[Advertisements⬇️]

MISBAH CHAPTER 2 BOOK 2 BY SA'ADATU WAZIRI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MISBAH CHAPTER 2 BOOK 2 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Bahijja da Mislihu aikinsu ba sana’ar su bane kadai, tamkar (passion) din dake ciki yana basu nutsuwa da farin ciki da kwanciyar hankali.
Hakika ba abinda ya fi taimakawa wanda suke bukatar taimako farin ciki, a duk lokacin da suka dafawa mai bukata suna tsintar kansu cikin tsananin farin ciki da nutsuwa.
Mislihu ya zama shi ne komai na Bahijja, haka itama. Suka gina rayuwar su da duniyar su

kan soyayya da kuma yarda tare da hakuri da
junada yafe laifin juna.
Bahijja mace ce abar so ga kowa, balle ga
mijinta. Mace ce da tasan hakkin mutane da basu
hakkin su, tare da tsananin kulawa da nuna
damuwa ga mijinta. Tasan yadda zata kula da
kanta da kuma mijinta da duk wanda yake tare
da ita ko yake karkashinta, don haka ma’aikatan
su ke matukar jin dadin aiki da ita.
Komai tsananin abu ta iya maida shi mai
sauki, mace ce mai so da kuma kokarin aika
gudunmawarta ga al’umma, a duk lokacin da ta
samu wata ‘yar dama komai kankantar ta tana
amfani da ita don tura sakonta ga al’umma a fili
ko a boye a zahiri ko a badini. A duk lokacin da
ta so tura sakon da bata so a santa ko a san ita ce,
to takan yi amfani da sunan (MISBAH), wato ta
hada sunanta da na mijinta, farkon sunansa da
farkon sunanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kansa Doctor Mislihu bai jima da gane
wacc ce MISBAH ba, saboda bata fada masa ba,
a fadinta ta ce bata yi don a santa ba, sai don
bukatarta ta biya, ta tura sakon da take son
turawa kuma ya isa. Wanda ladanta gun Allah
take so ba mutum ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Wannan halayyar nata shi kekarawa
mijinta sonta, yake gani kamar ba irinta a
duniya. Bahijja bai ce ta hada komai ba, dan
Adam take (She is not 100%) amma halayenta
masu kyau da niyyarta sun maida ta (100%) da
har ba a kula da sauran illolin nata.
Bahija (MISBAH) mace mai aiki da
niyya, mace mai akida da ka’ida, me yin abinda
ta ce da abinda tayi niyya. In tayi alkawari zata,
Cika, in kuwa tayi magana gaskiya ce zai fito
daga bakinta.
Bayan aikinta ba inda take samun matukar
nishadi da jin dadi kamar ta tsinci kanta a gaban
(computer) tana bincike ko ta fada duniyar
rubutu, tana aika sakon zuciyarta da iliminta da
iya fahimtar ta ga al’umma.
Tana kula da bangaren mata a asibitin su,
shi kuma bangaren maza. Suna kula da damuwar
juna da farin cikin juna, suna bawa juna lokaci
da kula, suna tsananin farin ciki a duniyar su.
Lokacin da ta cika shekara goma da aure Www.bankinhausanovels.com.ng
Allah Ya azurta su da haihuwar da namiji mai
kama da Bahijja, yayin da ya biyo mahaifinsa ta
hanyar halittar sa. Farin cikin su ya karu, suka
yiwa Allah godiya.
Bahijja ta rungumi danta da mijinta wanda
suke sune duniyarta da farin cikinta gaba daya.
Bahijja ta samu dukkan abinda take so, sai
dai ta inda tayi rashin sa’a ta bangaren dangin
mijinta, wani lokaci uwar mijinta da ‘yan uwansa
za suzo har gida su zageta su ci mutuncin ta
gaban ma’aikatan ta. Suna tunanin ta mallaki
Mislihu, gata tsintacciyar mage, bata da asali. Ba
irin cin mutuncin da ba sa mata, amma bata taba
nunawa Mislihu ba balle ta fada masa, har ya
gane da kansa, sai dai bai nuna mata ba tunda ya
lura bata so ya sani balle har ya nemi fada da
yan uwansa akanta. Don haka ya yi yadda take
so, bai musu maganar ba balle su samu rashin
fahimta.
