[Advertisements⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI - Bankinhausanovels
Sat. Oct 1st, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RANA DAYA CHAPTER 10 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya.
Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance.
Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.”

Ta tsugunna ta gaida shi, ya amsa tare da fadin “Mike.” Ta mike tsaye tana wasa da gefen hijabinta. “Ya karin hakuri?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce, “Kin daina kuka ko?”
Ta ce, “Ai tun da ka hana ni ban kara ba.”
“Yauwa, ki dangana. Yanzu wace shawara ki ka yanke, ko in ee me ki ke so in yi miki?”
Ta kalle shi tayi dan guntun murmushi, sannan ta sunkuyar da kai. Ya ce, “Ki fada ni na baki zaɓi kuma na dauki alkawarin ko me ki ke so zan miki, ko nawa zan kashe. Gidanku kuma naso  ace zan gyara muku amma ina cikin shirin bikina.”
Tayi ‘yar dariya “Aure zaka yi?” Ya ce, “Aure zan yi, za ki zo min ko?” Ta ce “Zan zo.’ Daidai lokacin Bakaniken ya sauka a Mashin. Ya ce “Ina zuwa, bari muyi magana da Bakanike.”
Sun kusa minti takwas sannan ya bar shi yana duba motar ya dawo gurinta. Salma ta rasa yanda zata yi masa maganar. Ya ce, “To karatu ki ke so ne ki ka kasa fada?”


Ta ce, “Karatu naso Yaya, amma dai akwai burin mahaifina a kaina, kuma har a ranar da zai mutu sai da ya maimaita yana kuka…Hawaye suka soma zubo mata, tayi kokarin Isayar da kukan sannan ta ci gaba da magana cikin raunanniyar murya mai cike da tausayi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Naso in zama ‘yar Jarida a rayuwata, amma dole in shafe babin haka in yi aure kamar yanda Mahaifina ya bar wasiyya..”
“Aure!?” Shatima ya katse ta cikin mamaki.
Ta kalle shi fuskarta sharkaf da hawayè. “Aure Yaya.”
“To dama kina da saurayi kenan ko?” Ya tambaye ta.
“Akwai wani Basiru da yake sona.”
Kanshi ya sake kullewa, ‘yar yarinyar nan tana soyayya! Ya kalle ta. “Tun yaushe ku ka fara soyayya da shi?” Ta ce. “Zai kai wata biyu dai yana zuwa gurina, tun ina zuwa Makaranta ya taba cewa yana sona na ce mishi karatu zan yi.
Da na daina zuwa kuma sai ya dawo lokacin
Baba ya soma zancen aurar dani sai na hakura na saurare shi.
Ya ce, “To ke kina sonshi ne?” Ta ce, “Ni ban san wani so ba.” Tayi ‘yar dariya tare da rufe fuska. Ya ce, “Ban gane ba?” Ta ce, “Ni dai
kawai in aure shi amma Yaya wallahi ban san so ba.”
Ya ce “Misali ba ki tunanin shi? Ba ki son ganinshi da makamantansu?” Ta ce, “Yaya ni fa in ya zo yazo, in bai zo ba har mantawa ni ke Allah yayi ruwan tsirar shi.”
Shatima bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba, domin yanda ta fadi kalmar ta ba shi dariya sosai. Ya ce, “Har akwai wani ruwan tsirar mutum? Lallai Salma kin iya magana. To kin ga ba son wannan Basirun ki ke yi ba.”
Ta ce, “To ko bana son shi Yaya zan aure shi haka don in cika umarnin Mahaifina, kai sai ka yi min kayan daki ka aurar da ni kawai.”.
Yayi shiru yana kallonta. Itama ta kalle shi, sai taji kunya. Ta saka tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce, “Mamakin ki ni ke yi Salma, yanzu in aka yi miki aure kin san ya za ki zauna a gidan mijin?”
Ta kama gefen hijabinta ta rufe fuska, “Zan koya Yaya.” Ya ce, “Karatunki ya zama tarihi kenan yanzun?” Ta ce, “Ya zan yi, dole in hakura.”
“Sana’ar me shi saurayin naki yake yi?” “Gyaran famfo, da kuma Achaba.”Ya sake kallonta cikin tausayi. “In kin samu wanda zai ba ki dama kiyi karatu, kuma ya aure ki za ki bar Basiru?”
