[Advertisements⬇️]

RAWANIN TSIYA CHAPTER 6 BY FADEELAH - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RAWANIN TSIYA CHAPTER 6 BY FADEELAH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

3 days later!!+

BUGAJE INDUSTRIES

KANO- CENTRAL

Zaune yake a ofis dinshi yayinda yake qoqarin kammala project dinshi na online course din da yake yi.

It’s been 3 months kenan da yayi registration na wani advanced course mai suna Strategic Business Analytics a ESSEC Business school na qasar France. Sadiq dai yayi Online business courses dayawa, wannan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya zama professional when it comes to business dealings. A yanzu haka wannan particular course din ba kowa ne zai iya yin shi ba domin kuwa sai kana da wasu special qualifications.. Course din yana da bala’in wahala sannan ga tsada. Lokutta da dama Sadiq yakan yi da-na-sanin yin course din saboda yana draining mishi energy da time sossai.. though he has gained alot from it don kuwa it’s an advanced business strategy wanda yake applying in both companies that he is running toh amma dai kawai ya gaji.3

Ranar Saturday da Sunday ne za’a yi presentation na final project through Zoom wanda daga shi an gama sai karbar certificate. Sossai ya qagara a gama ya huta.7

He has spent alot of his time and energy, infact harda sleepless nights in order to get his project done.. Yanzu haka yana finishing touches ne and going through to correct the minor errors he’s made..

Hanifa ce ta shigo office din kai tsaye ba tare da tayi sallama ba balle ta qwanqwasa qofar.. ita dai Suzan tun tana zuwa tana ba Sadiq haquri akan yadda Hanifa take shiga ofis dinshi har ta daina tunda dai ta kula ‘yar mai kamfanin ce kuma da alama bazata taba dainawa ba.

Wasu files ne na gani a hannun ta yayinda ta qaraso wurin shi tana hararar shi ta zauna ta tura mishi su gaban shi a wulaqance ba tare da tace komai ba.

Har yau idan Hanifa ta tuno yadda Sadiq ya barta ta kwana a Cell ji take yi kamar ta shaqe shi.. A yanzu haka sai gabza mishi harara take yi wanda bai ma san tana yi ba!

Sadiq wanda as usual bai dago kai ba balle ya kalleta ne yake mamakin halin banza irin na Hanifa.. and this brought him back to the conversation he had with her Dad 3 days ago.

A ranar dai Sadiq ya lallaba Paapa ne ya ce mishi zai yi tunani akai and he will get back to him.. he couldn’t say no amma kuma its definately a NO.. Babu yadda za’ayi ya dauki yarinyar da ya tsana ya kai ta gidan shi.. dukda kuwa dalilin yin haka is something he’d love to do amma still.. Tsanar da yayi ma Hanifa is just out of this world.4

Addu’a yake yi akan Allah yasa kar Paapa ya qara dauko mishi zancen wanda in less than a month da ya rage mishi ya tattara yayi tafiyar shi..

Hanifa wadda take zaune tayi zooming takardun da suke gaban shi da kuma manyan litattafai na Business.. hakan ya tabbatar mata da lallai karatu yake yi.

Bata ankara bane ta ji wayar shi tayi ringing yayinda ta ga ya duba..

Video call ne from his Mini-Me

Answering yayi tare da saita wayar da kyau a kan phone stand yadda zata dinga ganin fuskar shi.. Ko da na leqa, fuskar wata kyakyawar cute yarinya na gani, tana yanayi da Sadiq amma ta fi shi haske.

“Assalamu alaikum” ta fada cikin zazzaqar muryarta mai masifar dadi.

“wa’alaikis Salam Asma’ul Husna sarauniyar mata” ya fada yana murmushi.

STORY CONTINUES BELOW

“ni fa ba wani dadin bakin da zaka yi mun Big B.. ina ta jiran call dinka na ji shiru and I called you baka yi picking ba.. I am sure kunyi waya da Ya Hanan” ta fada cikin shagwaba

“hey my love yi haquri.. Your Big B has been soo busy with his project, remember I told you cewar gobe da jibi ne presentation din mu? infact mine is tomorrow.. Gani nan ina qoqarin in kammala ne. kiyi haquri I swear I was gonna call you.. kin san Big B cannot survive a day without hearing from his Mini”

Hanifa wadda take sauraron su da farko tayi zaton budurwar shi ce wanda har tana mamaki ya bar conversation din open tana ji amma kuma yadda sukayi addressing juna da ‘Big B’ and ‘Mini’ ne ya sa ta gane qanwar shi ce… Haka kawai sai ta ji sun bata haushi, ko meyasa???

Murmushin Jin dadi na ga tayi sannan tace “I missed you alot Big B.. rabona da ganin ka fa kusan five months.. tunda ka fara zama a Kanon nan baka qara zuwa Switzerland ba unlike before that you come even twice in a month..”

“Sorry my love.. you know abokin Abba needed my help shiyasa amma I am almost done here  plus ke ma ai saura two weeks ki gama Zurich ku dawo gida and we will all be back together insha Allah”

“Yes Big B.. wallahi na qagara in gama mu dawo. Dagaske a Nigeria zan yi Masters dina and please don’t say no”1

Murmushi yayi yace “I wont my love, duk abinda kike so shi za’ayi..”

“Yauwa, thank you so much, you are the best big brother and I love you”

“You are the best little sister and I love you too Mini-Me.. and please kiyi karatu sossai, I just dont want you to pass, I want you to graduate as the best student in Zurich.. please do make me proud”

“Insha Allah Big B, I wont let you down”

Murmushi yayi yace “thats my Mini, Now can I get back to my project work??”

“Yes you can..”

“toh ki gaida mun da Naana, ki ce mata I love her to the moon and back and that I will call her later”

Shiru tayi bata ce komai ba yayinda take kallon shi tana ta turo baki..

Murmushi yayi yace “Okay, Okay.. I love you too my dearest Asmy, more than life itself and I will call you too later”

Murmushi tayi tace “I love you”

“bye???” ya tambaye ta

“No”

“what again Mini??”

“My kiss”

Gani nayi yayi mata blowing kisses yayinda ta cafke tana murmushi tace “thank you Big B, Bye”

“Bye”

Bayan ya kashe wayar ne ya cigaba da project dinshi yayinda Hanifa take zaune…

Wayar shi ce ta qara ringing.. Ko da ya duba sunan productions Manager ya gani – Isma’il

Yana answering ne yace “Mr Isma’il how is it going??”

