[Advertisements⬇️]

TSINTACCIYA CHAPTER 8 BY NIMCY LUV - Bankinhausanovels
Thu. Oct 6th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSINTACCIYA CHAPTER 8 BY NIMCY LUV

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yana zuwa bakin ƙofar ya tsaya yana jiran fitowar Akeem, gently ya buɗe ƙofar ya fito idanunsa a lumshe ga yadda jijiyoyin kansa suke a mimmiƙewa fuskarsa tayi jajirrr da ita alamun har yanzu yana cikin ɓacin rai.

Ganin Akeem cikin wannan halin wanda bai taɓa ganinsa a ciki ba yay saurin faɗin “Dr” idanuna da suke a Lumshe ya buɗe tare da sauke ganinsa akan fuskar Abbu,wani irin bugawa zuciyar Abbu tayi saboda wani irin jaaa da idanun Akeem sukai har wani ruwa suke fitarwa. Muryar sa na rawa yace “what… what happened to Akeem?” Lumshe idanunsa yay kana ya buɗe kamar wanda baya son yin magana ya buɗe baki da ƙyar yace “noting” yana faɗin hakan ya nufi shiga cikin gidan da idanu kawai Abbu ya bisa yana mamakin baƙar zuciya irinta Akeem. Girgiza kai kawai yay tare da nufar cikin gidan kai tsaye part ɗinsa ya nufa, Akeem na shiga Amani na ganinsa ta miƙe tana faɗin “Abbie na” bai ko kalli inda take ba sai hannu daya sanya yama ture ta kai tsaye upstairs ya nufa yana dafe kansa yana jin yadda Amani ke kuka amma yau banza da ita, Didi dake zaune tayi saurin faɗin “Au! Yarinya ba sai dai kiyi tayiwa Ubanki istigifari ba, daɗin abin ko kashe ki yay shine ya haifa a toh” Aleema ce ta kama hannunta tana rarrashinta kasancewar weekend ne duk suna gida. Akeem na shiga side ɗinsa rest room ya nufa cire farar jallabiyar jikinsa yay tare da saƙale ta a hanger, fure fresh skin ɗinsa ta bayyana wani irin

ƙwantaccen baƙin gashi ne a saman mararsa mai matuƙar ɗaukan hankali jikinsa a sanyaye ya nufi cikin tube tare da shigewa ciki, wani irin sauke numfashi yay a hankali kuma ya ƙara nutsewa cikin ruwan dake cike har bakin tube ɗin, zafin da zuciyarsa ke masa ya sanya gaba ɗaya yama mance a cikin ruwa yake, idan ya tuna irin faɗan da Ummi da Abbu sukai masa sai yaji wani abu ya tsaya masa a ƙirjin, cikin ficewar hayyaci da kuma zallar damuwar dake ransa ya ƙara nutsa kansa cikin ruwan a hankali kuma ruwan ya fara shige masa cikin baki da hanci.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

