[Advertisements⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 5 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya 

Tayi yar dariya tare da sake matse wayar a
kunncnta don dadin hira da shi. Ta ce Tun ranar
da na kira ka ka ce zaka kira ni in ka samu sukuni,
sai yau ka samu sukuni din?
Ya canza kunne da ya manna wayar zuwa
dayan kunnen don ya ji SOsai, saboda Amna bata
magana da karfi ko. kuma ba ta
son hayaniya. Wannan tsarin nata yana matukar
birge Shatima.
Ya ce, “Ba za ki gane ba, amma lokaci ya kusa
da zamu zama tare. Ta ce, “Wane lokaci kenan?

“Idan mun yi aure mana, kin san fa bana son a
dauki lokaci me yawa nan gaba.”
Ta ce, “Ban san ya zan ji ba in aka ce yau gashi na aure ka, ina tsananin sonka Shatima.” Sun jima suna hira kafin suka yi sallama da
alkawarin zai kira ta gobe kamar yanzun.
Lamo ya yi a kwance yana tunanin cikin su ukun nan bai fi son Amna ba kuwa? Wata zuciyar ta ce, ‘Ina ka bar Aliya mai hankali da sanin ya Www.bankinhausanovels.com.ng
kamata, ga kuma Nafisa itama ba baya ba…?” Da wadannan tunanikan bacci ya yi awon gaba da shi.

********

Tana tsaka da tuyar Awarar ta ga yara sun zagaye ta tana son ta sallame su gashi itacen duk danye ne, sai faman hayaki yake yi. Idanunta sun yi jajir, zuciyarta tana can gurin
Mahaifanta tana kokarin ta kammala tayi abinci ta
kai musu, sai taji Horn din mota a kanta.
Da sauri ta dago ta kalli motar, ranta ya dan sosu, don ita dai tasan ba a kan hanya take tuyarta ba bare ta ce, amma masu motar nan sun nufo ta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Tasan dai ba siyan Awara zasu yi ba tunda bata taba ganin wani mai mota ya tsaya da sunan siyan Awara ba.Yaran suka kauce motar ta tsaya daf da kaskonta. Cikin tsananin tsoro ta mike tsaye tayi baya. Motar taja baya taje gefe tayi parking, ita kuma cikin sauri taje tana tsame Awarar da ke cikin man don kar ta kone.
Tana ta sauri jikinta yana ɓari, tana yi tana kallon inda motar ta tsaya. Yaran da suka dare suka dawo don ta kunsa Awarar. Sai da ta zuba dayan a mai sannan ta shiga kunsa musu.
Tana sallamar su ana bude motar, ta tsura ma gurin ido gabanta yana wata irin faduwa. Sai kawai taga Alhajin nan. Ba ta san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba tare da hadiye miyau, sai ta ji ta dan samu nutsuwa.
Ta mike tsaye ta dan risina ta dafa gwiwarta alamun girmamawa ta ce, “Ina yini Alhaji?” Ya ce, “Ba sunana kenan ba, lafiya lau.” Ya kalli kayan “Dama nan ku ke?” Ta. ce, “Eh.” Ta nuna wani ribabban gidan sama na kasa, ginin tamkar ya zubo in ya ji kwakkwarar iska.
Ya kalli gidan na tsawon minti biyu, sannan ya dubi kayan suyar tata, sannan ya yi magana. “Salma me ki ke saidawa a nan?”
Itama ta kalli kayan sannan ta dube shi da ‘yar fara’a.
“Awara ce ni ke saidawa.”Ya ce, “Shi ne ki ke zama a nan gab da titi? Ba kya gudun mota ta kwace ta nufo kanki ta taka kamar yanda na kwatanta din nan?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta sake kallon gurin, kamar zata yi magana sai kuma ta fasa. Ya ce, “Nasan za ki ce ba ki hau titi ba, amma mota tana kwacewa, me zai sa ba za ki yi a cikin gida ba?”
Ta ce, “Ai in ana yi a cikin gida ba su sanin ana masu siyan, sai dai in je talla, kuma Innarmu da Babanmu basa son in je yawon talla.”
Ya ce, “Gaskiya ne. To ki dan kara ja baya kadan ko?” Ta ce, “To na gode.” Ya ce, “Ina zuwa nan unguwar layin can na sama shi ne gidan Kakana.”
Ta kai kallonta inda ya nuna. Ta ce, “Layin Shatima ko?” Ya ce, “Ai nan ne gidan Kakana.” Ta dan zaro ido “Laahh! Nasan gidan, muna zuwa ranar Juma’a karɓar sadakar waina, ko shinkafa da wake.”
Ya tsura mata ido, ta ce “Yanzun dai bana zuwa sai kannena.” Ya ce, “To ya jikin Babanku?”
Ta dan fadada fara’arta “Ya samu sauki, har ma yana tashi zaune tunda aka yi mishi gashin kashi sau biyu. Kuma naku mara lafiyar ya samu sauki?”Ya ce, “Ai mu ba a kwance ta ke ba, Maman abokina ce muna kai ta gashin Kashi ne.” Ta ce, “Allah Sarki! Allah Ya bata lafiya.”