Shiru yayi yana sauraron abinda Isma’il din yake fadi.

Ji nayi yace “ah okay, I am coming” sannan ya kashe wayar ya miqe tsaye..

Da sauri Hanifa ma ta miqe tace “ban gane ba.. ya za’ayi in shigo ofis dinka in dade a zaune sannan ka dade kana hirar banza a waya ka kasa tambaya na what I’m here for and now you just stand up and leave me here??? like what do you mean??”1

Sadiq wanda ko kadan bai bi ta kanta ba ya nufi mini lounge dinshi ya dauki wani file da yake kan centre table sannan ya wuce zai fita..

“You need to sign these papers now, its urgent” Hanifa ta fada da sauri da ta kula dagaske fita zai yi ba tare da ya saurare ta ba.

STORY CONTINUES BELOW

Har ya bude qofa ne na ga ya juyo ya kalle ta sannan yace “leave them there, idan na dawo zanyi signing. if they were urgent you would have asked for my signature as soon as you came in instead of sa mun idanuwa da kika yi kamar mayya”4

Daga nan ya juya ya fita yayinda ya bar Hanifa tsaye cike da mamakin kalaman shi…

Ranta ne yayi mugun baci.. wato dai Sadiq baya taba missing opportunity na ya wulaqanta ta..

Ni kuwa nace ke kina missing ne???2

tsaki tayi sannan ta wuce ta fita.

********************

Hanifa dai har ta shiga ofis dinta ta zauna sai kawai ta tuno da kalar wulaqancin da Sadiq yayi mata..

Zaraf na ga ta miqe yayinda ta fara kai da komowa a tsakar ofis dinta..

Ji nayi tace “this is enough Hanifa.. dole in nemi abinda zanyi mishi da zai bata mishi rai shima, bai kamata in barshi ya dinga wulaqanta ni ba yadda ya ga dama simply because da kudin shi ake running kamfanin nan..”

Cak na ga ta tsaya yayinda ta saki murmushi tace “I know what to do” Daga nan kuma na ga ta wuce ta fita da sauri.

Ni kuwa nace ina zata je??

Ko da Hanifa ta fito daga ofis dinta gani nayi ta wuce ofis din Sadiq straight.. Tana qoqarin shiga ne Suzan tace “Ma’am he is not back..”

“I know, I just want to pick up something I left” ta fada ba tare da ta jira jin abinda Suzan din zata ce ba ta shige ofis din.

Da sauri na ga ta nufi desk dinshi ta zauna kan kujerar shi ta janyo Macbook dinshi..

Project work dinshi da yake yi ne akan screen din.. briefly na ga tana ta scrolling tana kallon abinda yayi. Dukda she is not familiar with abinda ta gani ta sani cewar it’s an outstanding work wanda babu qarya aikin natsuwa yayi shi.2

Ban ankara ba na ga hannun ta ya kai kan ‘delete’1

Hankalina ya tashi yayinda nake ta fadin No no no amma inaaa.. bata ji ni ba!

Da farko dai kamar ta ji ni don kuwa gani nayi tayi pause for a while tana tunanin tayi ko kar tayi..

Runtse idanuwa tayi ta bude sannan tace “I need to hit him hard no matter the consequence.. zan ga yadda zai yi presentation din gobe”

Ba tare da bata further time ba kuwa ta danna ‘DELETE’

Da sauri kuma na ga ta shiga Recycle Bin shima tayi permanent delete yadda bazai iya recovering ba and just like that project din Sadiq ya bace…4

Nikuwa hannu na sa a kai cike da tsananin tashin hankali.. me kenan Hanifa tayi??

Miqewa tayi da sauri ta wuce ta fita daga ofis din.

*****************

Sadiq ne ya shigo ofis dinshi tare da Hafeez da Isma’il suna magana akan production din da ake yi.

“I am impressed gaskiya, na tabbatar sabon method dinnan zai fi yielding result. Well done Mr. Isma’il” Sadiq ya fada yayinda ya zauna a kan kujerar shi.

“Thank you Sir, Yanzu abinda muke jira shine approval dinka na expenses din da muka yi magana da kai..”

“Yes please, kar ka damu.. just prepare everything and I will approve”

“Okay Sir” Isma’il ya fada tare da miqewa yace “excuse me”

Hafeez ne yace “Go ahead”

Bayan Isma’il ya fita ne na ga Sadiq ya janyo files din da Hanifa ta ajiye mishi ya bude yayinda ya fara going through.

STORY CONTINUES BELOW

One thing da ya kula da Hanifa shine tunda ta fara aiki a kamfanin bai taba ganin mistake ko error ba a few assignments din da yake bata.. infact she does an extraordinary job, he believes ko ya tafi ita da Hafeez will take the company to greater heights baya shakka a kan wannan. Her problem will be her character and attitude towards work wanda zai zama major set-back domin kuwa a leader is always suppose to lead by example sannan idan har subordinates dinta are not happy with the way she treats them, productivity will definately be low!!

Bayan ya gama signing files din ne na ga ya danna wani button akan intercom yayinda Suzan tace “Sir”

“please come”

“okay Sir”

Nan da nan ta qwanqwaso ta shigo ofis din.

Files din Hanifa ya dauka ya miqa mata tare da fadin “take this to Hanifa, tell her to make sure she investigate before proceeding”

“Okay Sir” ta karba sannan ta fita.

Agogo ya kalla sannan yayi relaxing bayan shi a kujerar da yake zaune yace “Ya Salam.. I really cant wait to finish up this course in huta”

Hafeez ne yace “Gobe ne zaka yi presentation dinka ko???”

“Yes bro.. and I have to submit my work today” ya fada yayinda na ga ya gyara zama ya janyo Macbook dinshi.

“All the very best Bro.. bari nima in…”

“Wait what am I seeing????” Sadiq ya fada yayinda ya miqe tsaye a rude yana kallon screen din Macbook dinshi.

Hafeez wanda ya cika da mamaki bai taba ganin Sadiq ya rude haka ba… Da sauri shima ya miqe yace “what happened???”

Gani nayi Sadiq ya koma ya zauna yayinda yayi wasu ‘yan latse-latse. Dafa kai yayi da hannuwan shi biyu yace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un”

Hafeez ne yace “bro what is it?? please tell me”

“My project is gone..” ya fada cikin wata irin murya -Murya mai dauke da tsananin bacin rai, rudewa da kuma damuwa…

“what??? Kana nufin…” ya dan yi shiru sannan ya cigaba da fadin “wait amma ba ka ce you were on it ba lokacin da ka same mu a factory?”