A hankali wata baƙar mota mai ƙirar Audi RS5 ta fara shigowa ciki Nasarawa daga farko farkon Nasarawa harya gifta sai kuma ya dawo baya a hankali yana zare baƙin glasses ɗin dake idanunsa,  saurayi ne ɗan kimanin shekaru 27 yana sanye da wani farin voyal wanda yay masa kyau sosai kasancewar sa farin bafulatani kana ganinsa Kasan cewar kuɗi sun zauna masa, a hankali yake tafiya da motar zuwa baya kasancewar shike driving ɗin ganin hakan yasa wanda ke kusa dashi yace “Ajmal me kake haka ne?”shiru Ajmal ɗin yay domin baya jin akwai abinda zai iya faɗa, a hankali ya gama tsayar da motar  tare da buɗe murfin motar ya fito ganin hakan yasa Karim yay saurin fitowa yana faɗin “wallahi kaifa ba hankali gare ka ba, kana ganin aikin dake gabanmu dole ne a wannan satin mu samu mu shawo hankali duk raguwar jama’ar” ina Ajmal baya gane yaran domin tuni idanunsa suka sauka akan fuskar Akeela dake kwance a ƙasan wata bishiya wallahi wallahi a wannan lokacin duk wanda yaga Akeela dole zuciyarsa ta buga domin ba zaka taɓa cewa ƴar hausawa bace, tana kwance kanta na zubda jini saboda wata muguwar faɗuwa da tayi gaba ɗaya kayan baccin dake jikinta sunyi wani bala’in yin datti gashinta ya wargatse yay ɗai ɗai, tsaye Ajmal yay akan Akeela yana jin zuciyarsa na bugawa, a hankali kuma ya tsuguna a gabanta dai-dai lokacin da Karim yake ƙarasuwa wajan cikin sauri yace “wai Ajmal meke damunka ne? Baka tsoran abin cutarwa ne? Kilama ba mutum bace Aljana ce, ina ka taɓa ganin mace mai gashin wannan?” Banza Ajmal yay masa domin yadda idanunsa suka sauka akan fuskarta yasa baya fahimtar komai dukkan wani abu na kansa sai da ya kunce, hannunsa ya miƙa tare da tattare sumar data rufe mata fuska cikin sauri ya rufe idanunsa yana faɗin “Ohh God”  Karim yay saurin faɗin “is she died?” Girgiza masa kai kawai Ajmal yay yana ƙoƙarin sanya hannunsa ya ɗauke ta Abbu dake ƙarasuwa wajan yace “Akeela! Allahamdulillah”

Da sauri ya sanya hannunsa ya ɗauke ta tare da kallon Ajmal yace “thank you son, wallahi tun jiya mukai missed nata yanzu na ƙara fitowa ne, kamar daga sama na hangeka ji nai kawai ina son ganin Meke faruwa cikin ikon Allah kuma naga Akeela thank you” jinjina kai kawai Ajmal yay yana shafa wuyansa sosai ya gane Abbu amma shi Abbu sam bai gane waye Ajmal ba, kamar bazai magana ba sai kuma yace “Dad! A nan kuke ne?” Kallon Ajmal Abbu yay yana karantarsa sai kuma yace “eh cikin Railway quarters no 112” idanunsa akan fuskar Akeela yace “ok Thank you” yana faɗin hakan ya nufi cikin motar tare da zama wajan driving ba ganin hakan yasa Karim shima ya shiga cikin motar da gudu Ajmal yaja suka bar wajan, mai makon yaje inda zashi sai kawai ya juya kan motar ya nufi hanyar gida da Mamaki Karim yace “wai Ajmal Meke damun ka ne?” Cikin ɓacin rai Ajmal yace “ban sani ba, banza shege munafuki kawai haba” ya faɗa cikin ɓacin rai yana ƙara sharara gudu.

Abbu shima cikin farin ciki ya nufi motarsa bai yadda ya ajjiye ta a back seat ba a nan saman jikinsa ya barta key yaywa motar ya juya zuwa gida tun a hanya ya kira number Ummi da sauri tai picking call ɗin tana faɗin “Something news?” Cikin ƙasa da murya yace “I’ve seen her Ummi on my way yanzu” Murmushi tayi tace “Allahamdulillah”

A wahala Akeem ya ɗago kansa daga cikin ruwan yana sauke wahalallan numfashi a hankali kuma ya buɗe idanunsa da sukai wani mahaukacin ja, ya jima cikin ruwan kafin ya fito ya ɗauki  bathrobe ya sanya a jikinsa, ruwa na zuba a jikinsa ya fito kai tsaye ya nufi cikin wani special bedroom ɗinsa Yana zuwa ya rufe ƙofar da key, derect bed ya nufa yana zuwa ya faɗa tare da jan duvet ya rufe jikinsa tass domin wani mugun bacci ya keji, kamar yadda ya saba haka yanzu ma ya jawo pillow ya rungome a tsakanin ƙirjinsa yana sauke numfashi a haka bacci ya ɗauke sa da tunanin yadda zai rama abinda akai masa akan wannan yarinyar.

