[Advertisements⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.” Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa.
Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.”
Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu.

Daya ledar takalma ne sawu ciki kala biyu, sai turaruka da agogo mai kyau a kwalinsa. Hajiya ta fadada fara’arta.
“Lallai abu yayi, masha Allah.” Alhaji ya ce, “An zo gurin, irin wadda ki ke so ko? Ma su kumbar susa.” Ta cc, “A’a Alhaji, ai mu ma ba a tsiyace muke ba.”
Ya ce, “Amma tunda a ka ambaci Alhaji Baita ki ke washe baki.” Shatima ya ce, “Badi’atu kwashe ki maida, amma ki bar ma su Hajiya turarukan.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Alhaji ya ce, “Kwashe masa abinsa kin san dai na maza ne, me za ki yi da shi?”
Ya nufi hanyar fita yana fadin “Sai na dawo.” Hajiyar tana fadin “Allah Ya shi maka albarka, sai ka dawo. Badi’atu ta nufi saman shi tana fadin “Don Allah Yaya ka jira ni.” Shi dai ya tafi yana mamakin Hajiyarsa, a nasa sanin Hajiyarsa bata daga cikin mutane masu kwadayi.
Ginin Shatima da ke Rigachikun ya kankama, domin aiki ake yi babu dare babu rana, ko’in ce ba-ji-ba-gani, Flat ne guda hudu aka yi su suna kallon juna, kowanne yana dauke da manyan dakuna guda uku, kowanne da bandaki.Sai makeken falo da kicin babba, sai sito da ke manne da kicin din. Akwai Baranda a gaban kowane gini, sannan ga fili ishasshe wanda zai dauki sama da mota goma.
A tsarinshi yafi son sai ya kammala gininshi tsaf! Sannan zai tunkaro maganar aure. Yasan jan aiki ya dauko, komai sai ya yi uku kila ma hudu, don har yanzun yana ji a jikinsa ta hudu tana tafe.
Ranar wata Asabar suna tsaye a harabar gidan nashi da yake gini, lokacin ana yin rafta ne.
Munnir ya ce, “Gaskiya abokina kana matukar kokari. Dubi yanda aiki ya yi nisa sosai.” Shatima ya ce, “Ba a magana. Yanzu haka na soma tunanin shiga asusun su Hajiyata da Alhaji.”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Munnir ya ce, “Ai ginin akwai shi da cin kudi. To yanzun kowace tasan da wata kenan?” Ya ce, “Duk sun sani, yanzu zan tsara ma kaina yanda zan yi hulda da su kafin lokacin auran.”
Munnir ya ce, “Har da wani tsari da zaka yi musu?” Ya ce, “Sosai ma kaga dai zan dinga ziyartar su ne bayan kowane karshen wata sau daya. Sannan kuma zan ke kiran su sau biyu a cikin kwana goma. Www.bankinhausanovels.com.ng
Zan ke tura musu katin waya na Naira dubu daya a duk sati. In nayi haka ba zan gundure su ba, suma ba za su gundire ni ba.”Munnir ya ce, “Kamar kiran da kace a waya sau biyu a kwana goma ya yi kadan Shatima ya ce, “Ba ni da wani aikin kenan sai nasu, kiran ma awa dai-dai ne.”
Ya ce, “To in wata cikin su ta kira ka fa?” Ya ce, “In ina da abin yi ba zan daga ba, in bani da shi zan daga in ji dalili, in abin mai mahimmanci ne in saurara, in ko shirme ne in ce ina da abin yi.”
Munnir ya ce, “To in wata tayo message fa?” Ya ce, “Zan karanta in na amsawa ne in ba da, in ko akasin haka ne in share.” Munnir ya yi ‘yar dariya, “Lallai mutumina kana yin abubuwan ka da tsari.”
Nafisa tana kwance cikin bargo, da zazzabi ta dawo daga Makaranta. Duk da ta sha magani bata daina jin sanyin ba. mama tana gefenta tana yi mata dan fada cikin damuwa ta ce, “Haba Nafisa, duk kin sa kanki damuwa tun daga ranar da ki ka san maganar nan kin bi kin damu.
Sai kin sa ma kanki wani ciwon sannan za ki ji dadi, shi fa ba zai fasa auren sauran ba, ke in kin je babu lafiya yaushe za ki yi wata gama a idonshi.
Wayar Nafisa tana ta ruri, har sau biyu. Mama ta ce, “Ina wayarki ta shiga ne? ina jin kararta daga cikin bargon.” Ta ce, “Bar ta kawai kila Mufida ce A na uku Mama tasa hannu ta ciro wayar a kusa da filon da ta tada kai. Ta kalli wayar “Ai Shatiman ne ma ya ke kiran ki.”