“I was on…” bai qarasa magana bane na ga yayi saurin danna intercom.

Tun kafin Suzan ta yi magana ne yace “please come”

Nan da nan ta shigo ofis din domin a yadda ta ji muryar ogan nata ta tabbatar akwai matsala.

“Sir” ta fada yayinda ta qaraso jiki a sanyaye.

“Who came into my office when I stepped out??”

“Uhm, Ms Hanifa..”

“there…” ya fada tare da dukan table dinshi wanda har sai da Suzan ta razana.

“I am sorry sir, she said she forgot something in..”

“Just go Suzan.. thanks”

Hafeez wanda ya cika da mamaki ne yace “kenan Hanifa tayi maka deleting project??”

Sadiq wanda ya cika fam da bacin rai yace “let’s find out”

Gani nayi ya janyo wani remote ya kunna wata screen da take jikin bango yayinda yayi wasu ‘yan latse latse..

Ni kuwa ina kallo sai na gane Screen ne na CCTV cameras din da suke ofis din.. Ya Salam, Hanifa is sure in trouble!2

Yayi playing daidai lokacin da ya fita daga ofis din inda ta tsaya kadan sannan ta bi bayan shi ta fita itama..

Haka suka cigaba da kallo har few minutes later da ta dawo ofis din da yadda ta zauna tayi deleting sannan ta fita.

Sossai hankalin Hafeez ya tashi da ganin wannan al’amari.. Kallon Sadiq yayi wanda ya runtse idanuwa ya bude sannan ya miqe tsaye..

Da sauri shima ya miqe yace “Bro..”

“ina zuwa” ya fada sannan ya wuce ya fita.

*****************

Hanifa ce tsaye a jikin table dinta yayinda hankalinta yake a matuqar tashe.. Da ganin yanayin fuskarta ka san a rude take don ko da Suzan ta shiga ofis dinta dazu sai da ta zabura saboda a tunaninta Sadiq ne.

Aikuwa tana nan a tsaye ya banko qofar ya shigo fuskar shi a murtuke.

Zuciyarta ce ta buga da ganin yanayin shi..

Gani nayi ta ruga a guje ta koma bayan kujerar ta tsaya yayinda take kallon shi a tsorace.1

“how dare you?? ina wasa da ke ne?? do you have the slightest idea of what you just did to me?? is this some sort of a game to you??”

A tsorace tace “Yes it is, you started it and ni kuma na rama abinda kake yi mun.. I told you I was gonna..”

“You are very stupid Hanifa..”

“I am not stupid, sai dai idan kai ne Stupid din”

Cike da mamaki yake kallonta, like did she just insult him??

Runtse idanuwa yayi ya bude sannan yace “Well guess what??? you just signed your ticket to hell.. I assure you, zakiyi regretting abinda kika yi for the rest of your life” bai tsaya sauraron ta ba ya fita yayinda ya barta a rude.5

Sossai kalaman shi suka firgita ta.. haka kawai ta ji for the first time ta tabo abinda bazata iya accommodating ba, something she cant even handle.. his threat really hit her hard.

Gani nayi ta zame a lungun da take tsaye dafe da zuciyarta wadda take bugawa kamar na wadda tayi gudun kilometer dari yayinda ta zama so confused.3

“what have I done??” ta fada yayinda na ga ta hada kanta da gwiwa. Tuni kanta ya fara ciwo!!2

BUGAJE INDUSTRIES

KANO- CENTRAL+

Zaune yake a kan daya daga cikin kujerun lounge dinshi yayinda yake magana a waya.. Wayar ma ajiye ta yayi a kan centre table yayinda ya sanya ta a Speakerphone. Da ganin yanayin shi zaka gane yana cikin damuwa..

Hafeez wanda yake zaune a gefen shi har ya fi shi shiga damuwa. He is a living witness to what Sadiq has gone through in order to compile his project work, he knows the time, energy and sleepless nights he has spent just for this project, infact tun kafin shi da Hanifa su fara aiki a kamfanin nan yake yin project din and just like that Hanifa ta ruguza mishi komai..

“Sir please can I have a grace of one week to see what I can come up with?”

“I am so sorry i really can’t help you Mr Bunza, you will have to make the submission before the end of today and do your presentation tomorrow”

Ajiyar zuciya Sadiq ya saki sannan yace “Okay Sir.. merci”

“de rien Bunza..”1

Bayan Sadiq yayi sallama da Professor din ne ya koma ya kishingida..

Allah ya sani ran shi ya baci, bai taba yin course mai wahala da cin lokaci ba irin wannan… just when he thought ya gama finally Hanifa tayi mishi wannan lalatar… Yes he has the knowledge amma Certificate din fa???

“Gaskiya Hanifa bata kyauta ba.. instead of ma ta baka haquri sai ta zage ka?? ka tabbatar baka son Paapa ya ji wannan zancen??” Hafeez ya tambaye shi

“what’s the point? please ba sai ya sani ba.. bawan Allah yana fama da jikin shi bai gama warwarewa ba all thanks to the stupid garl. kar ka damu.. haka Allah ya so. As for her, ba dai game take playing ba? trust me, she just took on the baddest game player”5

Ghen ghen ghen!!!

☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE

NASSARAWA- GRA

Wuraren qarfe shidda na yamma Sadiq ne zaune a falon Paapa.

Asali dai yana tashi daga ofis ya kira Paapa ya sanar da shi cewar yana so ya gan shi idan da hali shi kuma yace mishi he can come whenever he wants to.

“Ya office din?? hope komai lafiya??” Paapa ya tambaye shi.

“Alhamdulillah Sir, everything is in order”

“Madallah.. thank you very much Son.. Ka taimake ni sossai.. Ubangiji Allah yayi maka albarka”

Murmushi Sadiq yayi yace “Ameen”

“Zuwa Monday Insha Allah nima zanyi resuming.. if not for doctor’s orders akan bed rest dinnan, I would have resumed already.. Zaman haka nan babu dadi wallahi”

“Kar ka damu Sir, komai yana tafiya smoothly.. besides, hutun yana da matuqar amfani a wurinka”

“Haka ne Son.. So tell me, to what do I owe this visit da har ka kasa isa gida ka huta??”

