[Advertisements⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 80 BY AZIZA IDRIS GOMBE - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

UMM ADIYYAH CHAPTER 80 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

“I don’t care.”

“Yau na ga ikon Allah, don Allah ka ba ni, zan

yi muni a duka hotunan.”

“Ki cire dayan, idan kin ga dama ko ki sa

Karami.”

“To ai ba za ka.. To a cikin mutane za ka… Ina

ce ba za ka taba kunnen nawa ba a

cikin jama’a, ka ba ni dan kunnena don Allah,

please, dan karamin Pretty please. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zan ba ka kyauta muna fitowa. Nayi alkawari.”

Ta fada hade da rike makogoronta da yat-

sunta, tana marairaice masa. Ya Salamn!

Yarinyar nan wataran za ta gama da zuciyarsa.

Hannu ya sa ya ciro dan kunnen,

sannan ya yi mata alama da ta janye lullubin

lufayan nata, a hankali ta janye, shi

kuma ya karkace ya sa mata, hade da sumbatar

wurin. Sannan ya koma ya zauna,

inda ya bar Umm Adiyya, a narke a wurin. Ta

san ya san abinda take zama ne, idan

ya yi hakan, shi ya sa ya matsa mata.

Daidai lokacin Takiyya ta bude mata murfin

gefenta, “Amarya oya, fito, a hankali.’
“Takis, mun gode, bari na rakata.” Zaid ya
fada cikin murmushi.
“Dolena ango.” Matsawa baya ta yi Zaid, ya
tsaya a gefen matarsa, hannunsa cikin
nata ko a jikin sa, suka jera har cikin rumfar da
aka shirya domin taron.
Kwalliyar da aka yi wa wurin, ya ta fi da tu-
nanin kowa, magabata shirin ne suka yi
maraba
da isowar manyan baki, aka kuma
shirya kowa a wuraren zamansu mata,
an ajiye su a bangare guda, yayin da mazan ma
aka ajiyesu a nasu gefen. Manyan
abokan Zaid da ma wadanda ya taba aiki da
su, da kawayen Umm Adiyya har da na
makarantar Sakandire ta gayyaci wasu. Kuma
da yawa sun samu halarta. Taro ne
da bai wuci mutane dari da hamsin ba.
Yau ma dai Salisu ne ya gabatar da taron, inda
ya bukaci abokinsu Barr. Fawzaan Lamido ya
gabatar da addu’a. Matarsa Rumysah sai fara’a
take yi daga gefe. Bayan
ya kammala addu’a ne. Engr. Sufyaan Bark-
indo ya bada takaitaccen bayani
kasancewarsa na babba a cikinsu gaba daya.
Ba a bar Mr. Femi ba a baya da matarsa
Bidemi. A bangaren amarya kuma. Takiyya
ce ta yi masu maraba da zuwa, kafin a bar filin
wa, manyan bakin da suka samu
halarta, domin gabatar da nasiha akan zaman
aure, da ma yadda za a ceci aure
daga rugujewa, ko yau aka daura ko kuwa an
riga an yi shekaru ashirin da yin
auren. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Umm Adiyya tana ganin wacce za ta gabatar
da bayanin, ta sakarwa Zaid da fara’a
sosai, hade da furta masa. “Jazakallahu
khairan”. Ba ta taba tsammanin zai shirya
abin har haka ba, domin ga dai Haleh Banani
wacce kowa ya sani da gyara aurarraki
da kuma bada shawarwari na tsawon shekaru
ashirin, sannan ga su Dr. Isa Ali
Pantami, duk sun samu halartar taron.
Ga Nasheeds da aka sa a bayan fage yana tashi
a natse, haka ba a bar baki haka a

zaune kyamas ba, sai da aka cika gaban kowa

da kayan tande-tande na tabi, kafin a

kai ga cin abinci mai rai da lafiya wanda MB-

catering Solutions hade da zuzu cuisine

da ChefsTalk Catering suka shirya.

