[Advertisements⬇️]

RAWANIN TSIYA CHAPTER 8 BY FADEELAH - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 RAWANIN TSIYA CHAPTER 8 BY FADEELAH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

BUGAJE INDUSTRIES

KANO- CENTRAL+

A yau Monday Hanifa tayi resuming aiki.. A yau din kuma tun da safe Paapa yayi tafiya zuwa qasar South Africa a dalilin wani business deal da zai yi sealing.

Hanifa dai a yanzu haka tun daga ranar da Sadiq ya zo suka yi exchanging words sai ta saki ranta.. Abin mamaki shine tun daga wannan ranar ta daina neman hanyar da zata bi ta wargaza maganar auren instead she is now looking forward to auren don kuwa ta riga ta gama shirya mishi kalolin bala’in da zata yi mishi a gidan shi wanda ko kwana uku bazata yi a gidan ba zata fitine shi ya gaji ya sallame ta.2

Wuraren qarfe Goma da rabi na safe suna zaune a conference room suna meeting.. Sadiq a matsayin shi na General Manager shine yayi chairing meeting din.. Yawanci kusan yana qara jaddada ma kowa muhimmancin role dinshi ne a kamfanin tunda dai as it is lokacin tafiyar shi ya zo, In less than 2 weeks zai tafi. har ma ya riga ya fara shirya hand over notes dinshi.. Gaba dayan su present a wurin idan ka kalli fuskokin su zaka gane they are sad, mai karatu ba wani abu ya sanya hakan ba sai don kewar Sadiq da suka fara yi tun kafin ya tafi..

Tun qarfe tara ne aka fara meeting din wanda kowa yana nan amma banda Hanifa.. Hanifa dai tana sane da meeting din kuma tana zaune a ofis dinta, Niyyanta shine sai ana daf da gamawa zata shiga ta ga tsiya.. Da alama dai ta shirya fara karta ma Sadiq rashin mutunci tun yanzu.

Aikuwa suna daf da rounding up ne ta shigo conference room din cikin isa da gadara.. Sanye take cikin wata doguwar rigar material mai kyan gaske peach color.. ta yafa gyale a kanta wanda bai hana dogon gashin nata fitowa ba.. sai baza qamshi take yi as usual.

Gaba dayan Unit heads din suka dago kai suka kalle ta cike da mamaki.. Ba tare da tace komai ba na ga ta nufi one of the empty seats zata zauna…

“why are you late?? baki ga meeting notification bane??” Sadiq ya tambayeta.

Hanifa wadda ta qarasa kujera ta zauna ce tace “Yes I did..” yayinda ta danna mishi harara

“So???” ya tambaya fuska a murtuke

“So I decided to come in now..” ta fada cike da gadara.

Gaba daya Unit heads sunyi mamakin attitude din Hanifa, Tabbas sun sani cewar bata jin magana toh amma kuma they thought bayan ta gane ko Sadiq waye zata shafa mishi lafiya..

“Okay Ms Hanifa.. you know the rule” ya kalli Musbahu yace “she should pay a fine of N5000 for coming late.. so take note”

Tun kafin ya rufe baki ta miqe tsaye tace “what???”

Gaba daya kowa ya mayar da hankalin shi kanta.. mamaki suke yi ganin reaction dinta, Babu wanda bai san rule na meeting a ofis din ba.. idan kayi latti ko na minti biyar ne sai ka biya fine na N5000 haka idan wayar ka tayi ringing sai ka biya N3000.. a gaban ta mutane sun sha biyan fines dinnan so why is she surprised don an ce zata biya???2

“You heard me right Ms Hanifa..”

“I wont pay a single dime, babu abinda zan biya.. You hear me??” ta fada with so much confidence.

Shi dai Hafeez wanda yake zaune kadan ta rage ya fashe da dariya.. shi fa dama ya san tun kafin ayi auren nan za’a fara drama.

Sadiq ya kalli Musbahu yace “HR deduct it from her salary if she refuse to pay..”

“Nah Mr Sadiq.. ka cire daga cikin kudin sadaki na instead..”9

“what???” gaba daya suka fada confusedly.

STORY CONTINUES BELOW

Sadiq na ga ya kalli Hafeez wanda ya fashe da dariya.. shima abin mamaki sai gani nayi ya girgiza kai yayi murmushi..

“ooh.. dama bai gaya muku aure na zai yi ba??” Hanifa ta tambaye su yayinda kowa yake ta qus qus.

“toh bari in baku labari.. this guy here da kuke gani yana ta stalking dina tunda na fara aiki a kamfanin nan wai he loves me and that he wants to marry me ni kuma nace bana son shi.. well, as you all know tunda kudin shi ke circulating a kamfanin nan yana ji kamar zai iya mallakar komai shine ya lallaba ya zagaya wurin Paapa yayi ‘yan qulle-qullen shi and here we are….”

