[Advertisements⬇️]

MISBAH CHAPTER 16 BY SA'ADATU WAZIRI - Bankinhausanovels
Sun. Oct 2nd, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MISBAH CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A wannan sati biyu mama tayi dukkan iyawarta da dagewarta akan Shamsu da farida,taga sun saki jiki da juna ,da kokarin nuna musu su rungumi kaddara suyi ibadar aure,su manta komai. In sunyi haka tabbas basu yiwa Allah butulci ba ,kumansun yarda da kaddara kamar yadda ake so kowane musulmi na kwarai ya yi. In sun haka kuwa Allah zai sa albarka a rayuwar su,ya daga darajar su a duniya da lahira. 

       Da irin wannan maganganun na mama yasa suka saki zuciyar su,musamman ma dai farida ta riga ta saduda,ta daura damarar manta baya,ta kuma cusa soyayyar mijinta da Allah ya kaddara mata a zuciyar sa.

        A satin biyin ta koyi abubuwa da yawa ,don haka tayiwa mama godiya sosai,gami da mata alkawarin zama mace ta gari,saliha ga Shamsu,zata yi kokarin kawo farin ciki da kwanciyar hankali tare da nutsuwa a rayuwar Shamsu ,ta riga da ta amince,ta karbe shi matsayin mijinta. 

  Wannan magana tayiwa mama dadi matuka da zancen da farida ,tayi ta saka mata albarka.

Shamsu shima bai yi kasa agwiwa ba ya kara jaddadawa mama rikon da zai yiwa farida bisa gaskiya da amana da kuma soyayya.

   Mama tayi ta sa musu albarka ,ta raka su har mota tare da hadawa farida guzuri iri-iri.

  Farida taji kewar mama sosai ,saboda shakuwa da sukayi a yan wadannan kwanakin da sukayi tare.

   Kauna da soyayya tare da kulawa da shamsu ya dinga nunawa farida. Ya tabbatar mata da soyyayr ta na tare dashi ,don haka itama ta saki jikinta da shi,ta mika wuya gareshi. Da kanta ta kai kanta gare shi har dakinsa,mutuncin mama kadai da girmanta da take gani ya isa ya hanata cutar da shamsu.

   Ta lura yana sonta da bukatarta ,amma ya kau da kai,bai taba nuna mata hakan ba ,don haka da kanta ta yanke shawarar mika kanta da rayuwarta gaba daya ga mijinta. Bazata iya raba kanta da son Deeni ba ,amma zata iya raba kanta da tunaninsa ta cusa na mijinta a zuciyarta.

     Wanka tayi fes ta feshe jikinta da kamshi ,tare da saka sexy dress ,ita kanta ta yaba kanta,ta zurawa kanta ido a mudubi .

   ” Yau ce ranar da zan ci gaba da rayuwata,ranar da zan mallakawa wani kaina,zuciyata da gangar jikina,wani ba deeni ba. 

   Ina fata zaka yafe mun ,ka manta dani a rayuwarka Deeni,na yankewa kaina hukuncin rungumar aurena da mijina hannu bibbiyu don nemar yardar Allah.

       Da wannan tunanin ta nufi dakinsa,tayi sallama ,yana zaune bisa gado sanye da kayan bacci,hannunsa rike da ipad yana danne dannen sa alamar wani aiki na office yake yi.

     Sallamarta yasa shi daga kai yare da amsawa,ganinta a yanayin da bai zata ba yasa shi kasa karasa sallamar. Ya yi saurin kau da kai zuciyar sa na bugawa,tuni ya ji ya rude musamman da ya jita dab da shi.

Hannu tasa ta karbi ipad din ta ajiye a gefe ,ta dare bisa cinyarsa tare da jawo shi jikinta ta rungume shi . Nan ya bata hadin kai ,shima ya kara mannata a jikinshi sosai yana shakar kamshi tare sauke wani irin ajiyar zuciya yana jin tsananin son ta da sha’awarta suna shigar sa.

  Cikin muryar rada idon sa a rufe yana manne a jikinta yace…

  Farida kin amince dani,ba kya tunanin dee…..

    “” shhhhhh” 

Ta fadi gami da saurin rufe masa baki tace ,,

   Karkace komai,na mika rayuwata da kaina ga mijina wanda shamsu shine mijina,gaskiyar rayuwata. Ni matarka ce,kanada hakki da damar yin duk abinda kake son yi dani,buri na a yanzun kawai in kyautata maka . Ina neman yardarka ,saboda Allah ya yarda dani.

   Nan ya dunga sauke ajiyar zuciya ,shi kadai yasan me yakeji a zuciyar sa da jikinsa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

  Bai bata lokaci ba ya dada cusuwa a jikinta ,tuni suka manta komai suka fada wata duniya. Farida ta mallakawa mijinta shamsu kanta ,, yayin da shimanya mallaka kansa da komai nasa ,yana mai sa.mata albarka gami da alfahari da ita  Tuni suka rungumi auren su suka rike hannu bibbiyu,suna kula da juna tare da tarairayar juna,suka bude sabon shafi na rayuwar su,iyaye nasa musu albarka.