Ajiyar zuciya na ga Sadiq ya saki sannan yace “dama akan maganar da muka yi ne 3 days ago”

“Maganar Hanifa???” Paapa ya fada with so much hope wanda didn’t go unnoticed by Sadiq.

“Yes Sir, Nayi tunani akai and I am willing to help you change her to a better person.. Zan aureta in tafi da ita kamar yadda ka buqata” Ya fada confusedly.1

STORY CONTINUES BELOW

Da alama dai a big part of him is telling him not to but somthing is pushing him to use the opportunity ya rama abinda tayi mishi…14

“Alhamdulillah.. nagode Son! Allah ya saka da alkhairi. Na tabbatar Baby zata gyara hali idan ta zauna da kai” Paapa ya fada cike da farin ciki.

Sadiq yayi dan murmushi yace “its okay Sir, I’d do anything within my power to help you, to me you are a father-figure”

“I really appreciate Son, duk lokacin da ka shirya sai ka sanar da ni”

“Insha Allah Sir”

“Sorry na manta ban tambaye ka ba, gobe ne presentation na project dinka ko???”

Sadiq wanda ya tuno da abin baqin cikin ne yace “eh Gobe ne”

“Masha Allah, Allah ya taimaka..”

“ameen Sir, nagode”

Daga nan dai suka cigaba da random hirar su as usual. A cikin hirar ne Paapa ya dinga jaddada ma Sadiq na lallai ya tabbatar ya hora Hanifa ba tare da tunanin wani abu ba.. according to him, the sooner he disciplines her, the faster she learn her lesson ya sallamo mishi ita.7

Ni kuwa nace haba Paapa, ba sai ka jaddada ba.. ai baka sani ba Sadiq is more than glad to have this opportunity.. No doubt about it!! tabbas Sadiq ba zai yi Mata da wasa ba and surely she will have a taste of her own medicine…

Ko da Sadiq ya bar gidan, Paapa ya sanar ma Mamy cewar yayi mishi tayin auren Hanifa kuma ya amince amma fa bai sanar da ita cewar auren na dan lokaci bane.. this will remain a secret on his end! Ita dai Mamy tayi murna sossai na jin cewar Hanifa zata yi aure.. Ko banza zata tafi ta barta ta huta.. Ta kuma tausaya ma Sadiq amma kuma sanin cewar he is a no-nonsense guy ne ta tabbatar zai ci qaniyarta idan tayi mishi shirme..4

Paapa ya so ya sanar ma Hanifa zancen amma dayake tunda ta dawo daga ofis tayi complain din ciwon kai.. ko da ta sha magani ta shige daki bata qara fitowa ba.

Asali dai ba wani abu ya janyo mata ciwon kan ba sai rikicin da suka yi da Sadiq da fargaban abinda zai yi mata… For the first time a rayuwarta tayi regretting yin wani abu. Haka kawai take ji a jikinta lallai consequence na action dinta will be drastic..4

Habawa Hanifa..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BRISTOL PALACE HOTEL

NASSARAWA- GRA

Wuraren qarfe tara da rabi na dare yana zaune a kan wani dogon stool na mini kitchen dinshi riqe da fork yayinda na ga wani plate mai dauke da slices na fresh apple a kan island din da yake gaban shi.. iPad dinshi ce ajiye a kan stand dinta yayinda na ga yana qoqarin kiran ta- Hanan

Kyakyawar fuskarta ce ta bayyana a screen dinshi tana murmushi.

“My handsome Chocopie.. how are you??”

Shima murmushi yake yi yace “fine my beautiful Hanan.. me kike yi??”

Pop corn ta kai bakinta yayinda ta hasko mishi TV briefly tace “kallo”

“Ke kam kin cika kallo, I wonder how many movies you’ve watched a rayuwar ki..”

“and still watching..” ta fada tana dariya

Slice na Apple ya kai bakin shi yana murmushi.

“Kan ka yana ciwo kenan”

ta fadi hakan ne a dalilin Apple da ta ga yana ci.. Shi dama Sadiq a duk lokacin da yayi anticipating ciwon kai zaka gan shi da Apple. As it is Apple yana boosting lafiyar qwalwa.. Yana yin haka ne in order to run away from magani.. a duniya idan akwai abinda ya tsana bai wuce magani ba!

STORY CONTINUES BELOW

“uhmm.. kinda, just taking precaution”

“eyyah.. Allah ya baka lafiya. the stress da kake undergoing ma yayi yawa.. dealing with two big comapnies is not easy at all”

“it’s almost over ai.. just few weeks to go”

Fork din hannun shi ya ajiye sannan yace “Hanan I have something to tell you”

“what is it handsome”

“I am getting married”

“what??” ta fada yayinda ta saki cup na pop corn din da yake hannun ta duk ya watse.

Fuskar Hanan tayi displaying tsananin tashin hankali yayinda yanayinta ya canza lokaci guda..

Shi kanshi Sadiq ya zama confused ganin reaction dinta.. her reaction seemed like that of a jealous lady. Tabbas ba tun yau ba Sadiq yayi sensing cewar Hanan tana son shi. Hatta ‘yan uwan su gaba daya sunyi sensing hakan. Ba tun yau ba ya sha confronting dinta amma sai tayi denying.. Ya so ace tayi admitting dukda kuwa he doesn’t care about the love tunda bayada ra’ayin soyayya, Ya so ace kawai ta amince ta aure shi because he believes cewar ita ce macen da zai iya zama da ita har iya tsawon rayuwar shi without any problem… Hanan ‘yar uwar shi ce (cousin) and she is his best friend.. ta san halin shi kamar yadda ya san nata sannan dukkanin sirrin junan su sun sani.. babu abinda zai fi mishi sauqi irin zaman aure da ita..3

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Chocopie au… re za.. ka..yi da.. wa??” ta fada muryarta tana rawa.

Shafa kan shi yayi da hannuwan shi biyu sannan yace “Hanifa”

Gani nayi ta runtse idanuwa sannan ta bude tace “dama son ta kake yi Chocopie?? I thought da Paapan ta yace ka aure ta you told me you won’t..”

“No Hanan.. wallahi bana son ta, kin sani cewar bani da ra’ayin soyayya much less with someone like Hanifa.. the thing is..” daga nan ya shiga bata labarin abinda ya faru.

“…so I am only getting married to her saboda ina so in saita mata hankali..”