“ke Hanifa.. please stop this nonsense, why do you have to lie??” Hafeez ya fada ran shi a bace3

Sadiq ne ya daga mishi hannu tare da fadin “dont worry Hafeez, Qyaleta ta cigaba”

Hararar Hafeez tayi tace “idan qarya ne, ba gashi nan ba??? ya fadi mana” ta fada with confidence yayinda ta saci kallon Sadiq wanda yake latsa wayar shi.

Unit heads din dai da suka cika da mamaki sun sa a ran su cewar tabbas qarya Hanifa take yi but they still want Sadiq to clarify because at a point yadda suka ga confidence din Hanifa yayi over sai suka fara tunanin there is an element of truth a maganar ta..

“Sir, wai dagaske Ms Hanifa zaka aura?? shin abinda ta fada dagaske ne??” Yahaya ya tambaye shi

Sadiq wanda ya ajiye wayar da take hannun shi ne yace “Yes its true..”

Daga nan fa wasu daga cikin Unit heads din suka dinga fadin “masha Allah” wasu suna fadin “Congratulations Sir” yayinda wasu suke ta qus-qus…

Sadiq kuwa har murmushi ya dinga yi yana amsawa..

Hanifa dai sakin baki tayi tana kallon shi yayinda ta ga ya miqe tsaye ya dauki file dinshi da wayoyin shi ya kalli Musbahu yace “dont forget to deduct N5,000 from Mrs Bunza’s salary”4

“what???” Hanifa ta fada yayinda Musbahu yace “okay Sir”

“the meeting ends here, everyone get back to work” ya fada sannan ya nufi hanyar fita..

Da sauri Hanifa ta tashi ta bi bayan shi tana fadin “kar ka qara kirana Mrs Bunza..”

Wannan maganar ta Hanifa ita ta sa Unit heads din suka fashe da dariya yayinda suke mamakin irin zaman da za’ayi idan aka yi auren…

Tsare Hafeez suka yi suna neman qarin bayani a wurin shi… qarin bayanin da baya da shi tunda shima har yanzu abun mamaki yake bashi!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Hafeez ne zaune a ofis din Sadiq yayinda suke hira..

“Na rantse da Allah kana da aiki a gaban ka… Hanifa fa bata jin magana. Yanzu fisabilillah meye na dauko zancen auren ku a meeting simply because an ce ta biya fine for coming late?” Hafeez ya fada yana dariya.

“Maybe she thought zan ji haushi ne..” Sadiq ya fada shima yana dariya.

“toh Allah dai ya kyauta.. toh wai yaushe ne bikin naku?? na ji baku ce komai ba..”

“My people are coming to see Paapa next week insha Allah”

“toh Allah ya nuna mana”

Sadiq wanda yake dariya yace “wato dai ka qagara in dauke muku ita kenan?? when you are fully aware of the difficulties she will face a wurina”

“ah, ai gwara ka tafi da ita din bro.. Allah ya taya ka riqo”8

Kafin Sadiq ya amsa ne Suzan tayi knocking qofar ta shigo a hargitse..

Sadiq wanda ya kula da yanayinta ne yace “Suzan what’s the problem?? are you okay??”

Muryarta tana rawa tace “Sir, I just received a call from my mum telling me that my sister has been rushed to the hospital so I need permission from you to please let me go….”

STORY CONTINUES BELOW

Tun kafin ta qarasa Sadiq yace “please go ahead Suzan.. I am so sorry! Hope she gets better soon”

Cike da girmamawa tace “thank you Sir”

“Sorry Suzan.. I wish her a quick recovery” Hafeez ya fada

Shima cike da girmamawa tace “thank you Sir”

Har ta juya zata tafi ne Sadiq yace “Suzan wait..”

Gani nayi ya bude wata drawer ya ciro bundle na 1000 naira notes sabbi gal guda uku (N300,000) ya miqa mata tare da fadin “take this with you and please as soon as you get to the hospital, call me to let me know the situation.. I will come check on you guys later in the day”

“Thank you very much Sir, I appreciate” ta fada tare duqawa cike da girmamawa ta karba.

Ba da don ta san Sadiq zai ji haushi idan bata karbi kudin ba she wouldn’t have collected the money don kuwa sunyi yawa.. ta sani cewar ko tayi insisting ya karbi kudin shi bazai karba ba don haka ne ma batayi insisting ba..

Bayan ta fita ne Hafeez ya miqe tsaye yace “Bro bari in je in cigaba da aiki.. na san kai ma you are busy with your hand over notes”

“Wallahi kuwa bro..”