Ba wanda ya kai mama farin ciki da kuma fargaba ,a kullum Deeni ya yi waya sai shamsu da farida sun tsinci kansu cikin sabon  tashin hankali . Sai dai a kwana a tashi har sun saba da hakan ,don kuwa mahaifin deeni ya hana ko da wasa a fada masa gaskia ..

  Lokacin da karatu yayi wa deeni yawa ma yana dadewa bai yi wayar ba.mahaifinsa yana yawan ziyarar sa,yana ganin yadda ya cigaba sosai a karatunsa,ya yi nisa kuma yana kokari sosai ,ya kwantar da hankalinsa,,saboda ko da wasa bai san me ke faruwa ba. Kullum da burin auren farida yake kwana yake tashi……..

 Kwanci tashi ba wuya a gurin ubangiji,sai ga ciki ya bayyana jikin farida,iyaye da ‘yan uwa kowa ya yi murna musamman iyayensu maza da mta. Suna shan addua da albarka a kowanne kwanan duniya.

   Shamsu dai kamar zai cinye farida,da yanada iko da numfashi ma sai ya mata. Baya bari tayi komai , yana bata kulawa ta musamman tare da kokarin ganin kullum tana cikin farin ciki . Kullum ana kan binciken lafiyarta data baby.

      Tun daga wannan lokacin mama ta kara tsinkewa da al’amarin auren farida da shamsu,ta kara tabbatarwa aurensu wani hukunci ne na ubangiji,rabon shamsu ne a jikin farida bana Deeni ba,wani baya haifar dan wani,haka wani baya auren matar wani

       Nan ta kara dukufa da yiwa deeni addu’a. Allah ya bashi ikon hakuri da juriya,ya kuma kawo masa nasa rabon ta wani wurin.

     Farida ta haifo danta santalele namiji mai matukar kama da shamsu,tamkar an tsaga kara. Nan zuciya ta cika da murna ,iyayensu sunyi matukar murnar samun zuri’a da akayi tsakaninsu . Wannan ya kara karfin zumuncin su da kara tabbatarwa sun zama daya.

      Farida da baby sun sha kaya da gata kala-kala. Sun zama abin so a dangi,kowa son su yake da sha’awar su.

     Shamsu ya fadawa iyayensa cewa ya yiwa yaro huduba da sunan kaninsa deeni,wato NURADDEEN . Sun yi murna kwarai,musammaman mahaifin deeni da mama.

     Tabbas deeni ya cancanci haka daga gare su,saboda dukkan su masoyan Deeni ne,daga shamsu har farida,haka nan shi masoyin su ne.

   Alh Umar ne ya bugawa deeni waya ya yi masa albishir da zuwan baby da kuma takwara da aka masa ,wato mai suna da shamsu ya masa.

  Kwarai Deeni ya ji dadi yayi murna sosai har ya cewa babansa zai zo in sunyi hutu,sai dai mahaifin nasa ya taka masa birki,ya nuna masa zuwa gida zai mai da masa hannun agogo baya ,ya daure dai ya karasa,sauran sa shekara biyu ya gama ,in yaso zuwa ya sayo wa mai sunan sa duk irin abinda yakeso.

Ba don yaso ba haka ya hakura ,ta wani bangaren yana ganin gaskiyar mahaifinsa ne. Tabbas inya dawo gida yaga farida sake tafiya ya barta zai yi wuya,don haka hakurin dai shi yafi masa.

   Haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu,shamsu da farida da dansu Deeni karami,suna rayuwa tare da rainon dansu cikin so da kulawa da juna ,tare da kulawa da juna ,tare da mahaifansu,yayin da deeni ya dage ya ci gaba da karatun sa.

* *        * *       * *     * *       * *

Tunda ya sauka kasar sa nigeria yake cike da farin ciki da wani irin dokin zuwa ya ga yan uwansa,lumshe ido yayi yana shakar iskar kasar sa mai albarka,kasar mama da baba,kasar masoyiyar sa farida.

     Sanye yake da red t.shirt hade da blue jeans ,idanunsa boye cikin fararen glass ,ya yi wani irin haske da kyau ,saboda samun hutu da canjin yanayi da ya samu.fuskar sa kunshe da murmushi,kana ganinsa kaga wanda yake cike da farin ciki.

    Hayar taxi yayi a nan cikin airport din,ya sa kayansa a boot sai gida.

      A cikin taxi din Deeni yana ta sake sake tare da tunanin shin wa zai fara zuwa ya gani?masoyiyarsa farida ko kuma iyayensa ko yaya shamsu da matar sa? Yana son basu surprise ne shi yasa ko baba bai fadawa yana zuwa ba ,yafi so sai dai su ganshi kawai,mahaifinsa ya zata sai wani watan zai gama ya dawo.

    Ya yi murmushi,”Farida zata ganni bazata,zanga ni da ita wa zai fi farin ciki da ganin dan uwansa?

   Yana wannan sake saken har suka iso cikin unguwarsu,a nan ya tsaya yana tunanin ina zai fara shiga gidnsu ko na su farida ,ko kuma gidan ya shamsu…………..??

To masu karatu ku bawa deeni shawarar inda zai fara shiga……..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]