Ummi da Didi ne suka miƙe lokacin da Abbu ya shigo da Akeela a hannunsa, kai tsaye part ɗin su Aleema ya nufa da ita, Ummi na biye da shi Mami ko motsawa ba tayi ba idanunta akan cineme,  yana zuwa su Afaf suka miƙe fuskarsu ɗauke da farin ciki, kwantar da ita yay cikin nutsuwa Ummi tace “bari na duba ta” gefe Abbu ya koma yana jin kamar ya kori kowa ya jata jikinsa ya rungome ya lallasheta da kansa amma no way ahlinsa na wajan dole yaja da baya da yaga yana neman zama wani uncontrol sai kawai ya fice daga part ɗin, a hankali Ummi ta zauna idanunta akan Akeela tace “Afaf jeki kawon warm water a bowl with towel” “ok Ummi” bathroom tayi ta shiga haɗa ruwan zafin kana ta fito ɗauke da towel ɗin “drop it and leave and you too Aleema” ficewa duk sukai gently Ummi ta zamewa Akeela rigar jikinta babu ko bra a jikinta cikin tausayin ta Ummi ta shiga goge mata Jikinta da ruwan zafin, sosai ta kasa mata Jikinta ta shafe ta da robe kana ta sauya mata kaya zuwa Sleeve Bodycon mai sauƙin nauyi saboda zafi ake da alama akwai ƙaramin hadari a ƙasa, kwantar da ita tayi ta rufe da duvet gudun a.c ta ƙaro mata ba mai cutarwa, fuskarta tabi da kallo ganin yadda take sauke ajjiyar zuciya a jajjere, fita tayi daga bedroom ɗin a Parlo ta samu su Afaf ɗin suna buga game ficewa tayi daga part ɗin nasu baki ɗaya.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Ummi na fita Akeela tai wani irin juyi tare da buɗe idanunta abinda basu sani ba idanunta biyu kawai har yanzu mutanan na kanta ne irin aljanun nan ne masu mugun abu wanda sai ansha wahala kafin suyi magana ma. Parlo Ummi ta dawo kusa da Mami ta zauna ba tare da tace komai ba, a hankali Abbu yake tafiya cikin tafkeken bedroom ɗinsa hannunsa goye a bayansa sai numfashi yake fitarwa, gaba ɗaya yama rasa yaya zai yi baya jin daɗin komai burinsa kawai yaga fuskar Akeela, wani murmushi yay yana jin daɗi domin sai yanzu ya tuna da Ƙofar dake bedroom ɗinsa wacce kai tsaye hanyar tayi har parlon su Aleema, jikinsa na rawa ya buɗe ƙofar tare da fita su Afaf na tsaka da buga game su kaga Abbu kamar daga sama kallonsu yay yace “bari na mata magani” jinjina kai kawai sukai, bedroom ɗinsu ya nufa jikinsa har wani tsuma yake tana zaune ta tura kanta cikin tsakiyar cinyoyinta, ƙarasawa yay tare da faɗin “Babyn Abbunta zo nan gani nazo rarrashin ki” shiru bata motsa ba hakan yasa ya ƙarasa inda take yana zuwa ya jawota jikinsa yana shafa kanta tare da faɗin “Babyna” jajayen idanunta ta ɗaga ta kallesa cikin wata kakkausar murya tace “Abbu Akeem” zuciyar Abbu ce ta buga da ƙarfi cikin damuwa yace “me Akeem zai maki” kuka ta sanya masa ko kuma aljanun suka sanya masa cikin wata iriyar Murya mara daɗin saurara tace “Akeem muke son gani Abbu” sai a lokacin Abbu ya fahimci ba ita take Maganar ba, shafa kanta kawai yay yana faɗin “sorry Babyna kina shan wahala ko? Dana aureki zan bar ƙasar dake” wani irin kallo tayi masa tace “kai ma baka da lafiya Abbu Meye Wannan a jikinka?” Bai tsaye jin zan canta ba ya ɗura bakinsa a kunnanta ya shiga yi mata addu’a, miƙa ta fara yi kafin kuma a hankali jikinta ya saki bacci mai nauyi ya ɗauke ta, Murmushi Yay yace “Babyna zaki sanya zuciyata bugawa idan kina kiran sunan Akeem, Tabbas ni kaɗai zaki so nasan Akeem bai taɓa cewa yana sonki amma yadda kike da mugun kyan nan masu kawo maki hari suna da yawa, ni kawai zaki so zaki zauna dashi, zan koyar dake zallar so da kuma ƙauna ta Akeem kuma duk yadda za’ai a watan nan sai na tura shi Germany zai nesa dake sai yay Shekaru masu yawa lokacin tuni kin zama tawa zai dawo” ya faɗa yana shafa kanta a hankali ya sumbaci goshinta..