Ta ce, “Sosai ma. Ban san adadin farin cikin da zan yi ba.” Ta runtse ido “Allah Ka tabbatar min da haka.” Ta manta a gabanshi take, sai taji an ce “Ameen.”
Ta bude ido da sauri, tasa hijabi ta rufe fuska. Ya ce, “Kina amsa addu’a ba ki san Yaya mijin yake ba?” Ta ce, “Ai ko wane iri ne in dai Musulmi ne shi.” Ya ce, “To zan je in yi shawara da shi in zai yiwu zamu zo da shi.”
Bata ma lura da wani bakanike ya gama gyara har ya dana motar ya dawo ba, sai da taga ya tsallako ya ba shi makulli. Ya ce, “To zan tafi Salma, sai dai na zo.” Ta ce, “To me zan ce musu a gidan?”
Ya ce, “Ki ce zan canza miki wani miji wanda zai bar ki kiyi karatu har ki cika burinki.” Ta ce, “Na gode Yaya. Dazu naji ka ce zaka gyara mana, ai haya muke yi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haya? Wannan gidan ne ake haya?” Ya tambaya cikin mamaki. Ya kalli agogon hannunshi, “Bari in tafi zan zo.” Ta ce. “To sai anjima.” Tana tsaye har motarsh ta bace.Hajiya ta kira shi, yana dagawa ta ce Momiyo tana ta kiran ka ba ka daga ba.” Ya ce, “Ina tuki ne shi yasa, sai na isa Kaduna zan kira ta.” Ta ce, “To shi kenan bari in fada mata.”
Momiyo karamar kanwar su Hajiya ce. Ita ce kuma za tayo masa odar akwatunan lefe. Sai da ya isa sannan ya kirata.
“Anty Mamiyo kina ta kirana ina hanya, ka’idata in ina tuki kiran Alhaji ko na Hajiya kawai ni ke dagawa.” Tayi dariya, “Za ka fara daga na matanka kwanan nan.”
Ya ce, “Su a wa? Za dai su san ka’idata a kwanannan.” Ta ce,
“Maganar akwatuna ce zan tura maka online sai ka zaba, saboda gobe zan yi odar.” Ya ce, “Kowace a dauko mata kalar da tafi so.
Ta ce, “Wace kala ce suka fi so?” Ya cc, “Ita dai Amna tun muna Makaranta tana son Lemon green, Aliya kuma na san tana son ja, Nafisa ce dai bari in kirata yanzun, sai kuma daya yarinya
Kin san na samu ta hudu a kawo mata baby
pink.” Ta ce, “Bana son wasa.” Ya ce, “Antywallahi babu wasa. Ke ce ta farko da ki ka san zancan nan, Ta ce, “Ka san me ka ke yi kuwa?” Ya ce
“Don Allah Anty kiyi yanda na ce, kar ki manta
baby pink, bari in kira Nafisa din.”
Take ya kira Nafisa ya tambaye ta best color dinta ta ce purple Ya kira Anty Momiyo ya fada mata.
Salma tana shiga gida ta samu su Innarsu tamkar ita suke jira, ta fada musu komai yanda suka yi ita da Shatima. Su Yaya Hadiza sun hau murna.
Inna kuwa ta dira ta ce “Ba ta yarda ba, ko dai mutumin nan da biyu ya zo?” Salma ta ce, “Inna biyu kamar ya ya?” Inna ta ce, “To ni ban gane ba, daga taimako sai kuma ya ce zai samo mata miji?”
Yaya Hadiza ta ce, “Haba Inna, ki kyautata zatonki a kansa.” Auwal ya ce, “Inna jikan gidan Alhaji Shatima ne fa, sanannu ne
“Shi kenan, Allah dai ya zaba mana mafi alheri.” In ji Inna. Suka ce “Haka za ki fada Inna.” Momiyo ta daga wayarta ta kira Hajiya. Tana dauka ta ce, “Momiyo ki bari zai kira ki.” Ta cc, “Ai ya kira ni Hajiya, wai seti hudu za a kawo masa, wai ya samu ta hudun. Haka ne?”
Hajiya cikin daga murya ta ce, “Abin hauka ne za a ce ya samu ta hudu! Kila dai ita Amna. za a kai wa saiti biyu, tunda kin ga tuwon girma miyarsa nama, a ce komai daya za’ayi?”
Momiyo ta ce, “Ni fa ya nuna min da gaske yake amma dai kyaji in ya dawo daga bakinsa. Ai ni tunda a ka ce flat hudu ya gina na san da wata a kasa.”