Ta tashi zaune da sauri ta amshi wayar, Mama tayi murmushi sannan ta fita. Nafisa ta daga. Ya ce, “Sweety ina ki ka shiga ina ta kira ba ki daga ba?”
Muryarta can kasa tana kuma rawa irin ta marasa lafiya. Ta ce, “Yaya bani da lafiya ne.” Ya ce, “Subhanallah! Tun yaushe?”
Ta soma shesshekar kuka. “Na kwana biyu.” Ya ce, “Shi ne ba ki fada min ba? haba Sweety! Ban so ba da ki ka yi haka, me ke damunki?”
Ta ce, “Zazzabi ne.” Ya ce, “To kin je asibiti?”Ta ce, “Mama ta ce muje na ce a’a, ina shan
magani a gida Ya ce, “Wa ya fada miki ana Www.bankinhausanovels.com.ng
zama da ciwo? Ina Mama din. ki bata.”
Ta yunkura ta tashi ta ce, “Bari in kai mata.” “Za ki iya tafiya amma ko?” Ta ce “Bari na kokarta.” Ya ce, “Ban ji dadi ba Sweety, na kira ki muyi hira sai kuma in ji kina ciwo?”
Ta ce “Ga Mama din.” Ya gaida ta, sannan ya fara korafın ya ya za’ayi a biye ma Nafisa don ta ce ba za ta asibiti ba?Mama ta ce, “Kaga Nafisa rigima ce da ita, tun daga ranar da ta ji cewa su uku ne rana daya tasa ma kanta damuwa take wannan ciwon. Ya ce “Au! Dama wannan ne?” Ta ce, “Shi ne.” Ya ce “To shi ke nan Mama bata wayar muyi
magana. Mama ta mika mata wayar, ta nufi daki tana “Hello!” Ya ce, “Sweety kin bani mamaki, kin san ya ki ke a zuciyata kuwa?”
Dadi ya rufeta, ta kara shagwabewa. “Ni Yaya
sai ina ganin don iyayenmu suka hada mu shi yasa
ka ke share ni, kuma ka fi son su.” Ya ce, “Ni na fi son wadda tafi sona, ke ga shi ma har yanzun ban tashi daga Yaya a gurinki ba.”
Ta ce, “To zan daina cewa, kuma Allah Yaya duk nafi sonka.” Ya ce, “Gashi kin sake fada bayan mun yi da ke sunan da zan kira ki da shi shi ne za ki kira ni.
Cikin shagwaɓa ta ce “To zan ce.” Ya ce, “To ce ina ji.” Tayi ‘yar dariyar kissa. Ta ce “Sweety.” Ya ce, “Kai! Kin iya fada, dan kara in ji.” Ta sake fadi. Ya ce, “To na kashe Yaya din nan ko matata?”
Ta cc, “Eh.” Ya ce, “Don Allah ki tashi daga ciwon nan kar ki zo ranar biki ba ki yi kyau ba. Ni fa kin san bana son mace ramammiya.Ta ce, “To ai ba ka kirana ne kuma baka zuwa.” Ya ce “Wannan ba shi ne yake nuna bana sonki ba, aikina yana da yawa, kullum fa Kaduna ni ke zuwa ina dawowa, ga aiki a gida, ga ginin ku da za ku zauna. Abubuwa da yawa.”
“To amma za ka ke kirana?”
“Duk lokacin da na dan samu sarari kamar haka zan kira ki, kuma zan zo yanzun dai kin warke?” Ya tambayeta cikin nuna kulawa.
Ta ce, “Na warke.” Ya ce, “Yauwa sweety, duk lokacin da ki ka tuno ni kiji a ranki cewa ina tare da ke dari-bisa-dari.”
Haka ya yi ta nuna mata sonsa har sai da ya
tabbatar ta gamsu, ta kuma yarda yana yinta sosai.
Tsawon awa daya kafin yayi sallama da ita.
Washegari misalin karfe takwas ya dawo daga Masallaci ya shiga motarsa ya zauna don ya yi waya da Aliya.
Daidai lokacin da kiran ya shigo wayarta an dace da zata duba kudinta, ta gama saka lambobi ta danna kenan kiran ya shigo, don haka ko ringing bata yi ba ya zama ta daga. Duk da taga sunan Shatimanta ne bata so haka
ba, sai ka ce tana zaman jiranshi. Amma sai ta sa a kunne cikin kissa tayi sallama ya amsa, sai ta ce, “Laa! Wai kai dinne da gaske?” “Kina zaman jirana ne?” Ya tambayeta.
“Ina yin mamaki ne a zuciyata ne naji cewa ina danna gurin amsa kira, nasa a kunne zan ji muryarka, lallai sona da kai wani abu ne na musamman.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Nasan haka, ba ki bukatar sai kin tuna min shekaru uku kina jiran soyayya, ba abin mamaki ba ne don kin ji a jikinki cewa kirana zai shigo.”