*Singapore*

Khoo Teck Puat Hospital

A hankali motar tai parking Meema ce a gaba sai mahaifinta President Ahmad Adil yana Cikin Wata dakakkiyar shadda dark blue mai kyau sai sheƙi yake, yayinda ita kuma take cikin wata milk ɗin abaya da red ɗin Stones tayi rolling kanta da vail tayi kyau sosai, hannunta riƙe da waya ga wasu manyan guards  kai tsaye cikin female sugical world suka nufa shiru asibitin saboda asibiti ne na masu kuɗi babu hayaniya ko kaɗan, cikin sauri Meema ta buɗe ƙofar office ɗin Dr ɗin ba tare dako permission ba, yana zaune yana duba wasu files Meema ta shiga tana faɗin “Dr what happened i saw your miss call” Murmushi yay yace “Na kira na faɗa maki yau za’a buɗe fuskar ƙaninki” wani daɗi taji da sauri ta rungome Dad tace “Dad bana faɗa maka ba” hannunta ya riƙe yace “ok be careful” Miƙewa Dr yay cikin so much respect ya shiga gaisar da Dad kafin yace “follow me” binsa sukai a baya har suka nufi wani room 11 buɗe ƙofar akai Dr na gaba Meema na baya sai Dad, cikin sauri ta zame hannunta ta nufi inda yake a kwance da kayan marasa lafiya Murmushi tayi tana riƙe hannunsa, ɗumin hannunta daya ratsa tafin hannunsa yasa yay sauri riƙe hannunta domin yau gaba ɗaya ba tazo hospital ɗin ba kamar yadda ta saba, kayan aiki Dr ya ɗauko Meema jikinta har rawa yake domin ta matso ta ganshi, cikin nutsuwa Dr ya fara ware masa bandejin fuskarsa yana cirewa, bakinsa ne ya fara bayyana mai ɗauke da jajayen laɓɓa, sai kuma hancinsa a haka har aka gama buɗe masa fuskar, idanunsa a rufe ruff fuskar Abbu kwance a saman nashi fuskar Dr ne yace “Congratulations now open your eyes” slowly ya shiga buɗe idanunsa kai tsaye ya sauke ganinsa akan fuskar Meema babu ko kifta idanu, cikin farin ciki Meema tace “Bro na” shiru yay mata bai ce mata komai ba ganin hakan yasa ta kwaɓe fuska tace “why baya magana?” “Ai sai ya koyi komai ba, kinga aiki ya sameki” Dad kam tunda aka buɗe fuskarsa yaji gabansa ya faɗi sosai ya san me fuskar amma mene haɗin Meema da wannan gske har ta sanya aka sawa wani ita? hannunsa Meema ta kama tace “I’m your sister” cikin kwaikwayon Abinda ta faɗa yace “I’m your sister” wani irin Murmushi Meema tayi tace “A’a ba haka za kace ba” kallon Dad tayi tace “Dad his name please” buɗe baki Abbu yay yace “Asheer” “Wow! Nice name” Meema ta faɗa tana faɗin “as from today sunanka Asheer amma zanna ce maka Bro ni kuma kace Sister” dry Dr yay yace “tab kina nufin a yanzu duk zaki koya masa komai? Mudai nan kafin ku tafi zamu kuya masa wanka,Sallah, cin abinci komai” Asheer kuwa tunda ya ɗura idanunsa akan Meema yaƙi ɗaukewa domin tsoran kallon mutanan wajan ma yake, miƙewa tayi zata ɗauko masa mirror da sauri ya riƙe hannunta yana juya idanunsa, da ƙyar dai ya sake ta lokacin da yaga kansa a madubi kansa ne yay wani irin sarawa da sauri ya saki madubin a ƙasa ji kake tasssss ya fashe a ƙasa cikin sauri kuma cike da tsoran abinda yayi ya ɓoye fuskarsa a bayan Meema..