Abu ne na manya ba kananan yara ba, an yi shi

a tsanake, babu gajiya bare

gundurarwa, an karu da ililimmuka. Manyan

bakin da suka samu halarta kuwa har

da Sagir Daggash da matarsa Aneesa Mah-

moud, ga Arch. Ammar da Dr. Nuwairah

har ma da ‘yan biyunta Nawwarah da mijinta

Hammad. Daga daya bangaren kuma

ga Jabir Qais da Intisaar.

Umm Adiyya ta ji dadi kwarai da ta hango

Maman Abul da mijinta, ga kuma Dr.

Astha ita ma ta samu halartar taron.

Daga gefensu kuwa na hagu ga Lt. Col MI

Kirfi da matarsa Hadiza Musa, kamar za

su hadiye juna, duk da kowa na zaune a ban-

garensa, ka na jin nasiha na shiga

jikinsu, kallon ma da suke yiwa juna na Www.bankinhausanovels.com.ng 

musamman ne. Ganin Dr. Zainab da mijinta

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ne, ya sa, ta kalli Zaid, shi ko ya mata mur-
mushi. Tabbas ba karamin shiri ya yi ba,
don har da makwabtan da ta zauna da su kan
su rabu duk ta gansu.
An dan fara jawabi ne. Masdook Abubakar
Sa’eed da Mihjanaa Suraj suka shigo,
saboda a ranar jirginsu ya iso daga birnin Ham-
burg, wannan ya sa suka dan iso latti
filin taron.
Ga Dr. Aliyu Kumo da matarsa Nana Fatima
da suka shigo tare da Mahmoud
Gamawa da Nana A’isha, abin dai ba a cewa
komai.
‘Yan gida na zaune an bar Ushers da hidimar
baki. Taro ya tafi tiryan-tiryan, misalin
karfe goma saura, aka kammala bayanai.
Rayyan Umar ne ya tashi ya yi jawabin
godiya, da sallamar baki, har ya bada wani
labari kadan game da rayuwar Zaid,
lokacin da suke makarantar kwana a Bwari,
aiko nan da nan aka saka dariya a cikin
filin taron.A gefe kuma ga dai mutane birjik! Masu bibi-
yar labarin Umm Adiyya sun samu
halarta, abinba a cewa komai, sai san barka,
yan matan kuwa ba wacce ba ta ki ina
ace Zaid bane mijinta, yadda suke ganin Umm
Adiyya ta gama taka sa’a, duk da dai
Adda Zubaida ta yi karamci, duka matan an
hada su a bangare guda, ba wacce aka
ware a gefe.
Yayin da Mazan ma bangarensu guda, kafin a
tashi masu mata aikin har sun shirya
wasu alaka ta harkar cinikayya a wurin.
Babu wanda ya kai Umm Adiyya farin-ciki a
wannan ranar, Zaid ya gama cika mata
burin ranar aurenta, har ma fiye da hakan.
Ana gama nasiha. Umm Adiyya ta hadu da
duka matan abokan Zaid da bakinta
mata da ‘yan-uwanta suka yi hotuna, haka nan
ta dauka da Sister Haleh Banani ma,
Sun yi wasu hotunan da Zaid kafin ya wuce
cikin abokansa, yi masu sallama, an
tattafi ba su wuci su shida su kayi saura ba a
filin taron. Lokacin ne wayarta ta yi
kara ta ciro ta duba fuskar wayar.
“Ammin Maama yaya dai?” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Asma’ ta sauke ajiyar zuciya, “Tun dazu muke
ta neman wayarku, mu fa daga wurin
walima mun taho asibiti da Adda Zubaida, hai-
huwa ta zo, amma ina ga koda matsala
ne, ban sani ba, sun dai shige da ita.”
‘Subhaanallah! Allah dai ya sa lafiya. Ya raba
su lafiya.”
‘Ameen. Na yi waya da su Maami suna hanya