Hanan wadda take kallon fuskar shi ce tace “Yanzu kana nufin course dinka ya tashi a banza Chocopie???”

“Wallahi kuwa Hanan… all my effort ya tafi a banza thanks to the stupid girl”

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “toh what if ka aure ta kuma ka fara son ta fa???”4

Murmushi yayi tare da girgiza kai yace “So fa kika ce… Haba Hanan, in rasa wadda zan so a rayuwa ta sai Hanifa? kin kuwa san irin tsanar da nayi ma yarinyar?? please stop”1

Shiru tayi ba tare da tace komai ba.. da alama dai she is worried wanda shi da kanshi ya sani. its unlike Hanan ace suna hira tayi sanyi haka.

“Hey why do I feel like you are worried?? are you jealous??…” Kashe mata ido daya yayi ya cigaba da fadin “…my offer still stands fa.. just agree to marry me and I swear zan fasa aurenta dukda dama ba dadewa zai yi ba”

Matse hawayen da yake neman zubowa daga idanuwan ta tayi yayinda tayi murmushi tace “Hell No Chocopie.. Hussain nake so kuma shi zan aura..”

Murmushi yayi yace “Shikenan.. ni dai I am available whenever you decide to change your mind”

Hanan wadda take kallon shi girgiza kanta kawai tayi bata ce komai ba…

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE

NASSARAWA- GRA

A yau da safe wuraren qarfe tara da rabi tana zaune a gaban Vanity mirror dinta yayinda take applying light make up. Daure take da wani dan qaramin towel Baby pink color.. da alama dai daga wanka ta fito.

STORY CONTINUES BELOW

Wayarta ce tayi ringing yayinda ta miqe da sauri don tayi picking.. The only ringtone da yake sa tana saurin picking call- Wanda ta sanya ma Paapa.

“Hello Paapa ina kwana”

“Lafiya lau.. idan kin gama breakfast ki same ni a falo na”

“toh Paapa” ta fada a sanyaye

Daga nan sai ta ji yayi disconnecting call din.

Cike da mamaki ta bi wayar da kallo.. wai yau Paapa ne yake share ta haka!

Hanifa dai da qyar ta shawo kan Paapa ya rage fushin da yake yi da ita.. A ranar da ya kore ta a gaban Sadiq, bakin qofar dakin shi ta je ta zauna ta dinga rusa kuka.. Dayake dai Allah ya dora mishi so da tausayin Hanifa babu yadda ya iya dole ya haqura amma dai still the relationship is not as before.. Sanin haka ne ya sanya ta qudiri niyyan yin duk wani abinda zai sa su koma normal tunda dai her Paapa is her life, tana zuwa aiki da wuri, tana gaida Mamy yadda yakamata and she try as much as possible to treat the maids yadda yakamata.. the only thing da ta kasa yi shine daina wulaqanta Sadiq.

“why does he wanna see me??” na ji ta tambayi kanta yayinda kuma na ji tace “maybe he has fully forgiven me and he wants to let me know”

Murmushi na ga tayi sannan ta ajiye wayar ta miqe tsaye ta wuce closet dinta.. Bangaren Native na ga tana dubawa yayinda ta fara bin su da kallo. Wata Red atamfa mai kyau ta janyo sannan ta koma wurin under wears dinta nan ma tayi selecting.

Nan da nan kuwa ta shirya cikin kayanta wanda aka yi ma dinkin fitted gown.. Sossai kayan suka yi mata kyau

Turaruka ta janyo ta dinga fesawa, aikuwa nan da nan dakin ya dauki qamshi.

Idan ka kalli Hanifa da yadda ta ci gayu sai ka rantse fita zata yi.

Wayarta ta dauko sannan ta wuce ta fita daga dakin.

A lokacin da ta shiga dinning room ta tarar da breakfast dinta a kan table, da ganin yanayin table din ta tabbatar kowa ya riga yayi breakfast dinshi don haka zama tayi tare da danna bell.

As usual mai aiki ta shigo da sauri ta duqa har qasa ta gaishe ta sannan ta zuzzuba mata abincin kamar yadda ta san tana so.

Bayan ta gama ta wuce dakin Hanifa don gyarawa.. da alama dai that’s the routine!

Hanifa dai sossai ta ci breakfast dinta don kuwa jiya da daddare bata ci komai ba ta kwanta saboda ciwon kai da ya dame ta.

Ina kallonta ta gama sannan ta tashi ta fita.

*****************

Zaune yake a kan three-seater na babban falon shi yayinda Mamy take zaune a gefen shi.

Hafeez yana zaune a kan single seater wadda take nesa da su yayinda suke hira suna kallon tashar BBC.

Hanifa ce ta shigo falon cikin sallama wadda ta ba Mamy da Hafeez mamaki. Lallai babu shakka Hanifa tana neman sulhu da Paapa tunda har yau da bakinta ta rangado sallama..

Paapa ne ya amsa sallamar yayinda ta qaraso ta zauna a kan kujerar da take kusa da tashi ta kalli Mamy tace “ina kwana Mamy”

Mamy tana murmushi tace “lafiya lau Hanifa.. kinyi kyau…”

Murmushi ta dan yi sannan tace “thank you”

Kallon Hafeez tayi wanda shima ita yake kallo tace “hey”

Yace “Hi” daga nan ya ja bakin shi yayi shiru.2

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “Paapa gani”

Remote din hannun shi na ga ya ajiye sannan ya kalle ta yace “Ya ciwon kan naki?? kin warware??”

STORY CONTINUES BELOW

“Yes Paapa”

“Allah ya qara sauqi”

“Ameen Paapa” ta fada harda sakin murmushi. Da alama dai she is happy da Paapa yayi enquiring about her health, this alone shows they are good!1

“I have something very important to tell you.. ga Mamy ga Hafeez…”

Zuciyar Hanifa ce ta buga jin kalaman Paapa.. tuni murmushin da yake kan fuskarta ya bace, haka kawai ta ji jikinta yayi sanyi yayinda ta ji a jikinta lallai abinda Paapa zai fada ba abu bane da zai yi mata dadi..

“Aure zan daura miki da Sadiq..”

Wani irin kallo tayi ma Paapa yayinda ta saki baki..

Hafeez na ga ya kalli Paapa ya kalli Mamy da sauri yayinda ya cika da mamaki yace “what??”