Today is Monday yau Akeem ya tashi da azumin Litinin da Alhamis kamar yadda ya saba, rabonsa da ganin Akeela wajan sati guda kenan, domin ko zama yanzu ba yayi a Parlo, a hankali ya fito daga motarsa lokacin ana ta kiran sallar magrib kai tsaye pampo ya nufa tare da ɗaura alwala, ko cikin gida bai shiga ba ya nufi cikin masjid ɗin, lokacin daya isa ana jiran zuwan liman amma Shiru ganin an rasa wanda zai ja sallar sai kawai yay gaba tare da tada kabbara, nutsuwa kowa yay a hankali cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗin gaske ya fara fidda kira’a yana fidda makarijil huruf, a can gida kuma Akeela na zaune domin ita sosai azumin ya wahalar da ita kuma ta saba tana yinsa ne, idanunta ta buɗe jin sautin Muryarsa ya daki kunanta rabon da taji Muryarsa haka harta mance, Miƙewa tayi saboda wani sanyi da jikinta yay a hankali ta nufi bathroom ta ɗaura alwala kana ta dawo tayi sallah ji tayi jikinta babu daɗi sai kawai ta zame hijab ɗin ta nufi bathroom, cikin sanyin jikinta ta buɗe ƙofar ba tare data rufe ba ta fara kwaɓe kayan jikinta ruwan zafi ta sakarwa kanta tana sauke ajjiyar zuciya.

Bayan an idar da sallah Akeem ya fito Abbu na bayansa a haka suka nufi gida babu kowa Parlo duk Sallah suke, part ɗinsa ya nufa Akeem kuma ji yayi yau babu abinda ya keso sama da zuma yasan kuma Didi kawai ke Shanta, part ɗin ta ya nufa a hankali ya shiga lokacin tana Sallah, wani daɗi yaji domin baya son masifar ta a yanzu, fridge ɗinta ya nufa gaba ɗaya robar zumar ya ɗauko Didi kam banda zare ido babu abinda take da taga abin bana wasa bane sai ta fara “ehem! ehem!” Ko Kallonta bai ba ya nufi waje ai da sauri tace “Assalamu alaikum” miƙewa tayi tana faɗin “Muhammadur Rasulullah s.a.w Audil sata ƙiri ƙiri Ubangiji dai yau ya nuna min ɓarawon zumata” jin tana kiran sunansa kuma ya tabbatar part ɗinsa zata bisa cikin rashin makamar yi kawai ya faɗa part ɗin su Aleema ga mamakinsa sai yaji tana faɗin “Munafikin ai na ganka” da sauri ya juya yana duban inda zai ɓoye ganin ƙofar bathroom a buɗe ya wani faɗa ciki da sauri yana murzawa ƙofar key…..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]