Ta ce, “To mu gaisa in ji lafiyarka.” Ya ce, “Ina cikin koshin lafiya, sai so da kaunarki da ke kara samun mazauni a zuciyata.”
Ta lumshe ido. “Ni ko ina nan ina tunanin ya ya ka kare da ‘yar uwata, ko ta amince zata zauna, da mu din?” Ya ce, “Ai tunda ki ka bani wannan shawarar naje na gwada. Tayi sosai, na kara miki lambar yabo a cikin kaunarmu.” Ta ce, “Naji dadin haka.” Ya ce, “Ke kamar kya yin kishina, wasu kuma suna cewa kishi yana daga cikin so, haka ne?”
Ta ce, “Ai kishin jahilci shi ke så wa ayi ta tashin hankali my love. Mu da muke Musulmi, gidan Manzon tsira (S.A.W) shi ne fitilarmu, kalar kishin matanshi zamu yi, kishin faranta maka tare da ba ka shawarwari nagari.
Kuma don ina kishinka ba zan kauda kai ga abin da ka ke so ba, zan danne in so abin da ka ke so tsakani da Allah. Ina jin sauran matanka dani zamu zauna tamkar ‘yan’uwa.”
Ya ji dadin kalamanta, har yace”Ke ta daban ce a mata my love, haka a zuciyata.” Taji dadi matuka. Suka ci gaba da hira har ta ke tambayar shi yana ganin auransu zai dauki tsawon wane lokaci?
Ya ce, “Me yasa take tambaya?” Ta ce, “Ka san an ce me kwarmin ido da wuri yake soma kuka.” Ya ce, “Haka ne. Ni dai a tsarina sai na gama muku wurin zama, sannan in zo kan batun biki, don bana son a sa min rana mai tsawo. Komai-da-komai dai bana son ya wuce na da wata tara.”
Ta ce, “Allah Ya nuna mana lokacin. To ammal kafin lokacin za a sa manya a ciki ko?” Ya ce, “Eh mana, da zarar sun gama bincike su za su zo ga manyanku, itama awa guda suka kwashe kafin suka yi sallama,
Ita ko Amna yafi jin dadin yin waya da ita in yaje kwanciya, Don haka sai da ya gama komai na al’adarshi kafin ya kwanta sannan ya kira ta.Yau ya ci sa’a a kiran farko ta daga, bai san ma ta dagan ba sai da ya ji ‘yar muryarta ta ce, “Hello honey.” Ya ce “My honey kina lafiya?” Ta ce, “Kamar yanda ka ke.”
Suka yi hirarsu irin ta so da kauna, bata kawo mishi batun sauran ‘yan matan ba, shima bai dauko mata ba. Tsawon awa daya yana yada manufarshi kafin suka yi bankwana.
Bayan duk bincike sai a ka tura neman aure, babu inda aka samu matsala sai gidan su Amna, in da suka nuna a dan jira in sun gama bincike za su neme su. Bayan sati uku sannan suka ce manyan su dawo.
Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne zai amso auran Amna, ya zama ko ina an ba shi. – Gininshi kuma ya kammala, amma fa asusun ya yi kat! Har sai da yayi aro gurin Babanshi. shi
Gida dai ba abin da yake jira sai masu gidan. Gurin tsara sadaki aka samu bambanci. Baban. shi shi ne zai ba da Nafisa, ya murza gashin baki ya ce dubu dari ne sadakin ‘yarsa. Baban Nafisa mai amsar ma Shatima aure ya ce “Haba Yaya, a dai rangwanta.”
Alhaji ya ce, “In suna so su bayar, ‘yarshi tana Www.bankinhausanovels.com.ng
da ilimi. Haka Baban Nafisa yayi masa transfer ta
dubu dari a nan take, abin gwanin sha’awa.Su ko gidan su Aliya hamsin suka saka mata, sai kudin gaisuwa ashirin, saba’in kenan. Amna kuwa dukiyar aure dari, sadaki kuma hamsin. Duk haka aka ba da, sannan aka tsaida lokacin aure wata sha biyu ishirin ga shi a lissafi sauran wata hudu kenan.
A son Shatima kar a kai wannan lokacin amma an duba lokacin da za’a samu hutu mai tsawo kowane bangare suna cikin kasa kuma suna cikin jihar.
Kamar yanda ya tsara a wata daya yake kai musu ziyara, ran Juma’a yaje gurin Nafisa. Sati Www.bankinhausanovels.com.ng
yaje gurin Aliya Lahadi kuma yaje gurin Amna. Haka duk karshen sati yake tura musu kati na dubu dai-dai. Haka kuma yake kiransu sau biyu a kwana goma, 
Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya
dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai
mata, dama oder take yi.
Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa lokaci.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]