Hanifa wadda da alama bata dauki zancen dagaske ba tace “Paapa this is not April oo.. We are in October”1

Murmushi Paapa yayi yace “I know Hanifa.. it’s not April fool besides ai ban taba yi miki April fool ba, ke ce kike yi mun remember??”

Zuciyarta ce ta buga yayinda ta dafe qirjinta daidai saitin da zuciyarta take. Idanuwanta ta runtse yayinda tace “No no no..”

“the truth is halin nan naki da kike displaying Hanifa ya ishe ni haka.. it’s like soyayyar da nake nuna miki ita tayi miki yawa da har kike wulaqanta mutane yadda kika ga dama.. nayi tunanin abinda zai iya sa ki canza hali and I came up with marriage. I am sure idan kika yi aure zaki fahimci rayuwa.. I know cewar at this point baki da saurayi shine na duba na ga Sadiq shine zai iya riqe mun ke yadda nake so and nayi mishi magana kuma ya amince…”

“no no no no no…” take ta maimaitawa yayinda ta toshe kunnuwan ta da hannuwanta wanda bai hana ta jin maganar Paapa ba.

Kuka kawai take rusawa babu sassauci..

Ban ankara ba na ga ta sauko qasa ta matsa wurin Paapa tare da riqe qafar shi tace “don Allah Paapa kar kayi mun haka, wallahi Paapa duk abinda kake so zanyi maka amma kar kayi mun aure, kar ka aura mun mutumin da na tsana a duk fadin duniyan nan, wallahi Paapa mugu ne.. qarya yake yi baya sona. Idan ka aura mun shi mutuwa zanyi..”

Hafeez dai tunda Paapa ya fara magana kan shi ya daure.. does this have to do with abinda Hanifa tayi ma Sadiq jiya?? Sadiq ya amince zai auri Hanifa?? how???

Gani nayi Hanifa ta koma wurin Mamy ta hada hannuwan ta guda biyu tana ta kuka tace “don Allah Mamy ki bashi haquri, wallahi zan canza hali na..”3

Mamy wadda ta sa hannu ta share mata hawaye ce tace “kiyi haquri Hanifa..”

Hanifa bata jira Mamy ta gama magana ba na ga ta sa hannu a kai tace “na shiga Uku..” ta koma wurin Paapa tace “Paapa please don’t do this to me.. idan akan laifin da nayi mishi ne wallahi zan bashi haquri..”

Paapa ya kamo hannuwanta biyu ya riqe yace “Baby, listen to me. this has nothing to do with wani laifin da kika yi.. believe me, I am doing this for your own good. Ni mahaifin ki ne kuma bazan taba yi miki wani abinda zai cuce ki ba don haka idan dai ni na haife ki kuma kin dauke ni da daraja you will have to accept…”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” abinda na ji Hanifa ta koma fadi kenan non-stop yayinda ta cigaba da kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.3

Ni kuwa nace ai wannan din qanwar saqon mutuwa ce… ah toh!!!BRISTOL PALACE HOTEL

NASSARAWA- GRA+

Wuraren qarfe Goma sha daya da rabi na safiyar yau yana zaune a kan kujerar lounge na suite dinshi riqe da iPad dinshi..

Yanzu haka tun da sassafe yake ta trying Hanan bai samu ba.. abin mamaki ita ma bata kira shi ba.

A jiya dai dukda sun rabu like there is no tension tabbas yayi sensing otherwise.. tun safe yake so ya fita yayi wasu ‘yan shopping amma ya kasa.. Sossai ya shiga damuwa saboda he didn’t hear from her this morning. Ya tabbatar maganar auren shi ne yayi hitting dinta hard toh amma his problem is why won’t she just accept his proposal a wuce wurin??

I wonder ooo!!3

Incoming call ne ya shigo iPad din nashi wanda yake hoping Hanan din ce amma inaaa..

Naana ce.

Yana answering na ga fuskar wata kyakyawar dattijiya ta bayyana a screen din.

Da ganin wannan dattijiyar dai tana hutawa domin kuwa yanayin jikinta ya nuna hakan.

“Angon Hanifa..” ta fada tana murmushi yayinda ya turo baki tace “Naana please stop..”

“ban gane stop ba.. ba ango bane kai ko me??”

“Kawai ban saba da title din bane Naana, kuma ma ai ban zama ba tukun..”

“Zaka saba kuma zaka zama insha Allah Abba.. ai wallahi na ji dadi sossai. tun jiya da daddare da ka fadi mun wannan zancen nake cikin farin ciki.. har salloli nayi cikin dare na gode ma Allah tare da yi muku addu’ar samun zuri’a na gari. Ai kam tunda kace ‘yar gidan Alhaji Aliyu Bugaje na tabbatar ‘yar mutunci ce..”10

Sadiq wanda yake kallonta murmushi kawai na ga yayi ba tare da yace komai ba.. A ranshi kuwa fadi yake yi if only she knows who Hanifa is.1

“Ka sanar ma su kawun naka ko??”

“Yes Naana, na sanar musu”

“madallah, yanzu zuwa yaushe suka ce za’a sa bikin??”

“Sai kun dawo Naana, for now dai idan Uncle Nazif ya samu lokaci ya zo Nigeria sai su hadu da Big Daddy da su Yazeed sai su zo neman auren”

“aikuwa hakan yayi daidai.. Allah ya sanya alkhairi. Na dai san amaryar ita zata hada kayan lefen ta da kanta ai ko?? tunda na ga haka ake yi yanzu”

Murmushi yayi yace “Naana duk yadda kuka ga ya dace haka za’a yi”

“ai dacewa kenan.. I am sure amaryar taka zata buqaci hakan. Idan mun dawo sai mu fara shirye shiryen shagalin biki”

“No Naana, daga daurin aure shikenan. You know I don’t like those things”

“toh Abba, duk yadda kake so haka za’ayi. Ai dole in lallaba ka kar kace ka fasa”

Fashewa yayi da dariya yace “ai bazan taba fasawa ba Naana… wannan auren da yardan Allah sai nayi shi”1

“Ikon Allah, lallai kana son yarinyar nan.. shine nake kiran ka ango kana wani noqewa”

Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.

“Ni da nake nan ina sa ran na gida za’ayi tsakanin ka da Hanan ashe ba haka bane”

Yana murmushi yace “Naana ai Hanan ta dage akan bazata aure ni ba”

STORY CONTINUES BELOW

“toh meyasa?? bayan kowa ya sani cewar tana sonka.. toh ai ga irinta nan garin kallon ruwa kwado yayi mata qafa”

Fashewa yayi da dariya yayinda ya canza topic din.