Hajiya cikin damuwa ta ce, “To maji-magani.” Suka yi sallama.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

**

Biki saura kwana ashirin da tara, ko ina kansu ya dau zafi, gobe yake son yaje gidan su Aliya da Nafisa ya kai musu makullan gida, don kowa yaje ya ga gida. Haka kuma yana son ya kai musu Amna, amma abin da yafi daga masa hankali yanda zai ga ya shigar da lamarin Salma ga danginsa, dole ya je gurin Munnir yanzun don ya fara samun goyon bayansa. Suna cin abinci a falon Munnir yana gefen fada masa abin da ke tafe da shi. Munnir ya aje cokali, ya ce “Ka ga abokina fada min kawai abin da ka ke son fada min. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima ya ce, “Kai tsaye ina son yin ta hudu da yarinyar nan Salma wadda Mahaifinta ya rasu.
Da karfi Munnir ya ce, “Me ka ce?” Har sai da faisal danshi da ke bacci a kan kujerar da ke kusa da shi ya tsorata ya farka.
Munnir ya dauki yaron tare da kwalana uwarshi kira. Fatima zo ki dauki wannan.” Ta shigo ta amshe shi tana cewa “Ya tsorata ne?” Munnir ya ce, “Magana ce nayi me karfi, shi ne ya fırgita.’
Ta ce, “Kana tunanin mata ukun sun yi maka kadan ne da har sai ka kara da wannan ‘yar babyn da bata fi ka haife ta ba, da a ce kayi aure da wuri. Wai me ke damunka?”
Ya ce, “Lafiyata lau, kuma ba wai wadancan ba za su ishe ni ba ne, taimako zan yi ina jin Tausayin yarinyar.” Ya fada mishi duk yanda suka yi da ita.Munnir ya ce, “Ban ga wata matsala a cikin bukatar tata ba. Ka sai mata kayan daki ka aura mata wancan shi kenan.”
Shatima ya ce “To karatunta fa?” Munnir ya ce “Kayi magana da mijin ya barta kai ka dauki nauyin karatun nata, kaga shi kenan ka huta da wasu surutai da zasu taso daga danginka, da kuma matanka.”
Shatima ya ce, “Ban yi wannan tunanin ba, amma na riga da na fada mata cewa zan kawo mata miji wanda zai barta tayi karatu, kuma tayi
murna. Munnir ya ce, “Ka ce mata kai ne?” Shatima ya ce, “A’a.” Munnir ya ce, “To kawai ka dauko batun wancan ka cire kanka.”
Shatima yayi shiru tamkar mai nazari, har
Munnir ya soma zaton shawararshi ta shiga har yana cewa kayi nazari da kyau abokina.” Sai yaga Shatima ya bude ido sannan ya kalle shi, ba wai na gamsu da shawarar ka ba ne, ina tunanin yanda za ayi fadan karshe ne tsakanina da su Hajiya.
Don tabbatar da yarinyar nan tana cikin mata hudun nan da na gani a cikin baccina. Sai yanzu na luna ban fada maka ba, akwai wata a mafi Kankanta a cikin matan mafarkina, babu shakka
Salma ce Tsaki Munnir yaja sannan ya ce, “Allah Ya taimaka.” Shatima ya ce, “Dama haka ka ce, tun Www.bankinhausanovels.com.ng dazu da yanzun mun kusa gidan Kaka.”
Munnir cikin jin haushi ya ce, “Ni babu inda zan fita, bacci ma nike ji.” Shatima ya ce, “Gurin Kaka dole ka zo muje, In na samu goyon bayanta kowa dole ya lafa min.
Sai dai ina ji a jikina, ba za ta ba da hadin kai ba itama. Munnir ya ce, “Allah Ya sa kar ta amince.” Shatima ya mike.
“Don Allah tashi muje koda zugata kayi ka
ji?” Abokina haka sai ya gaji da matsin Shatima ya tashi suka fita.
Allah yasa bata kai ga shiga cikin daki ba, lokacin da suka yi sallama a falonta. Bayan sun gaisa Shattima ya shiga kame kame ya rasa ta inda zai bullo ma al’amarin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Kaka nasan dai muna tare ko me nazo da shi, ba za ki kware min baya ba.” Hajiya ta ce, “Kayi magana kai tsaye ni bacci nike ji in shiga ciki, don ka taki sa’a yau a nan nayi sallah.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]