“anjima zamu je muyi reconciling issue dinnan a bank… Idan akwai wani abu sai ka kira ni..”

“I will Hafeez.. nagode”

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Da yamma bayan sallar La’asar yana zaune a ofis din nashi yana magana a waya.. Wayar dai ajiye take yayinda ya sanya ta a handsfree..

“I am glad you are finally coming home my dearest Mini..”

“Me too Big B, kai zaka zo ka dauke mu daga airport ko??

“No kiyi haquri kin ji Mini.. I still have some days to go a nan Kano so I wont be there to pick you up amma I will make sure your Favorite cousin does..”

“Yeeey..”

Girgiza kai yayi yace “hmmm… this one that you are happy.. tell me”

A daidai lokacin ne Hanifa ta shigo ofis din riqe da wani file yayinda fuskarta take a murtuke… as usual ba tare da tace komai ba ta qaraso ta zauna kan kujera ta tura mishi file a gaban shi…

Muryar Asma’u ta ji tana dariya tace “tell you what Big B?”

“abinda yake tsakanin ki da Faisal..”

Fashewa tayi da dariya tace “kamar yadda kuke da Ya Hanan Haka muke da Ya Faisal…”

“Okay oo.. if you say so but kar ki manta I am watching you guys closely” ya fada yana murmushi.

“bamu son sa ido Big B..”

“aikuwa baku isa ba sai an sa muku.. I am sure Naana ta san wani abu, I will confirm everything from her”

Asma’u dai dariya ta dinga yi yayinda tayi saurin canza topic tace “Me kake so in siyo maka tsaraba??”

Murmushi yayi yace “I just want to see my dearest Asmy and Naana back home safely”

I cant wait to see you and hug you tight Big B”

Murmushi yayi yace “cant wait for that too Mini-Me”

“Big B bari in barka haka.. Ga Naana can tana kira na”

“Okay dear.. Take care and my regards to Naana please”

“I will Big B, I love you”

“I love you so much more.. bye”

STORY CONTINUES BELOW

Bayan ya kashe ne na ga ya dago kai ya kalli Hanifa wadda fuskarta take a murtuke yace “Mrs Bunza how can i help you??”

On normal basis dai Sadiq ko kallon Hanifa bazai yi ba balle har yayi mata magana amma a dalilin ya kula ranta yana baci idan ya kira ta da ‘Mrs Bunza’ ne ya sa shi yi mata magana..

Da sauri ta dago kai ta kalle shi yayinda suka hada idanuwa… ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kasa a dalilin mugun kwarjini da Sadiq yayi mata, Yau itace rana ta farko da suka kalli juna directly at thesame time, Hanifa ta rasa ya zatayi da mugun kyan nan na Sadiq da yake ruda ta…

Da sauri ta saukar da idanuwanta yayinda zuciyarta take bugawa..

“nace ka daina kira na Mrs Bunza.. You know very well cewar I am getting married to you simply because of Paapa.. idan ba haka ba babu abinda zai hada ni da kai”

Ko da na kalli Sadiq wanda ya bude file din da ta kawo you could swear bai ma ji abinda take fadi ba don kuwa ya mayar da hankalin shi kan documents din da ta kawo..

Gani nayi ya natsu yana going through her report carefully.. as usual dai babu error ko alama sai ma outstanding work da tayi wanda da ace shi da ita din they are in good terms sai yayi commending dinta for a job well done..

Bayan yayi signing ne ya rufe file din sannan ya tura mata ya koma kan aikin shi..

Hanifa wadda ta dauki file din tana miqewa tsaye ta ji ta kamar ba daidai ba… da sauri na ga ta kalli kujerar da ta tashi daga bisa yayinda ta zaro idanuwa hankali a tashe…

Da sauri na ga ta koma ta zauna yayinda ta ajiye file din a sanyaye.. Gani nayi jikinta yana rawa yayinda hawaye suka fara bin fuskarta.. she looked super worried and disorganized.

Sheshekar kukan ta ne ya sa Sadiq ya dago kai ya kalle ta..

Why is she crying???

Ba tare da yace mata komai ba na ga ya girgiza kai ya cigaba da aikin shi..

Hanifa ta dora kanta bisa table dinshi ta cigaba da kuka.. Ni kaina na zama confused as to what is happening with her.. Yarinya kamar mai aljanu!!5

Kusan tsawon minti Goma Hanifa tana ta rusa mishi kuka ba tare da tayi magana ba… Sadiq dai gaba daya dauke hankalin shi yayi daga kanta as usual amma kuma at a point kukan nata ya fara cika mishi kunnuwa..