Munnir ya leko, “Abokina zo mu tafi mana.” “To, Ya dubi Munnir, sannan ya dubeta. “Sai an jima, amma don Allah ki matsa a titin.” Ta ce, yanzun zan matsa.”
Tana tsaye suka ja motar suka wuce, sannan ta zo ta kara komawa baya da kayanta.
Shatima yana harba motar kan titi, Munnir ya kalle shi rai a hade.
“Wai me yasa ká ke son shiga harkar yarinyar nan ne? ka tsaya kana magana da ita kamar wata sa’ar yin zancenka.”
Ya kalli Munnir, “Laifi ne kenan don nayi mata
magana ta tashi a titi?” Munnir ya ja tsaki. “Mene
ne to na fada mata kana zuwa nan ga gidan
Kakanninka, ga waye-waye?”
Shatima ya yi murmushi, “Ni kaina ban san dalilin da yasa ni ke son shiga lamarin yarinyar ba, amma dai nasan ina tsananin jin tausayinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Aliya tana tsifar kai da yamma ranar Lahadi, misalin karfe hudu. So take yi taje wankin kai don rana irin ta yau ne take samu tayi abubuwan da ba ta samu tayi ba saboda aiki.Wayarta ta soma ringing, ta dauka ta kalli fuskar wayar, gabanta ya fadi don ganin (My love) da ta yi. Ta jima tana jiran wannan kiran amma dole ta hakura don tuntuni ta san halin Shatima, ba ya daga cikin maza masu nacin kiran wayar budurwa ko mai son da yake mata.
Ta daga tasa a kunne tayi sallama. Ya ce, “My love fatan kina lafiya?” Ta ce, “Lafiya lau, ina
fatan kai ma haka?” “Hakan ne. Zan shigo bayan sallar Isha’i mu gaisa koda minti goma ne.”
Ta ce, “Sai ka shigo, amma ina neman alfarmar
a kara min yawan mintuna.” Ya ce, “To zan duba in gani.
Kafin takwas na daren, Aliya ta sha wanka sai kamshi take yi, tana son in ya zo ta ce ya shigo ya gaida su Mamanta, don bata basu labarin shi ba kar su karya tata, tunda ko yaushe tsiya suke yi mata, wai ta tsaya jiran Shatiman da bata san duniyar da yake ba, bai ma san tana nan ba.
Kannenta biyu suka yi aure bayan tafiyar Shatima, don haka tana shan gori a dangi.
Lokacin da take shirinta, matar wanta da Mamansu sai zancenta suke wai wane ne kuma ya samu shiga haka? Ta lura amma sai ta share tamkar bata san suna yi ba, ta dai tsara zata basu mamaki ne. Wani yaro yayo sallama. ‘Yar Yayansu ta amsa. Ya ce, “Wai ana kiran Aliya in ji wani mutum a waje.”
Yarinyar ta ce, “Kai Anti Aliya ake cewa.” Mamanta da ke bakin kofarta tana jinsu ta ce, “Ke Yusra ko! In ke Antynki ce shi Antynshi ce? Kije ki kira ta.” Aliya tana jin su.
Yusra ta leka dakinta ta ce, “Anti wai ki zo in ji wani.” Ta ce, “Ki ce ina zuwa.” Ba ta tsaya ɓata lokaci ba tun da ta san cikin lokutanta ne zata bata. Yana jingine a gaban motarshi, ta zaci su biyu ne sai taga shi kadai ne. Ta jingina itama sannan ta
gaishe shi.
Fitilar kofar gidan ta haska su, don haka ta lura da kallon da yake mata, tunda ta fito.
Ya ce, “Kin ganni sai yau ko?” Ta ce, “Ai nasan kana cike da tarin ayyuka da uzurori, sannan dole in koyi hakuri tunda nasan bani kadai ba ce ina da kannai.”
Kalaman Aliya suka yi masa dadi, da alamu ita ce zata fahimce shi fiye da sauran, don ya lura Nafisa tana da kishi sosai. Ita ko Amna har zuwa yanzun shakkar fada mata yake, don baisan yanda za ta dauki abin ba.Yayi murmushi, “Tun-tuni shi yasa ni ke ganin ki daban a ‘cikin mata, haka ma sonki daban ne a zuciyata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta gyara tsayuwa, “Nima a gare ni daban ka ke
a cikin maza, don haka da ba ka nan duk namijin
da ya zo sai in ga tamkar mace ‘yar’uwata.”
Ya ce, “Na yarda da ke tunda ki ka jira ni. Ke na fara so, ke ce za ki zama uwargidana.” Ta ce, “Kana ganin zan girme su?” Ya ce, “Za ki girme su, amma Amna kila kuyi sa’a, ko ki fi ta kadan.”