Bayan son Bahijja yana mugun ganin
girmanta da darajarta, wani lokacin yakan rasa
me zai mata don ya nuna mata jin dadinsa da
farin cikinsa da soyayyar sa gareta, ko me ya
mata sai ya ga ya yi kadan, don haka yake rokon
Allah Ya bata farin ciki da kwanciyar hankali
duniya
daukaka darajarta a duniya da lahira, Allah Ya
bata Aljannah.
A halin yanzu Bahijja na hutu tunda ta
haihu ba ta koma aiki ba, saboda Mislihu ya
hanata, ya ce sai ta huta na tsawon shekara guda.
Bata musa masa ba, tayi yadda yake so.
Sai dai fa Bahijja Bahijja ce, bata san zaman
banza ba, don haka ta bawa jikinta hutu amma
abinda kwakwalwarta kullum tana cikin rubuce-
rubuce, daga na Turanci har Hausa, daga,,,,,,,,
. Allah Ya daukakata, da ilmin addini har na zamani.
Wani lokaci (poem) take rubutawa daga
na Hausa har na Turanci, wani lokaci kuma ta
zauna tana koyon abinda bata iya ba matsayinta
na mace, kamar girke-girke, iya kwalliya,
(dressing) da sauransu. Don Bahjja kam tana da
mugun raunı a wurin, wani lokaci takan fi sati
bata shafa ko da (powder) a fuskarta ba, balle jan baki
Wani lokaci Mislihu ke zama yana mata Www.bankinhausanovels.com.ng
kwalliyar, har gyaran gashi. Wani lokaci yakän
tsokane ta, ya ce sai ya auro wacce ta iya
kwalliya da gayu.
Takan yi murmushi ta ce, “Wa ya hana
ka? Ni duk abinda kake so ina maraba da shi”.
Yakan jawota jikinsa ya tallafi kanta, yace.
“Ga abinda nake so, wannan halayyar,
wannan (personality) din ba kwalliyar fuska ba.
Ina miki fata da addu’ar ki zauna a yadda kike
kar ki taba canjawa. Ina son wannan Bahijja
kullum kwanan duniya ina dada sonta”.
Takan rungume shi ta ce”Ina sonka
Mislihu, ka kasance dani har karshen rayuwata”.
Yakan amsa mata da, “Inshaa Allah”.
Asibitin su Bahijja Alh. Umar ya yanke
hukuncin kawo Deeni, saboda yadda ya bincika
yaga ingancin asibitin, da tasirin da yayi sosai a
cikin al’umma, da kyakkyawan shaidar da suka
samu.
Shi kanshi yadda ya ga tsarin asibitin da
ayyukan su sai ya ji sun burge shi, har ma ya
yiwa dansa Deeni sha’awar bude irinsa in Allah
Ya bashi lafiya.Kamar yadda suka yi alkawari, washegari Alh. Umar ya kawo wa Doctor Mislihu (report) din Deeni na duk wani asibiti da suka taba zuwa, daga gida Nigeria har na waje. A nan Doctor Mislihu ya bashi kwana uku cewa zai neme shi bayan ya karanta (report) dinsa.
Tunda ya karbi (report) din bai samu zama ya karanta ba, saboda ayyuka da suka masa yawa, kuma gashi kwana ukun da ya basu saura kwana daya, don haka ya yanke hukuncin dawo da su gida ya duba, duk da baya hada lokacin iyalinsa da na kowa don haka baya dauko aiki ya kawo shi gida, haka itama Misbah. Wannan dama ka’ida ne a  gida basu da lokacin komai sai na kansu, sai dai ko in baya gida ita takan yi wasu ayyukan, in ta gama da ayyukan gida. Lokaci na farko kenan da Doctor Mislihu ya taho da aiki gida.
Ya dawo gida a gajiye, Misbah tayi masa duk wani abinda ya kamata, suka yi hirar su irin na ma’aurata masu matukar son juna. a
Can ta jiyo Muhammad yana ta rigima hannun Baba Andi, hakan yasa ta fice
wurinsu, lokacin Doctor Mislihu ya samu damar dauko (report) din Deeni yana karantawa yana bin (history) na ciwon nasa da matsalar sa.
Ya yi nisa sosai wanda har Bahijja ta shigo kusan sau uku amma bai ji shigowarta ba, ita kanta tayi mamaki, abinda bai taba yi ba. Yawanci ma in yana da aiki yakan je (office) dinsa ya zauna koman dare, amma baya dawowa da shi.