Gani nayi ya ture Macbook dinshi gefe sannan ya kalle ta yace “hey, what’s wrong with you?? meyasa kika zauna mun a nan kina kuka?? as you can see I am very busy so please leave my office..”

Dago kanta tayi tana kallonshi ba tare da tace komai ba… Gaba daya fuskarta tayi jajawur ta kumbura..

Shi kanshi Sadiq sai da ya cika da mamaki ganin fuskarta a hakan.. a yanzu ya tabbatar akwai problem domin kuwa girman kai irin na Hanifa bazai taba barinta ta zauna mishi tana kuka a gaban shi ba tare da dalili ba.. as it is people like her thinks kuka is a sign of weakness!!

Gani nayi ya shafa kanshi da hannuwa biyu sannan yace “kin ga kin ishe ni da kukan nan naki na banza so please if you can just go back to your office and continue your nonsense..”

Hanifa wadda ta kula idan bata sanar da shi abinda yake damunta ba lallai zai iya fitar da ita da qarfi ne na ga ta saki ajiyar zuciya yayinda ta kalle shi muryarta tana rawa tace “please help me”

…and Lo, for the first time Sadiq ya ga a helpless Hanifa!!

Cike da mamaki yace “help??? what kind of help??”2

“Nayi staining kaya ne kuma…” daga nan tayi shiru yayinda ta kasa qarasa maganarta.

“ban gane kinyi…” bai qarasa magana bane yayi shiru a dalilin ya fahimci me take nufi.

“how can you be so careless??” ya fada ran shi a bace cikin fada.

Ba tare da tayi tunani ba tace “toh ai ba laifi na bane.. its suppose to come in three days time kuma ma ni bana jin cramps a duk lokacin da zai zo, how do you expect me to know its com…” bata qarasa magana ba na ga ta runtse idanuwan ta.. da alama ta gane cewar she has gone too far.

Wani irin kunya ne ya cika ta yayinda na ga tayi saurin mayar da kanta bisa table dinshi ta cigaba da kuka..

Why will something like this happen to her?? why in front of mutumin da tafi tsana a duniyan nan??

Sadiq wanda bai bi ta kanta ba gani nayi yana shafa kan shi da hannuwa biyu.. da alama dai mafita yake nema mata.. Gashi Suzan wadda ita ce mace bata nan, asali ma yanzu haka niyyan shi idan ya tashi daga aiki zai je ya duba jikin sister din nata… again, dan uwanta Hafeez ma yana Bank even though ma ko yana nan me zaiyi mata tunda shima namiji ne.

Options biyu suka zo mishi.. either ya fita ya samo mace ‘yar uwarta tazo ta taimaka mata ko kuma ta kira gidansu..

Sanin girman kai irin na Hanifa ne yayi tunani ko ya kira mata wata ba lallai ta saki jiki da ita ba.. qarshe ma ta wulaqanta ta a banza don haka yayi deciding a kira gida..

“Ina wayar ki???”

ba tare da ta dago kanta ba tace “tana ofis dina”

Miqewa yayi ba tare da yace komai ba ya fita..

Bayan mintuna biyu sai gashi ya dawo riqe da wayar ya qaraso wurinta yace “gashi, ki kira Mamy ki gaya mata halin da kike ciki so that ta aiko driver ya kawo miki abinda kike buqata”

A sanyaye ta karbi wayar tayi dialing lambar Mamy.. aikuwa ringing na uku ta amsa.

Ko da Mamy tayi picking call din sai kawai ya ji ta fara bata labarin abinda ya faru in details da kuma abubuwan da take buqata a kawo mata..

Sadiq wanda yake qoqarin tattara kayan shi yana mamakin yadda take yi ma Mamy bayanin dukkan abinda ya faru dalla-dalla tana lissafo abubuwan da take buqata babu ko kunya.. He even expect her to like send a text message to Mamy ko don kunyar shi but she didn’t!

“unbelievable” na ji ya fada ahankali

Bayan ya gama ne ya kalle ta yace “Mrs Bunza I’m off, idan kin gama da ofis din just release the lock.. it will jam automatically from outside”

Hanifa wadda as usual ta ji haushin yadda yayi addressing dinta da ‘Mrs Bunza’ kasa yi mishi masifa tayi.. Da alama halin da take ciki is a more bigger problem for her at the time..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Haka yayi tafiyar shi ya barta tana jin haushin halin da ta shiga a gaban Sadiq da yadda duk kunya ta baibaiye ta..2