“Mini-Me har yanzu fushi take yi??”

“ai fa ka san an shiga uku.. zaka yi mata kishiya na tabbatar bani da sauran zaman lafiya.. gata nan zaune tana ta kumburi tun safe, karatun ma yau ta qi yi.. da alama ma baccin kirki bata yi ba”

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Mini please show your face..” Ya fada yayinda yake cikin tsananin damuwa.

Naana ce ta dora mata iPad din a kan cinya tace “gata nan sai ku sasanta” ta miqe ta fita daga falon.

Gani nayi ta dauki iPad din yayinda ta sa mishi idanuwa.. hawaye ne suke bin fuskar ta.

“My Mini ki daina kuka.. kamar yadda na fadi miki jiya babu macen da zata dauki spot dinki a zuciya ta.. You are my first and only Love, all others will have to follow far behind you”

Har yanzu dai bata ce mishi komai ba.. turo baki tayi tare da kauda kanta.

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Okay, let me tell you a secret. I dont even love her”

Da sauri ta kalle shi tace “what??? toh meyasa zaka aureta idan har ba sonta kake ba???”

Murmushi yayi yace “it’s a long story and I promise to tell you idan kin dawo.. besides she is not even the kinda girl I like. though zan fadi miki only if you keep it a secret”

“Top secret Big B, I promise” Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “thank God.. for a moment I thought ka samu wadda zata maye gurbi na a zuciyar ka Big B.. ko baccin kirki na kasa yi jiya”

“Hell no my Mini.. ke ce ta farko. I love you very much my jewel”

“I love you too.. yaushe ne Presentation dinka?”

Kai tsaye yace “sai qarfe biyu”

“toh bari in barka ka yi rehearsal kafin time dukda na san zaka yi clearing dinsu.. ni kam ban taba ganin mai irin qwalwar ka ba Big B”

Dariya yayi yace “I’m just struggling ne My Mini, kin fi ni qwalwa ai..”

Hararar shi tayi tace “hmmm.. tell the people that don’t know you”

Haka dai suka dan taba hira sannan suka yi sallama.

Gani nayi ya dauki wayar shi yayi dialing lambar Hanan yet again amma ta kai shi straight to voicemail.. don haka ne na ji ya bar Mata message kamar haka:

“Please Hanan call me, I am sick worried about you.. gashi it’s almost 12noon here in Nigeria and I didn’t hear from you. Not fair..”

Miqewa yayi ya dauko makullin motar shi da wallet dinshi ya wuce ya fita..

Ko da ya iso car park wayar shi ce tayi ringing wanda ya duba da sauri thinking its Hanan.. but unfortunately for him ba ita bace..

Cousin dinshi ne Faisal..

Yana answering call din ne ya ji sun fashe da dariya..

Girgiza kai yayi yace “guys meye haka??” yayinda ya bude mota ya shiga yayi setting din wayar ta carplay.

Faisal ne yace “hmmm.. gaya mana zaka yi yaushe ka zama Romeo da har ka fara soyayya bamu sani ba.. No wonder ka koma Kano kayi zamanka ka bar ni da aiki a nan, sai ka ga rashin kyautawar naka yayi yawa sai ka zo kayi kwana biyu ka koma”

“hey, ba fa abinda kuke tunani bane”

Muryar Yazeed ya jiyo yana fadin “shine kuma muka ji maganar aure ta fito?? I really cant wait to see the special lady that robbed you..”

STORY CONTINUES BELOW

“toh wai tsaya, yanzu shikenan ba da Hanan za’ayi ba kenan??” Faisal ya tambaye shi

“Hanan doesn’t wanna marry me besides tana da saurayi..”

“and you believe her???” Yazeed ya tambaye shi

“the thing is Hanan loves you kuma ka sani.. I am not sure why she says she doesn’t wanna marry you.. but na tabbatar she won’t be happy about this” Faisal ya fada.

“mu dai muna nan muna jira a sa rana mu shafa fatiha.. Allah ya sani I am happy” Yazeed ya fada

Sadiq dai can’t believe how happy everyone is just because yace zai yi aure.. if only they know cewar auren ba mai dorewa bane, if only they know cewar aure ne wanda babu soyayya babu jituwa a tsakanin shi da matar. Well, it’s a secret that only two people can keep for him- Hanan da Asma’u. same people that are not happy about the wedding.

☆☆☆☆☆☆☆

NAZIF ABU-DAWOOD RESIDENCE

SHEIKH ZAYED CITY- CAIRO EGYPT

Kwance take a kan cinyar Umma tana kuka yayinda Umma take ta masifa.. tun jiya da Sadiq ya fadi mata zai yi aure ta shiga tsananin tashin hankali.

Haqiqanin gaskiya shine Hanan tana bala’in son Sadiq but unfortunately for her shi din so na ‘yan uwanta yake mata. Sadiq is never a guy to fall in love easily.. ta san da hakan. On the other hand, Hanan mutum ce wadda take son soyayya, she wants to be loved kuma ta san bazata taba samun wannan daga wurin Sadiq ba.

Gaba daya dangin su always suspected cewar Hanan tana son Sadiq and kullum tana kan denying.. yanzu kuma da ta ji zai yi aure ta kasa boyewa.

“ashe dama son Sadiq kike yi dagaske shine kika dinga qaryatawa?? why didn’t you tell us the truth? toh yanzu da kike ta rusa kuka meye amfani??”

“Umma bazaku gane ba.. Sadiq ba sona yake ba”

“Ya zaki ce ba son ki yake ba kina matsayin ‘yar uwar shi??”

Wayarta ce tayi qara alamar message ya shigo.. Voicemail din Sadiq ne. Nan da nan tayi playing ta ji message dinshi kamar haka:

“Please Hanan call me, I am sick worried about you.. gashi it’s almost 12noon here in Nigeria and I didn’t hear from you. Not fair..”

Runtse idanuwa tayi yayinda wasu hawayen suka qara gangarowa… Umma wadda ta saurari Voice message din ce na ga ta girgiza kai.

Umma wadda ta ji voice message din ce ta girgiza kai tace “a gaskiya ban ji dadin wannan al’amari ba.. da kin fito fili kin sanar mana cewar kina son shi ai da yanzu ke zai aura.. a halin yanzu kuwa it’s too late tunda ya samu wadda yake so don haka dole ne ki rungumi qaddara kiyi haquri.. Allah yasa hakan shi ya fi zama alkhairi”1

Hanan wadda take sauraron Umma bata ce komai ba.. Fashewa tayi da sabon kuka.