Ta ce, “Kuma suma duk Sun san cewa a rana daya zamu yi aure?” Ya ce, “Nafisa ce ta sani, amma na lura ta damu. Ina ganin tana da kishi sosai. Aliya ta ce, “Sai lallashi tunda yarinya ce. To
ita fa dayar?” Ya ce “Ita kamma na kasa fada
mata, yanzun haka suna Umra da ‘yan gidansu, ina
son sai ta dawo zan je mata da žancen. Aliya ta sauke ajiyar zuciya, “Amma sai in ga da za ka dan tuntuba mata ko a waya, ba wai ka fito mata da zancen ba, ka nuna mata akwai fa wata muhimmiyar magana da za ku yi in ta dawo, kaga zata yi ta lissafin wace magana ce?
To in ka zo mata da zancen ba za ta ji komai
ba, don kila ta hasashi abin da yafi haka.”Ya ce”To zan gwada haka. Ya su Mama? Ya kamata in shiga in gaishe su ko?” Ta ce “To bari in fada musu.
Suna gama gaisawa da Maman su Aliya, Yayansu Aliyu yana shigowa, shi ne ma ya gane Shatima. Suka gaisa, da zai tafi ya aje musu dubu goma ya fito. Sun dan yi ‘yar hira sannan suka yi bankwana ya tafi.
Shatima da Mahaifinsa sun dawo daga sallar Juma’a, Mahaifin ya ce, “Mu wuce gidan su Hajiya in ba ka da wani uziri, don ban samu damar zuwa da safe ba.”
Shatima ya ce, “Babu uzuri Alhaji, ko ma akwai naka yana gaban nawa. Cikin jin dadi Alhaji ya ce, “Sai dai goron da na sai mata yana motata a gida.” Shatima ya ce, “Sai a sai mata wani yanzun da izinin Allah.”
Sun samu gidan cike da jikoki ‘ya’yan Marigayi babban wansu sun zo daga Kaduna su uku, biyun na gida. Sai kannan Nafisa Hamida da Momi, ga ‘ya’yan Anty Saude.
Shatima ya ce”Masha Allah, duk ‘yan hutun
satin ne haka fal a gida?” Ta ce, “Eh, ga su nan har gidan ya yi dadi, da ko shiru daga ni sai Maryama.”
Suka zauna suka gaisheta. Shatima ya bata goronta da Zuma. Ta dinga zuba musu godiya da sa albarka. Sannan ta ce, “Dama ina son ganinka, dazu da su Hannatu suka zo sai suke fada min wai saurayin Rahma zai zo gaishe ku gobe Asabar.”
Alhaji ya ce, “Allah Ya kai mu. A can Kaduna ta samu saurayin ita ‘Rahmar?” Ta ce, “Ban tambaye su ba, amma in ya zo ai ku za ku ji komai daga bakinsa.
Alhaji ya ce, “Haka ne.” Shatima ya ce, “Rahma ta gama karatun ke nan?” Kaka ta ce, “A’a, sauranta shekara daya. Ai yanzun in an samu miji ba a cewa sai an gama karatu, haka kuma tsakanin karami da babba ba a jira.
Ita Madina ai ta gama karatun yanzun bautar kasa ta ke. Da Allah zai kawo mijin ai sai duk a hada su.”
Alhaji ya ce, “Sosai kuwa. Yaran suka dinga zuwa suna gaida su Shatima. Www.bankinhausanovels.com.ng
Maryama ta kawo musu waina da miya, Shatima bai ci ba don yasan ‘yan aiki ne suka yi. Amma Alhaji da ya ke yana son waina ya ci kayansa.Suna ta hira har a ka zo kan batun auran Shatima. Kaka ta ce, “To kai yanzu gida daban daban za ka aje matan naka ko kuwa?”
Alhaji ya ce, “Yauwa, dama nayi wata shawara. Filayen da na raba musu shi da Mustapha da Badi’atu ya yi min ciko ya maido min da nashi sai in ba shi wani babban filina da ke Rigachikun, kawai ya yi ginin guri hudu shi da matansa kawai, ko ya ya ku ka gani?”
Kaka ta ce, “Amma kuwa kayi tunani mai kyau, ko ko kai ya ya ka gani Shatima?”
Shatima ya ce, “Ai ni Alhaji ka gama min komai, don ka ga na sami saukin zuwa Kaduna gurin aiki kullum, don da ina tunanin duk su zauna nan Zariya, ni kuma ina Kaduna sai su ke zuwa.”
Kaka ta ce, “Hakan shi ne daidai.” Ya ce, “Kaka a taya ni godiya gurin Alhaji, sannan a nema min alfarma, a rubuta takarda na yarda zan ba da cikon amma sai nan gaba, don kudin hannuna zan tada ginin da su.”
Ya ce, “Wannan hutun na karshen mako sai muje kaga gurin.” Ya ce, “Allah Ya kara girma da lafiya Alhaji, Allah Ya jikan Mahaifinku, ya raba ku lafiya da Kaka.” Suka ce “Amin.”
Nan suka ci gaba da tattauna al’amuran da suka shafe su.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]