Allah ya sani a rayuwarta bata taba shiga kunya irin na yau ba and it’s all thanks to nature.. But ta isa tayi complain ne???!! Nah…Abin mamaki tun daga wannan ranar Hanifa bata qara zuwa ofis ba.. abinda ya faru ya tsaya mata a rai wanda ya sanya ko kadan bata so ta hadu da Sadiq, gani take yi kamar idan suka hadu he will make fun of her with regards.. abinda bata sani ba kuwa shine tun ranar da abun ya faru ya manta tunda dai ko kadan baya sa al’amuran Hanifa a kan shi..+

Dayake dai Sadiq yana ta shirin barin kamfanin he didn’t even care ko Hanifa ta zo ko bata zo ba.. kai a dalilin how very much busy he has become bai ma san cewar Hanifa bata zuwa aiki ba…

Dawowan Paapa daga South Africa ne ya kula bata zuwa and da yayi mata magana sai ta ce mishi tana mura ne kuma ta saukar mata da zazzabi.. Da wannan ne Paapa yasa ta rubuta request na sick-leave ta aika office din…

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

One week later!!

A yau ne Sadiq yayi sallama da Bugaje Industries.. Sendforth lafiyayye aka yi organizing mishi..

Gaba daya ma’aikatan kamfanin were sad a dalilin zai tafi.. A lokacin da yayi farewell speech dinshi kuwa yawancin su sai da suka yi hawaye.. sun saba da shi sossai, Babu qarya Sadiq yayi impacting positively a rayukan ma’aikatan kamfanin.. Yayi upgrading dinsu, a dalilin shi dayawa ma’aikatan kamfanin sunyi discovering potentials dinsu, he was able to bring out the best in alot of them, a bangaren kyautatawa kuwa babu abinda zasu ce sai Allah ya saka mishi da gidan aljannah..

Suzan tayi ta kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.. Sossai take jin dadin aiki da Sadiq, haka shima a bangaren shi ya ji dadin aiki da ita.. Musamman ya ja ta gefe ya dinga lallashinta yayinda ya sanar da ita cewar zata yi aiki qarqashin Hafeez wanda shi zai yi taking over from him sannan ya jaddada mata cewar zata ji dadin yin aiki da shi tunda sun saba.. tabbas ta dan ji sanyi don kuwa ta sani cewar Hafeez baya da matsala. Haka ta dinga yi ma Sadiq godiya tare da yi mishi fatan alkhairi.

Paapa ne ya rufe taron inda ya miqa saqon godiya on behalf of himself and the entire staff of the company zuwa ga Sadiq.. Yayi mishi addu’a sossai tare da yi mishi fatan alkhairi. A qarshe kuwa haka staff din suka dinga presenting ma Sadiq gifts kala-kala yayinda ya cika da mamaki.. Yayi musu godiya sossai na irin karramawar da suka yi mishi.. there is no doubt Bugaje Industries and its entire staff means alot to him..

Ko da zai tafi ya rabu da su Paapa akan zai zo gida da daddare don su qara yin sallama..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE

NASSARAWA GRA

Wuraren qarfe takwas na dare suna zaune a dinning suna dinner- Sadiq, Paapa, Mamy da Hafeez

“I swear bro ji nake yi kamar in riqe qafafuwan ka don kar ka tafi” Hafeez ya fada yayinda su Paapa suke dariya.

Shima Sadiq wanda yake dariya yace “bro kar ka damu, ai muna tare kuma tafiya na shi zai sa ka gane how very good you are.. trust me”

“Still, you will be missed”

Mamy ce tace “gaskiya zamuyi kewar ka sossai Sadiq.. Allah dai ya saka maka da alkhairi yayi maka albarka sannan ya tsare ka daga sharrin masu sharri”

Gaba daya suka ce ‘ameen’

Paapa ne yace “ka yi sallama da Baby kuwa??”

“No sir, dama I wanted to see her saboda I don’t think zan samu zuwa tare da Uncles dina next week cos akwai tafiyar da zanyi…”

STORY CONTINUES BELOW

Paapa yace “I understand Son” ya kalli Mamy yace “tana ina ne bata sauko tayi dinner ba??”

Mamy ce tace “dazu dai Hannatu tace tana sashenta tana sana’arta ta rawa amma ban sani ba ko ta gama..”5

Cike da mamaki Sadiq ya kalli Mamy.. Rawa??? as in dance???

Hafeez wanda yake kallon Sadiq kadan ta rage ya fashe da dariya ganin yadda ya zama confused..

Matsowa yayi daf da shi yace “Your wife-to-be is a dancer bro.. you will be highly entertained by her dancing skills”2

Girgiza kai kawai yayi ba tare da yace komai ba..

Gani suka yi Paapa ya dauki waya yayi dialing.. sai kuma suka ji yace “Baby meet me in the dinning room now”

Bayan ya kashe wayar ko minti uku ba’a yi ba Hanifa ta shigo Dinning din.