Umma dai tuni ta daina masifa ta koma lallashi.. Nan da nan kuwa jikinta ya dauki zafi yayinda wani mugun zazzabi ya saukar mata.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BRISTOL PALACE HOTEL

NASSARAWA GRA

Sadiq ne ya shigo suite dinshi riqe da wata qaramar fancy bag yayinda Hafeez yake biye da shi a baya.

Asali dai Hafeez ya kira shi ne a waya ya tambaye shi ko yana nan amma yace mishi ya fita shine yace mishi idan yana dawowa zai kira shi sai su hadu a Suite dinshi.

STORY CONTINUES BELOW

“me zaka sha??” Sadiq ya tambaye shi yayinda ya shiga mini kicin dinshi.

Hafeez wanda ya samu kujera ya zauna ne yace “I am okay bro.. daga gida na fito”

Gani nayi Sadiq ya bude Fridge ya ciro bottle water ya bude ya sha sannan ya fito riqe da shi a hannun shi.

Tun kafin ya zauna ne Hafeez yace “wai don Allah dagaske ne zaka auri Hanifa? does it have to do with sakarcin da tayi maka??”

Sadiq wanda ya zauna yana murmushi yace “Not really Hafeez.. kawai Paapan ta ne ya roqe ni alfarma akan in aure ta toh kuma ka san babu abinda zai nema a wuri na in kasa yi mishi eventhough wannan din abu ne mai wahala…”

Wani irin kallo Hafeez yayi ma Sadiq yayinda Sadiq din yace “hey ka daina yi mun irin wannan kallon.. just leave it as it is please”

“hmmm.. well okay. Amma fa you need to see Hanifa da yadda ta rikice.. gaba daya ta hargitse. Idan ka ga yadda ta dinga roqon Paapa akan kar ya aura mata kai zaka rantse mutuwa zata yi. Yanzu haka da na bar gidan tana can ta rufe kanta a daki, I just pray she won’t do something stupid..”1

Murmushi na ga yayi sannan ya cigaba da fadin “…but hey, I am happy about this ko banza na san idan ta zauna da kai dole ta gyara hali. Discipline din da take lacking na san finally zata same shi overdose”1

Sadiq wanda yake dariya yace “I swear kai mugu ne Hafeez.. instead of ka roqar ma ‘yar uwarka mercy shine kake fadin haka? shame on you”

“kai bro bazaka gane bane.. Hanifa first class ‘yar wulaqanci ce.. Girman kanta da ji-ji da kanta is outta this world, gashi bata iya magana ba.. Da mun biye mata ni da Mamy da tuntuni ta sa an kore mu daga gidan. I swear Paapa yayi tunani mai kyau. Kai kadai ne zaka iya saita ta.. I am sure you will do well… Mu kam don Allah kuyi sauri kuyi auren ka tafi da ita mu huta”7

Sadiq wanda yake ta dariya ne na ga yana dialing lambar Hanan yayinda yace “for sure Hafeez, I will be glad to deal with her”

Wayar Hanan har ta gama ringing batayi picking ba.. Gani nayi ya dan bata rai yayinda yace “what’s wrong with you?”

“Kai da wa??”

“wallahi my cousin sis.. ina ta kiran wayarta tun safe baya zuwa yanzu kuma ya gama ringing batayi picking ba… Nayi dropping mata messages bata responding..”

Layin Umma na ga yayi dialling yayinda yace “let me call her mom”

Aikuwa a ringing na biyu tayi picking.

“Thank God Umma.. ina wuni”

“lafiya lau Ango, how are you?”

“I am fine.. please Umma ina Hanan?? tun safe ina kiranta amma bana samu?”

“bata jin dadi ne sossai Sadiq, Yanzu haka bacci take yi”

Tun kafin Umma ta rufe baki Sadiq ya miqe tsaye tare da fadin “what?? me ya same ta??”

“hey, calm down.. Kan ta ne yake ciwo kuma ta sha magani.. I am sure she will feel better when she wakes up”

“Ya salaam.. Please Umma idan ta farka just call me”

“I will Sadiq..”

Bayan sun yi sallama ne na ga ya jefar da wayar yayinda ya fara Safa da Marwa yana ta shafa kanshi da hannuwan shi guda biyu..

Hafeez ne yace “Bro ya dai??”

“She is not feeling fine..” ya fada a sanyaye

“Allah sarki, hope it’s not serious???”

“Her Mom said it’s not amma I have a feeling it is.. a minor headache won’t stop Hanan from calling or answering my calls, Something is not right”

“toh ba na ji kace idan ta farka a kira ka ba?? just wait zuwa anjima sai ka ji.. Allah ya bata lafiya”

Kafin Sadiq ya amsa ne wayar Hafeez tayi ringing.

Mamy ce ta kira shi..

Da sauri yayi answering call din yace “Mamy..” bai qarasa rufe baki bane na ji yace “subhanalillah.. what happened??”

Miqewa yayi tsaye yace “Gani nan zuwa”

Sadiq wanda yake kallon shi ne yace “hey me ya faru??”

“Hanifa babu lafiya, an kira likita yana duba ta. are you coming with me??”

Wani irin kallo Sadiq yayi mishi yayinda ya dan yi murmushi yace “Sorry, I thought since she is your wife-to-be maybe zaka so ka..”1

“Just go Hafeez, Allah ya bata lafiya”

“Ameen, I just hope ba maganar auren ku bane ya sa ta shiga wannan halin..”

“well, I hope shine” Sadiq ya fada yayinda Hafeez ya girgiza kai yana murmushi yace “da kyau discipline Master, I will call you”

Sadiq dai girgiza kai kawai yayi yana murmushi yace “Allah ya shirye ka Hafeez”

Hafeez ya fita yana dariya!

Gani nayi Sadiq ya janyo wayar shi da sauri yana latsawa..

Ko da na leqa gani nayi yana duba international flight going to Egypt a yau zuwa gobe da safe. aikuwa yayi sa’a ya samu mai tashi da asuba from Abuja to Cairo kuma fortunately for him akwai free seats dayawa meaning zai iya booking which means he will have to leave for Abuja yau dinnan.

Nan da nan na ga ya zauna ya fara following procedures na booking flight din..¹³

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]