dan kwalin. Ta yi kwalliya na sosai ta
feshe jikinta da turare, sannan ta tsaya
a kan na gaushi, shi ma ya ratsata da kayanta.
Sai da ta gama tsab! Sannan ta
sauka kasa, ta dora abinci mafi sauki.
Chicken Stir fry ta masu da Chow Mein.
Sweetened crusted plantain ta yi ta dora
akai, sai Pena colada drink. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Kamshinsa ta ji ta san ya fito. Juyowa ta yi ta
sakar masa da murmushi, ya yi
shigarsa cikin shigen T-shirt da Jeans. Shi ma
Karasowa ya yi inda take tsaye,
sannan ya ce, “Ki bar abincin tukun na, na
makara zan wuce masallaci.”
“To a dawo lafiya.”
Juyawa ya yi, yana daura agogonsa har ya kai
bakin kofa, kafin ya fita ta ji ya yi
magana, sai dai ba ta ji abinda ya fada ba.
Ganin ya makara ba ta tsayar da shi ba,
ta shirya komai a kan teburin cin abincin falo,
sannan ta yi sallah a nan falon nasa.
**********
Kwanaki hudu suka yi banda karbar baki, da fita
masallaci ba abinda yake dauke su
daga gangan juna. Kafin Mr. Femi da kansa ra-
nar Juma’a ya kira wayar Zaid.
“Zayid, you need to come back, these people
will kill me with work load. (Zaid ya
cancanta ka dawo mutanen nan za su kasheni
da ayyuka)”
Zaid ya yi dariya kamar meye, sannan ya ce,
“Na ce maka ka turo min duk abinda
ya yi maka yawa, na tayaka ragewa.”
“Hey! Ka na so Madam ta hanani shigowa gate
din Zaid Mansion kenan. No kawai
dai ka gama ka dawo da wuri, muna da
abubuwa da suke bukatar dubawarka. Ga
sabbin kwastamomi ga kuma tsoffin da za a
kammala ayyukansu.”
“Okay! Kar ka damu, ina fitowa gobe Inshaa
Allah. Idan ka tashi, sai ka san bayanin
da za ka yiwa Madam.”
“Kai dai ka na so ka hadamu fada ne kawai.”
Zaid na dariya suka yi bankwana da Femi,
yana gama wayar ya juyo ya ga ta kafa
masa idanu.
“What?”
“Dama ka na da aiki ka rinka cewa su Mr.
Femi suna nan.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Ahan, yanzu ko ke ba ki ga na fi miki kyau
ba, tsabar kwana biyu ba na tsilla-tsilla a
hanyar wurin aiki?’
Bude idanu ta yi tana kallonsa, “Yau kuma, kai
ne mai kin zuwa aiki? Koda yake ba
yau farau ba. Amma tunda ka ga Mr. Femi ya
kira, ka san abubuwan sun masa yawa
ne.”
Kai ya kada mata kawai.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]