Sanye take cikin wandon sweatpant three quarter na mata da wata top ‘yar qarama mai kyau.. A lokacin da ta shigo tana qoqarin kama dogon gashinta a tsakiyar kai don haka bata kula da Sadiq ba..

“Paapa ga ni….”

Qamshin turaren shi da ta ji ne ya sanya ta yin shiru yayinda tayi saurin qarasa daure gashin nata ta tsaya cak.. aikuwa tana ganin Sadiq sai kawai ta juya da sauri zata koma a dalilin tuno last encounter dinsu da tayi – encounter dinsu lokacin da al’adarta tayi mata zuwan bazata a ofis dinshi.3

“Baby come here.. ina zaki je kuma?”

Ba tare da ta juyo ba tace “uhm Paapa ai baka gaya mun akwai baqo ba..”

“Sadiq din ne baqo??”

Miqewa yayi tare da fadin “zo ki zauna yana so kuyi sallama ne kar ki bata mishi lokaci”

Hafeez ne da Mamy suka miqe suma.. Tare da Paapa suka fita.

Sadiq wanda yake latsa wayar shi har bayan da su Paapa suka fita bai daina ba.. he seemed to be doing something important all of a sudden ko kuma dai acknowledging presence din Hanifa ne bazai yi ba as usual..

Hanifa wadda take tsaye tana kallon shi sossai ranta yake a bace na yadda yayi kamar bai ganta ba..

Tsaki ta ja sannan ta nufi daya daga cikin kujerun dinning din ta zauna tace “Mallam fadi maganar da zaka fadi in tafi.. I have important things to do”

Yana kallon wayar shi yace “hold on Mrs. Bunza..”

“Ba nace ka daina kirana Mrs Bunza ba??”

“Yes.. there” ya fada yayinda na ga ya latsa wayarshi sannan ya ajiye ta a gefe ya kalle ta yace “kika ce me??”

Da alama kenan bai ji abinda tace ba..

Ranta a bace tace “nace kar ka qara kirana Mrs Bunza”

Murmushi yayi yace “actually I am not here for you to tell me what not to do or say…”

Gani nayi ya zaro wata takarda daga aljihun shi ya tura gabanta..

Ko da na leqa dai Cheque ne na gani…

Hanifa wadda ta janyo cheque din ce ta dago shi tana kallo.. it’s a blank cheque!!

“what’s this for??” ta tambaya yayinda take kallon shi confusedly

“its for kayan lefen ki da duk wani abinda zaki buqata na bikin ki.. feel free to write as many zeros as you want”

Ranta a matuqar bace ta ajiye cheque din ta tura mishi gaban shi sannan tace “hell you know I don’t need your money right??”

Miqewa yayi tsaye ya kwashi wayoyin shi da makullin motar shi yace “see you after the wedding Mrs Bunza”

STORY CONTINUES BELOW

Ko kafin tayi magana kuwa tuni ya fice abinshi..

Gani nayi Hanifa ta saki baki cike da mamaki.. Ji nayi tace “me yake ji da shi ne? wato don ya nuna mun yana da kudi shine zai dauki blank cheque ya bani har yana fadin in sa ko nawa nake so???”

Tashi tayi ta dauki cheque din tace “na fi qarfin wannan wulaqancin Sadiq.. I won’t take a single dime from you because I dont need your money.. Mayar maka da Cheque dinka zanyi wallahi”

Ni kuwa nace anya Hanifa??? duk son kashe kudin ki??? this is serious!!4

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!!

LATE ALHAJI ABUBAKAR MUHAMMAD BUNZA RESIDENCE- ASOKORO ABUJA

Wuraren qarfe shidda da kwata na yamma tana tsaye a tangamemen kicin din gidan wanda ya hadu iya haduwa.. Tsarin kicin din kamar na gidan turawa, ko ina tsab-tsab kamar ba’a amfani da shi…

Naana wadda take gaban Gas cooker ce take motsa farfesun kayan ciki.. Gaba daya qamshi ya cika kicin din..

Asma’u ce zaune a kan qaramin stool riqe da tabarya yayinda Sadiq yake zuba mata doya a cikin turmi…

Sadiq dai a yau tun da safe ya tattara kayan shi gaba daya ya baro garin Kano.. Gidan iyayen shi ya fara sauka saboda qagara da yayi ya ga Naana da ‘yar qanwar shi Asma’u wadanda suka dawo days ago..

Mai karatu idan ka ga irin murnar da suka yi da suka ka juna zaka rantse sun shekara Goma basu hadu ba.. Maqale da juna suka yini, hatta lokacin da aka kira sallah hana shi zuwa masallaci suka yi.. dole anan gida ya ja musu Jam’i na sallolin azahar da la’asar and from the looks of it hatta magrib da Isha’I duk tare zasu yi ..