tuni, shi kenan.”
“Wani asibiti ku ka wuce? Bari mu zo mu
ganta kawai yanzu.”
Asma
na tsakiyar yi mata bayani ne, sai ga
Zaid ya dawo don su tafi, bayan ya
gama sallamar sauran abokansu. Salisu ma
yana kokarin su wuce gida da
Mashkura, don tuntuni ta soma hamma.
“Adda Zubaida ce aka kwantar da ita, kamar
haihuwa ce, amma koda matsala ne ko
wani abin, ta dai ce an shiga da ita.”
“Subhanallahi. Allah ya raba lafiya.” Kallon
Bangaren da Salisu yake ya yi, “Uhm Dan group,
abinda za ayi mu je mu ajiyeku a gida da Madam,
sai mu wuce asibitin,
tunda mu Wuse muka yi, kuma ta can asibitin
yake.”
“Ah ba komai, mu je dai mu ga Adda
Zubaidan.”
k * ****k ***
Haka suka wuce asibitin gaba dayansu, suna
shiga can suka tarar da su Maami a
tsaye gabaki daya babu mai walwala dai a
cikinsu. Umm Adiyya ta yi wurin Maami
da sauri, ta riko hannunta cikin nata.
“Maami yaya Adda Zubaidan?”
“Suna dai dubata a ciki, hala ta sauka da kanta,
amma sun ce ba su son baby din ya
tagayyara so, sun fara shirin shiga tiyata.”
“Allah dai ya ba ta lafiya, ya raba kuma kalau.”
Gaba daya sun yi cirko-cirko suna jiran jin
bayani. Ga dare yana yi. Abba ne ya ce
da su Salisu su je gida duka, abinda ake ciki za
ayi waya a fada masu. Don haka
Fa’iz ne ya mayar da su, kasancewar da motar
Zaid dama suka taho.
Bayan kusan awa daya da isowar su Umm
Adiyya ne, har matan sun samu wuri sun
zazzauna. Sannan Nurse ta fito masu da baby
lullube cikin showel mai laushi.. Kai
tsaye ta mikawa Maami baby. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
“An samu bomboy.” Ta fada tana fara’a.
Maami ta karbi baby hannunta na rawa, tana,
“Mashaa Allah.” Take a nan ta yi masa
addu’a tana kallon sa, sai kuma ta dago kai ta
dubi Nas din. Ashe ba ita kadai bace,
don Baban Walid ko kallon baby bai yi ba, ya
nemi ya shige ganin matarsa.
Lokacin ne Nas din ta dakatar da shi.
Umm Adiyya ta ware idanu, tana kallonsu.
Take ta ji gabanta ya fadi. Ta dago kai ta
kalli Zaid da ke tsaye ta gefensu.
Hankalinsu gaba daya ya koma kan ma’ aikaci-
yar jinyar.
Karar waya ne ya ratsa cikin shirunsu, amma
ba wanda ya yi motsi, waya ta biyu ma
ta shiga kara, da wayoyin suka yi uku ne.
Maami ta ce, “Akwai wanda zai dauki
wayar nan a cikinku?” Da sauri Adiyya taa
bude Clutch dinta ta fidda wayarta.
“Yaya Saadik ne.” Ta fada tana kallon fuskar
kowa a wurin da ya zubo mata idanu.
Wannan ya saka ta dannawa nan da nan.
“Hello Yaaya?”
%***********
BABI NA ARBA’IN DA TARA
“Ummu A. Ku na asibitin ne?
ne?
“Ummu
Yaya
Zubaidan?”
“Ta sauka, amma ba su ce mana komai ba dai.
Opertion aka yi. Wani abu ne?”
“Uhm, ki bawa Maami, Saudat ce ina ga za ta
haihu a gida.”
“To! Kuma?” Da sauri ta isa gefen Maami “Ga
Yaya Saadik, Anti Saudah ce.”
“Hello?”
“Maami,
me zan yi?” Daga jin muryarsa a
kidime yake.
“Ba kowa ne a gidan? Ga-ni zuwa yanzu.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]