Shigowar da ta sake yi na hudu ne ta samu bacci ya kwashe shi da takardun a gabansa. Murmushi tayi ganin yadda ya karya wuya kamar wani karamin yaro yana bacci.
Bayan ta kwantar da Muhammad a gadonsa tazo ta gyara masa kwanciya tare da lullube shi, nan kuwa taga ya kara gyara
kwanciya ya jawota jikinsa yana fadin. “Na gode Bahijja, Allah Ya miki Albarka”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi tayi ta kara manna shi a jikinta yadda zai ji dadin baccin, har itama baccin ya fara daukarta. Nan ta farka ta zame jikinta a hankali sannan ta tattara takardun tare da canja kaya ta sa na bacci, har zata kwanta sai kuma wannan (file) din yaja hankalinta, wanne irin muhimmanci yake da shi haka da yasa Doctor dawowa da shi gida?
Nan ta bude ta fara bi a hankali tana karantawa, kamar wasa kamar gaske ta tsunduma cikin karatun, tana kokarin fahimtar (case) dinsa.
Tuni taji zuciyarta ta karaya, ta tausaya duk da ba ainihin tarihinsa taji ba amma (report) dinsa ya nuna ya kamu da ciwon (emotional disorder) tabbas yana bukatar taimako, yana bukatar (couseling) musamman ta fuskar Addini. Sannan yana bukatar a nuna masa (reality) gaskiyar rayuwa ta sauya masa, saboda tsawon shekarun da ya dauka a cikin wannan yanayi amma ba canji, ya rayu cikin bakin ciki, bacin rai. Wanda wannan ba karamin ciwo bane kwarai.
Ta so tasa kanta cikin (case) din don jin me ya jawo masa wannan (emotional pains) din? Amma tayi shiru ta yarda da mijinta fiye da kowane likita, fiye da ita kanta, ta tabbatar zai taimaka masa. Nan ta tattara ta rufe ta ajiye (file) din gefe guda, yayin da ta kwanta da tunanin abin a ranta.  Washegari da safe bai fada mata ba ita kuma bata tambaye shi ba, ta tabbatar in yana bukatar taimakonta zai fada mata.
Kamar yadda suka yi alkawari a washegari ya nemę su wanda ya yi dai dai da kwanakin da ya basu, anan Doctor Mislihu ya basu wani (form) su cike, sannan wata takarda wadda take cike da sharuddan asibitin kafin su karbi mutum, da kuma in sun karbe shi. Idan sun amince da sharuddan su to su sa hannu su kawo shi, in kuma basu amince ba to kar ma su dawo.
da Tun a wurin Alh. Umar ya karanta duk da halayyar da Doctor Mislihu ya nuna musu ya yi kama da gadara, amma ba yadda ya iya sai ya bi dokar don ya lura ba maganar Alfarma wa kowa a bisa dokar su da ka’idar su. Bashi da zabi saboda yana da bukatar taimakon su, ya yarda da sahihancin su da gaskiyar su, haka akwai tsaro na sosai. Dole ya amince da dokar su.
Doka mafi tsauri a cikin dokokin su shi ne ba a dauke mara lafiya har sai in su suka sallame shi bayan ya warke, haka nan basu da wani sauran iko ko isa akan mara lafiyar da suka kawo, basu da ikon wani yanke hukunci akansa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Alh. Umar ya so yaja baya, sai dai a lokacin da ya rufe ido ya tuno halin da Deeni yake, sai yaji hankalin sa ya tashi, tsananin tausayinsa ya ratsa shi, soyayyar dansa da tausayinsa yasa shi zub da hawaye tare da dora laifin halin da dansa ya shiga akansa. Haka nan zuciyar sa ta amince da wannan asibitin, yana da tsammanin Deeni zai samu lafiya a wurin. Don haka wannan ya bashi karfin gwiwar sa hannu, . ya yi cike-ciken da duk ya kamata tare da karbar (slip) don biyan kudin jinyar Deeni. Sun rabu akan washegari za su kawo shi.
A hankali ya turo kofar dakin nasa tamkar mai jin tsoron kofar, zuciyar sa na tsinkewa saboda tunanin wane hali zai samu dan nasa? Tsawon sati guda kenan bai leka shi ba, saboda gudun wani hali zai same shi.
Kamar kullum ya same shi makure a lungu guda tamkar mai jin tsoron kar azo a kama shi, fuskar sa daure tamau ba alamar fara’a a tare

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]