Yanzu haka gaba dayan su suka shiga kicin don dafa dinner, they decided to prepare Sadiq’s favorite wato Sakwara da kuma farfesun kayan ciki..

Mai karatu, na san zaka tambaye ni masu aiki fa??? Amsar dai itace Naana bata girki tare da masu aiki, duk arzikin Alhaji Abubakar Muhammad Bunza tun yana raye Cook ko Chef basu taba dafa abincin gidan shi ba, daga Matar shi (mahaifiyar su Sadiq) sai Naana sai kuma Asma’u wadda tun tana ‘yar qaramar ta Naana take koya mata girki.. A yanzu haka babu kalar abincin da Asma’u bata iya ba..

Sadiq wanda ya gama zuba mata doya ne yace “Mini kin tabbata zaki iya??? ko dai muyi a machine din ne???”

Naana ce take yi musu dariya yayinda Asma’u tace “ofcourse zan iya Big B.. ni ai ba ta wasa bace.. just wait and see besides na machine din baya yin danqo irin yadda kake so kamar wanda za’a daka a turmi”

“da kyau ‘yar lelen Naana.. I am so proud of you” Naana ta fada yayinda Asma’u take murmushi.

Shi dai Sadiq tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki yayinda ta fara daka doyar.. nan da nan kuwa sai ga Sakwara lafiya lau..

Aikuwa tana gamawa ya fara clapping yace “wow this is awesome.. I am impressed, I still can’t believe you did this my Mini..”

“i can do alot more Big B and it’s all thanks to Naana” Asma’u ta fada yayinda take qoqarin packaging sakwarar.

Girgiza kai yayi yace “hmmmm.. lallai kam duk wanda zan aura ma ‘yar qanwa ta sai ya biya mu double don kuwa she is a correct wife material”

Asma’u dai murmushi take yi yayinda Naana tace “aikuwa dara ce zata ci gida tunda dai dan uwanka zai biya double din..”

Sadiq yayi ma Asma’u wani irin kallo yace “kenan dai dagaske akwai wani abu tsakanin ki da Faisal shine kike boyewa??”

Asma’u wadda ta cika da kunya gani nayi ta juya zata bar kicin din yayinda yayi saurin cafko ta ya janyo ta jikin shi ya rungume ta yace “hey I am so happy about this.. Faisal dukda dan uwan mu ne and I know you know him well, I will still tell you cewar he is a super great guy.. he is my best friend and I am glad you will be in good hands my love”

STORY CONTINUES BELOW

Cike da murna tace “nagode Big B”

“and the fool never told me?? zamu hadu da shi, wannan respect din dai sai ya bani shi idan ba haka ba in hana mishi ‘yar qanwa ta”

Naana da Asma’u suka fashe da dariya yayinda Naana tace “ai kuwa idan dai akan Asma’u ne har durqusa maka qasa zai yi”

Breaking hug din yayi ya ja kumatunta yace “hmmm, I am glad I wont have to worry about how you will be treated a gidan auren ki because you will surely be in good hands. Allah ya sanya alkhairi”

Asma’u dai kasa amsawa tayi.. Murmushi kawai take yi..

Naana ce tace “ameen”

Asma’u wadda take so a canza zancen ce tayi saurin fadin “zaka sha Orange Juice???”

“Ofcourse yes My Mini, add some ginger too if you would please..”

“Sure Big B, bari inyi sauri in hada maka kafin Naana ta gama”

“thanks my love..”

Daga nan Asma’u ta tafi dauko abubuwan da take buqata na yin Orange Juice din.

Sadiq kuwa komawa yayi wurin Naana yayi hugging dinta ta baya tare da sakar mata light kiss a kumatu yace “do you need help??”

Tana murmushi tace “I got everything under control Abba amma zaka iya ka fara setting table while I finish this up tunda dai na ga kana son yin aiki ne”

“Toh ai Naana na ga bai dace in bar ku kuna ta aiki bane ku kadai.. I am a gentleman you know”

Murmushi tayi tace “ashe amaryar ka zata huta kenan…”

Murmushi kawai yayi yana mamakin yadda zai shiga kicin don taimaka ma sakarya yarinyar nan Hanifa!!4

********************

Zaune suke a danqareren dinning room din gidan wanda yake da masifar kyau.. Komai looking so classy and elegant.. Again, nan din ma tsab tsab (spotlessly clean)

“I swear I missed your food Naana.. rabona da cin abinci irin wannan tun last time da nayi visiting dinku a Switzerland.. God bless your hands”

Asma’u ce take ta yi mishi dariya yayinda Naana tace “yanzu kana nufin girkin amaryar taka bai kai wannan ba???”

Sadiq wanda yayi murmushi ne yace “Allah ma dai yasa ta iya”

“hmmm yaran zamani.. kana dai so kace abincin Chefs zaku dinga ci a gidan naku” Naana ta fada tana murmushi.

Tun kafin yayi magana ne suka ga Asma’u wadda ta bata rai jin an fara maganar Hanifa ta miqe tsaye tare da fadin “Ni na qoshi..” daga nan ta juya ta fita daga dinning din yayinda suka bi ta da idanuwa.

Ajiyar zuciya ya saki yayinda ya juyo yana kallon Naana wadda itama shi take kallo..

“Ya zanyi da ita ne???”

“kar ka damu zata daina.. ka san gani take yi kamar shikenan idan kayi auren zaka manta da ita ne kwata kwata..”6

“but you know it’s not gonna happen ai Naana.. Asma’u is my top priority a rayuwar nan.. she is my only sister for crying out loud” ya kalli plate dinta yace “look at her plate, bata ci komai ba ta tafi”

Miqewa yayi yace “bari in je in duba ta” ya dauki plate din abincinta da Orange juice sannan ya wuce ya fita daga dinning din..

Naana ta girgiza kai tana murmushi tace “Asma’u hoo… Allah ya shirye ki”

Wayarta ce tayi ringing yayinda ta duba ta ga sunan Mummy (Maman su Yazeed)

*****************

Kwance take a kan gadon dakinta mai masifar kyau.. Mai karatu idan na tsaya yi maka bayanin kyan tsari irin na dakin Asma’u zamu bata lokaci.. Daki ne kamar na sarauniya, duk wani abin jin dadi na rayuwar dan Adam akwai shi a wannan daki, komai na cikin dakin abin kallo ne.. Its an extremely beautiful room specially for a beautiful princess..

Sadiq ne ya nufi bedside drawer dinta ya ajiye abincin sannan ya haye kan gadon ya zauna..

“Mini…”

“leave me alone..”

Girgiza kai yayi yana murmushi yayinda na ga kwanta a gefenta yace “why should I leave you alone when you’re the only one I have a rayuwar nan??”

Shiru tayi bata ce komai ba amma dai kukan da take yi ta daina..

“Yes aure zan yi amma kuma ai na fadi miki cewar bana son matar.. and I even promised to tell you about it.. kin manta ne??”

Wannan karon ma shiru tayi bata ce komai ba..

“Well……” daga nan ya fara bata labarin haduwar shi da Hanifa da irin abubuwan rashin hankalin da ta dinga yi mishi har zuwa yadda Paapa ya nemi ya aureta da kuma dalilin da ya sanya shi ya amince din…

Asma’u wadda tuni ta tashi zaune tana kallon shi har ya gama bata labarin ce tace “like seriously Big B??? who gave her the right to treat you the way she did? I swear da ina nan bazan taba bari tayi maka abinda tayi ba.. ta san ko kai waye da zata wulaqanta ka haka?? does she know how very precious you are to us??”1

Sadiq wanda yake murmushi ne yace “kiyi haquri Mini.. ai yanzu zata gane”

“toh but wait Big B.. Yanzu kana nufin wai idan ta gyara hali sai kawai ka sake ta???”

“Yes”

“But…”

“But what Mini??”

“I mean idan in the process you fall in love with her fa?? ka san fa turawa sun ce Fights are a sign of Truelove.. dont you think one day everything will change??”3

Hararar ta yayi yace “I can’t believe ke da Hanan think thesame.. I don’t see the possibility of me falling in love with a lady, much less Hanifa”2

Murmushi tayi tace “ni na rasa dalilin da ya sa kai da Ya Hanan baku so kuyi aure.. I swear kun masifar dacewa”

“ita ce ai bata so but I am still hoping she’ll accept my marriage proposal don kuwa idan bata amince ba ban san ya zanyi ba”

Asma’u ce ta fashe da dariya yayinda yake murmushi..

“zaka yi competition da Ya Hussain kenan??”

“forget about competing with him, I know I will win besides blood will forever be thicker than water.. Yeah??”

Fashewa tayi da dariya tace “Yes Big B..”

Tashi zaune yayi ya janyo plate din abincin yace “Okay toh.. now its time to eat my Mini..”

Cikin shagwaba tace “kai zaka bani da kanka..”

“Your every wish will forever be my command Princess..”

Daga nan kuwa ya fara bata da kanshi yayinda suke ta hira… Mostly hirar Switzerland, Faisal da Hanan!!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]